Share this page
kallon Habeb can ya yi murmushi ya dubi Baffa"Dada wancan da wancan wa da ƙani ne?",shima murmushin ya yi wancan na zaunen shine Baban ka shi kama na tsayen shine kawun ka dukkan ku sunan ku ɗaya abin da yasa ba su kula ka ba duka iyayen ka mata biyu sun gudu",da irin mamakin nan yace"Nana da Maama",kwashewa akai da dariya saboda hausar ma taahi abin dariya ce da alama dai ya yi gadon zaro zance,tashi ya yi tsaye ya nufe su Habeb ya da fa ya juyo hannu ya miƙa masa suka gaisa sannan ya juya ga Baban sa ya miƙa masa hannu,ganin bai bashi ba yasa ya gyaɗa kai ya juya baya"shike nan in ba ka gaisa da ni ba bazan faɗa ma ka inda suke ba"da sauri Babban Yaya ya taso ya miƙa masa hannu shima ya basa harda irin jijjigawa nan shi ga babba"to faɗamim ina suke",kai ya juya ya sosa ƙeya"ta ya jan faɗa ma bayan ban sa ni ba",dariya aka kwashe da ita ana nu na su shima murmushin ya yi ya janyo yaron ya rungume shi wata ƙaunar na shiga jikinsa shima yaron rufe ido ya yi yana dariya,sai a sannan Iyyo da Alhaji Baffa suka shigo dama ankai su dubiya ne asibiti duk abinda ake basa nan da mamaki suke bin yaron da kallo Iyyo ce ta ce"kai amma wannan ɗan Nana ne ba?",dariya akai nan Alhaji Baffa ya ce"tw ya akai haka ta kasance?","Hajara ce kawai ta sa ni Baffa",cewa Baffan mu"to ina ta ke?",Iyyo ta faɗa,"bamu sa ni ba yaron kaɗai ta aje megadi ya kawo shi a yanzu ba wandw yasan inda take",Aunty Mama ta faɗa kaɗa kai Iyyo ta yi"Allah sarki Nana shi yasa ta ce ai bincike a bi a hankali ita ba ta yarda da vedion ba kunji fa ita mara kai ma tasan haka",Gwaggo ce ta miƙe"wa ya ce muku Nana bata kai garau ta ke tun kwana biyu da dawowarta"cik da mamaki ake kallon ta bama ya Babban Yaya wanda ya yi kamar zai shige fuskarta"haka batun yake Habib ya faɗa,salati aka saka Alhaji Baffa ya ce"da alama sai ta ce karku faɗawa kowa"a tare suka ɗaga Alhaji Baffa ya yi salati yana ce wa"da alama dai Nana ta haifeku bawai ku ka haifeta ba"dariya aka saka har Baffa nan Baffa ya ce"ya kamata gobe a nemo Hajara Nana kuwa da kanta za ta dawo in ta samu labarin ƴan biyun tata ta dawo",kowa ya gamsu da hakan nan yaron ya ciro takardar aljihun sa ya miƙawa Baban sa"Abbu ga shi inji Maama",karɓa ya yi ya buɗe a fili ya shiga karantawa kamar haka. "(Habib gaskiya ne da farko bana son Nana saboda kishin ka da na ke da fari nabi duk wa ta hanya wadda zan rabaka da ita amma na kasa nasha bin malamai da bokaye duk akan na rabaku amma ban sami nasara ba sai dai ban san me yasa ba ban jin shauƙin abinda nake aikatawa ba sai dai nasan zugar ƴan uwana ce ke tasiri akaina watarana na taɓa zama nayi tunani ta ya za ayi ace ƴan uwa suna ɗora ƴar uwarsu akan hanyar ɓata dimun da imun sai na ba raina hakan soyayya ce,ranar da Nana tazo ta nu na tana da ciki sai naji tashin hankali da fa ri harna faɗawa ƴar uwata nan ta shiga min famfo akan saimun ga bayan cikin,muna cikin magana sai ga Nana ta warce wayar nan ta fara ma ta maganganu sai naga yayar tawa ta fara tsorata da ita anan na gane Nana ƙalau take ashe,tana cikin yi wa yayata barazana sai ta kashe wayar anan Nana yarinya ƙarama ta shiga zayyane min wa ce ce ni ashe ni ba ƴarsu ba ce shi yasa suke kai ni halaka Nana tana sona ashe tun daga ranar na yakice komai na riƙi Nana da zuciya ɗaya,har Allah yasa