wani ɗaci amaƙoshinsa. Yanayin yanda yake sharara gudu akan titi yasanyasa isowa gida cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, ko jira agama buɗe masa gate ɗin gidan baiyiba ya tura hancin motar ciki.
Yana gama daidaita parking ya fito tare da buɗe gidan baya ya ɗauko ta, still akan shoulder ɗinsa yasake ɗaurata, wata hanya daban naga ya nufa ba wacce zata satadashi da babban falon dake cikin gidan ba, ajikin wata ƙofa naga ya tsaya tare da sanya key ya buɗe, ahankali yatura kofar ya shiga, wani ɗan corridor ne wanda gefe dashi wani haɗaɗɗen swimming pool ne wanda aka ƙawatasa, ruwan ciki gwanin ban sha'awa, sai kuma wasu ƴan tsirarun shukokin flowers da suka ƙara ƙawata kyawun wajen, wata ƙofar yasake buɗewa, wanda ya sadashi da ɗakin baccinsa, kasancewar bayan ƙofar shiga ɗakinsa wanda ke cikin babban falon gidan, akwai wata ƙofa ma wacce take ta bayan compound ɗin gidan. Ƙofar ya mayar ya rufe tare da murza mata key, ƙarasawa gaban makeken gadonsa yayi tare da birkito da ita ta dawo kan hannuwansa, cike da tsananin muguntan dake ransa yasaketa tafaɗa kan gadon da ƙarfi, atake ta saki wani ƙara tare da sakin wani marayan kuka, hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa, tare da tsayawa ƙyam yana kallonta, sam fuskarsa ko alaman wasa babu.
Agalabaice ta sanya hannayenta ta riƙe weast ɗinta dake ciwo kaman zai ɓalle, sam batama gama sanin awacce duniya take ba, kasancewar alluran baccin da akayi mata baigama saketa ba, azaban sakinta da ƙarfi da yayi akan gado ne yasanyata farkawa, ahankali idanunta suka ɗan soma washewa saidai duk da haka bata gani sosai, idanuntane suka sauƙa akan fuskarsa, adaburce taja jikinta baya, duk da cewa bata gama dawowa hayyacinta ba, amma hakan bai hanata tsorata data gansa ba, kukan da takeyi ta tsayar, tare da sanya white teeth ɗinta ta datse lips ɗinta, alaman wani waje nata nayi mata zafi.
Sooraj dake tsaye ya harɗe hannuwa ganin yanda take ciccije baki, yasanya cikin husky voice ɗinsa yace da ita "Tashi!"
Da sauri tasoma yunƙurin sauƙa daga kan gadon, tana aje ƙafafunta aƙasa, wani irin jiri ya ɗebeta tare da ƙoƙarin kada ita, da sauri tasanya hannayenta duka biyu ta dafe bango, siririn kuka tasaki marar sauti, don masifar tsoronsa takeji, kallon jikinta yayi sannan ya kalli white bedsheet ɗin dake shimfuɗe kan bed ɗinsa, idanunsa yaɗan zaro tare dasanya hannu ya dafe goshinsa, aɗan harzuƙe yace.
"Bakida hankali ko? Ɗauka maza kije toilet kiwanke minshi yanzunnan, sannan kuma ki tabbatar da cewa yafita!!" yafaɗi maganar agadarance yana meyi mata nuni da bedsheet ɗin. Dubanta takai kan gadon, nan taga jini yaɗan ɓata tsakiyan bedsheet ɗin, wani irin faɗuwa gabanta yayi take taji wani masifaffen kunya ya rufeta. Kanta aƙasa ta sanya hannu tashiga jan bedsheet ɗin, duk da cewa dishi dishi idanunta suke gani sannan kuma babu wani ƙarfi ajikinta, hakan yasa komai takeyinshi cikin sanyi, ɗaukan bedsheet ɗin tayi tare da nufar wata ƙofa ta daban atunaninta nanne toilet, daga yanayin tafiyarta kaɗai ya isa sanar dakai cewa bata cikin hayyacinta, don har yanzu pain ɗin bai saketa ba.
Hannunsa yasanya ya damƙo ta, yanayin irin riƙon daya mata ba na wasaba ne, don har saida wani ƙashi dake cikin hannunta yayi ƙara, ƙafarsa yasanya ya daki ƙofar toilet ɗin, take ƙofar ta wangale, hankaɗata cikin toilet ɗin yayi tare da jawo ƙofar ya rufe. Zama yayi akan wata kujera tare da ɗaukan laptop ɗinsa yashiga dannawa, gaba ɗaya wani irin takaicinta yakeji.
