baza ko ina haka ma ƴan sanda suna ta bincike shiru wayarsa ce tayi ƙara ya ɗakko ya duba BRO ya gani da sauri ya ɗauka"Bros ina kiran wayar yallaɓiya amma bata shiga",runtse idon sa ya yi yana jin kamar zuciyarsa zata fashe da ƙyar yace masa"tun safe nima nake nemanta ban ganta ba",wani irin ihu ya masa a wayar saida ya janye ta daga kunnen sa jin ya lafa ya mayar sannan yana cewa"kamar ya ba a ganta ba kuma ba a faɗa min ba why Bros","munzo airport na barta naje karɓa ma ta tiket shine na dawo aka ce min wasu sun tafi da ita",daga can dafe kansa ya yi yama kasa magana sai kawai ya kashe wayar,a dai ranar ba wanda ya kwanta daga addu a sai kuka hankalin kowa ya tashi Aunty Hajara kuwa duk tsamar da muke saida hankalinta ya tashi dan kana kallon kowa na gidan saika tausaya masa gida tashi guda ya zama kamar na makoki tashin hankali ba babba ba yaro jaruman kaɗan ne dan Baffa ma ba a barsa a baya ba ya nuna mutuƙar damuwarsa kan ɓatan ƴarsa shugaban kuwa ai har yakai ga baya gane gabansa sai dai ya yi komai a hautsine mutanen nesa dana kusa kowa ya sa ni dan wasu ma suna gida.
*KENYA*
Wani irin sanyin a zaba ne ya ke shiga sassan jikina hakan yasa na buɗe ido a hankali cikin jin kan yamin nauyi bin inda nake da kallo nayi sai naga ɗaki ne tafkeke bakomai ciki sai katifar da nake kai da wata tabarma a gefe banda shi ba wani abu na ruwa,da dabara na tashi na zauna na dafe kaina,kamar amsawar flash naji komai yana dawo min kaina da sauri na diro a katifar ina waige waige can gefe naga ƙofa naje zan buɗe amma taƙi buɗuwa hasalima ko motsi batai ba duka na shiga yi amma shiru hannu na ɗora aka ina salati da ƙarfi"ya Allah waye ya kawo ni nan"juyawa kaina ya shiga yi na koma da baya na zauna jaɓar na rasa ma ina na kama ni na kasa kuka kuma ba wanda ya shigo,ban jima da zama a wurin ba sai gashi an buɗe ƙofar an shigo da sauri na kalli ƙofar wasu gandaƙa gandaƙan ma ta ne suka shigo su wajen shida sai daga bayansu wata mata ce baƙa mummuna sai dai da ganin tafiyar da take kasan wace ita wata kujera suka shigo da suka sa ma ta ta zauna tana wani harɗe wai saika rasa me yasa idan mutum yana jin wata isa bazai zauna normal ba sai an nuna maka ƙafa sannan za a zauna sosai,kallona tayi tana wani kafirin murmushi"ƴan mata sannun ki ko",sheƙeƙe na kalleta"yauwa uwar ƴan mata amma kan ki fara magana ya kamata kisan mutum ce ni ba dutse ko sai abani ruwa da abinci",jinjina tamin"weldon Baby haka nake son mutum tsayayye Sara a bata abinci"wadda aka wa maganar ce ta juya zata fita na dakatar da ita"bana cin abinci ba nama ba lemo",wannan matar ce tace a kawo mata nama flat uku da abinci",kai waccan ɗin ta ɗaga sannan ta fita ba jimawa ta dawo da ƙaton tire a gabana ta aje ta matsa buɗewa na shiga yi dariya iskanci bayi na ɗago kallesu"amma a kidnppers ɗin ma manyan masu hankali ne ku sannun ku da ƙoƙari Madam",ɗan murmushi tayi"ci muyi magana"kai na ɗaga na shiga bawa cikina haƙinsa har saida na gama sannan na ture"ohhhh Babban yayana ko yana ina yanzu ko wane tashin hankali yake ciki",na faɗa a fili kallona matar tayi tace"kenan aure gareki?"kallon sama da ƙasa na ma ta nace"au da baki sanni ba kinka ƙwamuso ni to kuma duk Allah ya turo a sace ku"zabura tayi zata mare ni amma ta fasa"tana cewa"au ashe fa nace ba duka a tsakani na dake amma zan aje ki anan harki mutu"dariya nayi"haba dai na mutu sai kace wata kaza","kina tan tama kenan?","eh Wallahi ni ki maida ni wurin mijina ko nawa ne zan baku ina da kuɗi"ƴar dariya sukai matar nan tace"da gaske kina da kuɗi har nawa","billion goma"wani kallo tai maza ta ɗago tana min dan batai tunanin jin haka daga gare ni ba taɗauka zan mata lisaafin yara na bankin kuɗin makaranta"da gaske ki ke?","to ku da mai ku ka ɗauken kawai ku faɗan wa ya ce ku kawo ni nan"ƴar dariya ta yi"wato kinga ina wasa da ke shine ki ke tambayata wa yace na kawo ki nan to ki daina wannan fatan mu zauna da ni dake a haka kan tazo"kai na ɗaga",ashe kema ƴar aiki ce ai na ɗauka kece shegiyar"zaro ido sukai suna mamakin yanda nake magana ba tsoro,tashi ta yi tsaye tana gewaye ɗakin"to kuwa ki ku ka da kanki dan wancan saita saita miki tunani","ba komai indai banda haƙƙi ai Allah zai saka min",kai kawai ta kaɗa ta sa kai ta fita waɗannan matan suka take ma ta baya a ka barni ni ɗaya.
