ne a matsayin hanyar ta farko kafin tayi yunkurin aikata Wani abin,ta Kuma sayi sabon layi Wanda babu Wanda yasanta da shi da shi take rubuta masa sakon.
SAFIYA MAI CIKE DA AMICI A TATTARE DA KAI TAURARON TAURARI HAKIKA KAI na NA DABANNE ACIKIN MAZAJE KOMAI NAKA DABAN YAKE A KULLUM INA GANIN KANA DA BAN- BANCI TSAKANIN KA DA SAURAN MAZAJE DOMIN komi naka daban yake a tattare dasu,Ina fatan ka tashi cikin aminci Kuma Ina fatan zaka kulamin da kanka kafin lokacin da zan zo domin kulawa da Kai,Ina kewarka autan maza......
Yana zaune akan sallayar sa Yana karatu yaji Karan wayarsa jawota yayi da mamaki yaga number din jiya ita ce aka Kara yi masa Sako da ita wai wacece wanann?, tambayar da yasake yi wa kansa kelan sai de ba shi da wannan ansar tabbas yakamata nayi mata gargadi akan wannan abin da take wata zuciyar tace masa "Aah" kabarta idan taga baka mata reply ba da kanta zata hakura tadena yi maka
Bayan ya kammala karatun sa ya fito domin yaje yagaida momy da dady bayan sun gaisa Kuma ya wuce dakin gimbiya Samiha domin har ta tashi ta kammala duk Wani aiki na gidan tana da matukar kokari,kwankwasa mata yayi ta Sani cewa babu Mai zuwa a wannan lokacin sai shi mayafinta ta dakko ta lulluba akan ta tace masa ya shigo ta rusna ta gaidasa yadda ta saba bayan sun gama gaisawa taga yanayin sa Duk Wani iri tambayarsa tayi yaya Mai yake faruwane?,Kallonta kawai yayi ya sunkuyar da Kai Yana son yabata labarin abin da yafaru Amman Yana tsoron bacin ranta haka Kuma Baya son ya rika boye mata wasu abubuwa yafi son yadda suka taso wajan sanin sirrin juna da damuwoyin su suci gaba da tafiya a haka hakanne yasa ba zai taba iya jure wa ya boye mata abin da ya zo fada mata ba.
Samiha "na'am",ta furta da daddadar muryarta Mai Saka Mai sauraro nishadi Ina sonki Ina Kuma matukar kaunarki Bana kaunar duk abin da Zai rabani dake duk kankantar sa bazan taba iya rayuwa babu keba
Murmushi tayi Yaya Dr kelan wanann abune da min ruga minsami Amman Mai ke faruwa?,tabbas yanayinka ya fadimin akwai abin dake damunka tabbas akwai Samiha,nan ya labarta mata dukkanin abin da ya faru ya Kuma Bata wayan ta karanta, murmushi tayi tace duk tashin hankalin akan wanannne" em" Kai de aka turowa message dinannan ai ba Wani ba sanann Kuma Kai ne Wanda idan kace ka amince za acigaba da turomaka Amman idan baka amince ba akwai Mai cigaba da takuramaka "Aah",tom kaga zabi ya rage ya naka mikewa tayi zatayi waje Ina zakije?,zanje ne na cigaba da aikina na baka Damar yin reply na sakon wayarka haba samiha Dan Allah kiyi hakuri Bana son boyemiki komi shiyasa na fadimiki,nasan da Hakan na Kuma ji dadin Fadimin da kayi Amman tabbas wanannan damuwar da take ranka akwai wani abin idan so kake ka amince mana ni Ina ruwana ficewa tayi ta kyaleshi agurin ya ma rasa yadda zaiyi da ransa.........😍🥲ABOKIN YAYANA😭
Created af Written
By
🤗😍ZEEY NASEER 💗
💫 MOON LIGHT WRITER'S ASSOCIATION 💫
We shine all over the world
Page 11
