Share this page
yace da Sir.Yusuf suje ya samo mata malamin lesson su fara tun yau, hakan kuwa akayi, Wani Teacher Abdallah Sir.Yusuf ya samo mata, wanda shine zaina koyar da ita lesson everyday, hatta ranan saturday da sunday zai na zuwa koya mata gida, domin biyanshi za'ana yi. abubuwa masu sauƙi Teacher Abdallah yafara koya mata, sam babu wani abu da ta fahimta tana dai jinsane kawai, duk kuwa yanda taso ta fahimci abubuwan sam ƙwaƙwalwarta takasa ɗauka. *** Zaune yake atamfatsetsen office ɗinsa, dagashi sai dogon wandon suit da kuma rigan parking shirt dake sanye ajikinsa, laptop ɗinsa ne agabansa yana shigar da wasu bayanai gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗin, turo ƙofar office ɗin akayi tare da shigowa, yaji motsin buɗe ƙofar amma sam baiɗago kansa ya kalli wanene ya shigo cikin office ɗin ba, yau sosai ƴan miskilancin nasa suke kusa. Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar tana kallonsa, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta, kallonsa kaɗai idan tayi yakan sanya mata nutsuwa, sosai take jin son sa acikin ranta, komai nasa yana burgeta tana son duk wani abu nasa, musamman yanayin yanda yakeyin adonsa, uwa uba kuma kyau da kwarjininsa dake tafiya da imanin duk wata mace da zatayi tozali dashi, cikin takunta nason ɗaukar hankalinsa tasoma takowa zuwa cikin office ɗin. Ƙaran takalman dake ƙafanta shiya fara sanar dashi wacce ta shigo cikin office ɗin nasa, jiyayi wani abu ya toshe masa maƙoshi, sam yatsani ganinta ko kaɗan bayaso tana raɓarsa, baisan ita wace irin mace bace wacce bata da zuciya ko kaɗan. Harta ƙaraso gaf da inda yake bai ɗago dakansa ya kalleta ba, cikin muryar shagwaɓa tace. "Barka da hutawa ranka ya daɗe" Kamar ma baisan da mutum a wajenba haka yayi banza da ita, bakinta da yaji pink lips stick taturo gaba. "Maiyasa kakemin hakane wai Raj? at least dai ko kallona yakamata ace kayi wajenka fa nazo" taƙare maganar tana ɗan bubbuga ƙafafunta, alaman shagwaɓa. Sai alokacin Sooraj ya ya ɗago kansa, saidai bai kalli inda take ba. "Kina da buƙatar wani abu ne?" yatambayeta ata ƙaice. "Kainake da buƙata Raj, wallahi kainake da buƙata, kafi kowa sanin yanda na damu dakai, maiyasa kake min haka ne? kadubeni Raj nacika mace irin wanda take girgiza zuciyoyin maza amma maiyasa bazaka dubeni ba? na amince ma kayi duk wani abun da kakeso dani amma maiyasa bazaka amince min ba!" taƙare maganar kamar zatayi kuka. Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da tashi ya ƙarasa gaban fridge, buɗewa yayi ya ɗauko ruwa mai sanyi, saida yasha sosai kafun ya sauƙe goran ƙasa, inda suit ɗinsa ke aje ya nufa, ɗaukan suit ɗin yayi ya saƙala ahanunsa, touch watch ɗin dake hanunsa ya duba, gani yayi akwai sauran time sosai kafun lokacin tashinsa ya cika, amma a yanda Aneesa tashigo masa office baya jin zai ƙara mintuna biyu acikin office ɗin. Wayarsa ya ɗauka haɗe da rufe laptop ɗinsa, juyawa yayi ya nufi ƙofar fita yana mai karkaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa. Da sauri Aneesa tasha gabansa, idanunta cike da ƙwalla tace "Please Raj ka tsaya atare dani, kasani kaine burina da kuma fatana, maiyasa kakemin haka ne?" hawayene suka gangaro