albashin ma'aikata acire na kayan aiki sannan ku raba sauran wannan da zaku raba shine zaina zama asalin dukiyar ku na kayan aiki kuma sune na company za anayin hakan har sai kowa ya maida kuɗinsa kunga company ya zama ria kenan in an gamashi kuma baza'a karɓi hannun jarin kowaba sai wannan magana ta farko ta gama haɗuwa sannan za a bawa kowa damar shiga ayi dashi kama daga nan ƙasar da sauaran asashe,wannan aiki za haɗu ne ta hanyar ɗan kwangila Ni kenan babu wanda zamu ɗora mu zamuyi komai da kanmu kuma sauran masu ƴaƴa irina kowa ya nasa ya fito sai kowa ya hau kan abinda yafi ƙwarewa akai da Dr Kumar haƙƙin nemo wajen siya wato fili da ma'aikata da gamsar da tsaretsare na ƙasar su yana wuyansa,wannan ne zaisa bazamu matsala ba amma tabbas idan aka nemo bare to za ayi mana ƙisa kuwa,ni da zan jagoranci aikin zan zana wurin zannan kowa yana office a cikin ku kuma zai baza komar neman ma'aikata masu ƙwarewa akan hakan nan da can ƙasar,nayi alƙwarin wannan aiki bazan karɓi ƙwandalar kowa ba har agama shi muji dai da waɗanda zamu iba aikin,ku duba maganata",zama ya yi yana binsu da kallo kowa ya shiga hankalin sa sunji bayani zallar basira kaifin tunani da hangen nesa samun riba da haɓɓaka cigaban ƙasa samar da aiki ga mutane bila adadin kenan an rage ɓata gari an taimakawa masu buƙatar taimako,kowa ya gama nutsuwa da ƙyar Alhaji Abubakar jega ya buɗe ya yi kabbara"ALLAH YA MAKA ALBARKA YARO",sai asannan kowa yasamu bakin magana ana ta amen kuma ana gaisawa da juna alamar sun karɓa kenan,magannun amincewa ke tashi anan ɗaya daga cikinsu ya fara magana"to Alhamdulillahi dama haka Allah yake ikonsa duk mu ba muyi wannan tunanin ba gaskiya mungode da sako ɗanka da kayi a cikin wannan al'amari da tuni mune da danasani","haka zancenka yake Alhaji wannan yaro Allah ya masa albarka Alhaji Aminu mun yadda da duk abinda ɗanka ya faɗa kuma da zai tsara nan gaba kawai bayaninka zamuna saurara kuma ƴaƴan mu kaf zasu zo gareshi can garin kanon sai suna shirya dukkan abinda ya kamata tare saboda suna ƙara samun hasken kai irin nasa",shima tashi ya yi"ina godiya a gareku amma kusani wallahi bai faɗamin komai dangane da wannan ba anan ya tsara komai nasa nima bani da masaniya kan me zaice to nima nabi sahunku mungode Habib",dariya sukai nan sukaita bashi goyan baya Dr Kumar na sanar musu sati mai zuwa za'a fidda wakilai su tafi tare dan a samu wuri mai fasali asaya kamin nan kuma zaisa afara duba masa wurare masu kyau da fuska,asannan ya miƙe yace inada magana"kuyi takardar kunjanye bada hannun jarinku a wancan company ku aikawa musu dan nasan suna can suma suna shirya yadda zasu cucemu","hakane"kowa ke faɗa,sunfi awa huɗu tun 8 sai shabiyu da rabi sannan taron ya tashi ko gajiya ma basu yiba,Abdallah ɗan Alhaji Salihu ɓaɓura da Is'haq ɗan Alhaji Balarabe kano sai Sulaiman ɗan Alhaji Abubakar jega sune suka matso inda yake"aboki sannu da ƙoƙarifa",hannu ya basu suka gaisa"karku damu nan da lokaci kaɗan komai zai dai daita mu zama abu guda","hakane to zamu wuce saida safe mu anan muke kaga mayi sallama ko kafin ku wuce","ba matsala Allah ya kaimu",suka wuce sannan kowa ma ya kama gabansa ransu fess.
