Share this page
ba cikin hayyacin kuba itama momyn ki abin da tayi ba aikin hayyacinta tayi ba Ina fatan Zaki yafemana sanann ki tashi ka hado kayanki mu tafi gida. Wani sabon kukan farinciki ne ya kwacewa Samiha alhamdulillah alhamdulillah shine abin da take furtawa,momy tace "Samiha dan Allah ki yafemin inshallah haka baza ta sake faruwa ba" Dan Allah momy kidena ke mahaifiyata ce damab ban kullace ki da komi ba Ina fatan kema xaki yacemin duk wani abu da na miki " Nan suka shiga daki aka hada kayan Samiha suka koma gida. Wanann kelan ............... (DUK ABIN DA YAYI FARKO A RAYUWA DOLE ZAIYI KARSHE BABU WANI ABU DA YAKE DAWWAMAMME DUK WANI WANDA YAYI HAKURI TABBAS KARSHAN HAKURINSA NASARACE BABBA). yanzu aka fara wasan kuci gaba da bibiyar mu acikin wannan littafina mu mai suna ABOKIN YAYANA. Ubangiji ya datar damu ya sake rufamana asiri duniya da lahira ya zaba mana dukkanin abin da yake alkairai a rayuwanmu kar yabar mu da zabin zuciyoyin mu, ubangiji Allah ya rabamu da mummunar kaddara🤲🏼🤲🏼🤲🏼. Taku a kullum ZAINAB NASEER (ZEEY NASEER). Ina godiya agareku masoya da jimirin bibiyata. https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf CREATED AND WRITTEN BY ZEEY NASEER *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~~~ Page 29 Sun tattara kayan Samiha gaba daya sunkoma gida,BASMA kuwa tarasa yadda zata kwatanta farincikin da take ciki tabbas babu abun da yafi karfin ubangiji duk wanda zai mika lamarinsa ga ubangiji ya isarmasa zai sami duk wani biyan bukata,bayan sun karasa gida suka isa dakin samiha tsaf yake saboda momy kullum sai ta shiga ta gyarsa cike da kewar Samiha. Nan suka saka kayan suka fito bayan sun zauna momy tayi ta musu nasiha akan sukara dankon amintarsu sananan Kuma suna yaki da zuciyar su adullokacin da sukaji shedan yaraya musu su cutar da juna,Samiha basma kawace ta gari duk runtsi duk wiya karki yarda kirasata ki Kara riketa hannu bibbuyi inshallah momy. Samiha ce ta sakko kasa tace "Momy Ina mai neman afuwanki akan dukkanin abinda na miki kiyi hakuri ki yafemin inshallah zanyi iya bakin kokarina wajan kiyaye aikata ba dede ba,nagode sosai da sosai da irin rikon da kulamin ubangiji Allah yabiyaku" Momy ce ta kama hannun Samiha ta tasheta haba samiha bakiyimin komi ba dukkanin abin da yafaru ai ba lefin ki bane saboda haka ki kwnatar da hankalinki ubangiji Allah ya yafe mana baki daya. Nan sukayi Shira ta dan lokac kadan Basma ta tashi tace zata tafi gida nan sukayi mata godiya matuka,kamar yadda Samiha ta saba ta tashi tayi musu abincin dare kai abin ya baka mamaki matuka sai taga kaman ba itaba,tana tsakiyan aiki Yaya Dr ya shigo motsinta da yaji a kitchen ya sa ya shiga nan yakama mata aikin kamar yadda suka saba a baya ya tayata suna shira sun farinciki. Rayuwa ta cigaba da tafiya musu cikin farinciki da nishadi sunkuma sake rike addu'a da karatun allura hannu bibbiyu domin cigaba da kaucewa shedanu irin su nihal. Yadda suka saba ba wanda zai ci abinci ba tare da dan uwansaba Kuma yanzu da yake yagama makarantar masa shine ke tayata komi,duk da yana business amman business yafi ta allaka da online zai yi order din kaya za akawo za a zuba su a shago tom yaransa ke zama ba shiba,shi iya Kaci yana tallata kayansa ta wayane Kuma alhamdulillah yana samin matukar samu saboda kasuwar tasa ba karama bace, alhamdulillah komi yana tafiya