kalle ni tunkan ma ka kalleni sai dai ni nasan wace a kusa da kai","fita"ya nuna mata hanya,soƙo soƙo ta fita tan juyowa ta kalleni nan taga sai ruwan hawaye nake,kai ta kaɗa a ranta tana zan kama ki ne ta fita a ɗakin.
: Zaro ni ya yi a jikinsa ya tallabi fuskata tasa fuskar yasa yana gogawa kan tawa lumshe ido nayi dan salon na sa yamin wato wani sirrin ne wannan na goge hawayen masoyi ba murmushi na yi acan ƙasan raina ya jima yana min haka sannan ya ɗago"ki daina kuka kinji ki daina tsoron mutane kowa ya miki abu ki rama ni nan na tsaya miki,wa ya ce ki taho ma salon wani abu ya same ki"kwantar da kaina na yi a ƙirjinsa ina ajiyar zuciya kace ƙarti goma ne suka zane ni,hannuwa na ya kama ya zaunar da ni leda ya janyo ya zaunar da ni baki gadon ya janyo ledar da ya shigo da ita take a way na nama yamin ba sanya ba jira na hau zaƙalƙalar abuna ina lumshe sai da na gama yasa ni a gaba nayi brush sannan muka fito a toilet ɗin da kansa yasa ni ajikinsa yana lallaɓa ta har nayi bacci ban sa ni ba da dabara ya kwantar dani sannani ya tashi ya fita tana rashe akan gado ya shiga ko kallon sa batai ba haka shima ya wuce toilet ya gama abinda yake sannan ya fito,shirin sa ya yi cikin kayan baccin sa masu kyau sai ƙamshi yake a bakin gadon ya zauna yana addu a ido yakai gareta yaga wuyanta ya yi ja ɗan matsowa ya yi ya duba yaga shatin yatsu ido ya zaro yana dafe bakin sa saboda dariya da ta ƙwace masa a ransa yake cewa'ashe da gaske take shaƙa tasha to amma Nana wane irin ƙarfi gareta da zata shaƙi babba haka"bashi da amsa hakan yasa yay kwanciyar sa a hankali gudun karta tashi dan tana tashi sunan baccin sa ƙarantacce Allah ya taimake shi kuwa har ya yi baccin ba ta iya motsawa ba,kiran Assalatu ne ya tashe shi da azama ya wuce masallaci sanda ya dawo garin ya yi haske ina zaune akan sallaya sai gashi ya shigo a bakin ƙofar ya coge yana murmushi"ina sonki Nana harkin tashi kinyi sallah"murmushi na masa ina ɗaga masa hannu,ƙarasowa ya yi ya zauna kusa da ni yana jawo ni jikin sa ɗagowa na yi na kalle sa ina murmushi shima haka fuskata ya shafa"ranar talata zamu wuce india ko nakai ki asibiti a duba min ke"kai na ƙara ɗaga masa sannan na kifa kaina a ƙirjin shi ina shaƙo ƙamshin sa mai ratsa zuciya da wannan na yi bacci shi kuma ya jingina kansa da jikin mirrow ya shiga tunanin rayuwar baya.