cikin ta ya yi girma kwatsam saina tsinci kaina da samun barazana akan in ban kashe ɗan da zata haifa ba su zasu kashe ta,jin haka yasa na zaɓi kashe yaron amma saina kasa saboda ɗan NANA da BABBAN YAYA ɗana ne,amma dai ga ɗanka nan fatan komin daran daɗewa zaka sauwaƙemin kar in na yawo da auren ka akaina saboda kwasar zunubi ni marainiya ce bana da kowa sai dai Abba kan ya rasu ya haɗa ni da abubuwan da zanyi ingantacciyar rayuwa ta hannun Nana nasan sanda zaka sami saƙo na nayi daɗe da yin nisa dakai,a ɓangarena na yiwa Al'ameen ɗaki guda ka duba. Fatan alkhairi a gareku duka fatan zaku kulamin da My Son Habib don ina ƙaunar sa fiye da kowa a duniya sai anjima HAJARA Maama AL'AMEEN") UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 BABAN YAYA Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 39 Jin wannan saƙo na ta ya karyawa kowa zuciya Al'ameen kuwa ya lafe a jikin Baban sa duk ba gane me ake cewa ya yi ba shiru ne ya biyo baya kowa ya kasa magana dama su ya Hasiya basu ta fi ba itace ta ɗau yaron zuwa ɗakin Aunty Mama dama shi ba shi da damuwa tana kai shi ya kwanta sai bacci,sannan ta dawo"maganar gaskiya munyi babban kuskure a al amarin Nana da Hajara akwai alamar tambaya Nana akwai abinda yasa ta ɓoye ta warke sannan Hajara ba ta faɗi waye yasa ta ta yi kisan kai ba sannan ta ya ta shirya wannan dabara har shekara biyar ba tare kowa ya ga ne ba akwai sarƙaƙiya tabbas","hakane Ya Hasiya ya kamata dai a nemo su"cewar Ya Mabaruka"anan dai Alhaji Baffa yace"kowa yaje ya kwanta abarwa gobe a dudduba a ga ni a ina za a sa mo su". Ranar Babban Yaya kasa runtsawa ya yi sai zagaye ɗaki yake yana kallon gidan sa da ya zama kango sakamakon kuskuren sa ta ya akai ya yi haka yana zaune da Hajara shekara takwas ya kamata ace ko ɗan ta kashe ya nemi dalilin ta nayin hakan,haka dai ya kwana sai asuba sannan ya kwanta. ***** Ina tsaka da shan tea da safe nagan number Aunty Hajara tana kira na da saurin na ɗauka na shige ɗaki"Aunty Hajara dan Allah kina ina zan zo wajen ki nima bana gidan","me ki ka ce Nana ba kya nan kuma ina ki ka je?"turo baki na yi"bayan ke ce ki ka fara fita shine nima na fita na bar musu gidan su ci kayan su",ƴar dariya ta yi"ba ki da dama Nana kina ina nazo na ɗauke ki",da sauri na faɗa ma ta,tace na fito sanɗa na yi Umma na ɗaki na fita ba ta sa ni ba can kan kwana na tsaya sai gata da mota sabuwa mai ɗan karan kyau shiga na yi na kalle ta naga tanabfarin ciki ƴar dariya na yi"wallahi Aunty Hajara kin talauta Hajiya Fulera kinzo kina facaka da kuɗin ta",dariya ta yi ta tuƙa motar muka bar layin gidan na ta ma ya yi kyau sosai anan muka wuni cir da yamma tace na koma na ce bana zuwa konina a nan zan ta zama"to wai Nana haka zamu zauna da aure akan mu","eh mana ba ahaka suke so ba","to ɗanki kuma wazai kula da shi",da mamaki na dube ta"wane ɗan kuma?",murmushi ta yi"ai jaririn mu bai mutuba yanzu haka yana gida na kaishi tun jiya da magaruba",wani kallon ta maida ni mahaukaciya na ma ta,ƴar dariya ta yi ta ɗakko wayarta ta kunna wani vedio saida ta nu nan detail sannan ta kunna min tsaye na miƙe cike da tashin hankali hannuna na rawa na ɗauki wayar wani irin ruwan hawaye ne ke zuba a idona jikin ta na faɗa na fashe kuka rungume ni ta yi itama tana hawaye"ki yi haƙuri Nana ban barki kin