ya kawo Samiha,wani dadi taji aranta da alama tabbas aikin boka yafara ci wata zuciyan tace mata bakki hankali kide jira ki tambayeta idan ta fadimiki dalilin faruwan hakan sai ki yanke hukunci nihal tsayawa tayi Samiha ta karaso nan suka gaisa,ya naga dady ya kawoki Ina Yaya Dr din? ko Baya gari.
Wani kallo Samiha ta bita da shi zata wuce tace ya ina tambayar ki zaki wuce idonta ne ya fara ciccikowa da kuka kasa tare hawayen tayi nan wani zazzafan hawaye ya fito daga cikin idanunta,gaban nihal yayi mugun faduwa duk da yadda take son raba Samiha da Yaya Dr Bata son bacin ran Samiha tana son Samiha sai de tanayiwa Yaya Dr son da baza ta iya hakura da shi ba,hakuri ta kafa bata tana son taji mai ne yafaru domin tana ganin alaman kamar aikin bokane yafara aiki zuciyarta cike da Wani farinciki wanda itama bata san sanadin saba.....
Mai ke shirin faruwa da wannan soyayyyar da aka gina shekaru ana ginata?
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf
CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER
*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~
Page 15
Haka Nihal tayi ta lallaba Samiha suka shiga ciki suka wani dan lungu suka zauna nan ta fara xayyana mata duk abin da yafaru Samiha bata iya fadin sirrinsu ita da Yaya Dr amman ranar taji baza ta iya boyewaba ya zama lalle dole ta fadamusu ko zasu iya samo mata mafita,nihal kinsani cewa ina son Yaya dr bana kaunar duk wani abu da zai jawo matsala tsakanin mu bansan mai yafaru ba amman Yaya Dr da kansa yau yace na rabu da shi na kyaleshi nayi nayi ya fadimin abin da na masa amman yaki, mutumin dake kishina baya son ko driver din gidan mu ya daukeni shine yau yace naje na napep na taho,nihal akwai matsala baxan iya ganin Yaya Dr a hakaba Kuma yaki fadimin Mai ke faruwa na yarda da son da yakemin tabbas akwai dalilin da yasa yafaramin wanann wulakancin tom amman abin tambayar shine Mai ne dalili?
Kuka ta cigaba dayi nihal gaba daya tarasa mai zatace tasan ita ce sila da Kuma sanadin komi ta rasa murna takeyi ko bakinciki,gashi de burinta yacika sun fara samin sabani hakan na nufin nan ba dad dadewa ba Yaya Dr zai ce Yana Sonta 'Alhamdulillah' farinciki ya sake bayyana a fuskanta da Kuma zuciyanta nan ta dake ta kawar da shi ta kuma bawa Samiha hakuri akan ta bari Basma ta zo sai su san mai ne abinya suna zaune suna jiran ta amman bata zo da wuriba sai da aka kusa shiga jarabawa hakanne yasa sukace abari idan anfito sa yi maganan.