Kokarin kiranta yake domin yayi mata bayani yadda xata fahinta Amman bakinsa yayi masa nauyi ya rinjayesa ta yadda yakasa furta komi acikin bakinsa kalaman kasa fitowa sukayi Kuma duk Sanadiyyar fushin da yaga ta yini biyota yayi domin ko zai Sami Damar tse da ta a parlour domin yayi mata bayani Amman Kash!!!! Sai de Yana zuwa parlour ya iske dady da momy duk suna zaune can ya hango Samiha agefen momy tana zaune suna magana ji yayi kamar yaje ya kamo hannunta yayi mata bayani yadda xata fahinta Amman babu dama,abinci ta hada musu sukaci kallonta yake tayi domin su hada Ido Amman fur Samiha taki dagowa ta kallesa tabbas yau momy taga sanjin da Bata taba ganiba tsakanin Suraj da Samiha sanjin da za ace har sun fito sun fara cin abinci basu yi maganaba Hakan ya fara Saka mata zargin kode Wani abinne ya hada su Amman sai ta tuna ai yanzu ya zo ya shiga dakinta gaskiya sai de kawai maganan ne basuyi ba suka gama cin abinci sun saba tare suke tattara kayan,su mayar kitchen haka kuwa akayi suka dauki kayan domin mayarwa suna shiga Samiha Tayi kokarin juyowa domin duk ta fuskanci Mai yake nufi so yakeyi yayi mata magana ita Kuma take kokarin kufcewa wanann hanyar "Samiha " ya kira sunanta ansawa tayi ba tare da ta juyo ba magana fa nake miki shine ma dalilin da yasa ai na tsaya ki juyo ki kalleni Ina tunanin Koda ban kalleka ba zaka iya fadin abin dake bakinka tundade Baki ke magana hakane Amman zan Sami karfin gwiwar furtamiki abin dake baki nane kawai idan Ina kallon idanuwanki da ke sakamin karfin gwiwa juyawa tayi zata fuce saboda Bata da lokacin sauraran wadan nan kalaman, da sauri yasha gabanta haba samiha Mai ne Hakan wane irin hukunci kike kokarin yiwa zuciyata kinsan bazan taba jure fushinkiba ko na sakan dayane Dan Allah kiyi hakuri,Mai kamin da xaka bani hakuri na baka dama fa kayi duk abin da yakamata kisan Allah Samiha ban kula taba ban San wacece ba hasalima ban mata reply ba ai na Baki wayan kin gani na gani Amman Kai bakka da bakin da zaka yi kokarin tsayar da abin dake kokarin faruwa ko da matan da suke cewa suna sonka ni nake koya maka yadda zaka rabu da su ita wanannan Mai yasa baza kayi mata abin da kake musu ba inde da gaske ne baka San taba zan mata Samiha Daman na fadimiki ne saboda Bana son a Sami matsala , wayarsa ya dakko ya Mika mata yace ki rubuta duk abin da kika San zai sa baza ta Kara yunkurin turomin sako ba karba tayi ta shiga lambar ta rubuta sako kamar haka......
BAIWAR ALLAH KIYI HAKURI KARKICE ZAKI SHIGO CIKIN SHUKAR DA NA YIWA YABAN YA TUN SHEKARU DA DAMA,KADA KICE ZAKI ZO KI TARWATSA MIN FARINCIKIN DANA DADE INA TANA DINSA DA LALLABASA NI CE WACCA YAKE SO KUMA YAKE BURIN AURE DAN ALLAH KARKI SHIGO RAYUWAR MU KI KAWO MANA MATSALA KIYI HAKURI KIJE KIBI WADANDA SUKE SONKI DAN NA TABBATAR BAZA A RASABA.
tana kara sawa ta tura ta Mika masa wayan Aah ki rike a wajanki Dan na tabbatar watakil zata iya Baki ansa idan kungama kya kawomin to tace ta juya zata tafi hannunta ya kama ya juyo da ita yace Samiha Ina sonki Ina matukar kaunarki Bana son duk Wani Abu da zai rabani dake Dan Allah kidena fushi Dani ki Kuma Dena Saka damuwa akaina ni naki ne babu wata ya mace data isa ta shigo rayuwata bayan ke Dan Allah Samiha ki fuskance ni na fuskanceka Yaya Dr Kuma kayi hakuri akan abun da ya faru karki damu Daman ni banyi fushiba burina kawai kidena fushi Dani domin Yana Dagamin hankali......
