Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ABOKIN YAYANA BY ZEEYNASEER PART ONE ABOKIN YAYAYANA littafine da ya samu rubutawa da karamar marubuciyarku wato zeeynaseer ABOKIN YAYANA littafine da ya kunshi abubuwa da dama daga ciki sun hada da soyayyya,ban tausayi tare da sanin maicece kaddara sannan kuma ubangiji shike yin abinda ya so akuma lokacin da yaso duk acikin ABOKIN YAYANA xakiga abin da ake cewa bazata ubangiji yakan yin abinda mike tunanin ba zai yiyuba kude ku biyoni cikin wanannan littafinawa domin ganewa kanku abinda nake fadimuku. SADAUKARWA Na sadaukar da wannan littafi ga mahaifina ubangiji Allah yayi masa rahama ya Kuma Kyautata makwancinsa da shi da duk wadanda suka rigamu gidan gaskiya,sannan Ina mai neman alfarama ga duk wanda yakaranta wannan littafi kar ya wuce ba tare da yayiwa abbana adduar samin rahamar ubangiji ba. ABOKIN YAYANA😭 Amincin Allah da yardarsa sukara tabbata agareku masoyana ,yau yayi Dede da 15/8/2024,kamar yadda nace littafin mu Mai suna ABOKIN YAYANA,Zaifara zuwar muku a wannan Rana. Acikin wanann littafi zakuga wasu maban ban ta abubuwa Misali: Nayi amfani da yankin da nake wajan rubuta littafin zakuji garuruwan da ke ciki wasu Daga ciki ba lalle Kun San suba. Nayi amfani da yankin da nake wajan rubutun littafina ba domin komi ba,sai Dan ganin ni yar Jigawace sanann Kuma abin zai Fi ace nayi amfani da garuruwan dake yankin mu wajan rubutun. Nagode sosai da kasancewar ku Dani,Ina Kuma fatan zakuji dadin wannan littafi,zakuma miyi amfani da darasin dake cikinsa. Wasu Daga cikin littafan da zasu biyo Baya,bayan min kammala wannan littafi da izinin ubangiji. ADDININA MARAICI SANADIN KAWA BAZATA MAI NE SILA MAHAIFIYATA Duka wadannnan littafai Zasu bayyanane acikin wanann gida Mai albarka da yardar ubangiji,Wanda dukkanin su Rubutune na marubuciyarku ZEEY NASEER. ABOKIN YAYANA😭😭 Page 1 Dan Allah yayah kabari,Kabarshi haka kullum Ina ce maka mina kula saboda wasu zasu iya kamamu,Idan har kana so na dagaske wannan abubuwan basu bane abin da suka Kamata,Kana da kudi,kana da rufin Asiri,kana da komi,ka aureni shine mafita,kaga shikkelau Daga nan xamu zauna tare miyi rayuwa tare ta har abada. Ki rufemin baki karki sake min irin wanann maganar,na fadimiki ba kya tsarin macan da Nike son aura, domin ajinki Bai Kai wacca zan aura ba,Ina rayuwa dake ne kawai saboda abin da Nike Samu Daga gareki,Kuma zamuci gaba da rayuwa a haka har karshan rayuwarki. Dan Allah yayah idan baza ka aure niba ka bari Wani ya aureni, kabarni na kula wadan da ke so na domin na Samu nayi aure,duk da wasu mutanan sun fuskanci rayuwata yanzu ta lallace,Na sauya Daga Mai mutunci,zuwa wacca ta tanbadar da shi,Amman nasan Hakan ba zai sa na rasa Wanda zai rufamin asiri ya aureni a hakaba,Dan Allah kafita a rayuwata,In har kana nan bazan iya kula kowa ba,Ina sonka fiye da yacca nake son Kai na. Tau ya dauketa da Mari..........