Share this page
tare da bawa Kamalu driver hannu suka gaisa, cikin muryarsa yace "Yauwa Kamalu barka da aiki!" Tunda suka baro airport ɗin Kamalu driver ke ta masa zuba, yayinda shikuma yawan maganartasa ba sosaiba saidai murmushi kawai da yakeyi. Gyara zama Shukra tayi cikin kulawa tace "Me yasa zaki tauyewa kanki haƙƙi Zieyaderh? indai kina sonsa kawai ki amsa masa, mene aibun Pharouk? Sam bashida wani aibu komai nasa mai kyau ne, inta ƙaicemiki babu wata ƴa mace da zataga Pharouk kuma ta ƙishi coz ba Namijin wasa bane" Sunkuyar dakai Zieyaderh tayi tare daɗan ciza lips ɗinta, "Bansan ya zanyiba Shukhra amma karki manta nafaɗa miki matsayina bai kai ace naso Pharouk ba, duk da bansan wanene shiba amma nasan ko sama zata haɗe da ƙasa yafini tsatso me kyau, da kuma gata, banason na tozarta rayuwata Shukhra!" taƙare maganar idanunta cike tab da ƙwalla. Ajiyar zuciya Shukra tayi tare da sakin murmushi "Wannan ba hujja bane Zieyaderh, ana iya auren shegiyama wacce bata da uba, balle keda kike da uba, balallaine don bakisamu kulawan mahaifanki yazamana kin tauyewa kanki haƙƙi ba, ke macece idan baki zaɓi mijin da zaizame miki garkuwa ba me kenan kikayi? Ki farka daga baccin da kike Zieyaderh akowacce ƙwanan duniya ƙara girma muke, ayanzune yakama musan dacewa muma matane sannan ayanzune yakamata mukau da wani shashanci da yarinya wanda ke cikin sense ɗinmu, yes nasani bamu da wasu shekaru masu yawa amma kuma babu wani abu na ƴan matanci ayanzu daya ɓoye kansa ajikinmu, zamu mori damarmu ne kaɗai idan mukayi amfani dashi tun muna ƙanana, alokacin da muka girma kuwa bazamu taɓa morarta da kyauba, saboda alokacin bakowa ne zaizo ya kallemu yace yana sonmu ba, ayanzu kuwa kowa so da sha'awarmu yake" Ɗan tsagaitawa da maganar tayi tare da sanya hannunta ta dafa kafaɗan Zieyaderh. "Ki amincewa Pharouk Zieyaderh, inada tabbacin Pharouk bazai taɓa nuna miki tsana tsangwama da kuma kyara ba!" Wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi Zieyaderh ta sauƙe, tabbas tasan abunda Shukhra ta faɗa gaskiya ne, saidai kuma tayaya zata furtawa Pharouk cewa tana sonshi? Idan har taso Pharouk menene matsayin tunanin Mr.helper dake kwance acikin zuciyarta? Da sauri takawar da wannan tunanin acikin zuciyarta. Murmushi tayi cike da son samawa kanta ƙarfin guiwa tace "Zan faɗa masa komai game dani Shukra, idan har zai soni ahaka to nima zan amasa masa, saɓanin haka kuwa shikenan zanjira wata ƙaddaran" "Bazai taɓa gudunki ba Insha Allah!" cewar Shukra. Dariya suka sanya su dukansu. 5:10 pm zaune take acikin motar gaba ɗaya tunaninta yayi nisa izuwa maganganun da sukayi da Shukhra, sanyin AC'n dake tashi acikin motarne ya cakuɗa da daddaɗan ƙamshin turaren sa, duk da cewa baya cikin motar amma zaman dayayi acikin motar da safe yasanya har yanzu ƙamshinsa bai bar cikin motarba, hakan yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi wani iri, jingina bayanta tayi da jikin kujeran motar tare da lumshe idanunta, sosai ƙamshin yake jefata cikin wani irin yanayi. Sam batasan da cewa sun iso gidan ba saida taji Kamalu driver ya tsaida motar. Jiki asanyaye take tafiya harta kawo ƙofar falon, tura ƙofar falon tayi ta shiga, da