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf
ABOKIN YAYANA 😭
Created and Written
By
🤗😍 ZEEY NASEER 💗
💫💫 MOON LIGHT WRITER'S ASSOCIATION 💫💫
We shine all over the world
Page 12
Nasani nasan baka San damuwata ba kuma kasan abin da zai batamin rai amman dole naji babu dadi Yaya Dr dole saboda shigowar wata rayuwan ka na nufin tarwatsa rayuwar da mika jima mina shimfidawa ni da kai wanda ni kuma bazan so hakan ba "inshallah Samiha babu wata wacca ta isa ta tarwatsa rayuwan soyayyyar da Mika jima mina shimfidawa cikin aminci ni dake babu wata wacca ta isa ta rusa wanann abin da Mika jima mina ginawa ki kwantar da hankalinka"
Shikkelau Yaya ya wuce "Inshallah" zan kiyaye" kusa da ita ya karaso ya manna mata Dan karamin sun Bata a goshinta ya fice nan ya barta cikin Wani tunani Mai zurfi da shauki Wanda kullum idan tana tare da Yaya Dr take cikinsa,taya wata zatayi kokarin shiga rayuwarsu ta Ina zan fara kokarin ganin wannan abin Bai faruba bani da Wani farinciki da ya wuce Yaya Dr shine abin dake raina Kuma nike fatan kasancewa da shi akowane lokaci bazan taba bari wata ta shigo rayuwan saba in de Ina nunfashi zanyi iya bakin kokarina wajan ganin Hakan Bai faruba da izin Allah,fitowa tayi ta koma dakinta domin tagama dukkanin aiki.
Zama tayi tana Kara duba sakon da yarinyar ta turo abin Kuma na sake Bata mamaki,Daga bangaran Nihal kuwa tana tashi da safe ta duba taga babu Wani Sako jiki babu kwari ta mike Amman da fata da tunanin baza ta gajiyaba saboda ta tabbata dole zai iyi Bata ansan sakonta tana zaune tana cin abinci kamar Daga sama taji Karan wayarta cikin sauri ta dauka ta Bude ganin layin Yaya Dr yasa ta saki wani murmushi Wanda batasan ma tayi saba cikin sauri da hanzari tayi kokarin budewa domin tana tunanin tunda har Yaya Dr ya biyata ya Bata ansar sakonta koda zagi yaturo mata tabbas da alamin nasara,abinda ta ganine yayi matukar tayar mata da hankali yabata mata rai wanda da kyar ta Samu tayi saisaita kanta lalle ma yaraina mata hankali yanzu Samiha yabawa wayan ta rubuta mata ansa kelan yakasance Da gaske basa boyewa juna komi tabbas dole ta sauya taku wannan hanyar baza ta bulle mata ba zata tafi Abu nagaba babu ruwanta da cutar da su da zaiyi ita de inde zata Sami nasara akan Yaya Dr tom Bata da wata matsala akan haka,cikin sauri ta shirya ta dauki mayafinta ta nufi gidan su kawarta shigarta ke da wiya ah!!! Nihal kece agidan namu"Kede bari atika ya zama dole me mije de mi zauna na Baki labari".
Zuwa sukayi suka zauna nan nihal ta debe labarin komi ta fadi mata atika dariya tayi Mai isarta sannan tace "Keda in ba Koda human ci ba kina Dani Zaki tsaya kina Bata lokacinka kinsan Allah da kinzo tun bayan ba da tuni mingama da wanann babin",wai Allah kawata Yoh ba sai ki zauna anan ba yanzu abin da xakiyi shine kije ki tattaro kudadde gobe zamu shirya zanfara kaiki gun Boka na kan tudu na tabbata cikin kalilan din Lokaci za'asami nasara,"Kinsani sarai cewa kudi ba matsala ta bane kawai ni biyan bukata Nike so"angama kuwa dan bakki da matsala gobe xamije da la'asar yau ma Dan zanyi bakone amman da yau din xamije babu komi Allah ya kaimu goben Ameen
Atika tace "Kede kawai ki kwantar da hankalinki in de kikaga Baki aure yaya Dr ba tom tabbas ba mije gurin wanann bokan ba" murmushi tayi wallahi sai yanzu na Sami nutuswa Amman bazan iyi kayyade Miki kalan tashin hankalin da nike ciki ba nagode sosai kawata bara na tafi sai goben.
Cikin farinciki nihal aka koma gida domin gani take ai bukatarta ta gama biya.....
Shin Mai zai faru?
Nihal zata Sami nasarar raba wanann soyayyya?