Har ɗakinsa Alhaji ya rakosa yana tafe yana kallonsa mamakin yaron yake ashe ganin da ya masa a titi baiga komaiba yaron baiwa garesa a ɓoye,kallonsa ya yi yace"Habib lamarinka ya ɗaure min kai sosai wallahi amma bari da safe mayi magana ka faɗamin da yaushe kayi wannan hasashen kai daka san maganar jiya ni da najima da sanin maganar ma banyi wannan tunanin ba kwata kwata ko ince mu",ya faɗa yana dariya,shima dariyar yabyi"karka damu Abba wannan mai sauƙi ne nayi wannan tunanin ne tun sanda ka faɗa min naga ba hannun jari ya kamata ku sa ba kamata ya yi asa muku kuma wallahi kaji na rantse waɗannan turanwan wayo sukai niyar muku dan sunsan kaf ɗinku baku da kotun da za'a iya gurfanar dasu nasan irin waɗannan matsalolin na karanci halayensu sosai alittafan tarihi da dama da kuma maganganun manya na ƙasar hausa dake a ƙunshe a waƙoƙi da kuma takardu,muddin kaga bature ya maƙalewa abota da kai to tabbata kanada mamora mai gwaɓi danshi baisan faɗuwa ba sai riba shi yasa baya jure baƙinci sai ya kashe kansa in daɗi ma ya masa yawa sai kashe kansa",ajiyar zuciya Alhaji yayi"lallai kai mai ƙwazone kuma ina jinjinawa iyayenka fatan zasu bani aron ka",dariya ya yi kawai yana shafa kansa"Nana ko bazaka iya tahowa wurina ba mu zauna saboda ita",da sauri ya ɗago kai ya kalleshi"ba haka bane Alhaji","hakane mana amma dole ta haƙura wannan karon kaima haka da hakane zata gane cewa waye kai sannan kaima zaka gane wacece ita bayan mun koma zanzo naga iyayen naka","to shikenan Abba Allah ya kaimu lafiya"sannan ya fito zuwa nasa ɗakin dake can sama,shi kuma ya cire kayan ya watsa ruwa abinci yaci ya ƙoshi sannan ya janyo wayarsa 1:45 am kwanciya ya yi yana tunanin yanda zai fara rayuwa ba Nana.
Vote
Share &
Comments
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
chapter 1️⃣1️⃣
*****
Ana sallar magariba kaf ɗinmu muka shige gidan Iyyo rawa tai tayi ita dai Allah ya ma ta gata jikoki ta ko ina dariya mukaita ma ta anan muka raba dare sannan muka shigo gida Ya Usaina ce ta kwanta a gadon Aunty Mama da yaranta na shigo kenan na hangesu har sun yi bacci"kam bala'i wallahi kowa bai isaba a ƙasa ake nufin zan kwanta lallaima"fuuu na fito daga ɗajin Aunty Mama na falo naje na tasheta hannuna ta kama zuwa ɗakin saboda masifa na cina na manta tana jingine katifa janyo min ita tayi na kwanta kai sannan ta fita ta koma ta kwanta,ina kwanciya bacci ya sace ni.
Da safe kafin mu tashi su Mama har sun gama abin kari,dama al'adar gidanmu kana tashi da wanka zaka fara shi yasa kullum bama rabo da ruwan ɗumi,yanzun ma wankan mukai sannan kowa yaja abin karin sa mukai da'ira kamar a tsangayar ƙauye.
