ya kaimu goben suna jiran zuwansa,bai nemi Hajara ba sai washegari yaje amma bai faɗa ma ta komaiba dan ba yanzu ya kamata tana sanin irin wannan ba sannan ya faɗa ma ta Kakansa na nan zuwa asatin ayi maganar aurensu ba kunya tashiga murna a gabansa wai ta matsu ma ta gama karatun ayi aurensu susha soyayya shi dai da ido ya shiga bin ta yana mamakin ita ƴar kunyar nan ma ta ƴan mata bata da ita kodan suna gidan masu kuɗi ne.
Vote
Share &
Comments
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
chapter 1️⃣2️⃣
A ranar da yamma misalin biyar drivern da ya kawo Babban Yaya waccan ranar yawa Alahji jagora har ƙofar gidan mamaki da ganin motocin shi ya shiga yawo a zukatan ƴan layin babu jimawa da tsaiwar su ya fito a gidan zuwa wajen motocin Alhajin ne ya fito a motar yana kallon layin sannan ya kallesa"Habib na ɗauka Nana zaka turo min ta tareni","afuwa Abba bansan kafi son haka ba dana turo ta amma bismillah" nan ya masa jagora zuwa cikin gidan Alhaji Baffa cikin karramawa da mutuntawa Alhaji Baffa ya fito yana masa sannu da zuwa cak maganar tasa ta maƙale"HABIBU KAINE DA GASKE"kallon kallo aka shiga yi wai da wane Habibun yake ne,ganin basu fahimcesa ba yasa ya fara kiran Iyyo"A'i Ai fito ga Habibunki abokin Aminun ki",kamar zata kifa ta fito a ɗaki"yana ina Alhaji"turus tayi a wurin "Habibu Allah mai iko kai Habibu a ina kasamo wannan mutumin",ta faɗa tana nuna Babban yaya,saƙare ya yi yana binsu da kallo"Iyyo nifa ban gane ba shima sunansa Habibu ne a ina kuka sanshi?",dubansa Alhaji Baffa ya yi"jeka zo da Ummanku da Halima babba",juyawa ya yi ya fita ya rasa ma wane tunani zaiyi saida ya taho da Umma sannan suka shigo suka tasa Mama a gaba ta ƙofar da aka tsaga wa su Iyyo ta gidan suka shiga,Alhaji da ya yi saƙare kansa na bugawa kallonsu yake yi yana ganin tamkar yasan fuskokin nan amma ya manta inda yasan su,Alhaji Baffa ganin bai gane su ba yasa yace"mu shiga daga ciki mana,ko kuma A'i sa shimfiɗa nan baranda cikin zafi su sun saba da ac",dariya tayi ta ɗakko tabarma da ƙatuwar darduma ta shimfiɗa a barandar suka zauna,tunda suka doso wajen Umma da Mama suka cika da mamaki ganin fuskar da bazasu taɓa mancewa da ita ba a rayuwar su,Mama harda Saurinta gun ƙarasowa wajen"YAYA HABIBU"ɗagowa ya yi ya kalleta"wallahi Yayana ne wannan Sa'adatu kalleshi da kyau",Umma kuwa kasa magana tayi da ƙyar tace"dama kana nan bawan Allah",saƙare Alhaji da Habib sukai suna binsu da kallo,Alhaji Baffa ne ya kalli Habib"jeka zo min da Nuhu da Liman ma za yanzu ana ƙara lokaci za'a samu matsala sauri",da saurin ya fita sukai kiciɓis da Kawun a waje"yauwa kawu kazo inji Alhaji bari na kira liman",baiji me zaice masa ba ya wuce a masallaci ya samesa ya isar da saƙon Alhaji Baffa atare suka taho cikin gidan,Alhaji Baffa ne ya kalli Liman yace"Liman ga mutumin da nake ta baka labarin nan yau sanadi ya kawo shi gida amma da alama abin yana nan bai baje ba dan bai gane mu ba",gyara tsaiwa Liman ya yi"Allahu akbar Alhaji yanzu shine wannan haka cikakken babban mutum amma gaskiya an ƙwareshi an cutar da rayuwarsa ace mutum irin wanan baisan kowa nasa ba bakomai zamu warware koma miye kai Nuhu fara karatu Habib a ina za'a samu zuma","akwai wurina"Iyyo ta faɗa,tana tashi taje ta kawo masa,karɓa ya yi yace abashi faranti nan ya juyeta ya fara karatu a fili haka ma Kawu Nuhu cikin ƙanƙanin lokaci kamar