Share this page
da takeyi atsorace takeyinsa, fatanta ɗaya kar tayi kuskure yayi mata masifa, tana tsaka da goge kan haɗaɗɗen royal table ɗin yatashi cikin tafiyarsa ta isa yanufi ɗakinsa. Tana ganin shigewarsa ɗaki, ta saki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, tare da share hawayen dasuka silalo daga cikin idanunta. 28/May/2020 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SOORAJ!!!* *Written By* Phatymasardauna *Dedicated To My Life (Sardauna)* *🌈Kainuwa Writers Association* _{United we stand and succeed;our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_ *https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation* *WATTPAD* fatymasardauna #romance *Chapter 26* Hanunta tasa da sauri ta goge hawayen daya sauƙo mata akan ƙuncinta, kitchine ta koma ta tare da cigaba da wanke wankenta...... RAJ Tsaye yake agaban shower ruwa na dukan jikinsa, hannayensa duka biyu ya sanya ya dafe jikin bango, idanuwansa wanda suka sha ruwa sukayi jajur ya buɗe tare da furzar da ruwan dake bakinsa. Maganganun Abba gaba ɗaya sun gama dagula masa lissafi, ko tantama bayayi koda sun nemo zaɓinsu sun aura masa awannan karonma bazai iya jure zama da mace ba, dole zai saketa, sannan kuma dole ne zasuyi fushi dashi, ayanzu kam baya tunanin zai sake yarda alaƙa ba masa nauyin wata ƴa mace akansa, koda sau ɗayane yanason iyayenshi su fahimcesa amma kuma hakan ya gagara, kashe shower'n yayi tare da jawo towel ya ɗaura akan weast ɗinsa, baidamu da yanda jikinsa ke ɗigan ruwa ba ya buɗe ƙofar bathroom ɗin ya fito, idan yace zai iya baje damuwowin dake ranshi to tabbas ƙwaƙwalwa da zuciyarsa bazasu iya ɗauka ba, kaya ya sanya ajikinsa tare da ɗaukan car key ɗinsa yafice daga cikin ɗakin, direct compound ɗin gidan ya nufa, wata baƙar 4matic ya buɗe yashiga tare dayi mata key, tun mai gadi baigama wangale gate ɗin da kyauba ya cilla hancin motarsa waje. Tafiya yake amma gaba ɗaya hankali da tunaninsa suna wani waje daban, ababban ƙofar asibitin yayi parking, yau bakamar ko yaushe ba, don bai shigar da motar tasa ciki ba kamar yanda ya saba. Direct office ɗin Dr.Yunus ya nufa, yana knocking aka bashi izinin shigowa, kujera yaja ya zauna tare da miƙawa Dr.Yunus hannu sukayi musabaha, cike da fari'a Dr.Yunus yace. "Yajikinnaka ina fata dai ankama waƴanda suka aikata laifin?" "Dasauƙi!" Sooraj yafaɗa aɗan gajarce kasancewar bayason zancen yayi tsawo. Murmushi Dr.Yunus yayi domin sarai yasan halin Sooraj sai mutum ya shekara yana masa magana baitanka ba. Gyara zama Dr. Yunus ya sakeyi tare da cewa "Result ɗinka yana ajiye tun after 1 week" Wata ƴar drawer dake jikin table Dr.Yunus ya jawo tare da zaro wata farar envelope. Miƙawa Sooraj yayi tare da cewa "Komai yananan daidai, nayi duk wani bincikena dazanyi Sooraj amma gaskia bangano wata sabuwar matsala ba, magungunan dana baka acan baya sune kawai zakana sha har abubuwa su daidaita!" Dr.Yunus yafaɗi haka cike dason kwantar da hankalin Sooraj. Wani murmushin gefen baki wanda yafi kuka ciwo Sooraj yayi, shikaɗai yasan wani irin zafi zuciyarsa keyi masa awannan lokacin, karɓan takardan kawai yayi tare da sake bawa Dr. Yunus hanu sukayi musabaha, daganan yafice daga cikin office