Wayarsa ƙirar Galaxy S20 ne tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ko kallon wayan baiyiba yasakai yafice daga cikin ɗakin, yayarda da abun da zuciyarsa tagama yanke masa, bazai bari awannan karon yasake faɗawa cikin irin halin daya faɗa abaya ba, ɗaukar ƙaddara yazame masa dole, don hakane ya yankewa kansa hukuncin nesantar duk wata ƴa mace, mahaifiyarsa ce kawai bazai iya nesanta kansa da'ita ba, amma sauran mata kam hakan yazame masa dole, kodan rufewar sirrinsa.
***
"Nagama yanke shawara Aure zamuyiwa Ziyada" Inna Ma'u tafaɗi haka ga Malam Garba bayan takai loman tuwo bakinta.
Malam Garba dake zaune akan ƴar tabarma ya ɗago kansa ya kalleta, cikin murya mai sanyi, yace... "Aure kuma Ma'u?"
"Ƙwarai kuwa Aure, ko so kake muzaba mata idanu tacigaba da yawon bin maza? to idan kuwa haka kakeso wallahi saina cire hanuna akan lamuranku!" Inna Ma'u tafaɗi haka cikin ɓacin rai.
"A'a bawai nace bazatayi aure bane Ma'u, duk hukuncin da kika yanke akan Ziyada aini bazance a'a ba, amma kinsan banda kuɗin aurenta a yanzu!" ya ƙare maganar cike da tsoron Inna Ma'un.
"Kai dai kawai kazubamin ido, domin nariga dana gama yanke shawara, gobe Tsoho ɗan dashe yace zai kawo kuɗin aurenta, kuma kadai san yanda tsoho ɗan dashe yake, idan yace zai auri yarinya, to baya buƙatar komai daga wajen iyayenta, hakanan zamu kaita mu wurgar "
Da sauri Malam Garba yasake ɗagowa ya kalli Inna Ma'u bakinsa na rawa yace
"Tsoho ɗan dashe kuma? ɗansa zaki aurawa Ziyada'n?"
Harara Inna Ma'u ta watsa masa cike da takaici tace "Atunaninka akwai wani matashin saurayin da zai jajiɓawa kansa wannan maƴyar ƴartaka? Ɗan dashe ne ke nemanta kuma nariga dana basa, ko kana da maganane?"
Kansa yagirgiza alamar "A'a" amma kuma har acikin zuciyarsa baiji daɗin hakan ba, kowa yasan Tsoho ɗan dashe ba mutumin kirki bane, tsohon banzane dabai riƙe mutumcin kansa ba, sannan kuma sam baisan darajan aure ba, ya auri mata sama da 15, daya auri mace tana samun ciki, zai koreta tare da takardan sakinta. To amma mai zaice, shi awajensa komai Inna Ma'u tayi dai dai ne...