Kwana na goma sha huɗu a wannan gidan ba mai dukana ko zagi wannan matar kuwa na maida ta kamar kakata itama har zuwa take wai na bata labari randa na bata labarin gidan mu saida tai ƙwalla ta dubeni tace"anya kuwa mutum ce ke yanzu nan har kishiya kin hana ta miki makirci","tabbas ma kuwa to kanwa na kasa da zan bari tamin hauka","haka ne kam ki shirya mai fushi dake gobe zata zo",ɗan jim nayi sannan nace"to wai ita uwar me ma na ma ta"kafaɗa matar ta ɗaga"nima ban sa ni ba","to shike nan saita zo",da yammar ranar ina zaune kewar gida duk ta dame ni naji an turo ƙofar an shigo waɗannan shirga shirgan matan ne sai kuma wata mata fara ƙal kyakykyawa tasa ado cikin wani arnen material an mai ɗin ƴan tasha kanta ba kitso ta saki gashin kuma kana ganin sa na gaske ne ba ƙari ba sauke idona nayi a kanta ina kallon wani wurin dan da alama wannan ba mutunci zatai ba kamar waccan dana raina,kujera aka sa ma ta ta zauna tana nunan ƙafa amma ko kallo bata ishe ni ba"sannu uwar son dangi",kallon mamaki na ma ta dan bangane nufinta ba"baki gane me magana ta ke nufi ba ko? to ni budurwar Habib ƙanin mijinki ce"dariya na kwashe ta ita ina nuna ta"to miye haɗina dake da ki ka sato ni kamar ƴarki?",kwaɗa min mari tayi saida naga taurari,da sauri na dafe fuskata"kin mari wuta muguwa"cike da mamaki take bina da kallo dan bata ga alamar zanji tsoron ta ba ita da take razana mutane"ƙara min wani marin tayi saida bakina ya fashe wannan matar da nake wasa da ita runtse ido ta yi kamar ita ake duka ƙafa tasa ta tankaɗa ni nai adungure a ƙasan tasa aka janyo ma ta ni gabanta haɓata ta kama ta jijjiga kaina"kin san kuwa dawa ki ke ja?",tofa ma ta yawu nayi"dawa zanja banda jahila jaka mai son maza",sakin haɓata tayi ta goge fuskarta sannan kwaɗa min mari a karo na uku matan nan ta kalla"ku zane min ita,da azamar kamar zasu ɗau buhu suka rufu a kaina da hanzari wannan matar ta tare su"ku bari",dakatawa sukai sannan ta kalli matar tace"Madam wannan fa yarinya ce bai kamata a ma ta wannan dukan ba",tashi tsaye matar tayi tana bin ta da kallo"da kyau Baira ashe harkin fara sanyi haka","ba haka bane wannan ɗince dai kar a daketa",hasala matar tayi ta kifa ma ta mari sannan ta dubesu tace"ku ja min ita zuwa mota zan ɗauketa daga nan dan naga ba zaki min abin da nake so kuma kin san sakamakon hakan ko,ta na gani aka jawoni ina kuka suna duka na da ƙafa har suka fito daga ginin gashi da tsawo ta saman ta leƙo taga sun sa ni a boot sannan ta shiga suma suka shiga tasu motar suka bar lungun,jungina da bango tayi tana jin wani ɗaci a zuciyarta kai ta kaɗa" muja dake Aisha".