Sun shiga hall din jarabwan amman abin da zai baka mamaki shine Basma takasa rubuta komi kuma bawai dan bata iyaba domin rashin kartunta najiya ba wai yana nuna bata san komiba samiha yarinayace mai matukar haxaka kafin mamalami yayi abu ita taje ta bincike ta sansa,kuma duk tambayar da akayi babu wacca bata saniba amman ta tsinci kanta wajan kin rubuta komi haka akayi jarabwan aka gama ta Mika booklet dinta batare da ta rubuta komi ba,futar su keda wiya akayiwa Basma bayanin duk abin da yafaru kukan da Samiha keyine yasa itama hawaye yafara yawo acikin kuncinta kiyi hakuri na tabbata akwai dalilin faruwan haka yadda Yaya Dr yake sonki haka kawai ba zai aikata miki hakaba ki kwantar da hankalinki ki maida komi bakomi ba dole sai kin nutsu zamu Sami mafita yanzu Abu na farko da yakamata miyi shine mai nene dalilin da yasa Yaya Dr yake miki haka daga nan Kuma sai misan hanyar da zamubi wajan gyra komi,caraf nihal ta katse su babu wani dalili sai de halinsu na maxa kinfi kowa sanin su waye maza idan suka so rabuwa da Kai duk da hakama dole miyi bincike ba zamu yanke masa hukunci lokaci daya ba,haka Basma tayi ta kwantar mata da hankali har suka ta shi,da ta fito wani zazzafan hawaye ne ya bayyana a fuskanta da tuni fa yanzu yaan nan yana jira ta fito su tafi,ji tayi gaba daya ta muzanta duniyar ta dena yimata dadi bata san lokacin da hawaye ya wanke fuskantaba nihal ce ta jiyo tace mata ke wai ba za kidena bata wanann hawayan naki masu tsada a aikin banza ba na fadamiki inshallah zami sami bakin xaran komi zaiyi Dede,alokacin driver din Basma ya zo tace mata ta zo su shiga su tafi haka tabita jiki babu kwari.
Bayan ta koma gida yanayin da momy ta gantane yayi matuakar firgitata idanuwanta gaba daya sunyi lubu-lubu sunyi jajir tsabar kuka ta sowa tayi tana tambayarta Mai yafaru da ita cikin karfin hali tace mata "Babu komi momy kawai de kai nane kemin ciwo Kuma ya takuramin sosai "Ayyaha!!! maza jeki cire kayan makarantar ki fito kici abinci Kisha magani kije ki kwanta dan babu wata islamiyya da zakije yau yanayin jikin naki daga gani yana takuramiki,itama daman bata tunanin tana da karfin halin da zataje islamiyya haka ta shiga da kyar ta iya watsar ruwa ta fito,momy har ta zuba mata abinci zama tayi xataci amman da mamaki tana fara ci ta fashe da wani matsiyacin kuka mai rikirkita zuciyar duk wani mai sauraro lokacin momy ta tashi taje dakko mata magani,abin da yasa ta kuka ta tuna tunda take koda da makaranta Yaya Dr sai yabaro ya zo sunci abinci tare amamn wai yanzu it ce ke cin abinci babu shi,adede lokacin Yaya Dr yayi sallama dagowa Kai tayi ta kallesa suyi Ido hudu kawar da kansa yayi Yana yunkurin shiga dakinsa da sauri ta taso ta zo kusa da shi ta zube dan Allah Yaya Dr kadena wahalar min da zuciyata haka bazan iya jurewa ba,kada Kai kade da karagemin Kai ma ka rabu dani,dan Allah Kayi hakuri akan duk abin da na maka tsuka yayi yayi ball da ita ya wuce daki, "Innalillahi wa inna Ilaihi raji'un "shine abin da take ta furtawa na shiga uku ya zanyi da rayuwata nan ta kwanta tayi ta rusa kuka anan momy ta zo ta sameta Samiha lafiya ko kan ne daga mata Kai tayi domin bata da bakin da zata iya yin magana,tom ai bakici abincin ba bare iisha magani bazan iya Ciba momy,yanayin halin da Samiha ta shiga yayi matukar tayar mata da hankali bara Suraj ya dawo muje asibiti,cikin zuciyarta tace in de yaya Dr ne ya dade da dawowa yana daki momy ce ta tallafamata suka shiga daki ta kwanta da ita amman duk hankalinta a tashe sakamakon ta kasa cin abinci bare ta Sha magani.