ƴar siririyar muryarta tayi sallama, Amustapha dake tsaye acikin falon ya juyo ahankali yana me amsa mata sallaman, idanunsune ya sarƙe acikin na juna, da mamaki akan fuskarsa ya shiga kallonta, Itama kallonsa take, "Almustapha" Muryar Ummu da suka ji yasa suka ɗauke idanunsu akan juna. Ummu ce taƙaraso cikin falon fuskarta ɗauke da murmushi. Kallon Zieyaderh tayi tare da cewa "Zieyaderh ga ɗana Almustapha" Mamakine ya bayyana akan fuskar Zieyaderh amma saita share,cikin sakin fuska tare da murmushi taɗan rusuna tagaidashi, shima murmushinne akan fuskarsa ya amsa mata, har yanzu yana me dubanta don baigaji da kallonta ba. Harta haura steps bai ɗauke idanunsa akanta ba, Murmushi Ummu tayi sannan ta juya tafice daga cikin falon don dama fita zatayi. Da ƙarfi ya buga table ɗin dake gabansa ransa amatuƙar ɓace yace "Get out Aneesa!!" Murmushi Aneesa tayi tare da juya idanunta dake cike da ruwan hawaye, laɓɓanta ta ciza, "Bazan tafi ba RAJ Why kake kyarata? menene bani dashi? Kyau,Ilimi, dukiya, ko kuma me?" Ta tambayeshi hawaye suna mai sauƙa daga cikin idanunta. Ransa amatuƙar ɓace yace "Kifitarmin a office!!!" Murmushi mai ciwo Aneesa tayi cike da son ƙuntata masa tace "Baka sona saboda kai bakayarda da kanka bako? Hmmmm najima da sanin abunda kake ɓoyewa RAJ, najima da gane cewa kai Rago ne, Kafito fili kafaɗamin cewa kai ba Namiji bane mana, Ohhhhhh nagane kanajin kunyar sanar da duniya cewa kai wani marar amfanine ko, bansan meyasa ba duk da nasan cewa kai ba Namiji bane amma na liƙe maka, wallahi RAJ saika aure ni koda......" Wani irin bahagon mari SOORAJ ya sauƙe mata akan fuskarta wanda saida yagigita ta. Bata gama dawowa cikin hayyacinta ba ya ɗamƙi wuyanta da ƙarfi, mannata yayi da jikin bango tare da sanya hannunsa da ƙarfi ya yaga rigan dake jikinta, dayake doguwar rigane ajikinta hakan yasa ya yagata har ƙasa, take surar jikinta ya bayyana, idanunsane suka rikiɗe sukayi wani irin jaaa tamkar anwatsa masa barkono, lokaci guda jikinsa ya ɗauki ɓari tamkar wanda aka jonawa shocking. "Ni ba Namiji bane ko? Yess niba Namiji bane, amma yanzu zanyi miki abun da wanda ba Namiji ba bazai taɓa iya yimiki shi ba" yana gama faɗan hakan ya wurgata saman table, tare da sanya hannu ya zare belt ɗin dake jikinsa. 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SOORAJ!!!* *Written By* Phatymasardauna *WATTPAD* @fatymasardauna #romance *This page is dedicated to my Brother HAMEED ALI (@Hameed29) I really ❤ You Brother* *Chapter 33* Wani irin jiri ne ke ɗibansa, duhu shine abun dake neman mamaye ganinsa, jin duniyar yake gaba ɗaya tana juya mai, da ƙyar ya iya buɗe ƙofar ya fito hannunsa dafe da kansa. Jefa ƙafafunsa kawai yakeyi batare da yana kula da inda yasa gaba ba, da ƙyar ya iya kawo kansa wajen motarsa, yana shiga yayi mata key. Sam baya wani iya ganin gabansa da kyau, yanayin yanda gateman yaga yayo kansa da motar ne yasanya babu shiri da sauri ya buɗe masa gate, mamaki kwance akan fuskarsa na irin tuƙin gangancin da yaga yanayi. Da wani irin speed yake tuƙa motar shikansa baisan wani irin gudu yakeyi ba, babu babban abun tashin hankali da tsoratarwa kamar yanda ƙwayoyin idanunsa suka rikiɗe suka