zuciyarne tasoma ƙoƙarin kawo mata wani mummunan tunani, hakan yasa tayi saurin ɗaukar lufayanta tasanya, tare da ɗaukan takalmi flat shoe ta zura aƙafafunta, lokacin da tafito falon a tsaye ta sameshi yana ta kaikawo da alama yana cikin damuwa.
Yanaganinta yace "Yauwa muje ko" haka suka fito yana gaba tana biye dashi abaya, gani tayi ya tsaya yanawa me gadi magana , hakan yasa taɗan tsaya itama agefe.
Tafiya suke babu wani wanda yace da ɗan uwansa wani abu. Har saida sukayi nisa da gidan kafun yaɗan rage gudun motar, kallonta yayi tare da cewa. "Inaso daga yanzu ki fara amsa sunan ƙanwata, SOORAJ baida lafiya yana asibiti yanzu haka, nasan yana da buƙatar kulawanki adaidai wannan lokacin, please Dan Allah Ziyada ki kula da Sooraj, shiɗin mai rauni ne akowani ɓangare, kulawarki kaɗai yake da buƙata"
Ji tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, yayinda idanunta suka cicciko da ƙwalla, damuwa ƙarara ta bayyana akan fuskarta, duk da batasan asalin sunansa ba , amma jikinta ya bata cewa SOORAJ shine me taimakonta. Har suka isa babban asibitin bata sake cewa komai ba, saidai gaba ɗaya bata da natsuwa. Haka suka shiga cikin asibitin jiki asanyaye, direct wani ɗan ɗaki suka nufa, suna shiga Mas'oud ya durƙusa tare da sake gaishe da su Abba da Umma, Abba ne kaɗai ya iya ƙarfin halin amsawa domin Ummu kam Kuka take har yanzu, cike da ladabi Ziyada ta durƙusa har ƙasa ta gaidasu, Abba ya amsa yana me kallonta, sai alokacin Ummu dake kuka ta ɗago kanta ta kalli Ziyada. Ganin irin kallon da Ummu keyiwa Ziyada yasa Mas'oud cewa.
"Amm Abba dama wannan ƙanwatace ƴar Baffana ne dake Sokoto, tana karatune anan, sannan kuma suna da kyakkyawan alaƙa tsakaninta da Sooraj, shine nace mai zaihana tazo tana tayaku kula dashi tunda yanzu sunyi hutun makaranta" Yaƙare maganar yana ɗan sosa bayan kanshi, domin shi kansa yasan ya shiryota.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da cewa "Tabbas hakan da kayi ka kyauta Mas'oud, domin dama kaga zaman Ummu'nku anan bazai yi wuba, saboda tunda tazo kuka take, nikuma banason kukannan!" Abba yafaɗi haka cike da damuwa.
Ɗan ɗagowa Ziyada tayi ta kalli wacce ake ƙira da Ummu, tsananin kaman da tagani na me taimako akan fuskar matar shiya sanya tayi tunanin ko mahaifiyarsa ce, to amma idan da yana da iyaye aida tasan bazai zauna agidansa shi kaɗai ba, dole ne zai zamana iyayensa suna tare dashi.
Kallon Ziyada Ummu tayi sosai, wani tunanine yake ɗarsuwa acikin ranta, bazatace bata yarda da maganganun da Mas'oud ya faɗa ba, amma ita ta haifi Sooraj tasan kusan gaba ɗaya halayyarsa, mutumin da bayason mu'amala dako wacce irin mace yau shine za'ace wai akwai kyakkyawar alaƙa atsakaninshi da wata?.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ !!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 23*
Abba da Mas'oud ne suka tashi suka fice daga cikin ɗakin, kasancewar alokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Magriba. Ummu ne tafito daga toilet ɗin dayake cikin ɗakin, fuska da hannayenta duk ruwa da'alama alwala tayi.
Kallon Ziyada dake zaune jigum tayi. "Jekiyi alwala" Ummu tafaɗa tana mai ƙoƙarin shimfuɗa darduma akan tiles. Sumu sumu haka ta wuce toilet ɗin ta ɗauro alwala, hanu tasanya acikin hijab ɗin dake jikinta, ta zaro ɗan kwalin dake kanta, shimfiɗawa tayi akan tiles, sannan ta hau tare da daidaita tsayuwarta, akan ɗan kwalin ta gabatar da sallan Magriba, ko da ta idar da sallan, samun kanta tayi dayin shiru, tare da jingina kanta da jikin bango, gaba ɗaya jin zuciyarta take babu daɗi, babu wani abu da takeson gani sama da Helper ɗinta, sosai hankalinta yake atashe, sannan gefe guda kuma, ga kukan da taga mahaifiyar Sooraj ɗin nayi yasake ɗaga mata hankali.
