Share this page
bata kuma san bikin waye za'ayi ba. Tazo wucewa zata shiga banɗaki wata ƴar addar babanta ke cewa "Amarya Amarya bakya laifi Amarya agidan Tsohon najadu" Jitayi gabanta yafaɗi cike da mamaki tajuyo tana kallon Hajara wacce tafaɗi maganar, bakinta na rawa tace. "Yaya Hajara wacece amaryan?" Harara Hajara ta watsa mata domin dama tun can su bawani sonta suke ba. "Wace amarya kuwa inbanda ke, ko baki da labarin cewa gobe za'a ɗaura miki aure da tsohon najadu?" Dariya Hajara tasanya haɗe dacigaba dacewa "Abun yayifa yarinya ta auri wanda yagirmi ubanta" sai takuma sake bushewa da dariya. Jikin Ziyada ne yasoma rawa, lokaci guda taji cikinta yayi wani irin murɗawa atsorace ta ƙaraso gaban Hajara tazube aƙasa, murya na rawa tace "Dan Allah Adda Hajara kifaɗamin gaskiya, auren waye za'ayi?" Kallon kinma rainamin wayo Hajara tashiga yiwa Ziyada ahasale tace.. "Bansaniba munafuka, waye baisan cewa kema son auren kikeba? dama ai kowa yasancewa ke tsohuwar hanuce, wayasanima koshima Tsohon najadun ya ɗana" Kuka Ziyada ta fashe dashi da gudu ta tashi tanufi ɗakin Inna Ma'u, tana shiga ta zube agaban Inna Ma'u dake tsaye, cikin kuka tace. "Dan Allah Inna Ma'u kimin rai, kifaɗamin cewa maganar da Adda Hajara kefaɗi bagaskiya bane, wai dagaske aurena za'ayi, kuma ɗan dashe zan aura?" Wata uwar tsuka Inna Ma'u taja haɗe da ɗauko ashar ta bankawa Ziyada cike da takaici tace "To idan bakiyi aure ba kwaɗaki zamuyi mucinye? inbanda ƙaddarama me Ɗan Dashe zaiyi dake, shima dai dayake tsohon maye ne shiyasa, amma bacin haka banga maiyagani awannan busheshshen jikinnaki ba, da Allah nitashi kibani waje, kuma aurenki da ɗan dashe babu fashi, gobe iwar haka kinzama matarsa" Kuka Ziyada tashiga rerawa hadda majina tana roƙon Inna Ma'u, amma Ina Inna Ma'u haka ta murje idanunta. Komawa cikin ɗakinta tayi hankalinta amatuƙar tashe, zama tayi daɓas aƙasa haɗe da ɗauko wani mayafin mamanta ta rungumeshi ƙam acikin ƙirjinta, kuka take tamkar zararriya... "Wayyo Mamana kinga rashinki abundaya jawomin, Ya Allah kataimakeni kakawomin ɗauki!" Ziyada tafaɗi haka cikin matsanancin kuka. Tsabar kukan da Ziyada tayi harsaida muryarta ta dashe. Tana zaune aɗaki taji muryan Babanta, a tsakar gidan nasu, da sauri ta ɗaga labulen ɗakin tana leƙensa, sosai takejin tsananin tausayin mahaifinnata, duk da cewa tana da ƙananun shekaru amma hakan baisa takasa fahimtan cewa wasu abubuwan dayake aikatawa ba acikin hayyacinsa yakeyinsu ba, ganin yafice daga cikin gidanne, yasa tafaki idon mutane tarufa masa baya, zaune ta iskeshi akan ɗan dakalin dake ƙofar gidannasu. Tsugunnawa tayi agabansa Cikin da shashshiyar muryarta da ta ƙoshi da kuka tace "Baba!" ɗagowa yayi ya kalleta, batare da ya amsa mata ba. "Dan Allah Baba kataimakeni, wallahi banason ɗan dashe!" tafaɗi haka hawaye suna mai kwaranya daga cikin idanunta. Shiru Malam Garba yayi cike da tausayin ƴartasa, lokaci guda kuwa ya zabura kamar anjona masa shocking. "Uban maikikeyi anan?" yatambayeta atsawace. Jikintane yasoma rawa, yayinda kuka yasakecin ƙarfinta, cikin kukan tace. "Dan Allah Baba kaceci rayuwata, katunafa ni amana ce Allah yabaka, dan Allah Karka bari acutar da rayuwata!!" Wata uwar tsawa yakuma doka mata, haɗe da rufe idanunsa yakorata gida. Haka takoma