ya tuna da cewa sam bayashan maganinsa. Wanka yayi kana ya ɗauro alwala, towel ɗaure a weast ɗinshi ya fito, black jeans and black t-shirt ya sanya, duk Almustapha na kallonshi, ganin zai fita baice dashi komai ba yasanya Almustapha tashi da sauri ya bishi, atare suka tafi masallaci.....
Saturday.
Kasancewar yau ba makaranta hakan yasanya tun tashinta tashige kitchine, zuwa yanzu ta iya abubuwa da dama na dangane da girki, saboda haka kafun Ummu ta sauƙo ma ta kammala kusan rabin aikin, ɗauke da murmushi Ummu ta shigo cikin kitchine ɗin.
"Zieyaderh!" Ummu taƙira sunanta.
Barin aikin da takeyi tayi tare da juyowa, cikin ladabi tace " Ummu ina kwana"
"Lafiya lau" Ummu ta amsa mata tana me ƙarasowa cikin kitchine ɗin.
Atare suka kammala aikin, kamar koda yaushe Zieyaderh ne ta jere duka abincin akan dinning, Ƙamshin turarensa ne yafara sanar da ita zuwanshi, hakan yasa ta kasa ɗaga idanunta. Shine agaba Almustapha na biye dashi abaya haka suka nufo wajen dinning ɗin, Ummu naganinsu tasaki murmushin jin daɗi.
"Morning Maaa!" Sooraj ya faɗa agajarce yana me ƙoƙarin zama akan kujera.
"Morning" Ummu ta amsa tana me ɗan shafa kansa.
Rungumeta Almustapha yayi tare da yimata kiss a forehead ɗinta cike da kulawa yace.
"Good Morning Ummuna!" Murmushi Ummu tayi tare da shima da shafa kansa tace.
"Morning My Son"
Tana ɗago idanunta suka faɗa cikin na Almustapha hakan yasa ta saki murmushi tare da cewa "Ina kwana"
Murmushin shima yayi mata haɗe da cewa "Kintashi lafiya?"
"Lafiya" ta amsa tana me ƙoƙarin serving ɗinsu.
Ɗan satan kallon Sooraj tayi, taga gaba ɗaya hankalinsa nakan wayarsa, cikin sanyi tace.
"Yayah Ina kwana!"
Shiru yayi kamar bazai amsa ta ba sai kuma ya amsa mata da "Lafiya" acan ƙasan maƙoshinsa.
Kamar yanda tasani kuma taga bashida wani abun sha daya wuce fruit salad, hakan yasa ta ajiye wani glass bowl wanda ke ɗauke da fruit salad agabansa.
Serving ɗin kanta tayi sannan ta zauna, Ummu da Almustapha ne kawae keta hira, itakam dama mezatace acikin hirarsu, shikuwa SOORAJ dama kowa yasan ba magana yake ba.... Jin hirar su Ummu na damunsane yasanyashi miƙewa tsaye yabar wajen, da kallo Ummu tabisa har ya shige ɗakinsa.
Ahankali Zieyaderh itama tamiƙe tsaye don dama tuntuni ta ƙoshi da abincin, damar tashi kawai takejira. Sunanta da Ummu taƙira yasanyata dakatawa daga yunƙurin barin wajen da takeyi.
"Zauna inason magana dake" Ummu tafaɗa tana me ƙokarin aje kofin tea din dake hannunta.
Ƙirjinta ne yashiga bugawa lokaci ɗaya taji gabanta ya faɗi, aɗaɗare ta koma ta zauna akan kujera, miƙewa tsaye Almustapha yayi tare da ɗaukan kofin tea dinsa yabar wajen.
"Zieyaderh!" Ummu taƙira sunanta.
Bata iya amsawa ba saidai ɗago kai da tayi ta kalli Ummun jiki asanyaye.
Ummu bata wani damu da rashin amsawannata ba tace "Nayi magana da Mas'oud saidai abun da yafaɗamin akanki ya matuƙar girgizani, inaso kifaɗamin gaskiyar wacece ke? sannan kuma inason sanin ina mahaifanki suke da har zaki nesanta kanki dasu, karkimin ƙarya don banason ƙarya, Inajinki!" Ummu tafaɗi maganar tana me maida gaba ɗaya attention ɗinta ga Zieyaderh.