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf
CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER
*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~
Page 13
Washegari kamar yadda Atika tace mata haka suka shirya suka nufi wajan wanann boka,suna zuwa boka yace "Ba sai sun fadi abin dake tafe dasu ba ya xayyana duk abin da ya kawota tace masa"Eh"hakane yace tom yanzu mai take so ayi musu,bana Son ayi musu wani sbu da zai cutar da su saboda Samiha kawace tagari tana matukar girmamani Kuma nima haka wanann yasa ni kawai Yaya Dr nake so na kwace ita kuma bana son komi ya tabata iya bakincikin rabata da shima ya isheta,ba yadda zanyi bazan iya hakura da shi ba Ina sonsa matukar so, tomshikkelau yanzu zan baki magani ki tabbatar kin zuba masa a abinci yaci, kallo ta bishi da shi mutumin da kallon banza ke hada su da shi shi za a Bata ta zubawa magani a abinci,Atika ta fahinci haka hakanne yasa tunkan ta kwafsa tace wani abin ta bawa boka ansa da zasuyi hakan nan ya dakko maganin yabata yakuma sake tabbatar mata da cewa inde ta zuba masa yaci a abinci ko da Sau dayane tabbas ya zama nata,na so na duba nayi miki aikin daga nan tom amman ta ko Ina nakasa saminsa Yaya Dr mutum ne Mai matukar Shiri yana da ibada haka Kuma yana da yawan karatun alkur'ani kafin na same shi za ayi matukar Bata lokaci zakuma asha wahala,shiyasa na Baki kibashi abin da zai ci za afi saminsa cikin sauki.
Tomshikkelau babu damuwa inshallah zanyi bakin kokarina wajan ganin an dace hakan baza ta gagaraba suka tashi tadauki makudan kudi ta basa ba tare da tayi tambaya nawa yake so ba saboda ita kudi ba matsalarta bane,nan suka tafi ta fara tambayar Atika tom yanzu ta Ina zamu fara karki damu Wannan ba zai zama matsala ba,taya zakice kar na damu wannan kuwa ai shine babbar matsala taya xan zubawa Yaya Dr magani a abinci,na tambayeki? Ina jinki akwai abinda Samiha zatabawa Yaya Dr aduniya yaki karba yaci"Aah" tom kinga zakiyi amfani da ita wajan bashi na fahinceki yanzu ya za ayi Mai Samiha tafi kauna a abinci? Samiha na matukar son danbun shin kafa haka shima Yaya Dr Dan nasha yiwa Samiha danbu Daga gida na kaimata kawai saboda nasan tana so Au daman kina da wanann Damar har kika tsaya zaki bata mana lokaci kawai kiyi amfani da wannan Damar sai kiyi flask biyu nata Dana shi Amman da idan zan Kai hadewa nake karki damu yanzu ki rarraba Kinga idan takama kiyi flask uku ma kiyi momy da dady suma kiware musu nasu a flask daban,gaksiya kawata Ina sonki kina da duk wata hanyar mafita aduniyarnan kinsanta,haka sukayi ta shira har suka koma gida.
Kamar yarda suka tsara kuwa haka nihal tayi wannan dambu lafiyayye ta shirya shi tsaf cikin flask guda uku ta dauka ta nufi gidan su Samiha.
A bangaran Samiha kuwa yini tayi da wayan Yaya Dr a hannunta tana tajiran adawo mata da sakon da ta tura Amman shiru kikeji hakanne yasaka tayi hammdala ga Allah domin gani take watakil wanann yarinyar ta hakura,ana Kiran sallan magrib taji sallamar nihal momy Bata nan taje unguwa da murna ta fito sannu yar halak har na gaji da Kiran wayanki akashe tun dazu Basma ke kirana mince zamije miyiwa yayanta barka da zuwa Amman shiru ba mije ba har tayi fushi tom ya zamiyi gobema tunda bammu jarabawa sai mije okay tom,Mai ne acikin flask haka?abin da kika fiso na kawomiki farinciki ne ya mamaye Samiha domin a duniya tana son dambu,amman ya naga har flask uku,naki na yaya Dr na momy da dady,"Em"gaksiya ne ana haka suna tsakiyar Shira sai ga yaya Dr yayi sallama da sauri Samiha ta tashi taje ta tarosa sannu da zuwa Yaya sannu sarauniya inafatan kinci abinci,banciba amman ba sai da nakiraki nace kici abinci ba yau bazan dawo da wuriba kai ma kasan ai ba iya ci zanyiba mije ki zauna kici abinci tom yaya gama dambu karde shi kikayi yau aah nihal ce ta kawomin "ok" shine kawai abin da yace wucewa dakinsa zaiyi ta katse sa da Ina yini,bayan ya wuce nihal tace ki dauka ki Kai masa nasa nasan Yana jin yunwa aikinsan de tare mikeci sai kitafi da flask biyu kowa yaci nasa,tana sani sarai Samiha ta taba fadimata yaya Dr Baya son Dan Dano yayi yawa a abinci ita Kuma Samiha tana Matukar son Dan Dano Amman haka take hakura saboda shi,hakanne yasa ta dedeta Dan dano ana Yaya Dr na Samiha Kuma ta zabga dan dano tayarda babu Wanda zai iya cin na Dan uwansa sai de kowa yaci nasa,nan fa tace tom ni sai da safe inshallah goben duk in da Sha Daya take sai mije mugaida yayan nata okay tom babu damuwa.
