ba tashi maza kiyi wanka kinga amaren can atsakar gida amma babu ke Alhaji Baffa harya far faɗa",share fuskata na shigayi sannan suka tasa ni nayi wanka kayana suka tattaro suka zaɓo wani shegen material da aka min doguwar riga sky blue ne da ratsin dark blue sai walwali yake da kansu suka shiryani kwalliyar ma da kansu sukai min dan sun iya dama musamman ma Ya Hasiya har shago gareta,a gaban mudubi suka tsaida ni"kalli kanki Nana",Ya Usaina ta faɗa,a hankali kamar mai tsoro na ɗaga kan na kalli mudubin ni kaina banda nasan kaina da nace bani bace wannan zankaɗeɗiyar baiwar Allahr, gaba suka taso ni zuwa tsakar gidan ya Allah raiiii haka mutane sukai min amma saida muka wuce can inda su Ya Dijama suke nan suka kaini Alhaji Baffa farin ciki ya kamashi yay murmushi sannan ya bar wurin su Ya Ashiru ne sukazo nan fa flasher waya ta fara aiki dukkan abinda ake ƙirjina tara tara yake duka ina tunanin haɗuwa da Babban Yaya nasan wallahi saiyaci ubana dan zaisan ni nace amin auren,har yamma can sai gashi ya shigo gidan wuf na tashi zan gudu Ya Dijama ta riƙeni a dole na zauna amma tamkar zanyi fitsari a wando nakji,su Walida ne suka janyo shi"Big Uncle zokaga Aunty Nana ta zama queen",biyosu ya yi har wurin da muke fuskar nan kamar haɗuwar kaka amma daya ƙaraso saiya saki ransa ya zauna kisa dani wayoyinsu suka ɗakko suna ɗaukar mu hoto gaba ɗaya zamansa yasa na ƙara tsurewa shi kuwa sai ya sau fuska kamar ba shiba,tun zamansa baimin maganaba harya gama yabar wurin ya shiga cikin gidan ganin yanda ƴan uwan Umma suka taru sosai hankalinsa ya tashi baiwa kowa magana ba sai Ya Hasiya da ta hangoshi ganin ya koma ta tashi da sauri da bishi dan tasan kwanan zancen,"Habib Habib"take kiransa amma bai juyoba bare ya tsaya tana gani ya wuce can ɓangaren Abba inda ya rufe bai bar kowa ya shiga ba dama,ciki ta juya jikinta a sannan ya ye tabbas tasan sai yafi kowa jin rashin Ummansu dan yafi kowa kusanci da ita ana cewa mace ce ƙawarki in kika haifa amma bandashi,kasa nutsuwa tayi koda ta zauna ta rasa taya zataje inda yake gashi waccan matar tashi tana hauka an ma ta kishiya ita kuma uwar sanaben taga duk afirgice take amma duk da haka saita tura ta ƙila ya nutsu,muna nan zaune sai ga Ya Hasiya kusa dani ta zauna"amarya kinsha ƙamshi ɗan biyoni mana",tashi nayi na bita duk inda muka bi kallona ake kamar mutane zasu sauyan halitta,a can ta ƙofar shiga ɓan Abba ta tsaya"shiga ciki maza akwai saƙo dana aje ki ɗakko min",batare da tunanin komai ba na shige,ita kuma ina juya tabar wurin tana dariya,ƙofar falon na tura na shiga ko ina fes amma bakowa aciki shiga na gama yi ina dube dube amma banga komai juyowa nayi zan fita naji kamar nishin mutum juyawa nayi can ƙaramin falon dake hannun damana na hango Babban Yaya ya kifa kansa da kujera amma bansan meyake ba saidai numfashinsa har inda nake inaji,kamar zan fita dan tsoronsa nake amma na daure na shiga inda yake kamar kaza mai ƙwai a ciki haka nake tafiya harna ƙarasa inda yake kamar ace ƙyat na gudu haka nace"Babban Yaya"ajiyar zuciyar da yake ya tsayar yana ɗago kansa"innanillahi"na faɗa ina juyawa da gudu dan idanuwansa kamar sunyi taruwan jini kuma ba kuka yake hakan dana