mazari jikin Alhaji ya fara rawa kar kar hannunsa Alhaji Baffa ya riƙe ana cigaba da karatun wani sautin ihu ne ya fita daga jikinsa kamar turiri sannan ya yi baya ya kwanta,zumar Liman ya ɗiba ya cire hular kansa ya shafa masa akan take ya fara wani ihu yana magana"zan fita zan fita malam","waye kai me ka ke ajikinsa shekara da shekaru saboda tsabar rashin imani ko da yake nasan ƙaton kafiri ne kai shi yasa ka aikata hakan","wallahi malam zan faɗa wancan ya daina ƙonani","kai Nuhu cigaba","wallahi zan faɗa zan faɗa","muna jinka Alhaji Baffa ya faɗa"wani ɗan ƙara ya yi sannan ya fara magana bama da kalar muryar Alhajin ba"ni sunana Oju kafiri ne ni wannan aikin wani bokan kan dutse ne yasani,kuma shima wata mata ce tasa shi an haɗani dashi ne dan na shiga jikinsa da sunan kurciya shine na ɓatar dashi amma na kasa hanashi ya yi kasuwanci duk garin dana kaishi farin jini yake hannun ƴan kasuwa yanzunma bansan ya akai ya haɗu da ɗansa ba kuma dama makarin abin shine ya yi magana ko a rashin sa ni ne da ɗansa tofa asiri zai tuno sai gashi lokacin ya yi ashe",liman ne ya katse shi"ka kyauta ai ka cutar da mutum na shekara talatin da biyu zakaiwa Allah bayani yanzu ka faɗi mana waye yasa amai aikin kurciyar",tunkan ya gama maganar ya fara bashi amsa"kishiyar Babar abokinsa Aminu"salati Iyyo tasa tana juya kai,liman ne ya ƙara magana"to mun jika yanzu zaka fita ko mu babbake ka","zan fita mana aiko baku cireni ba ruhin ɗansa bazai barni na zauna lafiya ba","to fita yanzu kuma karka cutar dashi kar ka ƙara dawowa wannan ahalin kuma wancan ahalin nasa karya manta su","bazan ƙaraba suma bazai manta ba",wani baƙin hayaƙi ne ta baki ta hanci ya fara fita na ƴan mintuna yana gama fita Alhaji ya fara tari ruwa aka kawo aka bashi sannan Habib da yay saƙare ya taso yana goge mai zumar kansa,yana cikin shan ruwan kamar wanda ya tuna wani abu ya janye kofin bakinsa yana kallon su Alhaji Baffa"Baffa kaine anan"kallon mutanen wajen ya shiga yi"Halima Sa'adatu Nuhu",duk amsawa sukai,ai sai ya zabura"Baffa ina Aminu da Haruna",Iyyo ce ta fashe da kuka"Habibu !Aminu ya rasu shekara goma sha uku kenan yanzu kasan ka dawo hayyacinka",fashewa ya yi da kuka sosai ya koma ya zauna sai juya kai yake"nasani Iyyo nasan na dawo hayyacina yanzu abokina ɗan uwana ya tafi ya barni ashe ba rabon mu gana"kallon Habib ya yi"dama kai ɗan wannan a halin ne ashe shi yasa naji a jikina duk duniya kai ɗana ne ashe banyi kuskure ba",Alhaji Baffa ne yace"wannan ba ɗan Aminu bane ɗanka ne shima sunan sa Habibu",ba Babban Yaya ba Alhajin ma ya fishi ruɗewa,da ƙyar Babban Yaya ya haɗa kalaman bakinsa yace"bangane ba Alhaji Baffa shine kuma Babana to margayi fa","wannan batu ne mai tsawo Habibu ya kamata ayi shi agaban iyalansa wato matansa",cikin sanyin jiki ya dube su"Baffa za'a zo dasu yanzu",wayarsa ya ɗauka ya kira Hajiya Fulera jin muryarsa cikin sanyi yasa ta faɗin"lafiya Alhaji","ki faɗawa sauran ƴan uwanki da yara kaf ku fito yanzu za'a zo ɗaukarku akawo ku inda nake","kamar ya Alhaji meke faruwa ne","ina gidanmu ne nima naga iyayena da ƴan uwana dana faɗa miki ina nema","ka warke ne Alhaji","sosai ma kuwa na koma kamar da sanda baku sanni ba kawai ku fito","to Alhaji",yana kashewa ya kira waɗanda ya bari a waje ya basu Umarnin suje su ɗakko su hajiya acan gida su kawo su nan suma,kowa jigum ya yi abin kamar almara.