daga cikin idanunta. Sai alokacin Sooraj ya ɗaura idanunsa akanta, kallonta yayi tun daga samanta har zuwa ƙasa. sannan yasaki wani killer smile. "Bani hanya na wuce" ya faɗa mata haka cikin halin ko inkula. "Bazan baka hanya ba Raj, harsai kamin abinda nakeso, please Raj kasani akullum da buƙatarka nake kwana, please kabani dama ko sau ɗaya ne." Ƙanƙance idanunsa yayi haɗe da tamke fuskarsa alokaci guda, cikin takaici yasanya hanunsa ya turata gefe, harsai da kanta ya bugu da bango, ƙofar office ɗin ya buɗe ya fice abunsa. Kuka Aneesa tasanya mai ɗauke da tsananin ɓakin ciki da takaici, takardun dake kan table ɗin office ɗin ta soma watsarwa a ƙasa tana kuka, ta tsani wannan banzan halin na Sooraj, a kullum baida wani buri da ya wuce ya wulaƙantata, mai tarasa wanda har zai tsaneta haka? alƙawari tayiwa kanta matuƙar ta rasa Sooraj to kowacce mace aduniya ma tarasashi domin bazata taɓa ɓari ya auri wata mace ba idan ba ita ba. Yana fita ya wuce wajen da yayi parking motarsa, sama sama yake amsa gaisuwar ma'aikatan dake gaidasa. Yana shiga cikin motar yayi mata key haɗe da ficewa daga cikin bank ɗin, direct wani hotel ya nufa...... Sosai Teacher Abdallah ya dage ya zuba mata lesson, lokacin da aka kaɗa ƙararrawan tashi ga duka ƴan makarantan dai dai lokacin shima ya dakata daga koyar da ita english lesson ɗin da ya keyi. Tana fitowa ƙofar ajin taga cincirondon ɗalibai maza da mata kowa na ƙoƙarin kama gabansa, ko ta ina acikin makarantar ɗalibaine, yayinda parking space ɗin makarantar kuwa ke cike da tarin motoci, har waje motoci ne a fake, duk wani ɗan makarantan dazaka kalla, kallo ɗaya zakayi masa ka hango alamun zaman naira ajikinsa, domin daga mata har mazan gaba ɗayansu ƴan gayu ne, da alama kuma kowa yanaji da kansa. Kamalu driver ta hango ya nufo inda take, wata ajiyar zuciya ta sauƙe, domin kuwa da har tafara tunanin yanda za ayi ta koma gida ita kaɗai. Gaba ɗaya yau tsananin farincikinta ya kasa ɓoyuwa, jinta take cikin farinciki. Haka ta koma gida zuciarta cike da jin daɗi. Wunin ranan gaba ɗaya haka tayishi cikin jin daɗi, duk yanda taso ganinsa tayi masa godiya abun yaci tura, domin kuwa ko motsinsa bata jiba *** *** *** Kullum sai Ziyada taje Lesson Kamalu driver ne ke kaita shine kuma ke dawo da ita, sosai ta kejin daɗin lesson ɗin nata, yanayin yanda ta dage tasanya son karatun acikin ranta shi ya ƙara sanya teacher Abdallah dagewa wajen ganin ya koyar da ita yanda zata fahimta, zuwa yanzu dai tana ɗan fahimtan abubuwa da kaɗan kaɗan, musamman ma wajen karatun Hausa da kuma rubuta shi, ta ɗan ƙware ta wajen wannan fanni, har ma idan taga abu zata iya karantashi, English ɗinne dai sai a hankali. Tun ɗazu aka tashe su saidai ga mamakinta yau Kamalu driver baizo ɗaukanta ba, gashi ɗaliban da suka rage acikin makarantar basu wuce ƴan tsiraru ba sam basu da wani yawa. Kalle kalle take tayi ko zata hango Kamalu driver amma babu shi babu alamarsa. Tsaye take a harabar makarantar, sanye take da doguwar riga da kuma Hijab, hannayenta nannaɗe suke akan ƙirjinta. Tun daga nesa yayi parking ɗin motar, jingina bayansa yayi da jikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, ahankali ya ware idanunsa