zama jajur dasu, gaba ɗaya jijiyoyin dake jikinsa duk sun tashi sunyi raɗo raɗo, mussamman forehead ɗinsa wanda jijiyoyi suka fito sukaɗi raɗa raɗa. Irin gudun da yakeyi akan hanya ne, yasanya mutane da yawa ke kauce masa, da ƙarfi ya daki gate ɗin gidan wanda don kansa saida ya buɗe, aguje mai gadi ya fito don kowa yaji irin dukan da akaiwa gate ɗin yasan ba lafiya ba. Da gudu yashigo cikin gidan kodamuwa da gaban motarsa da ya lotse baiyi ba. Wani irin bahagon parking yayi. Ummu da Almustapha ne suka miƙe atare sakamakon jin yanda aka buga ƙofar falon da ƙarfi, waigawansu yayi daidai da shigowansa cikin falon, ƙirjin Ummu ne yashiga bugawa da sauri ganin yanda yake tafiya yana gauraya hanya tamkar wanda ke cikin maye, sannan kuma ga hannunsa dafe da forehead ɗinsa. "SOORAJ!" Ummu taƙira sunansa aɗan razane. Bai waiwayo ba baikuma tsaya da tafiyan dayake ba kana kuma bai amsata ba, ya nufi hanyar da zata sadashi da ɗakinsa. "RAJ!" Almustapha yaƙira sunansa, kamar yanda bai amsa Ummu ba haka bai amsawa Almustapha ba, haka ya buɗe ƙofar corridor ɗinsa ya shige. Da sauri Ummu tarufa masa baya, baifi saura taku uku tsakaninsu ba ya shige cikin ɗakinsa tare da murzawa kofar key, mamakine ya kashe Ummu hakan yasa ta tsaya cak, don tunda ta haifeshi bata taɓa ganinsa acikin irin wannan yanayin ba. Ajikin ƙofar ya zame tare da sanya hannuwansa ya dafe kansa dake barazanan tarwatsewa. "Me yasa bazaka fito ka faɗawa duniya cewa kai ba Namiji bane? RAGO!" waƴannan kalaman suke ta yawo acikin brain ɗinsa suna me hautsina duk wani lissafin nutsuwarsa. Idanunsa da suka kaɗa suka zama jajur ya buɗe tare da sauƙesu akan mirror, zumbur kamar wanda akawa allura haka ya tashi ahankali yashiga takawa har ya ƙarasa gaban mirror'n, tsayawa yayi yana me kallon kansa, da sauri sauri yashiga cire rigan dake jikinsa, take murɗaɗɗen surar jikinsa da buɗaɗɗun muscles ɗinsa suka bayyana acikin madubin, 6 packs ɗin dake kwance raɗa raɗa akan cikinsa yakai hannu ya shafa, ɗauke hannunsa daga cikinsa yayi ya taɓa fuskarsa da tayi jajur tsaɓan tsananin ɓacin rai da yake ciki. "DA GASKE KAI BA NAMIJI BANE!!" Zuciyarsa tafaɗa masa haka batare daya shiryawa jin hakanba, wani irin ihu yayi tare da sanya hannunsa ya naushi madubin, take ya tarwatse awajen, hannunsa ne ya shiga ɗigar da jini amma ko ajikinsa, wani ƙaton glass wanda yake kamar madubi ansanya rose aciki ya ɗaga tare da wurgi dashi, ƙaran fashewan Glass ɗin take ya cika ɗakin, tamkar wani zararre haka SOORAJ yaci gaba da wurgi da duk wani abun daya gani, gaba ɗaya ya watsar da kayan shafan dake kan mirror'n sa, kalmar da akace shiba Namiji bane, ita ce kawai keta yawo acikin brain ɗinsa, haka yakeji kamar zai haukace. Hankalin Ummu ne yakai ƙololuwan tashi jin irin ƙaran fashewan abubuwa dake fitowa daga ɗakin Sooraj, Almustapha ne yaƙaraso da hanzari cike da mamaki yake kallon Ummu, hankalinsa atashe yace "Meke damunsa ne haka?" Hawayene kwance acikin idanun Ummu amma saitayi ƙoƙarin maidasu cike da damuwa tace "Almustapha bansani ba, kafun nazo ma ya rufe ƙofarsa, bantaɓa ganin Sooraj acikin irin wannan yanayin ba, bana fata acemin shaye shaye Sooraj yayi, domin sam ni