😭 Yayah Dr.mari na fa kayi,yaushe zan Dena lefin da zaka dena Mari na,Mai yasa Mari ya xamo tamkar daukar Yartsanar wasan yara agurinka,Mai yasa baka tausayi na,Mai yasa duk da kana ikirarin so na baka gudun abin da zai batamin rai,Dan Allah karika tausayamin Ina jin babu dadi ace Wanda nafi so da kauna acikin mazaje shine Wanda a kullum yake zama Sanadiyyar zubar da hawayena,kaji tausayi na ko domin son da nake maka. Kaji tausayina ko domin maraicin da Nike ciki,kada kamanta Kai ne ka zamo uba agareni alokacin da na rasa kowa nawa,Mai yasa kake so ka zubar da dukkanin wanann abin,Mai yasa kake so ka mayarni tamkar Bai wa? Kingama wanann shine abin da taji anfurta Daga ban garansa,Sanin kanki ne Samiha kin sani cewa Ina sonki,Ina Kuma kaunarki,Taya Zaki fadimin maganar wai na barki kije ki auri Wani,Taya kike tunanin zan zuba Ido,Ina kallonki kina rayuwa agidan Wani a matsayin matarsa,sanin kanki ne kin San cewa Wanann abin ba Mai yiyu wa bane,Ni kade ne Wanda zan rayu dake domin ke akayi ni,babu Wani na miji da zai rayu dake bayanni tabbas dullokacin da kikayi yin kurin shigo da Wani cikin rayuwarki,Wallahi sai na Kasheki na kashe sa,na Kuma kashe Kai ma,bazan taba jurar Ina tare da ke Wani na miji ya kasance da keba,Wanann ya zama lokaci na karshe da Zaki sake yimin zance Wani namiji,in ba hakaba zan Miki hukuncin da ban taba yi Miki irin saba. Kasa motsi tayi saboda Zafafam kalaman da taji ya furta,kelan haryanzu soyayyyarta na cikin zuciyarsa,ammam Mai yasa yake wulakantata,Mai yasa ya Dena Bata kulawa,kullum kalar rayuwar Tasu tana Bata mamaki,Bata taba ganin wadan da ke soyayyya hakaba,Bata taba ganin masoya irin su ba akullum masoya burin su su ririta juna,Kulawa cike da shauki Amman shi a kullum Bai da buri sai muzgu na mata,Bai da buri sai wulakantata,tana mamakin yacca kwata kwata Baya tausayinta,tana mamakin yacca kwata kwata Baya son faranta mata,Amman duk da wanann musgunawar da take fuskan ta agurinsa Hakan Bai sa ta sare ko Kuma Tara sa yacca zatayi ba,a kullum son sa da kaunarsa sake shiga cikin zuciyarta suke,ita kanta tana mamakin yadda takejin sa,domin babu Wani Abu na kyautatawa da yake mata da zai sa ace yayi sandin sace zuciyarta da shi,wanna wane irin musibace,Bata iya yi mas musu a dullokacin da ya Bukaci Yana son su hadu,Bata iya mas musu a dullokacin Daya Bukaci yake be da ita,ya mayar da ita tamkar matarsa,yakan yi abin da yaga dama da ita,a Kuma lokacin da yaga dama,Wanda Kuma da ba haka suke ba,duk tsawon shekarun da suke abaya,Dede da hannunta Baya taba yunkurin kamawa ballantana har yaketa iyakar ubangiji,Amman lokaci daya ya saya,sauyin da haryanzu ta kasa gano dalilin sa,tom Amman Mai a dullokacin da Samiha ta koma gida,da na Sani mara adadi ke tun kararta,da na Sanin da take tunanin Mai yasa tasan zatayi shi Amma ta biyewa Yaya Dr.,suke aikata abin da suke aikatawa ita kanta bata Sami wanann ansar ba haryanzu Amman kullum cikin addua take ubangiji Allah ya Bata ikon Dena rayuwar da sukeyi, Ubangiji Yabata ikon gyarawa,Sai kace bani bace Samiha Mai addini da mutunci,Mai kulawa da karatunta,mai ya Sami rayuwata hakane,Mai yasa rayuwata