Nan Samiha ta dauki wanann abinci,abincin da ya zamo Sanadiyya da Kuma sila ta sanja komi na rayuwarsu abincin da ya zama silat tar watsa farincikin su tabbas Samiha da tasan Hakan zata faru baza ta taba garajan bashi wanann abincin ba Sanadiyyar sauyin kaddararsu ,yadda suka saba cin abinci cikin farinciki suna Shirar su ta masoya haka sukayi suka gama kowa ya nemi makwanci, kamar yadda sukayi alkawari sun shirya domin zuwa gidan su Basma ,Samiha Kuma Yaya Dr ya barta.
Adede lokacin da sukayi sallama Yaya Ahmad na zaune kan kujera xazzakar muryar da yaji ce ta katse sa Daga abin da yake dagowa yayi domin ganin ma mallakiyar wannan murya Samiha yaga ta shigo ita da Nihal amman tabbas alamu sun nuna muryar ta Samiha ce ba nihal ba,nan suka russuna suka gaidashi har lokacin pyakasa dauke idonsa daga kan Samiha a dede lokacin Basma ta fito ah sannunku da zuwa sai yau kiyi hakuri min so ace damu aka taresa amman kinsan kana naka Allah yana nasa hakane guri suka Samu suka zauna nan ta farayiwa Yayan ta bayani da su waye nan cikin fara'a yace yaude nagan su sune Daman kike ta damuna Samiha da nihal mashallah Allah yakara tabbatar da abotarku (Triple)mikewa yayi,Yaya Ina zaka? "Zan shiga cikine "Aah" kayi xamanka ciki zamu shiga ku zo mije na
baku tsarabanku da ya kawo muku tashi sukayi suka barshi anan
Nan fa Ahmad ya shiga wani yanayi da kuma wani tunanin da
bai taba shiga irin saba, tunda yake
bai taba budurwa ba saboda gani yake bai Sami wadda ta dace da shiba amman a yanzu Yana ganin Samiha ita ce irin yarinyar da ya dace yayi rayuwa da ita....
Ana wata ga wata .....
Mai ke shirin faruwa da wanann kauna
A ta bangaran Yaya Dr nihal na kokarin shiga
Ta bangaran Samiha Kuma ga yaya Ahamd na kokarin cusa kansa.
Shin nihal zata Sami nasara asirinta ko yaya kuci gaba da kasancewa da mu.....domin jin yacca zata kaya.
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf
CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER
*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~
Page 14
Su Samiha ana daki ana ta shirme nan momy ta shigo ta dawo daga unguwa Ahmad ta gani a parlour nan yayi mata sannu da zuwa ya naji gidan shiru ina Basma tana daki ita da kawayanta hala su Samiha ne "eh" sune amman momy mai yasa direct kikace sune? saboda Basma bata da wasu kawaye da suka wuce su tana matukar kaunar su em gaskiya ne,nan momy ta wuce ta leka ta dakin Basma suka gaisa da su,momy na matukar kaunar Samiha saboda yarinya ce mai matukar nutsuwa wannan yasa momy ta dade tana son ta fadiwa Samiha kudirinta akanta amman tanajin tsoro tana kira sai Ahmad ya dawo taji ta bakinsa tukun idan ya amince sai suje neman auranta domin ta tabbata yadda Samiha take da hankali koda bata so baza ta bijirewa umarnin mahaifanta ba,zancan da ta riskesu sunayi a dakin ne da zata shiga yayi matuakar tsoratata da tayar mata da hankali labari taji Samiha na basu na yarda kullum yaya Dr ke kara karfin kulawarsa akanta momy tace"Kelan Samiha na da wanda take so? shikkelau duk burin da naci akan Ahmad ya Sami wannan yarinya ya tashi abanza tabbas yadda naji tana bada labarin wannan saurayin nata tana matukar sonsa shikkelau Allah yasa hakane yafi alkairai,Daki ta wuce badan ranta ya so ba gaba daya take Jin ranta babu dadi saboda samin Samiha a matsayin suruka ba karamin sa'a bane amman babu komi.