*MAROCO*
Cikin wani katafaran gida tasa aka aje ma ta ni kwana goma suna min allurai sannan ba a bani abinci na zama kamar mahaukaciya,yau da wuri tazo inda nake ina zaune nayi jigum bana iya tunanin komai dan alluran amfanin su kenan a gaba ta tasa ni tana duka saida taga bana motsi sannan ta barni ruwan zafi tasa aka kwara min saboda tsabar azaba ko motsin zafin ma ban ba gashina ta danƙo ta ɗago kaina sama cikin idanuwa na ta kalla ta yi wata shegiyar dariya"haka nake so dama na maida ke mahaukaciya"murmushi na ma ta na kaɗa kai"cikin mamaki take kallona"kina nufin allurar da ake miki bata hanaki waɗannan mugayen tunanin naki ba",kai na kaɗa ban ma ta magana ba ta kuwa yankan mari a baki take bakina ya fashe jini ya shiga zuba ta watsar da ni gefe"ki tabbata a nan gidan zaki mutu waye ya gaya miki ana gasa dani waike me amana shine kika ba Habib dukiyar da ko ubana sai ya masa ladabi ko kin san kuwa yadda suke da Babana kamar wuta da ruwa suke naso Habib iya so amma ban san miye a tsakaninsu ba da Babana ba ya tsane shi ada shima yaso ni amma tunda ki ka shiga rayuwarsa a lokaci ɗaya ya juyan baya saboda munafurci harda shiga gaba ya auri yayarki ko ni banga abinda ki ke da shi ba da har mutane suke miki biyayya",katseta nayi"kinga ki kashe ni da wannan maganganun da ki ke dan ba ganewa nake ba",juyowa ta yi"au harma magana ki ke","to ke ki ka haliccen da za ki hanani magana",kaina ta ƙaraso zata daken"kina duka na yau zaki mutu"turus ta yi gabanta na mugun faɗuwa da ƙyar na tashi tsaye na tsaya a gaban ta inajin azaba a cikina ga yunwa ga ciwo amma na cije nace"Aisha ki ke kowa kina nufin ke ki ka sato ni ko to bari na faɗa miki wani abu ubanki ne yasa ki ki ka sato ni baki sa ni ba dan ya fiki matsala da ni kinga wannan gidan da yasa ki ka kawo ni to gida na ne shi yasan hakan kina tunanin ya baki bayanai ne akan nasa Habib ya auri ƴar uwata ina ba haka bane ya baki bayanai ne dan ki kawo masa ni cikin sauƙi dan shi sace ni zai masa wuya dan kamar ƙarfe nake bana lanƙwasuwa ni da kika ganni bana laushi sai dai na lausasa wasu,ke kima yi a hankali fa kamin masoyin naki yazo nema na tabbas ki ka bari yasan ke ki ka ɗauke masa matar wa saiya ya rabaki da numfashin ki",shiru ta yi kaf maganar tawa bata gane ba"ki daina dogon tunani ƙawata zaki mutu a banza a kaina,kije ga mahaifinki dan shirin kashe ki yake saboda ya dawo da dukiyar daya mallaka miki gunsa dan yanzu yasan ke ba ƴarsa bace uwarki siyo ki tayi kuma itama ɗin shi ya kashe ta hunmm baki san waye wannan mugun mutumin ba ko to yana daga cikin tarko na nan da ki ka ga ya dawo da zama kin ɗauka kamar da ne kasuwanci ya kawo shi ha ha ha yarinya gudowa ya yi dan yana gudun haɗuwa da ni saboda nasan sirrin sa dukkan rayuwar sa atafin hannuna take"shiru nayi na kama kaina da hannu biyu na jijjiga dan ina jin kamar zan suma ƙara dubanta nayi"kije ki samawa kanki mafita kan ya sheƙe ki",a fusace ta danƙi wuyana ta jijjiga ni ta watsar jakarta ta fin ciko zaro wata kwalba ta matse ni ta ɗuran abin ciki sannan ta fita da gudu masu ma ta gadi na ne sukayo kaina zasu danƙeni ba zato sukaji saukar duka aka,jin sun faɗi yasa na jiyo wannan matar ce da gudu tazo ta kamani ta rungume ni"sannu sannu zo mu gudu"ganin bazan iya tafiya ba ma saita goya ni muka fito a gidan duk masu gadin gasu nan a kwance kashir ɓan.