Dukansu daga ita har Ummu babu wacce tatashi daga kan abun sallanta, har aka ƙira sallan isha, baga Ummu kaɗai ba hatta Ziyada saida tasanya Sooraj cikin addu'anta. Ƙoƙarin ɗaura ɗan kwalin kanta take, aka turo ƙofar ɗakin aka shigo. Alh.Mansur ne dakuma Mas'oud, Mas'oud ne ya aje basket ɗin dake hanunsa, tare da kai dubansa gareta.
"Ziyada ki zubawa Ummu abinci taci, kema ki ɗebi naki kici, zuwa anjima likitotin sun tabbatar mana da cewa zamu samu ganinsa!" Mas'oud yaƙare maganar cike da ɗan yanayi na damuwa. Alh.Mansur kuwa kasa ma cewa komai yayi, zama kawai yayi akusa da Ummu tare dayin shiru.
Ɗaukan basket ɗin Ziyada tayi tare da zaro wasu plate, kulan dake cikin basket ɗin ta buɗe tare da sanya spoon ta zuba lafiyayyar jalop rice wacce taji bushashshen kifi acikin plate ɗin. Cike da ladabi ta ƙarasa gaban Ummu, cikin muryarta dake rawa tace. "Ummu ga abinci"
Kai Ummu tagirgiza cike da damuwa tace.
"Banajin zan iya cin abinci batare da na sanya ɗana a idanuna ba, kici kawai!" gaba ɗaya muryar Ummu rauni kawai take bayyanawa.
Hanun Ummu Alh.Mansur ya kamo, cike da tsananin so da kuma nuna kulawa ga matartasa yace. "Ki kwantar da hankalinki Sulaimiyya, Isha ALLAH Sooraj zai samu lafiya, addu'an mu kawai yake da buƙata bakomaiba, kibar kukannan haka kuka banaki bane." Kallon Ziyada yayi tare da cewa.
"Miƙomin abincin nan na bata" karɓan plate ɗin abincin Abba yayi yashiga lallaɓa Hajiya Sulaimiyya akan taci, amma gaba ɗaya ta daburce taƙi ci, hawayene kawai ke silalowa daga cikin idanunta, shima kanshi Abban ƙarfin hali kawai yake amma damuwane ninke aƙasan ranshi.
Gaba ɗaya itama Ziyada kasa cin abincin tayi, lomanta uku ta ture plate ɗin abincin gefe, ji tayi ko kallon abincin batasonyi, hawayene suka ziraro daga cikin idanunta, da sauri tasanya gefen hijabinta ta share, tausayin halin da taga Iyayensa aciki take, musamman yanda taga hawayen mahaifiyarsa ya kasa daina zuba, jitayi gaba ɗaya zuciyarta ta karye..
Da ƙyar Abba yasamu Ummu taci 4 spoon na abincin. Dr.Mohd ne dakanshi turo ƙofar ɗakin ya shigo. Cike da tausayawa ya dubi dukkaninsu, da sauri Alh.Mansur yataso daga zaunen da yake yana cewa.
"Dr.Mohd ya dai, akwai wani cigaba ko kanaga kawai gobe mu wuce Germany ɗin?" Yanayin yanda Alh.Mansur yayi maganan kaɗai ya isa sanya zuciyar mai sauraro karyewa, domin kuwa kallo ɗaya zakayi masa kasan baya cikin wata nutsuwa, sosai rashin lafiyar Sooraj ɗin ke damunshi.
Ajiyar Zuciya Dr.Mohd yayi tare da kama hanun Alh. Mansur suka fice daga cikin ɗakin, ganin haka yasa Ummu fashewa da kuka, domin atunaninta wani abunne ya kuma sake faruwa, Mas'oud ne yayi ƙarfin halin fara rarrashinta.