Baƙaramin tashin hankali Hajiya Fulera ta shiga ƴan uwa kuma da dangi ita da take ƙara assasa abin dan kar ya gane kowa nasa hatr ya bar duniya'kunji kamar tasan shi zai fara mutuwa ko tasan gawar fari tsakaninsu dan hauka',wata number ta kira da wayarta tayi magana cikin wani yare na ƴan mintuna sannan ta kasheda ƙyar ta lallami kanta ta tura yaranta suka kai saƙon ga sauran matan sannan suka fito aka kwaso sunsha mamaki ganin unguwar da aka kawo su har ƙofar gidan aka buɗe musu mota suka firfito yaran sai tsalle suke nan aka nuna musu gidan suka shiga da sallama,wato kana ganin su kaga matan mai kuɗi saboda kalar fatarsu ma ta musamman ce,sannu da zuwa su Mama ke musu fuska sake suke amsawa dama an ƙara shimfiɗu a waurin nan duk suka zauna aka shiga gaisawa cikin girmamawa da mutunci dan Hajiya Fulera ganin Alhaji Baffa yasata ta shiga hankalinta dan ya ma ta kwarjini bana wasa ba,gyaran murya Alhaji Baffa ya yi ya dubesu dukkansu,sannan ya kalli Babban Yaya"Habibullahi Rayuwar da akai anan gidan a gaskiya da wuya ayi irinta a wani wuri a zauna lafiya Babanka Habibu shine mahaifinka na ai nahi wato wannan,shi Babanka Aminu abokaine na haƙiƙa masu sadaukarwa junansu farinciki,nasan kana mamakin wannan ce mamanka ko kana da yayu ƴaƴanta na wajan Aminu sannan ace ta haifeka kuma ace Babanka daban? sannan ga ƙanne ƴaƴan Aminu ko to abin inba bayani aka maka ba bazaka taɓa ganewa ba,amma zan warware muku abin yanzu",gyara zama ya yi haka kowa ya nutsu ana saurarensa"Asalin lamarin da ni da Baban Habibu abokai ne sosai acan garinmu kuma maƙotane iyayen mu tare muke komai na rayuwa dashi bamai rabanmu kuma, sanda na fito kusuwanci wannan garin tare muka zo dashi amma da muka koma sai Allah ya masa rasuwa alokacin yanada yara biyu Sadiya da Habibu nima ina da yara biyu Aminu,Haruna sai cikin Nuhu dana tashi dawowa inda nake kasuwanci saina ɗebo gaba ɗayansu ƴaƴana da matata da yaran da abokin nawa ya bari na taho dasu saboda asamu mahaifiyarsu tayi aure dan ƙauye ba ruwansu da yaranki aure zaki muddin mijinki ya mutu,sanda mukazo nan saina sa su a makaranta amma iya mazan dan Sadiya tayi ƙanƙanta kuma a sannan ba'a sa yara mata karatun boko,sanda nazo nan ƙasar gidan dana sauka da fari shi mai gidan shine yamin hanya nasai wani gidan babu jimawa da zuwa na haɗu da Haulatu ban taɓa jin ina sonta ba amma nace saina aureta,babu daɗewa da maganar na aureta kwananta arba'in A'i ta haihu ɗanta namiji Nuhu kenan tun sanda Haulatu taga A'i ta ƙara haihuwar namiji sai tasa wani hali aranta kullum tanawa A'i habaici itama ai mazan zata haifa,ni shaida neA'i bata taɓa tankawa Haulatu ba duk kuwa abinda take ma ta,har Allah ya bawa Haulatu ciki ta haifi namiji