Ko da ta isa gidan bata kula kowa ba ta wuce ciki Daddyn ta na zaune da wasu mutane ta shigo kusa da shi ta zauna tana shagwaɓa"yadai ƴata","Daddy nagaji ne","ok jeki huta zuwa anjima zamu unguwa","tom Daddy",ta tashi ta haye sama bata shiga ba ɗakin saita wayance ta sakko zuwa kitchen anan ta laɓe dai dai yana cewa mutanen"ita ce wannan zan kawo muku ita anjiman yanzu ku tafi ita akwaita da bincike yarinyar da nace muku nasa ta sato tana wajenta so nake na gama da ita wannan sannan waccan dan nasa tai ma ta allurori na fitar da mutum a tunanin sa",dafe kanta ta yi saida mutanen suka fita sannan ta fito ta haɗo abincin yara dan ita bata cin abinci kowane lokaci,a ɗakinta ta zauna duk a tsorace tana jin Daddyn shima ya fita aje abin hannun ta tayi ta jawo manyan jakun kuna ta kwashe kayanta da duk kayan amfanin ta ta jidi kayan takai mota da masu gadi suka tambayeta saita ce na ƙawarta ne zatai aure yau shine zata kai ma ta yanzu ma zata ta shirya,komawa ta yi ciki ta sauya kaya zuwa na party tayi kwalliya sannan ta fito zuwa ɗakin Daddyn dama tasan taya ake buɗe passwod ɗin ƙofar ta buɗe ta shiga safe ɗin ma tasan ya ake buɗewa dan haka ta buɗe duk takardun kadarar sa dana kuɗin banki da kuɗi billions tasa wata trolly ƙarama kamar ta ta ce ta amfanin wajen biki ta yashe kuɗin tas sannan ta rubuta masa gajeriyar wasiƙa kan ɗan table da yake ajiyar jaridu ta fito tana tafiya ƙwas ƙwas nan da nan kuwa taja hankalin mutanen sukaita kallonta taja mota ta fita agidan tana hawa titi ta fara yanka gudu gidan da ta aje ni tazo taga wayam dama saki na tazo tayi kuji muguwa ko in ta saken gidan uwarta zani,tana ganin bana nan ta fito ta gudu itama ba tayi tunanin komai ba ta auna kayanta a jirgi sannan itama ta auna kanta China wurin ƙwayenta.
*******
Koda ta ɗakko ni dama da pravet jet tazo dan haka daga nan sai 9ja tasa aka wuce ita direct,mota tasa wata abokiyar sirrin ta ta kawo ma ta airport ɗin bata san ina zata kaini ba kawai ta shiga wata unguwa dare ya yi sosai ƙofar wani gida ta shinfiɗa gyalenta ta kwantar da ni a wurin ta tafi tana waige na sha biyu da mintuna ɗan gidan ya dawo daga gantali da yake a mota yake horn ya yi aka buɗe masa ya danno haske zai murza taya ya murje ni maigadi ya lura da ni da hanzari ya shiga gabansa taka burki ya yi shi kuma maigadin ya yi kaina,buɗewa ya yi ya fito yana masifa amma sai ya yi shiru"kai Baba megadi miye wannan ka ke ɗauka","mutum ce aka yar yallaɓai","mutum to shine zaka ɗauka shin kasan illar hakan","ba wa ta illa saita mutu in aka barta a haka yallaɓai ka kaita asibiti",baya yaja yana dafe ƙirji"ni ɗin wallahi ban kaita",ya matsa gefe,mai adaidaisahun gidan ne ya dawo ganin mota a hanyar ya fito yana tambayar lafiya,Baba maigadi ne yace"yauwa Habu taimaka min wannan yarinyar a cikin mawuyacin hali take yarda ita akai anan kai da ganin yanda take a wurin kasan kwantar ta akai"da sauri ya ƙaraso ya taimaka masa aka sa ni a mashin ɗin megadin ya shiga suka bar ɗan masu kuɗi anan,asbitin wani ƙaramin pravet yaje maigadin yace"na gwamnati zaka kaimu nan wazai biya",kashe mashin ɗin ya yi ya fito"karka damu Baba yanzu muna zuwa na gwammati sai an ce mu kawo ƴan sanda anan kuwa muna cewa ƙanwata ce shikenan","to ɗan nan ai bamu da kuɗi","ka daina damuwa Baba akwai cinikin yau a hannuna muje",ɗakko ni ya yi ya shiga illai kuwa da saurin su suka karɓe ni suka shiga ciki bayan mintuna suka fito likitan