"Calm down Alh.Mansur kazauna!" Dr.Mohd yafaɗi haka akaro na uku kenan, domin kuwa tun ɗazu yaketa yiwa Alh.Mansur ɗin tayin wajen zama, amma saboda ruɗun da Alhajin ke ciki, sam ya kasa zama.
"Bazan iya zama ba Dr.Mohd, hankalina amatuƙar tashe yake, kafaɗamin maiyasa ka kawoni office ɗinka? Shin wani abu yasake faruwa da SOORAJ ɗinne?"
"Na faɗama ka kwantar da hankalinka Alhaji, Insha Allah Sooraj zai farfaɗo nan bada jimawa ba, sai dai kawai akwai wata matsalane da sai yanzu, da mukayi masa gwaji muka san da ita!" Dr.Mohd yafaɗi haka yana mai shakkan abun da zai faɗawa Alh.Mansur, kasancewar baisan tayaya Alhaji'n zai ɗauki maganartasa ba.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'n!! Doctor mai kuma yasake faruwa?" Alhaji Mansur ya tambaya cike da damuwa.
"Amm bawata matsalabace Alhaji matuƙar za akula, nace dama tuncan kunsan cewa yana ɗauke da ciwon zuciya ne?"
Ai tamkar rugugin aradu haka Alhaji Mansur yaji sauƙan kalaman Dr.Mohd acikin kunnuwansa.
Daɓas haka Alhaji Mansur ya zauna tare da sanya hanu ya dafe kansa. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!" kawai yaketa ambata acikin rai da zuciyarsa. "Shikenan kuma lokacin dazai rasa ɗansa mafi soyuwa agaresa yazo, haƙiƙa wannan ƙaddaran tana da girma agaresu baki ɗaya, Allah yabasu ikon cinyeta!" yafaɗi haka acikin zuciyarsa.
Aƙalla yaɗauki kusan sama da 12 minute ahaka,
Idanunsa da sukai jajur dasu ya ɗago ya kalli Dr.Mohd.
"Idan nafahimci kalamanka Doctor kanaso kace dani Sooraj ɗana yana ɗauke da ciwon zuciya ko?"
"Ƙwarai kuwa haka nake nufi Alhaji, amma ciwon batayi tsanani sosaiba, idan har ya riƙe magani da yardan Allah Zai iya warkewa ako da yaushe, kada ka tashi hankalinka Alhaji, Insha Allah komai zaizo da sauƙi!!"
Inji cewar Dr.Mohd wanda yake cike da buri da kuma fatan ƙarfafawa Alhaji Mansur ɗin guiwa.
Ajiyar zuciya Alhaji Mansur ya sauƙe tare da cewa.
"Ni musulmi ne kuma nayarda da ƙaddaran da Allah Ya aikomin mai kyau ko marar kyau, kowani cuta aduniya tana da maganinta, cutar mutuwa ce kaɗai bata da magani, haƙiƙa komai da komai na Allah Ne, samun cuta da kuma sauƙi duk waƴannan ikonsa ne, kafun ka tsara naka shi yajima da tsara nashi, idan Allah Ya ƙadarta maka ƙaddara mummuna babu wani mahaluƙi daya isa sauya maka ita, haka idan ya nufeka da kyakkyawa babu wanda ya isa sauya maka ita, babu wani abu aduniya da yafi ƙarfin ikon Allah da kuma Addu'a, zamuyita addu'a Insha Allah komai zai zamo tarihi watarana!!" handkerchief ɗin dake cikin aljihunsa ya ciro tare da sanyawa yaɗan share ƙwallan da suka cika idanunsa.
Murmushi Dr.Mohd yayi tare da cewa "Haƙiƙa duk wani musulmin ƙwarai irinka akeso yakasance Alhaji Mansur, Allah yayi mana jagora"
Da "Ameen" kawai Alhj Mansur ya iya amsawa, sannan suka tashi suka fice daga cikin office ɗin.
Direct ɗakin da su Ummu suke suka nufa.
"Hajiya zaku iya ganinsa yanzu" faɗar Dr.Mohd.