Rabilu,bayan ya ye shi tare suke da wani cikin nan Hankalin Haulatu ya tashi ta rasa ina zata sa kanta cikin A'i nada wata biyar ya ɓare murna sosai Haulatu tayi agaban kowa,amma ba wanda ya kulata,bayan ƴan watanni Haulatu ta haihu ɗa namiji Ibrahim murna tayi sosai in na mutu tanada kaso mai tsoka a dukiyata,bayan yaye Ibrahim Haulatu ta ƙara haihuwa amma mace to tayi murna amma burinta ta haifi maza da yawa sannan macen ta biyo baya,a gidan nan Haulatu ta takurawa Habibu da Aminu komai aka rasa agidan nan saitace sune ni kuma da yake nasan halinta bana kula maganarta har suka girma tsakanin Aminu da Habibu akwai abota ɓoyayya ta musamman,watarana na tura Habibu ɓaɓura bayan ya dawo sai yake faɗamin yaga wata yana so kuma zai koma,nayi murna sosai kwana kaɗan sai ni da Aminu mukaje Gaya anan Aminu ya gano Sa'adatu yace yanaso ashe wani ya ragashi bamu sa ni ba ni kuma danawa Babanta magana da yake abokina ne sai ya bani auranta,mun dawo gida akai shirin biki mukaje can ƙasarsu aka ɗaura auran dan ba ƴan nan haka ba ne,sanda aka kawo yarinyar ashe itace Habibu ya gani a ɓaɓura gidan yar babanta maganar da ya ma ta shine ta faɗawa mahaifinta tace yace zaizo,amma waɗannan yaran tunda ta shigo gida bai taɓa nuna yasanta ba itama haka,haihuwarta biyu Hasiya da Mabaruka,a sannan na haɗa auran Sadiya da Haruna,tare suka sake haihuwar mata,duk wannan abu da ake Haule na kallo amma bata magana tayi zuru ashe ta ciki na ciki ita taje tayo bincike miye tsakanin Sa'adatu da Haruna a ranar sunan haihuwar yaran da sukai Haule tai niyar yiwa Sa'adatu sharri da Habibu amma Allah ya yi musu taimako suna tare ne danta ɗauka shi kaɗai ya shiga ɗakin mejegon da asirinta ya tonu anan ta shiga fallasawa kuma aka tabbatar hakanne,kwanan Sa'adatu sittin da haihuwa batare da shawara da kowaba Aminu ya saki Sa'adatu saki uku,na shiga tashin hankali sosai da sosai amma ba yanda na iya,amma me sai Aminu yazo da wani wai saita gama ma idda sannan zata koma ma garinsu a haka na amince masa babu jimawa Aminu yazo ya tasa ni agaba saida na ɗaura auren Habibu da Sa'adatu abin saikace almara koda akai auran suna nan aɗinke suna kasuwanci gashi hannunsu akwai albarka komai suka taɓa sai ya hau,wannan aure ya baƙantawa Haule amma A'i murna tayi saboda halinsu ɗaya da Aminu suna son farantawa wani koda su zasu cutu,Haule tayi ta buge buge kan a raba auran nan amma Allah yace eh dole ta haƙura da abin yaƙi, bayan auran da shekara biyu sai kwatsam aka nemi Habibu aka rasa tashin hankali iya tashin hankali mun shige shi kullum Aminu a hanya yake wuni yana kwana neman abokin shi da haka har akai wata huɗu saiga cikin Sa'adatu ya bayyana wannan ciki Aminu ya ɗauki son duniya ya ɗora masa har