Ƙirjinta ne ya buga take idanunta suka cicciko da ƙwalla, bakinta na rawa tace. "Banda mahaifiya tun ina ƙarama ta rasu, natashi agaban Mahaifina da kuma matarsa sam bansan wani abu waishi soyayya ba, kullum cikin ƙunci da kaɗaici nake rayuwa, babu wani wanda yadamu da farinciki ko jin daɗi na, bansan kowa daga cikin dangin mahaifiyata ba saboda naji Babana yace ita ba ƴar garinmu bace, ban kuma san inane garinsu ba, tun ina ƙarama nayi sabo da wahalwahalun rayuwa, duk wani rashin gata ya ƙare akaina, sam babana bai ɗaukeni ƴa wacce ya haifa acikinsa ba, bansan daɗin mahaifi ba" Kuka ta fashe dashi tare da kifa kanta ajikin table, saida tayi kuka sosai sannan ta ɗago kanta hawayenta ta share kana ta cigaba da bawa Ummu labarinta, kama daga kan zancen aurenta da tsoho ɗan dashe har izuwa yanzu da take tare dasu, durƙusawa tayi akan guiwowinta cikin kuka tace "Ummu ki gafarceni saboda ni Ya Mas'oud yayi miki ƙarya."
Hawaye ne suka cika idanun Ummu, tabbas yarinya ƙarama kamar Zieyaderh bai kamata ace an banzatar da ita har haka ba, ya kamata ne ace anbata kyakkyawan kulawa.
Kafaɗunta Ummu takama ta ɗagota cike da kulawa tashiga share mata hawayen dake kwaranya akan fuskarta.
"Ya isa daina kukan haka nan, naga kanki yayi datti ɗauko mayafinki muje shagon saloon!" Ummu tafaɗi haka cike da kulawa.
Jiki asanyaye haka Zieyaderh ta haura sama don ɗauko mayafinta. Da kallon tausayi Ummu tabi bayanta, bawani jimawa sosai sai gata ta dawo sanye da hijab ajikinta.
Ko amota shirune ya biyo baya tsakaninsu, dan kowa da abun dayake saƙawa acikin ransa. Ummu kam tuni tagama yanke shawaran abun dake ranta, wayarta ta ɗauka ta turawa Almustapha da Sooraj text akan tanason ganinsu, daga haka ta aje wayarta.
Sosai aka gyarawa Zieyaderh dogon gashinta, lokaci guda ya ɗauki ƙamshi da walwali, daga shagon saloon Super market suka wuce, sosai Ummu ta sai mata kayan kwalliya dana sawa masu kyaun gaske, daganan suka ɗauko hanyar dawowa gida.
Tana sanya ƙafarta acikin falon idanunta suka sauƙa acikin na Almustapha wanda yasha kyau cikin baƙaƙen kaya. Da sauri tayi ƙasa da kanta, don har acikin ranta batajin daɗin irin kallon da yakeyi mata, kai tsaye ta haura sama nan tabar Ummu afalon.
Ummu na zama akan kujera Ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya fito, sanye yake da army 3 guater jeans da kuma black t-shirt, fuskarsannan babu alaman farinciki ko sakewa akanta, haka yaƙaraso cikin falon, akan kujeran dake facing na Ummu ya zauna tare da ciro phone ɗinsa daga aljihun wandonsa yasoma dannawa.
Gyara zama Ummu tayi cikin yanayi na kulawa tace "Banƙiraku nan don na faɗa muku wasa ba"Kallon Almustapha tayi cikin kulawa taƙira sunanshi, da "Na'am ya amsa mata tare da ɗagowa ya kalleta.
"Nasan banice na haifeka ba, amma kuma kana mini biyayya tamkar yanda zakayiwa mahaifiyarka, haƙiƙa amatsayina na yar mahaifiyarka inada ƴancin dazan iya zartar da duk hukuncin da naso akanka, kasani tamkar yanda nakeson ɗan cikina Sooraj kaima haka nake sonka, saboda haka na zaɓa maka matar da zaka aura ina fatan bazaka watsamin ƙasa a ido ba?"
Murmushi Almustapha yayi tare da sanya hannuwansa ya kama na Ummu. "Bazan taɓa iya bijirewa umarninkiba Ummu, ke uwace agareni saboda haka ina maraba da duk wani zaɓinki"
Murmushin jin daɗi Ummu tayi tare da sanya hannu ta shafa kansa cike da ƙaunarsa tace "Nagode sosai Almustapha Allah ya maka albarka!"