gida tana kuka maicin rai, lallai tasake tabbatarwa da kanta cewa ita cikakkiyar marar gata ce, zama tayi akan tabarmarta haɗe da sanya hanu ta share hawayenta, lokaci guda taji zuciyarta tayi wani irin bushewa, yayinda wani tunani yaɗarsu acikin ranta... (Menene ra'ayinku akan auren ZIYADA da Tsoho Ɗan Dashe? Bazan cigaba ba harsai naga ruwan comment da vote ɗinku, dama nace yawan comment yawan typing.) *✅OTE ME ON WATTPAD* @fatymasardauna 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SOORAJ* *Written By* Phatymasardauna *Dedicated To My Life (Sardauna)* *🌈Kainuwa Writers Association* _{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}_ *https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation* *WATTPAD* @fatymasardauna *CHAPTER 5* Wanene SOORAJ? Alhaji Mansur Mai Nasara shi ne yakasance uba ga SOORAJ, Alhaji Mansur Mai Nasara wani hamshaƙin mai arziki ne dake zaune acikin garin Kaduna, Alhaji Mansur tsohon commissioner'n Ilimi ne dake zaune a cikin garin Kaduna, cikakken ɗan boko ne shi, wanda yatara dukiya, sannan mutum ne dayake jure gwagwar mayar rayuwa, wannan yasa mutane suka masa laƙabi da suna MAI NASARA, saboda duk wani abu daya sanya agaba saiyayi nasara akai. Hajiya Sulaimiya itace matarsa kuma mahaifiya ga SOORAJ, Hajiya Sulaimiya dai irin wayayyun matan nan ne, don asalinta yar ƙasar Sudan ce, tana da kyau sosai, tsananin kyawunta yana ɗaya daga cikin abun daya sanya Alhaji Mansur, narka maƙudan kuɗaɗe wajen ganin ya aurota, zama sukeyi cike da so da kuma ƙaunar juna, koda yaushe cikin farinciki suke, shekaransu uku da aure Allah ya azurtasu da samun ƙaruwan yaro namiji, tun daga randa aka haifi SOORAJ Alhaji Mansur yaƙara ganin buɗi acikin arzikinsa, soyayyar duniya suka ɗauka suka ɗaura ta akan yaron nasu, komai Na SOORAJ irin na Mahaifiyarsa ne domin kyawunta ya ɗauko. sosai SOORAJ ke zuba tashen kyau da burgewa tun yana ƙarami, saidai yataso da wani irin hali, miskiline na ƙarshe, sannan sam baida yawan magana, komai nasa atsare yakeyinsa, tun yanada shekara 12 mahaifinsa ya turasa England acan yayi gaba ɗaya karatunsa, tundaga kan secondary school har zuwa Masters ɗinsa, P.H.D ɗinsa ne kawai yayi aƙasar America. Sosai SOORAJ yake da ƙwazo akan dukkan komai, babu ruwansa da kowa, rayuwarsa kawai yake, bashida wani aboki aduniya sama da Mas'oud, sosai abotarsu tayi ƙarfi da Mas'oud, kasancewar sun fara abotanne tun suna ƙanana, gaba ɗaya sirrin Mas'oud SOORAJ yasani, haka shima Mas'oud ɗin yasan wasu sirrukan SOORAJ, saidai akwai wani sirri da SOORAJ ɗin yaɓoyewa kowa, shikaɗai yasan matsalarsa. Tun daga kan SOORAJ Alhaji Mansur baisake haihuwa ba, amma hakan baisa sun tashi hankalinsu ba, kasancewarsu wayayyun ƴan boko, dama ba wani son tara ƴaƴa suke ba, ayanzu dai SOORAJ yana da shekara 30 aduniya, cikekken matashine mai tsananin ji da kansa, rayuwarsa yakeyi maicike da burgewa baruwansa da kowa, abune mawuyaci kaga dariyansa, duk yanda Ƴan Mata keson samun daman kai kansu garesa, hakan baya yiwuwa, domin SOORAJ wani irin mutum ne, da akomai nasa baya sanya mata aciki, duk wata mu'amalarsa baya sanya mace aciki, mace duk kyau da haɗuwarta sam bata gabansa, batama burgesa, duk wani irin karairaya da mace mai lafiya zata zo tayi agabansa bazata taɓa