ajinina ban haifi Mashayi ba, don Allah Almustapha kamasa magana ya buɗe ƙofarnan!" Duk yanda Ummu taso hana ƙwalla fitowa daga cikin idanunta saida suka fito. Hankalin Almustapha amatuƙar tashe yashiga bubbuga ƙofan yana ƙiran sunan SOORAJ. Ya soma fita daga hayyacinsa, gaba ɗaya ya birkita ɗakin, yayi watsi da komai. Jinine ke ɗiga ahanunsa sosai, gaba ɗaya ya ɓata ƙasan ɗakin da ɗigo ɗigon jini. Wani irin jiri ne ke ɗibansa, hakan yasanya shi faɗawa kan gado ya lumshe idanunsa, jiyake kamar duniyar zata kife tsabar tsananin ciwon da kansa ke masa. Tun yanajin yanda Almustapha ke buga ƙofar har ya daina jin komai, sakamakon wani wahalallen bacci daya ɗaukesa. Ummu kuwa ganin yaƙi buɗe ƙofan yasanya taje ta ɗauko spire key na ɗakinsa, Almustapha ne ya buɗe suka shigo atare, mamaki da tsorone ya bayyana akan fuskokinsu sakamakon yanda suka ga ɗakin ya sauya kammani, ga kuma ɗigo ɗigon jini akan tiles, kan gado Ummu ta kalla nan ta hangoshi yayi kwanciyar ruf da ciki, hannunsa kuwa duk jini ne wanda ya bushe. Da sauri taƙarasa tare da sanya hannu ta taɓashi "Sooraj!!" Ta ƙira sunansa murya araunane, kana taɗan leƙa fuskarsa. Wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe alokacin dataga bacci yake. Kallon Almustapha dake tsaye yayi shiru tayi, sannan tashiga ƙarewa ɗakin kallo, gaba ɗaya Sooraj ya hautsina komai, fasssun glasses da mirrors ne zube aƙasan ɗakin wanda idan baka kulaba tsab zasu raunata ka. "Mutafi" tace da Almustapha tana me wucewa gaba, babu musu ya rufa mata baya. Kallonta Almustapha yayi tsananin damuwa ne bayyane akan fuskarsa yace "Dama bashida lafiya ne Ummu? ko akwai wata damuwa ne?" "Lafiyanshi ƙalau Almustapha ko da safe ma anan yayi breakfast, bansan mene yasameshi ba, ban taɓa ganinsa acikin irin wannan yanayin ba. Ko na ƙira Abbanku ne?" Da sauri Almustapha yace "Karki ƙirashi Ummu, Isha Allah babu wata matsala maybe anɓata masa rai ne, kinsan Sooraj tun muna ƙanana bai iya ɓacin rai ba" Ajiyar zuciya Ummu ta sauƙe sakamakon jin abun da Almustapha yace, tabbas SOORAJ bai iya ɓacin rai ba sam, idan ransa ya ɓaci to sai gyaran Allah. Daga nan bata sake cewa komai ba ta haura sama. Zieyaderh ce zaune akan gado sanye take da dogon wando marar nauyi wanda yakasance rubber pencil, sai wata ƴar farar vest marar hannu, tayi shigarne saboda ana yanayi na zafi, jin motsi kamar za'a shigo ɗakin, yasanya ta ɗaukar hijab ɗinta dake kusa da ita ta sanya da sauri, tana gama sanya Hijab ɗin taji ana knocking ƙofa, bedroom slippers ɗinta ta sanya kana ta nufi jikin ƙofan, tana buɗewa tayi arba da Ummu, ɗan matsawa baya tayi zatayi magana Ummu tarigata da cewa. "Kije ki kimtsawa Yayanki ɗakinsa, sannan kuma kiyi hankali wajen shiga ɗakin akwai fasassun kwalba zasu iya raunataki!" bata wani tsaya jin ta bakin Zieyaderh'n ba ta juya ta nufi ɗakinta, Mamakine yaɗan kama Zieyaderh musamman yanda taga damuwa kwance akan fuskar Ummu, sannan kuma Ummu bata taɓa cewa ta gyara masa ɗaki ba sai yau, da wannan tunanin acikin ranta ta sauƙo ƙasa kai tsaye ta nufi ɗakinsa, ko lura da Almustapha dake zaune acikin falon ba tayi ba. Ahankali tatura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama, da