Allah yasa aka haihu ɗa namiji ranar suna Aminu ya saka masa Habibu tana arba'in bana nan a gidan haka A'i taje ƙauye sai kawai Sadiya da Haruna sukaga Haule na watso kayan Sa'adatu wai tabar gidan tunda bata da gado a cikinsa,tana kuka tafito anan Sadiya ta fito ta shiga da ita ɗakinta jifansu taita yi harna dawo na tarar kaca kaca na ma ta kuma na saketa saboda yau abin nata ya ishe ni na gaji da halinta,muna cikin haka Aminu ya dawo ya tarar tsaki ya yi jin me take ya fita ma agidan,itama kayanta ta ɗiba ta tafi babu jimawa aka kawo min gawarta tifar yashi ta bige ta bakin ti,anan gidana aka mata sutura aka binneta,tunda ta rasu A'i ta riƙe yaranta ba tsana ba tsangwama sai dai kash sun riga sun ɗauki halayenta kuma har yau kai a unguwar nan da muka dawo ba wanda yasa ba ƴaƴanta bane,bayan shekara biyu Aminu yasake maida auransa da Sa'adatu shike nan,amma kullum bai daina neman abokinsa ba,har Allah ya masa rasuwa da sunan Habibu a bakinsa ya tafi,Habibullahi ya tashi da wayo ga farin jini ga hikima dan in ya yi abu saika ɗauka ya shekara sittin wannan halin nasa yasa ƙannensa ke mutuƙar tsoronsa kuma suna girmamashi gashi nan ku yara wannan yayanku ne fa",iyayen share fuskarsu sukai saboda saida kowa ya yi kuka,yaran kuma na kallon Babansu na kuka su shine yasa su nasu kukan,jikin Babban Yaya suka haye suna kuka ganin babansu nayi saboda wasu dai basu san me ake cewa ba,ɗaga kai Babban ya yi nai sauri komawa soron ina Hawaye"zo nan Nana",cak kukan Alhaji ya tsaya ya ɗago kansa,Nusaiba ce tashiga goge mai fuskar"Abba na kayi shiru to",take tambayar sa"so ki ke sirikata ta ganni ina kuka",juyowa kowa ya yi yana dubansa shima kallonsu ya yi"Halima ai kina ganin Habib kinga Nana dan baya magana biyu bai ambaci Nana ba duk inda ya zauna sunan ta yake rubutawa,ƴar waye ne?",murmushi Iyyo tayi "ƴarka ce ai","ƴata Iyyo","eh mana Autar Halima ce",bakinsa ya dafe"lallai Allah mai iko",da sanɗa na shigo wuff naje na shige ƙarƙashin hannun Babban Yaya,ƴar dariya Alhaji Yayi"fito mana Nana na ganki ƙara ɓoyewa nayi naƙi fitowa,kama haɓa Umma tayi"Halima dama Nana nada kunya haka","nima yau dai nagani"duka dariya akai nan Hajiya Harira tace"a a kubarta ai wurinmu zata koma"da sauri na ɗago"ba inda zani na bar Aunty Mama"dariya suka saka,suna tambayar wace Aunty Mama",Iyyo ce tasa a kira ta nan sukaga kamar ita ta haifi Nana dan suma sunga ta fi kama da ita,gaisawa sukai da baƙin sannan Umma take faɗa musu abokiyar zaman Halima ce itama sunan ta Halimar,mamaki sukai tayi nan Alhaji Baffa yace ayi sallar isha sannan akira masa kowa yazo kafin su tafi sugan na gani sauran a haɗu daga baya,da wayo Babban Yaya ya ɓoyeni muka shiga gida sannan na fece aguje ciki.
