Share this page
mugunta yasa yace bazamu zauna a can layin su Alhaji Baffa ba,dan yasan ko ba komai zamuna shiga muci tsamiya girkin tsaffi da nama amma na gidan yara kamar a gidan yari","gaskiya ki ka faɗa kuma Hadiza ai kuwa wannan gidan saimun komashi zani na lallaɓa Alhaji ya bani mukulin mukoma shi sai ya zauna anan shi ɗaya",wani tafa cinya tayi"gwara dai Umma dan kuwa kinsan zaice bazai bimu ba","hakane fa Hadiza komawa kamar da ƙasa", Ana kiran isha wani yaro ya shigo gidan yana susar kai"wai ana sallama da Khadija a waje","kace ina zuwa",yaron ya fita yakai saƙo ga wanda ya aiko shi sannan ya wuce,ɗaki ta shige aka shafa turare mai mugun ƙamshi wanda ko mai aure ta shafa ba lallai ta wanye ƙalau ba wajen maigida bare budurwa wadda manemi take jira wasu riga da siket da suka matseta tasaka sannan ta yafa mayafi bashi da maraba dana after dress ta ƙara fesa wani turaren sannan ta sako takalmi mai tsini ta fito sama da ƙasa Fatsima ta kalleta tana gyaɗa kai tai gum dan tasan tana ma ta magana bazasu wanye ƙalau ba,ta gaban Umma ta wuce ta fita amma batai ma ta magana ba,tun da ta fito yake kallonta ta mudubin motar shafa kansa ya yi yana cizon yatsa"gaskiya yarinyar nan ta haɗu akwai kaya shi yasa su Mannir suka maƙale ma ta kenan"katse masa maganarsa tayi da ta ƙwanƙwasa glass ɗin motar,zugeshi ya yi yana murmushinsu na manyan mayaudara"ahhh Baby shigo mana tsaiwa anan ai ba girmanki bane",murmushi ta saki sannan ta buɗe ta shiga","Hii"tace tana tsuke leɓe tana juya ido,wani shork ne ya kamashi ya fara murza hannu"Hello Baby ya ki ke","normal ya garin",kafaɗa ya ɗaga"gashi nan sai a slow amma danai arba dake sai nake ji normal nima",wata ƴar dariya tayi tana kallonsa"Allah ko amma ban ganeka ba","ohhh am sorry Baby daga zuwa na kama miki surutu ban gabatar miki da kaina ba ko sunana Sultan anan ƙasan ku nake ƙofar ruwa karki damu da sanin waye ni a hankali zaki sanni muddin ki ka saki jiki dani dan gani ɗaya na miki na fara sonki amma sai yau na gano gidanku",wani murza ido tayi"karka damu indai a wannan ɓangaren ne nima na karɓeka hannu biyu","ok ina godiya ya 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 *𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔* 𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠 Story & written by *FATIMA AMINU* *Ummu Saddi'q* Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments 08146711395 chapter 9️⃣ ***** Yana fita bakin titi ya tare ɗan keke napep ganinsa ɗan zamani ya miƙa masa katin hannunsa''abokina wannan address ɗin zaka kaini fatan ka gane",ɗagowa ya yi ya ƙare mai kallo"kace wannan address ɗin zan kaika kasan kuwa ina zaka shigo muje fatan nima alkhairin ke kirana","au abokina wurin na musamanne kenan","kaidai shigo a kyauta ma zan kaika fatan zaka haɗani nima da wanda zaka wurinsa","bazan maka alƙawariba dan nima zuwan farko zanyi wajensa",burga babur ɗin ya yi suka ɗauki hanya suna tafe sai hira auke har Rijiyar zaki shi kanshi layinda suka shiga sunan dake cikin katin shine a jikin symboard ɗin mamaki ne ya rufe shi ganin kaf layin gida ɗaya ne amma fanni fanni kuma kowanne da