Share this page
daga gurɓacewa, bazata taɓa son wani abu ya sameshi ba. A Emergency Room kuwa sosai likitoti suka duƙufa akansa wajen basa taimakon gaggawa, da ƙyar suka samu suka shawo kan al'amuran, alokacin da suka gano matsalar kuwa baƙaramin mamaki sukayi ba, domin sun gano cewa allura akai masa ko yayiwa kansa, wacce take da mugun haɗari sannan tana da ƙarfin gaske, aƙalla idan a kayiwa mutum ita zai iya kaiwa sati ɗaya batare daya san inda hankalinsa yake ba, koda kuwa ya farfaɗo ba zai dawo cikin hayyacinsa da wuri ba, sai dai ma shi Sooraj ɗin yaci sa'a jininsa na da ƙarfi sosai, amma duk da haka ƙarfin alluran yayi tasiri acikin jikinsa. Drip suka ɗaura masa sannan suka wuce dashi wani ɗaki na musamman, kasancewar kusan duka likitotin asibitin sun sansa, don yana zuwa lokaci zuwa lokaci yana dubawa koda akwai waƴanda suke da buƙatar taimako shi yakan zuba dukiyarsa ya taimaka musu. Dr.Haisam wanda yake ɗaya daga cikin manya manyan likitotin asibitin ya kalli Kamalu driver, dawo da kallonsa ya kuma yi ga Ziyada wacce har yanzu kuka take.... "Tare kuke ne?" Dr.Haisam ya tambayi Kamalu yana maiyi masa nuni da gefen da Ziyada'n ke zaune. "Eh ƙanwar Oga ce" Kamalu driver yafaɗi haka, don ya rasa ma mai zai ce. Kai Dr.Haisam yajinjina alaman gamsuwa, kallon Ziyada ya kumayi wanda itama a yanzu kallonsa takeyi. "Biyoni Office" yace da ita yana mai nufar hanyar office ɗinsa. Kallon Kamalu driver Ziyada tayi, kansa ya jinjina mata alamar ta bi Dr. Haisam ɗin, jiki a sanyaye tabi bayanshi. Zama Dr.Haisam yayi akan kujera haɗe da yi mata nuni da wata kujera dage aje gabansa yace "Ta zauna" A ɗaɗare ta zauna akan kujeran tana mai murje ƴan yatsun hanunta. "Ya Sunanki?" Dr.Haisam ya tambayeta. Murya araunane tace "ZIYADA" Kansa yajinjina haɗe da maimaita sunan ZIYADA acikin ransa. "Ki kwantar da hankalinki Ziyada, ki daina kuka kinji, yayanki zai warke insha Allah, Ina iyayenku suke? don yana da kyau na tattauna matsalan dake damunsa dasu" Ɗago jajayen idanunta tayi ta kallesa, murya asanyaye tace. "Basanan sunyi tafiya!" ita kanta batasan ya akayi taji ta furta wannan ƙaryan ba, sai dai kuma bata da wani abun da zata ce masa ne wanda ya wuce hakan. Ajiyar zuciya Dr.Haisam yayi haɗe da cewa. "Shikenan ba damuwa, amma a wannan yanayin yayanki yana tsananin buƙatar kulawarki, bazance miki zai farfaɗo a yau ko gobe ba, wannan na Allah Ne, amma ki zauna atare dashi ki basa kulawa har zuwa farfaɗowansa, idan drip ɗin da aka sanya masa ya ƙare kizo ki ƙirani saina cire masa ko" Kanta kawai ta kaɗa masa alamar "To" "Tashi kije" yace da ita yana mai ƙoƙarin haɗa wasu takardun dake kan table ɗin gabansa. Tana fitowa Kamalu driver ya tambayeta wai me Dr.Haisam ɗin yace mata. "Babu" kawai ta basa amsa ataƙaice, wata Nurse ce tazo garesu, kallon Kamalu driver tayi haɗe da cewa "Oga yace katafi ƙanwartasa sai ta kula dashi" kai Kamalu driver ya jinjina alaman gansuwa, sannan nurse ɗin ta wuce gaba Ziyada ta rufa mata baya. Nurse ɗin na nuna mata ɗakin da yake kwance ta juya tayi tafiyarta. Ahankali tatura ƙofar ɗakin ta shiga. Yana kwance akan gadon asibitin, kansa da jikinsa duk suna fuskantar sama, yayinda