Yana jinginen sai maganar ta yaji akansa"sannu maci amana mugu kawai dan ba ta da lafiya sai kana ba ta kwana na wallahi bazan yafe ba"ɗago kai ya yi ya kalleta ya kaɗa kai kawai ya maida kansa yanda yake,abin da ya mata ne yay mugun ba ta hau shi sai taci gaba"kanrufe ido mana akan wanna ƙwailar batun yau ba ka ke min haka to ka sa ni kayi da ƴar halak saina lahanta ma ta rayuwa"ha ila yau shiru ya ma ta dan yanzu ba ya da lokacin kowa bare asa ma sa damuwa wadda yake ciki ma ta ishe shi,ina tsaka da barci naji masifa sama ta ka a razane na tashi ina dibi dibi yay saurin riƙoni ido da ido mukai da ita ja baya ta yi dan na bata tsoro cikin zafin nama na miƙe nai kanta kan tai wani yunƙuri na kai ma ta duka"muguwa muguwa mai ihu kawai"tasowa ya yi ya janye ni na kuma komawa ya ƙara riƙoni na ƙwace na koma kan nakai wurinta ta gudu,riƙo ni ya yi ya rungume yana jin yanda ƙirjina ke mugun duka ɗago kaina ya yi ya ɗora bakin sa kan nawa a jiyar zuciya na shiga saukewa shi kuwa sarrafa harshena ya shiga yi jikinsa sai tsuma ya ke leƙowa ta yi nan abin da ta gani ya ƙara ƙona ma ta rai tai tsaki ta koma"zaka zo ka samen ne malam in ka bari ka shigo ɗakina da yamma wallahi ba zaka fita ba",ya jima yana juya ni yadda yaso kamin ya zare bakin sa a nawa yana buɗe lumsassun idanuwan sa
kwantar da kaina nayi a ƙirjin sa ina ɓoye dariya ba shi ya barni ba saida yamin wanka ya shirya ni tsaf sannan ya kai ni wurin su Mama sai sannan ya dawo in da take shi wallahi in ma ya kalleta dariya take ba shi,saida ya gama shirin aikin sa sannan ta tare shi ya bata kuɗi zatai amfani da shi bai nemi ba asin komai ba ya ɗauka ya bata sannan ya fita to darajar wannan kuɗi da ya ba ta saita sassauto a fushin da take da shi,yana fita ba tare da ta faɗa mai ba itama ta fice dama bikin ƙanwar su za ai shine aketa feleƙe tun saura sati shida.
Yau ne tafiyar mu tun sassafe Habu da Umma da Baba suka zo zuwa nayi na rungumeta sannan na ɓuya a bayan ta har filin jirgin tare muka je da ita da ƙyar muka rabu,saukar mu ba jimawa su Ya Saddi'q suka zo ɗaukar mu Wallahi suna jin daɗi sun yi ƙiba sun ƙara zama farare,tunda suka ganni suke tausaya min ba ma da yana musu bayanin yadda nake ubana Ya Saddiq harda hawaye,sanda mukaje asibitin sun duba komai akan magani suka ɗora ni tunda sunce ai ba accident ba ne dama haka cocain take wasu ma inta haukata su basa warkewa sai dai mutuwa,bai damu ba tunda dai gani a gaban sa ai rashin nawa shine ɓarna,anan ma canja min gida ya yi ya shiga nuna min kulawa taban mamaki kafin wani ɗan lokaci na canja nayi fresh kuma yanzu ina ɗan ma sa magana ko na faɗi abin da nake so Habu nan su Ya Saddiq suka riƙeshi suna tafiya company tare gaskiya yasha mamakin yadda kayan kuɗi ke fita kullum ba almundahana ba cutar kowa haka ma aikata bakin ransu suke aikin dan ana bauta musu ana ji dasu komai na company da ban yake ƴan ƙasar dake aiki ma sunfi girmama baƙin.
Ba yanda ya iya magani baya aiki watan mu uku muka dawo tunda muka shigo gidan Aunty Mama ke bina da kallo"Nana me ke damun ki ne naga kin zama ƙatuwa kalli ƙirjin ki"murmushi kawai na yi"ke zonan"zuwa na yi na tsaya ta ɗaga rigata tana kallon cikina ɗagowa ta yi tana dariya"kice da Babyn ki ka dawo"saurin kallon ta na yi ta ɗaga kai da gudu na fita sai ɗakin Mama tana sallar nafila nai tsalle a gaban ta na ɗaga ma ta rigata ina nu na ma ta cikina sallamewa ta yi"ke kanki ɗaya kuwa miye hakan?"