get ɗinsa da number sa,get dake kallonsu anan ya faka sojoji sai zare musu ido suke,"ɗan uwa na kawoka fa",sakkowa ya yi yana kallon get ɗin"wannan ne gidan da gaske","kalli katin hannunka mana abinda yasa kagan munzo harnan ma saboda adaidaita sahu ne wai ko mata aka ɗakko shiyasa muke iya shigowa har anan","tabɗi nawane kuɗinka","kawai kawo ɗan uwa",hannu yasa a aljihu ya ɗakko kuɗi ya ƙirga ɗaribiyar ya bashi","nagode sosai aboki",ya juya kenan ya dakatar dashi ɗan uwa ga number wayata in wata dama ta samu digiri ne dani",dariya yayi ya ciro tasa ya miƙa masa ya karɓa yasa number ya bashi"me zansa to","kasa Abubakar mai mashin",dariya ya yi"ni kuma kasa Babban Yaya","yauwa zanma fi ganewa ba","to shike nan sai mun kuma haɗuwa",ya buga mashin ɗinsa ya bar wurin,ƙofar gidan ya ƙarasa ya tsaya kawai buɗewa akai akace shigo cikin mamaki da faɗuwar gaba ya shiga,gida ne ƙerarre na faɗa a jarida wani ne da uniform yazo"bismilla ance na shiga da kai ciki"sadda kansa ƙasa ya yi yabi bayan mutumin zuwa inda yaga ya dosa bin gidan da kallo yay tayi yara nata wasa wani babban wuri suka nufa wani ginine a gefe kamar rumfa amma wurin ya ƙayatu ga shimfiɗu na alfarma,mai masa jagorar wurin mutumin ya ƙarasa ya sunkuya daga baya "rakai daɗe ga shi ya ƙaraso",ɗagowa ya yi yana murmushi"tom sannu Musa","ba komai Alhaji",ya tashi ya bar wurin"bismillah mana Habibullahi","barka da warhaka Alhaji"ya hayo wajen nan gefe ya zauna ",Alhaji ya dubesa "zauna da kyau mana kaida kazo gida",gyara zama ya yi Alhaji yace"yauwa ko kaifa",wata ce da uniform itama ta ƙaraso wurin ɗauke da tire babba a gabansa ta aje sannan ta juya"Habibullahi bismillah","Alhamdulillahi Alhaji ina godiya","ba komai yarona"coffe kawai ya zuba sannan ya dubi Alhajin"Alhaji gani nazo me yasa kace kana nemana",numfashi yaja ya gyara zama sosai"Habibullahi nidai sunana Alhaji Aminu Tijjani inada yara bakwai duk mata kuma basu yi girma ba kai yaran ma duka bamai sha huɗu,ina da mata huɗu duka suna gidajan nan daka gani a lungun nan,ɗan kasuwa ne ni inada company guda uku fitattu a duniya sannan inada hannun jarika masu yawa a duniya, a gaskiya tun ganina dakai na wancan ranar naji kamin nai maka kallon ɗa kai tsaye shi yasa nace kazo inada matsaloli dayawa wanda da ace inada ɗa namiji nasan zai shige min gaba saboda na kawo inda ƙarfina ya yi ƙasa kuma duk na tare dani suna son suci riba dani ne ko amin wayo kuma harda na tare dani masu min aiki manyan wato manajojin da na ƙasa dasu,a yanzu wani lamarine ya taso kuma nayi iya bincikena naga kamar ba riba aciki sannan abin ya zama kamar gasa ne inaso na zame kuma bana so suce tsoro naji kasan dai masu kuɗi da ƴan kasuwa yanda suke","hakane Alhaji kukam akwai abubuwa dayawa na ƙalubale a gabanku kuma kuna ƙoƙari sosai","Habib wannan abu ba komai bane wani company ne a America na ƙera motoci kaf companyn shine na ɗaya aduniya gun sarrafa mota kowacce irice hannun jari zamu saka a wannan ma'aikata na zunzurutun kuɗi dala ba naira ba dala million dubu biyu a ayanda tsarin yake zai zama a komai da za'ayi ba mutum ɗaya zaina fitarwa ba rabawa za ayi kai ɗaya