ganine ya tsoratani na gudu,wani abu dake akusa dashi mai kama da remort ya dannan sai ƙofar tai garam ta rufe,burki naja ina riƙe da rigata,takusa naji na ƙanƙame jiki wuri ɗaya ina durƙusa awurin,inajin tsaiwarsa akaina naji rugugugu a cikina ƙanƙame jikina nayi na ɗaga hannu ina kare kaina kamar wadda za'a duka"wallahi Babban Yaya bansan kana nan Ya Hasiya ce tace nazo na ɗaukar ma ta saƙo kuma banga komai to ai nama manta banda hamaganci na wake aiken amarya ma kuma fa ba shiga nan ɗin ake bare nace da dagaske ta ajiye abu a wurin",yanda nake zaro zance kuma ina kaina shine ya bashi dariya da bazaiyi dariya sai ya yi murmishi"ni ne saƙon da zaki kaimata ai",sauke hannun nayi ina miƙewa da ƙyar dan nagaji da zuƙunnon"haba Babban Yaya goɗoɗo dakai zatace nakai ma ta kai","to tunda baki yadda ba kama hannuna ki kai ma ta ni kiji me zata ce",kunsan ni da wawta saina kamo hannun nasa kuwa muka fito riiiii duk inda mukai ana kallon mu ni kuwa ko ajikina tanacan tana rabawa yara lemo na hangota har qurin muka kai ta bayanta ba ta ganmu ba saida nayi magana"Ya Hasiya ga saƙon",jiyowa tayi na miƙa ma ta hannun Babban Yaya saida ta kama sannan na sakeshi,haɓa ta riƙe da hannu ɗaya"na daina fargabar zaki iya zaman aure dama kina hankali haka Nana nagode kuwa jeki abinki",da ɗi ne ya kamani yamin ram kamar nayi rawa ma kalli Babban Yaya na ɗaga mai babban yatsana alamar jinjina shi kuma ya kaɗa min kai,juyawa nayi ina dariya na tafi bayana yabi da kallo duk damuwar da yake ciki ya nemeta ya rasa Ya Hasiya ya kalla"to sake ni mana ai kin turamin maganin damuwar tawa ba komai yanzu Allah ya jiƙanta",hannunsa ta ƙanƙame"ameen ɗan uwana dan Allah ka riƙe yarinyar amana karka bari tayi kuka kaga yanda duk ƙanƙantarta amma take murna an ɗaura ma ta aure sai kaima da take tsoro karka ɗauka ita ta saka ayi hakan",ɗan tsaiwarsa ya gyara"ita tace ai hakan mana kuma akayin kinsan kamar uwa haka Alhaji Baffa yake jin maganarta",baki ta kama"kai Nana amma wannan yarinyar akwai taɓargaza tasan aure kuwa ta manta karatunta ajinta fa huɗu kwata kwata","tasan aure mana faɗa sukai da hajara akaina wai bata ta kwanta ma ta da miji ba shine ta nuna ma ta itace bata isa ba tunda gashi ta aure ni kuma ta ma ta alƙawarin saita kwana da ni yau yanda hakan kasance ne bansani ba kuma makaranta doke zatai karatu ai bazan barta hakaba makomar ƴaƴana fa",kansa ta dungura"kuma saura ka watsa ma ta ƙasa ido ƴaƴa sakoya a makaratarsu",bakinsa ya dafe"wane Habib ai dole nayi biyayya amma ƴaƴana wallahi da uwa me ilimi zasu zauna",ya faɗa yana dariya "bari naje wajensu Abdallah nasan suna jirana duk da babu matsalar komai da zasu buƙata"sakinsa tayi"to shikenan ɗan uwa sai anjima",ya wuce yana jinsa sayau kan ya kai inda ya musu masauki ya haɗu da Yasmin anan take zayyane masa duk abinda su Aunty Hajara da ƙan uwansu sukai,kanta ya dafa"karki damu Sis jeki aikin gabanki","ai Big Bro wajen Aunty Nana na fito zan gudu tun ɗazu an hanani fitowa","to jeki tanacan gidan mu bata gidansu","to Big Bro thanks",ya wuce yabi ta da kallo ko bata faɗa masa ba yasan za'ayi haka amma basu da hankali su ai dama anan ya musu mazauni tuni nan ya wuce ko ajikinsa.