ɗin, wani irin kallon tausayi Dr.Yunus keyiwa Sooraj, sosai matsalan Sooraj ɗin ke ɗaure masa kai, iya binciken duniya sunyi shida abokan aikinsa amma sam su basu iya gano matsalan Sooraj ba, hasalima komai nasa lafiya lau yake bashi da wata tawaya a halittar jikinsa. . Tunda yafito daga cikin office ɗin Dr.Yunus yake ganin duhu a idanuwansa, cikin cijewa ya ƙarasa wajen da motarsa take, yana shiga ya kifa kansa ajikin steering motar tare da fesar da wani breath me ɗumi, aƙalla yaɗauki kusan mintuna 9 ahaka batare dako motsi yayi ba, gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya cak. Da ƙyar ya iya ɗago kansa, idanuwansa tamkar jan garwashin wuta haka suka koma, Envelope ɗin da Dr.Yunus ya basa ya buɗe, tare da zaro wata ƴar farar takarda dake ciki, ahankali ya warwareta tare da sauƙe idanunsa akan rubutun dake cikin takardan . Yana gama karanta abun dake cikinta ya duƙunƙuneta tare da rumtse idanunsa da ƙarfi. Laɓɓan bakinsa yaɗan ciza tare da ɗauko wata lighter ya kunna, takardan yakawo jikin lighter'n take ta kama da wuta, sauƙe glass ɗin motar yayi ƙasa tare da cilla takardan waje, take takardan ta ƙone ƙurmus, key yayiwa motarshi tare da cillata kan titi yabar wajen.... Ziyada kuwa tana kammala wanke wankenta, ta shige ɗaki bata kuma sake fitowa ba, duk da cewa zaman ɗakin bawani daɗi yakeyi mata ba amma kasancewar bata da abunyi yasanya ta gwammacewa kanta zama waje ɗaya. *** After 3 days. Tunda Abba yayiwa Sooraj maganan aure sai ya zamana Sooraj baya zaman gida kwata kwata, idan yafita tun safe bazai dawoba sai after Sallan Isha, kafunnan Abba yajima da dawowa suna tare da Ummu, sam bayason Abba yasake ɗago masa da wannan maganan domin magana ta gaskiya aure agareshi bamaiyiwuwa bane. Itakuwa Ziyada adaddafe haka take rayuwar cikin gidan duk dama Ummu na sake mata amma bawai wani sabawa sukayiba shiasa takejin kanta atakure, kallone kaɗai abun dake ɗebe mata kewa ayanzu, daga gefe guda kuwa tana lissafin hutunsu wanda yanzu saura musu 1 week sukoma makaranta, har Allah Allah take lokacin yazo, duk da batasan menene makomarta a wajensu ba, batasaniba ko zasu koreta ko zasu barta... 5:15 pm. Kwance yake akan makeken bed ɗinsa wanda yaji bedsheet na alfarma, dagashi sai long pencil jeans yayinda earpiece ke saƙale a kunnuwansa, gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗinsa, Samsung Galaxy S20 ɗinsa ne tasoma ƙara alaman shigowan ƙira. Saida wayar takusa katsewa sannan ya zare earpiece ɗin dake kunnensa, ganin sunan Abba nayawo akan screen ɗin wayar yasanyashi ɗaga wayar da gaggawa, yana kara wayar akan kunnensa. Abba dake tsaye cikin falonsa jin Sooraj ɗin ya ɗaga wayan yasanyashi cewa. "Kazo kasameni yanzu afalona!" ƙit yakashe wayan batare dayaji me Sooraj ɗin zaice ba. Ahankali Sooraj yasauƙe wayan daga kunnensa tare da sauƙe ajiyar zuciya, rufe laptop ɗin yayi tare da zuro ƙafafunsa ƙasa, wata bruberry button shirt fara ya ɗauka ya sanya ajikinsa, bedroom slippers yasanya aƙafansa kana yafice daga cikin ɗakin. Tun da ya doshi falon Abban yaji zuciyarsa na bugawa, sam baison sakejin wani abu dazai ɗaga hankalinsa. Zaune yasamu Abba akan kujera yana duba jaridan daily trust dake riƙe ahanunsa, zama