Yaran Ya Fatu shida babbar itace sa'ata sai yaran Ya Usaina guda huɗu muka shirya zaga gidajen iyaye nice a gaba ba kwalliya ba komai sai doguwar riga da ɗan hijab dana saka,gidan Kawu Nuhu muka fara zuwa har kayan daɗi ta bamu dan tana gullisuwa da alawar madara,sai gidan Kawu Rabilu Umman su Ya Sumayya ce ta kula mu amma Haule ko kallo bamu isheta ba shi yasa muma da zamu fito ko kallonta bamuyi ba munaji tana mana habaici,sai gidan Kawu Iro shi kuwa aƙofar gida muka haɗu da gudu ya koro mu wai bazamu shigar masa gida ba harda zagi wai shegu masu kama da fara,haƙura mukai muka tafi gidan Gwaggo Asama'u jan magana dan munsan koro mu zatai amma sai mukai sa'a batanan ta shiga unguwa tsurku shi yasa mukai zaman mu da Ya Fatsima har ɗanmalele ta mana mungama muna wanke hannu ta shigo katsam sai idona cikin nata"lalala a gidan wa ku kai wannan abincin har ku ke tanɗe baki kamar baku taba cin abinci ba",ɗagowa nayi na kalleta"a gidan Gwaggon wadda har lahira uwarmu ce mukaci in wata zuciyar ta isa ta kore mu tace mu jininta bane",saƙare Gwaggo Ma'u tayi tana dubana tama kasa magana,Baba dake a bayanta ya yi dariya"to sannunku yaran Gwaggon su",juyawa tayi ta harare shi sannan ta wuce ciki fakan fakan,cikin raɗa nace"ku ɗakko hijabanku mu gudu kan ta fito kunsan ta sarauniyar mazga ce su Ya Fatsiman ma mazgar su take bare mu ƴan tsaki",ai kuwa da sanɗa muka janyo hijaban mu duk manja muka silale muka gudu Ya Fatsima sai dariya take,muna fitowa saiga Ya Hadiza wani ya ajeta a mota hararata tayi,na kuwa cije baki araina nace 'zaki gane baki da wayo'sai nayi sauri na ƙarasa ina yafito su Hameda da hannu ina zuwa saina duƙu har ƙasa suma sukayi yarda nayi "ina wuni Yayan mu",yashe baki ya yi"lafiya ƙanne na ya ku ke","lafiya lau Ya Hadiza ina wuni",wata harara ta zuba min a fakaice amma saita washe baki"lafiya lau Nana Hameda kunzo lafiya","au ƙannen ki ne da sauri na rigata magana"ni ƙanwarta ce su kuma waɗannan ƴaƴanta ne","kina nufin yaran Yayarta","yauwa ka gane ashe"tare mukai dariya hannu yasa aljihu ya fiddo kuɗi ƴan ɗari ɗari ya bamu kowa biyar biyar gamu da yawa mu shaɗaya ne dan har ta goye muka ɗakko,godiya mukai muka ƙara gaba muna karya kwana muka fara dariya dan muna kallonta kamar ta warce kuɗin,muna shiga gida aka fara lafiyanku Ya Fatu muka bawa kuɗin muna bata labari"ai kuwa ku shirya cin ubanku dan saita daki kuɗin saurayinta da ku ka karɓo",kar kace ƙugu nayi"wallahi bata isaba tunda ba danneshi mukai muka ƙwata ba kuma ba roƙarsa mukai ba ko ya kika ce Hameda","hakane ƙawata uwata",taban hannu muka tafa muna shigewa ɗaki ana wata dawarar,kai kawai Mama ta girgiza tana kallon Aunty Mama"wallahi uwar Nana rayuwar ƴarki na faɗar min da gaba ta iya kissa ta fitar hankali ga wayon masifa anya kuwa za'a wanye lafiya inta girma","kina ma ta addu'a Dada kamar yanda nake ma ta ni kaina Nana tsoro take bani kinganta fa amma inta kitsa abu ni kaina tunanin taya tayi hakan nake","addu'a kam zamu ƙara dagewa amma akwai babbar matsala agaba dan ina hangota kuma koda ubanwa muke yawo kinsan alƙawarin Iyyo baya tashi","hakane kam to Allah ya fisshemu alkhairi akansu baki ɗaya","ameen Halima mijinki yau banji ya kira waya ba","eh kinsan abi sai a hankali ƙila ya kira zuwa anjima","to Allah yasa lafiya",suna aikinsu suna hirarsu Ya Usaina nata musu vedio da wayarta tana dariya wai wallahi saita nunawa maƙwaftanta ga iyayenta su sun zauna kishi kullum gidajansu kamar filin yaƙi duk akan namiji wanda yake fita batare da sunsan ina zashi ba kai mata sun haɗu da wahala ki gama haukarki ya auro miki yarinyar da kika fi yadda da ita alayinku wadda take shigowa gidanki tayi yadda taga dama kai wallahi Allah ya sauwaƙawa maza,wayar Aunty