"Ameen Ummu, amma wace me sa'ace haka tayi gamdakatar ɗin samuna?" cike da zolaya yayi tambayar.
Dariya Ummu tayi tare da cewa "Kanason sani?"
"Sosaima" Almustapha yabata amsa cike da zaƙuwa.
Duk abunda suke yanajinsu yana kuma kallonsu, amma ko uhummm baice ba, azahirin gaskiya wayarsa yake dannawa abaɗini kuma gaba ɗaya hankalinsa na garesu.
"ZIEYADERH itace wacce na zaɓama kuma itace wacce zatayi daidai da rayuwarka!"
Maganar Ummu data faɗane yasanyashi ɗago da kansa ahankali ya kalleta..
"Zieyaderh!"Almustapha ya maimaita sunan abakinsa, kansa ya sunkuyar ƙasa fuska ɗauke da murmushi yace
"Na'amince!"
Tsaida duk wani abu da yakeyi yayi yana kallonsu, hakanan yaji tamkar ruwan jikinsa na ƙonewa.
(fever na damuna so banajin daɗin jikina please kuyi manage, wannan ma da ƙƴar nayi muku, idan naji sauƙi gobe Insha Allah zakujini🙏🏻)
Naziphi Yarima:
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
fatymasarduna
#romance
*Chapter 35*
Sunkuyar da kansa ƙasa yayi tare da ɗan ciza laɓɓansa, idanunsa ya mayar kan wayansa, samun kansa yayi da kasa cigaba da amfani da wayan, ji yayi gaba ɗaya jikinsa yayi weak.
"SOORAJ!" Oummu taƙira sunansa.
Ɗago kansa yayi ya kalleta batare daya amsa mata ba, itama bata nemi amsawar nashi ba taci gaba da cewa "Kaji abun da muka tattauna akai, amma bakace komaiba, sannan kuma inaso na yaba maka game da namijin ƙoƙarin taimakon da kayiwa Zieyaderh, insha Allah, Allah Zai baka lada!" Oummu tafaɗi maganar tana murmushi.
Ko Uhumm baice ba, sai ma kallon Oummu'n daya keyi, ganin damuwarta dana Almustapha zasu kasheshi yasanyashi tashi gaba ɗaya yabar musu gidan.
Kwance take luf akan bed ɗinta, biscuit ne ahannunta tanaci da kaɗan kaɗan, turo ƙofar ɗakin da akayi ya sanyata tashi zaune da sauri, ganin Oummu yasanya tasakin murmushi tare da cewa "Barka da shigowa Oummu"
Murmushi Oummu tayi tare da zama akan wata kujera, cike da kulawa tace. "Magana nazo muyi dake Zieyaderh!"
Gaban Zieyaderh ne ya faɗi, amma saita dake tare da cewa "To"
Murmushi Oummu tayi tare da dafa kafaɗun Zieyaderh'n tace "Inaso kishirya ƙarshen wannan week ɗin zamuje ƙauyenku dan inason naga mahaifinki!"
Dummm haka ƙirjin Zieyaderh ya bada wani irin sauti, hawaye ne suka cika idanunta alokaci guda, bakinta na rawa tace "To!"
Murmushi Oummu tayi don tafahimci cewa tsoron zuwa ƙauyen Zieyaderh keyi, cikin son kwantar mata da hankali tace "Kar kisanya tsoro aranki idan munje bazan barki ahannunsu ba zandawo dake nan, kawai dai naga ya kamata ace mahaifanki susan inda kike ne!"
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyaɗa kanta kawai, alaman ta gamsu. Oummu na fita daga ɗakin. Zieyaderh ta fashe da kuka, sosai tayi kewar babanta, ko awani hali yake ciki Allah masani? duk da cewa bai nuna mata ƙauna ba, amma ita har gobe, akwai ƙaunarsa acikin jininta, saboda koba komai Uba Uba ne koda baikasance na gari ba.
MONDAY
Cikin yanayi naɗan sauri sauri yake tafiya, don 8 daidai jirginsu zai ɗaga zuwa garin Lagos. Sanye yake da black and white suit wanda suka matuƙar yi masa kyau, black cover shoe ne ƙiran kamfanin Gucci sanye aƙafansa me tsadan gaske. ƙamshi kawai yaketa zubawa, yayinda gashin kansa keta shinning na mayukan da aka shafa masa, yau kam masha Allah Yayi kyau har ya gaji da haɗuwa.
