watarana saikin bani matsala a rayuwata to baki isaba yarinya kafin wannan lokacin da kike hasashe na gama dake ke yau ma basai watarana ba","anan ne kikai kaɗan mijinki nawane ni tasa ce tun inazanin goyo inbaki sa ni ba Babban Yaya nice rayuwarsa ko baki taɓa jiba ya kirani da MY LIFE"katseni tayi ta hanyar jifana da wani rose vase da sauri na kauce ta samu Tv dariya nayi"kin ɓata kayanki ɓuleliya baki sa ni ba ma angona ya tsani mace tiƙeƙiya Hhhhhhhh",tayo wani tsalke ta kawo min danƙa nai sufa ta bayanta na fice a ɗari"sai anjima uwargidana"kan ta fito ma na fita agidan gaba ɗaya ina sheƙa gudu.
Da gudun itama ta biyo ni amma batai nasarar ko ganin ƙurata ba komawa tayi tana kai komo"lallaima yarinyar nan yanzu ni take kallon tsabar idona tace zata kwanta da mijina ni dama na gaya Aunty wannan yarinyar shaƙuwarsu bata ƴan uwan taka bace daganin kallon da yake ma ta tun bata kai mace ba,to wallahi kin taɓo masifa da bala'i kozanyi yawo tsirara baki shigowa gidana",a haukace ta shige ɗaki ta janyo wayarta ta dannawa yayarta kira tasa a handsfree ta aje kan mudubi tana ɗagawa ta fara magana"dama na faɗa miki wannan yarinyar mijina take so yau gashi ta faɗan baki da baki shi dama basai ya faɗa ba dan nasa ni amma wallahi basu isaba","waime ya faru ne kike wannan masifar","au tambaya ma kike to bari kiji"nan ta zayyane ma ta komai"wai da gaske kike Hajara wannan ƴar yarinyar ta miki haka anya kuwa mutum zallace","ai bari kedai da alama tanada ƴan rakiya","kina jina ko Hajara ki kwantar da hankalinki ina nan zuwa","to shike nan saikin zo ina jiranki fa karki shakkar komai dan inada kuɗi masu yawa kuma komai zan iya yi akan mijina",ta kashe ta yar tana zama jaɓar bakin gadon,"lallai yarinya kin ɗebo ruwan dafa kanki.
Ban zame ko ina ba daga nan sai gidan Gwaggo Ma'u na tafi jan magana dan nasan dai wadda nake zuwa wurinta bata nan.
*******.
Bacci ya yi sosai bai farkaba,saida ya jima yana baccin sannan ya tashi agogo ya kallah shabiyu saura salati ya yi yana kallon inda yake tashi yay zaune saiga Abban ya fito a ɗaki"a a ka tashi sannu ga abinci can adining dan da kallon wannan fuskar yunwa kake ji jeka wanke fuskar ka aɗakina kazo kaci nayi baƙi zance can muyi magana kan ka gama zan turo Yasmin ta kaika can inda nake",kansa ya sunkuyar "to Abba",fita ya yi yana murmushi har wani faɗi yake ji in ya kalli Habib ace wannan ya kasance ɗansa ne guda,tashi Babban yaya yai ya shiga ɗakin bai kalli komai ba ya shiga toilet ya wanke fuskarsa da bakinsa ya fito a dining ya karya sosai dan baya son ya koma ya tadda taliyar nan ko shinkafa shi mamaki ma yake kamar ba ƴar zamani ba ko ƴan kayan ƙwalam ɗinnan na zamani ita bata iya ba ko ganda ce ohoo bai sa ni ba,bai jima da gamawa ba Yasmin ta shigo da gudu "Big Broo in ka gama kazo na kaika inda Abban yake",tashi ya yi yakama hannunta suka fito zuwa inda Abban yake bin Abban da kallo ya shiga yi ganin yanda gefen idonsa ya yi kore kuma idanuwansa kamar mai cutar asma,ɗauke kansa ya yai ya mai da kan mutanen dake zaune harda turawa da baƙaƙe ƴan uwa,da sallama ya ƙarasa nan suka bashi hannun suka gaisa yana mamaki manya mutane haka na bashi hannu a