Itakuwa Zieyaderh rasa inda zata sanya bedsheet ɗin tayi, wani irin bacci tare da jiri ne ke fusganta har bata iya ganin gabanta sosai, wani bucket ta ɗauka tare da sanya bedsheet ɗin aciki, ruwa ta zuba acikin bucket ɗin sannan tajefa sabulu, tsugunnawa tayi ta zubawa bucket ɗin ido, tama rasa ta ina zata fara, ganin tsayuwan ya isheta yasanya ta zauna daɓas aƙasan tiles tare da jingina bayanta da jikin bango, 5 minute kacal bacci ya ɗauketa awajen.
30 minute ya ɗauka azaune yana daddana laptop ɗinsa, kwata kwata shi yama manta da ita, ƙiran sallan magriba da akasomayi ne yasanyashi rufe laptop ɗin tare da miƙewa tsaye. Ahankali ya tura ƙofar toilet ɗin yashiga bakinsa ɗauke da addu'a. Hannayen rigarsa yasoma naɗewa tare da ƙarasawa gaban sink. Alwala yayi yana cikin wanke ƙafarsa na hagu idanunsa suka sauƙa akanta, saida yaji wani irin faɗuwar gaba domin shi sam yama manta da ita, cike da mamakin yanda tabaje tana sharar baccinta yashiga ƙare mata kallo, ga bucket agabanta sannan kuma ga bedsheet da sabulun wankansa nan acikin bucket ɗin, sabulun ya narke saboda yasha ruwa, itakuwa baccinta take tana sauƙe ajiyar zuciya. hankalinta akwance.
Ƙafansa yaɗan sanya ya zungureta, ko motsi batayi ba, wani murmushin da iyakansa leɓen baki yayi, gaban babban bathtube ɗin wankansa ya ƙarasa, ruwan sanyi ya tara har saida yacika bathtube ɗin, ƙarasowa gabanta yayi tare da ɗan durƙusawa ya ɗauketa, kamar wata ƴar tsana haka ya jefata acikin bathtube ɗin, aruɗe ta buɗe idanunta da sukayi luhu luhu sannan sukayi ja, wani irin sanyine ke ratsata. Juyawa yayi cikin halin ko inkula yafice daga cikin toilet ɗin, cikin daurayi ta fito daga cikin bathtube ɗin, gaba ɗaya kayan jikinta sun jiƙe jaƙab, ahankali take taka ƙafafunta da takejinsu kamar bazasu iya ɗaukanta ba. Bazata iya jurewa azabobin dayake gana mata ba, ganin bakowa acikin ɗakin yasanya tanufi hanyar fita, saɗaf saɗaf take tafiya kamar munafuka, ƙofar corridor ɗin ta buɗe ahankali, kanta tasako taɗan leƙa babban falon, kamar dai koda yaushe babu kowa acikin falon, da sauri ta fito ko tsaya rufe masa ƙofar batayi ba, daɗan sassarfa ta soma haura step ɗin dazai sadata da ɗakinta, tana tafiya tana waigen ƙofar ɗakin Ummu, kamar ɓarauniya haka ta buɗe ƙofar ɗakinnata ahankali tana shiga ta kulleshi gam, jiƙaƙƙun kayannata tasoma cirewa, sannan ta wuce bathroom. Adaddafe ta haɗawa kanta ruwan ɗumi, tayi wanka, har yanzu pain ɗin bai gama saketa ba, saima wani sabon fever daya sauƙa ajikinta, pad ta ɗauka ta kimtsa kanta sannan ta sanya wata doguwar riga me ɗan nauyi, domin kuwa sosai takejin sanyi, duk da cewa akwai yunwa sosai acikinta amma bata damu da neman abinciba, kan gado ta hau tare da jan blanket ta rufe gaba ɗaya jikinta, jikinta sai rawan sanyi yake, haka ta lumshe gajiyayyun idanunta da suketa ambaliya wajen fitar da hawaye.
Ganin har ƙarfe 7 Ummu bataji motsinta ba gashi yau bataga dawowanta ba yasanya hankalinta yaɗan tashi, saboda haka tafito don dubata.