*(A wannan littafin zan buga muku wasa mai zafi, kudai kucigaba da bina, sannan kada ku manta comment ɗinku shizai ƙaramin ƙarfin guiwa)*
*14/March/2020*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*CHAPTER 3*
Tunda yafita baidawo gidannasa ba har sai ƙarfe goma da rabi na dare, saida yagama daidaita tsayuwar motar tasa, kafun ya cire sit velt ɗin dake saƙale ajikinsa, aƙalla yakusan 7 minute acikin motar baifito ba, ahankali ya zuro ƙafafunsa waje cike da isa irin nasa, dama shi gwanine wajen jin kai da kuma miskilanci, baka gane gabansa baka gane bayansa. Sam yamanta da cewa wai yau aka ɗaura masa aure, saboda haka baiyi tunani ko tsammanin samun wata halitta acikin gidan nasa ba, kamar koda yaushe idan yashiga falon gidan direct bedroom ɗinsa yake wucewa, yauma hakance takasance. Wanka yasoma yi kafun yadawo yayiwa kansa mazauni akan gado, laptop ɗinsa yajawo yasoma latsawa, long jeans ne ajikinsa sai kuma wata farar riga wacce aka jere aninaye agabanta, saidai bai maƙala aninayen duka ba, hakan yasanya faffaɗan ƙirjinsa bayyana, kusan koda yaushe irin wannan shigar shine shigansa, duk da kasancewarsa farin mutum amma kuma yanason kalan fari, shiyasa yawancin kayansa suka kasance farare, duk da cewa idanu da nutsuwarsa suna ga abun dayakeyi acikin laptop ɗinsa, amma hakan baihanasa jiyo motsi a ɗakin dake kusa danasa ba, mamakine yakamasa don baiyi tunanin akwai wani agidan bayan shiba, sai alokacin auren da aka ɗaura nasa yau ya faɗo masa, jiyayi gabansa yafaɗi, yayinda bugun zuciyarsa ta tsananta, da sauri yakawar da ruɗun dayake ƙoƙarin shiga, tare da miƙewa tsaye, ƙirjinsa na bugawa haka yafice daga cikin ɗakin nasa.
7 minute yaɗauka yana tsaye yayinda yaɗaura hanunsa akan handle ɗin ƙofar, kokonto yake akan shigarsa cikin ɗakin, ganin baida wata mafita da ta wuce ya shiga yasanya yaturo ƙofar ahankali bakinsa ɗauke da sallama.
Daidai lokacin wata matashiyar budurwa da bazata wuce 21 years ba tafito daga bathroom jikinta duk ruwa da'alama wanka tayi, idanunsu ne yasauƙa acikin na juna, da sauri ya ɗauke kansa daga kallonta, itama akunyace tayi ƙasa da kanta, durƙusawa tayi har ƙasa cikin sanyin murya tace "Ina wuni" shiru yaɗanyi nawasu sakanni kamar bazai amsa mata ba. "Lafiya" yafaɗa ataƙaice haɗe da juyawa yafice daga cikin ɗakin, bayansa tabi da kallo tare da lumshe idanunta, wani irin sanyi taji na ratsata, ahankali tace. "Lallai samun cikakken Namiji mai kyau da aji kamar ka Sooraj babban sa'ane ga kowacce ƴa mace"
Yana fita daga cikin ɗakinnata yaji kansa dake tsananin yi masa ciwo, yayi masa nauyi. haka yaji gaba ɗaya duniyar na juya masa, ƙirjinsa ne keta luguden duka, da ƙyar ya iya dafe kansa yakoma ɗakinsa, faɗawa kan gado yayi tare da rumtse idanunsa, shikaɗai yasan abunda yakeji, Ƙunci, Raɗaɗi, sune suka mamaye zuciyarsa, haƙoransa yasanya ya datse laɓɓansa, acikin zuciyarsa yaketa karanto addu'o'i'n samun nutsuwa,, ahankali kuwa yaji nutsuwa tasoma sauƙar masa, yayinda yaji ransa nayi masa sanyi, bai tsagaita dayin addu'anba har bacci ɓarawo ya ɗaukesa.
Ɓangaren amarya kuwa kwalliya ta tsantsara tanajiran dawowan ango, saidai kuma ko motsinsa bata sakejiba, shiru shiru har 12 hakan yasa ta rakuɓe jikinta ajikin gado tasoma kuka, tun tana kukan har bacci itama ya saceta.
