Share this page
wanannan dan na wannan bokan ne sanann maganar da ta fada musu a baya karyane ta fada musu ne kawai dan kar ta fada musu waye ne hakikanin uban da.......... Kuka momy takeyi mara iyaka yanzu daman Sanadiyyar soyayyya kika jefa rayuwanki ciki matsala nan tagama kuke kukenta ta dau takardar da boye..... Taku a kullum ZEEY NASEER. https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙* We shine all over the world CREATED AND WRITTEN BY ZEEY NASEER https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~~~ Page 35 Rayuwa tafara tafiya amman kowanannan su kullum cikin tunane tunane yakeyi,momy ta fuskanci haka hakanne yasa ta kirasu ta xaunar da su tayi musu nasiha ta Kuma nuna musu cewa duk abinda Allah ya tsara shiyasan dalili sannan sudena tada hankalinsu wajan tunani akan abinda suka aikatawa nihal duk abin da suka aikata ai ita ta jawowa kanta. Nan momy ta kwakkwantar musu da hankali suka sami nutuswa,suna tsaka da wanannan shirane sukaji anyi sallama dagowa kai sukayi suna kallon mai fuskar kamar sun santa amman sun kasa gane waye kallon kallo akayi tayiwa juna. Momy ce ta mike tace "Abdallah ashe kana rayebaka mutu ba duk tsawon wanann lokacin". Alhamdulillah Allah mingode maka kai ne mai bayarwa kuma mai hanawa yau kadawo mana da Abdallah garemu ,Yaya Dr ne ya mike aguje yakarasa ya rungume Ahmad da tuni alokacin yarintarsu ta fara dawomasa ya tunano irin tsananin kaunar dake tsakanin su,nan sukayi ta kuka shi da shi da kyar momy ta rarrashesu suka zo suka xauna,ku rika abu sai kace ba maza ba ku baku iya daurewa ne. Bayan sun xauna Samiha ta dago kai ta kallesa kasa magana tayi saboda ta rasa mai zatace ashe da rabon xataga jininta wanda suka fito duniya tare uwa daya uba daya,kallonsa kawai takeyi kawai sai ta fashe da kuka sakkowa yayi ya dawo kusa da ita Samiha mai yasa kike kuka ba kya farinciki da dawowar yayanki, rungume shi ta sake sakin wani azababban kuka haba yaya kai kade nefe ka ragemin kai ma ka tafi ka barni a lokacin da nafi bukatar ka mai yasa bazanyi farincikin ganinkaba na rasa da wacce kalma zanyi amfani wajan nuna farincikinane hakika yaya nayi kewar rashinka dan Allah karka sake nisa dani "inshallah"Samiha na zo kelan babu wani abu da zai sake sakawa na barki. Nan momy tace suraj ku tashi ku shiga daki Abdallah yayi wanka ya zo yaci abinci ya huta sanann sai yabamu labarin mai yafaru da shi duk da naga babu alamin gajiya a tattare da shi tom momy sika mike suna murmushi. Bayan sun shiga daki Yaya Dr yake cewa"Hakika Abdallah minyi matukar kewanka minyi matukar rashinka rayuwa sauya mana tayi na rasa yacca zanyi da ka tafi kai kadene abokina wanda na yarda da shi nake son sa nake son rayuwa da shi tun bayan tafiyar ka bansa ke abokiba har nagama karatu sai kwa nan nan da nayi wani abokina Ahamd" Allah sarki Suraj tom gashi yanzu na dawo inshallah kuma bazan sake nisa dakuba albarkacin annabi. Nan Abdallah yagama komi ya shirya tsaf suka fito yaci abinci duk da cewa kana ganinsa kasan baya jin yunwa. Ana haka sai ga dady ya zo ba karamin farinciki yayi ba ganin dawowan Abdallah ashe zasu kara saka sa a idon su ashe bai mutuba. Bayan ya kammala cin abinci yafara basu labari kamar haka "Alokacin da na farka da asuba na fita agida a guje batare da nasan Ina nakeba na tsinci Kai na cikin wani daji wanda da kafata na kai kai na wanann dajin batare da na saniba,Ina zaune naji abin da yafaru yana dawomin Ina jin