na kokarin kwace musu amman suka danneta.
Gaba daya Basma tafita daga cikin hayyacinta sai da Yaya Abdallah ya sake kiran sunanta tukun ta waigo cikin wata xazzafar kunya,ya karasa bude mata murfin motar ta fita.
Tana fita suka ja mota suka tafi shi Kuwa Abdallah Jinsa yake Ina ma su koma ya sake zama da Basma dan bai gaji da ganinta ba lokaci daya yarinyar tayi masa kamin da shi kansa yana
Mamaki baya tsammanin zai iya samin farinciki a wajan wata yarinya mace idan ba Basma ba daman shi ba soyayyya ya taba yiba Basma ita ce yarinya ta farko da ya tabaaa soyayyya da ita a rayuwarsa.
Sun karasa gida sukaje.
Aka bajewa mommy kaya ta sanya albarka sannan aka jira dady ya zo shima ya gani"alhamdulillah komi yayi da shima yazid na nan da duk an hado,Amman ai yakusa dawowa da na so ayiyo har siyayyar sa amman yadda naga kowa anbashi dama yaje da matarsa shima zai fi kyau yaje da tasa matar idan Allah ya dawo dashi sai suje suyi siyayyar lefan"hakane kam alhaji Allah ya dawo da shi lafiya ameen yah rabb.
Abdallah ya batun gidan da zaku zauna shi Suraj yagama gidansa tom amman yanzu kowanannan ku ga gidanan na bashi kai Abdallah ga key din naka,Kai ma Suraj gashi,amman ni a so samuna ba ashi nake so ku xauna ba,sai yakara dakko wani key a aljihunsa guda biyu ya mika musu,wanann gidane mai bangare guda uku na bukaci ku hadu duka ku zauna kowa bangaran sa daban,tom amman momyn ku ta nunamin hakan bai kamata ba idan baku kuka yardaba,barin matar yazid da ba yar dangi bace ba lalle hakan yayi mata dadi ba,nima Kuma na gaskata maganar hakanne yasa na hakura da xaman yazid,kudin idan Kuna ganin babu matsala Ina son ku zauna agida daya hakan zai taimakawa zumuncinku.
"Yaya Dr ne yafara magana alhamdulillah gaksiya dady naji dadin wanann shawarar zumuncin Basma da Samiha zai kara karfi kuwa bade su kadeba har ku kanku zumunci zai karu,hakane dady Abdallah yace "Na tabbata Basma ma zataji dadin wanann labari".
Samiha ana ta magana bakice komi ba inji dady,"Aah dady ai duk wani hukunci da kuka yanke dedene domin kullum kana kan dede "hakane amman duk da haka Kina da hakki akan komi tomshikkelau de yanzu de Kun amince ,kai Abdallah sai kayi kokarin sanar da Basma, inshallah dady nasan ma babu wata matsala inshallah.
Ancigaba da shirye shirye Samiha da Basma komi nasu iri daya sunje sun dinka gown na futar biki wanda zasu saka ranar bridal da na ranar kamu da Kuma na ranar daurin aure,komi yana tafiya dede kuma cikin tsari da farinciki.
Ranar da yacika saura sati daya biki ranar yazid ya shigo cikin Nigeria ya Kuma zo gida cikin aminci yaya Dr da yaya Abdallah su sukaje suka dakkoshi,suna zuwa gida kowa murna yakuma samu tarba mai kyau daga gurin iyayansa.
Ankammala cin abinci anzo anzauna ya kalla Samiha lalle samiha wai kece kika girma haka, wanann da naga photonki ai ni zanyiwa Suraj kwace haka sukayi ta shira ana wasa da dariya sannan shima dady yace "yaje ya dauki amaryar sa su hado lefe"yace "inshallah gobe zasuje".
Ranar de gidan kowa na cikin farinciki domin rabon yazid da Nigeria yakusa shekara goma tun mutuwar Jamil yayan su Samiha abokinsa,da daddare bayan sun zauna da gashi sai momy ta bashi labarin dukkanin irin masifar da ta fadawa Suraj da Samiha ya tausaya musu sosai da sosai matuka, sannan ya kara adduar Allah yakara tsarewa.