ta lallace,Duk wani muradina yanzu ya tashi a banxa na kasa cika burina,Kuma burin mahaifana, ubangiji yayi muku rahama,ya Kuma bani ikon shiryuwa nadena abin da nikeyi,Kai Kuma yaya abdallah Allah ya dawomin da Kai,domin tsantsar Zalinci ne yasa aka bari kayi nisa Dani😭😭, rayuwata Bata da wani amfani a yanzu,Kiran sallan magri bane ya tsayar da ita Daga tunanin da take,tashi tayi ta shiga ban daki domin ta tsarkake jikinta,Ta fito ta shirya sannan ta dakko Abin sallah,bayan ta idar da sallah tayi addu akan Allah ya shiryar da ita,yakuma bata ikon Dena abin da takeyi,da adduar ubangiji Allah ya bawa yaya Dr.dinta masoyi daya da batta da tamkarsa Damar dena wulakantata,ya dawo yaya Dr.dinta na Baya mai sonta da Kuma kulawa da ita,Baya son bacin ranta a baya,Amma a yanzu ya sauya kullum cikin mu zantata yake,Mai yasa Mai ya sauyasa akan abinda yake mata...... Wacece Samiha Wayene yaya Dr....???? Kuma Mai ke faruwa tsakanin su,kuci gaba da kasancewa damu,domin ganin ansar Wannan tambayoyi . Bayan ta kammala addua ne ta zauna akan gefen gado tana tunanin yacca rayuwa ta sauya mata tana tunanin yacca komi yayi mata zafi,Tana jin Ina ma ita ma ta mutu tabar duniya kamar yacca iyayanta suka mutu,Ina ma ita ma ta koma ga mahaliccinta sai yafi mata sauki akan halin da take ciki,karan da wayarta ta yini ya tsaidata Daga Dan lukutin yanayin da take ciki na tunanina,Dammul jisim shine abin da ya bayyana a fuskar wayan,Duk Wani hali da take ciki idan ta Gansa takanji ta Sami nutuswa,Idan yakirata a waya kuwa ji take tamkar anbata kyautar duniya,duk da cewa shine sila da Kuma sanadin damuwarta,shine sila na shigar ta duk wata musiba,Amman takanji farinciki idan ta Gansa,abin dake saka mata rashin kwarin gwaiwa kuwa shine irin yadda yake treating dinta,Hannunta na karkarwa ta dauki wayar ta Daga tana Mai farinciki,Amman abin mamaki yacca ta saba jinsa babu fara'a haka ta jisa,ki fito ina kofar gida shine abin da taji anfada kiyat ya kashe wayan bin wayan tayi da kallo idan da sabo ta saba da irin wannan yanayin,Amman a shekarun da suka shude irin shaukin da Yaya Dr. Yakeyi adullokacin da yakirata ya linka Wanda takeyi,Mai yafaru,Mai ya shiga tsakaninta da masoyinta?,Wani wahalallan hawayene Wanda take son futar Dashi tun dazu shine ya zubo Mata, murmushi tayi Wanda iyakar fuskartane,tashi tayi ta shafe jikinta da turare ta fita,cikin fara'a tana zuwa taga fuskansa yadda ta saba ganinsa babu Wani sauyi. Sallama tayi da muryarta Mai dadi tare da taushi,Yaya Dr.ina yini,Wannan ita ne sallamar da kike min Daman,yanzu rainin har ya zama ki zo kimin irin wannan gaisuwar,Abin ya Bata mamaki duk da ba yau ya saba yi mata hakaba,tom Taya zata Sami karfin gwiwar tunkararsa,ba ya nuna mata Wani shauki ko farinciki da zai sa ta so kasancewa kusa da shi. Kara sowa tayi jiki duk babu kwari,tayi hugging dinsa yacca suka saba,A Dede lokacin ruwan hawayanta ya zuba akan gadon bayansa,shi kansa sai da yaji zuciyar sa,tayi masa Wani irin zafi Yana son ya rarrasheta،amman ba shi da