yace"akwai babbar matsala ku ƴan uwanta ne"kai mai mashin ɗin ya kaɗa likitan yace"kuna ina ƙaramar yarinya take allurar cocain anya kuwa anan ƙasar take ga yunwa ta taɓa ma ta hanji gaskiya a aikinta ana buƙatar kuɗi masu yawa dan haka yanzu kaje ka kawo dubu ɗari takwas a fara da cikinta kafin ƙwaƙwalwarta kayi hanzari nan da zuwa shaɗayan rana"kai ya kaɗa yana jin kamar zai faɗi a ina zai samo waɗannan kuɗaɗe haka masu yawan gaske,bayan wucewar likitan ya kalli matashin ya ce"Habu kaga irinta ko dama nasan hakan ce zata kasance su waɗannan kuɗi kawai suka sa ni",dafa shi ya yi"karka damu Baba muje waje",suna fitowa ya ce masa zai maida gida kamin goben sanda ya kawo shi Alhaji harya faɗa nan suka bashi haƙuri ya aje mashin ɗin da sassafe ya dawo ya ɗauka yaje asibitin likitan na ganin sa ya ce yafa dage ya kawo kuɗin tom ya ce ya fito ya fara aikin sa yana zaga gari wajen tara Habu yaje ya saida sabon mashin ɗin mutane da yake ba a daɗe da siyan shi ba kuma ga takardu har ƙari ma ya samu kan ɗari takwas ɗin da saurin sa ya kawo ya biya akace ya zauna anan ya wuni sannan likitan ya fito sukaje office nan ya bashi takar dar allura yace"duk ɗaya dubu goma ta kwana goma sannan a duba ƙwaƙwalwar ta ta",tom ya ce ya karɓa ya biya rabi sannan kuɗin gado ya tashi bako ƙwandala dan komai ya ƙare bai koma gida ba tun daga wannan ranar har bayan kwana biyar Alhajin nan kan kuɗi ko kayansa bashi da mutunci dan haka yaje har gida yacima iyayen Habu mutunci basu damu ba dan suna san waye ɗansu kuma dai suma ai basu ga dawowarsa duk da yadda duniya ta zama sunsan duk inda yake yana lafiya kuma suna masa addu a,ranar kwana na shida ya fita wurin abokinsa ya ranto dubu ashirin yana hanyar dawowa Alhaji ya gansa nan ya fito yasa aka kama masa yana ihu wai ɓarawo ne anan wasu ma suka kwashe kuɗin sannan yasa aka mai duka ya kira ƴan sanda suka kamashi ba imani suma sukaita dukan shi wai ina yakai mashin ɗin shiru ya yi musu ai kuwa sukaita laftarsa bisa ga umarnin Alhajin.
*NIGER*
A yanda ya shigo gidan ne ya bata tsoro kuma bai ma ta magana ba ya wuce ciki bin bayansa ta yi"lafiya kuwa Habib naga kana haɗa kaya","kema haɗa naki in ba haka ba na tafi na barki",da sauri ta shiga itama taja jaka ta fara zuba nata kayan batare da ta tambaye shi ina zasu ba tasan halinsa in ya tutse ba daɗin sha'ani gareshi ba,a tare suka zuge jaka ya jayo hijabin da take sallah ya ba ta sannan ya ɗauki jakunkunan ita kuma ta biyo bayan shi falon ya tsaya ya kashe komai sannan suka fito driver ne ya kaisu airport sai anan tasan ina zasu suna samun zama a kujera tace"me ya ke faruwa ne a gidan",batare da ya kalleta ba yace"Nana aka ɗauke",wani dam taji sai kuma abin ya ma ta ban barakwai"sata kamar ya saika ce wata jaka","yanda dai na faɗa mikin ne hakan tun safe kumankowa na inda take ya tabbatar sace ta akai",bai gama magana ba ta fashe da dariya,da mamaki yake kallon ta"kanki ɗaya mutum fa nace miki an sace kuma ma ƴar uwar ki amma shi ne ki ke dariya","wallahi ba dariyar murna nake ba kawai wanda ya jajibeta ne yake bani tausayi Nana bala i ce kuma bata da tsoro amma zasu ci ubansu dan zata wahalar dasu","ɗan murmushi ya yi"wato dai kema kinyi irin tunanina dan tabbas ba masu satar mutane ne suka sace ta ba","haka ne kam akwai dai wa ta a ƙasa","to Khadija sai muyi ma ta addu a","to shike nan amma harna tausaya musu wallahi"ta ƙara fashewa da dariya shi dai sai kai ya girgiza.