dede. Ranar dady ya xaunar dasu yace "Kaga yanzu kagama karatunka na likitanci wanda shine burinka Ina ganin yakamata ayi wani abu wanda zai taimaka maka wajan taimakon al'umma da ilimin da ka samu,na yanke shawarar bude maka asibitin ka na ka nakanka sai ka dauki duk ma'aikatan da kake bukata amman ya ka gani" Nagode sosai da sosia dady na dade Ina wannan tunanin araina amman kaga zantafi bautar kasa, ta Ina abin zai tafi yanzu idan ka tafi bautar kasar ka kafin kadawo komi ya kammala ya dedeta kana dawowa sai de shirye shiryen diban ma'aikata hakane dady ,nagode sosai da sosai ubangiji yakara budi. Ke Kuma Samiha ga matsalan da aka samu akan jarabawarki na yanke shawarar zan siya miki wata,Aah dady kabari zanyi jarabawa da kai na shekarar kaman yanzune zatayi na fi so ace da Kai na na rubuta jarabawata tomshikkelau Allah ya nuna mana da rai ubangiji Allah yayi muku albarka ameen dady . Basma tayiwa su Yaya Ahamd bayanin duk abin da yafaru saboda tsabar farinciki Yaya Ahamd har azumi yayi na kwana uku na godiya ga Allah da ya kawowa Samihan sa mafita,abin har mamaki yake bawa mamansu tabbas Ahamd na son Samiha amman babu yacca zai yi dole yayi hakuri. Ranar Samiha na zaune ita da Yaya Dr sukace Yakamata su shirya suje gidan su Basma domin yiwa mama godiya akan taimakon ta agaresu,bayan sun shirya suka biya wani gurin siyayya sukayi mata siyayya matuka leshine,atamfa shijabbai dan kunnaye,haka de suka hada mata ka yayyaki,Samiha tace "Yaya Dr mai yasa kace mu tsaya miyi mata siyayya"?domin a duniyar nan babu abin da ya kai kyautatawa dadi,aduniyar babu abin da yakai inde kana da shi ka kyautatawa mutanan da ke so ka domin Allah,duk kudin su duk mulkin su inde ka kyautata musu xasu ji farincikin abun aransu zakuma suji dadi, shiyasa kikaga inde Ina da shi bana kyashin kyatatawa kowa domin kyautatawa tana Kara soyayyya tana kuma tafiyar da makiya,hakane Yaya Dr Ina fatan ubangiji Allah yabani ikon koyi da halayanka na gari ameen Samiha ta. Haka sukayi ta shira har suka karasa suna zuwa suka tarar da yaya Ahmad zai fita gurin aiki, ya tsaya ya karasa gurin su suka gaisa sosai cikin faran faran yace "Allah yayi ma xamu gaisa fita xanyi amman alhamdulillah naji dadi da Allah yasa kuka sameni" Ayyah babu komi Ahmad ai anriga anxama daya inji Yaya Dr,dan made kai ka zubar da zumunci baka dan lekawa gida. Abubuwane yanzu duk sunmin yawa baba ya ajje komi na company nike yi shiyasa amman inshallah zan na kokartawa Ina zuwa tom Allah yayi mana jagoranci ameen ameen. Nan bayan sun gama Samiha tace "Yaya Ahamd Ina kwana fatan kana Lafiya"alhamdulillah Samiha yagida lafiya lau mashallah ya juya yace tom na tafi okay Allah ya tsare sukace masa a tare. Suka shiga gidan shi Kuma ya shiga motarsa yafita. Basma na zaune a parlour sukayi sallama murna kamar ta kasheta nan ta tarbesu ta kawo musu ruwa da abinci,sukace mata sunzo gurin mama ne ta kira musu ita ,mama ta zo hakika taji matukar farincikin ganin su a haka rayuwan su tayi kyau alhamdulillah. Nan sukayi mata godiya matuka,ita Kuma ta sake yi musu nasiha da kokarin tsare kansu daga mugun nufin duk wani mugu. Suka tashi suka koma gida wal wala da farinciki cikin fuskansu,yau kimanin wata uku kelan da dai daituwar al'amiran su shine ya Kai kimanin wata biyar da barin nihal daga cikin garinnan. Kamar wasa Basma da Yaya Ahamd sunfita