ƙasa ya zauna nan Abba yace ya dawo sama amma yaƙi,mutanen jinjinawa tarbiyarsa sukai nan Abba ya kallesu yace"gashifa MR Josep",kai ya kaɗa ya shiga miƙo masa takardu yana sa musu hannu har aka gama sannan suka faɗa masa angama sauran yaran naka a kira kowa yasa hannu, amma ko iyayensu basu sa ni ba saida aka gama sannan da kansa ya karɓi wasu yasa hannu ya miƙa musu bayanin"kayan suna a store a lagos komai yana akimtse a kawo min su zuwa dare bana so sukai safiya","ok"suka amsa sannan suka kwashi takardun suka tafi,"tashi ka zauna sosai Habib"zaman ya yi kamar yarda yace sannan ya dubeshi"ka saurare ni da kyau bani da wasu ƴan uwa sama da Halima bani da iyaye sama da Baffa da Iyyo Habib ka nutsu sosai ka sauarareni kuma kome zan gaya maka karka ɗaga hankalinka dan babu wanda ya isa ya hana Allah ikonsa,a yanzu haka akwai guba ajikina wadda watanta bakwai amma bata gama cika ba zuwa gobe ko jibi zata cika kai ko yau ma kuma hakan shine ƙa'idarta dan haka dole tana cika zan mutu"nan tarin da yake ya ƙara taso masa da sauri ya miƙe jikinsa na rawa ya tallabeshi"haba Abba taya zaka ɓoye wannan abu baka nemi magani ba kuma baka faɗamin ba"hawayen dake zuba afuskarsa ya share masa,"haka Allah ya nufa saboda da likitocin aka haɗa baki naje a dubani aka min abinda bashi naje nema ba kayi haƙuri Habib naso na faɗa maka suwaye amma sai nayi tunanin irin rigimar dazan haddasa a acikin al"saidai inaso ka kula da kyau da mutanen da zaka shiga cikinsu nan gaba dan abinda ka mallaka zaija maka ɗaukaka waɗannan gidajan kaf naka ne ba bu wanda na mallakawa ko ɗaya har matana duka na mallaka musu wasu dan bana son kowa ya zauna akusa da kai koda na mutu ka tattaro danginka duka ka zuba su amma wancan na kudun ba kowa ciki sabone kasa iyalanka ciki nawa Nana komai na ƴa nan da shekara goma kawai buɗe ma ta za ai ta shiga ka riƙe wannan yarinyar ina hango alkhairi masu yawa atare da ita kuma zata saka ka farin ciki karka damu da rigimarta duk Aisha ta duniya haka take Habib ga ƙannenka nan na bar maka amana duk nasan bayan babu ni suka tsinci wasiyyata bazasu baka riƙonsu ba amma ka zama idonsu aduka ƙasar da suke zaune nasan wannan zaman nawa da kai shine na ƙarshe sai dai ka riƙe wannan sirrin karka faɗama kowa amma kasan wani abu ɗana"kai ya girgiza hawaye kamar famfo na zuba a idonsa"ka zama namiji mana da wannan basirar taka nasan zaka gano masu hannu a wannan abin wataran Allah ya muku albarka da zarar babu ni mutane zasuyi ta zuwa wajenka saboda ina bin mutane da yawa bashi sai dai komai na bashin mallakinka ne na riga na zartar da hakan ba wani batun gado bayan na mutu dan bani da ƴan uwa bare ace na musu baƙinci kuma koda dasu kai ka kore komai kasan tuwarka ɗa namiji na halal",ya ƙarashe yana tari"kayi shiru da wannan bayanin Abba"hannunsa ya ƙara riƙewa sosai"ai na faɗa maka zafinta ya haɓaka fa abinda nake ji ba zai fasaltuba Habib ka kawo min Alhaji Baffa amma karka faɗa masa komai"kansa ya girgiza "bazan iya tafiya na barka ba",kafin ya gama magana tarin ya ƙara turniƙeshi,miƙewa ya yi kamar zai tashi sama ya fito a ɗakin da kansa ya fito da mota sai kallonsa ma'aikatan suke amma sunyi shiru