kowa ya fitar nasa inda yake so to wannan abu yasani a ruɗani sosai ina son shiga amma bana so kai me kace",tagumin da ya yi ya cire yana duban Alhajin "tabbas dole kayi tunanin wannan abu Alhaji kasan kuwa waye bature kasan wayonsa bazai taɓa haɗa abu dakaiba muddin ba zaici riba sama da uwar kuɗinsa ba,a yanzu ku nawa ne ƴan wannan ƙasar a cikin abin","to dai a yanzu waɗanda zamu sa hannu a Abuja zuwa dare mu talatin da ɗaya ne amma ɗayan ba indiye ne","talatin Alhaji kana nufin ku talatin da ɗaya kowa million dubu biyu tabɗijan amma baku da wayo wallahi gaskiya,a nigeria akwai irinku dama to wallahi karma ku fara wannan ta'asar",murmushi Alhaji ya yi yana jin daɗi aransa ganin yanda ƙaramin yaro har ta gano da illa a abin"ban ganeba Habibullahi ko kuma ba dani zakai wannan ba dakai zamu tafi Abujan kawai ayi acan ko",shafa kansa ya yi"dani Alhaji","eh mana kai ba ɗana bane suma suna zuwa da ƴaƴansu kuma zaka gani in munje yanzu kasanar da gidanku zuwa la'asar za'a azo a ɗaukeka kawo wayarka nasama number ta zuwa lokacin mai laukanka zai kiraka",bashi ya yi yasa masa shima ya ɗauki tasa sannan ya miƙe"au tafiya zakai ",sosa ƙeya ya yi"Alhaji ƙanwata ce Nana ba lafiya shine zanyi na koma na ganta"tashi ya yi shima "lallai wannan Nana da alama itace ƴar tawa",ɗan sos ƙeya ya yi"eh to Alhaji amma ai yarinya ce ba yanzu ba","ai wannan ba matsala bace yarona muje nasa akaika saima kawai ya gano wurin basai ma ana masa kwatance ba","hakane rankai daɗe",nan ya shiga gaba ya bisa a baya,wajensu Murtala ya nufa suna ganinsa suka miƙe"sannu da fitowa Alhaji","yauwanku Murtala kai wannan gida ka gano hanyar zuwa la'asar zaka koma ka ɗaukko shi","to Alhaji,rankai daɗe bismillah","ok Alhaji sai anjima","Allah ya nuna mana Habib ka gaida min da Nana ka ma ta sannu kafin nazo dubiya",ƴar dariya ya yi ya wuce dan har ya fito da motar nan ya shiga aka buɗe musu get suka fita. Sarakan gulmar unguwar majasar Iliya ne shayi na nan anyi do do sukaga babbar mota ƙirar zamani latest ta parker a ƙofar gidan su Babban Yaya acikin ƴan wajen wani ya kalli Ibrahim"IB kunyi manyan baƙi fa","wane irin manyan baƙi bansan gulma fa","inafa gulma ka taɓa ganin kalar wancan motar a layin nan idan ba wucewa tazo yi ba amma kalla yau a ƙofar gidan ku ta tsaya"..shiru ya yi sakamakon ganin wanda ya fito a motar,kuma driver ya fito suka ɗanyi magana sannan ya shiga ya juya ya bar layin,"kutumar kai IB ai Babban Yaya ne ya fito a motar can",wani ya faɗa yana ɗakabmai duka acinya mgana daɗi kenan"wallahi ka isheni Rabi'u kaga nabar maka wajen",yana wucewa suka dasa gulma daga ina yake kodawa ya haɗu haka dai sukaita yi baji ba gani,Ibrahim ma bai shiga gidan ba ya wucewarsa ya shige gidan kawu Rabilu an tafi musu dasu Sumayya da ya shiga ma basa nan suna gidan mu su Ya Fatu sunzo ana faɗa masa shima ya shiga. A tsakar gida yasamu su Umma suna tsigar zogale da sallama ya shiga suka amsa"a a harka dawo",a kan wata kujera yaja ya zauna yana dubanta"eh Umma dawowa nayi na shirya zamu Abuja da mutumin anjima da la'asar amma da alama sai gobe zamu dawo","to Habibu Allah ya tsare ya bada nasara a