Mama ke ƙara ta ɗauka ta duba Babban Yaya ne ɗagawa tayi tana amsa sallamar da yake ma ta"sai yaushe kuma Habib","ban sa ni ba dai Aunty Mama amma da wuya mu shige gobe","to Allah ya bada sa'a nasan dai mutuniyar ka ke nema ko",kamar tana ganinsa ya shafa kansa yana murmushi,kira naji Aunty Mama na feso min da gudu saura kaɗan na bi takan ƙwaurin Ya Usaina ta janye ƙafarta,wayar ta miƙo min tana faɗin "Yayanku ke magana",karɓa nayi naja gefe na durƙusa"hello Darling Yaya",tacan lumshe ido ya yi yana cizon lips ɗinsa"hello Darling Nana","ni Babban Yaya fushi nake da kai","akan mi",ya faɗa muryarsa can ƙasa"sai fa yanzu ka neme ni tun jiya daka tafi","am sorry Darling Sis jiyan bansamu kaina da wuri ba sanda na nutsu kuma dare ya yi bazan iya kira ba","um um bayan da ƙyar nayi bacci",na faɗa ina kwaɓe fuska,numfashi ya furzar"sorry fa nace","tom Darling Yaya ammanka dawo yau","an gama tawan me zaki tanadar min","um zanma wainar fulawa mai ƙwai da yawa aciki","ok ni kuma zanyo miki tsaraba wadda zata dace da wannan kyakykyawar surar taki",ƙyalƙyalewa nayi da dariya"Sweet bro dama ina da kyau haka","kaiii karki kuma wannan tambayar a fuskokin mata kaf waɗanda ke gilmawa a idona ko farcenki basu kama ba","Allah Sweet bro ka fini kyau ai","mari bakinki maza kan nazo kinyi saɓo",dariya nayi"hunm ai dama bazaka yadda ba amma wataran za'a baje wannan musun","ina fatan Allah ya nuna min wannan rana dana fi kowa farin ciki",nocking ƙofar akai"Nana kashe zan kira ki anjima anzo wajena ne","ok Darling Yaya karka kula mata fa","an gama Sweet sis"cire wayar nayi na kashe na miƙe arba nayi dasu Ya Fatu sun min duru duru,"zo nan dan ubanki abin naki har yakai haka ina ki ka koyi wannan lanƙwasa muryar da waɗannan sunayen","kai Ya Fatu harkin tsorata ni na zata bakya duniyar ai danaga kiyi foster,ni me nayi wai","zonan Usaina kinga makirar yarinya tun tana ƴar ƙarama","bari Maman Hameda wallahi na kasa magana ma",zuruu na musu danni banga me nayi ba suke wannan abin,"jeki Nana ta"Aunty Mama ta faɗa,wayarta na miƙa ma ta na shige ɗaki raina fess amma da duk cunkus nake jina,Aunty Mama ce ta kallesu Ya Fatu"ku basai ku zaunaba ƙaramar yarinya ta sace zuciyar ƙaton saurayi irin Habib bari na faɗa muku Habib ya gama mutuwa kan Nana ko wannan zancen auren da ake kamar dole ya zame masa dan baya ta kowacce sai Nana kunganta dai in Nana na kusa da Habib wallahi baya gane mutane sosai sai ita,mu kanmu abin mamaki yake bamu yadda yarinya ta iya sarrafa murya haka ta iya salo daban daban agaban Habib shi kuma duk sai ya rikice waccan goɗimar Ruma Hashim take so shima haka amma kowa ya kasa faɗa saidai ku duba yanzu haka kaf unguwar nan indai kana da hankali kasan me yake tsakanin Nana da Habib",ajiyar zuciya sukai suna jinjina kai"wallahi nima dai zan sauya caɓ kalli yadda jaririyar yarinya ta mallake namiji kamar wata uwar mata js 2 take duk da hakama a karatun dan tana da kwanya ne tai nasarar yin gaba haka","hakane kam Usaina lallai akwai kallo a gidan Babban Yaya Nana da kishiya","ni ai Maman Hameda har matar ta fara bani tausayi",Mama dake gefe kawai ta kaɗa kai tace musu "ai ni akan Nana tuni nake tausayawa duk wadda zata raɓi Habib tana kusa kuma wai a haka Alhaji Baffa ke cewa Iyyo ma haka take sai dai tanada kawaici da shanye al'amari kuma Nana ma haka take","ai Mama ba tambaya bakiga mugun son da take ma ta ba ido rufe kamar wasan drama","ai saiku tayata da addu'a Allah ya sassauta lamarin dan Nana a sha'anin ta za'a sha famar gaske ba wai na rigima ba zatasa shi ƙin aikata dai daito acinkin gidansa muddin tana da rabon shiga","lallaikam Mama to Allah ya shirya wannan kissa ta Nana",Umma ce ta shigo nan labari ya ɗora har ita akan Nana dai.