Manta biology text book ɗinta da tayi, yasanya ta taho cikin sauri don komawa ta ɗauka, sam bata kulaba saiji tayi sunyi karo da juna, wanda hakan yajawo zubewan documents ɗin dake hannunsa. Da sauri taja da baya ƙirjinta na bugu da ƙarfi, idanunsu ne suka faɗa cikin na juna, hakan yasanya taji tamkar an jona mata shocking, kallonta yayi sannan ya kalli ƙasa inda documents ɗinsa suka zube, da sauri ta durƙusa ƙasa hannunta har rawa yake wajen harhaɗa documents ɗin waje ɗaya. Agogon hannunsa ya kalla yaga 7:30 kuma sai ya biya ta office kafun ya wuce airport, gashi duk gani yake kamar bata sauri wajen tattara documents ɗin. Itakuwa bakomai ke cinta ba face tsoro hakan yasa gaba ɗaya bata sauri, ƙamshin mayen turarensa dake zautar da ita ne, ya daki hancinta sosai, hakan yasa ta ɗan ɗago da kanta, daidai lokacin shi kuma ya ɗan ranƙwafo don tattare documents ɗin, kanta ne ya bugi haɓanshi wanda hakan yasashi rumtse ido, ahankali yace "Auchhhh!!" dan ya ɗanji zafi sosai.
Sakin documents ɗin tayi tare da sanya hannuwanta ta rufe bakinta, wani sabon tsoro ne yasake kamata, baki na rawa tace "Kayi haƙuri Wallahi bansaniba ne!!"
Baikulata ba haka yasanya hannu ya shiga tattara papers ɗinsa da suka watse. ganin haka yasa itama tashiga tayasa tattarewa, gaba ɗaya ƙamshinsa ya jefata acikin wani irin yanayi, jin kanta take cikin wani baƙon yanayi, har wani iska ne ke shiga jikinta. Idanunta ne yakai kan wani papers da iska ke shirin kaɗasa wani wajen, da sauri takai hannunta zata kamo paper'n, shima hannunsa yakai batare
da yayi zato ba yaji hannunsa ya sauƙa akan nata, atare sukaji wani shock da sauri yajanye hannunsa daga kan nata tare da ɗaukan paper'n ya miƙe tsaye, baijira komai ba ya nufi wajen motarsa wanda tuni dama driver na jiransa, yana shiga gidan baya driver yayiwa motar key suka fice daga cikin gidan. Saida taji alamun fitansu sannan ta iya miƙewa tsaye daga tsugunnen da take, batare da ta saniba wani murmushi ya bayyana akan fuskarta take kuma saiga hawaye sun ziraro daga cikin idanunta, Wallahi ko za akasheta bazata iya fassara abun da takeji dangane dashi ba, tausayi ne? rauni ne? Ita duk takasa ganewa, tasan koma menene tabbas abun da takeji akanshi na musammanne, idanunsa kaɗai da ta kalla ya sanya taji wani iri ajikinta, tabbas da zata samu mai bata amsar abun da takeji dangane dashi da taso hakan fiye da komai, watarana idan tagansa sai taji kamar tasanya masa kuka, watarana kuwa jitake kamar taje da gudu ta shige jikinsa tayi kuka sosai, wataƙila hakan zai ɗan sama mata salaman abun dake ranta. Sam tama manta da cewa text book zata ɗauko sai kawai ta koma tashiga mota.