ƙafa na fara bugawa tai saurin riƙe ni"me ne ne kuma",a hankali na ce"waccan da nake a wurinta ce ta ce nazo da Baby"saurin zama ta yi a bakin gado tana kamo ni na zauna"da gaske ki ke","eh mana Mama"da hanzari ta kalle ni"Nana"gefe na kalla da sauri"juyo da kafaɗata ta yi"Nana nasan kin warke tuntuni miye na wannan abin kalla yanda ki ka sa kowa a damuwa haba Nana"fashewa na yi da kuka na faɗa jikinta"rungumeni ta yi tana shafa kaina"me yasa zaki na zama a haka"cikin kuka nace"Mama Abba in banyi haka ba za ana ɗaukar rai ɗaya bayan ɗaya a cikin ƴaƴan sa ","me yasa Nana","Mama kibar maganar nan dan Allah zan faɗa miki komai nan gaba kaɗan komai zaizo ƙarshe ne ranar da wannan ɗan na cikin yazo duniya don shine maganajin ba Babban Yaya da Habib ba suma basu gaji komai ba an san hakan shi yasa masu buƙatar abin zasu kawo kansu har inda muke","to shike nan ki tashi kije ki tafi ɗakin ki ko shara kya yi"tashi na yi ta biyo ni har wurin Aunty Mama tana dariya ta ce"ashe kaka zaki koma kwanan nan",tashi ta yi itama tana dariyar"sosai ma kuwa Dada gobe gobe nan zan tafi siyan kwalli saima na gayyaci Ma u dan nasan saita fi kowa murna dan ɗab Nana zai zamo laya tamkar da dubu ne","to Allah ya albarka ce shi","amin Dada godiya muke da wannan addu a",da kaina na tafi dan sun fita shida Habib saboda shigar safe mukai gyara ko ina na yi kafin shigar magariba dan Hajiyar gidan ba ta nan sai da na gama abin da nake sannan sai gata ta kamar tare suke tana shigowa shima yana shigowa wa ta fitar burgu na yi na bankaɗe ta na isa gare shi na rungume shi,taga taga ta yi zata faɗi ta samu ta zauna akan kujera da sauri ta kalle ni"keee mahaukaciya miye hakan ki ke yi kalla yadda ki ke nema kai ni ƙas me ke damun ki"a zafafe na yi kanta na ɗaga rigata na nuna ma ta cikina"Baby ne da ni kina so",wani wuuuu taji a cikin kanta saura kaɗan ta suma wani irin hayaƙi hayaƙi taji yana fitowa daga cikin idon ta,sama naji anyi da ni na kware baki zanyi ya juya da ni sannan ya dire"fuskata ya tallaba"ban taɓa jin labari mai daɗin wannan ba zo muje kiga wa ni abu",yaja hannuna muka fita,ta shi tayi tana wani kallon bayan mu,kwasar jakarta ta yi zuwa ɗaki a haukace ta lalubi wayarta ta dannawa yayar ta kira bugu ɗaya ta ɗauka"na kaɗe Yaya na shiga uku ance bazata haihu ba to wallahi ciki ne da ita kuma yarinyar ba ta ƙarya","kwantar da hankalin ki Hajar ciki a jikin mahaukaciya i bazai wahalar cirewa ba..."fauce wayar na yi"bada wannan cikin mahaukaciyar kina jina tsohuwar kilaki ƴan barikin zuwa lahira da ƙafa ke dai ina ganin da ƙafarki zaki lahira bata ƙarshin ƙasa ba anya kuwa ke mutum ce ace ke dai baki da aiki sai raka mutane halaka to wallahi baki isa Aunty Hajara ba zata taɓa zama bazawara ba in kin kashe ma ta aure in ya ya da mijin ƴar ƙanƙanuwa dani kuma cikina a hannun ta zata ɗauke shi tunkan a mai wanka kashe wayar nan kan na faɗa ma ta kin fita marmarin miji..."wuff ta kashe wayar ,juyawa na yi gareta na miƙa ma ta wayar"an faɗa miki a haka zan ta zama ne ban warke ba kin san tamsil inji balarabe to wannan shine kuma kin faɗa na warke ba mai yarda dan uwara tasan na warke Gwaggo na ta sa ni kune dai baku sa ni ba kuma bazaku taɓa sa ni saina haihu na kama ɓeraye a tarko"ina kaiwa nan na juya na fita,bina ta yi da kallo tana mamakin yanda nake abu jikin ta ne ya yi mugun sanyi nan taji wani mugun kuka yazo ma ta nan ta fashe da shi" wannan wace irin rayuwa ce Abba duk kai ka sa ni waɗannan abubuwan nasan ina kishin ta amma bana son mijinta ya rabu da ita dan in ya sake ta ni me zan sa mu da ita na ganshi da ita na same shi sai ace saina rabasu gashi ita tana da cikin ni kasa ni na lalata mahaifata ban san dalilinka na yi hakan ba Inna Fulera ta taya ka na lalata rayuwata ƴar mitsitsiyar yarinya zata haihu ni ina nan"kuka ne ya ci ƙarfinta ta yo hanyar fitowa nai ma za nabar wajen wani irin tausayin ta ne ya kama ni tabbas ita mace ce mai kishi amma abubuwan da take nasan sa ta ake da ace iya kishin ne nasan ya zanyi da ita amma matsalar an sata a hanyar banza da wannan hanyar ya kamata na fara rabata kafin tonuwar asirin iyayen ta bana son komai ya shafeta sai dai ya tsaya iya su dan mijinta na aura duk da ba ta yara amma ai mijinta ne ni ce nai ma ta kutse,na da ɗe ina wannan tunanin sannan naje nayi wanka na kwanta koda ya shigo ya gan ni ina bacci fita ya yi yaja min ƙofar juyowa na yi ina tausayawa rayuwar su shida ɗan uwansa amma Allah ya kawo mana ɗauki.