kwarin gwiwar Hakan,a dullokacin da yayi yunkurin yin Hakan ya kanji ya kasa,Zuciyarsa tayi ta masa sake sake iri daban daban ,tabbas yaji Yana son rarrashinta domin aduniya babu Wani Abu da ya tsana irin ganin hawayanta,Wanda yasan shine sila,Amman ba shi da wata dama ko ikon Hana su zubowa,a hankali ya zareta Daga jikin sa,domin radadin da yakeji da zafi aransa na damuwar da take ciki,murfin motarsa ya bude ya dakko katuwan Leda,gashi abinci na kawo Miki,naga Baki baro gurina da wuri ba,baza ki Sami lokacin daura abinci ba,karba tayi tana godiya ya juya ya shige motarsa. Wani Abu dake Bata mamaki,duk irin kalar musgunawar da yake mata,Baya taba barinta cikin matsala ta Wani Abu na rayuwa,tun iyayanta suna raye yake dawainiya da ita,Yanzuma haka Kuma Bai Dena ba,Gidan taf yake da kayan abinci Wanda ya zama duk watane sai ya kawo Mata abin da take bukata ,Baya taba barin ta rasa ko maggi,komi ya tanadar mata,Baya son ta zauna da yunwa,tom Mai Hakan ke nufi,Yana Sonta harynzu ko yaya?tambayar da take Tayi acikin zuciyanta kelan Amman ta kasa samin ansarta,kawai sai ta tsinci kanta da yin murmushi,tare da Bude ledan da yakawo mata,take a way ne yayo mata,jallof din shin kafane aciki wadda taji kayan Hadi matuka,sai Daya ledan gashashiyar kazace Mai Rai da lpy,Sai kuma drinks guda biyu da ya sako mata da su,Yaya Dr kelan,ko yamanta jiya ya kawomin drinks dina na wata suna nan jibge a fridge,dariya abin ya Bata,tabbas Haryanzu Yana son ta,tom Amman Mai yasa yake mata abin da yake mata?.......... Amsar na cikin wanann littafin na ABOKIN YAYANA,Kuci gaba da kasancewa damu ngd. Bayan ta kammala cin abincinta ta tashi taje domin yin alwalar sallan Ishan,ta idar da sallah tayi shafa'i da wutri,taje Kan gadonta domin ta kwanta,photonsa shine abin dake haskaka wallpaper din wayanta,shine Kuma abu na karshe a kullum da take kalla idan zata kwanta bacci, Murmushi tayi mai hade da ciwo tare da fadin yaya Dr.mai yasa,Mai yasa Kai da ka zamo farinciki na a baya a yanzu ka zamo damuwata,Dan Allah yaya Dr.kataimaka,Ka dawo tamkar da,muci gaba da rayuwa cikin farinciki,miyi aure miyi irin Kala rayuwan da Mika tsara lokacin mina yara. Tana wannan tunanin bacci ya dauketa misalim karfe uku na dare ta farka,Samiha duk da shedan cinta da irin Kalan rayuwan da sike da Yaya Dr.hakan Bai sa ta zubar da addinim da take da shi a bayaba,illa iyaka karuwa da yayi domin a kullum tana ganin tana bukatar Neman yafiyan ubangiji domin lefin da take tafkawa,Bata wasa da sallah,Bata wasa da ibada,ba Kuma ta wasa da addua,to Amman mai yasa duk da irin wanann abubuwan da take aikatawa ta kasa kufcewa tarkon sa,ita kanta a kullum tana yiwa kanta wanann tambakar Amman ta kasa saminta,Amman karku damu alkalamina zai sanar muku da ita. https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf ABOKIN YAYANA😭 Zamina posting na wanann littafi abokin Yayana Sau uku a duk sati,Sannan adadin reacting posting dina da kuke shine zai karamin karfin gwiwa wajan tabbas kunajin dadin karanta wanann