kula dai da shiga cikin manya","insha Allahu Umma","yauwa ga ƴan uwanka can sun iso gidan Baffan ku Fatima da Usaina","kai kice akwai baƙi a gidan bari naje ma mu gaisa","to ni naje suma yaran wasu nacan waɗannan dan su tayani aiki na hanasu zuwa","ai kuwa dai naje to". Tun daga sallamarsa Ya Usaina ta fito da gudu"bi a hankali karki faɗi da yara huɗu baki daina wawta ba",dariya tayi"ina Babban Yaya ai wannan halin bai ɓata shima maigidan haka yake shi yasa abin yaci gaba","kun haɗu da aiki da to,sannunku da zuwa ina yaran","sunacan sunbi Nana siyan wai alawar tsamiya","ita da ba lafiyar ƙafa ba amma ta fita yawo","to kai Babban Yaya manta Nana kayi ne kai dai mu shiga,Ya Fatu tace fushi ta ke da kai","nasani wannan Fatimar ƴar rigima ce","wallahi dai kam",tai sauri ta dafe bakinta ganin tana harararta ashe tana bakin ƙofar,shima murmushi ya yi yana faɗin"sakuwa waya taɓamin ke ne",da sauri ta juyo"kutt wace sakuwar taka wallahi ka girmeni innakai shekarunka ai na banu sai kishiyoyi","kai Fatu bansan me yasa bakyason kishiya ba","banaso kuwa amma shigo dai mu gaisa hirar tafi daɗi a zaune",ɗakin fal ya ganshi ya shiga shima"kai aku dalla kuyiwa mutane shiru","da sauri suka ɗago jin muryar Babban Yaya,Sumayya ce tayi gyaran murya"ansutu ko mutum yaci naman me kilago yanzu",dole dariya ta kamashi ya yi yana Sumayya daƙuwa"wallahi kun fiya surutu","kai Babban Yaya kaf dangin yawa saika same su akwai magana","ai kuwa kune sample ina makaranta fa duk naganku anan da ina cewa zamu KT gobe kuma wani uzuri ya taso min bazamu samu zuwa ba sai dai kadan wani satin",kai Aziza ta dafe"kash an ɓata min shiri tabbas","ya kuwa ɓatu tunda uzuri na yafi naki muhimmaci"nan ya zauna sukaita yi,hirarsu ba ƙarewa take ba sai kiran sallah ne ya fito dasu nan duk suka tsaya a tsakar gida"sannunku da zuba,dariya sukai suna faɗin"Aunty Mama zamuyi sallah muzo muci alala da kunun aya","saikun zo Habibullahi ga naka can akula ka tafi dashi ","na gode Aunty Mama",ya ɗauka ya fita,yana fita na fito a ɓuyar da nayi duk abinda nake Mama na kallona"Allah ya shiryeki Nana",Ya Fatu na dariya ta amsa da "ameen Mama ai da anyi hutu da ita zan tafi",tunkan ta gama magana nace"ban zuwa wallahi tabb ba Aunty Maman acan ban iya zama","to ai sai kuyi zamanku","yauwa Ya Fatu unmm ina ma wannan me aikin naki me bajajjen hancin nana",kai ta dafe"na shina ni Fatima ƴar yayar Hajiya ce fa wannan da ki ka gani ba me aiki bace","yo Ya Fatu nan ƴar gidace amma takeyi kamar ƴar wanke wanke",dariya sukai"Nana matsalu ita wannan haka take ko agidansu har dukanta ake","to Ya Fatu ai ma ta aure ƙauye mana","Innanillahi tayi auren ma ai Nana amma tana Abuja",zabura nayi kamar wadda aka faɗawa mutuwa"Abuja dai Abuja tamu ta state and capital amma wannan miji ko ɗan iska shi ya rasa wazai aura sai mai zubin ƴan ƙauye","ƙaniyanki Nana ke har kinsan matar da ta dace a aura","lallaima ya Fatun nan kullum muna yawo maƙota muna ganin ya ake rayuwar ai yaci muyi hadda","hakane kam amma dan ubanki inkina ƙarewa mutane kallon gidan su kema naki haka za'a ana masa kallon tsaf kuma duk kyansa sai an kushe",taɓe baki