Dukansu suka ɗunguma sukabi bayan Dr.Mohd ciki kuwa harda Ziyada. Wani waje suka nufa daganin wajen kasan na musammanne sannan kuma secret waje ne, wani ɗan corridor suka shiga sannan suka samu kansu a gaban wani ɗaki. Dr.Mohd ne ya tura ƙofar ɗakin ahankali, sannan suma suka rufa masa baya, Ziyada ce tayi na ƙarshen shiga. Tana shiga ɗakin idanunta suka hasko mata shi, kwance yake akan wani gado mai ɗan faɗi, fuskarsa na kallon sama, sanye yake da dogon wando babuko riga ajikinsa, sai bandage ɗin da aka lilliƙa awajen da akayi masa aikin cire bullet. Wata ƴar wayane aka sanya masa atacikin hancinsa, sosai ya ƙara haske, gashin kansa kuwa sun kwanta luf, sam batasan lokacin da hawaye suka gangaro daga cikin idanunta ba, jitayi ƙafafunta gaba ɗaya bazasu iya ɗaukarta ba. Hakan yasa ta jingina bayanta da wani dogon ƙarfe dake kusa da ita. Ummu kuwa sai aikin share hawaye kawai take da handkerchief ɗinta, shi kansa Alh.Mansur baƙaramin dauriya yayi ba da baiyi kuka ba, musamman ma da yanzu yasan cewa ciwukan ɗan nasa sun zame masa biyu. Mas'oud ma saida ya share ƙwallan tausayin abokinsa, domin kuwa duk wanda yaga Sooraj ahaka sai ya tausaya masa. Hannu Ummu takai ta shafi kansa, wasu sabbin hawayene suka sake fitowa daga cikin idanunta. Bazata iya jurewa ba, hakanne yasanya ta juya da sauri ta fice daga cijin ɗakin, koda ta fita waje tsayawa tayi ajikin wata rumfa tasaki kukan tausayin Sooraj, ganin Ummu tafita yasa Alh.Mansur binta saboda yasan aikin kuka zataje tai tayi, bayan kuma tana da Hawan jini, sam bayason ciwonta ya tashi.
Mas'oud ne ya kalli Ziyada dake ta zubar hawaye ta kafe Sooraj ɗin da kyawawan idanunta, duk abun da ke wakana ma sam ita batasan anayinsa ba, gaba ɗaya hankali da tunaninta suna ga Mr.Helper ɗinta, har batasan sanda hawaye ke zuba daga cikin idanunta ba.
"Ziyadah!" Mas'oud yaƙira sunanta murya asanyaye. Sai alokacin ta dawo daga duniyar tunanin da take, bata iya amsa ƙirannasa ba, saidai ɗago kai da tayi ta kalleshi.
"Ki share hawayenki ba komai kuka ke magancewa ba, kiyi masa addu'a kawai, yafi buƙatar hakan agareki" Mas'oud yafaɗi haka yana mai cusa hannayensa acikin aljihun wandonsa.
Kai kawai ta iya jinjina masa alaman "To" domin bazata iya cewa dashi komaiba ayanzu, gaba ɗaya jikinta ya mutu, zuciyarta tayi rauni, duk wani tunaninta ya tsaya cak.
Dr.Mohd ne yace sutafi hakanan saboda ba aso hayaniya tayi yawa a inda yake.
Alh. Mansur ne ya kalli Mas'oud tare da cewa. "Mas'oud kakaisu gida, nikuma zan zauna anan"
"Banajin zan iya komawa gida Alhaji, nikam nafiso na zauna anan" Ummu tafaɗi haka cikin muryarta da ta soma dashewa saboda kuka.
"Zaman asibiti banaki bane Sulaimiyya kuje kawai gobe da safe sai kuzo!" Alh.Mansur ya faɗi haka aƙagauce saboda sam bayason musu.
"Abba me zai hana kabiyomu na sauƙeku idan yaso ni sai nadawo na kwana anan ɗin"
"A'a Mas'oud baza ayi haka ba, nine nan zan kwana, kuje kawai saida safe idan Allah Ya kaimu, sannan kuma banyarda kabarsu su kaɗai agidaba, ka kwana agidan kaima" Alhaji Mansur yana gama faɗan haka ya juya ya koma cikin asibitin. Babu yanda Ummu ta iya haka ta shiga cikin motar Mas'oud ya ɗauki hanyar Maitaima dasu inda anan gidan Abba dake Abuja yake. Wani irin tamfatsetsen gida Ziyada taga sunshiga, gaba ɗaya ginin gidan, gidan sama ne, gida ne mai kyau da girma, komai na gidan gwanin ban sha'awa ne, ko ina dake cikin gidan awadace yake da hasken ƙwan wuta, Mas'oud ne yasanya key ajikin ƙofar ya murza. take babban ƙofar falon ta buɗu. haka suka kutsa kai cikin babban falon dake cike da kayan more rayuwa, kayan ƙyale ƙyale dana ado. Komai na cikin falon tsab tsab yake, Mas'oud ne ya buɗe gaba ɗaya bedrooms ɗin dake cikin falon, acan sama bedroom ɗin Ummu yake hakan yasa ya wuce sama direct ya buɗe mata nata ɗakin. Ɗakin dake kusa dana Ummu yace da Ziyada ta shiga, gobe zai kawo mata kaɗan daga cikin kayanta. Saida ya tabbatar da cewa dukansu sunshiga ɗakunansu, kafun ya dawo ƙasa shima ya shiga wani ɗaki.