Ana sallar la'asar wadda zatai lucture ta ƙaraso dama an shirya wajen ankonmu na atamfa duk muka saka sannan aka haɗa mu waje ɗaya akan dadduma sai kowa kuma ya zauna,wa'azi mai shiga jiki tayi da nasiha amma duk tsoratawa da take akan zaman aure baiko razana ni ba saima ƙwarin gwiwa da naji su kansu mamaki suke suna hawaye amma sukaganni ƙiyau miyau sai suka alaƙanta hakan da bani da hankali ne,ana kiran magaruba aka tashi a taron bayan raba kayan walima gaskiya hakan ma yafi party daɗi kuma duk duk taurin kai na Ya Hadiza saida Ya Aisha da Ya Zainab suka tasota agaba tazo ta shiga cikin mu.
Bayan antashi Ya Umme da Ya Sakina suka wuce gidansu ni kuma da Ya Dijama da Ya Nabila muka shige gida Ya Hadiza ma suka wuce,da yake ba duka ne auten cikin gidan ba su Ya Umme na komawa su Ya Sumayya suka shiga shirin miƙasu ɗakunan su yayinda Ya Ashiru aka fara shirin kaimasa Ya Nabila sai Ya Haruna aka fara ƙoƙarin miƙa masa Ya Dijama nasa gidan.
Duka hanani zuwa akai naita uban bori amma aka hana naje can kan gado na kwanta ina fushi har naji gidan tsit tasowa nayi na tafi wurin Iyyo tana ganina ta fara min waƙa ina dariya nan na kwanta,bayan awa biyu gidan ya ƙara kacamewa da hayaniya alamar sun dawo kenan ban fitaba saida Aunty Mama ta biyoni ita da Ya Hasiya dama Ya Usaina ta rigasu yo gaba,a nan Alhaji Baffa ya taresu da maganata dariya Ya Hasiya tayi badan sai an zauna ba a ayau za'a miƙa Nana ɗakinta dan tana komai a gidanta Abba ya siya ma ta komai kan Allah ya karɓi abinsa,mamaki kowa ya shiga yi anan Ya Usaina ta shiga nuna musu komai a wayarta da ta ɗakko,Alhaji Baffa ne yace"Allah yawa yaron nan rahama yasa albarka a abinda ya bari","ameen Alhaji Baffa suka faɗa",yace"to yanzu abinda za'ayi gobe in Allah ya kaimu kuje ku gyara ma ta komai dan zaman ɗakinta zatayi itama",da to suka bishi nan sukai cikin gida Aunty Mama kuma ta ɗakko ni muka shiga tare can ƙuryar ɗaka tasani sannan ta fita,tsaye na miƙe ina tunanin me zanyi Babban yazo yanzu kaina na ɗaga sama ina tunani.
Tunda ya sallami abokansa bayan sallar isha ya shiga gidan dan ya wtsa ruwa koya kori gajiyar da ta masa yawa,yana shiga ya fara karo da kaya kai ya ɗaga yaga falon kaca kaca dukkan katan ɗakinsa ne ta farfasa na fasawa sannan suturarsa kaf ta yanka masa ita gata nan a ƙasa,wani irin yanayi ne ya ziyarce shi na ɓacin rai da danasanin aurenta da ya yi ayau duk abinda take baijin ya yi danasanin aurenta sai yau,kan kujera ya ganta ta harɗe ƙafa tana riƙe da almakashi tana yanka masa zanin gadon sa da niyar ya ma ta kaca kaca ya ɗaga ƙafarsa amma photon Abba dake saitinsa ya taka masa burki ganin kamar yana masa murmushi,a wurin da yake ya tsaya ya ɗakko wayarsa ya yi kira ba jimawa ya kashe ita kuwa tanajinsa yana magana amma bataji me yace ba dan yau antuna asali da fitanci yay maganar,Aunty Mama ce ta shigo"sako hijabinki ki biyoni",da hanzari na saka nabi bayanta Mama dake tsaye tace"ku muje"nidai binsu nayi sai naga sunyi fannin Babban Yaya ban tankaba har suka tura ƙofar suka shiga nima nabi bayansu.