Jiki babu kwari momy ta fita daga dakin tom lafiyar Samiha kuwa? tana fitowa sukaci karo da Suraj ya fito wato Yaya Dr daman kadawo gidan tom maza shirya bara naje na shirya Samiha zaka kaimu asibiti,momy Ina da uzuri yanzu ma ta kardu na zo dauka zan koma makaranta kisa driver ya kaiku kawai ya wuce ba tare da ya ko kalletaba,suman tsaye momy tayi anya kuwa auraj dintane Suraj din dake hakura da jarabawa saboda matsalan Samiha inde abu na tane yakan hakura da komi domin ta amman shine yau yake fadimata cewa driver yakaisu yana da uzuri gaba daya ruwan jikin momy ya kafe tom maike faruwa?ita de ta sani ko fada sukayi suna shirya kansu kafin wani yasani Kuma duk fadan da sukayi basa taba yini ba suyi maganaba bare su rage kulawan da suke bawa juna tabbas akwai wani abu da safema haka yaki kaita makaranta,amamn de bazan yi saurin maganaba bara na zuba musu Ido nasan zasu gyara komi............
Dullokacin da kake tare da masoyinka yana da kyau murika addduar Allah yakare soyayyyar mu Daga sharrin makiya,domin babu abinda dan Adam mara tsoron Allah bazeyiba saboda cimma burinsa
Ubangiji Allah ya tsaremana imanin mu ya hanemu kokarin lalata farincikin wasu saboda namu yakuma rabamu da kawaye makirai.
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf
CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER
🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~
Page 16
Haka momy ta xauna da tunaninka nika iri-iri aranta tabbas akwai wani abu tsakanin Suraj da Samiha amman Mai nene shi mai ne ke shirin shiga rayuwarsu ya bata farincikin su,yah Allah na rokeka ka kawo komi cikin sauki domin kasancewar yarannan cikin farinciki shine abu mafi muhimmanci da nafi so a rayuwata yah Allah Kaci gaba da tabbatar da farincikin su wanan abun ko mai ne shi dake kokarin shiga tsakanin su kada ka bashi dama,haka tayi ta addua har ta gaji da zama tashi tayi takoma dakin samiha ta isketa tana bacci sai taji dadi domin tasan zata Sami nutsuwa, dawowa ta itama ta shiga dakinta tace idan dady ya dawo sai suje asibiti.
Fitar yaya Dr ke da wiya adede lokacin Nihal zata shigo gidan basarwa tayi Kaman bata Gansa ba cikin sauri ya matsa yayi mata magana Nihal shine kina ganina zaki wuce ko gaisuwar babu afuwan ban kula ba Ina yini,ba tare da ta tsayaba take yin gaisuwar lafiya lau fatan kina lpy alhamdulillah gabanta yasha yace dan Allah nihal ki dan tsaya ina son xamiyi maganane fa mai matukar muhimmanci Ina sauraronka
Nihal dan Allah kiyi hakuri da irin abubuwan da nike miki abaya na rashin ganin girmanku,nihal zuciyata ruhina da kuma gangar jikina sunfada soyayyyar ki a lokacin da basu tsammata ba kada kiyi amfani da abubuwan da nayi muku abaya kice ba kya so na dan Allah, idan har kikaki amincewa da soyayyya ta tabbas zan shiga cikin wani yanayi wanda bansan kalar saba ina matukar sonki nihal.
Dadi har tsakiyar Zuciyarta wayyoh dadi ynz ita Yaya Dr zai ce Yana so na yau wace iriyar ranar farinciki wace rana ce wacca bazata taba mantawa aryuwar taba ji tayi tamkar tayi tsallle saboda tsananin murna,amman sai ta make tace "Wane irin tunani gareka da wane Ido zaka kalleni kacemin kana so na ka manta budurwan ka Samiha wacece agurina taya zanyi soyayyya da saurayin kawata"
Dan Allah Samiha kada kice Aah ni yanzu bana son Samiha ke nake so dan Allah kada kice Aah saboda ita,kuma idan kina ganin zata Miki kallon banzane sakamakon soyayyyar mu tabbas zanje na fadimata da Kai na ni a yanzu kece wacca nake so Kuma dake zanyi soyayyya eh toh idan kayi hakan watakil xan iya amincewa mi shiga gidan ma na fadimata agabanki Aah kabari de ka fadimata daga baya saboda karkasa taga lefina tomshikkelau duk yadda kikace haka za ayi,nagode sosai Samiha da Baeki amince dani ba bansan yadda xanyiba nagode sosai,kaga kadena wata godiya saboda har yanzu ba wai na amince da Kai din bane nasan zaki amince ma.