*** Kamar koda yaushe kuma kamar kowacce rana, ƙiran sallan asuban fari akan kunnuwanta, duk da cewa bacci bai isheta ba amma kuma tashi yazame mata dole, kodan aikin gida dake kanta, tashi tayi daga kan ƴar tabarmar da take kwana akai ta zauna, hanunta takai kan wuyanta tashiga sosawa, daren jiya saurayene sukayi lugude ajikinta, suncijeta son ransu, dama ɗakinnata bawani wadataccen rufi yake dashi ba, gashi ko ƙofa babu, labulene kawai da aka sakaya ajikin ƙofar, ako wani dare sauro cizonta suke sosai, tun bata saba da cizon nasuba harta saba, kuma sosai cizon dasukeyi mata ke illatata, saboda kusan kullum fama take da zazzaɓi da kuma ciwon kai, amma dayake bata da wani gata haka take yawo cikin ciwo, saidai idan wahala tayi wahala tasamu ruwa akofi ta tofa Fatiha ƙafa uku tasha, da yardan Allah shike yaye mata ciwon kai.
Ruwa ta samu tayi alwala haɗe da kabbara salla tana idarwa kuwa ta ɗauki tulu tawuce rafin da suke ebo ruwa. Sanyi ake busawa sosai amma haka take tafiya babu ko mayafin kirki ajikinta, tunda tafito daga gida harta isa rafi bata haɗu da kowa ba, kowa nagida yana bacci banda ita wahalalliya marar gata. Zama tayi agaban wawakeken kogin haɗe da ƙurawa ruwan dake gudana acikin kogin idanu, wasu hawayene masu ɗumi suka gangaro daga cikin idanunta. akullum kuma ako da yaushe, addu'a take Allah yakawo mata ɗauki, tana buƙatar farinciki acikin rayuwarta, Kwantar da kanta tayi akan guiwowinta, hawaye nacigaba da tsiyaya daga cikin idanunta. Tajima sosai tana zubda ƙwalla kafun daga bisani ta ɗauki ruwan da ta iba tabar wajen, lokacin har gari yasomayin haske. Gaba ɗaya ayyukan gidan ita tayisu tundaga kan shara da wanke wanke harzuwa ɗumamen tuwo, tana tsugune agaban murhu tana ta kiciniyar iza wutan murhu, Inna Ma'u tafito daga ɗaki hanunta ɗauke da tulin kayan wanki, watsawa Ziyada kayan tayi, ayatsine tace.
"Nanda mintuna 20 nakeson nagansu awanke"
Idan da sabo Ziyada ta saba da wannan wahalan, saboda haka bataji komaiba taɗauki kayan tasomawa wankewa.
***
Yafi mintuna 20 yana juya biron dake riƙe ahanunsa, gabansa kuwa wata ƴar ƙaramar farar takarda ne aje, so yake ya rubuta abun da shine mafita agaresa amma kuma yana fargaban abun da zaije yadawo, maganganun Mahaifiyarsa ne suka shiga yi masa yawon acikin kunnuwansa, inda take cewa..... "Wallahi kaji na rantse ma awannan karon kasaki matar da muka aurama, ranka saiyayi mummunan ɓaci, zakuma kaga fushinmu irin wanda baka taɓa gani ba!"
Tun ɗazu kalamannata keyawo acikin kansa, lumshe idanunsa da suka soma sauya kala daga farare zuwa jajaye yayi, tare da sanya haƙoransa ya datse lips ɗinsa, tsikar jikinsa ne yasoma tashi yayinda gashin jikinsa suka soma mimmiƙewa tsaye, jiyayi kansa yasoma juyawa, yayinda tunanin wasu abubuwa ke son hautsina masa ƙwaƙwlwa, da sauri yaɗaura alƙalami akan farar yakardan yasoma rubutu, bawani rubutu mai tsayi yayi ajikin takardan ba, ya nannaɗeta tare da sanya ta acikin wani envelop.
Tashi yayi daga zaunen dayake yashige cikin bathroom. Wanka yayi kana yafito sanye da rigan wanka ajikinsa.
Kayan training ɗinsa da sukeyi masa matuƙar kyau yasanya, tare da ɗaukan wata ƴar doguwar jaka, ɗaukan takardan dayayi rubutu acikinta ɗazu yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin.
Yana murɗa ƙofar ɗakin ta buɗe hakan yasa ya kutsa kansa ciki.