Bayan sallar isha kowa yazo dan antafi kiran matan Kawu Rabilu saiga Gwaggo Asama'u a hanya itama amma abinda ya kawota daban,samun abubuwa biyu a rayuwa farilla ne wato farin ciki ko baƙin ciki,to hakan ne ya faru yau muraran wasu suka nuna farin ciki wasu kuma suka shiga yaƙe saboda abin bai musu daɗi ba,amma duk wannan abin ƙiri ƙiri naƙi zuwa,ina nan laɓe ina leƙensu na sakankance naji caraf an kama min hannu ihu na buɗe baki zanyi naji Abba na magana"to gashi yanzu na kamaki kuma ƙafata ƙafarki","wayyo Abbanmu kayi haƙuri","to shiga ciki",saɗaf saɗaf na wuce dama falon Mama ake na zauna can gefe ranƙashina Ya Sumayya tayi"munafukar ƙarya waike mai wayo ko","wayyo Babban Yaya",kafin na rufe baki ya zuba ma ta rankwashi aka ita batasan ma sanda yazo kusa da ita ba,Allah yasota ma kanta ba kitso da taji ajikinta,dafewa tayi tana tashi da gudu"Allah shi ƙara waya ce ki daki waccan tsuwwar kinsan yana nan",Ya Dijama ta faɗa tana dariya,hararar ta tayi"wallahi zan kama ki","ba komai in kama ni nasan ba iya dukana zakiyi ba",ƙwafa tayi tana shafa wurin,dariya su Hajiya Fulera suka yi nan ta dubi Iyyo"Hajiya muna neman alfarma guda ɗaya","tame Fulera","a bamu Habib mu tafi dashi saboda gidan nan na buƙatarsa ni nasan matsalolin Alhaji lamarinsa yanzu sai ɗansa",dariya sukai,nan Iyyo tace"ai wannan Sa'adatu zaki tambaya",da sauri Umma tace"a a Iyyo gashi nan su ɗauka ai dama namiji shi ɗan zaga duniya ne ba mai zama wuri ɗaya ba ne","mungode sosai da wannan alfarma da ki ka mana kuma Habib har abada naki ne ki ƙaddara ko ya yi nesa dake tofa yana nan a zuciya da ruhinki kina binsa da addu'o in nema tsari da kariya kina sawa rayuwarsa albarka sai komai nasa yana haske","insha Allahu Hajiya",wannan maganganu yasa zukatan matan Kawu Iro da Gwaggo Asama'u baƙi sosai,kishin bata haifi ɗa namiji ba ya kamata inama sanda Habibu ya nuna yana sonta ta amince da yanzu tasan itama tana ɗa dashi amma wai kaf dangin ace Habib ne magajin wannan dukiya wallahi tayi alƙawarin saita lalata mai rayuwa,ido da ido sukai da Hajiya Fulera kamar tasan me Gwaggo Asama'u ke saƙawa aranta ai kuwa ta kwaɗa ma ta harara da kashedin kar ki soma yin me ki ke tunani da ido dan san Habib take ita da gaske ta tabbar da zata tara abin duniya a hannun Alhaji muddin yaga tana sonsa da gaske,sai wajen goma sannan duk suka fito aka musu rakiya bakin mota,amma Babban Yaya bai bisu ba yace sai gobe zai shigo,koda ya shirya kayansa tare da Umma da Aunty Mama sukaje sun yaba da yadda suka tsara masa inda zai zauna sannan an tarbesu da mutunci sosai.
Vote
Share &
Comments
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
chapter 1️⃣3️⃣
Bayan wata ɗaya yau Babban Yaya yake shirin barin ƙasar gaba ɗaya ina ɗakin Aunty Mama ya shigo"zo nan Darling sis",da sauri na taho wajensa"gani Sweety Babban Yayan mu","yauwa zauna"ina zama ya juyo ya kama hannayena,cikin murya mai sanyi ya fara magana"kinga zan tafi ko kimin alƙawarin zaki dage kina karatu kinji banda wasa so nake naga kinyi har digri",murmushi nayi"insha Allahu zan dage","Yauwa Sweety ƙanwa"ya kamo hannuna muka fito a lokacin da ƙyar muka rabu,ina ta kuka baji ba gani ranar da fushi na wuni sai masifa nake da haka aka ɗebi kwana uku da tafiyarsa ganin ba sarki sai Allah na haƙura tunda dai banga zai dawo ba bare yace ya fasa ne.