zasuje unguwa ranar ma gidan su Samiha zasuje kawai sunzo wucewa sukaga wata mai ciki cikin nata ya tsufa da alama takusa haihuwa domin yadda cikin ya zama katoto sosai Basma ta tausaya mata yadda take tafiya da kyar son tsallaka kwalbati take amman takasa cikin sauri Yaya Ahmad yace Basma je ki taimaka mata,da sauri ta karasa sannu baiwar Allah nan ta kamata suka tsallaka wannnan kwalbatin nagode sosai baiwar Allah tunda nake son tsallaka wanann guri amman ya gagara nagode sosai,gaban bamsa ne ya fadi saboda muryar da taji tamkar ta san muryar juyowa tayi da sauri domin tabbbatar wa idanuwan ta abin da take zargi aiko abin da take zargi shine ya tabbata wannan matar ba kowa bace illa nihal,Basma ce ta kama sunan ta nihal da sauri ta waigo taga ashe Basma ce matar da ta taimaka mata cikin sauri take ta sauri domin bata son ta sake furta wani abu nihal ki tsaya mana miyi magana Yaushe kuka dawo yaushe kikayi aure Ina ai nihal ta manta da cikin dake jikinta saboda tantarayyar tashin hankali gudu tafara mai isarta ... Ikon Allah!!! ta koma gun Yaya Ahmad kasan wacece waccan Aah,nihal cefa wai Allah!!!! daman tayi aure ne?shine tambayar da nake tayiwa kai na Kuma kaga da ta ga ni ce sai taki tsayawa ta gudu, koma de mai nene ita ta sani ki kyaleta ita ce a wahale hakane Yaya,haka sukayi ta shirarsu har suka karasa gidan su Samiha suka shiga a parlour suka iske su baki daya nan suka gaida momy Ahmad ya koma kusa da Yaya Dr domin yanzu sun zama amine kullum suna cikin Kiran juna ko zuwa gurin juna,haka suka zauna akayi ta shira har da momy dady Kam Yana gurin aiki. Can Basma takasa jurewa tace wai kunsn mai Aah,yanzu fa nihal na gani a hanyar tahowar mu gidan nan..... Tashin hankali ba asaka masa rana shi Kuma alhaki ai abiye yake da kai duk abin da ka shuka shi xaka girba kuci gaba da kasancewa dani acikin littafin ABOKIN YAYANA...... Taku a kullum ZEEY NASEER. https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf CREATED AND WRITTEN BY ZEEY NASEER *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~~~ Page 30 Da sauri Samiha ta dago kai tace nihal Kuma Basma,yaushe ta dawo ko ta zo yin wani abune gaba daya Samiha ta tsorata lokaci guda jikin ta yayi sharaf da gumi kana gani kasan tana cikin matsanancin tashin hankali da damuwa,ke miye hakanne ki kwnatar da hankalinki bafa ca nayi miki lokacin mutuwarki yayi ba kiga yadda kika bi kika daga hankalinki miye ne hakan Kuma,baza ki ganeba Basma bana son duk wani abu da zai sake jefani irin kalar halin da na shiga abaya kar ki damu da can ma ba ita taje faki ba,Allah ya riga ya kaddara hakan na rubuce acikin littafin kaddararki nihal Kuma ita ta zamo sanadi saboda haka ki kwnatar da hankalinki. Yaya Ahmad da yaya Dr sosia suke tayi mata dariya saboda yanayin yadda ta tsorata yayi matukar basu mamaki,matsoraciya kawai Yaya Ahmad yace,Yaya Dr kuwa ya ma kasa tsagaitaqa da dariyar saboda yana iya tuna duk abin da yafaru ya tabbata shine abin da yasa tayi wanannan tsoratar. Kuka Samiha ke kokarin kufcewa da shi momy ta daka musu tsawa ku miye ne hakan manyan banza zaku sakata agaba Kuna mata dariya saboda rashin mutunci lokaci daya sukayi shiru kowa yace shikkelau kiyi hakuri yar momy. Momy tace "Dariya ba ita bace abin da yaka maceku Kamata yayi ku fara bincike akan abin da yasa nihal ta dawo garinnan,duk da cewa daman kunce