Aƴan kwanakinnan tasaba duk dare saitayi wanka kafun ta kwanta saboda yanayin zafi da ake ciki, amma yau hakanan tasamu kanta da rashin duk wani kuzarinta, damuwar dake kwance aranta ma bazata bari tayi wani baccin kirkiba balle har aje ga yin wanka. Hijabin jikinta ta cire tare da ɗalewa kan gadon ta kwanta jigum, yayinda ta sanya hannayenta ta tallafe ƙuncinta. Tunanin Mr. Helper ne ya tsaya acikin rai da zuciyarta, ganinsa da tayi acikin ciwo yau yasanya hankalinta gaba ɗaya ya tashi, wani abu takeji agame dashi, wanda takasa tantance menene amma ta ta allaƙa abun da sunan TAUSAYI, juyin duniya tayi amma bacci yaƙi ɗaukarta, haka tayita saƙe saƙe har kusan asuba sannan tatashi ta ɗauro alwala.
Kamar yanda bacci ya guji Ziyada haka ya gujewa Ummu, haka Ummu ta kusan kwana tana sallah, sauƙi kawai take nemawa ɗanta awajen ALLAH, kuka kam tayishi, domin tun tanayinshi da iyaka ƙarfinta, har hawayen suka daina fita.
7:30 daidai taji anayi mata knocking ƙofar ɗakin da take ciki, dama tana zaunene akusa da ƙofar hakan yasa ta miƙe taƙarasa jikin ƙofar. Koda ta buɗe Mas'oud tagani tsaye. kafun yace wani abu tayi saurin cewa "Ina Kwana"
"Lafiya lau" ya amsa yana me miƙo mata wata leda dake hanunsa.
"Kayankine kishirya, saiki fito kiyi breakfast, anjima zamu koma asibiti"
Amsar kayan tayi tare dayi masa godiya, ta koma cikin ɗaki, shima juyawa yayi ya koma wajen Ummu dake zaune afalo, tun ɗazu ba abun da yake sai aikin rarrashi.
Wanka tayi sannan ta ɗauki doguwar rigan material blue wanda yakawo mata tasanya, ɗinkin rigan irin rapper gown ɗinnan ne, sannan tana da ɗan guntun hanu, kallon kanta tayi acikin madubi, tare da kallon rigan azahiri, mamakin inda yasamo rigan take, domin kuwa tasan baya ɗaya daga cikin kayanta nacan gidan, gaba ɗaya ma kayan daya kawo mata sabbi ne, kuma duk daga ɗinkin materials sai wasu atamfa guda biyu wanda aka musu ɗinkin riga da sket. Jihabin data gani haɗe da rigan material ɗin ta ɗauka tasanya ajikinta, kasancewar white skin gareta saigashi kayan sunyi mata kyau sosai. Afalo ta iskesu duka suna zaune, cike da ladabi ta rusuna ta gaishe da Ummu, amsa mata gaisuwan nata Ummu tayi tanaɗan dubanta.
Akan sofa ta zauna tare da tanƙwashe ƙafafunta, Mas'oud ne ya turo mata plate ɗin soyayyen chips gabanta tare da kofin tea.
Bata wani iyacin abincin sosaiba, tea ɗinnema ta ɗansha da yawa. Mas'oud ma sama sama yaci abincin, Ummu kam adole takecin abincin, hakan ma saboda umarnin da Alh.Mansur ya bata ne, da yace "Idan tasan bataci abinci ba karta sake tazo asibitin, idan bahaka ba kuwa zata gamu da fushinsa." banda haka babu abun dazai sanya tasanya wani abu na abinci acikinta.