shayar da ɗanki ba na cuceki",wata irin zuciya ce tazo min wuya ta shi na yi ina go ge hawayen"waye ya miki wancan sharrin?","ba sharri ba ne haka abin yake kawai dai an canja abin ne amma kinga na asalin",kunna min ta yi na kalla duban ta na yi ya akai haka ta kasance ba ki faɗa min ba suwaye suka saka ki?",kama hannuna ta yi na zauna sannan ta ce"cikin ki na wata takwas watarana na je gida sai na tarar da Abba da baƙi duk baƙuwar fuska amma abin mamakin kin a ganin su masu kuɗi ne sai dai suna cikin shiga kamar marasa ƙarfi ban daɗe da zama ba aka ce nazo inji Abba wallahi Nana saida gaba na ya faɗi da zan gudu ne saina yi wani tunani in ma ban je ba koma miye za a sa wani ya yi sannan ya cutar da ke kawai sai naje tasa ni sukai da barazana zasu kashe Abba zasu kashe Umma haka dai sannan suka ce in ban kashe ɗan da zaki haifa ba to su zasu kashe ki ba zasu kuma fasa ba sanin halin Abba da abinda ki ka nu na min yasa nasan zasu yi abinda suka ce shi yasa sanda ki ka fara naƙuda ban faɗawa kowa ba sai na kai ki asibiti ni ɗaya da farko haihuwar ta gagara sai daga baya sanda aka ba ni jaririn da ki ka haifa take naji kamar ni na haife shi rasa ya zanyi nabyi ga wasu mutane kamar likitoci da nurses suna ta kallo na duk sai na gigice,wani ɗaki na faɗa ban sa ni ba ashe wata mata ce a ciki matar me kuɗi ce shi yasa aka ware ma ta ɗaki daban,ga ni na da tai a gigice saita daina kukan da take tace min"ƙawata ya haka zaki faɗi fa",kasa magana na yi kawai na fashe da kuka"da ƙyar ta samu ta taso da nata ɗan a hannun ta tazo kusa da ni hawaye ta ke itama tana leƙa ɗan hannuna sai taga yana motsi sannan ta kalli na ta"kinga fa nawa ɗan baya da rai ma ke naki yana da rai amma ki ke kuka haka",dakatar da ita na yi"ba ɗana ba ne ɗan kishiyata ne ance in ban kashe shi ba za a kashe ta kuma naga masu aikata hakan a asibitin nan",dakatar da kukan ta yi cikin zaro ido gefe da gefe ta kalla sannan tai ma za ta karɓi ɗan hannun nawa ta ban na ta,akan hannuna ta ɗora na ta"kimin alƙawari zakiwa ɗana sutura ni kuma zan reni naki cikin aminci amma a yanzu ina da ƴar matsala mijina ya rasu ga number waya ta ki kira ni sai muyi magana",kallon ta na shiga yi ba wai na ƙin yarda da ita ba ne a a na mamakin abinda take niyar yi ne,kai ta ɗaga min tana murmushi"kije da ɗan a haka ana cewa ya mutu za a ce a wannan ɗakin da ki ka shigo ne ki ka kashe shin tunda kinga ba wanda yasan da mutum a ciki"kai na ɗaga na fito,ta wata ƙofa na shiga inda ki ke na aje jaririn sannan na fito na kira gida sanda suka zo nurse suka duba sai suka ga yaron mutu shine aka ba mu gawar Nana akan wannan yaron na koyi wankan gawa in zaki lura ni na masa komai,sanda akai kwana uku sai na kira wannan matar tana ɗagawa ta fara dariya ajiyar zuciya na sauke sannan na koma can ƙuryar ɗaki ina ce wa"ƙawata ina ɗana","gashi nan ƙawata sai lan karan kuka",murmushi na yi"ai dole ya yi kuka uwar sa fitinanniya ce"ƴar dariya ta yi tana cewa"to kuwa gashi nan yana yi,dama nace miki ina da matsala ɗaya ko ni a ƙasar Egypt nake mijina ba bahaushe ba ne ɗan can ne daga karatu na aure shi muna cikin rufin asiri mai kuɗi ne sosai bayan ya mutu sai dangin sa suka zo suka ƙwace komai a hannuna bayan haka da wani ɗan lokaci sai ga ciki ya bayyanar min saina dawo nan gida harna na haihu