haɗe da sauƙesu akanta, hakanan ya tsinci kansa da tsaida idanunsa akanta, kusan 2 minute ya ɗauka yana kallonta, mai da idanunsa yayi ya rufe, wani irin gajiya haɗe da kasala ne yaji sun sauƙar masa alokaci guda. Buɗe murfin motar yayi haɗe da zuro ƙafafunsa waje. Tun fitowarsa daga cikin motar idanun ɗaliban da ke wajen ya dawo kansa. Yanayin yanda yake taku cike da nutsuwa shine abun daya burgeta, har batasan sanda ta saki wani murmushi ba. Yana ƙarasowa inda take yace. "Kijirani a mota" baijirayi mai zata ce ba, yayi gaba abunsa, tana kallonsa ya shige cikin office ɗin principal. Juyawa ita tayi ta nufi inda ya aje motar tasa, jingina tayi da jikin motar tana jiran zuwansa. Baiwani jima ba ya dawo hanunsa riƙe da wata leda. Tunda suka ɗauki hanya babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu kowa da irin tunanin da yake saƙawa acikin zuciyarsa, yarda da abun da zuciarta ke gaya mata da tayi yasanya ta gyara zama cikin wata murya mai sanyi tace. "Nagode Yaya" Bai kalli inda take ba, bai kuma tanka mata ba, jin yayi shiru bai ce da ita komai ba yasa taji jikinta yayi sanyi. Saidai kuma kamar daga sama ta tsinkayi muryarsa. . "Waye yayan naki?" yafaɗa cikin tsare gida, batare daya kula sashin da take ba. Jin tambayar nasa yasa ta ɗago da kanta ta kallesa, tsintar kanta tayi da kasa ɗauke idanunta akansa, musamman ma data ga hankali da idanunshi ba akanta suke ba. "Kallon kuma fa?" yafaɗa adaidai sanda yake shiga wata kwana, da zata sadasu da gida. Da sauri ta janye idanunta daga kan nasa azuciyarta tanajin wani iri..... Monday. Yau ne zata fara shiga Class itama tayi karatu kamar yadda ko wanni ɗalibi keyi. Fitowarta daga wanka kenan. Ledan daya bata jiya da dare ta ɗauko, kayan shafa ne aciki sai kuma uniform da takalman makarantar ta. gefe kuwa wasu biscuit ne manya manya. Sama sama ta shafa mai ajikinta, babu powder bare wata uwa kwalli haka tabar fuskarta, uniform ɗinta wanda suke riga da wando ta sanya, wandon irin mai tsukakken ƙafannan ne amma ba har canba, yayinda tsawon rigan ta kasance har zuwa guiwarta, rigan milk colour ce, wandon kuwa shike da kalan maroon. Warware hijab ɗin makarantar tayi tana ƙare masa kallo, bashi da wani girma da kaɗan tsawonsa ya wuce cikinta. Tana sanya hijabin taje gaban makeken mirror'n dake ɗakin ta tsaya tana mai kallon kanta aciki, duk da cewa uniform ne amma sosai tayi kyau, white skin ɗinta yasake fitowa acikin maroon colour hijab ɗin, jinta tayi awani ta kure, sam batajin zata iya sakewa acikin mutane da irin wannan shigartata, sam bata saba ba,hakan yasa take ganinta wata daban. Zama tayi akan gado haɗe da ɗaukan safanta ta sanya, tana kammala sa safa ta zura takalminta me kama da toms, sosai takalmin yayi mata kyau gashi milk colour kalan riganta. Tunowa da maganan teacher Abdallah tayi inda yake ce mata "tazo da wuri kada ta sake ta makara" tashi tayi da sauri tafice daga cikin ɗakin. Tana fitowa falo daddaɗan ƙamshin turarensa da daɗinsa ke sanya taji wani bacci ya daki hancinta, hakan ya tabbatar mata da cewa bai jima da fita daga falon ba. Da saurinta itama ta fita daga cikin falon, tana fita ta hango ficewar motarsa daga gidan. Ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da nufan inda Kamalu ke tsaye, ba wani ɓata lokaci ta shiga suka ɗauki hanyar makarantar... Suna zuwa direct office ɗin teacher Abdallah ta nufa, don dama anan yace ta sameshi. Teacher Abdallah yana ganinta yasaki murmushi.. "Student!" yace da ita yana mai faɗaɗa fari'arsa. Murmushi kawai tayi masa haɗe dayin ƙasa da kanta. Yana kammala abubuwan da yakeyi ya ce suje ya nuna mata ajin da zata zauna, yana gaba tana biye dashi a baya. S.S 1 A shine abun da aka rubuta asaman ajin daɗan manyan baƙi, ɗalibaine waƴanda aƙalla zasu kai su 25 acikin ajin maza da mata, wasu suna zazzaune, yayinda wasu kuwa ke tsaye, wasu kamma akan desk suke zaune, suna ganin shigowar Teacher Abdallah ko wanne daga cikinsu ya shiga cikin nutsuwarsa, cike da girmamawa suka tashi tsaye dukansu suka gaidashi, amsa musu yayi haɗe da basu izinin zama. Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da cewa "Ga sabuwar ɗaliba nan nakawo muku, ina fata zaku karɓeta hanu bibbiyu, sannan idan bata gane abuba, inaso kuyi mata ƙarin haske" cikin harshen turanci yake maganan. Kallon Ziyada dake tsaye tama kasa ɗago kai ta kalli mutanen ajin yayi. "Ga wajen zamanki nan daga yau" yafaɗi haka yana maiyi mata nuni da wata kujera wacce take tsakiyan wasu ƴan mata... (Kuɗan ƙara haƙuri show ɗin yana gaba.) 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SOORAJ !!!* *Written By* Phatymasardauna *Dedicated To My Life (Sardauna)* *🌈Kainuwa Writers Association* {United we stand and succeed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} *https://ww.facebook.com/kainuwawritersassociation* *WATTPAD* @fatymasardauna #romance *Chapter 15* Cikin sanyinta ta nufi inda teacher Abdallah ya nuna mata. Ɗaya daga cikin ƴan matanne ta bita da wani irin kallo. teacher Abdallah yana ganin ta zauna ya fice daga cikin class ɗin bayan ya bata jakar makarantarta mai kyau. Gaba ɗaya jinta take atakure, kasancewar kusan gaba ɗaya rabin ƴan ajin idanunsu na kanta. "Sannu!" matashiyar budurwan dake gefenta ta faɗa, wacce aƙalla bazata wuce sa'an Ziyada'n ba. Sai alokacin Ziyada ta ɗago da kanta ta kalli wacce tayi mata maganan. murmushi tayi mata haɗe da cewa "Yauwa!" Murmushi itama yarinyar tayi tare da sake cewa. "Sunana Nasmah, kefa?" "Sunana Ziyada" Ziyada ta bata amsa tana mai ɗan faɗaɗa fari'an dake kan fuskarta. "Nice name!" Nasmah tafaɗa tana mai ɗaukan wani text book dake gabanta. Ɗan satan kallonta Ziyada tayi haɗe da yin murmushi, duk da cewa bata fahimci me Nasmah'n take nufi ba. Shiru Ziyada tayi bata sake cewa komai ba, yayinda suma ƴan matan sukayi shiru, Nasmah gaba ɗaya hankalinta nakan littafin dake hanunta, yayinda wacce ke gefen Ziyada ta ɓangaren damanta kuwa ko ƙala bata ce ba, sai dai time to time tana yawan kallon Ziyadan, maganane abakinta amma saboda halin jin kai irin na Shukhra ta kasa cewa komai. Wani malami ne ya shigo cikin ajin, dukansu ɗaliban suka tashi tsaye haɗe da gaidashi, sai da ya ɗan yi rubutu kaɗan akan white board ɗin da ke cikin ajin sannan ya basu izinin zama. Darasin Maths yake koyar musu cike da ƙwarewa, yayinda gaba ɗaya ƴan ajin suka bada attention ɗinsu gareshi, ciki kuwa hadda