kamar na dawo gida,amman gaba daya sai naji natsani gidan bazan iya rayuwa acikin gidan ba a haka na shafe kwana uku acikin wannan daji,watarana wani makiyayi ya zo wucewa ya ganni yamin tambayoyi sai na fadimasa cewa ni marayane. Nan ya tafi dani cikin gari yacemin mije shima shanun maigidan sane wannan yake kiwo muje idan Allah yasa ya daukeni aiki nima nake samin na abinci,haka na bishi mika tafi gidan da mikaje ne yabani mamaki wani kantameman gidane kana ganin gidan kaga gidan attajiri. Mina shiga yagabatarwa mutumin ni nan alhajin yace nafadi masa wayene ni ban boye masa komi cikin labarina ba na fada masa komi da komi yace na shirya ya mai doni gida nace masa ni bazan koma gida ba,yace tomshikkelau yayi alkawarin rikeni har lokacin da xanje Ina son na koma gida,ya tambayeni nayi karatu nace eh yamin magana da turanci yaga Ina mayar masa nan fa yace tabbas wannan makaranta yakamata na sakaka ataikace de ya turanci kasar waje tare da yaronsa guda daya na miji da Allah ya bashi ,naje na karanci aikin tukin jirgi a yanzu haka ni matukin jirgin samane bayan mundawo kowannen mu ya bamu jari mai matukar yawa,yanzu haka zan iya ce muku ni kai na bansan iya adadin dukiyar da nake da ita ba,domin dana fara kasuwanci Allah ya sakawa kasuwancina albaraka. Lokaci daya Ina zaune naji Kun fadomin Ina Kuma son na zo na ganku,naje na sameshi na fadamasa Ina fadamasa yace "alhamdulillah "daman yaje ance masa asiri akamin ya dage da addua inshallah watarana zai karye shine yamin izini da na shirya na zo shima gobe zai xo yau yana da taro a office. Murna sukayi ta taya sa da kuma murant dawowa cikinsu . Anan dady yace yana da wadda yake so yace Aah ,yace tom na zaba maka Basma kawar Samiha a matsayin matar da xaka aura inafatan baza ka bijire ba dady siko batamin ba dan farincikin ka xan karbeta, bana son ka karbeta dan farincikina Ina son ka karbeta domin kana so dady na karba,zanje na sami mahaifanta naji idan basu mata mijiba sai a fadamata idan ta amince kaga shikkelau sai na saka ranar auran tare da naka da na su Samiha. Nan yace Samiha da Suraj suka dago kai inshallah sati biyu masu zuwa za'a daura muku aure ya juyo ya Kalli momy yace "Sai ki fara shirya yarinyar ki dan da man Ina son na yi muku bazatane"saura kwana goma sha hudu daurin auransu.. https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf CREATED AND WRITTEN BY ZEEY NASEER *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~~~ Page 36&37 Murna kamar ta kashe Samiha da Yaya Dr shikkelau yanzu zasu mallaki juna a gaban dady ma sun kasa boye murnar su. Nan suka mike sukayi dakin samiha da Yaya Dr da Abdallah dukansu,suna shiga Abdallah ya Kalli Samiha yace "Oh ni Abdallah wai yanzu Samiha ce ta isa aure na so ace su baba suna nan suga wanann rana sai de Allah bai so hakaba ubangiji yayi musu rahama"Ameen suka ansa masa.Nan Yaya Dr yace "Tom kai ma gashi zaka angonce"hmm kamanta sai anje nemomin matar yanzu idan akaje tace bata so nafa kaga ni nasanta shiyasa na amince tunda lokacin da na bar gidama ai sun dantasa amman ita fa ba lalle ta ganeniba. Samiha ta dago Kai tace "Ina da yakinin Basma baza ta taba watsa maka kasa a ido ba Ina da yakinin tabbas zata amince da auranka da izinin ubangiji haka sukayi ta fira abinsu kamar kar su rabu sai da dare yayi sosai tukunna suka bar dakin samiha suka koma dakinsu. Da safe sun tashi suna cin abincin safe yazeed babban yayan Yaya dr yakira dady a waya