Ahankali Ummu tatura kofar ɗakin tashigo bakinta ɗauke da sallama, ganin Zieyaderh nannaɗe acikin bargo yasanya Ummu ƙarasawa wajenta da sauri cike da kulawa tace.
"Zieyaderh lafiya kike kuwa?"
Zieyaderh da duk jikinta ke rawan sanyi, ta girgiza kanta cikin ciwo tace.
"Ummu zazzaɓine ke damuna!"
"Subahanallah shine kuma bakizo kin faɗamin ba? ba'a zama da ciwo ae, sam hakan ba kyau, kin maci abinci kuwa?" Ummu ta tambaya.
Kai Zieyaderh ta girgiza alaman.
"A'a"
Juyawa Ummu tayi tafice daga cikin ɗakin.
Mintuna kaɗan saiga Ummu ta dawo hannunta ɗauke da plate da kuma cup ɗin tea, kan bedside drawer ta aje plate da cup ɗin, bargon da zieyaderh ke lulluɓe dashi Ummu taɗan yaye tare da miƙar da ita zaune, cup ɗin tea ɗin Ummu ta bata, babu musu ta amsa, ahankali takeshan tea ɗin, sai da tasha kusan rabin cup ɗin, kafun Ummu ta amshi cup ɗin, plate ɗin soyayyen dankali da ƙwai wanda yaji sauce Ummu ta miƙo mata, nanma bata musaba ta amsa, ahankali takecin abincin duk batajin wani daɗin bakinta. Pain reliever Ummu ta bata tasha, sannan tace da ita ta kwanta tayi bacci, luf tayi akan gado tana maida numfashi ahankali, cikin wasu mintuna ƙalilan bacci ɓarawo yayi gaba da'ita.
Tunda Yafita sallan Magriba bashi yadawo gidanba sai 9 pm, direct toilet ɗinsa ya wuce, wanka yayi yafito ɗaure da towel a weast ɗinshi, sama sama yashafa body lotion, white trouser yasanya, tare da feshe jikinsa da turare me daɗin ƙamshi, Luf yayi akan gadonsa tare da cusa kansa cikin pillow, sanyin AC ne ke ratsa naked skin ɗinsa, ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya, ƙoƙarin faɗa da tunaninsa yake, sam bayason wani abu yasake damunsa, a ƴan kwanakinnan yana yawan jin zuciyarsa nayi masa zafi, sam bayason ciwonsa yayi ƙarfin da harsai kowa ya gane yana ɗauke da ciwon zuciya, akullum yanaji ajikinsa bashi da wani sauran farinciki daya ragemai, numfashi ya fitar ta bakinsa tare da lumshe idanunsa, duk yanda zuciyarsa taso da yayi tunani yaƙi bata daman hakan, yajima sosai kafun yasamu bacci ya ɗaukesa.
Washegari.
7:00 am daidai yagama shirya kansa cikin navy blue suit, Sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake, waya da key ɗin motarsa ne riƙe ahanunsa, cikin nutsuwa yake takunsa har yakai bakin ƙofar da zai fitar dashi daga cikin falon. Muryar Ummu da yaji abayansa yasanyashi tsayawa, juyowa yayi cikin ɗan rusunawa yace.
"Good morning Maaa"
Murmushin daya bayyana tsananin kamanninsu dashi Ummu tayi tare da cewa
"Morning how are you?"
"Am fine!" ya amsa ataƙaice yana me gyara wrist watch ɗinsa.
"Kasanar da Mas'oud Zieyaderh batajin daɗi, sannan yau bazata samu zuwa school ba ya kamata asanar" Ummu tayi maganar tana me ƙoƙarin zama akan kujera.
Kansa kawai ya jinjina alamar yaji kana yafice daga cikin falon.