Ba bu wanda yasan zasu zo shi yasa a dole suka hau taxi ta kawo gida anyi mamakin ganin su dan dare ya yi a wannan yanayi dai suka kwana amma Hajara ko inda yaje bataje ba dan tabbas ta tsorata da shi a kan Nana,duk ake bincike sun zaga amma ba labari sai dare Alhaji Baffa yace su dawo kawai ayi addu a duk inda take zata fito a dole suka dawo amma Babban Yaya yama rasa ina ya kama gani yake abin kamar almara,kwata kwata baya bacci kullum yana gaban ubangiji yana kai kukansa gare sa,Hajara ta yi iya binciken ta akan ta gano ko Abban ta ne amma bashi ba ne shi yasa take a tsorace gashi baya ma ta magana an yace duk ita ta jawo,da wannan abin ya fara nisa amma shiru ga bincike dai ana yi kuma Habib bai koma ba.
****
Da iyayen Habu suka zo suka ga halin da ya ke ciki hankalin su ya yi masifar tashi Baban sa dai yasan ɗansa mutumin kirki ne nan ya lallaɓashi ya faɗa masa me ya yi da kuɗin daya siyar da mashin ɗin mutane faɗa masa komai ya yi nan Baban ya tausaya masa kuma yace insha Allahu zai biya masu mashin ɗinsu yanzu zaije ƙauye ya saida gona kin sa yazo biyasu,saida zasu tafi sannan mamar tace"a ina aka kwantar da yarinyar",kwatan ta ma ta ya yi sannan suka tafi suna gida Baban ya tafi ƙauyen su ita kuma ta tafi asibitin bata sha wuyar nema aka nuna ma ta faɗa likitan ya shiga yi nan taita bashi haƙuri har ɗakin nake ta shigo ina kwance ido na biyu amma bana gane kowa bin ta da kallo nayi kawai likitan ne yace ma ta bata gane kowa amma ina saran in an aka gama ma ta allurorin zata iya dawowa hayyacinta,ta tausaya min sosai nan ta falwa likitan da zarar mijinta ya dawo za a ƙarasa biyan komai kwanan Baban biyu ya dawo amma kuɗin mashin basu kai ba saboda zalinci kuma wai kuɗin aikin da ya yi da yake basu sunce ladan amanar su da ya ci duk kuɗin da Baban Habu ya basu,basu sa an sake shi ba saboda wulaƙanci ce masa ma sukai in bai ciko ba zaisa a saida gidansa ya ɗauki kuɗin sa Baban baice komai ba ya fita ya basu wuri,asibitin shima yazo sauran abin da ya ɓoye ya biya a asibitin,bayan kwana goma ta cika binciken su ya nuna musu sai dai akai ni waje amma in basu da hali to su cigaba da zama da ni a haka har Allah yasa na warke,hakan kuwa akai likitan ya sallame ni suka zo da ni gidan su ya yinda Habu yana can ana bashi wahala a haka har nai sati uku hannun su na shaƙu da Baba da Umma suna sona sosai.
******
Yau Babban Yaya ya karɓi baƙo Abdallah ya janjanta masa sosai sannan ya jashi shida Habib zuwa wurin ƴan sanda daya sa ni bayan sun fito suka sami Baba da wani ɗan sanda sai faɗa baban yake ya zasuna dukar masa ɗa haka ɗan sandan sai nuna shi yake da hannu anan Acp Zubair ya daka masa tsawa"ya zaka na yiwa babba haka baka da hankali ne",ƙamewa ya yi ya sara"sorry sir",juyawa ya yi ga Baban ya ce"kayi haƙuri Baba me ya faru ne","rankai daɗe ɗana aka kama wajen sati shida kenan wata matsala ce ta faru da ƙanwarsa ban sa ni ba ma yaje ya saida adaidaita sahun mutane ya biya kuɗin asibiti yaron nan shekara wajen huɗu yanawa mutanen nan aiki suna ƙarar masa da ƙarfinsa ya yi karatu sosai suna da yadda zasu nema masa aiki amma sunƙi shine yau daga wannan kiskuren suka tozar ta shi haka kullum duka kamar wanda ya yi kisa",kai Asp ya kaɗa"kayi haƙuri Baba muje na ganshi abokaina muje tare mana kuga ciki",tare suka shiga sunsha mamakin yadda masu lefi suke
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 32