Yauma dai aɗakin jiya suka zauna, gaba ɗaya zuciyoyinsu babu daɗi. Sai ƙarfe uku sannan Dr.Mohd yayi musu jagora zuwa ɗakin da Sooraj ɗin yake.
kamar jiya haka Ummu tayita aikin ƙwalla, Ziyada ma idanunta sunyi tab da hawaye, ɗan matsawa kusa dashi tayi tare da kafesa da idanunta, gani takeyi kamar zai buɗe idanunsa, gani take kamar bacci yake idan katasheshi zai tashi, gani take kamar duk abun da suke yana jinsu, dubanta takai kan ƴan yatsun ƙafarsa, ƙurawa babbar yatsar ƙafansa ta dama idanu tayi, gani tayi kamar yatsar nasa tana motsawa, gefen hijab ɗinta ta sanya ta share ƙwallan dake cikin idanunta, wanda suka sa take ganin komai dishi dishi, sake kallon yatsar ƙafannasa tayi, sai kuma taga bata motsi, da alama gizone idanunta keyi mata.
Kallon Alh.Mansur Dr.Mohd yayi tare da nuna Ziyada yace.
"Matarsa ce?"
"A'a ƙanwarsace" Alh.Mansur yabashi amsa shima yana mai kallon Ziyada wanda idanunta ke cike da ƙwalla.
Kai Dr.Mohd ya jinjina tare da cewa "Inaganin ka ɗauki Hajiya ku koma gida kawai, ita sai kubarta anan, naga kamar yarinyar bata da hayaniya zamanta awajensa bazai kawo wata matsala ba, amma idan Hajiya ce zata zauna kasan dole saita ƙara ta da hankalinta"
Cike da gamtsuwa da kalaman Dr.Mohd, Alh.Mansur ya jinjina kansa. "Tabbas maganarka haka take doctor, yanzu kuwa zamu tafi insha Allah"
Da ƙyar da dabara Abba yasanya Ummu agaba yana rarrashinta sukabar cikin asibitin, tare da Mas'oud wanda shine ke tuƙasu.
Ziyada ita kaɗai akabari acikin ɗakin daga ita sai SOORAJ wanda bashida maraba da gawa. Akan kujeran dake gefen gadon ta zauna, tare da kifa kanta ajikin gadon. Tananan zaune har aka ƙira sallan Magriba, Sallah tayi sannan ta dawo ta zauna. Kallon kyakkyawar fuskarsa tayi, zara zaran eye lashes ɗinsa ne suka kwanta aƙasan idanunsa, sukayi luf dasu gwanin burgewa, gani tayi gumi nata fesowa akan goshinsa, mamakine ya kamata domin kuwa sanyin AC har yaso yin yawa acikin ɗakin. ɗan kwalinta ta ɗauka tashiga goge masa gumin. Atunaninta ko sanyin AC'n ne yayi masa kaɗan hakan yasa taɗan ranƙwafo da kanta zuwa daidai fuskarsa, ahankali tashiga hura masa iskan bakinta akan fuskarsa. hannunta takai kan nasa hanun tashiga goga masa taushin tafin hanunta akan fatar hanunsa, tanayin hakane cikin wani irin yanayi mai ɗauke da nutsuwa. Aƙalla taɗauki kusan sama da mintuna goma tana yi masa haka. Jin ana ƙiraye ƙirayen sallan isha ne yasata miƙewa daga zaunen da take, ta juya kenan kamar amafarki haka taji ya damƙi hanunta.
*(Alhamdulillah! This is to inform all my lovely fans that this will be my last update and i will insha Allah continue after ramadan. Thank you🙏🏻.)*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*Wattpad*
fatymasardauna
#romance
*Taƙabbalullaha Minna Wa Minkum. May Allah make us stead fast on the path of the righteous,elevate our iman, forgive our sins and bless us abundantly. Ameen Ya Rab!!!*
*🥀EID MUBARAK My Lovely Fans🥀*
*Chapter 24*
Kamar amafarki haka taji sauƙan hanunsa acikin nata.