nayi"sun haɗu da wahala kuwa ni kinga na tafi gidan Gwaggo Asama'u jan magana kinsan kullum naje saita min tass tace min mai kama da aljanu ita kaf danginta ba mai kama dani anya kuwa uwata da tana da cikina batai gamo ba",dariya sukaita yi ni kuwa ko ajikina kuma nasa hijabina na fita inaji Mama na kirana nai burus da ita. Huɗu saura ni asannan nake cin nawa abincin a tsakar gida sai masifa nake an shanye kunun aya ba'a rage min ba naji muryar Babban Yaya na sallama,tashi nayi da gudu na ɗane masa jiki cak ya ɗagani sama "Darling sis ashe kin warke",kai na sunne"eh mana dama can na warke ai sonake kawai ka rama min shi yasa nayi wannan lamfar",sauke ni ya yi"kin kyauta ai ina su Mama","suna ciki kazo muci abinci","ni naci abinci kije kici naki",buga ƙafa nayi na fara wulla hannu zanyi kuka,da sauri ya riƙoni"sorry zanci muje",a tabarmar ya zauna munaci tare kallona ya yi"Sweet sis zan tafi Abuja fa yanzu",baki na hangame "Babban Yaya Abuja tamu ta Nigeria zaka","eh mana kimin addu'a","Allah ya kaika lafiya ya tsare yasa kayi nasara a abinda kaje yi",lumshe ido ya yi ya haɗa hannunsa da nawa"naji daɗin addu'arki bari nayiwa su Mama sallama","to kayi na rakaka waje"ciki ya shiga ya musu sallama suka masa addu'a sannan ya fito na bishi har gidan Umma da zai tafi harda kukana,shima da kansa da saida jikinsa ya yi sanyi yasan bana son kotafiyar wuni ya yi bare yau ta kwana ka rantse aurena yake. Saida naga motar ta ƙule sannan na koma cikin gidan"Umma ina kunun","to Nana ya fushi kuma yanzu yanzu",kukan daya maƙale min na saki"ni Umma kice ya dawo"bokitin hannunta ta aje tazo ta kama hannuna"kiyi shiru mana bakyason yayanki yazama wani a duniya","inaso mana","to kiyi masa addu'a Allah yasa yasamu nasarar abinda yaje yi","to Umma","yauwa ƴar albarka jeki ga kunun can ki ɗauka in bai isheki ba kizo ki ƙara","zaima isa Umma na tafi gida","au bazaki tsaya ni ba","to Ummata gama ina jiranki","yauwa Nanan Iyyo Nanan Alhaji Baffa Nanan Yayanta",ƙafa na buga aƙasa nai juyi"wayyoUmma kamar na goyaki",ranƙwashi naji na dafe kan"kai kai"na juya da sauri"Ya Maryam daga tafiyar Babban Yaya har an fara cinzalina",dariya tayi ta janyo hannuna"bana son sharri Nana yi haƙuri kar yana dawowa ki ƙala min kisa ya mazgeni dan ba kunyar dukanɓ na zaiji ba","to kinyi sa'a Umma ta ceceki sabida ta razgan kirari mai daɗin gaske","Allah ya shiryeki Nana","amen inda gaske ki ke","ohh ni Maryama","bakiga komaiba muddin kina tare dani",tafiya tayi tana dariya nima haka,Umma na jira ta gama sannan muka tafi gidan mu tare tana ɗauke da bokitin kunu,tsabar gulma nacin Saude har ta kusa faɗawa kwata tana waigen Umma ni na lura da ita nai saurin ma ta magana"zaki faɗa kwata fa",da ta sauri dai daita kanta tana hararata,hannuna Umma ta kama muka shige gida sai sheƙa dariya nake kamar taɓaɓɓa"ku kuma fa haka Umman yara",Mama da ke gab da soro ta fara tambaya"bari Halima wannan yarinyar sai fatan shiriya","ai Nana sai addu'a wallahi"duk ina jinsu amma nai burus,yaran su Ya Fatu ma naja muka shige gidan Iyyo. 