Ziyada, wacce ɗigo ɗaya na daga cikin abun da yake koyarwa bata fahimta ba, jinsa kawai take, tana kuma kallon yanda yake solving guestions. Tambaya yayi da sauri wacce ke gefen hagunta, wato Shukhra kenan ta ɗaga hanu, ya ta da ita ta bashi amsa, ƴan ajine suka hau yi mata tafi. Haka dai ya gama yi musu karatun ya fita abunsa. Yana fita baifi da mintuna 5 ba wani Malamin Biology ya kuma shigowa. Tunda malamin yafara darasi'n ta kafe allon da idanu, turanci yakeyi musu cike da ƙwarewa, sannan gaba ɗaya explanation ɗin da yayi musu da turanci yayi su, tunda ya shigo babu wani wanda yayi Hausa haka kuma shima ko A akalmar hausa bai ambata ba, kamar dai yanda wancan malamin maths ɗin yayi haka shima wannan ɗin, hakanne ma yasa sam bata fahimtan komai, domin kuwa turanci zalla suke basa ko ɗan surkawa da yaren da zata gane wato Hausa, lokacin da taga kowa ya ciro littafinsa yana rubutu itama sai ta buɗe jakarta wanda Teacher Abdallah ya bata, bayan littatafai dake cikin jakan hadda wasu tarin kayan snacks. Wani littafi ta ciro haɗe da pen. Dayake Teacher Abdallah ya ɗan koya mata rubutu a lesson ɗin da sukayi, hakan yasa rubutun bai wani bata wahala ba, sai dai kuma bata wani ƙware sosai ba. Gani tayi shima kafun ya fita saida yayiwa ƴan ajin tambayoyi, amma inda Allah Ya taimaketa ita bai tambayeta ba, kuma ko dama ya tambayeta saidai ta bashi amsar shiru. Yana fita wani malamin yakuma shigowa shima dai yaɗan jima yana musu darasi kafun ya fita. Yana fita aka buga ƙararrawan fita break, gani tayi da ɗai ɗai ɗaliban ajin ke ficewa zuwa waje, Shukra ce ta miƙe tafice daga cikin ajin. "Bazaki fita break bane?" Nasmah dake ƙoƙarin tashi tsaye ta tambayeta. Samun kanta tayi dayin murmushi haɗe da cewa. "Zan fita" Ganin kowa yana fita da jakarsa rataye akafaɗarsa ne, yasa itama ta ɗauki ƙatuwar jakarta ta rataya akafaɗanta, sai da ajin ya zama babu kowa acikinsa sannan ta miƙe ta nufi hanyar fita, awani babban barandan dake gaban ajin ta tsaya tana mai bin ɗaliban dake ta hada hadarsu a harabar makarantar da ido, kowani ɗalibi ka gani yana tare da abokinsa, yayinda wasu kuwa sukaiwa kansu mazauni akan kujerun da akayi da siminti wanda ke ƙarƙashin wasu bishiyoyi dake harabar makarantar, zama tayi akan makeken dakalin dake ƙofar ajinsu, yayinda ta zuro da ƙafafunta ƙasa, aranta wani daɗi takeji wai yau itace acikin makaranta makarantar ma ta boko, yunwa takeji na ƙwaƙulan cikinta don haka ta buɗe zip ɗin jakarta, wani cake dake cikin wani haɗaɗɗen leda ta ciro, tare da fito da goran peach ɗin dake cikin jakar, ɓare ledan cake ɗin tayi ta soma gutsura ahankali, gani take kamar idanun gaba ɗaya ƴan makarantar akanta suke, musamman ma da taga duk wanda yazo gilmawa ta inda take sai ya kalleta, tana cikin cin cake ɗinne, ta hango Nasmah da Shukrah na tahowa zasu dawo aji. Suna ƙarasowa gareta Shukra ta wuce yayinda Nasmah ta tsaya akusa da ita, cike da kulawa tace. "Me kikeyi ke ɗaya anan?" "Babu" Ziyada ta bata amsa tana karkaɗe Hijabinta da burbuɗin cake ya ɗan zuba akai. "Tashi muje Class, ko kin gane lecture's ɗin da akayi mana yau?" inji cewar Nasmah. Ɗago kanta tayi ta kalli Nasmah'n, samun kanta kawai tayi da girgiza