fasassun glasses ɗin dake ƙasa tasomayin arba, baki buɗe take ƙarewa kowani kusurwa dake cikin ɗakin kallo, mamakin yanda aka hargitsa ɗakinne ya kamata, don kuwa ancire komai daga ma'ajinsa anyardashi ƙasa. Kallon Beedshet ɗin dake yashe aƙasa tayi sannan ta dawo da kallonta kan gado inda yake kwance, ƙirjinta ne taji yaɗan buga don ayanda taga ɗakin ahaukace batayi tsammanin ganin wani acikinsa ba. Idanunta ne suka sauƙa akan hannunsa wanda ke ɗauke da jini, wani irin tashi tsikar jikinta yayi, har saida ta ɗan ciza laɓɓanta. "Kenan shine yayi duk wannan abun?" tambayar da tayiwa kanta kenan tana me duban jinin dake jikin tiles ɗin. cikin takatsantsan ta ƙarasa gaban gadon tare da kafeshi da ido. "Meke damunshi? Bashi da lafiya ne?" zuciyarta ta tambayeta tambayar da bata da amsa. Ganin saƙawa da kuncewa ba nata bane yasanya ta ɗauki abun shara da packer tashiga tattara glasses ɗin, tana kammalawa ta ɗauko moper tayi mopping ɗin wajen, room freshner ta fesa acikin ɗakin take ko ina yaɗauki ƙamshi, kayan shafansa ta jere masa akan mirror sannan ta ninke bedsheet ɗin dake ƙasa ta ɗaurasa akan gado, saida ta maida komai dake cikin ɗakin nead kafun ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa wanda bashi da sanyi sosai, audugan da ta gani acikin drawer ɗinsa ta ɗauko, ahankali taƙaraso jikin gadon tare da zama daɓas akan carpet ɗin daya kewaye gadon, dayake hannun nasa me ciwon ba'akan gadon yake ba hakan ya bata daman sanya hannunta ta kamo nasa hannun, ruwa ta ɗiga ajikin auduga sannan tashiga goge masa busashshen jinin dake hannunsa, ahankali takeyi kuma cikin nutsuwa gudun kada ta tashesa. Ahankali yaɗan buɗe idanunsa da suka ƙanƙance, cute face ɗinta ya kalla da kuma small lips ɗinta, maida idanunsa yayi ya rufe yana mejin yanda take lallaɓa hannun nasa tamkar wanda aka bawa ajiyan ƙwai, sam batasan da cewa ya farka ba,domin gaba ɗaya tabada hankalinta ga aikin da takeyi, tas ta goge masa jini har ya zamana tana iya ganin yankewan da yayi, wani irin tausayinsa ne taji ya kamata, tasan dole idan ya farka sai ciwon yayi masa zafi, wata ƙila yanzu ma yanayi masa zafi, tunowa da haka yasanya taɗan sunkuyo da kanta, ahankali tashiga hura masa iskan bakinta adaidai kan ciwon, tayi hakanne saboda ta sama masa sauƙi, kasancewar idan taji ciwo in tana hurashi baya yi mata zafi, hakan yasa tashiga yi masa. Wani irin sanyi yakeji na ratsa jikinsa, duk da cewa ciwon bayayi masa wani zafi sosai, amma hakan da tayi masa ya sanya ya samu relief, don har wani sabon bacci yaji yana fusgarsa, luf yasakeyi akan gadon tare da sake lumshe idanunsa. Sai yanzu yakejin ya dawo cikin sense ɗinsa, sai yanzu abubuwan da yayi ɗazu ke dawowa cikin brain ɗinsa, shiru yayi yana mejin yanda zuciyarsa ke bugawa, tabbas SHI BA NAMIJI BANE yau ya sake tabbatarwa kansa da hakan, duk da cewa tuntuni yasan yana da rauni ta ɓangaren mu'amala da mace amma baiyi tunanin matsalartasa takai har haka ba, bazai taɓa iya biyawa wata mace buƙatarta ba, sannan bazai taɓa iya alfahari da kanshi amatsayin cikakken Namiji ba, baisan menene Sha'awa ba, bai taɓa jiba bai kuma san ya akeji ba, baisan ya Sex yake ba bai kuma san ya daɗi da