Tanaganinsa tatashi zaune daga kwancen da take, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke idanunsa akanta, a kuma wannan kallon dayayi matane ya gane cewa taci kuka ta ƙoshi.
Cikin takunsa na isa yaƙaraso har wajen da take zaune.
Miƙa mata takardan hanunnasa yayi batare dayace da ita komai ba.
Karɓan takardan tayi tana mai kafesa da idanunta, juyawa yayi yanufi hanyar fita daga ɗakin, har yakai bakin ƙofa saikuma ya tsaya cak, murya ashaƙe yace.
"Kada kiga laifina, haka tawa ƙaddaran take"
yana gama faɗin haka yafice daga ɗakin, ko waiwayowa gareta baiyiba.
Kallon mamaki tabisa dashi
"Kenan miye maganganunsa suke nufi?" tatambayi kanta tambayar da babu amsa. Buɗe envelop ɗin daya bata tayi tare da zaro ƴar ƙaramar takardan dake ciki.
Wani irin bugawa zuciyarta tayi yayinda gaba ɗaya jikinta yaɗauki rawa, sake waro idanunta tayi tana karanta abun dake rubuce ajikin takardan. Kukane yaƙwace mata, lokaci guda ta shiga Jijjiga kanta, azabure tatashi daga kan gadon tafice daga cikin ɗakin.
Tana ƙarasawa compound ɗin gidan shikuma motarsa na ƙarisa ficewa daga cikin gidan. Wani irin ƙara tasaka haɗe da zubewa aƙasa tashiga rera kuka, ganin kukan bazai mata maganin komaiba yasa ta koma cikin gida, mayafinta kawai taɗauka saikuma envelop ɗin dake riƙe ahanunta.
Tazo fita daga gidan maigadi yatsareta da tambayar lafiya take kuka. Ko kallonsa batayiba tafice tana ƙara volume ɗin kukanta..
Shikuwa Tanimu mai gadi komawa yayi kan benci ya zauna, aransa kuwa yana tsananin mamakin hali irin na SOORAJ, ko tantama bayayi abun da yafaru da sauran matanne itama yafaru da ita, shiyasa tatafi tana kuka...
Yana tsaye agaban madubi, wani ɗan madaidaicin towel ne riƙe ahanunsa, yana goge gumin dake tsastsafowa ta goshinsa, kasancewar yanzu gama training ɗinsa.
Wayarsace tasoma ƙara alaman shigowan ƙira, saida yaji gabansa yafaɗi alokacin dayaga sunan dake yawo akan screen ɗin wayartasa, maganganun Ummu ne suka shiga dawowa kunnuwansa filla filla. Jiki a sanyaye ya ɗauki wayar tasa ya kara akan kunnensa.
Ko sallaman da Sooraj ɗin keyi masa bai amsa ba, cike da ɓacin rai yasoma cewa..... " Yau katabbatarmin da cewa kacika ishashshe Sooraj, yau kuma kaƙara tabbatar min da cewa kai mutumin banza ne, wanda baida tunani, ashe har abada bazaka daina kunyatamu ba? shikenan kaci gaba duniyace, ita kuma yarinyar da kayiwa saki har uku kasani wallahi Allah bazai barkaba, sai ya saka mata, Shashasha kawai!!!"
Jikin Sooraj ne yaɗauki rawa cikin inda inda yace "Dan Allah Abba ka sau....."
"Bazan taɓa sauraranka ba Sooraj, wallahi ko ganinka banasonyi, gargaɗi na ƙarshe kada kasake ka zomin gida, tunda haka kazaɓa kaci gaba, mukam munzare hannuwan mu daga cikin al'amuranka!!!"
Abba yafaɗa murya a kausashe.
Baibawa Sooraj damar sake cewa komaiba yakatse wayar.