mata kai alaman "A'a" "Okay to muje Class" Nasmah tafaɗa tana mai ƙoƙarin haura dakalin ƙofar ajin nasu. Tare suka shigo ajin ita da Nasmah, Nasmah ne ta ciro littafin Maths ɗinta, ahankali ta shiga yiwa Ziyada bayani dalla dalla da Hausa yanda zata fahimta, abun mamaki kuma sai gashi ta ɗan gane wasu abubuwan, tana kammala koya mata Maths ɗin ta ɗauko Biology shima ta koya mata, aikuwa harma tafi gane Biology'n akan Maths ɗin, kasancewar shi baida lissafi, bakamar Maths ba, har subject ɗin da akayi musu na ƙarshe kafun break wato Agric science saida Nasmah ta koyawa Ziyada, Alhamdulillah kuma ta fahimta sosai, akuma ɗan lokaci ƙanƙani wata ƴar shaƙuwa ta shigo tsakaninsu da Nasmah, duk abun da sukeyi Shukrah na jinsu, amma ƙala bata ce musu ba, saima wata fakekiyar wayarta data ciro ta soma latsawa. Suna kammala karatun aka dawo break. Sosai suke shan karatu basu suka samu kansu ba sai ƙarfe 1 na rana nan ma sallah aka fito dasu. Nasmah ne ta jata suka nufi masallacin dake cikin school ɗin, Nasmah saida ta jirata tayi alwala sannan itama tayi, atare suka shiga cikin masallacin nan suka iske Shukrah tana sallah, gefe suma suka samu suka tada nasu sallan, suna idarwa Nasmah ta sake kama hanun Ziyada suka fito daga cikin masallacin. Aji suka koma kowa yaciro abincinsa yafara ci, ita dai da bata da wani abinci sai snacks shi ta ciro ta ɗanci kaɗan, Nasmah ce tayi mata tayi'n soyayyen doya da naman kaza wanda tazo da shi, amma sam taƙi ci babu yanda Nasmah batayiba akan taci amma taƙi dolenta ta haƙura. 5:00 pm daidai shine lokacin tashinsu akowacce rana, yauma biyar na cika dai dai aka kaɗa ƙararrawan tashi. Tare da Nasmah suka fito tana fitowa ta hango Kamalu driver tsaye ajikin mota, sallama tayiwa Nasmah da Shukrah sannan tanufi inda yake tsaye. Tana shiga yaja motar suka bar haraban makarantar. Tana shiga cikin falon, daddaɗan ƙamshin turare ya daki hancinta, ko ina na falon a gyare yake tsab. Ƙofar ɗakinsa ta kalla, sannan ta wuce ɗakinta. Tana shiga ta soma cire kayan uniform ɗinta, ban ɗaki ta shiga ta yi wanka, yanzu babu abun da bata iya amfani dashi ba na cikin banɗakin. Tana fitowa awanka ta sanya kaya haɗe da faɗawa kan gado, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, wani irin gajiya haɗi da bacci takeji, basaban ba, idanunta ne suka sauƙa akan wani ƙaton akwati dake aje cikin ɗakin. Tashi tayi ta nufi inda akwatin yake tana buɗewa taga kayane shaƙe acikin akwatin, kama daga kan dogin riguna riga da sket ƴan kanti, da kuma dogin wanduna, murmushi tayi haɗe da lumshe idanunta, batasan da wani baki zata gode masa ba, amma tabbas Ya Zama MADUBI acikin rayuwarta, da sannu itama zata haskaka ta zama kamar wata TAURARUWA. Komawa tayi ta kwanta cike da ɗokin sababbin kayan da tayi masu yawa. Jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne yasa tatashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala bata tashi akan sallayan ba saida ta yi sallan Isha, tana gama naɗe sallayan da tayi sallah akai, ta faɗa kan gado, wani irin baccine ke fusganta, tana kwanciya kuwa bacci ya ɗauketa ko lufayan dake jikinta bata cire ba. Duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa abun yaci