Shirye shiryen biki sunci gaba da gudana,nan Abdallah yace "yakamata suje gun kakansu baban mahaifiyarsu su fadamasa, daman shi kadene yasan kauyan shine dalilin da yasa dady bai taba kai Samiha ganin suba domin basu san Ina bane"haka kuwa akayi suka shirya Samiha Yaya Abdallah Yaya Dr suka je yayi matuakar farincin ganinsu kwana daya sukayi suka dawo gida yakuma yi musu alkawarin inshallah shi da Yan uwan mahaifiyar su duk zasu so .
Rana bata karya sai de uwar diya ta ji kunya yau alhamis ake gudnar da bridal na bikin Samiha,Basma , Abdallah, Suraj,yazid da matarsa Zainab.
Taro yayi taro abinka da Yan dangi sanann Kuma masu kudi, bridal dinsu yayi matuakar kayatuwa kowa anyi masa photo xafafa shi da da amaryarsa,amman akace komi na babba yafi na yaro duk yadda suka kai ga kyansu.
Inde kaga Samiha da Yaya dr sai ka sara musu domin kuwa zakayi tunanin cewa ba daga kasar suka zoba,kyau iya kyau Kamala tare daukan hankali sai Samiha da Suraj ba karamin da cewa sukayi ba.
Ana tsakiyar shagali Samiha ta Kalli yaya Dr yace "ABOKIN YAYANA ya zama sanadin matsalata ya kuma zama sanadin farincikina, ABOKIN YAYANA ya zamemin komi na rayuwata, ABOKIN YAYANA ya zama dukkanin wani jingona".
Kawai ana tsakiyar biki sukaga ta zo wajan mai dije ta ansak loud speaker din hannunsa"Tace nasan kowa zai yi matukar ganin mamakin mai yasa na taso na zo wanann waje a matsayina na amarya Ina son na Kara tabbatar muku da irin son da nikewa Yaya Dr wato ABOKIN YAYANA,Yaya Dr wani jigone acikin rayuwata farinciki ne shi wanda ba zai misaltuba a kalla yau kimanin shekara goma sha biyu Yaya Dr na cikin zuciyata,ya shiga zuciya tunkan nasan mai nene so ya saka farinciki cikin zuciayata tunkan nasan mai nene farinciki,yaya Dr Ina son kasani Ina yi maka irin soyayyyar nan mai taba bargo da zuciya sai Kuma sukaga ta ajje speaker ta matsa kusa da shi,Ta dakko wani abu cikin jakanta mai matukar sheki ta bude sa,wani a warwaro ta dakko na maza kana ganin sa kasan diamond ne mai matuakar tsada ta kama hannunsa ta saka masa, su kuwa masu photo an sami abin nema ta ko ina dauka sukeyi,Yaya Dr rasa mai zaiyiwa Samiha yayi wanda zai sakata farinciki kawai rungume ta yayi yana zubar da hawaye kai kace macane,kuka yakeyi sosai Ina sonki Samiha kece adukkanin farinciki na dakyar Samiha ta samu ta kwace ta koma mazuninta,mutane kuwa abin na basu mamaki suna kwanta girman wannan soyayyyar ta bayin Allah nan.Haka aka gama shagali aka watse cikin farinciki kowa bakinsa da gulmar Samiha da Yaya Dr.
Bayan sunkoma gida misalin 11 har suna shirin kwanciya wayarta tayi kara number din yaya Dr ce ta bayyana wani farinciki ta ji aranta ta daga cike da farinciki da wanann ladabin nata,ki zo Ina falo Ina jiranki mamakine yakamata tasan de shigowansu akwai baki da mutane tom bata saniba ko sun tashi,shijab dinta ta dauka ta fito tana zuwa falo ta tararshi yayi ta gumi yana zaune kusa da shi ta zauna yaya Dr lafiya ya naga kayi ta gumi,Janta yayi ya rungume ta tamkar ba zai sake taba sai da suka dau lokaci mai tsawo a haka tukunna ya saketa.
Yace "kawai naji Ina son ki zo ki xauna miyi shirane"
Haka suka zauna a wannan falon sai da suka dau kimanin awa biyu kawai suna ta zance ana ta tsara irin rayuwar da za ayi idan anje gidan auran sai wajan karfe daya sukaje suka kwanta,washegari anyi kamu.