Sosai tasha bacci sai 10 tafarka, Alhamdulillah ta ɗanji sauƙin jikinta, saidai kuma duk da haka bakinta babu daɗi, fitowarta daga wanka kenan, wani riga da sket ƴan kanti tasanya, sket ɗin irin rubber pencil ɗinnan ne yayinda rigan takasance me buɗaɗɗen kafaɗa, sosai kayan sukayi mata kyau ajiki, rubber hijab tasanya ajikinta, sannan tanufi ƙasa, ahankali take saƙƙowa daga kan steps ɗin, Ummu ce zaune afalon tasha ado cikin wani tsadadden lace maroon colour wanda yayi matuƙar amsar jikinta, gefe da ita wata matace wacce bazata wuce shekarun Ummun ba itama zaune ta caɓa ado, dagani basai anfaɗa ba kasan naira yazauna musu su dukansu. Cikin ladabi taƙaraso tare da durƙusawa ta gaidasu, fuska ɗauke da murmushi Ummu ta shafa kan Zieyaderh'n tare da cewa
"Kintashi? har baccin ya isa kenan, to ga can break fast akan dinning"
Murmushi Zieyaderh tayi tare da miƙewa tsaye tanufi dinning area. Hajiya Munah dake zaune tabi Zieyaderh da kallo, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da duban Ummu cikin yanayi naɗan mamaki tace.
"Hajiya Sulaimiyya ina kikasamo wannan kyakkyawar yarinyar kodai daga ƙasarku take ne?"
Murmushi Ummu tayi tare da cewa. "Ƙanwar Mas'oud ne abokin Sooraj, ai kindai san Mas'oud?"
Murmushi Hajiya Munah tayi tare da cewa "Ayya gaskiya balaifi yarinyar akwai hankali, uwa uba gata da kyau masha Allah!"
"Wannan halayyan nata shiyasa nakeson haɗata aure da Almustapha, nasan bazaiyi takaicin samunta amatsayin mata ba" Cewar Ummu wacce ke sipping pineapple juice ahankali.
Murmushi Hajiya Munah tayi tare dacewa "Gaskiya kinyi tunani me kyau, amma ae zai fi kyau ki haɗata da Sooraj, don aganina yafi Almustapha buƙatar mace akusa dashi"
Aje glass cup ɗin hanunta Ummu tayi tare da duban Hajiya Munah, wani murmushi me ciwo Ummu tayi cikin wani irin yanayi tace "Saikace bakisan waye Sooraj ba Hajiya Munah? hmmm Sooraj ɗin da baibzauna da matan da suka amsa sunansu mata ba ma, mene zaiyi da ƴar wannan ta tsitsiyar yarinyar da duka duka shekarunta basu wuce 18 to 19 ba"
Ajiyar zuciya Hajiya Munah ta sauƙe tare da cewa "Allah ya kyauta"
Da "Ameen" Ummu ta amsa daganan suka ci gaba da hiransu.
Zieyaderh kuwa zama tayi akan dinning tare da zubawa kanta pepper chicken soup, and chips, ahankali take tsakalan abincin don gaba ɗaya bawani daɗinsa takeji ba. Koda ta kammala ɗakinta takoma magungunanta tasha kana ta kwanta, tashar Mbc Action take kalla da haka har bacci ya ɗauketa.
Dayake magungunan da tasha suna da ƙarfi sosai hakan yasa ba ita ta tashiba sai wajen 5 na yamma, wanka tayi tare da sanya wata blue gown marar nauyi, yunwa takeji sosai hakan yasa tashiga ƙoƙarin zura hijab ɗinta don sauƙa ƙasa, jin anturo ƙofar ɗakinne yasanyata waigawa da sauri, ido biyu sukayi da Ummu wacce fuskarta ke ɗauke da murmushi.
"Barka da yammaci Ummu" tafaɗa murya asanyaye.
"Yauwa, dama wai me gadine yanzun yashigo yace wai wani yana sallama dake awaje, shine nace ko kunyi da wani zaizo wajenki ne?"
Idanu Zieyaderh ta zaro, lokaci guda ƙirjinta yashiga wani irin bugu, bakinta narawa tace "Ni....ni...kuma?"
"Eh haka dai yace, yanaga kin tsorata? Maza kije kiga ko wayene bakyau kabar mutum yana jira!" Ummu nagama faɗan haka ta juya ta fice daga cikin ɗakin.
Tsorone ya kama Zieyaderh adaburce ta sanya hijab dinta,kana ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice. Bataga Ummu afaloba kai tsaye saita nufi hanyar waje.
Koda tafito compound ɗin gidan idanunta tashiga warewa ko zata hango wanda akace na nemanta.