Da sauri ta waiwaya zuwa gareshi, amma sai taga ko motsi baiyi ba, hasalima idanuwansa akulle suke da'alama bai dawo cikin hayyacinsa ba. Ahankali ta koma ta zauna tare da kafe sa da ido, zara zaran eye lashes ɗinsa da suka kwanta luf luf take kallo, ahankali tayi ƙasa da idanunta tana kallon ɗan ƙaramin pink lips ɗinsa wanda suka ɗan bushe. Idanunta ta sake mayarwa kan lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa, baƙaƙen hairs ne kwance luf akan fatarsa, komai nasa me kyaune kuma gwanin burgewa. Kanta ta mayar jikin gadon tare da lumshe idanunta. Wani irin tausayinshi takeji, daga wani ɓangare na zuciarta kuwa tunanin Farouk ne yazo yayi tsaye. Bazata iya faɗin me takeji game da shi ba, amma tabbas akansa tanajin wasu baƙin al'amura suna ziyartan ta. Zare hanunta dake cikin nasa hanun tayi tare da miƙewa tsaye, toilet tashiga ta ɗauro alwalan sallan isha'i.
Tajima tana zaune akan sallayan. Wasu siraran hawayene suka silalo daga cikin idanunta, kallonta takai zuwa garesa, wasu sabin hawayene suka sake fitowa daga cikin idanunta, hakanan batasan me yasa ba aduk sanda ta ɗaura idanunta akansa takanji zuciarta ta karye, tasan da cewa ita mai raunice tun tuni, amma akansa raunin da takeji na dabanne. Tajima zaune akan sallayan har kusan 9 pm sannan ta tashi ta koma bakin gadon ta zauna. Kanta ta ɗaura adaidai saitin kanshi tare da lumshe idanunta. Mintuna goma tsakani bacci ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba.
Ahankali breath ɗinta ke fita, yayinda hucinsa ke sauƙa adaidai saitin kunnensa, ahankali yasoma buɗe idanunsa har ya waresu gaba ɗaya, akan zanen pop'n dake cikin ɗakin ya tsayar da idanunsa, sosai idanun nasa suka sauya kala daga farare zuwa kalan ja, sannan lokaci guda suka ƙanƙance sai tarin eye lashes dake samansu wanda yayi wara wara, wani irin ciwo yakejin kansa nayi masa, yayinda yakejin wani zogi na musamman adai dai chest ɗinsa. Lumshe gajiyayyun idanunsa yayi tare da sauƙe wata gajiyayyar ajiyar zucia. Ahankali ya ɗan yunƙura tare da ɗan jingina bayanshi ajikin pillow, saida ya ɗan cije pink lips ɗinsa sakamakon wani irin zogi dayaji ƙirjinsa nayi, hanunsa yakai kan wani ɗan madanni dake gefen gadonnasa ya ɗan danna da ƙarfi har saida yayi ƙara. 3 minute tsakani saiga wata Nurse tashigo cikin ɗakin da gaggawa. Ganinsa azaune yasa tashiga tambayarsa jikinnasa. Da kai kawai ya iya amasa mata, ganin haka yasa tafita da hanzari don ƙiran Dr.Moh'd.
Baƙaramin daɗi Dr. Moh'd yaji ba sakamakon jin cewa wai Sooraj ya farfaɗo, da ƙwarin guiwarsa haka ya nufo ɗakin da Sooraj ɗin ke kwance.
Checking ɗinsa yayi sosai sannan ya tambayesa ko akwai wani abu dake damunsa. Kai kawai Sooraj ya iya girgizawa, sannan yayi masa nuni da chest ɗinsa daidai inda aka ɗaure da bandage. Alaman nanne kawai ke masa zafi.
Wasu magungunan kashe zogi Dr. Moh'd ya basa ya sha, sannan yace masa yaɗan kwanta zuwa da safe. Har Dr.Mohd yagama abun da zaiyi yafita Ziyada na bacci bata sani ba. Shiru haka Sooraj ya koma ya kwanta tare da lumshe idanunsa, tunanine cunkushe acikin ransa, _ƘADDARA_ itace abun dake ɗawainiya da rayuwarsa, sau da yawa yakansamun kansa acikin ƙuncin rayuwa, sai dai dole ayanzu zai daure don yaga yayi faɗa da zuciyar da take ƙoƙarin hanasa ɗaukar ƙaddaransa.
6:00 am dai dai Ziyada ta buɗe idanunta, awahalce tayi miƙa saboda wani
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 38