Luf tayi ajikin kujeran motar, ƙamshinsa da har yanzu takejinsa acikin hancinta shiyayi fatali da duk wata nutsuwarta, sam tarasa me yasa takejin ƙamshin nasa har yanzu duk da cewa baya tare da ita, hannunta takai tashafi fuskarta, sai alokacin ta gano daga inda ƙamshin ke fitowa, sake kai hannunta kan hancinta tayi tare da shunshunawa, tabbas hannunta da ya taɓa ne ke ƙamshin, wani irin sanyi taji acikin zuciyarta, ɗaura hannun tayi akan fuskarta tare da lumshe idanu, ahaka har suka iso cikin school ɗin. Yau kam tayi late duk da cewa bahaka tasoba, don sunada biology, kuma shine first period, bakuma taso tayi missing lecture ɗin biology ko kaɗan, ai kuwa tana zuwa bakin class ta iske malami aciki, da ƙyar ya barta tashiga cikin ajin, tana zama akan chair ta sauƙe ajiyar zuciya, hannu Nasmah tasanya ta ƙasa ta muntsineta akan cinyarta, ƙasa ƙasa tayi dariya tare da rumtse ido alaman taji zafin muntsinin, hakan da tayi kuma sai ya tuna mata da MR.HELPER ɗinta, yanayin yanda ya rumtse idanunsa da kuma yanda yace "Auchhh!!" Baƙaramin kyau yanayin yayi masa ba, musamman yanda pink lips ɗinsa suka motsa abun saiya ɗauki hankalinta, sai ayanzu moment ɗin kedawowa cikin brain ɗinta da kyau, wani murmushi tasake tare da lumshe idanunta.
"Kenan shima yanajin zafi idan abu yasameshi?" A zuciyarta ta tambayi kanta, wani murmushin ta sakeyi alokacin da ta tuna da kyawun idanunsa, a iya tsawon rayuwarta itakam bataga irinsa ba, bata kuma tunanin zata taɓa ganin wani irinsa. Ataƙaice dai har biology teacher'n yafita, bata tsinci komai daga cikin darasin daya koyar ba, gaba ɗaya hankali da tunaninta yau akan Mr.Helper yake.
Su Shukra da kansu yau sun fuskanci cewa tana cikin farinciki, don koda aka fita break zagewa tayi tayita zuba musu surutu.
7:59 AM
Gyara zama yayi tare da ɗaura sit belt ajikinsa, bayansa ya jingina ajikin luntsumemiyar kujeran dake cikin jirgin, 8:00 daidai jirginnasu ya ɗaga zuwa sararin samaniya, tafin hannunsa yakai ya rufe fuskarsa, ko hakan zaisa yaɗan rage stress ɗin dayake ciki, ahankali yaji wani baƙon ƙamshi na ratsa cikin hancinsa yana me cakuɗa da numfashinsa, mamakine yakamasa don sam baisan daga ina ƙamshin ke fitowa ba, ɗan waigawa bayansa yayi, dayake ɓangaren business class ne kowa sha'aninsa kawai yake, babu kowa kuma akusa dashi dasai yace na kusa dashine ke ƙamshin. Sake shunshuna hannunsa yayi, sai alokacin ya tabbatar da cewa tabbas hannunsa ne ke ƙamshin, bawani turarene me ƙarfi ba, irin dai turaren nanne da idan mutum yasa saima ka matso kusa dashi kafun kajiyo ƙamshin. "Itace!" yafaɗa in a silent voice ɗinsa, sake kai hannun kan hancinsa yayi tare da ɗan taɓe lips ɗinsa. Azuciyarsa yace.
"Su ƙamshi manya" Jarida ya ɗauka yashiga karantawa tare da watsar da duk wani tunani dake ransa.
Hadari ne sosai ya haɗu agarin kasancewar anacikin yanayi na damuna, 3:30 pm, fitowarsu sallan La'asar kenan.
Tana idar da sallan ta fito daga cikin masallacin, sosai take matuƙar son yanayi irin wan
nan, ahankali sanyin iska ke busa ko ina, hijab ɗinta iska keneman yayewa, da sauri tasanya hannuwanta ta kameshi ƙam ajikinta. Yanayin na fusgarta hakan yasa kai tsaye ta nufi wajen da garden ɗin makarantar yake.
Ƴan tsirarun ɗalibai ne awajen, kowa harkan gabansa kawai yake. Gefe da garden ɗin wasu kujeru ne masu kyaun gaske da aka tanada don zama, tana zama aka soma yayyafi hakan yasa tatashi da sauri don komawa cikin makaranta. Idanunta ne suka sauƙa akanshi, tsaye yake ya sanya duka hannuwansa acikin aljihun wandonsa, idanunsa ƙyam akanta fuskarsa ɗauke da beautiful smile, cike da mamakin ganinsa tasaki murmushi tare da sanya hannu ta kare kanta, kasancewar zuwa lokacin ruwa ya fara sauƙa kaɗan kaɗan. ganin haka yasanyashi takowa yazo gab da ita, cikin sexy voice ɗinsa yace.