masu abu da abunsu,ɗakin ya koma yatarar Abba ya faɗi jini ta ko ina a fuskarsa har ido,jajircewa ya yi ya danne zuciyarsa ya fito da Abba shi ɗaya suna ganin haka hankali ya tashi nan danan gidan ya hargitse amman kafin kowa yazo ya fita dashi daga gidan security's suka mara masa baya,da gudu Yasmin ta shiga ɗakin Hajiya tana ihu"Mommy Abba bashi da lafiya gashi can Yaya ya fita dashi ko ina ajikinsa jini",lumshe ido tayi"naji jeki ganin zan fito"da mamaki take bin ta da kallo ganin bata nuna razana ba sai dai ta fito,tana fita Hajiya ta janyo wayarta ta kira wata number"Hello Alhaji lokaci fa ya yi gashi can antafi asibiti dashi",magana akai can ɓangaran ta amsa da "yanzu ma kuwa",ta kashe ta ɗau mayafi tana ƙaƙaro kuka ta fito fuskarta sharkaf da hawaye,kallon mamaki Yasmin ta bita dashi ita dama tasan ta faɗawa Mommy hakan ai dole tayi kuka sai yanzu ta aminta da Mommyn,atare suka fito nan sukaga matan ma duk sun fito ko wacce da kuka a fuskarta amma kana gani in kana da hankali kasan abin baikai zuci ba,motoci suka shiga aka fita dasu zuwa asibitin.
Vote
Share &
Comments
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
chapter 1️⃣7️⃣
P17
Yana shiga asibitin motar kawai aka kalla nan danan likitoci sukaiwa motar dafifi da kansu suka fito dashi zuwa ciki shi kuma yabi bayansu emagency sukai dashi nan aka shiga dubashi aman fin lokaci mai tsayi ba labari yana nan a wurin sai safa da marwa yake bai sallah ba har suka fito kowa ya jigata kallonsu sukai dan sun cika wajen,nunashi sukai "biyo mu",abin mamaki kafin su gama magana Hajiya ta katse su gun faɗar"Doctor damu zakai magana ba dashi ba saboda basu jima da haɗuwa ba duk da yana ɗansa baisan komai nasa ba",gyara tsaiwa Dr ya yi"to waya gaya miki wani abu na Alhaji muke son sa ni kuma ina ruwan mu da basu daɗe da haɗuwaba ko jiya suka haɗu ya fiku matsayi a wurinsa duk da kuna matansa kuma hakan da kikai ya nuna bakece ki ka haifi ɗan ba kenan dan haka maida harshenki taho rankai daɗe"ya juya zuwa wani lungu,wani kallo Babban Yaya ya watsa musu wanda yay bala'in kaɗa musu hanji amma suka shanye suna ƙara kalar tausayi,bin bayan Dr ya yi zuwa inda yaga sun shiga shima ya shiga wani falo ne kamar wurin meeting duk zama sukai shima ya zauna,mai yanayi da shugaba acikinsu shine ya fara magana"am sorry yallaɓai mahaifinka babu abinda za'a iya masa sai dai a zubawa sarautar Allah ido kafin lokacinsa ya yi saboda komai na jikinsa ya lalace har ƙwayar idanunsa kuwa saidai bamu gano komai dan gane da abinda ya haifar da hakan ba",numfashi ya yi kansa na bugawa ya miƙe tsaye yana sa hannu a aljihu"ba komai Doctor Allah ya kawo sauƙi ya yin tafiyarsa inaso karka bari kowa yaga Abbana koda kuwa matansa ne har Allah ya amshi abinsa","karka damu game da wannan zamu kaisa inda ma ba wanda zai ya shiga sai dai munso kafaɗa mana meke faruwa dan munsan abinda ke iya zama haka amma munaso muji nasa dan da alama kasani","ba ƙarya a wannan abin Doctor gubace aka masa allurarta amma ba a ƙasar nan ba nasan kunsan ta sai dai samunta anan yana da wuya dan haka nasan komai ina godiya agareku"ya fito aɗakin ya bar asibitin duka batare da kowa yasa ni ba.