Wata washegarin Kuma takama asabat ranar daurin auran su kelan za a aduara aure da misalin sha daya day yace musu "Su tabbatar sun shirya da wuri yazid ne yafara shiryawa saboda baya san bata lokacin ya fito ya duba baiga Yaya Dr da Abdallah ba nan ya zo yana fitowa ya gano Yaya Dr da Samiha a bayan gida suna zaune suna ta shira,nikam na rasa wane irin jarababbune ku yaufa za a daura auran akai maka ita gidan ka,amamn kunkasa hakuri shikkelau yaya yazid kayi hakuri bara naje na shirya.
Nan yace wa Samiha "AMARYAR YAYA DR SAI MIN HADI IN ANKAWOMIN KE GIDANA"
Murmushi tayi itama ta mike domin zasu je wajan kwalliya.
Sun shiga suka tarar da Abdallah har yariga ya shiga wanka nan Suraj ya jira Abdallah yafito yana fitowa shima ya shiga sun fito kowannen su ya shirya cikin farar shaddarsa tsadadda ta sha aiki na gani na fada gaba daya ukun yazid ne yadin ka musu hatta aikin da akayi ajikin shaddar iri dayane.
Suna kokarin fita kawai sukaga Yaya Dr ya ja da baya................😀😍
Taku a kullum ZEEY NASEER
Typing din yau duk sai a hankali typing error yayi yawa ayimin uzuri nayi shine a agaggauce.
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf.
CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER
*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~
🤗😍This page is the best page for me to the entire part of whole the book, I love this page and I like it I hope it will be the most interesting page to you.......🥲🥲🥲
Page 40
Abdallah ne ya juyo da sauri "Aah ango mai yafaru karkaman ta fa yau zaka zama angon Samiha wato kanwar abokin ka wacca kafi so duk duniyar nan,ya da ja da baya ko har ka fara tsoaratane kafara tunano kai ma ka kusa zama uba".
Murmushin dole Yaya dr yayi ya ga tsayuwar baza ta masa ba yayi maza ya hau kan gado,yaya yazid ne ya wai go yace kai Suraj wai mai ne hakan ka tashi mutafi kasani cewa mu kade ake jira kuma babu gargadin da dady bai yi mana akan miyi sauri ba,ganin yanayin yaya Dr yasa dukkanin su suka tsorata cikinsa suka ga ya kama sosai yakasa ce musu komi kawai da idanu yake binsu Abdallah ne yayi matuakar tsorata yafara matsawa kusa da shi"Suraja lafiya wai mai ke damunka?".
Yaya yazid ne shima yayi sauri yakarasa Suraj lafiya,sunkuyar da idan sa yayi yaga yaga yadda Yaya Dr ya kame cikinsa kamar mai shirin na kuda hakanne ya tabbatar masa da cewa tabbas cikin ke masa ciwo nan ya mike aguje yafita yaje ya sami dady a harabar gidan suna gaisawa da mutane ka sa ce masa komi yayi ya riko hannunsa,da yake da kofar baya daga dakinsu hakanne yasa sukabi ta kofar bayan,suna zuwa sukaga Suraj har ya zube akan katifa kawai murkususu yakeyi"innalillahi wa inna ilahiee raji'un shine abin da dady kawai ke furtawa,mai ke faruwa da Suraj mai yafaru?"bamu sani ba dady mingama shiryawa mina shirin fitowa kawai mikaga yakoma da baya amman da dukkanin alamu cikinsa ke masa ciwo.
Na dady yacewa Abdallah yaje ya janyo mota yakawo ta kofar daki kar yayarda wani ya fahinci wani abin hakan kuwa akayi,suka dauki Yaya de suka saka shi cikin mota sukayi asibiti da shi,suna zuwa emergency aka kai sa nan da nan likitoci sukayi kansa ammman ina shi komi na ubangiji a atsare yake babu Kuma wanda ya isa ya kaucewa kaddara da hukuncin ubangiji kowa yana rayuwane karkashin hukuncin ubangiji da kuma abin da ya tsara masa.
Likitoci sunyi iya bakin kokarinsu wajan ganin sun ceci rayuwar yaya Dr amman ubangiji ya riga ya gama tsara masa rayuwar da yake so yayi rai yayi halinsa Allah ya dauke Yaya Dr a ranar da taxa mana rana mafi muhimmanci cikin rayuwarsa.