yayi akan sofa tare da tanƙwashe ƙafafunsa. "Sannu da hutawa" yace da Abba cikin nutsuwa. Gyara zama Abba yayi tare da aje jaridan dake hanunsa. Kallon Sooraj ɗin yayi sosai tare da ɗanyin gyaran murya. "Ina ka ajiye maganan da mukayi dakai? Shin kasamo wacce kakeso ɗin kokuwa?" Abba yatambaya babu alaman wasa akan fuskarsa. Ɗan shiru Sooraj yayi tare da haɗiye wani yawu me ɗaci da lokaci guda ya tsaya masa amaƙoshi. "Kayi haƙuri Abba, amma Bansamuba!" yafaɗi haka cikin raunanniyar murya. "Shikenan babu ma buƙatar kasamo da kanka, Na auramaka ƴaƴan abokaina basau ɗaya ba basau biyu ba kana sakosu babu wani babban dalili, to ayanzuma zan sake ɗaurama aure da ƴar abokina Alhaji Naseer, ina tabbatarmaka da cewa wannan shine naƙarshe, sannan kuma koda wasa idan ka sake kayi gigin sakinta wallahi! wallahi!! babuni babu kai, zan janye hanuna daga duk wani lamarinka, ai kai ba ƙaramin yaro bane kasan daidai kakumasan ba daidai ba, wannan umarni nake baka saika shirya inaso acikin satinnan kaje ka ganta, sannan kuma tana shekaran ƙarshe na kammala degree ɗinta, saboda haka da zaran tagama za a ɗaura muku aure, tashi kabani waje!!!" Abba yaƙare maganar murya akausashe. Sooraj dake zaune wani irin jiri ne ke ɗibansa, tamkar sauƙan garwashi ajiki haka yaji sauƙan maganganun abba acikin kunnuwansa, take idanunsa suka sauya kala daga farare zuwa jajaye, wani irin ɗaci yakeji amaƙoshinsa, da ƙyar ya iya tashi yanufi hanyar fita daga falon, da kallo Abba yabisa har ya ɓacewa ganinsa, shikam har acikin ransa yasoma zargin ko aljana ce ta shafi Sooraj ko kuma asiri aka mishi, saidai koma menene shidai yana kan ra'ayinsa na dole Sooraj sai yayi aure, domin aganinsa idan da akwai mace akusa dashi to ko bakomai zata rage masa kaɗaici. Sooraj kuwa koda yabar part ɗin Abba kai tsaye garden yanufa, wani irin ƙunci yakeji azuciyarsa, jiyake kamar yaita tsala ihu kozai samu relief, zama yayi akan wata beautiful chair tare da lumshe idanunsa, wani irin zafi zuciyarsa keyi masa ahankali yake ambaton sunan Allah acikin ransa lokaci guda yaɗanji zuciyarsa tayi sanyi, sake lafewa acikin kujeran yayi tare da maida idanunsa ya kulle tamkar wanda yake bacci. Ziyada ce ta fito daga part ɗinsu, hanunta ɗauke yake da wani bowl me kyau, sanye take cikin riga da wando na Indian mai kama da pakistan, dayake kalan kayan blue ne shiyasa suka mata kyau sun karɓi white skin ɗinta sosai, ɗan kwalin kayan ta yafa daga kanta zuwa ƙirjinta. Kai tsaye take tafiya zuwa Inda Ummu tace taje ta ciro mata mango, zatayi mango juice. Tana jefa ƙafanta acikin garden ɗin wani Irin sassanyan ƙamshi yadaki hancinta, wani irin ni'ima ne ke tashi acikin garden ɗin, sanyine me daɗi yake ratsa ko ina najikinta, baki buɗe haka take kallon komai dake cikin garden ɗin sosai wajen ya ƙawatu, ƙamshin kayan itatuwane kawai ke tashi. Cikin nutsuwa take tsinkan jajayen mango ɗin. Ahankali ya ware idanunsa ya sauƙesu akanta, lumshe idanunsa yayi tare da sake buɗewa, duk da cewa bayanta kawai yake iya gani amma yanayin yanda take motsa jikinta yasanyashi kasa ɗauke idanunsa akanta, tana kammala tsinkan mango'n tajuya daniyan barin wajen, batare data kulaba tayi tuntuɓe da wani ɗan itace take