🤚🏻😂🤚🏻 Shagali Nana Vote Share & Comments Ƴan uwa Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂ 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 *𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔* 𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠 Story & written by *FATIMA AMINU* *Ummu Saddi'q* Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 chapter 1️⃣0️⃣ A filin sauka da tashi na Malam Aminu Kano suka sauka garin luf luf ba rana mai zafi sosai motoci na musamman ne suka zo ɗaukarsu har hotel ɗin da zasuyi zaman dan abin na kusa ne ba a buƙatar kowa ya yi nesa shi yasa aka bawa kowa masauki anan,shima ɗaki daban aka kaishi nana Abba ya yace ya huta sosai kamin lokacin yayi da to ya bishiya zauna shi kuma Alhaji ya fita zuwa nasa masaukin ransa fes,bai jima da fita ba wani ma'aikaci ya shigo janye da keken da ake sagale kaya tashi ya yi ya aje masa kayan a wurin yana risinar da kai cikin harshen turanci ya fara magana"Alhaji yace ka shirya bayan sallar isha zanzo na raka ka inda yake",shima amsa masa ya yi sannan ya fita,kallon set set na suit ɗin ya shiga yi gasu nan har bakwai kuma kana gani kasan ba ƙana na bane,kuma zama ya yi ya janyo wayarsa ya kira ƴar nokiar Umma ya faɗa ma ta sun sauka lafiya addu'a tamai sannan ya kashe yana ajiyar zuciya,bai kuma magana da wani ba har ya fita ya yo sallar magaruba yana shigowa wayarsa tayi ƙara ɗaukkowa ya yi yaga Hajara kan kujerar wurin ya zuna yana ɗagawa"barka da sauka shine baka kira kasanar min ba","mun sauka lafiya ban kira ki bane ko kin manta kin faɗan bakya gida zaki kai amarya","eh hakane am sorry amma komai normal","sosai ma","to sai anjima",kan ya yi magana ta kashe,bin wayar ya yi da kallo shi baisan meyasa bata iya magana ba saita suyi aure ayi kaza ayi kaza Babban Yaya sarkin wanka yanzumma shi ya shiga ya jima sannan ya fito,saida ya shafa mai da yake ajiyeye a kowanne ɗaki na hotel ɗin dan dama Alhaji yace daga shi sai kayan jikinsa zai taho,sanda ya gama shirin ana sallar isha tasa ya yi sannan ya zauna jiran lokacin,ba daɗewa saiga Alhajin da kansa ma yazo kallonshi ya shiga yi kamar maisonntuna wani abu amma ya kasa gano komai game dashi saima murmushi da ya yi"lallai ɗana ashe babban mutum ne kai haka",kansa yaɗan shafa yana risinar da kai"haba Alhaji waye babban wannan ai sai ku","Habib"ya kirasa cikin muhimmanci"na'am Alhaji",kaɗarsa ya dafa"karna ƙara jin ka kira ni da Alhajin nan ni Abbanka ne ka ɗauke a haka har ƙarshen rayuwar mu dama ni a ɗa na ɗaukeka tun ganin farko","shike nan Abba bazan kuma ba insha Allahu","madallah muje bana son shiga wuri ana ƙarshe","hakane"nan ya shige gaba yabi bayansa amatsayinsu na maza to duk inda suka bi kallonsu ake sama da ƙasa,har ɗakin taro hakanne kuwa ba a gma taruwa ba,bin Alhajin suka shigayi da kallo suna mamaki dama yana ɗa babba haka amma ya ɓoyeshi,gaggaisawa akai sannan sauran suma suka gama shigowa tunkafin fara kowacce magana ya gabatar musu dashi amatsayin ɗansa,sannan aka fara abinda ya tarasu a wurin wakilin kowa na wurin Alhaji Abubakar jega shine ya fara gabatar da asalin abinda ya haɗa su wurin cikin harshen turanci saboda akwai yare waɗanda hausar su batayi nisa ba sosai sannan