Zamewa Sooraj yayi daga tsayen da yake yazauna daɓas, hannayensa duka yasanya ya tallafi kansa, idanunsa ne suka kaɗa sukai jajur, take jijiyoyin dake kwance akan goshinsa suka fito raɗa raɗa, saurin rumtse idanunsa yayi, domin idan yace zai barsu a buɗe, to tabbas ruwan hawayene zasu fito daga cikinsu...
*ZIYADA*
Tun safe take ta faman jibgan aiki kamar wata jaka, har zuwa yanzu kuwa bata huta ba. Shigowarta gidan kenan tasamu Inna' Ma'u tsaye sai rangaɗa guɗa take, hanunta riƙe da kuɗaɗe masu yawa, gefenta kuwa Malam Garba ne zaune yayi jigum, shidai baida tacewa, komai Inna Ma'u ne keyi, tamaidashi kamar wani yaronta, shikuwa biyayya yakeyi mata kamar raƙumi da akala duk hanyar da ta jasa nan yake bi.
Harara Inna Ma'u ta aikawa Ziyada da ta tsaya tana kallonta.
"Mayyar banza miye kika tsaya kina kallona?"
Da sauri Ziyada tayi ƙasa da kanta, sumu sumu ta wuce cikin ɗakinta, hakanan taji gabanta na faɗuwa, jitake ajikinta kamar wani babban al'amari na kusantota, wanda kuma da dukkan alama ba abubane mai daɗi.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*CHAPTER 4*
Tunda ya zauna ya tallafe kansa da duka hannayensa biyu baisake wani ƙwaƙƙwaran motsiba, numfashi kawai yake fitarwa a hankali..
Mas'oud dake tsaye akansa tuntuni yasanya hanu ya dafa kafaɗansa.
Jin sauƙar hanu akan kafaɗansa ya tabbatar masa da cewa Mas'oud ne, ɗago kansa yayi ya kalli Mas'oud da rinannun idonsa.
Yanayin yanda Mas'oud yaga cikin idanun SOORAJ saida ya tsorita, saboda bai taɓa ganin abokinnasa acikin matsananciyar damuwa irin wannan ba. Zagayowa yayi ya zauna akusa da SOORAJ ɗin. Cike da kulawa yace.
"Basai na tambayeka ba RAJ nasan kana cikin damuwa, amma kuma bantaɓa ganinka acikin irin wannan yanayin ba, ina fata dai ba halinnaka kasake gwadawa ba?"
Sauƙe hannayensa dake kansa yayi ƙasa, haɗe da furzar da wani irin iska mai zafi daga bakinsa, kallon Mas'oud ɗin yayi kamar zaice dashi wani abu saikuma ya fasa, kawai ya kawar da kansa gefe.
Murmushi Mas'oud yayi tare da girgiza kansa, tun suna ƙanana suke tare shida SOORAJ saboda haka kusan gaba ɗaya halayyar SOORAJ ɗin Mas'oud yasani, idan SOORAJ bayason yin magana, akwai wani irin kallo dayakeyi, dazaran Mas'oud yaga SOORAJ yayi irin wannan kallon, to yasan mene kallon ke nufi.
"Bazan tilastaka kacemin wani abuba RAJ amma kuma kada kamanta cewa nidakai tamkar ƴan uwan juna ne, har sai yaushene zaka tsaya kana ɓoye damuwarka? yanada kyau ko bazaka faɗa duniya tasani ba, muda muke tare dakai, muncancanci musan damuwarka, amma maiyasa ako da yaushe kake ware kanka? idan har bazaka iya faɗamin damuwarka ba RAJ banda wani amfani awajenka, haka tarayyata dakaima bata da wani amfani!" Mas'oud yafaɗi haka cikin ƙunan zuciya, saboda shi kansa al'amarin SOORAJ yasoma basa haushi, koda yaushe SOORAJ acikin damuwa yake, abune mawuyaci kaga dariyan SOORAJ, gaba ɗaya yasamo wani banzan hali ya arawa kansa, baida aiki sai zaman ƙunci.