bowl ɗin dake hanunta ya faɗi mangon ya watse. Bisa tsautsayi itama ta faɗi akan guiwowinta, rumtse idanunta tayi cike dajin zafi, ɗan cije laɓɓanta tayi tare da miƙewa tsaye bowl ɗin ta ɗauka tashiga bin Mangon da ya watse tana ɗauka da ɗaɗɗaya, tana maidawa cikin bowl, kanta aƙasa yake hakan yasa sam bata lura da akwai mutum awajen ba. Batare data luraba taji tataka wani abu tamkar ƙafan mutum, tana ɗagowa sukayi ido huɗu dashi, wani irin faɗuwa gabanta yayi take ƙirjinta yashiga dukan uku uku, ɗago idanunta dake ƙasa tayi take suka faɗa acikin nasa idanun, wani irin abu taji, wanda yataso tundaga ɗan yatsan ƙafarta har zuwa kanta da jijiyoyin jikinta. Pink lips ɗintane suka soma rawa da'alama magana takesonyi amma ya maƙale, ahankali yayi ƙasa da rikitattun idanunsa, sauƙesu yayi akan small lips ɗinta wanda suketa ɓari sukaɗai. (Note editing🙏🏻kuyi haƙuri yau nashiga busy shiasa banyi muku update da wuri ba please kuyi manage!) 30/May/2020 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SOORAJ!!!* *Written By* phatymasardauna *Dedicated To My Life (Sardauna)* *🌈Kainuwa Writers Association* *WATTPAD* @fatymasardauna #romance (🌺I'm really proud of you my Wattpad fans, i felt happy with the way you are commenting and voting my work therefore I dedicate this page to you🌺) *Chapter 27* Kauda idanunsa gefe yayi tare da ɗauke duk wata annurin dake kan fuskarsa. Ziyada dake tsaye tsaye still akansa cikin wata sarƙaƙƙiyar murya tace. "Kayi haƙuri....ban...kula bane!" Bai juyo ya kalleta bama bare tasa ran zai tanka mata, saboda haka ta ɗanja da baya tare da nufar hanyar fita da ga garden ɗin, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi wasu ruwan hawayene suka cika idanunta, itakam batasan me yasa tazama wawiya har haka ba, sam batasan meyasa dazaran abu yashiga tsakaninta dashi take saurin kuka ba, da wannan tunanin ta isa ga babban ƙofan da zai sadata da falon Ummu, hannayenta tasanya ta share hawayen dake kan fuskarta, sannan ta buɗe ƙofar tashiga. Shikuwa Sooraj tunda yakawar da kansa gefe baisake koda ƙwaƙƙwaran motsi ba, lumshe beautiful eyes ɗinsa yayi tare da maida kansa jikin kujeran, daddaɗan iskan dake hurawa acikin garden dinne ke ratsa ko ina na jikinsa, hakan yasa yaji zuciyarsa ta ƙarayin sanyi. Zieyada kuwa atare da Ummu suka haɗa Mango juice, babban jug ɗin da mango juice ɗin ke ciki Ummu ta bata tace tasanya a fridge, koda tasanya mango juice ɗin acikin fridge kaitsaye ɗakinta ta wuce, faɗawa kan gado tayi tare da lumshe manya manyan idanunta, da sauri ta ware idanunta tare da tashi zaune, hannayenta tasanya duka biyu ta murza eyes ɗinta, wani irin ƙaton ajiyar zuciya ta sauƙe alokacin da ta fuskanci cewa gizo ne idanunta ke mata, bawai shiɗin bane, wani irin yaar taji ajikinta sakamakon tunowa da cikin kyawawan idanuwansa da tayi, tabbas idanunsa kaɗai sun isa rikita duk wata ƴa mace, matuƙar zata kallesu, wani irin sirrin kyau ne ke ƙunshe acikin idanunnasa, aduk randa tsautsayi yasanyata kallon cikin idanunsa ji take kamar zata suma, wasu abubuwane ke yawo ajikinta yayinda takejin kanta kamar wata wawiya, eye balls ɗinsa tamkar magnet ne acikin nata idanun dake matuƙar zautar da