min da yiyuwar zasu dawo domin babansu yafi son xaman nan,sanann ku binciko ya akayi take da ciki ko aure tayi".Amman momy duk mu ina ruwan mu da wanann yaya Dr ne ke fadin haka ,idan Kai babu ruwanka da shi mu ai muna da ruwa da shi inji Samiha. Inshallah xamu binciko momy Yoh kodan mu tsuyeta mi dan dana mata irin kalar madacin da ta dan dana mana ai ma yi bincike akayi. Nan Basma da Samiha suka mike Ina xaku?zamuje gidan su nihal ne,mai zakuje yi gidan su karkuje ku ballomin rigima karki damu momy duk abin da akeyi maman su bata saniba bata da masaniya akan dukkanin abin da yake wakana xamujene domin ganewa idanuwan mu da Kuma tabbatar da abin da ake tunani. Tom sai kundawo kude Kula,Yaya Ahamd yace Suraj tashi mu shiga ciki danni bacci nakeji su Kuma wadannan idan sun dawo daga yawan binciken sa fadimana abin da suka samo. Murmushi sukayi suka mike suko su Samiha suka fita suna tafe suna shira cike da mamaki akan abinda yafaru su kade suke ta cece kuce,nifa Samiha Ina ganin nihal ba aure tayiba saboda ayanain cikin ta yafi wata bakwai Kuma Kinga tunkan su bar garinnan kelan,kingade Kuma tana garinnan batayi aureba tom da ace de ba babba bane sai nace aure tayi,karki damu zamu sami ansar duk abin da mike bukata mide karasa gidan. Amman kina ganin zata biyamu har ta bamu wani labari haba Basma sai kace kin manta wacece Samiha dinki kede kawai mije. Suna tafiya suna shira har suka isa gidan,suka kwnakwasa mai gadi ya bude ya ruga da ya sansu babu bukatar ya hana su shiga suka gaidasa suka wuce. Momyn su nihal suka iske zaune akan kujera tana kallo sukayi sallama suka tsugunna har kasa suka gaidata fuskar ta dauke da murmushi irin wanda idan kajima baka ga mutum dinann ba,yarannan ba ku da kirki kwata kwata kuka dauke kafarku daga gidan nan har nayi jajanku na gaji alhamdulillah naji dadin ganinku Kuma naji dadi ganin da nayi muku na haraynzu Kuna tare da tarbiyyar ku hakan yayi matukar yimin dadi ubangiji Allah yaci gaba da kare muku mutuncinku ameen ameen momy Ina nihal din ko tana ciki. Lokaci guda sukaga momy ta sauya daga ambaton sunan nihal,basu fargaba sukaga ta fara zubar da hawaye Samiha dake yarinyace mai tsoro tayi matukar tsorata tom mai nene dalilin wanann hawayan na momy tsintar kanta tayi wajan yi mata tambaya momy lafiya mai ne ya sakaki kuka,dan Allah ki fadamana Ina nihal ko wani abune yasameta baku dawo tare da ita ba wallahi duk hankalina ya tashi . Momy ce ta dago kai tace " Aah mindawo tare da nihal yanzu hakama bata dade da fita ba" Tom amman mai nene dalilin hawayanki? Naji matukar faring ganinku da irin yadda harynzu kuka cigaba da rike tarbiyyar ku ya yara mata hakan yayi matuakar yimin dadi,tabbas bansan lokacin da rayuwan nihal ta lalaceba bansan lokacin da ta jefa kanta cikin masifa da bala'i ba,Allah yayi mana dukiya dede gwargwado duk wani abu da nihal ke bukata bata taba nema ta rasaba ammam bansan mai yasa ta zabawa kanta kalar rayuwan da takeyi ba. Ba zan so Kuga nihal ba,saboda ayanzu nihal ni Kai na dani ni na haifeta shiaysa nake jimirin zama da ita. Mahaifin nihal ya sami sanjin gurin aiki zuwa gumel hakanne yasa mika hada kayan mu mika koma can amman da yunkuri da Kuma tunanin zami dawo hadejia adullokacin da mika sami dama,tunda mikaje yake ta fafutuka wajan ganin andace mindawo nan. Watan mu daya acan naga nihal tafara wasu halaye