bayan sun gaisa yake sanar dasu cewa inshallah rabb nan da sati uku zai dawo "alhamdulillah"gaskiya nayi farinciki sosai ai ni nayi tunanin sai nan da wata uku zaka dawo Aah dady sun rage mana semester dinne okay Allah yakawo mana Kai lafiya, Allah yayi baka nan za ayi bikin yan uwan naka su wa kelan dady?auran Samiha da Suraj da Kuma Abdallah da Basma kawar Samiha duk da ma de shi banje na tambayo ba tukunna amman Inshallah Ina saran zasu bamu. Abdallah Kuma Dady yaushe aka gansa? nan ya labarta masa duk abin da yafaru yayi matukar farinciki sosai,amman dady Ina neman wata alfarma Ina ganin bai kamata ace anyi auran nan babu ni ba dan Allah dady kabari na dawo tukunna sai ayi,nariga da nasaka ranar aure sati biyu ansami matsaltsalu sosai a baya akan maganar auran nan bana son na sake dagawa,dan Allah dady kataimaka ni kadene fa yayan su guda daya da suke da shi dukan mu dan Allah dady kabari na dawo shikkelau naji na amince zanjira kadawo amman da sharadin kana dawowa kai ma za a hada da naka nikuma dady "eh"idan bakka wacca kake so ni zan samo maka kan kadawo "Aah dady Ina da ita akwai wata yarinya akalla min shekara uku mina tare Ina matukar sonta ita nake so na aura amman dady ni ban shirya aure yanzuba Ina son sai nan da shekara biyu"tom inde zanjira kadawo sai de na hada auran su da naka shikkelau dady kawai ba sai an jirani ba ayi,tom na tambayeka shin wane irin shirine na aure da ake bukata wanda baka dashi mina da kudi mina da komi dan mai zakace baza kayi aureba,nan dady yayi ta masa nasiha har ya sami nasarar amincewarsa ya fadi masa yarinyar da yake so dakuma yar gidan waye,mahaifin yarinyar shima hamshakin mai kudine nan dady yayi alkwarin shima zai je yana. Ya nema masa aure amman duk wata daya auran zai kasance kelan yana dawowa gida Nigeria da sati daya za ayi auran,dady yayi murna sosai xai aurar da yaransa duka alokaci guda alhamdulillah nan yayi maza ya tashi ya nufi gidan su Basma. Yaya zuwa ya sa akayi masa sallama da mahaifinta yana zuwa yaga shine yayi masa iso ya shigo cikin falo,nan babu nata lokaci ya fada masa duk wani abu da yake tafe da shi hakika mahaifin Basma yayi matukar farinciki domin kuwa babu wanda zai ki kai yar sa gidan mutunci irin wanann,ba karamin abun alfahari bane mahaifin su Yaya Dr ya zo nema wa dansa auran yarka. Nan yanuna masa jindadin da yayi amman yace masa "Yanzu zamani ne ba ayiwa yara auran dole saboda haka zan fadiwa yarinya kasa yaronka anjima da yamma ya zo yaganta idan ya so Idan taji ya kwanta mata mashallah shikkelau sai ayi"yayi farinciki sosia yace inshallah zai fadawa Ahmad akan ya zo yaganta. Yana tafiya ya koma ya fada musu duk yadda sukayi sanann yayiwa Ahamd umarnin da yamma yaje yaganta suga juna. Sanann yayi musu gargadi da kar Yaya Dr ko Samiha wani yabisa domin baya bukatar a takuramata ganinsu Kuma zai sa taji kunyar kin amincewa. Shima ciki ya shiga ya sami mahaifiyar Samiha yayi mata bayanin komi sanann yace tafadamata anjima inshallah zai zo. Maman Basma taji dadi sosai saboda ita tana matukar son ta hada jini da Samiha tunda Allah yayi danta Ahamd bai auri Samiha ba,tana fata Allah yasa Basma ta amince da auran Abdallah,ta kira basma tayi mata bayanin komi duk da batasan Abdallah ba lokacin suna yarinta amamn tana iya tunano kirkinsa da sanyin halinsa lokaci daya taji tana son anjima tayi domin ta gansa takuma ga ko zata iya amincewa. Kamar yadda dady ya umarci Abdallah da