wayyo ni jama'a
Hhhhhhhhh
******
Tashi ya yi ya buɗe ƙofar yaga Abdallah da Is'haq ne,matsawa ya yi suka shigo yana musu sannu da zuwa,dawowa ya yi suka gaisa"badai shirin tafiya kayi ba",kansa ya shafa yana murmushi"na dai shirya ne amma sai anjima zamu tafi","gaskiya aboki ka haɗu sosai dama akwai mutane masu kishin ƴan uwansu a ƙasar hausa har yanzu kasan anwa bahaushe shaida kan beson cigaban ɗan uwansa"gyara zamansa ya yi yana murmushi"wannan ra'ayin wasu ne da kuma camfawa da akayi amma miye dan wani yasamu cigaba ta hanyarka ai abin farin ciki ne,kuma kowa zai iya taimakon kowa da izinin Allah in mutum ya ƙudurta","hakane",cewar Abdallah"amma a wannan zamanin masu zuciyar hakan kaɗanne sai dai fatan dacewa a wannan rayuwar dan asamu tsira ranar gobe","tabbas to Allah yasa mu dace",Babban Yaya ya faɗa,hira sukai kamar sun jima da sanin juna har saida Alhaji ya shigo sannan suka kuma fita tare mutane daban daban yay ta haɗuwa dasu dan Alhaji da gaske yake ya maida shi ɗa na halal,basu samu hutuba sai bayan la'asar sannan suka wuce airport.
******
GIDAN GWAGGO ASAMA'U
"Ke Fatsima ubanwa zai miki wannan wanke wanken kin tara yara sun ɓata min gida dan sakarci har kina dafa musu abinci tunda ke ki ka aje min",da sauri ta fito ta ɗauki omo kan windo ta nufi bakin rijiya amma ƙala bata ce ba"au ina miki magana kin maidani banza","kiyi haƙuri Umma bazan kuma ba","kaiii kima kuma mana ai saikin je gidajan su kin anso min abuna"juyawa tayi kawai ta fara wanke wanken tana sauri gudun wata fitinar,Baba ne ya shigo yana dariya ya kalli Fatsima"ƴata Fatsima albishirinki",tana dariya ta juyo"goro Babana","gobe zaki makarantar da zaki zana jarabawa a miki tambayoyi kawai saiki koma can ki ƙarasa",wani miƙewa tayi tana tsalle"wayyo Baba amma naji daɗi sosai Allah ya kaimu goben","ameen gama aikinki kizo kiji","to Baba gani nan",ta saurin duƙawa tana ƙarasawa zuciyarta kamar ta fashe dan murna ko a ina Baba yasamu kuɗin canza ma ta makaranta,tsaki Ummansu tayi"aikin banza kawai kalli yadda ku ke wani abu kamar ƙananun yara",ko kula ta ba wanda ya yi Baban da ciki zai shiga amma yay fitarsa yana kallon Hadiza amma ko kallo basu ishesa ba ya kuma wuce su ita kuwa banzar ko tacema saurayin ga Babana saima ta ɗauke kai,Fatsima na gamawa ta kwashe kayan ta wanke wajen ta zari hijabinta"Umma na tafi na samu Baba a waje",bata jira me zatace ma ta ba tai wuf ta fito tasan tsaf zata hanata,ilai kuwa Umman niyar dakatar ta take amma kafin tayi magana harta kai soro,tsaki tayi"kuyi tayi keda shi amma agidan nan sai anmin aikin komai sannan za'a wata makaranta ta ƙaƙale"ta miƙe tana buga cinya Hadiza ce ta shigo kaya niƙi niƙi da sauri Umma ta tareta"ƴar albarka har kin dawo lale maraba ƴata", *('kuji saikace wata wadda tazo daga wata uwa duniya kuma wai tana tambatar harkin dawo')* ,tsaki ta ma ta"Umma wannan yarinyar mai zubin aljanu sainaci ubanta wallahi",kayan ta aje ta riƙe ƙugu,cikin fushi Umman tace"waye ya miki wani abun badai waccan shegiyar yarinyar ba Fatsima","inafa Umma Nana mana wai wannan yarinyar ta jawo yaran nan duka hartana wa saurayina bayanin su suwaye kuɗin dazai bani ya kwashe ya raba musu","lahhhh amma wannan yarinya ko ƴar buƙulu yanzu haka ta miki zan kamata kuwa saina ma ta kashedin ko a hanya ta ganki karta kuma nuna tasanki","yauwa Umma dama kinsan in ni na ma ta magana saita ma ga dama zata fuskanci me nake faɗa","barni da ita kinji taho",suka shige ƙuryar ɗaka.