"Kina tsoron ruwa ne?"
Murmushi tayi wanda har saida ya bayyana white teeth ɗinta, kanta ta kaɗa masa alamar "Eh" ruwane ya ɓarke me ƙarfin gaske hakan yasa lokaci guda ta ruɗe, shikansa ƙarfin ruwan yabasa mamaki, hannunta ya kama zuwa wani ɗan rumfa dake wajen, duk da shigarsu rumfar iya kawunansu kawai ruwan zai tare amma banda gangar jikinsu. Cikin yanayi na tsoro ta naɗe hannayenta akan ƙirjinta, kallonsa tayi da fuskarta dake jiƙe da ruwa. Murmushi yayi mata tare da ɗage mata giransa ɗaya, itama murmushin tayi masa tare da sake takure kanta waje ɗaya, don bawai sun tsirane daga ruwanba, har yanzu yana dukan jikinsu, tuni uniform ɗinta yajiƙe sunbi jikinta sun lafe, shikansa Pharouk gaba ɗaya ya jiƙe duk da cewa akwai denim Jacket ajikinsa hakan bai hanashi jiƙewa ba. bakinta har rawa yake saboda sanyi.
"Zieyaderh!" yaƙira sunanta akasalance.
Ɗago fuskarta tayi ta kalleshi, idanunsa ya sauƙe akan beautyful lips ɗinta wanda suka jiƙe suke kuma ɗigar da ruwa, wani irin tashi yaji tsikar jikinsa yayi, take lissafin kansa suka shiga kuncewa, wani irin saliva dake maƙale a maƙoshinsa ya haɗiya, sam bata ɗauke idanunta akansa ba, yanayin sanyin da take ji yasanyata lumshe idanunta tare da ɗan buɗewa alokaci guda, hakan da tayi baƙaramin kyau yaƙarawa face ɗinta ba, take yaji wani irin different feelings na sauƙa ajikinsa, ji yake kamar yajawota jikinsa ya bata professional kissing, amma mene sunansa idan yayi hakan? jingina bayansa yayi da jikin bango tare da lumshe idanunsa, bugun zuciyarsa ƙaruwa take, wani irin maganaɗisun sha'awarta ne ke fusgarsa, lokaci guda mood ɗinsa ya sauya. Cikin zaƙuwa da tsayuwan Zieyaderh ta juyo ta kalleshi acikin yanayinta na shagwaɓa tace "Am tired!!" Ahankali ya buɗe idanunsa wanda sukai ja ya sauƙesu akanta, wani irin yarrr taji ajikinta sakamakon kallon cikin idanunsa da tayi, batasan irin wannan yanayin ba hakan yasa ahankali tace "Are you okay?"
Akasalance yayi murmushin daya bayyana dimples ɗinsa.
"Yes am okay!" yafaɗa yana me ƙare mata kallo, murmushi tayi masa sannan ta juya tacigaba da kallon ruwa sam ta manta bata maida hannuwanta ƙirjinta ta kare baiyanar dasukayi ba, don saboda yanayin sanyin da ake ciki yasanya tsikar jikinta mimmiƙewa, hakan yasa nipples ɗinta ma suka miƙe tsaye, har idan kayi mata kallon tsab zaka iya ganinsu. Sauƙan idanunsa akan ƙirjinta baƙaramin gigita masa tunani yayi ba, take yaji tunaninsa ya tsaya cak, da sauri ya ɗauke idanunsa daga kanta tare da sanya baki ya cije laɓɓansa. (Nasan team RAJ, zasuce inama da ita da Sooraj ne😝) Wani irin tsawa da aka buga ne ya matuƙar firgitata har batasan sanda ta dawo baya da sauri ba, sambata kula ba ta faɗa jikinsa, ƙamƙame jikinta tayi ƙaƙam tare da rumtse idanunta. "Innalillahi" kawai take ambata acikin zuciyarta don ta tsorata, ashe ba ita kaɗaice ke ambatan hakan ba harda Pharouk don alokacin da bayanta ya mannu da ƙirjinsa baƙaramin ruɗewa yayi ba, har numfashinsa saida yashiga seizing na ƴan wasu minutes. Hanneyansa dake rawa yaɗaura akan shoulder ɗinta, hakanne ya bata damar dawowa cikin hankalinta, da sauri ta matsa gefe, cikin wani irin kunya ta jawo hijab ɗinta ta rufe fuskarta. "Me na aikata haka?" ta tambayi kanta cike da nadama.