yamma ya shirya yaje gidan su Basma bayan yaje ne maigadi ya bude ma gate ya shiga da motarsa sannan yaje ya isarwa da Basma cewa tayi bako nan ta nemi alfarmar da ya shiga da shi dakin baki,ya bude masa ya shiga wani sanyi mai ratsa zuciyane ya shiga cikin jikinsa daga can Kuma hancinsa ya jiyo masa kanshin wani dadddan turare da aka saka acikin dakin, Abdallah mutum ne mai matukar san tsafta nan kawai yaji Basma ta shiga ransa domin ya tabbata duk gyaran nan tayi domin shine. Nan ya samu gu ya xauna bayan wasu yan mintuna hankalin sa na kan wayarsa sai yafara Jin sabon canji akan turaran da yaji wani turaran yaji wanda ya keta wancan kanshi,dagowa kansa ke da wiya sukayi Ido hudu da ita da yake labulan dakin a dage yake suna hada Ido gaba daya sukaji bugun zuciyar su ya sauya,nan fa basma tayi saurin sun kuyar da kanta dakin tashigo bakin ta dauke da sallama da yar siririyar muryarta. Tsugunnawa tayi agabansa ta ajjja farantin da ke hannunta ta xauna akan kujera ta rusna ta gaidasa ya ansa fuskarsa dauke da murmushi. Nan ta sakko ta zuba masa lemo ta mika masa da hannu bibbiyu,gaba daya salon yarinyar ya gama kashe masa jiki yama rasa mai zai ce mata nan bayan yasha lemon sun dauki mintuna a haka babu wanda yace komi. Yayi karfin hali yace mata "Na zo ne daman domin miyi magana akan tsare tsaren da zamiyi abikin mu,kinga yakamata ace min tsara komi yadda yakamata" Mamaki abin yabata kelan de shima Abdallah ya amince yana sonta tundade yake wanann maganar amman mai yasa bai fara tambayar ta tana sonsa ko ba ta sonsa ba yafara yi mata maganar biki" Kan ta na sunkuye tace "Aah yaya Abdallah ai naji ance bikin tare za hada duka da na Samiha tom duk tsare tsaren da mikayi zata fadamaka" Samiha zan aura ko Basma ke da kanki zaki kirani ki fadamin tsare tsaren da kukayi aike zan aura ba itaba. Tomshikkelau Yaya Abdallah inshallah, bani wayanki na saka miki number ta ta mika masa bayan yasaka ya kirayi layin sa nan shima number dinta ta bayyana akan screen din wayarsa. Ya mike sai ya dakko wani abu a gefansa acikin wata Leda haka mai dan girma ya mika mata,Aah yaya kabarshi ban gane na barshi ba,rokata kikayi Kuma idan rokata kikayi ma aikin kai ki rokenine idan ni da nake sonki bakii tambayeni na miki abuba wa zaki tamabya. Ki dauka na bakine domin kyautatawa kuma daga yau ki dauka duk wani Abu da kike bukata kofa abude take zaki iya tambayata, idan ban kwatan ta kulawa dake ala yiba taya zaki sami karfin gwiwar zan kula dake idan mikayi aure. Tom yaya nagode sosai da sosai ubangiji yasaka maka da alkairai yakarawa nemanka albarka ya rabaka da dukkanin sharri yakaremin Kai aduk inda ka shiga. Adduarta tayi matukar yi masa dadi ya sami ansar abin da yake bukata batare da ya tambayeta tana son sa ko Aah ba,nan ya tafi ya barta. Basma tunda take wani na miji bai taba rikitata da salon saba ya tafi ya barta da tunaninsa,tana shiga gida daki ta wuce ta kwanta kan gado tana tunano wanan fitinann kallon da yayi mata Lokacin da ta zo shigowa dakin,ai Basma gaba daya lokaci daya ta tsunduma kogin son Yaya Abdallah bata tunanin zata ki amincewa da auran,ita Kam alhamdulillah ta sami miji irin wanda ya dace,ranar nan de haka Basma ta yini cikin tunanin waannn dan bawan Allah yaya Abdallah.. https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf CREATED AND WRITTEN BY ZEEY NASEER *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~~~ Page 38&39 Yaya Abdallah yana