littafi,Amman muddin zanyi posting babu reacting a lokacin da kuka karanta,zanga tamkar ba karantawa kukayiba sannan bazan na samin karfin gwiwar posting ba,sannan Koda posting din Bai yi muku dadi ba,akwai alama da zaku danna wacca zanga Hakan at least de ace in de kukaga posting kuka karanta,kuyi liking wajan nuna alama,Wanann zai karamin karfin gwiwa,Sannan Kuma zan ware Rana Daya a sati wacca zan Bude group domin comments Daga baku nan ku,Nagode sosai da kasancewar ku cikin wanann group,Allah yabani ikon kawo muku abin da zuciyarku zatayi dadi. Page 2 Soyayyya ta zamo min Karfan kafa,ta zamo matsala ta,Bantaba tunanin soyayyyar Yaya Dr.Zata zamo matsala a rayuwata ba,Dan Allah yaya Dr.Ka dawo tamkar da,ka tausayawa Maraicina,a yanzu Kai kadene farinciki na da Kuma fatana karka bari rayuwata ta kare a haka,Kuma takeyi wiwi,ta rasa Mai ke mata dadi Tana cikin wanann tunanin ta mike domin Ta shiga tayi alwala,ta fito Ta dauki abin sallah,Ta idar da sallah tajira tayi sallan asuba,ta dauki kur'ani ta karanta yadda ta saba,duk da ba Wani nisa tayiba,Amman tasan surori da yawa,Wanann shine al'adarta Koda kuwa tana period Bata taba bari dare ya wuceta,ta kan raye daran ta wajan bautawa ubangiji da adduar Allah yakara shiryar da ita,Bayan ta kammala ta koma Kan gado domin taci gaba da bacci,Wanan shine al'adar ta akowane dare,Bata komawa bacci sai tagama duk wasu ibadu,kama Daga karatun alkur'ani da Kuma azkar sanann idan Takoma bacci da wiya kaga ta shi sai wajan azahar,ko Kuma idan yayan Nata yakirata wannan ita ce rayuwarta a kullum Bata da Wani buri ba Kuma ta da Wani fata,A yanzu Bata san Ina rayuwarta ta do saba. Samiha wacca ada take da buri na zama shahararriyar Likita,tamkar yayan nata ita ce wacca yanzu ta zamo Bata da Wani fata illla na zaman gida,har fargabar fita take saboda sa idon Jama'a,Gaba Daya rayuwar ta ta zama cikin kunci da damuwa,yah rabbi Ka kawomin agaji. A Dede lokacin tana tsakiyan bacci ne tayi mafarki da mahaifiyar ta,tana ce mata Samiha ki tashi tsaye ki gyara rayuwarki,hakika akwai dalilin faruwan duk wanann abubuwan dake faruwa dake karki bari rayuwanki ya lallace a aikin banza,kiyi yaki domin dawo da rayuwanki kamar da,kici gaba da addua,kici gaba da Neman agurin ubangiji inshallah zai shiryeki,Fitik ta mike sharaf da gumi jikinta,tana Kiran sunan Allah hade da zazafan hawaye a fuskarta,sallamar da ta Jine ya sa mata karfin gwiwar mikewa domin ta San wace Mai sallamar ita kadece wacce ke shigowa in da take tun bayan rasuwan mahaifanta,ita kadece wacce take shigowa ta Bata shawarwari wadan da ke mata dadi,ita kadece wacca ke jurar zama da ita,ita kadece wacce Bata kyamatar ta a halin da ta tsinci kanta,wanan dalilin yasa take matukar kaunar ta,yanzu a duniyar Samiha bayan Yaya Dr,babu Wanda take so irinta,Babu abin da Samiha baza ta iya yi mata ba in de tana da shi,domin ta gama mata komi a rayuwarta,Bata kya mace taba,bata nuna mata komi ba,Kamar yadda mutanan anguwan ke kyamatar ta,babu Wanda ke kulata ta Kai ta kawo manyan