Matsowa yayi gab da ita tare da sanya hannu ya ɗ
ago haɓanta, hijabin ya ja baya fuskarta ya bayya, da sauri ta kulle idanunta don batajin zata iya haɗa idanu dashi.
Murmushi yayi mata ahankali ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta, kiss yayi mata a forehead ɗinta, tare da kai bakinsa daidai saitin kunneta ahankali yace "Ki kulamin da kanki!" Yana gama faɗan haka ya juya acikin ruwan ya tafi, yayi hakane saboda matuƙar ya ƙara some minutes awajen, zai iya hugging ɗinta. (Chab lallai Pharouk yau zakasha zagi awajen ƴan team ɗin SOORAJ)
Buɗe idanunta tayi ahankali cike da fargaba da kuma tsoron abun daya mata, babu wani namiji daya taɓa yi mata kiss saishi, mekenan hakan yake nufi? ta tambayi kanta cike da mamaki, kallon bayansa tayi don zuwa yanzu yayi mata nisa, tafiya yake kamar baidamu da ruwan dake dukansa ba.
*SOORAJ*
Tsaye yake acikin wata baranda, dagashi sai wani white crazy jeans dake sanye ajikinsa, bashida ko riga sosai murɗaɗɗiyar surar jikinsa ta bayyana, glass cup ne ahannunsa wanda ke ɗauke da ruwan inibi, ruwa da iska ake sosai, amma ko kaɗan baijin wannan sanyin ajikinshi. Hakanan yakejin kansa cikin wani bad mood, baikuma san dalilin hakan ba, tunanin dake maƙale azuciyarsa ayanzu yafi komai damunsa, meyasa yake ganinta acikin idanunsa? meyasa yakeji tamkar anrubuta wani abu daya shafeta acikin zuciyarsa? yana da buƙatar sanin meyakeji, da kuma dalilin dayasa yakejin hakan acikin rai da zuciyarsa.
Ahankali ƙarfin ruwan ke tsagaitawa, ganin haka yasa cikin sauri ta nufi farfajiyan makarantar, harda ɗan sassarfa take haɗawa wajen shigewa cikin ajinsu, Nasmah da Shukra dake tsaye bakin window sukayo wajenta da sauri cikin damuwa suka haɗa baki wajen tambayanta ina taje "Garden" ta basu amsa ataƙaice. Sunyi mamakin hakan amma sai kawai suka share suka cigaba da hiransu.
Ruwan na tsagaitawa aka tashesu ko 5 ma batayi ba, saboda sosai garin ya ɗau sanyi. Atare suka fito ita dasu Nasmah, daidai lokacin wata baƙar Car ƙiran Jeep ta kunno kai cikin makarantar, tsayawa sukayi a compound ɗin makarantar Zieyaderh na ta baza idanu ko zata hango Kamalu driver. Ƙasa yayi da glass ɗin motar tare da kafeta da idanunsa, ahankali ya danna horn, hakanne ya ɗauki hankalin ɗalibai da yawa har kowa yajuyo yana kallonsa, idanunta ne suka sauƙa akanshi, tsananin mamakine ya kamata, tabbas tasan ita yazo ɗauka, to ina Kamalu driver? ya ma akayi yasan antashesu? Duk bata dame amsa mata waƴannan tambayoyin, hakan yasa tayiwa su Nasmah sallama tanufi inda yake. Tana buɗe murfin motar wani sassanyan ƙamshin turare ya daki hancinta, saidai wannan turaren sam ba irin wanda yake gigita tunaninta bane. Ɗan satan kallonsa tayi tare da cewa "Ina wuni"
Bai amsa mata ba sai dai murmushi da ya bayyana akan fuskarsa. Har suka soma tafiya babu wanda yasake ce da ɗan uwansa wani abu, saidai kuma yana yawan satan kallonta lokaci zuwa lokaci, aranta mamakin yanda halinsu ya kusan zuwa ɗaya take. "Kenan su duka familyn su haka suke?" ta tambayi kanta azuci. "Uhmmm gwara wannan ma ae yana murmushi amma wancan Mr.Helper ɗin kam,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 38