tafiya cikin nutsuwa ya sanya sautin karatun alkur'ani yana saurara a motarsa, tunano abubuwan da suka faru tsakanin sa da Basma yayi shi kade yake murmushi tabbas ya kamu da soyayyyar yarinyar nan domin daga kallon farko ya fuskanci tabbas ta tattara duk wani abu da ake bukata agun mace daman Samiha tagama fadi masa halayyan Basma Kuma ya ruga yayi na'am dasu amman yanzu da yazo idanuwan sa sun Kara tabbatar masa da wacece Basma sannan zuciyarsa ta gansu matuka da ita,yanayin takunta yanayin kallonta da Kuma yanayin yadda ta iya sarrafa harshanta wajan furta kalamai cikin nutsuwa,shi kade cikin mota yake ta sumbatu Ina sonki Basma kawai yaci gaba da tukinsa . Yakarasa gida yana shiga gida ya tarar da dady, momy, Samiha,Suraj ,duk sunyi zugum a falo suna jiran dawowan sa domin suji mai yafaru yana sallama yanayin da sukaga ya shiga da shi cikin gidan shine ya tabbatar musu tabbas akwai nasara zama yayi ya gaidar da su dady. Sai Kuma ya kona gefen yaya Dr ya zauna ya kalle dady yace "Kamar yadda dady ka umarce ni da naje naga Basma naje Kuma alhamdulillah da dukkanin abinda na fuskanta daga gareta ta amince dani"alhamdulillah shine abinda dukkanin su suka furta dady yace "Shikkelau komi yazo karshe shima yazeed naje gidan su yarinyar mahaifanta sun amince yanzude dukkanin ku na saka auranku wata daya inshallah" Washe gari da safe weekend ne kamar yadda Yaya Dr da Samiha suka saba fita yawan shakatawa haka kuwa akayi sukacewa yaya Abdallah shima ya shirya su fita tare,tom ammam Abdallah mai zai hana kakira Basma ka fadamata zaka zo ku fita yanzu ta shirya,haba kai kuwa Suraj kawai daga fara zuwa gurin yarinya sai nakirata nace mata zamu fita, haba karka bani kunya mana wannan fitar zata Kara sakawa ku shaku da juna hakane Kuma bara na gwada ,yawwa zaka iya fadamata ma tare zamu fita duka okay. Nan ya jawo wayansa ya nemo lambarta yakira tana aiki a kitchen taji wayanta yayi Kara dubawan da zatayi taga shine mai kiran dan dama tayi saving number dinsa da Yaya Abdallah,bata dagaba sai da wayan yakusa tsinkewa ta daga tayi sallama da daddadar muryan ta.Yaya Abdallah na kwance amman saboda tsabar yadda muryar ta ta shigesa yasa shi mikewa ba tare da ya shiryaba jikinsa yaji ya dau kyarma domin muryar Basma irin muryar nan ce mai rikita dukkanin mai sauraro irin muryar da zata saka kajika a sabuwar duniya ba tare da ka shiryaba. Yunkurawa yayi ya tattaro dukkanin wata nutsuwar sa guri daya ya ansa mata,nan bayan ya tambayi lafiyarta sun gama gaisawa ya fadamata yana son idan bata wani uzuri zasu fita anjima tare harda su Samiha. "Okay babu damuwa amman bara na fadiwa mama duk abin da tace zan kiraka na fadamaka" "Babu damuwa nagode sosai" Bayan ya sauke wayan ya jingina kansa ajikin gadon yana wani nishi yadda kasan yayi wata doguwar tafiya gaba daya muryar Basma tagama gigitasa duk wani salonta sake birgeshi yakeyi. Suna gama wayan tafito falo ta fadawa mananta,"Tace babu matsala amman ta kula sannan kuma kar ta jima" "Tom mama inshallah nagode" Nan ta dawo takirasa ta fadi masa mama ta amince, okay tomshikkelau Allah ya kaimu anjiman. Kamar yadda suka shirya fita sunfita sai suka dauki mota Daya suka fita da ita,Yaya Dr na tuki tauraruwar sa farincin sa Samiha na kusa da shi,sai kuma yaya Abdallah na baya zasu biya daga gidan su Basma sai su dakkota suna zuwa yayi mata waya ta fito. Tana zuwa ta bude mota ta shiga gidan baya itama ta zauna kusa da nata angon