ita, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta wanda bata san ma tayi ba, sakamakon tunawa da kyakkyawar fuskarsa da tayi. "Yana da kyau sosai!!" Tafaɗa abayyane cikin wata irin murya me sanyi. "Ko abacci ma kyau yakeyi, shi komai nasa me kyau ne!!!" Tasake faɗa tana me murza ƴan yatsun hanunta, itakanta batasan maganganun da take faɗa suna fitowa fili ba, gaba ɗaya ashagalce take, fararen ƙafafunta ta zuro ƙasa tare da tashi tsaye, direct wajen window ta nufa, ɗan yaye labulen window'n tayi tare da soma bin ko ina dake cikin compound ɗin gidan da kallo, idanunta ta tsayar asetin ƙofar shiga garden ɗin, dai dai lokacin yafito daga cikin garden ɗin hanunsa riƙe da wani green apple, tafiya yake kansa tsaye yayinda skin ɗinsa keta walwali kallo ɗaya zaka masa kasan hutu da kudi sun zauna masa, tundaga wajen da take tana iya hango yanda tarin suman dake kansa ke sheƙi, gashi ya kwanta luf luf tamkar sajen dake kwance akan fuskarsa, bata taɓa ganin wani irinsa ba, shi na dabanne ko acikin maza, hannunta takai ta dafa glass din dake jikin window'n, fuskarsa kawai take kallo, akullum tana mamakin yanda yake rayuwarsa babu annuri akan fuskarsa, koda yaushe haka yake baka taɓa ganin dariyarsa, kafun kaji maganarsa ma wahala ne, shi komai nasa is difference, Maganan aurensa ne ya faɗo mata lokaci guda ta marerece fuska tare da ɗan taɓe soft lips ɗinta. "Wace zata aureshi?" tambayar da tayiwa kanta kenan azuci, amma sam batasani ba har sautin maganan yafito fili. Soft lip ɗinta na ƙasa taɗan tsotsa tare da soma karyar da yatsun hanunta, idanunta ne sukayi raurau kamar wacce zatayi kuka, ɗago kanta tasakeyi da niyan kallonsa, amma kuma saitaga kome kama dashi babu awajen, sake labulen tayi tare dakomawa kan gado ta zauna. "Mene nawa? Meyasa nake tambayar kaina abubuwan da basu shafeni ba? No wannan ba halina bane kawai sharrin zuciya ne!" Tafaɗi haka cike da tuhuman kanta, domin sam tasan tunanin rayuwarsa ba huruminta bane. Remote taɗauka tare da kunna ɗan madaidaicin tv plasman dake ɗakin, tashar MBC Bollywood takamo inda tasamu suna nuna film ɗin Sushant Singh da Kriti Sanon wato Raabta, yanayin film din sosai yaɗauki hankalinta musamman yanda taga suna wata kalan rayuwa a daji, sam saita manta da tunanin komai ta bada hankalinta ga kallo. _RAJ_ Koda yabar garden direct babban falon gidan ya nufa, babu kowa afalon kamar koda yaushe hakan yasa kaitsaye yawuce ɓangarensa, yana shiga ya murzawa ƙofarsa key, gaba ɗaya zaman gidan ya ishesa, ayanzu bayason damuwar kowa ta dameshi, saboda haka yaciro wani tablet dake jikin bedside drawer ɗinshi, ɓare maganin yayi ya jefa abakinsa sannan yabi da ruwa, toilet ya wuce ya ɗauro alwala domin alokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Magriba, direct masallaci ya wuce, tunda yayi Sallah Magriba bai tashi ba har saida ya sallame isha yayi azkar, yana fitowa daga cikin masallacin yasoma jin jiri na ƙoƙarin kadashi, lokaci guda kansa yayi masa nauyi, idanunsa sukayi luhu luhu, cikin dauriya yake tafiya ahaka har ya isa gida, yana shiga cikin bedroom ɗinsa ya soma rage kayan jikinsa, dagashi sai long jeans haka ya faɗa kan royal bed ɗinsa tare da jawo pillow ya ɗaura kansa akai, wani