idanunsa kuwa suke a rufe ruf, wata na'ura ne mai kamar computer agefensa, yayinda aka saƙala masa wata ƴar waya da tafito daga jikin na'urar a ƙirjinsa. Wasu hawayene taji sun taru sun cika idanunta, wani irin tausayinsa ne mai ƙarfi ya ɗarsu acikin zuciyarta. Ahankali ta taka har zuwa jikin gadon, kan kujeran dake kusa da gadonnasa ta zauna, a kusa da inda hanunsa yake ta ƙifa kanta. Kusan 30 minute ta ɗauka tana zaune a wajen, a hankali ta ɗago kanta haɗe da duban ledan ruwan da aka ɗaura masa, gani tayi saura kaɗan ruwan ya ƙare. Dawo da kallonta tayi zuwa jikinta, kwata kwata ta manta da shigan dake jikinta, baƙar doguwar riga ce ajikinta mai dogon hannu, sai kuma mayafin rigan dake ɗaure akanta, warware mayafin rigan tayi da yake yana da girma ta rufe jikinta dashi, fita daga cikin ɗakin tayi, da ƙyar ta iya gane office ɗin Dr.Haisam, yana zaune tashigo tasanar masa cewa ruwan yakusa ƙarewa.. Cire masa ledan ruwan Dr.Haisam yayi kana ya barsa sai zuwa anjima asake sa wani. Dr. Haisam na fita daga cikin ɗakin tasoma jin ƙiran sallan Magriba, wanda yake fitowa daga cikin masallacin dake gefen asibitin. Kallon ƙofar da Dr.Haisam yace mata nanne banɗaki tayi, ahankali tatura ƙofar tashiga, banɗaki ne mai kyau da tsafta, gaban sink taje ta ɗauro alwala sannan ta fito. Tsayawa tayi tana nazarin yanda za'ayi tayi sallah babu sallaya, duk da cewa rayuwar rashin ƴanci da kuma ƙauyanci tayi, hakan baisa ta zamo mace mai wasa da sallah ba, duk da bawani ilimi take dashi akan addini ba, amma tana kyautata zaton wajen bazaiyi sallah ba idan har ba a shumfuɗa sallaya ba, kallonsa tayi yananan dai a yanda yake, ahankali ta ƙarasa jikin gadon, aƙalla ta ɗauki sama da 7 minute tana kallonsa, jitayi duk ƙwalla suncika idanunta, buɗe ƙofar ɗakin tayi ta fice. Tana fita daga ɗakin taga wata nurse zata wuce, da sauri ta ƙarasa gareta haɗe da gaisheta. Amsa mata gaisuwar nurse ɗin tayi tana mai ƙare mata kallo. "dama Sallah zanyi shine kuma banda sallaya ko zaki ɗan aramin" Ziyada ta tambayi nurse ɗin tana mai sanya mata fuskar tausayi. "Biyoni muje ki amsa" nurse ɗin tafaɗi haka tana mai ci gaba da tafiyarta. Sallaya hadda Hijab nurse ɗin ta bata, ta kumace ta riƙe a wajenta zuwa gobe, godia Ziyada tayi mata sannan tadawo ɗaki, shumfuɗa sallayan tayi haɗe da tada Sallah. Sosai ta jima a sujjadanta na raka'an ƙarshe, addu'a tayi sosai akan Allah yabawa Mai taimakonta lafiya. "Mai Taimako" shine sunan da Ziyada ta raɗawa Sooraj acikin zuciyarta. Tananan zaune akan sallayan har aka ƙira sallan Isha.. Shima a sujjadan ƙarshe saida tajima tana addu'a kafun ta ɗago. Shiru haka ta zauna akan sallayan haɗe da jingina bayanta ajikin bango. Har ƙarfe 9 Ziyada na zaune agefen gadon, sannu ahankali yunwa ke ƙwaƙulan cikinta, gyan gyaɗi ta fara mintuna kaɗan bacci ya ɗauketa. Cikin dare Sanyin AC ya dameta, tashi tayi ta lulluɓe jikinta sannan ta koma bacci. Washe Gari. Tunda ta tashi da asuba tayi sallah, wani bacci yasake ɗaukanta, ba ita ta farka ba sai wajen ƙarfe 8 na safiya. Ban ɗaki ta wuce taje ta wanko fuskarta, tana zama akan kujera Dr.Haisam ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, gaishesa