Turus Mama dake gaba tayi ta fara salati"naga takaina ni Sadiya miye hakan Hajara kalli yadda kika ɓatawa mijinki kaya dan rashin hankali kishi haukane",tana inda take batai motsiba ni kuma ina ganin haka sai na matsa kusa dashi na saƙala hannuna a nasa na kalleshi shima ni yake kallo murmushi nayi"ba komai Mama ai tayi da mai arziƙi da ace matsiyaci kamar saura da sai ransa ya ɓaci amma wannan kayan da tawa haka ai kanta ta ɓatawa lokaci shi kuma ta rage mai aiki dama in sutura ta taru da yawa bakasata tsinema take kinga saita kwashi wannan takai bola sai muyi sabon zubi ko Babban Yaya",murmushi ya yi yana danƙe hannuna sosai"hakane ta wajena,tunda na fara magana tamin zuru tanaji aranta kamar ta daɓa min wuƙa kamar walƙiya sai gata agaban mu Babban Yaya na tura baya na shiga gaba na kame ƙugu turus tayi tana bina da kallo ɗan baya taja yau sai taji wannan yarinyar in bata kasheta ba sai ita ta mutu wato ma nan shigar masa tayi kenan,juye juye ta shigayi a wurin ta ɗakko wani yankakken glass tayo kaina shi kuwa Babban Yaya yau yaga abin na manya ne sai yasa hannu a aljihu yana kallon ikon Allah,da sauri Aunty Mama ta yunƙura zata tare na ɗaga ma ta hannu tana ƙarasowa ta kawo min yanka dashi na goce ina tura Babban Yaya a ƙasa ta faɗi na kama hannun Babban Yaya muka shige ɗakinshi ina ma ta gwalo,su Mama dariya ma abin ya basu suma suka fita ba wandda tace ma ta cikanki,muna shiga ɗakin na kulle na zauna a ƙasa ina dariya ganin yanda tasa jambaki ta ɓata bangon ɗakin da rubutu wai SAINA KASHE NANA shi kansa dariya abin yabasa ya zauna gefen gado da shima akasa reza aka zazzanawa katifar,ƙofar ka shiga bugu amma da yake ta gaske ce sai takeyi kamar ana bugawa da key,da hannu ya yafito ni na miƙe naje na tsaya agabansa kusa dashi ya nuna min na maƙale kafaɗa hannuwansa na kama na buɗa na juya na zauna a ciyarsa ina dariya,fari nayi da ido cuna baki kamar gidan tsutsa"ai Babban Yaya ka rage min matsayi ka manta ada ma anan nake zama bare yanzu da nasamu lasisi".