Da tafiyarsa abubuwa da yawa sun faru saboda sun masa albashi yana turo mana kaf abinda yake samu ga Abban ya dawo gida kullum yana nan wajen Iyyo wai ƙara'i yake sai ya rama zaman da baiba na da a gidan haka zai tasa mu yay ta kallon ƙuruciya,makaranta kowa yana zuwa haka su Ya Ruma can gidan Umma Ya Fatsima dasu Sumayya su dama basa biyewa yayyensu da iyayen su muna kula juna kuma ko zamuje gidan akoro mu sai mun koma,Umma hankalinta ya kwanta dama akullum tana rayawa aranta Abban Babban Yaya na raye ashe hakanne tana farin ciki yanzu ƴaƴanta kaf suna da abinyi kuma sunaji da ita tunda Isma'il ma na aiki haka Hashim ga Ibrahim shida baima gama karatun ba ga su Khalid da Umar duk suna karatu abin dai ya yi dai dai.
******
Acan ma bayan sun sauka su goma ne wakilai suka tafi Kumar ya yi bajinta an samu fili mai fuska kuwa a nan garin GOA sannan aka siya komai dai na buƙata sun nemesa hakanan sun samu ma'aikata bila adadin,sati da fara ginin labarin ya fita nan da nan masu buking aikin suka fara wasu ma cos aka ƙara turasu kamin lokaci ya yi ana haka ya saka takardun Saddi'q da Haruna saina Isma'il, babbar magana sanda kira yasame su Abba dakanshi yaje gidan kuɗin jirgi ya tura ma saddi'q da Isma'il nan da nan suka dawo abinka da manya asati visa ta haɗu nan Abba ya sako su a gaba suka taho tare suma cos aka tura su,koda Abba ya gama bincikar gini abin gwanin sha'awa sunyi ƙoƙari sosai su kansu sauran da sukazo daga baya sukaga ƴaƴansu a wannan halin saida abin ya burgesu wato girman kai ba abinda yake ƙarawa face ƙasƙanci yau ga yaransu suna aiki tuƙuru dan ba zaman kallo suke ba kowa inda basirar sa take anan yake aikinsa sunata tsare tsare batare da kowane ɗan ƙaƙale ya taya su ba bare asamu mana ƙisa,koda Parker yasamu labarin abinda sukayi bayan sun sanar musu sun fasa saida baƙin ciki ya kamasa ashe wayo sukai bai sa ni ba,a wayance yazo har india yaga me suke yi takaici na sashi ya yi ya koma aranar dan bazai iya kallaba ya tabbata suka buɗe wannan company sai sun doke shi ashekara guda,haka dai abin yake tafiya kullum yana waya da gida ga Hajiya Fulera da Hajiya Harira dake janshi a jiki abin da yasa Alhaji ke warware musu account kenan yana basu kulli waisu ƙaru,Hajiya Salma da Amaryar Alhaji Safiyya su basa nuna komai ba yabo ba fallasa da yaje akwai wani babban sirri agidan Alhaji wanda yake ɓoye tsakanin Hajiya Salma da Safiyya akwai ɓoyayyar alaƙa wadda ba wanda yasan da ita sai iya su kaɗai ko iyayensu basu san da hakan ba alhalin ansansu a inda suke ƙawaye ne amma sunyi faɗa harda zubda jini tun daga nan akai baran baran ba ne kula wani sanadin iyayen ma suka raba wajen zama,amma su ashe manyan munafukai ne zamuji me ne alaƙar su ta auren miji ɗaya kuma suka ɓoye hakan ba wanda ya sa ni.
Wannan abu na ɗaukar su Saddi'q ya haddasa rigima agidan dan ƙiri ƙiri su kawu Rabilu suka yima Baffa magana ba'a haɗa da ƴaƴansu ba saboda ana musu baƙin cikin kar ƴaƴansu ci gaba kaf abinda suke Abba najinsu basu sa ni ba,ƙarasa shigowa ya yi ya kalli su kawun yace"duk suje su kawo masa takardun karatun yaran ko na secondry ne shi zai basu aiki amma har bayan sati shida Abba ya dawo ba'a ƙara tayar da maganar ba saboda ba takardu kuma sun san sauran dai takardu aka kai amma su nasu yaran bama su tsaya karatun ba kullum akoro su ake saboda rashin ji da jan magana.
Yau gidan mu a farin ciki muke Baffa zai dawo,ko ina na gidan yasha
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 32