tayi cike da girmamaw, fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata. Checking ɗin Sooraj ya sakeyi, yaji daɗin ganin komai Normal kuma zai iya farfaɗowa ako wani lokaci. Hannayenta ta ɗaura akan kumatun ta haɗe da kafesa da manyan manyan idanunta, kyakkyawar fuskarsa take kallo, babu wani abu dayafi saurin ɗaukar hankali akan fuskarsa kamar yalwataccen sajen sa, wanda yake baƙi siɗik, ga zara zaran eye lashes ɗinsa da suke a mimmiƙe, sosai suka ƙarawa fuskartasa kyau, hakan yasa bata taɓa gajiyawa da kallonsa... Wasa Wasa har ƙarfe 5 na yamma Sooraj bai farfaɗo ba, haka Ziyada ke zaune awajensa, batare da ta ci wani abu wai sunansa abinci ba, ruwa kawai take ta zubawa cikinta. Tun yunwar na damunta har tazo ta daina ji, yanzu bata da wani buri daya wuce taga Mai Taimakonta ya buɗe idanunsa. 9:30 pm Babbar yatsan ƙafarsa ta dama ne ta soma motsawa sai kuma yatsun hanunsa, sannu sannu bugun zuciyarsa ta dai dai ta, yayinda cikin sakannin da basu wuce huɗu ba brain ɗinsa ta soma aikin. Ahankali ya soma buɗe idanunsa, da kaɗan kaɗan yake ware idanun nasa hakan yasa ya soma ganin komai dishi dishi. Sannu ahankali idanun nasa suka washe, kallon saman ɗakin daya gansa aciki ya soma yi. Sake ɗan lumshe idanunsa yayi, komai daya faru ya dawo cikin kansa, ɗan yunƙurawa yayi ya tashi zaune haɗe da jingina bayansa da pillow, juyo da kansa yayi zuwa gefen damansa, idanunsa suka sauƙa akanta, tana zaune akan sallaya ta jingina bayanta da kanta a jikin gadon da yake, bacci takeyi cikin yanayi na takura, da dukkan alamu bata shiryawa baccin ba ya ɗauketa, domin kuwa hadda goran ruwa riƙe ahanunta, ƙurawa fuskarta idanu yayi, hango wasu zanen busassun hawaye yayi kwance akan fuskarta, kallon yanda ɗan ƙaramin bakinta ke ɗan buɗe yayi. Janye idanunsa yayi daga kanta, haɗe da ɗan tattaro ragowan ƙarfin daya rage masa ya sauƙo daga kan gadon. Ƙofar da yake tunanin nanne toilet ya nufa, yana shiga ya soma rage kayan jikinsa. Kunna shower yayi ya tsaya ruwa ya dake shi sosai. Dogon wandonsa kawai ya maida batare da ya sanya rigar shi ba ya fito daga cikin toilet ɗin. Zama yayi abakin gadon haɗe da sanya hanu ya dafe kanshi dake yi masa ciwo sosai, hakanan yakejin shi wani iri, gaba ɗaya babu wani isashshen kuzari ajikinsa, yasan hakan kuma duk yana daga cikin sharrin Alluran da yayiwa kan shi ne. Kallon shi ya kuma maidawa zuwa gareta, har yanzu tananan tana wahalallen baccin daya ɗauketa, gaba ɗaya jikinta a tukuikuye yake da Hijab, tashi yayi ya ƙarasa jikin window'n ɗakin, hanu yasa yaɗan buɗe labulen window'n kaɗan, gani yayi gaba ɗaya duhu ya mamaye sararin samaniya, hanu yakai yashafi aljihun wandon dake jikin shi, atunanin shi wayar shi na tare da shi. sai dai kuma saɓanin haka yaji shi wayam, ɗan kalle kalle yasomayi acikin ɗakin ko zai hangota amma baiganta ba, komawa yayi ya zauna akan gadon yana mai lumshe idanunsa, saboda wani juwa da yaji yana neman ka da shi. Aƙalla yakusan mintuna goma idanunshi suna lumshe, jin da yayi juwan yasoma lafawa ne yasanya ya tashi tsaye, inda take zaune ya nufa, tsayawa yayi akanta ya kasa ta ɓuka komai. Ɗan ranƙwafowa yayi ya ɗagota caɗak, kan gadon