tura, kwance yake akan makeken Royal bed ɗinsa wanda yaji lallausan bedsheet. Idanunsa dake alumshe ya buɗe haɗe da sanya hanu ya dafe kansa dake wani irin sara masa kamar zai faɗo ƙasa haka yakeji. Gaba ɗaya duniyar bata yi mashi daɗi, ƙuna yakeji acikin zuciyarsa abubuwa da yawa ne suka haɗe masa, hanunsa na dama ya sanya akan cikinsa wanda ke ɗauke da manya manyan 6 packs, ahankali ya ke murza fatan cikinsa, idanunsa gaba ɗaya sun kaɗa sunyi jajur dasu. Cigaba yayi da murza fatar cikinsa da ɗan ƙarfi haɗe da cije laɓɓansa. "Sai yaushe ne zai zama mutum me cikakken lafiya? sai yaushene zai san cewa shima Namiji ne? yaushe ne damuwarsa zata gushe? yaushe ne zaiyi bacci acikin farinciki da nishaɗi? yaushene zaiji abun da yake buri da fatan ji watarana? Abun tambayar aransa shine yaushe ne yazama haka? yaushe ne kuma zaici wannan jarabawar tasa mai wahala?" waƴannan tambayoyin su yakeyiwa kansa akullum, sau tari yakan cire rai amma yasan Allah na sane dashi idan yana darai watarana zai dace, amma kuma yaushene wannan ranan zata zo? shine abun da baisani ba, tashi yayi ya zauna still hanunsa nakan fatar cikinsa yana murzawa. Ƙafafunsa ya zuro ƙasa tare da sauƙowa daga kan gadon, gaban window ɗinsa ya nufa, tsayawa yayi ajikin window'n haɗe da sanya hanu ya yaye labulen window'n, buɗe glass ɗin window'n yayi take wata iska mai daɗi ta bugi fuskarsa, lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu alokaci guda, ɗaga kansa yayi yana kallon sararin samaniya, farin wata ne ya haske ko ina da ina. Ahankali ya kejin nutsuwa na sauƙar masa, sosai yakejin daɗin ni'imar dake hurawa, yajima tsaye ajikin window'n kafun ya dawo cikin ɗakin. Kwanciya yayi akan gado yayinda ƙafafunsa ke ƙasa, ahaka wani bacci ya ɗaukesa, dagani kasan bajin daɗin baccin yake ba. ** ** Tun 7 ta kammala duk wani shirinta, saboda ta fahimci ba aso azo late a makarantar, duk yanda ta buga sammako wajen fita, amma bata iske shi afalo ba, saidai ta iske daddaɗan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa, haka tashiga mota Kamalu driver yaja motar suka tafi batare da tayi tozali dashi ba. Kamalu driver na tsaida motar ta ɗauki jakanta haɗe da soma ƙoƙarin buɗe murfin motar. "Ga wannan Oga yace abaki" Kamalu driver ya tsaidata tahanyar faɗan haka, yana mai ciro kuɗi acikin aljihunsa. Kallon kuɗin tayi sannan ta kalli Kamalu driver. "Ni kuma mai zanyi dasu to?" ta tambaya cike da mamaki. "Haka dai yace abaki, hala ko kuɗin taran ki ne" Kamalu driver yafaɗi haka yana me ƙara miƙo mata kuɗin. Cikin sanyin jiki tasa hannu ta amshi kuɗin, sannan tafice daga cikin motar aranta tana mai cewa da zaran takoma gida zata tambayeshi, hala ko wani abu ya keso tasayomasa da kuɗin. Yau ta riga Shukra da Nasmah zuwa saboda haka ita kaɗai ta zauna tayi jigum, ba wani jimawa sosai sai gasu sunzo atare, ga mamakinta yau fuskar Shukra asake take babu tsumewa kamar na jiya, Nasmah na ganinta ta saki murmushi haɗe da ƙarasowa ta zauna akusa da ita. "Yau munyi late kin rigamu zuwa" Inji cewar Nasmah dake ƙoƙarin sauƙe jakarta dake kafaɗarta. Ta buɗe baki zatayiwa Nasmah magana kenan malami ya shigo ajin. Sai bayan yafita ne suka ɗanyi taɗi

Chapter 7 of 38