Baki ya kama yana karkato kai yana min kallon mamaki,kunyace ta kamani na sunne kaina akafaɗarsa murmushi ya yi ya bubbugi kafaɗata"ɗago ki faɗamin lasisin me ki ka samu",tashi nayi da gudu na koma bayansa na haye gadon ina dariya gyara zamansa ya yi yana fuskantata"a ina zaki kwanta da ki ka kawo mu nan kallafa ko ina glass ne",sakkowa nayi ina cire hijabin jikina"anan zamu kwana mana saidai ɗan baƙin ciki ya mutu bari kaga"dama nasan inda ake aje tsintsiya a ɗakin dan haka ita na ɗakko na dawo inda yake"Babban Yaya tayani mu ɗaga wannan katifar dan nasan nauyi zatai",tashi ya shima ya zare rigar jikinsa dama ya cire babbar rigar tun aɗakin Abba acan ma ya barta dan da ya barta anan data kassarashi inta yanka mai rigar tarihinsa,a gefe ya ajeta ya zagaya ya ɗaga katifar shi ɗaya kifata ya yi saman ya koma ƙasan sannan na fara tattaro komai ina sharewa duk da ransa yana ɓaci in ya kalli abinda ta masa dan har funitures ɗin tasa zarto ne ko wuƙa ta kakkarce su, amma duk da haka ganin yanda nake sharewa sai shima ya basar kawai ya shiga ɗauke abinda tsintsiya bazata iya kawar wa ba da haka na share ko ina sannan naje toilet na ɗakko towel ɗinsa na jiƙa nazo na goge duk inda ƙafa zata taka gudun tsakin glass ɗin dire towel ɗin nayi"wash Babban Yaya wannan matar taka wallahi gobe ka kaita Dawanau a buɗe ma ta file ƙato"na faɗa ina wara hannuwana,mumushi ya yi ya gigiza kai,ya fito ni ya yi da hannu alamar zo da sauri naje"gani","baki gajiba ne"ƙugu na dafe"tsabar gajiya ma bacci nakeji a tsaye","to jekiyi wanka kizo ki kwanta"ido na fiddo na matsa baya"wanka a ina kenan anan ɗakin wallahi a a","meyasa bazakiyi ba anan ɗakin",kaina na sunkuyar"kunyarka nakeji mana kawai ka gane min jiki bayan matarka tace ba komai ajikin nawa tafini komai inka kalleni ma amai zkaji",kiji sharri,,,matsowa ya yi"to bari na miki da kaina tunda nima na samu lasisi ai kuma duk maganarta ki share yanzu fa kikace akaita Dawanau"aguje na juya na shige toilet ɗin na rufo ƙofar lin yace zai min tsaf nasan halin Babban Yaya wallahi saiya tuɓeni yamin ba kunyar da zaiji shi an faɗa masa duk haukar da nake zan tuɓe rigane agabansa,anan ma ina cirewa amma gani nake kamar yana kallona ne da ƙyar nayi wankan nasa under wares ɗina na ɗaura towel na yafa wani,na jima abakin ƙofar sannan na buɗe na fito da sanɗa yana jikin gado a tsaye bansan tunanin me yake ba nagadai yanata juya tafin hannunsa sannan ya juya bayan ta bayansa na tsaya nace"Babban yaya na fito gashi ba ko ƙyalle aɗakin nan bare mutum yasa ga waccan matar taka har yanzu bugun ƙofa take nace tayi bacci ko riga mai yagace na lallaɓa na ɗakko nasa",murmushi ya yi ya durƙusa jikin locker da yake mukullin jiki ya murɗa saigata ta zaro wata leda mai ƙyalli ya ɗakko ya miƙe tsaye yana fuskanta ta ɓareta ya yi ya zazzago koma miye aciki saiga wata jar riga mai mugun kyau miƙo min ya yi"zaki iya sawa dan ki faranta min",da sauri na saki towel ɗin kaina gashina ya zubo janyewa nayi na karɓi rigar na koma toilet ɗin na saka innanillahi dana kalli kaina a mudubi nima ban gane kaina ba bare wani ya gane ni ba wata fargaba na fito daga toilet ɗin baki ya buɗe yana kallo na"tsaya anan"yace yana ɗaga min hannu tsorata nayi amma sai naga ya ya ɗakko ipad ɗinsa ya shiga min photo kamar ƴar fation ɗin nan na kayan bacci da ake liƙawa a jikin kwalin da ake sawa aledar rigar sai ya