burgesaba, duk tsananin kyawun mace, SOORAJ bata burgesa, shi yariga daya sanya aransa cewa mace bata cikin tsarinsa. Ayanzu yana akine a babban bankin Nigeria dake cikin garin Abuja wato Central Bank Of Nigeria (CBN) yanzuma hutu ya ɗauka shiyasa ya zo Kaduna wajen iyaye da danginsa. A rayuwarsa yana tsananin son iyayensa, sai gashi kuma daga zuwansa sun laƙaba masa auren dole. Wannan shine taƙaitaccen tarihin SOORAJ MAI NASARA. Kamar koda yaushe idan yana acikin damuwa yakan fita yazaga gari, wani lokaci har ƙauyukan dake kusa dasu yake zuwa, sosai yakejin daɗi idan yaziyarci ƙauyuka musamman irin ƙauyukan da fulani ke rayuwa acikinsu, yauma hakance takasance dashi, hakanan yaji yanason fita daga cikin gari, bayaso yakoma Abuja baije yaɗan zaga gari ba... Tsab yashirya kansa cikin long pencil jeans black colour,and Black t-shirt, agaban t-shirt ɗinnasa anrubuta ( THE MAN) da farin fenti. white denim jacket fara irinta maza yaɗaura akan rigar dake jikinsa, sosai kayan suka amshi jikinsa kasancewarsa mai farin fata, wasu fararen takalma combat wanda aƙalla kuɗinsu zasu haura sama da 30k yasanya aƙafarsa, hmmm SOORAJ yanason gayu sosai, hakan yasa koda yaushe cikin ɗaukar hankali yake. Da turarukansa masu tsada ya feshe jikinsa, take ko ina naɗakinnasa ya gauraye da ƙamshi. Wayoyinsa haɗe da key ɗin Range Rover ɗinsa ya ɗauka, kana yafice daga cikin ɗakin. Yanashiga cikin motarsa ya kunnata, maigadi ne ya wangale masa gate, yana cilla motar tasa kan titi yasoma murza steering motar ahankali cike da salo.. *ZIYADA* Gaba ɗaya ko ina acikin garin yaɗauki shiru, babu wani abu dake kai kawo, kowa yana gida akillace, adai dai irin wannan lokacin mafi yawancin mutane suna kwance ne aɗaki suna bacci, duhun dare ne sosai, babu wani abu dake motsi, sai ɗan abun da baza'a rasa ba, kamar yanda ko ina yaɗauki shiru haka gidannasu ma yake shiru, babu motsin kowa, gaba ɗaya jama'ar gidan suna bacci, amma banda ita, idanunta sun ƙeƙashe sun bushe, babu wani alamun bacci acikinsu, tun tana kuka da iyaka ƙarfinta, harta koma sauƙe ajiyar zuciya akai akai, babu wani abu dake ɗaga mata hankali, kamar idan tatuna cewa gobe za'a ɗaura mata aure da Tsoho Ɗan Dashe, tsohon dakowa yasan cewa ba mutumin kirki bane, shiru tayi tana mai sake nazartan abun da zuciyarta ke raya ma ta. Tabbas awani ɓangaren tunanin dake kwance cikin zuciyarta awajenta shine daidai, amma kuma tawani wajen tanaga kamar hakan ba daidai bane, duk duniya bata da kowa sai mahaifinta da kuma danginsa da suka ɗauki karan tsana suka ɗaura mata. Tana zaune awajen taji ansoma ƙiraye ƙirayen sallan asuba, jitayi gabanta ya tsananta bugawa, lokaci ɗaya taji zuciyarta na ingizata, ɗan dangwalin kayanta taɗauka, haɗe da yaye labulen ɗakinnata tasako kanta kaɗan tana leƙa tsakar gidannasu, ganin bakowa yasa tafito saɗaf saɗaf ta nufi hanyar fita daga gidan, saida takai bakin ƙofa kafun ta tsaya tare da juyowa tana mai kallon ƙofar ɗakin Babanta, wata irin karyewa zuciyarta tayi, take sai ga hawaye nasauƙa akan kumatunta, sosai takeson Babanta, tasan duk wani abu dayakeyi mata balaifinsa bane, amma bata da yanda zatayi, dole ko duniya ne ma tashiga, dole tanesanta kanta ga faɗawa halakar auren tsoho ɗan dashe. Juyawa tayi aɗari tabar cikin gidannasu, gudu