Shigewa tayi ta barshi anan yana sambato,ita ko tana cewa aranta ashe haka aikin boka yakeci amman na tsaya da Ina ta bata lokacina alhamdulillah yanzu na xama (MRS SURAJ YAYA DR),gaksiya yau ranace ta musamman agurina bansan da wane suna zankirata ba,shigarta ciki keda wiya ta iske momy a falo suka gaisa tace mata Samiha na ciki tana ciki nihal amman bata jin dadi da kyar yanzu dana koma dakin naga bacci ya kwasheta amamn ki shiga kiga ko ta tashi Aah momy batta dan dazu ma a makaranta tacemin jiya batayi bacci ba kinga tunda yanzu minsmau tayi kar a tashe tomshikkelau nihal,sai anjima momy idan ta tashi kice mata na zo,tom nihal kigaida babartaki.
Nihal ce ta futa daga cikin gidan zuciyarta fes ranta kal tana Jin dadin ta sami cikar burinta bata tsaya ko Ina ba sai gidan su Atika nan ta labartama ta dukkanin abin da yafaru,nan sukayi murna matuka daga nan ta wuce gida,bayan anyi sallar magrib Yaya Dr ya baro makaranta zai dawo gida yaga ba zai taba jurewa ba sai ya karasa gidan su nihal nan ya dedeta sitiyarin motarsa yayi gidan su Nihal,ya Saka akirata yacewa yaron yace mata Yaya Dr ne,yaron ya shiga tace waye? Yace yace"Nace Miki Yaya Dr ne"wani wawan tsalle ta daka tace kace masa Ina zuwa,boka yabata Wani turare yace duk ranar da Yaya Dr ya zo ta tabbatar da fesashi ajikinta wanann zai sa bazai taba barintaba zai yi ta zama da ita har abada son kaunarta zata cigaba da ruruwa acikin zuciyarsa,nan ta shirya tsaf taci ado ta danko wannan turare ta shafa yana da matukar karfi sanann an hada shi da sinadarai kala-kala na asiri wanda duk karfin tsarinka kaji shi sai yakamaka,nan ta fito tana tako dos-dos tundaga nesa Yaya Dr yake kallonta yaji tamkar ita kadece kyakkyawa adinya ji yayi ya matsu ta karaso domin ya matsu yaga tana kallonsa da kyawawan fararan idanuwanta.
Tana karasowa tayi wani juyi akusa da hankali wanda sai da yakusa zautar da shi jiyayi kamar ya rukota amman wata zuciyar nace masa karka fara irin wanann soyayyyar yadda katsaratar da imaninka akan soyayyyar ka da Samiha baku taba sabawa ubangiji ba yanzuma kayi hakan kuyi soyayyyarku sai ka aure nihal da wuri yadda xata zama mallakinka kasami damar yin komi da ita
Yana cikin wanann tunanin tace"Barka da zuwa Yaya Dr "barka farincikin raina fatan kina lafiya yasu mama alhamdulillah,nakasa jurewane har zan wuce gida naji bazan iya jurewaba sai na zo na ganki,ina sonki nihal dan Allah ki daure ki karbi soyayyya ta,kada kadamu Yaya Dr Nima Ina sonka Ina kuma kaunarka amman bazan taba ansar soyayyyar kaba sai kafadiwa Samiha tukun dan bazan zo nafara soyayyya da Kai ba Kuma daga baya tana sani a sami matsala babu wata matsala da za asamu Samiha na son duk wani abu da nake so,dariya tayi tace"Bandade wanan taya kake tunanin Kuna soyayyya kadawo guna kace zata so hakan kadeje kafidimata"shikkelau inshallah nayi miki alkawarin xan fadamata tom،murfin mota ya Bude ya dakko wata katuwan leda ya Mika mata mai ne wannan?ki buda xaki gani naje na Danyi yomoki shopping ne na kayan ciye-ciye em nagode sosai zan koma sai da safe,tom sai da safe farinciki na Yaya Dr yace.