irin duhu yake gani a idanunsa, har takai ma da ƙyar yake iya buɗesu mintuna kaɗan wani irin nannauyan bacci ya ɗaukesa, daga yanayin yanda yake baccin idan ka gani kasan bana lafiya ba.... Washegari. Tun da safe Ummu da Ziyadah keta ƙoƙarin haɗa breakfast a kitchine kasancewar yau Abba zai koma KD, jirgin ƙarfe 9 zaibi shiasa Ummu keta ɗawainiya tanason yayi break kafun yatafi, don ita tace dawowarta ba yanzuba saboda Sooraj. Ba abun da Abba yakeso kamar Tuwo hakan yasa yauma Ummu tuwo takeyi masa da moringa soup wanda yaji cow meat da biscuit bone, ƙarfe takwas daidai suka kammala gaba ɗaya aikinsu, Ziyadah ce ta jere komai akan dinning table, Koda Ummu tagama serving ɗin Abba kujera taja ta zauna, har Abba yafara cin abincin ya ɗago ya kalli Ziyada wacce tayi shiru kamar me tunani. "Jeki ƙiramin yayanki" Abba yafaɗa yana me duban tsadadden agogon dake ɗaure a hanunsa, cike da ladabi tamiƙe tare da nufar inda zai sadata da ɗakinsa, duk da cewa ƙirjinta dukan uku uku yake, amma haka ta daure, tana tura kanta acikin corridor ɗin da direct zai kaika ɗakinsa ta shaƙi daddaɗan ƙamshinsa wanda yake matuƙar hautsina tunaninta, wani irin sanyi taji yana busata cikin sanyin jiki taƙarasa jikin ƙofar ɗakinnasa, hanunta na rawa tayi knocking amma shiru ba'a amsa taba, cike da tsoro tasakeyin wani knocking ɗin nanma shiru babu amsa, ɗan jim tayi tare da juyawa zata koma, tunani tayi idan takoma me zata faɗawa Abba tace tayi knocking ba a buɗeba ko me? hakan yasa tayi karambani'n murɗa handle ɗin ƙofar, kamar da wasa kuwa taji ƙofan ta buɗe, wani daddaɗan ƙamshi tare da sanyin AC ne suka daki fuskarta har saida ta lumshe idanunta. Ahankali taɗan kutsa kanta cikin ɗakin, kwance yake akan bed yayi irin kwanciyarnan ta ruf da ciki, dagashi sai dogon wando gaba ɗaya gadon a hargitse yake tamkar wanda akayi kokuwa akansa, kallonsa tayi tundaga ƙasa har sama, gaba ɗaya kwanciyanma baiyita a dai dai ba, domin kusan rabin ƙafafunsa suna lilo suba a sama ba suba a ƙasa ba, gangarjikinsa ne kawai ke kan gadon, idanunta ne suka sauƙa akan bayansa inda fresh white skin ɗinsa ke shining yana fidda ƙyallin zufa, mamakine yakamata ganin jikinsa na fidda gumi, domin kuwa sanyin ac ne keta tashi acikin ɗakin, hatta tiles ɗin dake malale aƙasan ɗakin yaɗauki sanyi sosai, sam takasa sanin bacci yake ko kuwa idanunsa biu, cikin yanayi naɗan tsoro ta ɗan tako zuwa tsakiyan ɗakin, muryarta akarye tace "Yaa..." kasa ƙarasawa tayi, ɗan cije laɓɓanta tayi tare da rumtse idanunta, gaba ɗaya jarumtarta ta tattaro tace "Ya--yah!" Jin shiru bai amsa ba yasanya tace "Dama Abbane yace naƙiraka!" shima dai shiru babu amsa hakan yasa taɗan matsa kusa dashi, jin zuciarta take kamar zata fashe saboda fargaba, da ace zai juyo ya kalleta alokacin to tabbas abu me sauƙine ta sume masa awajen. "Ya--Yah katashi!" Ta sake faɗa tana ɗan leƙa fuskarsa, domin yanzukam taga alamun cewa bacci yakeyi. Ko motsi baiyiba balle tasaran zai bude idanunsa har yatashi kamar yanda take ɓuƙata, cike da karanbani taɗan sanya hanu ta bugi katifan da yake kai, tun tana ɗan bugawa ahankali harta gaji taɗan buga da ƙarfi, still ko motsawa baiyi ba, hakan yasa tasa hanu tashiga jan bedsheet ɗin