Daya daga cikin likitocin ce ta fito tace"Sai de miyi hakuri Allah ya anshi abinsa"
Basu san lokacin da Abdallah ya zube ya fadi kasa ba, kawai jiyowa sukayi suka ganshi a sume Abdallah Abdallah yazeed yake ta fada amman Ina bai san ma mai yakeyiba,nan shima likitoci suka daukeshi suka shiga ciki da shi,tashin hankali ba a saka maka rana dady ya rasa mai zaiyi kawai guri ya samo yafara zabgar hawaye tamkar karamin yaro,haka yazeed gaba daya ya gigice tamkar mahaukaci Suraj autan momy da dady wanda da dady ke hakura da abun da yake so yabi xabinsa shine yanzu yabar duniya ya ansa Kiran ubangiji,haka sukayi ta kuka har sukayi mai isharsu da kyar dady yayi karfin gwiwa yace"Ina son a hada Suraj anan kafin muje gida domin idan minje akace a can za a hadasa za'asami matsala za'ajima"tom dady.
Wayoyin su kuwa sai kururuwa suke ana ta Kiran su amman sun kasa dagawa daga karshe kowannen su ya kashe wayan,anan aka hada yaya Dr aka saka masa suturar sa ta gaskiya.
Kafin agama Abdallah ya farfado nan suka dauki gawar yaay Dr sukayi gida da ita, tunanin su yakoma ta ta Ina zasu fara yiwa gkda bayani ta kofar baya sukabi sakamakon kofar gida cike yake da yan daurin aure.
Sun shiga sun ajje gawar Suraj a farfajiyan gurin sai suka zauna suka sanya gawar agabansu gaba dayan su suna tunanin ta Ina zasu tunkaresu su fada musu kamar ance Samiha ta yiyo bayan gurin kawai sai gata tana zuwa taga su dady sun sanya mutum agaba cikin likkafani gaban ta taji ya fadi duk da daman tun dazu jinta take tamkar mara lafiya duk takasa samin nutsuwa,da gudu ta karaso gurin mai ke faruwa Yaya Abdallah Yaya yazid ku fadamin Ina Yaya Dr wani mayan kuka Abdallah ya fece da shi ya nuna mata gawar dake gabansu,hakan ya tabbbatar mata tabbas Yaya Dr ne karasawa tayi zata bude dady rike hannunta sai de miyi hakuri Samiha Suraj ya rigamu gidan gaskiya,wani wawan ihu ta saki wanda ya dawo da hankalin matam dake falo duka da gudu sukayiyo gurin kafin su karaso Samiha ta jima da faduwa.
Yayar momy ce da kanwarta a falon suna zuwa dady ya fadamusu abin da yafaru yace"Shi bai san yadda zaiyi ya fadawa momy ba,sukace bara suje sun san yadda zasu mata".
Nan fa hankalin dady ya dawo kan samiha ya Saka yazid ya zuba mata ruwa amman shiru nan fa yace "daya daga cikinsu ya tashi ya kaita asibiti"Abdallah ne ya dauketa suka tafi ya barsu zai fita dede lokacin ya tarar Ahamd zai shigo gidan bai sami nutuswar tsayawaba Ahmad yana tayi masa magana wannan ya tabbatar masa da ba lafiya ba,saboda daman an bar daurin auren duka anace a adura agidan su Samiha.
Nan fa yafara wurge wurgen idanuwa Koda wanda zai gani ya tambaya a dede lokacin kanwar momy ta fito ita ya tare yake tambaya daman watasan wayeshi hakanne yasa ta bashi anasa a gajarce da Suraj ne ya rasu,gabansa yaji yayi mummunar faduwa amman de ba Yaya Dr ba bata tsaya ba shi ansaba ta wuce abinta gaba daya ya rikice ya shiga tashin hankali Abdallah bayan fitarsa ya kira basma ya fadamata abin da yafaru hakanne yasa tabaro taron bikin ba tare da sun saniba ta taho tana zuwa ta tarar da Ahamd da gudu ta karasa ta rungume shi tana ta kuka yi hakuri Basma bade kema anfadamiki ba nan ta kwashe komi ta fada masa,kasa tsayuwa yayi dukkanin su suka xauna.