Nan suka gama shirarsu suka fito sukayiwa yaya Ahamd sallama hankalinsa na kan Samiha ji yake kamar yakara sa yace zai rakata amman Baya son zubar da girman sa domin Ahmad mutum ne kamili nagari mai kirki sannan ga nutsuwa banbancin su daya da Yaya Dr shi Yaya dr yana da girman Kai shi Kuma yaya Ahmad mutum ne mai saukin kai faran faran da kula mutane.
Bayan ta koma gida abin da ta tarar nane ya bata mamaki yaya Dr ne ya dawo yana cin abinci shi kade ba tare da ya jirataba abin da tunda suka taso a rayuwarsu bai taba yiba kelan,da kallo ta bisa yaya ya naga kana cin abinci ban ganeba cin abincin ne bakon abu agurinki ko Mai?
Mamakine yakama Samiha matuka saboda yanayin yadda yake mata maganar babu alamin wasa a tattare da shi nutuswa tayi tukun ta xauna yaya Dr lafiya kuwa ? Mai yake faruwane? wani yabatamaka Rai ne? haka tayi ta binsa da tambayoyi kala-kala kallon da taga yayi matane ya sake tabbatar mata da cewa lalle yau yaya Dr akwai matsala a tattare da shi tashi tayi ta wuce daki saboda zuciyarta ta fada mata taje daga baya idan ya huce ta dawo suci gaba da magana saboda da dukkan alamu anbata masa rai ne.
Daki ta shiga cike da zullumi da tarin tsoro saboda tunda take Bata taba ganin tashin hankali da damuwar sa ba irin yau hankalinta yayi matukar tashi amman ta rika addu'a ubangiji Allah ya yaye masa damuwarsa ranar nan haka Samiha ta kwana tana tunani Dan batayi bacci ba ko daya ga washegari suna da jarabawa ko damar karatun bata samu ba in ta dakko ma kasawa takeyi,ta shirya da safe kamar yadda ta saba bayan tagaama yi musu abinci tunda jarabwan sai karfe goma hakanne yasa take tsaywa tagama komi karfe tara ta fito ta tarar momy da dady ta gaidarsu tambayarsu tayi bai fito ba sukace mata eh,dakinsa ta wuce tayi ta bugawa da kyar ya samu ya zo ya bude mata da sauri ta gaidarsa bai amsaba illa da yace mata lafiya tambayar ta rugurguza mata lissafi amman haka ta daure tace na gama kazo muci abinci mutafi yau ina da jarabawa kije ki nemi abin haya ki hau bani da lokacin da zan kaiki tom abincin fa Yaya?bazan ci ba wai wanann wace iriyar jarabace Samiha ki kyaleni ki fita a rayuwata tunjiya na nuna Miki amman Ina ganin kamar Baki Gane in da na dosaba ko? tom bana son abin yakaimu da wulakanci kifita a rayuwata Yaya Dr wai da bakinka kake furta wannan kalmar Dan Allah mai nayi maka kataimaka ka fadimin na gyra komainene kasan zan iya gyarashi inde saboda Kai ne dan Allah karka gujeni kai kade ne farinciki na a rayuwar nan narasa kowa nawa Idan karabu dani ya zanyi dan allah ka fadimin Mai nayi na gyra dan Allah.
Tsuka yayi ya tura kofan da matukar karfi wanda sai da ya bigeta kuka tayi mai isarta sannan ta dedeta kanta ta fito tambayan ta sukayi yana Ina sai tace musu bacci yakeyi Bata son ta tasheshi bara ta tafi,abin yabasu mamaki Samiha duk tsawon shekarun da tayi aduniya ba su taba gani tafita ba tare da shiba dady yace" Tomshikkelau mije na ajjeki ai nagama abinda nike naci abinci kizo kici abincin sai mu tafi" 'Aah' dady na koshi na makara mutafi idan naje makarantar na siyi wani abin fita sukayi dady ya dauketa dede lokacin da ya ajjeta dede lokacin motar da ake kawo nihal ta sauka,da mamaki nihal ta fito tana jiran taga wa zai fito a motan ganin Samiha abin yabata mamaki tom Yaya Dr mota ya sakene ko mai? abin da ta ganine ya sake daure mata kai ganin dadyn su Yaya Dr da tayi shi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 15