da aka ajiye musamman don taya majinyaci kwana ya ɗaurata, a hankali ya zare hijab ɗin dake jikinta ya ajiye mata shi agefe. Ziyada da baccinta yayi nisa sam batasan meke faruwa ba, saima ƙara gyara kwanciarta da tayi, sakamakon jin ta samu sauyin makwanci. Komawa kan nashi gadon yayi ya kwanta, lumshe idanunsa yayi bawai kuma don yanajin bacci ba saidan kawai babu wadataccen ƙarfi ajikinshi.. Yatsun ƙafanta ya ƙurawa ido, azahirin gaskiya yatsunnata yake kallo, amma kuma hankali da tunaninsa ba agareta suke ba, yayi nisa acikin wani tunanin daban, baiso ace ya biyewa zuciyarsa ba, baiso ace ya kasa haƙurin ɗaukar ƙaddaransa ba, duk da cewa shiɗin mai raunine amma yana fatan dacewa anan gaba, saidai aduk sanda yayi wannan tunanin sai wata zuciyar ta gargaɗesa da kada ya yaudari kansa, dolensa haka yake haƙura ya watsar da tunnin acikin ransa. Buɗe gajiyayyun idanunta tayi, ganin haske tarwal acikin ɗakin yasa ta tashi aɗan zabure, kallonta takai wajen window gani tayi har hasken rana yasoma bayyana ta jikin window'n. Da sauri ta zuro ƙafafunta daga kan gadon, dai dai lokacinne kuma idanunta suka sauƙa akansa, yana kwance ya bata baya. Sake waro idanunta tayi haɗe da mutsutstsukasu atunaninta ko gigin bacci takeyi ganinsa da tayi babu riga, bayan koda zata kwanta tabarshine sanye da riga ajikinsa. "Kodai likita ne yazo ya cire masa riga'n tana bacci bata sani ba?" tambayar da tayiwa kanta kenan. Ahankali ta sauƙo daga kan gadon, cikin sanɗa tataka harzuwa inda yake kwance. Kanta ta ɗaura ajin gadonnasa, lokaci guda idanunta suka kawo hawaye murya araunane tace. "Mai Taimakona Allah yabaka lafiya, tausayinka nakeji sosai, banso wani abu ya sameka!" taƙare maganar daidai lokacin da hawayen dake cikin idanunta suka samu daman gangaro zuwa kan fuskarta, daidai lokacinne kuma shima da tun tashinta zuwa yanzu yanajin abun da takeyi ya ɗan buɗe idanunsa kaɗan.... *Vote Me On Wattpad* @fatymasardauna 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SOORAJ !!!* *Written By* Phatymasardauna *Dedicated To My Life (Sardauna)* *🌈Kainuwa Writers Association* *WATTPAD* @fatymasardauna #romance *Chapter 13* Wani numfashi mai ɗumi ya fesar daga bakinsa, haɗe da maida idanunsa ya rufe, kalamanta ne suka shiga yi masa yawo acikin kunnuwansa, ji yayi tsikar jikinsa na tashi, hakanne ma yasa ya kasa yin koda kyakkyawan motsi ne. Ban ɗaki ta wuce ta je ta ɗauro alwala, sam bata san ya akayi bacci ya ɗauketa ba, taso ace bata makara ba, kasancewar yanzu har hasken rana ya bayyana. Tana idar da sallan ta gyara zamanta akan sallayan, sai alokacinne ta tuno da cewa aƙasa ta kwanta ba akan gado ba, "To kenan ya akayi ta koma kan gado?" tambayar da tayiwa kanta kenan, ƙaran buɗe ƙofar ɗakin da akayi ne ya katse mata tunaninta. Dr.Haisam ne yashigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa tayi haɗe da gaidashi. Fuska asake shima ya amsa mata gaisuwar. Ƙarasawa gaban gadon da Sooraj ɗin ke kwance yayi. "Ya jikinna ka dai?" Dr.Haisam ya tambayi Sooraj wanda har yanzu bai sauya kwancia daga juya bayan da yayi ba. Ziyada nashirin ce da Dr.Haisam bai farfaɗo ba, taji muryarsa ta doki dodon kunnenta. "Da