Kallon takaici Mas'oud yashiga bin SOORAJ ɗindashi, ganin ko alamar ɗaukar maganarsa baiyi ba, azuciye yatashi zaibar wajen. Riƙo hanunsa SOORAJ yayi, cikin wata irin murya mai sanyi yace.
"Bazan iyaba Mas'oud, niba namiji bane dazai iya riƙe mace, itama Nasaketa!"
Idanu Mas'oud yazaro waje cike da mamakin jin kalaman dake fita abakin SOORAJ ɗin.
"Kasaketa fa kace?" Mas'oud yatambaya cike da mamaki.
Kai kawai SOORAJ ya kaɗa masa alamar "Eh"
Wani irin tuƙuƙin baƙinciki da takaicin SOORAJ ɗinne suka turnuƙe Mas'oud, yanzu kam ya yarda cewa akwai matsala a ƙwaƙwalwar SOORAJ domin maihankali bazai aikata irin abun da SOORAJ ke aikatawa ba.
"Anya kuwa kana cikin hankalinka RAJ? kodai asiri akayi maka ne? shin kakuwa san abunda kake aikatawa? kasaketafa itama kace? mata huɗu fa kenan yanzu ana aurama kana sakinsu, daga ankai maka mace yau washe gari kake sakota, wai kodai aljanune dakai ??" Mas'oud yatambayesa cike da tsananin mamaki, saboda duk wani maihankali dole ya tsoraci lamarin SOORAJ.
Kallon Mas'oud ɗin SOORAJ yayi da jajayen idanunsa, araunane yace "Inada hankali Mas'oud kamar yanda kaima kake dashi, abu ɗaya kawai nasani shine wannan itace ƘADDARATA!" yana kaiwa ƙarshen zancennasa ya miƙe tsaye tare da soma tattara kayan training ɗinsa, Mas'oud na kallonsa ya tattara komai nasa yafice daga cikin ɗakin training ɗin. Mas'oud kam kasa tashi yayi yazauna daɓas, sosai al'ajabi da kuma mamakin abokinnasa RAJ ke ƙara kamasa, shikam yanzu yayarda cewa aljana ce tashafi Abokinnasa.
SOORAJ kuwa yana fita daga wajen training ɗin direct motarsa yanufa, yana shiga yayi mata key tare da cillata kan titi..
Yana komawa gidansa yayi wanka, dakansa yashiga cikin makeken kitchine ɗinsa, wanda yazuba masa kayan amfani, babu abun da babu na amfani acikin kitchine ɗin. Ruwan tea yadafa kana ya juye a flask, kan dinning area yadawo yazauna tare da haɗa tea, ahankali yake sipping tea ɗin yayinda ɗayan hanunsa ke riƙe da wayarsa yana latsawa. Safiya rana dare SOORAJ bayida wani abinci sama da ruwan tea, arana sai yasha tea sama da sau uku, abune mawuyaci yazauna yaci abinci kamar yanda kowa yakeci. Yana shanye tea ɗin ya miƙe tsaye, mug ɗin da ya haɗa tea ɗin aciki ya ɗauka ya wuce kitchine, wankewa yayi yamaida shi mazauninsa.
Falo yadawo yazauna akan ɗaya daga cikin lallausan kujerun falon, remote ɗin receiver yaɗauka, ya sanja tasha. Knocking ƙofar falon akasomayi, cikin gajiyawa yace "Yes come in"
Piter ne yashigo hanunsa riƙe da wasu zabga zabgan tsintsiyaye dakuma moper, ɗurƙusawa yayi cike da ladabi yace "Good Morning Sir"
"Morning" kawai yace tare da tashi yatattare wayoyinsa ya nufi bedroom, don bawa piter daman yin aikinsa da kyau.