Alhaji Baffa ne yaganshi ya shigo kamar zai faɗi da sauri ya tareshi ya zauna akan ɗan bulon barandar ginin dafashi ya yi"Habibu lafiya kuwa",shiru ya yi ya kasa magana Iyyo ce ta fito"kai kuma miye hakan ina iyalin taka",nan ma shiru ya yi saida Baffa ya gaji da magana sannan ya buɗe baki daƙyar yace"Abba ne",ya yi shiru kuma"faɗi mana Habibu ko sokake ka ƙarasa mu dama zuciyar ta tsufa",Iyyo ta faɗa"Abba ne Iyyo zai mutu sun kashe shi",yana kaiwa nan ya fashe da kuka mai taɓa zuciya, saurin ja baya Iyyo tayi tana salati"ban gane sun kashe shi ba Habibu yimin baya ni sosai",dakatar da kukan ya yi,tsaf bayanin Abba yawa Alhaji Baffa,wannan batu ya kaɗa Baffa dayawa dan saura ƙiris ya fita ahayyacinsa da ƙayar ya dawo dai dai,jin motsi yasa su juyawa Mama ce tsaye fuskarta sharkaf hawaye alama taji komai kenan ƙarasowa tayi"kaini nagansa Habib ko kallon ƙarshe na masa",tashi ya yi ba wani bayani har Iyyo da Alhaji Baffan suka shiga motarsa zuwa asibitin da isarsu suka tarar su Hajiya Fullera nata hauka sai ankaisu inda yake amma likitocin nan sunyi mirsisi kamar ba dasu suke magana ba,yana shigowa suka nutsu abin har mamaki ya ba mutane kuma kana kallonsu shi suke kalla shi kuwa ko kallo basu ishesa ba bare yasan me suke,ta wani ɗaki suka kaisu inda yake idonsa biyu amma baya hayyacinsa kana gani,duk ƙarfin zuciya irin na Alhaji Baffa saida ya fashe da kuka"Habibu kaine ka zama haka kalli yadda ka koma dama rashin zuwanka duk wannan ne kace ba komai da nace maka zanzo Allah yasaka maka ɗannan yasa can tafi maka nan",Mama dake akansa ta toshe bakinta hawaye kawai ke zuba a idanuwanta baya ta matsa dan bazata iya kallonsa ba saidai addu'a da take masa can ƙasan zuciyarta,kusa dashi Habib ya matsa yaga hawaye yana zuba a idonsa da sauri ya ƙarasa ya kama hannunsa mara ƙarin ruwa ajiki,muryarsa na rawa ya fara magana ahankali "Abba kayi min magana please waye da wannan abin suna kawai ba bayani ba dan Allah Abbana",tari ya yi sannan ya mai alama ya durƙuso numfashi yaja na ƴan mintuna sai kuma ya yi shiru yana salati,bai ɗago kansa ba yanaji yagama salatin a kunensa saida ya gama ya ɗago idanuwansa na hawaye,baya Iyyo taja ta fashe da kuka hakama Alhaji Baffa,cikin dauriya ya rufe masa idanuwansa yaja masa mayafin ƙarin ruwan ya cire da duka na'urorin yaja baya ya jingina da bango yana jin tashin hankali na shigarsa da gudu likitocin suka shigo ganin yanda aka masa suma da kansu suka matsa dan sunga manya ne awurin sunsan komai ya kammala Allah ya jiƙansa,atake suka basu shi nan suka turo shi waje ai su Hajiya da yaran na ganin haka sai suka hau hauka suna faɗuwa awurin sai burburwa suke a wurin kota kansu ba wanda yabi aka fito dashi zuwa motar jinya mallakin asibitin ba a wani ɓata lokaciba zuwa gidansa dan masa sutura hakama daga asibitin duk nacan suka dawo gidan kowa ka kalla kuka yake sosai kan kace me can unguwar ma kowa yazo dan har Hajara Umma ta turawa tazo itama ta shiga tashin hankali dan mijin ƙanwar ubanta ne,shaƙiƙansa ne su Kawu Nuhu sukai mai wanka aka shiryasa tsaf zuwa gidansa na gaskiya ana ta mai addu'ar dacewa halinsa nagari ya bishi,inka kalleni agidannan ka ɗauka Baffana ne ya mutu saidai kowa yasan Abban Babban Yaya ai Abbana ne nima kuma gaban kowa yake nuna min so.