gama Dr Kumar wanda ya zaɓi zaman ƙasarmu saboda yaga amanar mu ta masa,kamar yadda ku ka sa ni zamu saka hannayen jari ga babban company na motoci dake ƙasar america kuma ayau muka yanke zamu sa hannu a takardu na yarjejeniya sai dai tun awancan lokacin Alhaji Aminu bai gama yadda da wanna magana ba yace abari dai zuwa yau aƙara tattaunawa akai kuma kowa nada damar ya amince ko akasin haka ko kuma ku kawo shawarwari waɗanda suka danganci wannan batu sannin kanku ne zamusa kuɗi a wannan harka saboda cigaba ne ba wai faɗuwa ba"hannu ya ɗaga masa nan take ya yi shiru ɗago kai ya yi yakallesu kowa ya shaida ransa aɓace yake ga wani kallo yana musu tsit sukai kamar suna gaban ubansu ƴaƴan saura dake wurin mamakin irin wannan nuna ɓacin rai sukai,jayo ƴar loudspeaker ta gabansa ya yi ya miƙe tsaye dan abin yafi gaban zama kamar zai rufesu da duka ya fara magana"bazaku sa hannun ba kuma bazakuyi haɗin gwiwa dasu ba"kallon kallo aka shiga yi ya yinda wani sanyi ke ratsa zuciyar Abba yasan tabbas dama za ayi haka,katsewa kowa tunani ya yi"ku yanzu banda abinku dama kuna da irin waɗannan dukiya haka amma bazaku taimaki ƙasarku ba ku kalla yadda muke fama masu digiri ba aiki amma kuna son ƙarawa masu ƙarfi me ku ke tunani ne waɗannan turawan zasuti harka daku ne batare da sun gano zasu sami riba mai gwaɓi ba,to bari kuji wallahi tallahi bature bature bazai taɓa aminta da baƙar fata tafishi ɗauka ka ba wayo kawai zasu muku su kaiki ƙas kai bawai Allah ana ganin ka ba indiye ne dan Allah faɗa musu suwaye turawa dan ina tsammanin kunfi kowa shan wahala ahannun su sannan ku ka sami ƴanci,wannan ƙasa ta Nigeria a kaso ɗari na India ko ɗaya bamu ɗauka gaba ɗayan ƙasar Nigeria mu million ɗari da sittin ne ko kana zaɓe ko baka yi ƙasar india su million dubu ne da ɗari biyu ko ɗari uku kunga ko yawan ƴan sandan su bamu kaiba amma anan ƙasar bamu iya komai ba sai zaman banza da gulmar duk wanda ya gilma,to wallahi bazaku yi wannan harkar ba kun ma ji ai ni ɗanku ne ko to saurareni da kyau",kamin ya gama maganar Dr Kumar ya miƙe ya fara tafawa sannan kowa ya shiga tafawa suna murmushi dan ya birge kowa sai sukaji inama ɗan su ne wannan yazo da wannan babbar fasaha murmushi ya yi ya gyara tsaiwa dan ya kasa zaman ma ji yake kamar ya yi bindiga dan haushi"abinda nake so kowa yasa nutsuwarsa akan maganar da zanyi,a madadin shiga harkar mota wadda tazama gama gari bakanike ma sai ya haɗa mota,mai zai hana mu zama masu ƴan kasuwa ta fannin daban daban,ma'ana zamu yi company da za'ana sarrafa copmuter ta ma'aikata da laptop,ipad wayoyi na zamani manya da ƙanana waɗannan kaya dana lissafa akullum kasuwarsu sama takeyi bata ƙasa kuma kullum kasuwa ake shiga dan yin harkarsu,wannan company zaiyi mazauni ne aƙasar Dr Kumar sabida sun fimu igiyar sadarwa mai ƙarfi,za 'ayi wannan aiki kamar yadda ku ka ambata akan kuɗaɗen da ku ka yanke,ba ƙarin ko ƙwandala da kuɗin za'ayi aikin a zuba kayan aikin sannan aɗebi ma'aikata,wannan company kayan da za'a sarrafa cikinsa ba dun ƙuleshi za'ana yi ba rabashi za ayi kowa ya fitar dukkan abinda kasuwa tayi anan za a haɗa a cire

Chapter 4 of 32