dayake kai cikin shagwaɓan da batasan ta iyaba tace. "Please Ya--yah wake up!" cikin bazata taga ya mirgino tare da juyowa hartana iya kallon fuskarsa saidai kuma bai buɗe idanunsa ba, da sauri taɗauke idanunta daga kan faffaɗan chest ɗinshi, cike da ƙosawa taɗan bubbuga ƙafafunta aƙasa murya agajiye tace "Nidai dan Allah katashi aikoni fa akayi!" Bawai baitashi bane duk abubuwan da takeyi masa yana jinsune tamkar amafarki, sam ƙarfin maganin baccin da yasha baigama sakeshi ba, ko sallan asuba daƙyar ya iya tashi yayi nanma agida yayi baije masjid ba, ƙasa ƙasa yaɗan buɗe sexy eyes ɗinshi wanda sukayi masa matuƙar nauyi, dishi dishi haka yake ganinta hakan yasa ya maida idanunsa ya kulle, sam batama lura da cewar ya ɗan buɗe idanunsa ba, blanket ɗin dayake kai taja da ƙarfi waiko zai tashi amma sam ko sake motsawa baiyi ba, hawayene suka cika idanunta sai kawai ta juya tabar masa ɗakin. Tana shigowa cikin falon tasamu Abba da Ummu tsaye harsun kammala cin abincinsu. "Ya haka naganki ke ɗaya ina Sooraj ɗin?" Ummu ta tambaya tana me ƙarewa Ziyada'n kallo, domin kuwa baƙaramin jimawa tayi aɗakin Sooraj ɗin ba. Sunkuyar dakai ƙasa tayi cikin muryarta me sanyi tace. "Bacci yakeyi, tun ɗazu nake tashinsa kuma baitashi ba!" "Bacci?" Ummu ta tambaya cike da mamaki. Kai Ziyada ta ɗaga mata alamar "Eh" "Badamuwa ku barshi idan yatashi zamuyi waya, yanzuma haka nakusa makara!" Abba yafaɗi haka yana me nufar hanyar barin falon, Ummu ce ta rufa masa baya, ita kuwa Ziyada ɗakinta ta wuce domin kuwa lokacin da MBC Bollywood zasu fara haska series ɗin Ishqmeinmarjawan *(حب خادع)* ya kusa kuma bataso tayi missing saboda sosai series ɗin keyi mata daɗi. 11:00 am daidai ya soma ware idanunsa ahankali har ya buɗesu duka, gani yayi kamar ɗakin na juya masa hakan yasa ya maida idanunsa ya rufe, mintuna uku tsakani yasake buɗewa, yanzu kam daidai yake ganin komai, jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi wani iri tamkar anyi masa duka, hannunsa yakai ya shafa tulin sumar dake kansa wanda yasha askin afro, ƙafafunsa ya zuro ƙasa tare da miƙewa tsaye, hannu yasanya ya zuge zip ɗin wandon dake jikinsa, yana tafiya haka yacire wandon sannan ya buɗe wata ƴar glass drawer sabon white colour bathrobe na maza ya ciro ya sanya ajikinsa, direct bathroom ya wuce, wanka yayi sannan ya haɗa da brush, yana fitowa ya jona handryer, dashi yayi amfani wajen busar da lallausan gashin kansa, sama sama yashafa mai ajikinsa, wani oil and body perfume me daɗin ƙamshi ya shafa ajikinsa. Kasancewar yau Jumma'a yasanya shigar da zaiyi yauɗin ta da bance, duk da cewa shi baiwani damu da manyan kayaba amma time to time yana ɗan sanyawa, wata haɗaɗɗiyar getziner blue colour wacce kuɗinta ya haurawa 40k ya zaro daga cikin tarin kayansa wanda yawansu basu faɗuwa, wani haɗaɗɗen half cover shoe me kalan blue wanda akawa samansa ado da ɗan ratsi ratsin golding ash ya zaro daga ma adanan takalmansa, takalmine me kyaun gaske wanda aka sanya kuɗaɗe wajen sayansa, Hulan daya zaro ma ta musammance itama ajikinta akwai ratsi ratsin golding ash da blue, Saida yagama kimtsa kansa cikin getziner'n wacce tasha ɗinkin half jumper, sosai yayi wani irin kyau me

Chapter 14 of 38