sauƙi!" Sooraj ya bashi amsa ataƙaice, sai alokacin ya juyo ya fuskanci Dr.Haisam ɗin. "Masha Allah dama kullum haka mukeso, yanzu babu wani inda yake maka ciwo?" Dr.Haisam yatambayeshi cike da kulawa. "Babu" ya bashi amsa ataƙaice. "Masha Allah zamu baka sallama zuwa anjima, amma yana da kyau ka riƙa kulawa da lafiyarka, kasan fa lafiya itace komai arayuwa, sai da itane mutum yake sanin daɗin rayuwa, saboda haka kakiyaye abun da zai cutar dakai!" Kai kawai Sooraj ya jinjina alamar yaji, sam baison magana mai tsawo. Kallon Ziyada dake zaune tana kallonsu Dr.Haisam yayi. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace. "Congrat ƴar ƙaramar ƙanwa, da alama brother ɗinki ya samu lafiya" Murmushin daya bayyana kyawun fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa, hakanan taji wani irin sanyi acikin ƙirjinta. Dr.Haisam na fita ta ɗago da kanta takai dubanta ga Sooraj wanda yake ta murza fatan hanunsa, kallon yanda jijiyoyin jikinsa suka fito sukayi raɗa raɗa tayi, gani tayi ya sanya haƙoransa ya danne lip ɗinsa na ƙasa, tamkar wani wanda yakejin wata azaba ta daban, tashi tayi daga kan sallayan cikin sanɗa tashiga takowa zuwa inda yake. Muryarta na rawa tace "YAH...YAH!!" ita kanta batasan ya akayi ta ƙirasa da wannan sunan ba. Cak ya tsaya daga murza hanunnasa da ya keyi haɗe da buɗe idanunsa da suka zama jajur dasu, ɗago da kansa yayi ya kalleta. Sai da taji gabanta ya faɗi alokacin da idanunsa suka sauƙa acikin nata idanun, bakomai ya tsorata ta ba kamar yanda taga idanunsa sun rikiɗe daga farare zuwa jajaye. Ko second biyu bai ɗauka ya na kallonta ba ya sauƙe idanunsa ƙasa. Ƙwalla ne suka cika idanunta, murya araunane tace "Dama.... dama.. Bansani ba ne ko kanajin yunwa" tafaɗi haka tana mai murza ƴan yatsun hanunta. "Miƙomin rigana" yafaɗi haka batare daya ɗago kansa ko ya tanka mata maganan da takeyi ba, babu musu ta ɗauko rigan nasa tazo ta miƙa masa, tashi tsaye yayi daga kan gadon haɗe da sanya rigarsa, Kallon ƙafansa ƴayi yaga ko takalmi baida shi. Hanu yasa ya dafe goshinsa. "Ina wayata?" yayi mata tambayar yana mai tsareta da idanunsa. "Wayanka?" tafaɗa tana mai rarraba idanunta. Yanayin yanda tayi maganar ne yasashi ƙanƙance idanunsa haɗe da ware su alokaci guda. "Wa ya kowani nan?" ya tambayeta yana mai ƙoƙarin maƙala aninayen dake gaban rigarsa. "Ni da Kamalu driver ne" tabashi amsa tana mai wasa da ƴan yatsun hanunta. Ɗauke kansa kawai yayi daga kallonta, dai dai lokacin Dr.Haisam yashigo cikin ɗakin. Sooraj na ganinsa yace "Ko zan iya samun aron waya?" Murmushi Dr.Haisam yayi haɗe da cewa "Eh" ciro wayarsa yayi ya miƙawa Sooraj ɗin. Number'n Khalid yasanya acikin wayan Dr.Haisam haɗe dayin dialing. Ringing biyu Khalid yaɗauki ƙiran, "Ina Mahfuz Specialist Hospital, kazo kayi dropping ɗina a gida" Baijira mai Khalid ɗin zaice ba ya kashe wayan, miƙawa Dr.Haisam wayar yayi. Takardan sallamansa Dr.Haisam ya miƙa masa. Mintuna kaɗan Khalid ya iso cikin asibitin. Yana shigowa ɗakin, cikin tashin hankali ya kalli Sooraj cike da kulawa yace "Raj maiyasa meka haka, harda zuwa asibiti?" Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da cewa " stress ne kawai, muje ko" yaƙare maganar cikin yanayi na ƙosawa. Motar Khalid suka shiga, suna zaune agaba ita kuma tana zaune agidan baya, Khalid ne ke ta tambayar Sooraj jikin nasa cike da kulawa, amma kuma shi Sooraj ɗin cikin halin ƙosawa yake mayar masa da amsa. Suna isowa gida Khaleed yayi musu sallama ya koma, dama aiki yabari a office ɗinsa ya zo. Wanka yayi haɗe dayin brush sai alokacin yaji wani ɗan iskan yunwa na ƙwaƙulan cikinsa, dogon wando yasanya da wata riga marar nauyi, kana ya zura slippers ɗinsa ya fita zuwa falo. Direct kitchine ya wuce, ruwan zafi ya tafasa haɗe da juyewa acikin flask. Cup ya ɗauka ya haɗa tea, hannayensa ya sanya akan waist ɗinsa, yana ƙarewa kitchine ɗin kallo. itace ta faɗo masa arai, yasan gaba ɗaya zaman yunwa tayi acikin a asibitin. Ruwan zafi ya ɗaura akan gas, mintuna ƙalilan ruwan ya tafasa indomie ya jefa acikin ruwan haɗe da sanya spiece. yana tsaye acikin kitchine ɗin, har Indomie ɗin ya nuna, acikin wani plate na tangaran mai kyau ya juye indomie'n. hanunsa riƙe da plate da kuma cup ɗin tea ɗin ya fita zuwa falo. Zaune take akan gado, tayi jigum fitowanta daga wanka kenan, ta sanya wani riga da sket ƴan kanti. Zuwa yanzu idanunta har sun soma rufewa sbd yunwa, gaba ɗaya ƙarfin jikinta ya gudu, duk da zama da yunwa ba sabon abu bane a wajenta.. Wani irin murɗawa taji cikinta nayi. Hanu yasa ajikin ƙofar ya ƙwanƙwasa, batare daya jira anbuɗe ƙofar ba ya juya ya koma cikin falon. Zama yayi akan kujera haɗe da ɗaukan cup ɗin tea ɗinsa ya soma sipping da kaɗan kaɗan. Cikin rashin ƙarfi ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito, ganinsa zaune a falon yasa ta nufo cikin falon. Durƙusawa tayi agabansa, kafun tace wani abu, ya turo mata plate ɗin imdomie ɗin gabanta. Ɗago da kanta tayi ta kallesa, gani tayi kwata kwata idanunsa ba'akanta suke ba. Ɗaukan plate ɗin tayi ta ɗaura akan cinyarta, loman farko da tayi ta lumshe idanunta, wanda suke cike da gajiya da kuma bacci, sosai takecin indomie'n harta manta ma da cewa agabansa take. Duk abun da takeyi yana lure da ita, duk wani motsin da tayi yana kallonta ta gefen idanunsa. Bata gama cin indomie'n ba har ya kammala shan tea ɗinsa yatashi yabar wajen, tana kammala cin indomie ɗin taji wata nutsuwa ta sauƙar mata, ɗaki ta koma tana kwanciya bacci yaɗauketa. *** *** *** Tun tashinta yau ta riga da ta gyara ɗakin da take kwana tsab, hakanan taji sha'awar shiga kitchine ɗin gidan, gani take kamar wahala take bashi don kullum saiya saya mata abun da zata ci, duk da cewa baya wuni agidan amma yana turowa ana kawo mata. Yanzu rabonma da ta sanya shi acikin idanunta kusan kwana biyu kenan. Tsayawa tayi a kitchine ɗin tana ƙarewa ko ina da ina kallo, ita sam bata wani iya girkin zamani ba, shinƙafa kawai ta iya dafawa, wata drawer dake cikin kitchine ɗin ta buɗe, kayan abinci ta gani shaƙe acikin drawer'n, ruwa ta ɗaura akan gas, wanda da ƙyar ta iya kunnasa, saura ma kaɗan wuta ya kama hanunta. neman inda zata samu kayan miya tashiga yi, saidai neman duniya tayi bataga wani abu mai kama da kayan miya a kitchine ɗin ba, dolenta haka ta kashe gas ɗin ta fito daga kitchine ɗin. Fitowarta yayi daidai da shigowarsa