Yana shiga ɗaki yafaɗa saman gado haɗe da jawo pillow yaɗaura kansa akai. Shiru yayi yana mai lumshe idanunsa, tun ɗazu kalaman Abbansa ketayi masa yawo acikin kunnuwansa, tabbas yasan dolene iyayensa suyi fushi dashi, amma shima bayin kansa bane, ƘADDARA ce baikuma isa kauce mata ba, amma yanda iyayen nasa suka ɗauki zafi sosai shine abun dayasanya yaji gaba ɗaƴa duniyar tayi masa ɗumi, shi kaɗai yasan kansa, shikaɗai yasan wanene shi, shine wanda yasan matsalarsa, taya ayanda yake zai iya zama da mace? sai yaushene iyayensa zasu fahimci matsalarsa? sama da shekaru 7 kenan yana fama da matsala guda ɗaya, shiɗin namijine, baida wani wanda zaije yafaɗawa damuwarsa, dole shine zai nemi maganin matsalarsa, haryau kuma akan neman maganin matsalannasa yake amma baidace ba, shikansa bazai iya fitowa fili yafaɗi abun dake damunsa ba, yabarwa kansa cewa matsalansa itace sirrinsa, zama da mace kamar mafarin tonuwar asirin sa ne, yajima yana tunanin cewa shi ba'ayisa don yazauna kuma yasan wata ƴa mace ba, amma dazaran yafara wannan tunanin yake saurin furta astagfirullah domin yasan saɓone yakeyi, to amma yazaiyi shima bayida zaɓi ne, akullum akuma koda yaushe da Allah kawai ya dogara....
*** Tana zaune aɗaki tayi jigum abubuwane suka haɗe mata, aƴan kwanakinnan sosai take mamakin sauyan da Inna Ma'u tayi, tarage sata yawan aikace aikace, sannan kuma koda aikanta ne yanzu andainayi bakamar daba da kullum ƙafarta na waje tana yawon zuwa aika, yanzuma tana zaune ne aɗakinta tana sauraran hayaniyar ƙawayen Inna Ma'u dake tashi a tsakar gidan, itadai batasan meke gudana acikin gidannasu ba amma tabbas tasan cewa akwai wani abu da za'ayi acikin gidan. Zulai ƙawar Inna Ma'u ce ta yaye yagalgalellen labulen dake ƙofar ɗakin nata. Ayatsine ta watsowa Ziyada dake zaune harara, "Uwar munafurci saiki fito ae" cewar Zulai, tana gama faɗan haka kuwa tasake labulen tayi tafiyarta.
Jiki asaɓule Ziyada tafito daga cikin ɗakin nata, Gani tayi su Inna Ma'u sun baje akan tabarma yayinda suka kwaɓa lalle awani babban fanteka.
"Zo maza ki zauna" ɗaya daga cikin ƙawayen Inna Ma'u tace da Ziyada.
Cikin sanyin daya zame mata sabo taƙaraso ta durƙusa agabansu, ƙirjinta sai bugawa da sauri yake saboda tsabar tsoronsu da take.
Zaunar da ita sukayi agabansu, yayinda suka sanya ta kwaye musu cinyoyinta, da ƙarfin gaske suka shiga durza mata ƙwaɓeɓɓen lallen ajikinta, hatta fuskarta saida suka mulke mata shi da lalle, itadai ganin abun take awani baƙon yanayi, saboda tasan agarin nasu idan za'awa mace aurene kawai ake yi mata haka, suna gama shafa mata lallen sukace taje ta wanke, wani irin daɗine yaziyarci zuciyarta, domin albarkacin wannan lallen da suka shafa mata yasa zatayi wanka, bata mantawa rabonta da wanka yau sati guda kenan, dokace mai zaman kanta Inna Ma'u takafa mata akan cewa duk randa tayi wanka, bazata sake yi ba sai bayan wani satin, ruwa takandama abaho tayi bayinsu, alokacin da tacire kayanta tasoma watsawa jikinta ruwa, saida ta sauƙe wasu lafiyayyun ajiyar zuciya harsau uku, saboda wani irin sanyin daɗi daya ratsata, dama ita tuncan haka nan Allah yayita, tanada tsananin sonyin wanka, amma kuma bata samu tanayi saboda uƙubar Inna Ma'u.