Tace"yacemin gawar da su dady suna bayan gida daga bangaran dady duk da cewa yan gidane agurin bazan iya jurewaba sai naje"
Mu tafi tare suka mike dede lokacin da suka karasa dady yana magana da yazid yana cewa"Babu abin da zai hana auran nan inshallah ana kai gawarsa za adawo a daura aurannan kai yazeed kaga daman kai ne yayansa uwa daya uba daya, saboda haka kai yakamata ka auri Samiha yanzu za adaura auran ka da mata biyu kelan".
Aah dady da wane Ido zan kalli Zainab nace mata su biyu na aura,Kuma duk da abin da Samiha ta aikata na badala da fasikanci ace ni na aureta,tom uban waye ya lalatata ba dan uwanka bane gaskiya dady kayi hakuri amman bazan iya auran Samiha ba,momy ce ta dago kai tace"Yazid tunda mike da kai baka taba maana musuba amman yau da mu kake musu".
Kyaleshi hajiya na tabbata kyakkyawan zuciyar samiha da irin kaddarar da take gani a rayuwarta zata iya saka ta sami mutum na gari.
Kamar daga sama sukaji Ahmad yace "a karo na biyu inde dady ka amince Ina son abani auran Samiha na yi muku alkawarin bata farinciki da jure duk wani wulakancin da zatamin har ta dawo dede daga radadin mutuwar Suraj".
Allah yayi maka albarka Ahamd mingode.
Nan aka sanar da mutanan jana'iza aka fita akayiwa yaya Dr sallah aka kaishi gidansa na gaskiya bayan andawo aka daura auran.
AHMAD DA SAMIHA
ABDALLAH DA BASMA
YAZID DA ZAINAB.
ita kaddarar bawa arubuce take babu wanda ya isa ya dau kadararar wani kuma babu wanda ya isa ya sauya kaddararsa kamar yadda matar mutum kabarinsa babu wanda ya isa ya auari matar wani.
Ita kaddarar mutum a rubuce take kuma abiye take da shi.
Bayan daura aure Kuma anci gaba da zaman makoki kamar yacca yake a al'ada na tsawon sati guda
Bayan an kammala zaman makoki an kai amae gidajen su amman fa har lokacin Samiha bara farfado daga suman da tayiba.
An dawo da ita gida ancigaba da bata dukkanin wata kulawa Ahamd kodayaushe yana zirya cikin gidan sai da tayi wata guda sanann ta samu bude idanu a ranar kowa yana cikin farinciki,harta Basma da Abdallah ranar agidan suka yini saboda Samiha ta bude ido,bayan kwana biyu Kuma gangar jikinta ta fara motsawa alhamdulillah ranar Samiha ta farfado amman sai de banda hawaye babu abin da yake zuba daga cikin idanuwanta fuskarta ta kumbura tsabar hawaye sai da tayi kwana biyu tukunna tafara magana,Basma ta dawo gidan gaba daya da zama kullum ita take kara kwnatar mata da hankalinta da yi mata nasiha tare da sakata yin addu'aoi da salloli a haka aka Kara shafe wata guda tukun ta dan dawo cikin hayyacinta ta nutsu tana cin abinci dede gwargwado amman fa fara'a babu ita a fuskarta kwata kwata.
Har lokacin babu wanda ya sanar da ita andauramata aure.
Ranar dady yasaka taro ciki har da Ahamd anan aka sanar da ita komi, wani kukane yakare yanke mata yanzu da wani zatayi rayuwar auranta ba yaya Dr ba yanzu duk wani abu na farinciki da ta tsara zata basa shikkelau babu dama wani ne zai mallaketa a amtsayin mata,nan dady yayi mata nasiha mai ratsa zuciya sannan yace "A daran yau za a kaita gidanta".
Sabon tashin hankali bata taba tunanin zai ce hakaba haka tayi ta kuka kamar momy tace kar akaita yau sai de gwammah akaita saboda cigaba da xamanta agidan xai cigaba da tuna mata Yaya Dr da rayuwar da sukayi.
Nan fa ta mike ta shige dakin Yaya Dr take ta kuka ko Ina ta kalla gani take kamar zata gansa,daga filonsa tayi ta ga wata farar ta karda.