rashinsa yake ba. Tabbas shi gwanine akowani ɓangare amma awannan ɓangaren shi rago ne. Zuwa yanzu ƙwaƙwalwarsa takusa daina aiki domin kuwa tunani na neman illata ta, Meyasa bayajin Sha'awar mace? Me yasa bazai taɓa iya yin sex da mace ba? Me yasa bayajin wani abu na musamman ajikinsa dan gane da kowacce mace? Waƴannan tambayoyin sunjima suna barazanan tarwatsa zuciyarsa wajen neman amsarsu amma har yau baisamu amsan ba, hakan yasa ya rufe sirrinsa yabar abun amatsayin ƘADDARA me girma agareshi. Ajiyar zuciya me ƙarfi ya sauƙe, tare da rumtse idanunsa da ƙarfi, shi LOOSER ne, amma duk da haka baya fatan ci gaba da zama looser akoda yaushe, saboda haka ayanzu baijin zai baiwa hawayen dake cikin idanunsa daman fitowa...... (Kowani bawa da irin ƙaddaransa, haka kuma kowani labari da irin yanda aka tsarashi, tabbas nasan nan gaba kaɗan zanzo wajen da bazai taɓa yi muku daɗi ba, bakuma zanzo wajen ason raina bane ba, labarinne yazo ahaka, sai ansha gwagwarmaya, sai anfuskanci ƙalubale, sai kuma anjure ake kaiwa ga daɗi, tabbas wasunku nasan bazasu iya juran wannnan wajenba, nasan ƙorafe ƙorafen ku zaita iskeni, nasan zakuyi challenge's ɗina, wasunku zasu faɗamin magana mai daɗi, wasunku kuwa zanji saɓanin haka daga bakunansu, tun ayanzu ina fuskantar challenge's daga wajen wasu, tabbas nice me labari kuma nice me rubutu, idan asonane ako da yaushe nayi abun dazai faranta ranku, wannan shine kullum fata na, watarana inada important abun da zanyi amma haka nake squeesing nayi typing duk dan nafaranta muku, shin me zanji araina idan kuka jefeni da magana marar daɗi? kunaga zanji ƙarfin guiwa da farincikin sake yi muku wani fejin da zaku karanta? Tabbas nasan kuna ƙoƙari sosai sosai,musamman yanda kuke mini votes da comment, har acikin raina ku na dabanne My Wattpadians people, acikinku wasu ke faranta raina akuma cikinku wasu ke disturbing ɗina, amma nidai ina muku son so, nasan wasu mutane dagangan suke faɗan wata maganan duk dan su ɓata raina, amma babu damuwa dukanku ni inasonku.... Ni mutumce me ƙaunar duk wani maisona.... Please! Please!! Pleaseeeee!!! Idan kinsan nan gaba kaɗan zaki fito kiyi challenging ɗina akan labarinnan don Allah ki haƙura da karantawa wannan roƙo ne nayi muku masu challenge's ɗina. Love You all and Son So My lovely fans❤* *Vote and Comment*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SOORAJ!!!* *Written By* Phatymasardauna *Dedicated To My Life (Sardauna)* *WATTPAD* @fatymasardauna #romance *Chapter 34* A hankali idanunta ke lumshewa da alama bacci takeji, amma kuma har izuwa wannan lokacin bata daina hura masa iskan dake bakinta ba. Ahankali yake fitar da numfashi, yana mejin sanyi na sauƙa acikin zuciyarsa, juyo da kansa ɓangaren da take yayi tare da sauƙe gajiyayyun idanunsa akanta, itama ɗago manya manyan idanunta tayi ta kalleshi, hakan yabawa idanunsu daman sarƙewa acikin na juna, wani irin mimmiƙewa gashin dake jikinta sukayi, take tsikar jikinta ya shiga zubawa, tamkar wacce aka watsawa ruwan sanyi, ba komai ya haifar mata da hakan ba kuwa, face arba da sexy eye balls ɗinsa da tayi, wanda suke lumshewa ahankali tamkar na mejin bacci. ƙasa tayi da idanunta, batare da