takeyi sosai harta yi nisa da gidajen dake cikin ƙauyen tasoma shiga jejin dazai sadata da bakin hanya, komai tanayinshine acikin ƙarfin hali, amma har aƙasan zuciyarta tsorone shimfuɗe.. Bai kwana acikin garin Kaduna ba, kasancewar dare yayi masa, sam shi ba mutum bane mai son tafiyar dare, hakan yasa ya gangara gefen hanya, anan ya kwana cikin motarsa. Asuban fari yakamo hanyar dawowa cikin gari, saboda yau ɗin yakeso ya koma Abuja. Gudu sosai yaketa shararawa akan titi kasancewar babu wasu yalwan motoci dake tafiya akan titin. Ba ƙaramin tafiya bane daga cikin ƙauyen nasu zuwa bakin titi saboda haka sosai tagalabaita, ganin takusa kawo bakin titi ne yasa ta rage sauri tasoma tafiya ahankali, dama ƙarfinta yasoma ƙarewa. Jitayi kamar anabin bayanta, da sauri tawaiwaya aikuwa wasu maza tagani su biyu abayanta, waro manya manyan idanunta tayi cike da tsoro tana kallonsu, dariya suka bushe dashi, ɗayanne ya sanya harshe yalashi laɓɓansa, cikin yanayi irin na ƴan iska yace. "Baaba yau fa munyi babban samuwa, ɗanyen kaya ce" Dariya wanda aka ƙira da suna Baaba yayi, ya karkace tsayuwarsa tare da kai hanunsa kan belt ɗin wandonsa. "Ay gaye yau zamu more" yafaɗi haka yana me zare belt ɗin wandonsa. Ganin haka yasa Ziyada shiga cikin wani irin matsanancin firgici, aruɗe tasoma ja baya, da ƙarfin gaske ɗayan ya fusgota, ihu tashiga yi tare da yunƙurin ƙwace kanta amma riƙon da yayi mata bana wasa bane, ɗan kwalin dake kanta ya fusge ya yi cilli dashi gefe, ganin haka yasa taƙara fasa ihu haɗe da turjewa, amma takasa ƙwacewa, hanunsa yasanya da iyaka ƙarfinsa ya ja rigan koɗaɗɗiyar atamfan dake jikinta, ɓesss kakeji rigar ta yage, dama tuni kayan sunyi laushi. Ganin saman ƙirjinta ya bayyana afili, yasa samarin suka bushe da dariya, kowanne acikinsu jikinsa yaɗauki mazari, burinsu kawai shine suga sun farketa. Wani irin ihu Ziyada tasa tare da kafa bakinta akan hanun wanda ke riƙe da ita ta sakarmasa cizo, awahalce yasaketa yana fidda wani irin ƙaran azaba, itakuwa aguje ta lula cikin jejin. Ganin haka yasa suka rufa mata baya, gudu take sosai suna biye da ita, sam batasan cewa takawo bakin titi ba, aguje ta zo zata bi takan titin tasake faɗawa wani jejin... Kafun ƙiftawan ido wata mota da tataho aguje tayi sama da ita, tim haka ta faɗo ƙasa. Amatuƙar razane yafito daga cikin motar yayo kanta, waro kyawawan idanunsa waje yayi tare dasa hanu ya toshe bakinsa, lokaci guda jikinsa yaɗauki rawa ganin irin ɓarnar da yayi, kwance take cikin jini ba ako iya gane kamanninta, wani irin rawa jikinsa keyi kamar anjona masa shocking, hannayensa duka yasanya yaɗagota, buɗe motar yayi yasata agidan baya, yanashiga wajen driver ko gama rufe murfin motar baiyiba, ya figi motar da gudun gaske. Samarinnan naganin abun daya faru sukayi saɗaf saɗaf suka bar wajen, cike da haushin rashin samun nasara da basuyi ba. Gudun da yakeyi har ya wuce hankali, tamkar zaitashi sama, gaba ɗaya ya ruɗe, ganin yanda jini ke fita ajikinta. Alokacin daya shigo cikin garin Kaduna, gani yake kamar motar tasa bata gudu, hakanne yasanya yaƙara gudun motar mintuna kaɗan saigashi a cikin asibiti, amatuƙar ruɗe yaje yaƙira likitoti suka zo suka ɗauketa aka wuce da ita emergency room. Ganin yanda kanta ke zubda jini yasa likitoti suka