"Assalamu alaikum Baba gani","zoki zauna ƴata",kan bencin da yake ta zauna"Fatsima ɗazu nayi wani baƙo nima bansan sa ba yazo min da maganar yasan inada ƴaƴa amma sun daina makaranta to akan maganar yazo duk maison karatun shi zai ɗauki nauyi take na gaya masa akwai ke ɗaya kina aji biyar yanzu dan nasan ko nace da Hadiza bazata yi ba","amma Baba ai daka gwada","ki barshi kawai yanzu nifa Hadiza ko gaisuwa ba ta haɗa ta dani koma ko a ina zata ganni bata kulani","nasani Baba kana ma ta addu'a kawai Allah ya shiryeta","ina ma ta ƴata amma zan ƙara kije gida ki gama aikin kafin lokacin islamiya ko","to Baba nagode sosai",ta tashi ta tafi Baban nabinta da kallo"Allah ya yiwa rayuwarki albarka fatan karna mutu sai kinga tushenki Fatsima badan Yayanku yace karna faɗa miki gaskiyar sanadin karatunki ba dana faɗa miki Allah ya miki jagora.
******
Suna sauka a filin jirgi sun nufo motocin da zasu ɗauke su Alhaji ya kalle shi yaga yanata murmushi,dafa shi ya yi"na Nana duk ka ƙagu ko kaje kaganta",shafa ƙeyarsa ya shiga yi yana murmushi"kanaji ko karɓi waccan motar kai tsaye ka wuce gida motar takace dama Abdallah da Is'haq ne suka baka tun jiya",da sauri ya kalle shi"kar kai mamaki kaje da abarka ta halal ce ikonka ce dama haka Allah ke lamarinsa ita ɗaukaka lokaci guda take zuwa muddin ka kasance mutum nagari",kasa magana ya yi yana jinjina abin mota shiɗin da gaske,da ƙyar ya lalubo kalmar godiya ya yiwa Alhajin"daina gode min ni ai Babanka ne",murmushi ya yi suka zo bakin motar tare sannan na ciki ya fito ya miƙa masa mukullin addu'a ya yi sannan ya shiga,ko anan saida yaƙara birge Alhaji akan idon Alhaji ya fita a wurin sannan ya shiga motocinsa suka wuce gida,koda suka isa matansa da yaransa sunsan yana cikin farin ciki sosai,Hajiya Fulera uwargidansa mai yara Mata uku itace tama tambayeshi amma yace ma ta ba komai irin abinda take baƙinci kenan da yake ma ta baya taɓa faɗamata sirrinsa kamar yasan cewa ba zuciya ɗaya take zaune dashi ba.