Nihal juyawa tayi ta nufi gida ta rasa yadda xata kwatanta farincikin da take ciki ashe haka bokaye suka iya aiki(auzubillahi ya Allah katsaratar mana da imaninmu)
Yaya Dr yakara gida ya tarar da momy dady Samiha suna zaune,bayan dawowar dady Samiha ta tashi sai ta fadimasa bata jin dadi yace taje ta dubo idan ta tashi ta duba ta tashi,"Shine yace tazo suci abinci sai yakaita asibita aduba mai ke damunta"adede lokacin da zasu fara cin abincin Yaya Dr ya shigo nan ya tarar su ya gaidasu momy tace Ina katsaya yau momy na tsaya a makarantane kinsan saura jarabwa daya migama,nan tace ya zo suci abinci,Samiha murna tayi matuka da taga Yaya Dr ya xana zasuci abinci tare wannan ne yabata karfin giwawa tayi tacin abinci dayawa batare da ta saniba momy taji matukar dadi, alhamdulillah Samiha da alama kin fara samin sauki gashi kinci abinci da yawa momy gashi nande karamin ma na kusa cinyewa nan bayan sungama dady yace "ta tashi suje asibiti"Aah dady jikina yayi sauki fa kawai zan Sha magani na nane momy tace eh kabari miga zuwa gobe idan ciwonkan ya sake tashi sai aje okay tom,nan momy ta bataa magani tasha tace musu sai da safe zataje tayi sallah ta kwanta duk abin da akeyi Yaya Dr yana kallon su cikin sa Bai ce musuba,nan ta koma daki bayan tagaama komi ta kanwata ta janyo wayan momy lamabar Yaya Dr tadanna ta tuna kullum muryanshi ne abu nakarshe da take ji amman yanzu abu yagagara Mai nayi maka Yaya Dr?mai nayi maka?nan ta kace da wani kuka Mai matsanancin kunci kukan yinsa take tunkarfi har sai da nunfashin ta yafara daukewa.
Takasa dedeta kanta sai ta tsinci kanta da furta "Innalillahi wa Ina Ilaihi rajiun allahumma ajirni min musibatin wa aklifni kairan Minha"
Haka tayi ta furtawa tukunna ta dan sami sauki cikin zuciyarta amman ita kade ta San Mai takeji aranta.
Adede lokacin ne yaya Dr yayi sallama ya shigo cikin dakin kamar daga sama taji hamdala tayi tayi aranta da alama koma mai nene yanzu yaya Dr yadena fushi da ita tunda har shigo cikin dakinta,da suari ta mike daga kwanciyar tace"Yaya dr shigo mana"fuska a murtuke ya shigo,na zo ne Ina son xamiyi magana Ina sauraronka.
"Nan yace mata Samiha nine wanda ada nace Ina sonki alokacin babu wanda ya tambayeni dalili Kuma idan nace Bana sonki babu wani wanda ke dadaman tambayata dalili,Samiha Ina son daga yau ki fidda tsari da tunanin rayuwa tare dani Bana sonki bana kaunarki yanzu,Ina son na fadimiki cewa nihal kawarki ita ce wacca nake so a yanzu Kuma nake son ta zama uwar yarana,Ina son kisani cewa kada kiyar kice zaki nunawa su momy damuwarki,ki nuna musu ke kika amince da hakan domin Idan bakiyi hakan ba gaisuwa ma da kyar zatana shiga tsakanin mu,amman idan kikayi Hakan shikkelau zamuci gaba da rayuwa yadda muka saba a amtsayin yaya da kanwata".........