unguwar kansu ba kowa ke ansa gaisuwar taba,Hakan yasa ma ta hakura ta Dena gaida kowa,ita kanta da take zuwa gurinta,mahaifanta Basa so. Tayi kokarin ganar da su da kyar mahaifiyar ta ta fahinta ta bar ta taci gaba da mu'amala da Samiha,shima Dan anace ciwon ya mace na ya macane,Wanann yasa mahiafiyarta ta fuskance ta ta Kuma barta ta cigaba da mu'amala da ita,tare da fatan Allah ya sa yarta ce Sanadiyyar shiryiwar Samiha,Amman har yau duk da tsawon shekarun da suka shude kwata kwata mahaifinta yakasa fahintarta,Hakan yasa Bata samin Damar shigowa gurin Samiha sai bayanan. Wacece ita Wane matsayi ne da ita a gareta agurin Samiha Mai yasa take son zuwa gurin Samiha ? Mai yasa Kuma ta kasa rabuwa da Samiha? Cikin farinciki ta tsallako Daga Kan gado ta nufo falo da saurinta ta zo ta rungumeta ai nasani sarai Daman kina nan kina baccin asarar nan taki,ke bakki da aiki sai bacci,ke kullum baza ki Samu Wani Abu da zakiyi ba sai bacci. Dan Allah Samiha ki Samu ki koma makaranta,Koda baza ki koma Boko ba,ki koma islamiyya Hakan zai taimaka Miki wajan sake sanin abin da yake Dede sanann ya sa kisake rage abubuwan da kikeyi sanin kanki ne Bana son wanannan rayuwar da kike,Ina jin babu dadi idan naji yadda mutane ke xaginki acikin gari,Ina jin ciwo idan naji yadda ake muzantaki,Samiha Dan Allah ki gyra halinki,Besty shine sunan da Samiha takira da wadda ke mata maganar,sanin kanki ne kinsan ba haka nake ba,narasa Mai ya sauyani,narasa mia yasa na daukawa Kai na wanann rayuwan,Mai yasa haka ke faruwa Dani,a kullum addua ta Allah ya shiryeni ya Kuma gyaramin rayuwata,Kuma inshallah na tabbata albarkacin Imani da nayi da shi da Kuma addua da nake dare ba Rana,na tabbata xai shiryeni,zai Kuma dawo Dani Dede da izinin ubangiji,Nasani besty daga Daya bangaran matar tace da Samiha,Amman kisani kullum sake girma muke idan mune yau bamu bane gobe,Dan Allah ki gyara inshallah Samiha tace. Tom yanzu Zaki koma islamiyyar Dan Bata Rai tayi,tace kinsan sarai yadda mike karkewa da dalibai da Kuma Malaman makarantar,kwata kwata basa son ganina kowa kyamatata yake,sauran malan Kuma wasu Daga ciki suna wulakantamu saboda naki karbar soyayyyar su,nayarda na aure su,na rabu da Yaya Dr.ke kinsani duk Wani Abu da zai Nisan tani da shi Bana so Bana Kuma kaunar sa,na gwammatah na rayuwa da shi,shi kade cikin duniya Koda kuwa kullum zamu rayu cikin bani madaci da rayuwar axaba da yake yanzu. Nunfashi ta ja,Samiha wanann wane irin rayuwane mara karshe,Basma,sunan da naji ta kirane yasa na wai waya ita wacca aka kira da besty dazu Ashe sunan ta Basma,Sun ta so tun suna yara su uku acikin unguwar su,duk da cewa dukan yaran talakawane Amman suna da rufin asiri Dede gwargwado Sannan suna rayuwa cikin farinciki da aminci,Samiha,Basma,nihal,Su uku suka tashi a unguwar su,babu Mai jin kansu kullum suna tare makaranta Daya sukayi, Islamiyya da Kuma Boko,Kafin Kuma Samiha ta sauya halayyarta da Kuma dabi'arta,saboda tsabar amincin dake tsakanin su,Har suna suka hadawa junansu """Bashal""an dauki