SAMIHA NASANI KINA SONA KINA KAUNATA AMMAN BABU WANDA YA ISA YA KAUDA KADDARAR UBANGIJIN SA SAMIHA INDE DA GASKE KINA SONA KINA KAUNATA KIYI BIYAYYA MATUKA GA DUK WANDA YA ZAMA MIJINI, KARKI YARDA KI KAI KANKI WUTA SANADIYYAR KAUNATA KARKI YARDA KI KAI KANKI WUTA SANADIYYAR SONA,NI TAWA TA RIGA TA KARE NASAN ZAKI KARANTA TAKARADR NAN ALOKACIN DA BANA RAYE,NA RUBUTATANE LOKACIN DA CIWON CIKI YA MATSAN TAMIN.INA SONKI SAMIHA NA RAYUWA DA SONKI KE KADE KUMA NA MUTU DA SHI NA KI A KULLUM YAYA DR DINKI KUMA FARINCIN KI.
Wani kuka ta sake kecewa da shi da kyar suka zo suka fitar da a dakin aka shiryata aka kaita gidanta.
Adaran daman Yaya Ahamd bai yi yunkuri n shigowa inda takeba saboda yana matukar tausaya mata dole ta shiga wani yanayi duba da irin kaunar dake tsakanin su.
Da safe bayan ya tashi ya dafa abinci yaje ajjemata adaki yasan ba bacci yeakeyiba kawai baya son ya takura mata ne.
Haka sukayi tayi har tsawon wata guda.Wata rana ya zo yace mata "Samiha Ina son na baki hakuri kidena kokarin ja da hukuncin ubangiji,yayi mata nasiha mai matukar rastsa zuciya,kuka ta fara mai tsuma zuciya nan ya ja ta ya rungume ta ya rarasheta ta bashi hakuri akan yayi hakuri ta kasa dedeta zuciyarta ne"
Karki damu inshallah zaki dawo dede Samiha,rayuwa ta fara sauya ta fara tashi tayi masa girki da komi,sannu a hankali har yafara shiga dakinta watarana mai afkuwa ta afku tsakaninsa abunda ya bashi mamaki shine,ance Yaya Dr ya lalata rayuwar Samiha amman ya akayi ya sameta cikakkiyar budurwa ya kasa jurewa hakane yasa ya tambayeta.
"Yaya Ahamd tunda nike da yaya Dr bai taba saduwa daniba na sha bukatar hakan amman yaki duk da asiri na yawo acikin jikin Yaya Dr amman hakan bai sa yaketa iyaka ba,kullum idan yazo yayi abubuwnasa dani yakan ja gefe yayi ta hawaye yana dana sani amman asirin dake jikin baya hana gobe ya dawo ya Kara sabawa ubangiji ".
Dukkanin yabo da godiya yakara tabbata ga Allah nan yaja Samiha ya rungume yana godiya ga Allah.
Samiha ta haihu ta haifi Yan biyu maza da mata Ahmad yaa saka sunan yaya dr Suraj,macan Kuma aka Saka mata Samiha.
Suraj suna Kiran sa da da Yaya Dr.
Amman har abada tunanin Yaya Dr ba zai taba barin Samiha ba duk yanzu tana kaunar mijin ta amman soyayyyar Yaya Dr ta dabance.
Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah ina godiya ga Allah subhanahu wata'atala da yabani ikon kammala wannan littafi,abin da na fada dede ubangiji Allah yakai ladan kabarin mahaifina, wanda nayi ba dedeba ubangiji Allah ya yafemin albarkacin annabi.
Na sadaukar ga wannan littafi ga mahaifina malam Nasir amarous ubangiji Allah yayi masa rahama ya Kuma kyautata makwancinsa yasa yana aljanna da shi da dukkanin musulmai baki daya.
Na tabbata makaranta yau basu ji dadin wanannan posting din ba,amman Ina son na tunatar damu wani abu bakomi bawa yake nema ya samu a rayuwaba,haka kuma wasu abubuwan da mike so ba alkairai bane a arayuwar mu,duk yacca Mika kai ga son Abu ubangiji yafi mu sanin abin da ya dace damu .
Ina godiya agareku masoyana
Mu hadu a littafi na gaba wato (ADDININA).
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 15