Mai zai faru da Samiha sakamakon Jin wanan maganar?
Wanann wace iriyar musibace ke faruwa da Samiha
Samiha tunda ta so ta taso cikin jarabwan rayuwa
Ta rasa mahaifanta da Yan uwanta duka
Ga yanzu shima Yaya Dr din da ta dauka a matsayin jigonta ya gujeta
Da wane Ido nihal zata dubi Samiha a amtsayin sabuwar budurwan Yaya Dr
Alkalamina na tafe da dukkanin wanann tambayoyi
(Yah rabbi mina ta wassali da sunayanka tsarkaka ka tsermana imanin mu karabamu da son zuciya albarkacin annabi)
Page 17
Amman tabbas kika yarda kika nunawa su momy cewa ni namiki tilas akan ki rabu dani ba ra'ayin kan kibane narantse da Allah zaki rayu cikin kunci damuwa bakinciki acikin gidan nan,idan kinkiyaye kintaimaki rayuwanki.
Kalaman Yaya Dr sunayiwa Samiha nau yi kasa furta komi tayi ta sake dedeta zamanta mikewa take kokarin yi ta dawo kusa da shi domin ta fuskanci abin da yake nufi amman takasa,wanann wace iriyar Bakar ranace,wanann wace iriyar kaddarrace ina ma na mutu na huta sai yafi min akan ganin wanann rana mai cike da damuwa da kunci Yaya Dr mai yasa? acikin zuciyarta take fadi amman batasan cewa maganar ta riga da tafito fili ba, ji kawai tayi yace sai ki mutu ai waye keda asara jitayi zuciyarta tace dirim mikewa tayi da karfi ammmn Ina jigib kakeji ta fadi a kasa bata ko nunfashi bare motsi da gudu ya matsa inda take Samiha yafara Kiran sunan ta hakanne yasa shi matukar tsorata sai de da yake likitane ya fuskanci suma tayi hakanne yasa ya jawo hijab ya saka mata dau kanta yayi cilak yayi waje da ita momy da dady na zaune sunyi matukar tsorata Suraj lafiya mai yasami Samiha babu komi momy ta fadine mina magana momy hijab dinta ta dakko ta Saka ta bishi tare suka tafi asibitin suna zuwa aka Kai ta emergency nan akayi maxa aka bata taimakon gaggawa lokaci daya numfasin ta ya dawo sama-sama duk da bata farfado ba bacci ya dauketa,sai a lokacin hanlinsa ya dawo domin duk da andauke masa hankalinsa daga kan soyayyyar ta amamn akwai wanann soyayyyar ta farko ta Yan uwantaka a tsakaninsu.
Bayan wani lokaci Likita ya zo yace yana tausayin son ganinsu bayan sunje yace"Tabbas akwai gagarimin abin dake damun wannan yarinyar kuma idan ba ayi gaggawan shawo kan lamarin ba zuciyarta zata iya bugawa saboda yanayin abun dake cikin zuciyarta ba karami bane ta saka tunani aranta matuka Kuma tabbas idan ba a samar mata abin da take so ba za'asami matsala"momy ce ta dago kai ta Kalli Suraj ta tambayesa mai yake damun Samiha?momy ban saniba ni Kai na nayi mamaki da yace tana cikin damuwa momy ban saniba,amman kwana biyu naga yanayin rayuwar da kuke mai yasa ba kwa kula juna haba momy kinsani cewa sarai minsaba irin wanann idan mikayi fada,tom amamn Mai kaje kace mata a daki har yayi sanadin faduwanta babu komi momy na shiga mina Shira ta tashi kawai sai ji nayi ta fadi .
Innnallillahi momy take ta furtawa tabbas Samiha ta zamo wani jigo na gidan mu rayuwan gidan baza ta taba tafiya dede ba tare da ita ba, inshallah zan samawa Samiha abinda take bukata ko zan rasa farinciki na.....