wadan da a da can bansan ta dasu ba,zata fita ba tare da na saniba sanann zata raba dare,zanjira har sai ta dawo nayi ta mata fada har dukan nihal nayi amman abin bai yi amfani ba,takai ta kawo saboda fadan da nake mata idan tafita sai ta kwana ba xakiga ta dawo ba sai can tsakiyar rana,na shiga cikin matsananciyar damuwa kafin an ankare watarana nihal take ta kela amai nayi matukar tsorata saboda jikina ya gama bani cewa tabbas ciki gareta. Bance mata komi ba sai bayan mahaifin ta ya dawo na labarta masa dukkan abin da yafaru na sanjin da nihal tayi fada yayi tamin mai yasa ban fadi masa da wuriba nace masa nayi tunanin zan iya sai sai ta komi,yanzu Ina nihal din take?tana daki je ki kiramin ita. Kamar yadda yace taje ta kirawao nihal tazo ta xauna nan yafara yi mata tambayoyi akan Ina take zuwa amman kunsan mutum mai shegen taurin kai fur nihal taki bashi ansa har yayi ya gaji nan yace ta tashi ta shirya zata rakashi unguwa batare da tunanin komi ba ta mike taje zata shirya. Momyn suce tace "Alhaji Ina Kuma zakuje?" Xanje na kai ta asibitine saboda gaba daya wanann bayanin da kika min yasa banyar da da itaba zanje aduba ta kar mije ta debo ciki ma bamu sani ba. Mummunar faduwar gabace ta ziyarci momy amman ta basar tayi shiru,saboda ta tuna aman da taga nihal nayi dazu amman tayi shiru da bakinta tana mai fatan Allah yasa ba ciki bane. Suna isa asibiti dady yacewa likita dubata xasuyi suga idan tana da ciki,nan likitoci sukayi gwaje gwajen su sukace su dan jirasu bayan dan wani lokaci likitan yafito fuskar dauke da murmushi yana mai taya dady murna da cewa matarka na dauke da ciki. Wani kallo yabi da likitan amman sai ya daure ya ansa yace ya gode tunda suka bar gun yafara ball da nihal har sukaje cikin mota kafin suje gida kuwa nihal kuka take baby adadi yanayin da suka shiga dashi gidane ya tabbatar wa momy cewa tabbas nihal nada ciki "Innalillahi wa inna ilahee raji'un"tashin hankali ba asaka masa rana dady yaje ya sami gu ya xauna ganin tashin hankalin da yake ciki ya sa momy taje ta dakko masa ruwa mai sanyi ta zuba cikin Kofi ta zo ta bashi . Bayan yasha yace "Ke zo nan ki zauna nagode sosai da sosai da irin abun kunyan da kika jawomin ke kadece yarinyar da Allah yabani nayi komi domin inganta rayuwanki babu abin da banni babu abin da ban baki ba amman ni kika zubarwa da mutuncin ko" Gata nan kijata ki tambayeta ciki gareta har na wata hudu kuma de watan mu biyu da dawowa nan bare ace anan tayi cikin kelan tun mina hadejia tayi. Momy ta rasa mai zatace kawai ta fashe da kuka zuciyar ta tayi rauni batasan mai zata furta ba tashi tayi kawai ta bar gurin saboda bata son bacin ran da take ciki yasa tayiwa yarta baki,wanda tasan ba gyrata zai yiba sai de ya sake lalatata. Tana jiyowa dady yana ta jibgarta kamar jaka,ita Kuma da shegen taurin kai taki fada masa waye ne sai da taga yana kokarin rabata da rayuwarta tukunna tayi magana,wani saurayina ne lokacin mina hadejia shine yamin Kuma duk futar da nikeyi shine idan ya zo nake fita naje gurinsa yana zuwa nan garin lokaci xuwa lokaci gurina. Dady dakatwa yayi da dukanta yanzu har iskancin nihal yakai baza su iya jurewaba har sai ya biyota. Kasance mata komi yayi shima yakoma daki Tom Basma, Samiha kunji abin da yafaru yanzu haka nihal na dauke da ciki ajikinta wanda yakai kimanin wata bakwai ni kade nasan damuwar