Tunda yashigo layin da motar ake binsa da kallo a ƙofar gidan Iyyo ya gyara parking ya jima aciki sannan ya fito,baki ƴansa ido suka shiga hangamewa ciki harda Sadis da Khamis ƙannensa"kai Khamis wancan ba Babban Yaya bane kalli fa kayan jikinsa harda mota",kallonshi Khamis ya yi ka sa ni ko arowa ya yi tunda yana neman auren ƴar masu kuɗi","haba yauwa sai dai hakan amma fa komai ya shiga da shi ina ma nasa ne wayyo ai wallahi saina ari motar naje nayi burga sosai a gari","wallahi bansan me yake damunka ba Khamis yanzu a ina zai samo wannan motar saikace ɗan mafiya kaidai a bari a arotan ya yi",mukkullin ya danna ta kulle sannan ya shiga soron gidan,muna cikin alwalar sallar magaruba naji sallamar muryar Babban Yaya watsar da butar nayi na yanko a guje na daka tsalle sai ajikinsa"oyoyo Darling Yaya",saurin riƙeni ya yi yana dariya ya rungumeni"oyoyo Darling Sis amma saikin faɗi kinji ciwo kinja min masifa kin manta banaso ko ƙurji ya fito akan wannan fatar dan kar ta sauya launi",a kunnensa na raɗa masa"na daina Babban Yaya",dire ni ya yi yana kama hannuna muka ƙarasa ciki,Ya Fatu da Aunty Mama da akai komai akan idonsu kallon juna sukai Ya Fatu tace"zahiri Aunty Mama akwai babbar drama nan gaba kaɗan dan bana tunanin Nana Babban Yaya zai bari tayi girma ba a hannunsa ba kalli yadda kaf idanunsa suka rufe ƴar yarinya ƙarama ta taɓashi ina kuma ga ta cika tayi fam dama gata ɗiyar fulɓe gaba da baya gata shuwa'arab tabbas a kula da jikin Nana wannan ƙashin ya kama gabansa","kin fahimta kenan Fatu nima na fara wannan shirin da ta shiga aji uku a makaranta","kin kyauta saura ni",Yaran ne suka taho duk suka yanyame shi suna hayewa jikinsa amma yana riƙe tam da hannuna yaƙi saki sai amsa gaisuwar yake,sunkuyowa ya yi dai dai kunnena ya raɗa min"nayi mota tana waje",gwalo ido nayi na wani fasa ihu saida suka baje yaran nayi waje da gudu,dariya ya yi ya juya yana gaisar dasu Mama,Ya Usaina dake riƙe da haɓa dan mamaki tace"Babban Yaya meka faɗawar jaririyar taka ta baza yara haka",murmushi ya yi"ƴarsa ido kina nan da halinki ashe to bazaki ji ba ki bita kiga me taje yi wajen",ba musu kuwa suka biyo bayana,ina fito nao arba da mota me shegen kyau a ƙofar gida,ihu na fasa"MOTAR BABBAN YAYA",cak masu wucewa masallaci suka tsaya suna juyowa hakama ƴan gidanmu masu biyoni,su Sadis da maganar ta sauka a kunnen su ai kamar sa kifa suka ƙaraso"ke Nana wannan motar ƙatuwa mai tsada itace ta Babban Yayan a ina ya samota",juyowa nayi cike da masifa"kai Ya Sadis ka daina gulma amma muje na rakaka ka tambayoshi a ina ya samota",waigawa bayansa ya yi"ke yarinyar nan munafuka ce wallahi daga tambaya","munafukai dai dani damai dattin hula",ya ɗaga hannu kenan zai kaimin duka ya tsinci waɗannan fusatattun idanun na Babban Yaya yana kallon sa da sauri ya sauke hannunsa ya matsa a wurin gudun karshi yasha marin dayay niyar min,wurin ya ƙaraso yana faɗa musu tashi ce dan mu a dangin mu ba mai tsoron maganar wani banda haka aida Babban Yaya zaiyi shakkar cewa wannan motarsa ce kai tsaye,a magarubar nan ba wanda bai fito ganin mota ba Iyyo rawa ta shiga yi wai jinin ta akwai albarka ga farinjini da kwarjini aiki ɗaya na magana ya kawo sauyi a rayuwar jikanta,farin ciki ya cika zuciyar wasu yayinda baƙinci da hassada suka turniƙe wasu dan wani da yanda zaiyi ya ɓatar da motar adaina kallon ta ma da ya yi sai dai kash lamarin Allah ba mai ja dashi,a ranar ya haɗa Alhaji Baffa Iyyo Umma Mama da Aunty Mama ya musu bayanin komai tun daga farko har ƙarshe,sunsha mamaki gaskiya sannan sukai masa addu'ar fatan nasara a lamarin sannan Allah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 32