a yanzu ina da gida acan sai dai ki ɗau nauyi na na ƙara komawa can na reni ɗanki",ajiyar zuciya na yi cikin farin ciki nacean gama kiban address nazo"ba ni ta yi a ranar da yamma na fita naje inda ta ke nayi murna da naga yaron cikin ƙoshin lafiya kuɗi na tura ma ta account sannan na ba ta wasu wallahi ban ma san nawa ba ne,sannan ta ce na sawa yaron suna shine nasa masa HABIB amma tanance ma sa Al'ameen haka ta yarda da abinda nace sannan taban kwatancen inda ta ke a can,na daɗe a wajenta sannan na dawo gida in kin lura ko sati biyu baki yi da haihuwa ba nace zan fara kasuwancin turare Habib ya amince zan na zuwa Misra da Sudan sarin turaren shine nake zuwa duk wata ko wata biyu a haka muka re ni Al'ameen har Allah ya kawo ranar da Hajiya Fulera tazo zata miki wannan abin na shiga shine sukai min haka dan ɗaukar fansa kin san maganar ki ta tabbata da naje gidan korata sukai kuwa",hawayen fuskata na share ina dariya"an gaishe da uwar Al'ameen ni Habib ba ɗana ba ne ɗanki ne na bar miki duniya da lahira"saurin kallo na ta yi"da gaske kimke dan Allah",hannun ta na kama"da gaske nake wallahi na bar miki",shiru ta yi"to Nana har ina murna ni da zama a sake ni...","WA ZAI SAKE KIN?",muka ji maganar sa akan mu. : Da sauri muka miƙe muna hangame ba ki ƙarasowa ya yi ciki hannun sa sanye a aljihu ya yi kyau sosai cikin ƙana nan kaya zama ya yi ya harɗe ƙafar sa yana kallon mu yana murmushi"me kuka ɗauke ke ni ne wai?ko in ce kallon me ku ke min ne?"kallon juna mukai sannan muka haɗe rai a tare muka nufi ɗaki murmushi ya yi yana gyara zaman sa ya ciro wayar sa ya yi kira ba jimawa aka ɗaga"in baku ganni ba karku da mu abokina nakai asibiti ba shi da lafiya",yana faɗar haka ya kashe ya ajiye shiru shiru ba mu fito ba har dare ya yi. Kallon ta na yi"Aunty Hajara kije mana kin gan shi can fa anya kuwa ma yana cin abinci",hararata ta yi kije kai ni dai ba zanje ba tunda ya mare ni har wani riƙe shi ake wai zai da ke ni kamar yana faɗa da ƙato ɗan uwan sa"kwashewa na yi da dariya sannan na miƙe to bari nidai na kwanta da safe ma haɗu"tasowa ta yi daga gadon please mana Nana kije dan Allah ko kiss ki masa ya rage zafi",ɓoye dariya na yi"ai wannan kin fi ni iyawa kefa tsogon hannu ce"saurin sakkowa ta yi na shige toilet ina dariya tsayawa ta yi" kuma akwai riga a ciki ki saka ta ki fito kije sama ma masa me zaici"komawa ta yi ta kwanta dama maganin mura ta sha nan da nan tai bacci koda na fito ina ta magana naji shiru na zata da wasa ta ke ashe da gaske ne rigar dana sa na kalla ai wannan tsirara ce tabɗi na gyaɗa kai turare mai ƙamshi na jaka ta na saka sannan nasa hijabi na fito,yana kwance kan kujerar nazo na tsaya akan sa kun san ni ba hankali ɗaka masa duka na yi hannun kan fuskar sa ya janye yana bi na da kallo a hijabi na ke amma ya ƙurawa ƙirjina da na turo ido,ƙara gan tsarewa na yi"wai dan Allah Babban Yaya ba ka ce baka son mu ba"murmushi ya yi a cikin ransa sannan ya tashi ya zauna yana taune leɓe,juyawa na yi zanyi tafiya ta ya fizgo ni na faɗo jikin sa matseni ya yi ya ɗago fuskata yana gewayeta da idanuwan sa,cikin sanyin murya ya fara magana"dama zaki iya tafiya ba bisa kuskure ba ki barni Nana kinsan dai bazan iya rayuwa ba ba bu ke me yasa zaki min haka",hawaye ne ya zubo min na kwantar da kaina a ƙirjin sa"ba