kalma dai dai cikin sunan kowa,Tom Amman yanzu Ina nihal,Ko ita ma ta guji sami hane?,ni kai na ban saniba Amman bincike zai tabbatar man da Ina take. Basma karki damu ajikina nakejin inshallah zamu rayuwa da Yaya Dr.zai aureni zakuma miyi rayuwa cikin farinciki,Amman Samiha Taya kike tunanin kunyi rayuwa irin wanann sanann Kuma kike tunanin zai aureki,tom idan ya aureki Mai zai Samu, soyayyya ta da Yaya Dr.ba soyayyya bace domin jikina ko Wani abin, soyayyya ce Daga ruhi zuwa gangar jikin mu,Amman Kuma kuke irin wannan rayuwar?,Basma baza ki Gane komi ba, kede kici gaba da tayani da addua, ubangiji ya kawomin komi cikin sauki alfarmar annabi, tomshikkelau Samiha inshallah da yardar ubangiji,Kuma nima Ina jin komi zai yi dede inshallah ngd sosai kawata Allah yasaka Miki da alkairai ngd sosai kawata. Bazan taba mantawa da halaccinki zuwa gareni ba,bazan Kuma manta dake a rayuwata ba,kidena min godiya domin ba Kawa na daukeki ba na daukeki ne tamkar yar uwata,bayan mahaliccina da manzonsa,da Kuma iyayaena,tom sonki me zai biyo Baya,Ina sonki fiye da komi nawa,nima Ina sonka Basma ta,ki tashi ki Dora mana girki,Aah nikam yau ba girkin da zan Dora duk ranar da zan yini agidannan gandarki baza ta bari kiyi girkiba,naki din sai da naci na koshin na taho ki ma tashi ki Dora,Dan Allah basmata Allah na gaji tomshikkelau bara na Dora mana,kinci abincin safane Aah,wai Mai yasa ba kyajin magana,Mai yasa kike wasa da lafiyarka,ki kwanta kiyi ta bacci mara amfani baza ki tashi kici abincin ba,yi hakuri besty kinsan bana son bacin ranki aishikkelau Basma ta furta tana nufar kitchen,babu abin da Basma ta tsana irin samiha tace Bata ci abinci ba,damuwar da ta Saka aranta har yakai tana kasa cin abinci. Samiha kuwa murmushi tayi tana kallon kawartata cike da farinciki da Kuma kaunarta,tana kaunar Basma tana son Allah Yabata abin da xata faran tamata,akoyaushe burinta shine ganin farincikinta. Shiga kitchen tayi tafara kokarin Dora musu abinci,Basma ki Dora da Yaya Dr.nasan tunda naga Bai zo da wuri ba yau anan zai ci abincin Rana,Allah ya kyauta shine abin da Basma tace,azuciyarta kuwa tace Banda masifa sunki rabuwa da juna,Sanna sunki yin aure,sanann rayuwa suke tamkar ma'aurata Amman Mai makon ace suna cikin farinciki kullum cikin fada ake,Kuma idan basu ga juna ba su tashi a hankali,Amman da Bafa haka rayuwar su takeba,tsaftatacciyar soyayyya ce a tsakanin su,Mai yakawo wannan sauyin Allah kashiga lamiran wannan bayin naka,Amman tabbas ina tausaya musu,suna cikin Wani hali Wanda ba kowa zai iya fuskanta ba. Bayan ta kammala abinci ta kawo musu zasuci,Haba Basma sai kace kin manta duk girman yunwar da nake ji Bana son naci ni kade,a takiace ma Bana iya ci idan har Baya nan, Aishikkelau Kun dorawa kanku aiki. Abincinta taja tana ci suna taba shira,sallamar da sukajini yasa su tsagaita zancan,Wani kayataccan murmushi ta fidda jarababbu shine ko,Dan daukanta tayi a kafada ta mike ta fita,sannu da zuwa Yaya,ko kallonta Bai yiba ya wuce daki,Yana zuwa

Chapter 1 of 15