da nike ciki amman naga bata da amfani hakanne yasa na kwnatar da hankalina na Kuma cigaba da addu'a ubangiji yasa wanann shine na karshe baxata sake aikatawa ba. Na so azubar da cikin amman dadyn ta yaki yace "Baza a kara wani sabon ubangijin da sanin saba" Samiha da Basma gabadaya kuka suke saboda ko babu komi nihal kawarsu ce wadda suka ta so tare Kuma tabbas sun tana kaunar su sai de tabiya rudin soyayyya da Kuma son zuciyarta ta bata zumunci. Samiha ce ta sakko ta dawo kusa da momy ta goge mata kwallan da ke fuskarta kiyi hakuri momy inshallah haka bazata kasanceba Kuma ki dauki hakan a matsayin wata jarrabawa da Allah yayi miki idan har kika jure inshallah zakiga komi ya tafi dede momy. Ubangiji yayi muku albarka Allah yaci gaba da tsare nuk mutuncinku ameen momy. Ana haka kawai sai ga nihal tayi sallama idanunta ta sauke akan Samiha tana juyawa gefe ta ga Basma sauri tayi zata wuce daki momy tace mata "Ki tsaya gurin kifa suka zo" Akwai abinda zanyi ma hadu wani lokacin kwata kwata takasa dago idanuwanta ta hada da nasu fiyau ta wuce daki. Yah Allah ya ubangijin sammami da kassai ka hanemu aikata aikin da nasani,yah rabbi Kaci gaba da karemu da karemana mutuncin mu,kasa mufi karfin shedan... https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf CREATED AND WRITTEN BY ZEEY NASEER *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~~~ Page 31&32 Nihal nihal baza ki tsaya ba mangana fa nake miki ammna babu alamar xata juyo balle ta saurari momy. Samiha ce tace "Kyaleta momy zamu hadu wani lokacin zanyi mata magana ta Whatsapp inshallah xan Kuma yi mata nasiha sosai akan ta kiyaye gaba". Bani number dinta dan banni da ita a wanann layin tom shine abin da momy tace ta dakko wayan ta ta bawa Samiha number din nihal tana karanto mata ashe Basma caraf ta rubuta number din ita ma. Nan sukayiwa momy sallama suka fita suna fita Basma ta kalli Samiha tace "Alhamdulillah allah ya nuna mata ishara tun mina raye aduniya idan har aikin mutum shine cin amana dama karshan sa ai ba zai taba yin kyauba nayi matukar farinciki da abin da ya sami nihal babban darasi ne agareta da dukkan wanda ke kokarin aikata cin amana". Haba Basma sai kace ba keba wanna mai tausayin da son mutane,sai kace bakeba wanann wacca idan kuda taga ya taba dan uwanta sai hankalinta ya tashi yanzu kece ke yin murna dan wani abu ya sami wani haba bamsa. Yanzu ke Samiha har nihal wacce za a tausayawa ce wallahi ko zanganta tana ranga rangar mutuwa ba zan tausaya mata ba,ita Lokacin da take aikata rashin mutuncin ta ta tausaya miki ne sai mune zamu tausaya mata. Duk da haka Basma dukkan abinda mutum yayi kansa Kuma duk abinda mutum yayi zai bishi iya isharar da ta ganima kawai mubarta da ita ta isheta mukuma cigaba da yiwa kanmu addu'ar Allah yaci gaba da tsaremu. Hakane Samiha tom Allah yasa midace yanzu da kika karbi lambarta mai zakiya da ita?ina so nayi mata maganane akan ta manta da dukkanin wani abu da yafaru tsakanin mu ina son ta dauka aranta babu abinda yafaru a tsakaninku mu. Ke Samiha wai kina da hankali kuwa mai kike nufi nihal xaki dawo mana da ita cikin rayuwar mu tom gaki ga ita kije kuyi rayuwanku na dau lambarta da momy na fadamiki da niyyar nayi mata magana na kuma nuna mata sakayyar da ta gani amman na fahinci ke wani abin kike tunani ma daban,tom gaki ga nihal narantse

Chapter 11 of 15