kai ne ina cewa karka koreta ba saida ka koreta ni kuma nasan ƙarya ake ma ta dama","to kiyi haƙuri itama haƙurin nazo ba ta ku yafe min","ni na yafe maka saura ita ta yafe maka",ƙara rungume ni ya yi yana ajiyar zuciya"rabona da abinci tun randa ku ka daka min barkono"ɗagowa na yi ina dariya"to basai kana shan sa ba harka ƙoshi",baki ya kama"au kashe ni zakuyi kenan",ɗaga sgi nayi ina murmushi na zare hijabin"mun insa mu kar Babban Yaya bari na sama ma ka abinda zaka ci",na wuce shi ina sauya tafiya bayana yabi da kallo ina kallon sa,ina shiga kitchen ɗin ya biyo ni,ji nayi kawai an jawo ni ba ya an haɗa ni bango runtse ido na yi dan nasan yau bakina zaici uban sa kafin na gama tunani naji saukar bakin sa a nawa haka hannayen sa na zarya a ciki rigata abincin da ba a nema ba kenan daga ƙarshe sai tea ya sha dama ta aje boga sai ita ya ci anan falo muka kwana asubar fari ya tashi ina nan naɗe a jikin sa kwantar da ni ya yi ya nufi ƙofar ɗakin da ya ga mun shiga gadon ya kalla ya kaɗa kai yana wucewa toilet da ya fito sallah ya yi sannan akai assalatu tashi na ya yi na wuce sannan shi ya fita dan jikin gidan akwai masallaci. Umma koda ba ta gan ni ba ba ta damu ba tasan halina sarai bazanyi wani abu da bai da ce ba. Saida gari ya yi haske sannan ya dawo muna falo da sallama ya shigo muka bishi da kallo zama ya yi a kujera saboda neman tsokana sai na dube shi na ce"Babban Yaya ina kwana ta shi lafiya"kallona ya yi na tashi lafiya mana ko kinga wani abu dabai kwana lafiya ba ajikina",ɓoye dariya Aunty Hajara ta yi tana kaɗa kai"a a Babban Yaya daga tambaya","na kwana lafiya amma in hakan ki ke son sa ni bari na nuna miki" tasowa ya yi da gudu na ɓuya a bayan ta shima yazo gaban ta ya tsaya mamaki yake yanda ko kallon sa batai ba,ya maida hankali kanta na zame na fece kitchen a raina ina Allah yasa ta haƙura mu koma gidan mu inga Al'ameen naga da wa yake kama,hannu yasa ya ɗago fuskarta"haba Hajara ki kalle ni mana",ɗagowa ta yi tana hararar sa,murmushi ya yi"kiyi haƙuri ki yafe min please",kai kawai ta ɗaga"na haƙura ai tuni kodan ɗanmu me zaisa in na fushi dakai bayan kayi abu ne a rashin sa ni ba bu sauran ɓacin rai tattare da ni da ace nayi abin da aka ce ne shine zan dauwama a ɓacin rai",hannun ta ya kama"to mu koma gida kinga kowa na cikin damuwa","ai dama zamu koma karyawa kawai zamuyi"fitowa na yi ina ta fi da rawa,bina sukai da kallo kawai waya ta na ɗakko na saita camera basu sa ni kiɗa na kunna na fara tiƙa rawa da sauri ta fito a kichen ta shiga ta ya ni shi kuma yana zaune yana dariya saida na gaji sannan na zauna ina dariya"kai Babban Yaya ina farin ciki wallahi ɗan mu bai mutu ba ga Aunty Hajara ta nutsu ta ga ne masu cutarta shike nan sai muyi rayuwar farin ciki",da sauri ta tari numfashi na"ban baki wani labari ba Nana Yaya ce ta raka ni wajen wa ni Boka dan nace yaban maganin da zan koreki daga gida na shine yace wai sai na kawo masa gashin hammatar ki dana kanki sannan da gashin gwaiwar jaki",kwashewa mukai da dariya"jaki jaki dai namu ƙasar Hausa to ke me ki ka ce ma sa"ai ni a sannan na fara dawowa hayyacina kuma a gidan uban wa ya taɓa ganin jaki da gashi a gwiwa banda rainin hankali,kawai sai nace ai ke hammatar ki ba ta gashi kan ki kuma kamar gwaiwar amale ya ke shi jaki me gashi a gwiwa ai