Bayan andawo abinneshi nan duk aka zauna anata jimantawa juna,cikin sati baƙi kala kala sun zo gaisuwa masu zaman gulma kuma a washegari kowa ya kama gabansa sai masu takaba da yaransu.
Bayan sati huɗu:
Hajiya Fulera ke sanye da wani uban material mai ƙyalli sai shining take su Hajiya Harira da haɗa a falon,tana zaune a kan kujera ta naɗe ƙafa ta kalle su tana wani yatsina,abin haushi kaf ka kallesu baka cewa masu takaba ne dan sunsha ado iya ado"nasan baku san me yasa na taraku ba ko to inaso ne muyiwa wancan taka hayen dukiyar ya bamu dukiyarmu dan nasan shida wancan tsohon suna ƙulla yazasuyi damu ne",Hajiya Salma ce ta kyaɓe baki tanawa Safiyya signa nan kuwa ta gyara zama"ai dama Hajiya ke muke jira kiyi magana tunda kece babbar gidannan duk a ƙarƙashin muke",wani fasuwa kanta ya ƙarayi"to ku kwantar da hankalinku ranar arba'in gaban kowa da kowa zamu dizga shi mu wullaƙantashi sannan mu koreshi agidannan dan abinda bai sa ni ba nice kawai nasan sirrin Alhaji kuma duka abinda yake dashi nasa ya yi singhning da sunayen yaranmu bai sani ba",heeee sukai shewa,murmushi Babban yaya ya yi yakoma sama dama yana ɗakin Yasmin ne suna karatu ya fito yajisu suna wannan maganar saida suka tashi sannan ya sakko ya fita.
*****
Da sallama ya shigo gidan Iyyo ina kwance baccin iskanci ya zama na gaske a kusa dani ya zauna yana gaida Iyyo,tana cikin amsawa naji sautin ta tunkamin na buɗe ido nasan dawa take magana,ido na ƙyallarawa na ganshi yana sanye da yadi mai laushi ɗinkin ya amshi jikinsa gashin kansa kamar kan mace ƴar gayu sai shining yake kai gaskiya Babban Yaya ya haɗu,bai jimaba ya tambayeta Alhaji Baffa ta faɗa masa ya fita amma zuwa anjima zai dawo,kishingiɗa ya yi nan kusa dani bai daɗe ba Bacci ya kwasheshi Iyyo ba ruwanta ita ta tashi tai fitarta zuwa tsakar gida.
Umma ke sallama da Hajara dama tana gidanta tun ɗazu an zo shigar da kai kamar yarda Yayarta ta koya ma ta harda dafo farfesun kifi dan gulma tana fitowa ta shigo gidan Iyyo tana ta sallama shiru,inajin muryarta na tashi da sauri na cire ɗan kwalin kaina na baza gashin na raɓo jikinsa na kwanta fuskata na kallon tashi na kulle idanuwa na adole mai bacci,Iyyo da ta shiga ɗaki bataji sallamar ta ba dan haka ta ɗago labulen ta shigo kyakkyawan gani tayi mijinta kwance da wadda ta tsana kuma da alama wani abu sukai danta gama lura ƴan gidan ma sun mutu akan wannan shashashar soyayyar,wani irin bugu ƙirjinta keyi dan haka batai maganaba a hankali ta juya ta fita daga gidan da yake ba nisa da ƙafar da tazo ta koma tun a falo ta fara jefar da kayan jikinta dan wani masifaffen zafi take ji,tuƙuƙi zuciyarta ke ma ta tama rasa me zatayi kome zata tuna,da ƙyar ta ƙwaƙulo ashar taita ƙundumawa ita ɗaya kamar mahaukaciya.