Inna Ma'u kuwa masifa ta rufe ƙawayennata dashi wai akan mai zasu kwaɓa lalle su shafawa Ziyada. Zulai ce tagyara zama haɗe da turo ɗaurin ɗankwalinta gaba. "Wallahi yanzu na tabbatar baki da wayo Ma'u, kinga wannan lallen damuka shafa mata, shizai sanya jikinta yaƙara kyau, hasken fatarta yasake fitowa, kinsan yarinyar shegiya ɗanbanzan kyaune da ita, to kinga yanzu zata ƙara kyau akan nada, idan Tsoho Ɗan Dashe kuwa yaganta, saiya ƙara susucewa akanta, kinga ke kuwa kinsamu hanyar da zaki amshe masa ƴan kuɗaɗe kice kuɗin gyaran jiki, ai abirni haka akeyi kinsan nifa nayi zaman birni"
Shewa Inna Ma'u tasanya haɗe da bawa Zulai hanu suka tafa, cike dajin daɗi tace "Wallahi shiyasa nake mugun sonki Zulai, kinsan kan duniya, aikuwa ayau yau saina karɓi wani abu daga wajensa" sake tafawa Inna Ma'u da Zulai sukayi daidai lokacin Ziyada tafito daga wanka, zanine ɗaure aƙirjinta kanta gaba ɗaya yajiƙe yake da ruwa, tana shigewa ɗakinta, Zulai tadawo da kallonta ga Inna Ma'u cike da mamaki tace "Wai Ma'u dama haka wannan yarinyar keda diri da kyau? nikuwa anya basu haɗa iri da larabawa ba?"
Taɓe baki Inna Ma'u tayi, domin ita aduniyarta babu abun datafi tsana kamar taji anyabi Ziyada, "To wama yasanine tsinannu, ai tunda nasamu nagama da uwarta itama yarinyar bawuya zata bani ba, wannan shegen idanun nasu masu kama dana aljanu yana ɗaya daga cikin abun dayasa na mugun tsanarsu, gashi komai na halittar uwarta ta kwashe!" Inna Ma'u tafaɗi haka cike da baƙin ciki.
"Aikuwa Ma'u kinyi farar dabara da kika haɗa auren ta da Ɗan Dashe, kinga zata ƙare rayuwarta cikin ƙasƙanci, kinsansa baya riƙe aure, duk da yagama tsofewa, amma baijirayi kansa ba, dakin tsaya kuwa kina nan zakiga wani sarki ko senata sunzo neman aurenta" cewar wata daga cikin ƙawayen Inna Ma'un, wato Lantana.
"Cab iye bakinki Lantana, ina darai kam ƙaryane wani mai arziki ya raɓi Ziyada, sam hakan bamai yiwuwa bane, koda kuwa zanyi yawone tsirara na gwammace nayi, dana bar jinin Maryama ta auri wani mai kuɗi, nama kashe maciji bansare kansaba kenan" Faɗar Inna Ma'u. Dariya suka sanya sudukansu, yayinda ƙawayennata sukacigaba da fonfata....
Ziyada kuwa tsabar taji daɗin jikinta da tayi wanka tana kwanciya kawai sai bacci ɓarawo ya saceta...
Washe Gari.
*** Tun tashinta yau takejin faɗuwar gaba, babban abun daya ɗaure kanta shine, ƴan uwan mahaifinta da tagani sun cika gidan, da'alama dai kamar biki za'ayi agidannasu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 38