UMMU SADDIQ CE
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
BABAN YAYA
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
37
Tana tsaye jikin mirrow ya shigo da sauri ta nufo shi"ya Nanan ta ke?"da mamaki ya kalle ta sai kuma ta basar tana ɗan in ina ta ce"am am ya Nana?"zama ya yi a bakin gado yana kamo hannun ta"kinga Hajara Nana ba ta da matsala da, ke ki ke janta da rigima bari na faɗa miki kina wa Nana kallon yarinya amma tunda ta tazo gidan nan take wahalar da ke ina sa ne da komai kuma ina lura da ke bata taɓa janki da faɗaba ita sai dai tsokana zan roƙeki dan Allah badan ni ba kinga ni namiji ne dole zan fita kinga dai halin da take ciki ki taimaka ki taya ni kulawa da ita"zama ta yi tana ɗora hannun ta akan nasa"namaka alƙawarin bakin raina zan kula da Nana komai na da ya wuce Wallahi zan kula da Nana ka yarda da ni",murmushi ya yi"na yarda da ke saboda dama can ina yarda da ke kece kawai ki ka canja komai tashi ɗaya daga sanda ki ka fahimci tsakanina da ita Hajara Nana ta shiga rayuwata tun tana zanin goyo shi yasa ban bari kowa ya shiga rayuwar ta ba sai ni ɗaya na dasa ma ta yadda zata so ni ne tun ba ta da wayo shi hakan da na ma ta shi yasa kwata kwata Nana akaina ba ta da kunya koma kome girman ki ki ka nu na kina so na tabbas zata tsaneki kome zaki ba ta kuma bazata soki ba ke Nana tana da ƴan family in wata tace ina burgeta to ta daina kulata in ma zata kulatan to kullum faɗa ne aikin nasu,halayen Nana ba zasu fasaltu ba amma ke tana raga miki harma tasan cewa in ta saɓa miki ba ta kyauta ba tunda mijin ki ta aura amma fa da ita ce farko to da bazata taɓa ɗaga miki ƙafa ba Hajara kin san me na sakawa Nana da shi a duk wannan soyayyar da ta ke min da waɗannan hannauen nawa da wannan gangar jikin nawa wasu shashashai suka saka ni na gana ma ta azabar da ko maƙiyinta ba zai ma ta haka ba nasan baki fahimta ba naso na raini Nana ba tare da tasan me ne aure ba duk wannan feleƙen da ki ka ga tana yi batasan me ne auren ba amma hakan bai samu wai ni ne na maida matar aure a gaban ƴan fashi dalilin da ya kawo wa Nana jinya da fita hayyaci na tsawon watanni hakan yasa na gujeta saboda ina tunanin ban kyauta ba sai dai yarinyar ita nema na tavke ido rufe ta yi ciwo ta yi kuka duka akaina haba Hajara yanzu wannan yarinyar ba ita ce ya kamata a aura ba ya kamata ta zama kishiya ba,kin san wa zan kwaso in ban zauna da Nana ba"fashewa ta yi da kuka sosai"innanillahi wa inna ilaihi raju un dama abin da ka aikatawa yarinyar da ta ke matuƙar ƙaunar ka amma yarinyar kullum nu na wa take a sauƙi komai yazo ma ta wayyo baiwar Allah dama tafiyar da kukai ta dawo ita ɗaya kana bin ta a baya baka magana da ita wallahi ka nemi yafiyar yarinyar tun kafin Allah ya yi fushi da kai",tashi ya yana zagaya ɗakin"Hajara tun kafin na nemi yafiyar ta yafe min sai dai ni yanzu ya wajaba akaina na kare lafiyar ta da taimakon ubangiji da taimakon ki saboda Nana na dawo da Habib nan da aiki amma zai koma ƙasar sa bayan wasu shekaru",ta shi ta yi"to shike nan Allah ya mana jagora amma zaka fahimci matsaloli daga gareni dan Allah kar kai min muguwar fahimta","na fahimce kinkice halayen dai baza su sauya ba agaban mutane amma a baɗine ke ɗin kin canja",murmushi ta yi kawai ranar cikin farin ciki suka kwana.