Tana fita na miƙe na maida kaina yanda yake ba jimawa ya farka yana kallona,shafa fuskata ya yi"uwar rigima har yanzu yi ake kenan"ɗan motsawa nayi madadin ya barni a a"ke tashi bakiga time ɗin islamiyya ya kusa ba",buɗe ido nayi ina hammar masu bacci cikin idanuwana ya kalla ya girgiza kai"ba bacci ki ke ba kuma baki da gaskiya faɗa min me ki ka aikata",wuri wuri nayi kamar zanyi kuka,muryar shagwaɓa nayi"Darling Yaya ni banyi komaiba",kaina ya dafa tashi muje gidana na baki wani abu",watsal nayi na miƙe naja hijabina"Iyyo nabi Babban Yaya",na faɗa da ƙarfi"ku gaida nagaba ja'irai",dariya nayi na kama hannunshi muka fito ni kaɗai nasan me nake girbawa a araina yau matar nan zataga wata masifar dan nasan tana can ta hau kamar an ma ta ɗurar yist.
Yana gaba ina bayansa ya yi sallama yana tura ƙofar falon,zumbur tayi ta miƙe tayo kansa ta shaƙeshi zatai magana kenan ta ganni a bayansa sakin sa tayi tana nufoni"au biyoshi kikai nan dan ki ƙara tabbaɓe min shi wato kin nuna min kin kwanta dashi ɗin da gaske ko",zaro ido nayi kamar zanyi kuka"ni ɗin Aunty Hajara miye kwanciya dashi kuma"ya yinda Babban Yaya ya kira sunan ta da ƙarfi" Hajara kina da hankali kuwa Nana ki ke faɗawa ta kwanta dani dan hauka me wannan tasani da ki ke ma ta irin wannan zancen",da hanzari ta juya gareshi"me kace wannan ƴar barikince yarinya bata san komai ba to bari kaji daga kai har ita baku isaba wallahi saina yi maganin ku ke kuma",ta kawo hannu ta danƙeni mari ta kifa min saida naga taurari saurin riƙeta ya yi yajanyeta gefe"dama baki da hankali Hajara a gabana zaki daki RAYUWAR TAWA",wani dam ƙirjinta ya bayar ta fincike kanta cikin tsantsar masifa take dubansa kamar zata rufeshi da duka"Habib a gabana kake kiran wata da rayuwarka to kasani yau rayuwar taka zata ƙare dan saina kasheta a gabanka",gyara tsaiwa ya yi yasa hannu a aljihu ya matsa ma ta yanda tana fuskanta ta"kasheta Hajara gata kashe wallahi tallahi dasai kaf na ƙarar da danginki sannan nazo kanki",batai gigin taɓa ni ba sai dai kumbura da take,ni kuwa kamar na sheƙe saboda dariya amma na basar sai matsar ƙwalla nake,matsowa ya yi ya kama hannuna yaja ni zamu fita,kamar walƙiya naganta zata daki baya na nai saurin juyo ma ta ƙirjina ta sameni baya nayi zan faɗi darajar hannuna dake anasa ban kai ƙas ba ya janyo ni jikinsa nai saurin ɗauke numfashina kifani ya yi a ƙirjinsa yana kiran sunana amma ina na suma dan sheri,silalewa nayi ƙasa ya bini yana riƙeni da kyau,''Nana!Nana!!"amma ina nayi shiru bayan ina jinsa hannunsa ya ɗora akan ƙirjina ya danna amma shiru,kwantar dani ya yi flat sannan ya haɗa hannayensa duka biyun ya ɗora aƙirjina ya danna nan ma shiru,lumshe idanuwansa ya yi ya buɗe da sauri sunkuyowa ya yi ya buɗe bakina yasa nasa yana hura min iska,buɗe idanuwana nayi sai cikin nata,damabtun tunda taga na faɗi ta ɗora hannu aka yau tana ganin rashin mutunci ruwansa, ido ɗaya na kashe ma ta sannan na ɗaga ma ta babban yatsa