Tun fitowarta daga cikin falon yake kallonta, sosai tayi masa kyau acikin hijab ɗin dake jikinta, ashe sosai uniform ke ɓoye kyawunta. Kamar wanda akace tawaiga bayanta, hangosa tayi tsaye ajikin black car ɗinsa mercedes benz, sanye yake da riga da wando na bugaggiyar shadda Blue colour wanda tayi matuƙar yi masa kyau, mamakin ganinsane kwance acikin ranta amma saita sunkuyar da kanta ƙasa tare da nufar inda yake, murmushine kwance akan fuskarsa yana me kallonta harta ƙaraso. Cikin siririyar muryarta tayi masa sallama. Bai amsa sallamannata ba saima tsayawa kallonta da yayi, jin shiru bai amsa mata ba yasanya ta ɗago kanta ta dubeshi, idanunsune suka sarƙe cikin na juna, yanayin kallon daya mata yasanya ta sauƙar da idanunta ƙasa da sauri tana murmushi. Kansa yaɗan sunkuyo yana leƙa fuskarta, ganin haka yasa tasanya tafukan hannunta ta rufe fuskarta da sauri.
"Jiya nakasa bacci saboda bansan wani hali kike ciki ba, amma ganinki danayi yanzu yasa naji sanyi araina, basai ma kin faɗa ba nagane kinji sauƙi" Yafaɗi haka cike da tsantsar nuna kulawarsa gareta.
Har acikin ranta taji daɗin maganganunsa, domin tanada buƙatar kulawa sosae.
Ɗan matsowa kusa da ita yayi hartana iya jiyo sassanyan ƙamshin dake fita ajikinsa. Hannayensa yakai ya zame hannunta dake kan fuskarta.
Cikin wata irin sweetness voice yace "Kullum ƙara kyau kike, komai naki me kyaune, zanso kasancewa dake akoda yaushe sannan akowacce rana, please faɗamin kina sona?" yaƙare maganar yana me juya idanunsa akan kyakkyawar fuskarta.
Lumshe kyawawan idanunta tayi sosae zuciyarta ke bugawa, batasan me zatace masa ba, sannan kalamansa sunyi mata nauyi sosai, shikaɗai ya lura da mota ƙiran black range rover dake shigowa cikin gidan, kasancewar ita tabawa ƙofar gate baya, sannan gaba ɗaya tunaninta yatafi izuwa wani wajen daban. Ahankali taɗan buɗe idanunta tasaci kallonsa, abun da bata saniba shima kallonta yake sai kawai idanunsu ya sauƙa acikin na juna. Da sauri ta kawar da kanka gefe tare da sanya hijab ɗinta ta kare gefen fuskarta, idanunta ne suka sauƙa akan motar da ta shigo cikin gidan, wani irin masifaffen tsorone ya kamata take jikinta ya soma ɓari, lokaci guda jikinta yashiga fidda gumi, yana gama daidaita parking ɗin motar yafito, sanye yake da white t-shirt and combat army jeans, baƙaramin kyau yayi ba sosai kayan suka fitar da kwarjininsa. Cikin isa yake takunsa yana me dosowa cikin gida, saidai abun mamaki bai ɗago kai ya kallesu ba, bawai kuma don baigansuba tun shigowansa idanunsa sukayi masa tozali dasu, baya baya Zieyaderh keyi tana me ƙoƙarin ɓoyewa abayan Pharouk, tuni hawayen tsoronsa sun cika idanunta. Yayinda shikuma yake daɗa kusanto inda suke, fuskarsa sam babu alaman wasa ko murmushi akanta.
*Vote*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
#romance
*Chapter 32*
Cikin nutsuwa yake takunsa, tuni Zieyaderh ta koma bayan Pharouk ta ɓoye, rumtse idanunta tayi ƙam cike da fargaba. Ƙamshin turarensa da yacika hancinta ne yasanya jikinta ya soma rawa, saboda tasan zuwa yanzu yana gab dasu. Sam bai kallesuba balle yasa aransa cewa da gaske mutanene awajen, kansa tsaye ya wuce.
Aƙalla taɗauki kusan 5 minute ahaka, idanunta a rufe suke, jin shiru bataji motsin kowa ba yasanya tasoma buɗe idanunta ahankali, da beuty face ɗinsa tasomayin arba yayinda ya kafeta da sexy eyes ɗinsa, waro idanunta waje tayi tare da ɗanja da baya tashiga waige waige.
Murmushin daya bayyana dimples ɗinsa yayi, tare da ɗan kashe mata idanunsa ɗaya.
"Tsoron me kikeyi haka? ba Brother ɗinki bane?"