Tun farar safiya na tashi yana zaune bakin gado yana kallo na da mamki nake bin sa da kallo sannan kuma na lura da ita tana tsaye jikin window kallon rashin fahimta na musu dariya ta matso tana yi"kin ganmu cirko cirko ko gadin ɗan Babban Yaya da Nana masifa muke"shi kansa sunan da ta faɗa saida ya yi dariya ta shi nayi ina musu alamar ina kwana wani kallo tamin a ranta tana cewa"wannan sheɗaniyar yarinyar wallahi tai tsawon rai za ai kallo Allah yasa ɗan ya yo halinta shike nan mun samu gidan kallo a gidan mu",abin mamaki kwana goma sha shida amma banga wani mugun hali ba tare da ita sai dai ni kota ƙyaleni saina tsoka ne ta sai naga ba ta fushi tun daga nan na fara sakin jiki da ita sai na ga taji daɗi,matsalar farko da ta fara fuskan na lura hakan kuma shine ƴan gidan su kusan kullum sai sunzo ko Abban ta ya turo ta je sautari takan ɓoye ɓacin ranta inta ganni amma batasan na riga na ɗago ba.
Bayan wata biyu cikina ya tonu kowa ya sa ni a sannan yana da wata biyar dai dai amma fa iskanci sai abin da ya yi gaba yanzu Babban Yaya hankalin sa kwance ya ke yama yi tafiya kaf dangin suna ba ni kulawa da sunan mara lafiyar tunani Umma bata barni ba nima haka kuma a ɓoye ina kula da su sosai suna rayuwar sa ada.
Yau da azahar ina ɗaki baccin ƙailula naji hayaniya fitowa na yi da ciki ina turo shi Aunty Hajara ce da yayar ta ta yi kicin da rai tana gani na taɗan harare ni ina ganin haka na gane mugun nufi aka ƙullo kenan yayar ta ta ce kalle ni"sannu masu ciki"ban kalle ta ba na kalli Hajara"Umma zanci abin ci",cikin sauri ta ɗago ta kalle ni a ran ta ce"wannan tashar kuma aka kama Nana"tasowa ta yi kama hannuna"zo ki koma ɗaki zan kawo miki kinga nan na yi baƙuwa",haɗa ido mukai da yayarta ta na ɓalla ma ta harara"kar ki yarda da wannan zubin ƴan wuta ne da ita",zaro ido sukai atare suna kallon juna cikin zafin nama ta taso"ke mahaukaciya nice mai zubin ƴan wutar"kai na ɗaga"eh mana yanzu ba munafirci Babanku ya turo ki yi ba in ki ka kuma zuwa gidannan saina tona masa asiri a duniya harda ke karuwar gida",da sauri Aunty Hajara ta rufen baki"muje muje karki tonawa kowa asiri dan Allah wannan fitinar ta ki bazata haifar da ɗa mai ido ba",ɗaki ta shigo da ni ta sake ni dariya ta saki sai kuma ta kama bakin ta ta fito tana zare ido tare ta ta yi"kin gani ko Hajara ki zuba ma ta wannan maganin kawai ta ƙara sa haukacewa duka"karɓa ta yi"an gama Yaya amma yanzu ki tafi dan tana kuma ganin ki zata kawo duka kuma gata kamar doki shekaran jiya da ƙyar na sha a wurin ta","ai shine ki ma ta amfani da wannan maganin ta fice ma a gidan dama cikin tana sha sai wa ni",da di hakan ta rako ta ta tafi ɗakin ta ta wuce ta zuba maganin a masai"Allah ya tsare ni haukata wa ni da ɗin ma da na yi niyya na tuba kuma dama ku ku ka zagani","nagode Aunty Hajara",ta ji an faɗa daga bayan ta jiyowa ta yi"ba komai Nana gwara ma da nasan halin su kinga a yanzu na samu damar gane sirrin su",murmushi na yi"zo muje kiji wa ta kitirmurmura dana ƙullawa Innar ki"biyo ni ta yi tana dariya har ɗakina zama ta yi kan sofa na je can ƙuryar gado na ɗaga capet na ɗakko wani file na dawo inda ta ke zama na