duƙufa akanta wajen bata taimakon gaggawa. Shikuwa SOORAJ yana nan awaje yakasa zaune yakasa tsaye, hankalinsa amatuƙar tashe yake, tsoronsa ɗaya kar ace masa ta mutu, wani irin gumi ne ke fesowa ta goshinsa, kowa yagansa yasan cewa yana cikin tashin hankali. Aƙalla sama da awa ɗaya da rabi likitoti suka ɗauka suna bata taimakon gaggawa, cikin ikon Allah Kuwa sun shawo kan lamarin, saidai bata farfaɗo ba, amma sun tsaida jinin dake fita daga goshinta dakuma gefen kanta da ya fashe. Yana tsaye likitotin suka fito daga Emergency room ɗin. Da sauri yataho wajen Dr.Salees, baikai ga cewa komaiba Dr.Salees yasakar masa murmushi tare da sanya hanu ya dafa kafaɗan SOORAJ ɗin. "Karka damu SOORAJ munshawo kan matsalan, sai dai mujira farkawanta, muje office saina ƙarasama sauran bayanin" Babu musu SOORAJ yabi bayan Dr.Salees zuwa office ɗinsa. Suna shiga cikin office ɗin Dr.Salees ya nunawa SOORAJ wajen zama, kana shima ya zauna. Sakeyin musabaha sukayi kafun Dr.Salees yacigaba da cewa. "Ka kwantar da hankalinka ba wani babban damuwa bane, buguwane kawai, tabugu sosai gaskiya, amma dayardan Allah munshawo kan komai, saidai kuma bamusan awani irin yanayi zata buɗe idanuba, amma muna kyautata zato, Insha Allahu ma zata tashi lafiya, Allah dai yatsare na gaba" Da "Ameen" Kawai SOORAJ ya amsa yana mai sauƙe ajiyar zuciya akai akai. Bisa umarnin SOORAJ aka maidata wani special room,,,, ahankali yaturo ƙofar ɗakin yashigo, sauƙe idanunsa yayi akanta, tana kwance flat kanta na kallon sama, gaba ɗaya rigar dake jikinta ta ɓaci da jini, kanta kuwa a ɗaure yake da farin bandeji (bandage) yayinda tulin gashin kanta ke watse akan pillow, ɗauke kansa yayi daga kallonta tare da ƙarasowa cikin ɗakin, kan wata kujera yaje ya zauna haɗe da kai dubansa kan ledan ruwan da aka saƙalashi ajikin wani dogon ƙarfe, yana shiga cikin jikinta ahankali, kallonsa yakuma dawowa dashi kan agogon kamfanin Gucci dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa. Ƙarfe goma na safe daidai haka agogon yanuna masa, hanunsa yaɗaura akan haɓansa haɗe da furzar da iska daga bakinsa, miƙewa yayi tsaye tare da nufar ƙofar fita, haryaje bakin ƙofar kuma sai ya tsaya juyowa yayi ya kalleta, idanunsa ne suka sauƙa akan ƙirjinta da kusan rabin breast ɗinta suke a bayyane, da sauri yakawar da kansa, wani irin bugawa yaji kansa yayi, kamar andoka masa guduma, jacket ɗin dake jikinsa ya cire tare da nufar inda take kwance, saidai koda wasa baisake barin idanunsa sun kalli ƙirjinnata ba, jacket ɗin nasa yarufa mata ajikinta, kana yafice daga cikin ɗakin. Office ɗin Dr.Salees yaje ya biya kuɗi, aka tura nurses guda biyu wanda zasu tsaya akanta don bata kulawa, shikuwa motarsa yashiga yabar asibitin. Direct gidansa ya nufa ransa ajagule, sam baiso haka takasance ba, yau yatsara tafiya Abuja, amma ga abun daya faru, zaman cikin Kaduna yakamashi dole harzuwa farfaɗowar yarinyar. Wanka yayi kana yazo ya kwanta akan gado, lamo yayi yana tunanin yanda accident ɗin ya kasance, sai alokacinne ma mamaki ya kamasa, ƙaramar yarinya irinta mai zai fito da ita awannan lokacin? da dukkan alamu kuma ba acikin hayyacinta take ba. "To kodai mahaukaciya ce?" ya raya hakan azuciyarsa, da sauri ya kawar da wannan tunanin acikin ransa, wayarsa yaɗauka ya kunna