gaji dayi sannan ya aje"zo nan"zuwa nayi ina sunkuyar dakai sai murɗe yatsu nake hannauwan nawa ya kama ya ɗagosu bansan me zaiyi ba naji ya ɗauke ni sama dariya nayi"kai Babban Yaya kamar ka ɗau kara","to ke kin zata nauyi zaki",murmushi nayi ina kwantar da kaina akafaɗarsa"to ai Babban Yaya ance mace duk sirantarta nauyi gareta","banda ke "ya faɗa yana murmushi ,a gadon ya ajiye ni yajawo min filo ya ɗora kaina"ma za yi bacci tawan"shagwaɓe fuska nayi"kaifa ina zaka","wanka zanyi mana yanzu zanzo na kwanta dake tawan",tashi nayi zaraf da gaske Babban Yaya","sa wasa yarinya kawai ki shirya badai bazaki musu ba",babban yatsana na ɗaga ina jinjina masa"ai kasanni ba musu a tsakanin mu","to kwanta ina zuwa"ya juya ya sauka ya shige toilet yana mirmushi, ni kuma nai girif ta baya na kwanta ina wulla ƙafa sama"woni woni Nana na zan kwana da Babban Yaya na"ya jima sannan ya fito yana ɗaure da towel gadon ya kalla ya ganni nayi bunga tuni,murmushi ya yi ya ƙarasa jikin locker ya buɗe ya ɗakko nasa kayan farare tas marasa nauyi yasaka ya maida towel ɗin kusa dani ya zauna yana kallona"waida wannan yarinyar mai ta ɗauki kwanciyar ne nafa fuskaci batasan komaiba kawai fitinace ita adole saita nuna tasan komai"ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa dan wani nishaɗi yakeji yau ji yake kamar an masa gafara wani irin yanayi yakeji a ransa da jikinsa kai gaba ɗaya duniyarsa ta canja yau,addu'a ya tofa min sannan ya kwantar da kansa akan filon da nake hannu biyu yasa ya ɗakko ni cak ya ɗora akansa gyara kwanciya nayi na tura kaina a wuyansa dafe bayana ya yi yashafa kaina ya sumbaci goshina ya lumshe idonsa ba wani tantama ko fargaba tuni bacci ya kwashe shi.
Aunty Hajara kuwa tafi awa uku tana bugawa amma ba'a buɗebe gashi duk windows na ɗakin sunƙi buɗuwa safa da warwa ta shigayi tana hauka da zage zage amma ba abokin yi da yake bacci ba ƙanin uwar kowa bane kuma shi duk duniya ba wanda yakaishi ƙarfi in yazo ɗaukarka koda babanka kake yawo saiya sureka to itama hakan tana shiga ɗakinta ta zauna bakin gadonta tana ɗure ɗuren ashar anan bacci ya kwashe ta bata sa ni ba.
Mama suna komawa mamaki ya kashesu nan suka faɗama Baffa,shima yace abarta zatayi ta gama ai dama wasu matan haka kishinsu yake.
Kiran sallar farko ya tashi Babban yaya yana salati sai ya jishi wasai kamar ya kwana ya wuni yana baccin a hankali ya gyara min kwanciya shi kuma ya shiga toilet saida ya watsa ruwa sannan ya fito kayansa na jiya ya mayar akan tiles ya tayar da sallar nafila ni kuwa ina shan bacci na manta ma inda nake saida za'a shiga sallah sannan ya tasheni ina ganinsa na fara zare ido ina masa kallon tuhuna dan na manta meya faru jiya jijjigani ya yi dan ya fuskanci ina wannan kallon ya nufa "tashi kiyo al'wala muyi sallah saiki cigaba da tunanin",banyi musu ba sakkowa nayi na shiga nayo al'wala sannan na fito siket ɗina da hijabin nasaka nima nabishi mukai sallar a wurin ya daɗe yana addu'a ya shafa ya juyo kenan ya ganni nayi nisa a bacci ɗaukata ya yi ya ɗora agado sannan ya kishingiɗa a gefen juyowa na zata filo ne na ɗaga kaina na ɗora acinyarsa murmushi ya yi ya gyarani sosai shi kuma ya cigaba da tunaninsa a haka har rana ta fito kumatuna naji ana bubbugawa a hankali na buɗe ido na sauke a kansa murmushi nayi"ina kwana Babban Yaya"wani daɗi ne ya kamashi"lafiya lau tawan ya rigima da neman tsokana",dariya