Yau ba ranar posting bace na baku dan kadan saboda nayi making day dinku
Thank you masoyana Allah yaci gaba da kareku
Page 18
Cikin gaggawa da sauri ya shigo cikin dakin Kai tsaye kan Samiha yayiyo saboda ji yake kamar yakasheta saboda masifar bacin ran da yake ji akanta ta rasa waccaa zata batawa rai sai farincikin sa abin kaunar sa nihal,gabanta yaje yace ke Samiha ashe Baki da hankali har kinsami karfin gwiwar batawa nihal rai daga hannu yayi ya wanketa da mari irin wanda tunda ta zo duniya babu wanda ya taba yi mata irinsa tabbas marin Yana da matukar zafi amman zafin sa ba shi ya sanya Samiha kuka ba,bacin rai da bakinciki shiya sakata kuka yanzu ita yaya dr ya daga hannu ya mara mutumin da ko kuda yaga ya zo wucewa daga inda take sai ya kawar mata(innalillahi wa inna Ilaihi raji'un waannan wace kalar sabuwar jarabawar nake ciki) yah Allah na rokeka kabani ikon jure wanannan sabon bala'in da ya riski rayuwata kuka take mai matukar zafi da tsuna zuciyata Basma tsabar bacin rai da bakinciki da yadda kukan Samiha ya gigitata batasan lokacin da ta zo aguje tace
"Haba Yaya Dr wannan wane kalar abine baka da hankaline ko kasha wani abine ya gusar maka da hankali yarinyar tana kwance a gadon asibiti zaka zo Kayi mata kalar wannan marin,kuma in banda toshewar kwakwalwa taya samiha da take kwance xata aikata duk wanannan abubuwan da waccar minafikar ta fadamaka tom Samiha bata yi komiba tana kwance ni nayi mata komi Kuma ni naci mutuncin ta ni xaka hukunta ba ita"
Yayi matukar mamaki da magan ganun da Basma tayi masa matar da take Jin tsoron sa da fargaban sa ita ke masa wanann magan ganun daga Kai yayi yace
"komai ne ni ba matsala ta bane kawai baba bukatar acigaba da batawa nihal rai Wallahi dagake har Samiha duk wanda yayayarda yakara furta kalma mara dadi akanta zanyi ji masa rauni"
Fu yafita kamar an han kadasa Basma ita ma bata san lokacin da ta fashe da kuka ba ta zo ta rungume Samiha tana Kara bata hakuri cikin kuka haka sukayi tayi har sukayi ya ishesu bayan anyi sallan magriba Basma ta taimakawa Samiha taje tayi alwala sun idar da sallah kelan sai ga momy ta shigo da kulan abinci Basma ce ta mike dan taimaka mata.
Momy ce ta Kalli Samiha tace "Ya jikin naki"da suaki sosai momy likita yacemin xasu iya sallamar mu gobe nan momy ta Saka Basma ta hadawa Samiha abinci amman Ina cin abincin yagagara kawai ta fashe da kuka matsawa kusa da ita momy tayi tace
"Samiha a yanzu baki da wasu iyaye da suke waucemu ke ya tace ni kuma mahaifiyar kice dan Allah ki fadimin matsalarki ki fadimin abin da yake faruwa na tabbata inshallah ba zai Fi karfin mu baIna sonki Samiha ke ma dayace daga cikin yarana babu abin da bazan iyaba domin ke dan Allah ki fadimin abin dake damunki "
Matukar karfin hali Samiha tayi ta tseda hawayen da ke cikin idanunta momy nasan kinyarda dani kin Kuma san bana miki karya momy banda ciwon kan dake damuna babu wani abu da yake damuna,momy ke mahaifiya tace idan ban fadimiki abin dake damuna ba wa zanfadawa hakane Samiha tom Allah yabaki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 15