Samiha na ta zolayarta tana kawata ta zama aunty na. Haka sukaje ya wace yawancen su da guraran shakatawa bayan sun kammala suka wuce sukayi shopping kowannan cikin su ya tsantsare budurwan sa da siyayya iri-iri suka dawo gida. An dau kimanin sati biyu kelan kullum shakuwa na Kara shiga tsakanin Basma da yaya Abdallah alhamdulillah su fara fahintar juna kuma kowannen su yana son dan uwansa. Saura sati biyu ayi bikinsu suka yanke shawarar hada lefe suka zo suka sami momy tace"Aah ita ba ita zataje hado lefe ba ta basu dama ko wannen su yaje ya sami budurwansa sune tare su hado lefe"amman momy ba kyaga yan uwa xasuyi korafin hakan. Wacece mahaifiyar ku?kece momy tom na baku dama ku shirya dukan ku ku tafi da Samiha Kai ma Abdallah kaje ka dakko Basma aje a hado lefe Kuma ku tabbatar ansaka musu duk abinda suke bukata. Suna haka sai ga dady ya shigo ta fadi masa suna tattaunawa ne akan maganar lefe nan ya karbi account din kowa acikinsu ya saka musu million biyar biyar yace gashi sa Kara akan kudin da suka ware na siyayyar sukayi masa godiya suka tashi . Yaya Dr yakira Samiha ta zo nan bayan lambu agidan inda suke shira yana ta tambayarta de irin abin da take so. Samiha ta dago kai tace "Yaya Dr kaine farinciki na a duniya bayan mahaifana da na rasa kai ne wanda nakeyiwa soyayyyar da bana yiwa kowa irinta Ina sonka Ina kaunarka,dan Allah karka barni Kaci gaba da kasancewa dani bazan taba iya rayuwa babu kai ba burina a rayuwa na rayuwa da Kai a kowane hali duk muninsa Ina son ka Yaya Dr dan Allah karka barni,kawai sai yaga ta durkusa tana kuka,Yaya Dr inde kabarni zan shiga damuwa zan dawwama cikin bakinciki na tabbbata idan kabarni nima bazan cigaba da rayuwa ba" Tsugunnawa yayi ya kamo hannunta ya tayar da ita tsaye sannan ya sanya harshansha ya share hawayen dake kan fuskar Samiha tas, dagowa idanun ta tayi kawai tana binsa da kallo. "Samiha Ina son kisani babu wani abu da zai rabani dake ko da ma da kikaga wannan abubuwan da suka faru sun farune ba tare da ina cikin hayyacina ba,kisaka aranki Yaya Dr nakine ke kade,ke kade nake nufi Samiha babu wani gurbin da wata mace zata samu damar shiga acikin zuciyata,Ina sonki da dukkanin nun fahina zuciayata da Kuma ruhina,Samiha kece farinciki na Kuma bazan taba barinki ba" https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf CREATED AND WRITTEN BY ZEEY NASEER *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~~~ Continuation of Page 39 Kamar yadda suka tsara sun shirya tsaf sun tafi domin zuwa hada lefe anje andakko Basma duk sun tafi tare. Abin da xai baka mamaki shine duk wani duk wani abu da Samiha ta dauka shi Basma ta dauka harta kalar akwatinan su duk dayane alhamdulillah sun hada lefe iya lefe. Da suka fito Basma tace "su ajje ta agida ita baza ta karasa gidan momy ba"kamarya Basma mu karasa na fadamiki fa yau favorite dinki na dafa"Aah fa Samiha ni wallahi kunyar momy nakeji Kuma ace Ina surukarta an wani shiga gidan dani mindawo daga siyo kayan lefe ni kawai ku ajjeni agida" Abdallah yace "Kinga Samiha ya isa haka ya da takurawa amaryata jaaan zami ajjeki agida kinji,tom ruhi nagode " Suna tafiya suna shira abinsu har aka Kara so gidan su Basma nan zata fita har ta bude kofa Ahamd yakira sunanta "jaan"na'am "ruhi"tana juyowa yabata wani hot kiss a goshinta lokaci daya ya tsayar mata da ruwan jikin ta ta kasa gaba da kasa baya,Samiha da Yaya Dr na ganowa ta glass dariya

Chapter 13 of 15