Kanta ta sunkuyar ƙasa tare da sauƙe ajiyar zuciya, duk da bata ganshi awajenba amma amatuƙar tsorace take domin batasan wani hukunci bane zai biyo baya.
"Meyasa kikejin tsoronsa? Ya hanaki kula kowa ne? Waye shi awajenki? Please tell me karkimin ƙarya!" yafaɗi haka yana me gyara tsayuwarsa tare da kafeta da idanunsa....
Sallama ɗauke aƙasan maƙoshinsa yashiga cikin falon, kai tsaye ɗakinsa ya nufa.
"SOORAJ!" Ummu dake zaune acikin falon taƙira sunanshi.
Cak ya tsaya da tafiyan, ahankali ya ɗan juyo ya kalleta.
Fuskarta babu alaman wasa batare da ta kalleshi ba tace "Badai ka ɗauki maganganun da Abbanka yayi maka amatsayin wasa ba?"
Shiru yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, baijin zai iya furta wata kalma awannan lokacin.
Sanin halinsa yasanya Ummu cigaba da cewa. "Kashiga hankalinka Sooraj, yakamata ace kasan mekakeyi, sai yaushene zaka fuskanci cewa ka girma? sai yaushe ne zaka nemawa kanka mutumci da daraja tahanyar yin aure? Ashe kafiso koda yaushe muta faɗa muna nanatawa duk akanka kai kaɗai? Idan kasake mahaifinka yayi mummunan fushi dakai to wallahi ba zakaga da kyau ba, sannan kuma gobe Almustapha zai dawo ka tura mota a ɗaukosa!" Ummu tafaɗi maganganun fuskarta babu alaman wasa.
Kansa kawai ya jinjina alaman yaji, ko 1 second baiƙara ba ya juya ya shige ɗakinsa.
Da kallo Ummu tabisa, tarasa hali irin na sooraj wani kalan alfano gareshi, ita tahaifesa amma batasan a ina yasamo wannan miskilancin nasa ba, sam itakam ba haka take ba.
Yana shiga cikin ɗakin ya murzawa ƙofarsa key, kayan jikinsa ya shiga ragewa, towel ya ɗaura ya shige bathroom, ruwa ya sakarwa kansa tare da sanya hannunsa na dama ya dafe bango, lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kansa ya ɗaga sama ruwa ya shiga dukan fuskarsa, saida numfashinsa yasoma barazanan ɗaukewa sannan ya sauƙar da kansa ƙasa, numfashi yashiga fitarwa akai akai, yana mejin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.
Ƙanƙance idanunsa yayi tare da lumshesu alokaci guda. "Zieyaderh!!" yaƙira sunanta in a cool voice ɗinsa.
Kanta ta ɗago tare da ɗan satan kallonsa, cikin muryarta me sanyi tace. "Na'am!"
"Inasonki!" Yafaɗa asanyaye yana me karyar da kansa gefe.
Kanta tajinjina tare da ɗan sakin murmushi, ƴan siraran laɓɓanta dake motsawa ahankali ya kalla.
Da alama maganace abakinta amma tanajin nauyin furtawa.
"Bakiji daɗin zuwana ba ko?"
Kanta ta girgiza alaman "A'a"
"To meyasa ba kya farinciki? Natafi ko kin gaji da ganina?" Ya tambaya yana me zura hannayensa acikin aljihun wandonsa.
Kanta ta girgiza cikin wani irin yanayi na shagwaɓa tace
"A'a nifa bance haka ba!"
Idanunsa ya lumshe har cikin ransa yaji salon shagwaɓan nata ya taɓasa, cikin ƙasa da murya yace "to faɗamin"
Tafukan hannayenta tasanya ta rufe fuskarta tana dariya.
"Pleaseeee mana baby faɗamin kina sona?"
Kasa jurewa tayi da sauri tajuya cikin yanayi na ɗan gudu gudu sauri sauri ta nufi cikin gida, murmushi Pharouk yayi tare da binta da kallo, wani irin sanyi yakeji acikin ransa, duk da cewa bata furta masa da bakinta ba, amma tabbas yasan bataƙinsa, don baiga ƙiyayyarsa acikin ƙwayan idanunta ba, motarsa ya buɗe ya shiga tare dayi mata key, mai gadi ne ya wangale masa gate, haka yabar cikin gidan zuciyarsa da tunani kala kala, gaba ɗaya ayar tambayarsa ya ɗigata ne akan SOORAJ.