nayi ina tashi zaune"ai Babban Yaya jiya naga drama saura ta yau kuma","to kafin afara tashi na maidaki gida"sakkowa nayi na kama hannunsa muka fito yana taɓa murfin ƙofar na ƙanƙame hannunsa,juyowa ya yi"matsoraciya ai in kina wurina haka to ko mutuwa zatayi karar ta tunkaro ki danta ɗauke ki a gabana bare wata Hajara",dariya nayi"wallahi Babban Yaya jiya da taga fuska a nan zaka kwana agabanta kamar ɗanta",ɗan murmushi ya yi yana buɗewa muka fita abinda bamu sa ni ba tanacan tanata bacci kamar mushe har muka isa gida shiru a bakin ƙofa ya sake ni ya juya"bazan iya shiga naga Baffa ba yanzu inajin kunya na kwanta masa da ƴan sai anjima ke jeki"hannu na ɗaga masa na shige inajin kunyar maganar da ya yi, sallama nayi suna ganina suka fara dariya Ya Amina ce tace"a a amaryar rabon faɗa daga rabiya sai mujiki shiru",baki na turo"ina ruwanku to naga mijina ne kome mukayi ba ruwanku"na shige ɗaki su kuma suka shiga dariya ina zama Aunty Mama ta shigo"sannu matar Habib",dariya nayi ina jin kunya"kai Aunty Mama","to mezance Nana"ta faɗa tana ɗaukar jug akan frig ta fita a kujera na kwanta nan bacci ya ɗaukeni ban sani ba,hayaniyace tayi yawa yasa na tashi ashe su Ya Usaina ke break fast dire ƙafata nayi ina ƙare musu kallo"to ina nawa kuke ci ku kaɗai","karki mana masifa uwarmu gashi"Ya Ruma ta faɗa tana miƙo min hijabin na miƙe na cire na juyo zan zauna naga sunmin zuru nima binsu da kallo na shiga yi abinda suke kalla na kalla ashe rigar jikina suke kallo,baki na taɓe"wai Ya Amina me ku ke kallo ne?","rigar jikiki mana matar aure",Ya Fatima ta faɗa"au wannan rigar bari ma kuga kyau gareta" na sunkuya na cire siket ɗin lahhhhhh suka saki salati"Nana miye hakan a haka kika tsaya agaban Babban Yayan",ido na juya"sosaima duk wannan yanka kayan da matarsa ta yi to nawa daren na gidanta ina da riga wadda bata san inda take ba bare ta haɗa da ita",mamaki na ne ya kamasu na zuƙunna na ɗau abincina na wuce ɗaki a haka ina juya musu ƙugu kallon juna suka shiga yi can Ya Asma'u ta kallesu tace"kishiyar Nana zata Dawanau tabbas kowa ya shirya jin wannan labarin wataran",dariya suka kwashe da ita nan sukaita hira akaina ina jinsu sufa basu san kar nake kallon kowaba.
A ranar suka kuma yawon gidan amare amma saida na bisu dan Ya Aziza ce ma ta tambayomin amma nasan dan suna tare dasu Baffane ya amsa naje,duk inda mukaje saina goga musu shaƙiyanci muke tafiya munje ko ina amma banda gidan Ya Hadiza wai a daren bayan kaita suka hau jirgi zuwa Abuja mudai da Allah ya kiyaye muka bisu ana azahar muka dawo nan suka wuce wai gidana suka fara jere dan kayan su suke jira dama sosai suka haɗa ko ina ɗaki uku kowanne da kayansa kuma kala daban haka falon akwai ƙarami amma kayansa sunfi na babban kyau komai na nan yellow ne ba sirki hatta cafet da center cafet ga kayan kallo tv ƴar dai dai ta babban falonce kanta me miya kamar mutum ke atsaye sai bayan sallar isha suka gama nan suka baɗeshi da turaren wuta kaminsu kulle su fito.
Tun safen nan bai koma ba Alhaji Baffa ne ya hanashi yace wai ya batta tasha iska dan in tana ganinsa abin ruruwa zaina yi da wannan yasa ya tare ɓangaren Abba dama akwai kayansa nan tunda Abba ya nuna masa su bai saba sai yau,ana gama sallar Isha ya shiga amma ko ina arufe mai gida da gidansa wani key ɗin ya ɗakko ya buɗe ya shiga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 32