ta sake hannunsa dake cikin nata ba, ƙofar ɗakin aka buɗe hakan yasa ta ɗago kanta da sauri ta kalli ƙofan, Almustapha ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, da sauri tatashi daga zaunen da take tare da sakin hannunsa ta koma gefe. Ƙarasowa cikin ɗakin Almustapha yayi yana me ƙare mata kallo, cikin muryarsa me sanyi yace. "Ya tashi ne?" Kai kawai ta iya gyaɗa masa alamar "Eh" Raɓawa tayi tagefenshi ta fice daga cikin ɗakin. Binta yayi da kallo harta fice, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da juyowa ya kalli Sooraj wanda ko motsawa baiyi ba. "RAJ" Almustapha yaƙira sunanshi. "Ummm!" Sooraj ya amsa masa akasalance yana meƙoƙarin tashi zaune. Kallonsa Almustapha yayi sosai sai kawai yayi murmushi tare da cewa. "Ya jikin naka?" "Wani yace maka banida lafiya ne?" Sooraj ya faɗa yana me ƙoƙarin sauƙa daga kan gadon. "No ni ne kawai nake tunanin baka da lafiya, ko dai mutanen naka ne suka motsa?" Almustapha ya tambaya yana me ƙoƙarin gimtse dariyan dake bakinsa. Hararansa Sooraj yayi baice dashi komai ba ya nufi hanyar da zai sadashi da bathroom, sarai yasan iskancin Almustapha yawane dashi, yanzu idan ya tsaya yadinga ɓata ransa kenan. Dariya Almustapha yayi tare da jawo laptop ɗin Sooraj ɗin yashiga amfani dashi. Luf tayi akan gado tana me sauƙe ajiyar zuciya akai akai, ƙwayan idanunsa ne keta yiwa nata idanun gizo, lumshe idanunta tayi tare da sakeyin hugging pillow'n dake hannunta, hancinta takai kan hannunta wanda tariƙeshi dashi, sosai hannunnata ke ƙamshinsa, wani irin kasalane taji yana sauƙa mata, tabbas ayanzu tayarda da cewa shiɗin na musammanne, kamar yanda komai da ya shafesa yake na musamman. Tari yake sosai acikin toilet ɗin, wanda har hakan yaɗauki hankalin Almustapha dake zaune akan gado, ɗan tsayawa yayi ajikin ƙofar toilet ɗin, tare da cewa "RAJ are you Okay?" shiru baiji ya amsa masa ba, hakan yasa ya tura ƙofar bathroom ɗin, da sauri ya ƙarasa wajen Sooraj dake tsaye agaban sink yana goge bakinsa da tissue. Idanu Almustapha ya zaro tare da duban tissue ɗin dake hannun Sooraj hankalinsa amatuƙar tashe yace "RAJ jinin mene wannan?" Hararansa Sooraj yayi cike da ƙosawa yace "Amma dai ban gayyatoka ba ko?" Fuskar Almustapha babu alaman wasa ko tsokana yasake cewa. "RAJ jinin menene wannan? please tell me dama baka da lafiya sosai har haka ne?" Gaba ɗaya Almustapha ya ɗaga hankalinsa. "Bakina ne ya fashe!" Sooraj yafaɗa ataƙaice yana me sanya ruwa ya shiga wanke bakinsa. Kamar statue haka Almustapha ya tsaya yana kallon Sooraj, sam bai yarda da cewa wai bakinsa ne ya fashe ba, cikin yanayi me ɗauke da tsananin damuwa yace "Shi kuma tarin da kake fa?" "Uhhhhhh! am tired, please Mustapha leave me alone!!" Sooraj yafaɗi haka yana me dafe forehead ɗinsa, sam bayason irin wannnan tambayoyin da Almustapha keyi masa. Jiki asanyaye Almustapha ya juya ya fice daga cikin toilet ɗin, saidai har cikin ransa yasan wannan jinin daya gani abakin Sooraj bana lafiya ba ne. Almustapha na fita Sooraj ya sanya duka hannayensa ya riƙe weast ɗinshi, iska ya fesar ta bakinsa tare da lumshe idanunsa, shikansa yasan bai taɓayin tari yaga jini ba sai yau, sai alokacin

Chapter 18 of 38