Da ɗan gudunta tashigo cikin falon, tana rufe ƙofar ta saki wata ajiyar zuciya tare da sanya hannu ta dafe ƙirjinta, ƙoƙarin daidaita nutsuwarta tayi sannan takalli ɓangaren Sooraj, jin gabanta ya faɗi yasanya ta haura sama tana shiga cikin ɗakinta tafaɗa kan gado tare da lumshe idanunta, wani iri takeji azuciyarta, batasan dalilin da yasa takejin Pharouk awani ɓangare na zuciyarta ba, saidai kuma ako da yaushe kalamansa daɗi suke mata.
Luf yayi akan gadon tare da sake cusa kansa cikin pillow, gaba ɗaya ya rasa inda zai tsoma kansa yaji daɗi, ba yason yakai gayin abun dazai dameshi daga baya hakan yasa ya jure duk wata damuwarsa, sosai yakejin rauni azuciyarsa, musamman dangane da matsalarsa,,, yajima yana saƙawa da kuncewa acikin zuciyarsa kafun daga bisani bacci ɓarawo ya sace sa.
Washegari.
Alhamdulillah yau taji daɗin jikinta sosai hakan yasa ta shirya kanta tsab cikin shigar uniform ɗinta, hakanan takejin sanyi azuciyarta, ahankali take saƙƙowa daga kan step ɗin. Ƙaran takun takalmanta yasanya shi ɗago da kansa, dai dai lokacin itama ta ɗago kanta, idanunsune ya sauƙa cikin na juna, da sauri tayi ƙasa da kanta, shima kansa ya kawar tare da ci gaba da sipping coffee ɗinsa.
Sumu sumu haka taƙarasa sauƙowa daga kan steps ɗin, ahankali take tafiya harta ƙaraso inda yake, cikin wata irin murya me sanyi tace "Ina kwana!"
Bai amsata ba hakan yasa taɗan ɗago kanta ta kalleshi, ganin kamar baisan tana wajenba yasanya ta soma wasa da yatsun hannunta tana me murzasu, cikin yanayi naɗan shagwaɓa tace "Ina kwana Ya...yah?"
A yanzu kam ɗago kansa yayi ya kalleta saidai haryanzu bai amsa mata ba, jiki asanyaye ta gyara zaman school bag ɗinta sannan tanufi hanyar fita daga cikin falon.
Kamalu driver tasamu tsaye ajikin mota, da sauri ta ƙarasa tare da buɗe gidan baya ta zauna, tana ƙoƙarin aje school bag ɗinta, ya buɗe ƙofar motar ya shigo, ƙamshinsa take yacika ko ina dake cikin motar, mamakin shigowarsa cikin motar ne ɗauke akan fuskarta. School bag ɗinta ta rungume aƙirjinta tare da duƙunƙune jikinta waje ɗaya, tunda suka ɗauki titi yake ta faan latsa wayarsa, gaba ɗaya kwarjininsa ya cika mata ido, musamman yau da yasha ado cikin white and black suit, sai ya zamana yaƙara kyau. Aƙofar makarantar tasu Kamalu driver yayi parking motar, kamar marar gaskiya haka ta buɗe ƙofar motar tafice, ko taku uku batayiba taji ƙaran tashin motar, tana waiwayawa taga sunbar wajen, tana shiga cikin school ta haɗu dasu Nasmah, gaba ɗayansu hankalinsu atashe suke tambayarta yaya jikinta, sosai taji daɗin kulawarsu agareta da haka suka wuce class.
Ƙarfe Biyu daidai jirginsu ya sauƙa ababban airport ɗin dake cikin garin Abuja, wani kyakkyawan saurayi wanda aƙalla bazai haura 29 years ba, shike sauƙowa daga kan matattakalan jirgin Sanye yake da riga da wando na jeans masu kyaun gaske, kai tsaye baza'a ƙirasa da fari sol ba, sannan kuma shi ba baƙi bane, yana daɗan tsayi daidai misali sannan yana da faffaɗan jiki, daga yanayin shigarsa kaɗai zai sanar maka da ɗan gaye ne, fuskarsa ɗauke take da murmushi, Kamalu driver yana hangosa ya ƙarasa garesa da sauri cikin yanayi naɗan girmamawa yace "Ranka ya daɗe barka da zuwa"
Murmushi Alhmustapha yayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 38