cikin falon. Sanye yake da suit coffee colour, ya yinda ƴar cikin rigan ta kasance milk colour, Sosai yayi kyau. Har batasan sanda tasake baki tana kallonsa ba. Kallonta yayi tare da kawar da kansa gefe. "Ɗauko mayafinki" yace da ita ataƙaice. Babu musu ta koma ɗaki ta ɗauko mayafinta. Tafiya suke kowannensu da abun dayake saƙawa acikin zuciyarsa. Gaban wani tangamemen gate taga sun tsaya yayinda yasoma danna horn ɗin motar. Wangale musu gate ɗin akayi ya tura hancin motar ciki. adai dai wani ƙaton parking space ya yi parking motar. "Muje" yafaɗa yana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar, yana gaba tana biye dashi abaya, gaba ɗaya hankalinta naga tsirarun mutanen da tagani suna shawagi a tafkeken farfajiyan wajen, daga mata har mazan dake wajen sanye suke da uniform maroon and milk colour. Direct office ɗin Mr. Isyaka Nuhu suka nufa, har cikin office ɗin akayi musu iso. Cike da mutuntawa Sooraj yabawa Mr. Isyaka Nuhu hanu suka gaisa. Fuska cike da fari'a Mr.Isyaka Nuhu ya dubi Ziyada haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj. "Wannan itace yarinyar?" Ya tambaya. "Eh" Sooraj yabasa amsa. Wayarsa ya ɗauka haɗe da danna ƙiran wata number, yanajin an ɗaga ƙiran yace "Kasameni a office ɗina" yana aje wayar bawani jimawa saiga wani mutumi yashigo cikin office ɗin. Kallonsa Mr.Isyaka Nuhu yayi haɗe da cewa. "Kuje da yarinyarnan kayi mata interview" "Okay Sir!" mutumin daya shigo ya faɗi haka haɗe da kallon Ziyada yace "Muje ko" Kallon Sooraj tayi saidai kuma taga sam idanunsa ba akanta yake ba, wayarsace ma ahanunsa yana dannawa.. (manage) 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SOORAJ !!!* *Written by* Phatymasardauna *Dedicated To My Life (Sardauna)* *🌈Kainuwa Writers Association* *WATTPAD* @fatymasardauna #romance *Chapter 14* Basu wani jima ba suka fito daga ɗakin da akeyiwa duk wani ɗalibi da yakasance sabon zuwa interview. Direct office ɗin principal ɗin suka koma zuciyar Ziyada cike take da farinciki da kuma jin daɗi, addu'anta ɗaya Allah yasa hasashen da takeyi yazamanto gaskia. "Har kun gama interview ɗin?" Mr. Isyaka Nuhu ya tambayi Sir. Yusuf wanda shine ke yiwa duk wani sabon ɗalibi dazai shigo makarantar interview. "A'a Sir ai ma bata taɓa zuwa makaranta ba, inaga kawai sai dai afarayi mata lesson" Sir.Yusuf yafaɗi haka cikin siga irinta bada shawara. Jinjina kai Mr. Isyaka Nuhu yayi haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj wanda har yanzu wayarsace riƙe ahanunsa yana latsawa. "To kaji abun da yace, ya kagani ko za'a fara yi mata lesson ɗin, idan ta ɗan soma iya wasu abubuwan sai abata ko s.s.one ne" Sai alokacin ya ɗago kansa, wannan murmushin nasa da baya wuce kan laɓɓansa yayi haɗe da cewa. "Bakomai hakan yayi, yaushe za'a fara lesson ɗin?" "Ai tunda kusan munkammala komai ko yau ma idan kun shirya sai afara yi mata" Inji cewar Mr. Isyaka Nubu (Principal). "Okay ba damuwa, ni zan wuce" Sooraj yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye, hanu yabawa Principal ɗin sukayi musabaha, kana yabawa Sir. Yusuf ma suka gaisa, ko kallon gefen da take baiyiba ya fice daga cikin office ɗin. Principal ne

Chapter 6 of 38