yi na ɗora ma ta akan cinyarta"buɗe ki ga ni",zazzago su ta yi ta fara dubawa ta shi tsaye ta yi"Nana mi ye wannan?","abin da ki ka ga ni haka ya ke takardun da ki ke nema ki kaiwa Abban ku bana Hajiya Fulera ba ne na ki ne",zaro ido ta yi ta zauna jaɓar duk ac dake a ɗakin amma fifita take da hannu"ban ga ne ba Nana","yanzu zaki ga ne Abba bai bawa Hajiya Fulera komai ba suanyen da ta ga ni liƙawa akai amma ba na ta ba ne kuma an ba ta tasa hannu a matsayin wakiliya ni nasa hannu a wajen da zaki sa saboda nasan sa hannun ki ke ma baki san na sa ni to wannan sirri ne kar ki ga no ni","wallahi saikin faɗan"dariya na yi"zan faɗa miki amma akwai wata a ƙasa zan faɗa miki kamin kowa ya faɗa miki kimin alƙawarin riƙe wanna har sanda abin zai tonu","na miki alƙawari Nana",ɗan sunkuyar da kai na yi sannan na kalle ta"ba Abban ku ne Baban ki ba kuma Hajiya Fulera ita ta kashe Mamar ki shi yasa ba sa son ki suke saka ki akan hanyar halaka..."
Miƙewa ta yi tare da watsar da takardun hannun ta cikin lokaci ƙalilan hawaye ya wanke ma ta fuska kafaɗata ta kama jijjaga"ke Nana kalle ni nifa ba sa ar ki ba ce kar kiga na fara kulaki ki tarwatsa min tunani",kama hannun ta na yi ta zauna"ki nutsu Aunty Hajara wallahi tunda na ke ban taɓa ƙin ki ba na dai tsani ƴan uwanki tabbas shi yasa na ke miki waɗannan rashin kunyar kuma da kin lura da faɗa da ki ke da zagi kwata kwata basa miki kyau kawai zuga ki da ake shi yasa ki ke min haka Aunty Hajara Mamar ki kishiyar Hajiya Fulera ce watarana Yayan ta wato Abban su dan ba Abban ki ba ne shi Abban ki mutum ne nagari shi kuma wancan saƙagon ɗan iskan ba Abban ki ba ne ko Abinci da ya ba ki da kuɗin mamar ki ya ba ki kuma ki ka yi karatu,Yayan ta yazo sai mamar ki tazo wajen ta da niyar magana sai ta shiga ba tare da ta nemi izni ba dan ta ɗauka ma ba ta nan al'amarin da ta gani ne ya sata naƙudar dole Hajiya Fulera da ɗan uwanta na fasiƙanci,tasowa sukai ba kunya suka kaita asibiti dan Abban ki sannan bashi nan yana wurin aiki can Lagos,bayan kaita ta haihu lafiya sai suka samo Allurar guba suka ma ta nan cikin lokaci kaɗan Allah ya ɗauki ranta ana mutuwar suka turama Abban ki da saƙon mutuwar bawan Allah garin ya taho cikin tashin hankali a motar sa zuwa tasha yay hatsari ya mutu shine saboda baƙin muna firci Yayan na ta ya ɗauke ki wai ita Hajiya Fulera aure zata yi Umman ku mutuniyar kirki ita tai miki reno na tsaka ni da Allah dan nonon ta ta ba ki sannan ita ta haihu amma ɗan babu rai",fashewa na yi da kuka itama ta shiga rera na ta kamar ranta zai fita tana riƙe da hannuna"Nana kina ƴar ƙarama kanki ya iya ɗaukar wannan babban al'amari haka dan Allah yafe min duk abin da na miki wallahi ba a son raina ba be",sakkowa na yi na zauna inda ta ke"ai wannan masu saki keda haƙi ko kin manta ni ba abin da ya same nifa asiri ba ya kamani dan bama asan a watan da aka haife ba kansu sukai wa kuɗin ki da ki ka ɓa ta in sun aje nasu kin gani ki sace kawai",dariya ta yi na shiri"kefa bakya faɗar abin arziƙi kullum saina tsiya sata kuma zaki saka ni",nima dariya na yi"to ai Aunty Hajara ni ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 32