karatun Al'Qur'ani mai girma, yana cikin jin karatun bacci ɓarawo ya sace shi..... (More Comment nd Vote more typing😝 kuyi haƙuri yau banyi editing ba... Zan fara halina fa readers idan nayi update yau sai jibi kuma🤣😝 Allah yasa bazaku takura ba. ) *🍇SOORAJ FANS GROUP🍇* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HFwwNXNTaW6HUbrbHjBHVM *Idan kinsan Bazakina Comment ba kada kishiga, ONLY NOVELS kawai mukeso, bayan haka bamason kowani irin post.... Bamason Talla kona menene, idan kinyi zaki ganki a waje* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *SOORAJ* *Written By* Phatymasardauna *Dedicated To My Life (Sardauna)* *🌈Kainuwa Writers Association* _{United we stand ans succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_ *https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation* *WATTPAD* @fatymasardauna *CHAPTER 6* Tunda ya kwanta bacci bashi ya tashi ba sai da aka soma ƙiraye ƙirayen sallan Azahar. Toilet yashiga yayo wanka. Still riga da wando na jeans yasanya ajikinsa. Masallacin dake kusa da gidansa ya nufa donyin sallah. Tun da yafita yin sallah baidawo ba sai ƙarfe huɗu na yamma, wanka yasakeyi. Combat jeans ne ajikinsa baƙi sai kuma wata farar riga mai ɓaƙaƙen aninaye. Yana tsaye agaban dressing mirror yana taje tulin sumar kansa, wanda yasha aski irin na zamani, screen ɗin wayarsa ya soma kawo haske, ɗan matsawa kusa da yawartasa yayi. Sunan Mas'oud ne ke yawo akan screen ɗin wayar, kasancewar ya sata a silent shiyasa batayi ƙara ba, ɗan ɓata fuska yayi haɗe da ɗaukan wayar yakara akan kunnensa. "Ina falo" Inji cewar Mas'oud. "Okay" kawai Sooraj yafaɗa akasalance tare da aje wayartasa, bai fita falon ba yaci gaba da taje sumar kanshi, saida ya kammala duk wani abu dazaiyi kana ya ɗauki wayarsa dakuma car key ɗinsa yafita zuwa falo. Cike da takaici Mas'oud ke kallonsa, duk da yasan cewa halin Sooraj ne shanya mutane, amma kuma abun da yayi masa yauɗin yayi masa ciwo. "Inakuma zakaje?" Mas'oud yatambayesa yana me ƙare masa kallo. "Asibiti" SOORAJ yabashi amsa ataƙaice. "Abiti kuma? Baka da lafiya ne?" Mas'oud yajero masa duk waƴannan tambayoyin alokaci guda. Ɗan ya mutsa fuska yayi haɗe da sanya hanu ya shafi kwantaccen sajen dake shumfuɗe akan fuskarsa. "Accident mukayi, zanje na duba yarinyar dana bugene kota farfaɗo" ya faɗi haka yana me nufar hanyar fita daga falon, kai kawai Mas'oud ya girgiza haɗe da miƙewa tsaye yabi bayan SOORAJ ɗin. SOORAJ ne ke tuƙa motar yayinda Mas'oud ke zaune agefen mai zaman banza. Tafiya suke babu wani wanda yace da ɗan uwansa wani abu, ahaka har suka kawo asibitin, sam Mas'oud baiwani damu da shirun da SOORAJ ɗin yayi ba, because yasan hakan halinsa ne, bakoda yaushe yacika yawan magana ba, amma idan kafahimcesa yana da daɗin zama, dan bayashiga abun da babu ruwansa... Atare suka jera suka shiga cikin asibitin. Office ɗin Dr.Salees suka nufa, shiyayi musu jagora zuwa ɗakin... dama yana shirin zuwa dubata kenan suka shigo. Tananan har yanzu bata farfaɗo ba, wasu allurai Dr.Salees yayi mata, juyawa yayi ya kalli SOORAJ dake zaune akan wata plastic chair.... "Zata iya farfaɗowa akowani lokaci da yardan Allah, Yana da kyau katsaya atare da ita." Inji cewar Dr.Salees. Kai kawai ya iya jinjina wa Dr.Salees alaman yaji, fita Dr.Salees