ba a hallice shi ba tukunna"shi kanshi Bokan dariya ya saka dan dama wani abun suna faɗa ne kawai dan su miki wayo in ki ka ce baki sanshi ba sai ace ki ba da kuɗi a sa aljani ya samo miki",dariya muka shiga yi kai ta girgiza"Allah ya yafe mana dai Nana amma Yaya ta cuce ni",tasowa na yi zuwa inda ta ke"karki damu fa itace da wahala ita kinsan sirrin ta ki bari zan faɗa miki"kallona Babban Yaya ya yi"nima zoki faɗamin sirrin me ki ke ta ɓoyewa ne amma kafin nan Hajara ta ya kai ki ka ɓoye Al'ameen?",kafin ta yi magana na fara zayyano ma sa yadda akai kamar a gaba na akai ba labari aka ba ni ba jiya jiyannan,ya sha mamaki sosai kuma ya jinjina ma ta ganin yana bina da kallo yasa na ce"sai mun koma gida yanzu inna fara faɗa maka sai mu wani anan",kai ya ɗaga sannan muaka karya muka kulle gida muka shiga motar da ya zo da yazo da ita"Aunty Hajara kinga kin mana guest house",dariya ta yi"lallai kam zamu sauya ma sa fasali da kayan ciki muna zuwa kawai mu huta",tafawa mukai shi dai yana tuƙin sa,koda muka isa an sha mamakin ganin mu tare kowa kan mu ya yo ana ba ta haƙuri da gudu ya fito daga ɗaki yana sanye da jeans blue da jar riga ƴar ƙarama gashin kan sa yasha gyara kurɗowa ya yi zuwa inda take ya rungume ta "Maama"lumshe ido tayi ta ɗauke shi suna dariya hancin ta ya ja"Maama na",goshin ta ta ɗora akan nasa"Al'ameenn ɗina"suka kwashe da dariya,da mamaki nake kallon yaron kamar mu ɗaya wayata na ciro na shiga musu hoto idon sa ne ya sauka a kaina murmushi ya yi"Nana"ya faɗa a bazata saida kowa ya juyo dan mamaki,ƙarasowa na yi"kasan ni ne?",kai ya ɗaga"kina zuwa in ina bacci kina ba ni madara kince kuma sunan ki Nana",cikin tausayi Hajara ta rungume shi"am sorry My Love duk laifina ne ni na rabaka da maman ka ka yi min afuwa"hawayen fuskar ta ya shiga sharewa sai ga nashi sharr,rungumeshi ta yi sosai ta fashe da kuka,zuciyar kowa saida ta karye nan Alhaji Baffa ya fara tambayar ya akai haka ta kasance,da kanta ta shiga faɗa musu sun sha mamaki sosai nan akaita ma ta godiya sannan muka shige ciki sai yamma sannan muka koma ɓangaren mu an gyara ko ina ɗakin kusa da ita ta buɗe saiga kayan yara na wasa da na sawa kallon ta na yi"Maama Al'ameen wannan fa duk muna ina akai haka?",dariya ta yi"ai ba zaki kura ba ke da ba komai ki ke kalla ba ke kawai ta mijnki ki ke",fuska na rufe dan naji kunya wayata na kunna muka shiga ciki naita ɗaukar su ina turawa ƴan gidan su saida aka kira sallah sannan mukanfito muka barshi yana ta wasa"Nana kin san me?","yazan san me ni ba ƴar akuya ba",kwashewa ta yi da dariya"kefa baki da kirki wallahi",nima dariyar na yi"to ai lefin ki ne Aunty Hajara me fa ki ka ce","to na ji yanzu mace zaki haifo min sannan ki haifi na ki",kai na ɗaga"tabb ai in na haifo mace tawace ke namiji zan ƙara haifo miki kuyi ta dambe suna aure matan su suna hararar ki",tsabar dariya saida ta zauna a wurin"gaskiya Nana yarinya ce ke","to da na mana kawai dan kin tunzura ni ne nasa akai min auren wuri ni da aka ce sai na digire zanyi aure",tashi ta yi"ke bana son iskanci a ina na tunzura kin"dariya na sheƙe da ita"kin manta ranar da ƙawayen ki suka zo ana gobe bikin naje ɓangaren ki ke zagina kina cewa ko ƙirgen dangin bai nuna ba nake son maza wurin ma kinsan ko pencil bazai wuce ba",baki ta rufe

Chapter 27 of 32