na,jin zai ɗago na koma yanda nake saida ya yi sau huɗu sannan na kawo numfashi da sauri ya tareni yana dafa ƙirjina ɗagani yay ya jingina da jingina da jikinsa"My Life sannu please kar ki kuma yimin haka badan ni ba wallahi bazan iya rayuwa ba babu ke",maganar da yake saki ce tasa Hajara ƙara danna hannu aka dan wanda tayi da bai ma ta ba,dan kana ganinsa bai san me yake cewa ba,murmushi na masa ina ɗaga kai alamar amsa abinda yace,cikin wani irin yanayi ya ɗago kai yana ma ta wani razanannan kallo zai yi magana na tareshi"indai ni ce your life karka kulata na yafe ma ta ai matarka matsayinku guda agareni Babban Yaya",kaina ya dafa Allah ya miki albarka zo muje nakaiki shan ice cream",ya ɗagani zuwa inda ya yi parking agidan,ita kuwa kallo bata ishesa ba tana gani muka fita a gidan ina ma ta gwalo,muna fita ta zube awurin ta rasa ma me zatayi kawai ta miƙe ta koma ciki ta fara maida kayanta itama ta fice agidan,muna tafiya amota yana bani haƙuri har mukaje wani babban mall fama yay tayi na fita naƙi dama ya matsan saina afashe da kukan iskanci,rufe ido ya yi ya jingina kansa da kujerar motar cikin sanyin murya yace"me kike so a miki",ɗan dakatawa nayi ina taɓe baki"ni bana son ice cream",yana a yadda yake bai gyaraba yace"saime ki ke so"ni ni muje danja kasai min kaya in nagani zan nuna maka","nagane me ki ke nufi ba danja zamuba bari kiga inda zamu",ya kunna yaja baya muka bar wurin,tabbas kamar yasan me nake nufi wajan kayan makaranta ya kaini naita jidar kaya mun gama ya biya muka fito muna shiga motar ya dubeni"ashe dai zakiyi karatun danake so",kai na rangwaɗa"sosaima ai saikace ya isa haka Nana" ƴar dariya ya yi yana kunna motar hargida ya kaini nida kayana,sannan ya wuce bansan ina zashi ba dai,Aunty Mama ce taganni da kaya niƙi niƙi tashi tayi ta karɓeni"Nana waɗannan kayan fa kamar wadda za a kai makarantar kwana" "aje na hannuna nayi"ba wata makarantar kwana Aunty kawai shirin karatu nake","a lallai nafi kowa murna to a dage kinji ƴar albarka","insha Allahu Aunty Mama na".
Koda ya koma gidan bata nan wanka ya yi kawai ya fito yana dawowa gidan Iyyo ya tarar Alhaji Baffa ya dawo anan ya zauna ya faɗa masa kaf abinda ake ciki"karka damu Habib masu haƙƙin wannan zaka wa magana aranar kowa ya hallara amma su tozarta ka basu isa ba jinin Habibu ya wuce wulaƙanci a wurinsu","insha Allahu Alhaji nawa Kawu Haruna waya yace zaizo kafin ranar","to shike nan anan ya zauna sukaita tattaunawa har akai magaruba sannan ya bar gidan,sanda ya koma ta dawo amma sai kumbura take ƙala baice ma ta ba ya shige ciki ya barta nan,ƙwafa tayi"zaka shiga hannuna Malam kome ka ke ji dashi saina zubar da shege Nana kuma ko a hanya ka ganta ta zama babbar maƙiyiyar ka" ta tafa cinya tana shigewa ɗaki,saida suka kwana biyar a haka sannan taga abin bana ƙare bane taje ta faɗawa Umma nan ta kirasa ta masa faɗa sannan komai ya wuce .
*****
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 32