yayi daga cikin ɗakin. Kallon Mas'oud daya kafe yarinyar da idanu SOORAJ yayi, tsayawa yayi yana kallon yanda idanun Mas'oud ke yawo ajikin yarinyar ko ƙyaftawa ba yayi, takaicin Mas'oud ɗinne yakamashi, sam shi kam baiga wata mace aduniya dazai tsaya ɓata lokacinsa wajen kallonta ba, yaga manyan mata da suka amsa sunansu mata baiji komai gamedasu ba balle wannan ta tsitsiyar yarinyar, inbanda ƙaddara ma maizai haɗashi da ita, sam shi baya shiga sha'anin mata, saboda yasan menene matsalarsa, wannan ma don dolene kawai, amma dazaran ta farfaɗo zaisa amaidata inda ya ɗaukota. "Tunda kana nan ni inaga kawai zantafi yau nakeso nakoma Abuja, please kakula da ita, idan tafarfaɗo tagayama garinsu saika maida ita!" SOORAJ yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye. Da sauri Mas'oud ya kallesa cikin mamaki yace "Zaka koma Abuja kuma?" Kai SOORAJ ya jinjina masa alamar "Eh" "Hmmm lallai SOORAJ baka da imani, kabuge yarinya kuma katafi kabarta? wato nine marainin wayonka shine kakeso katafi kabarni da ita ko?" Murmushin gefen baki SOORAJ yayi wanda yayi masifar ƙarawa fuskarsa kyau. "Mene matsalarka Mas'oud idan kakula da ita? Kasan inada abubuwan yi da yawa, banjin kuma zan iya ɓata lokacina akan mace" SOORAJ yafaɗi haka yana me kai dubansa ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa. "Nima ai bazaman banza ne sana'ata ba, kai kabugeta kuma kai kake da alhakin tsayawa akanta kakuma bata kulawa harsai ta warke, saboda haka ni kaga tafiyata" Mas'oud yafaɗi haka aƙufule, don ya lura tsagwaran iskanci ne ke damun SOORAJ ɗin. Still murmushin gefen baki yayi haɗe da bin Mas'oud ɗin da kallo harya fice daga cikin ɗakin. Kan kujera yakoma ya zauna, yayinda ya juyawa gadonnata baya, wayarsa yaciro ya soma latsawa.. Ahankali take ware manya manyan oily eyes ɗinta masu kyau da burgewa, dishi dishi tasoma gani, kafun daga bisani idanun nata suka soma washewa, ɗakin tasoma ƙarewa kallo, yayinda ƙwaƙwalwarta ke tunano mata abubuwan da suka faru, amatuƙar razane ta ƙwalla ƙara.. "Wayyo Allah Nashiga Uku dan Allah karku cutar dani!!" Azabure yajuyo jin ihunta abayansa, yunƙurin tashi zaune tasomayi amma ina jin kanta take yayi mata wani irin nauyi, ga wani raɗaɗin azaba dake ratsata... Tsuka yayi ƙasa ƙasa tare da maida kansa ga wayarsa yacigaba da latsawa, yatsani mutumin da baida nutsuwa. Babu yanda ta iya haka takoma ta kwanta tana gunjin kuka, saboda kotafi kowa ƙoƙari ayanzu bazata iya tashiba. Idanunta ne suka sauƙa akan bayansa, domin dama yabata baya. Ganin namiji na zaune ya bata baya yasa taƙara volume ɗin kukanta, jikinta na rawa tace "Dan Allah kuyi haƙuri ku ƙyaleni, nakoma inda nafito, wallahi nayarda ma ni Zan auri tsoho ɗan dashe'n, nidai kada ku cutar dani, wallahi ni marainiya ce, dan Allah ku ƙyaleni natafi!" kuka take tsakaninta da Allah tana zabga magiya da roƙo, amma ko motsi baiyiba balle tasaran zai juyo gareta, duk atunaninta shiɗin ɗaya daga cikin mazan da suka ka mata ɗazu ne. Ganin baijuyo gareta ba yasa tacigaba da kukanta, yana zaunene kawai amma jiyake kamar ana hautsina ƙwaƙwalwarsa, kuka yana ɗaya daga cikin abun daya tsana, wata tsuka yaja me ƙarfi haɗe da juyowa ya watsa mata wani irin kallo, idanunsu ne suka sarƙe acikin na juna, wani

Chapter 3 of 38