halin gidan sun tsinci kansu cikin tashin hankali mara lissafi irin tashin hankalin da rabon da su shiga irin sa tun mutuwar mahaifan Samiha (Rayuwa ba karabuwa da kalubalai da jarrabawa iri-iri matukar kaga kadena ganin jarrabawan rayuwa a tattare da kai sai de idan ka debe kayanka da ga gaban ubangiji,jarrabawa alama ce ta Imani da Kuma bauta ga ubangiji,ga dukkanin wani bawa hakuri da juriya shine abin da yake bukata dede yadda ka riki kaddaran da Allah yabaka dede cigaban da zaka gani a rayuwan ka, ubangiji Allah kabamu ikon cinye duk wata jarabawa da zamu fuskanta acikin rayuwanmu)Yanayi yayi tsamari damuwa tayi yawa tashin hankali ya bunkasa addu'a ita ce kawai abun da suke furtawa acikin baku nan su bayan wasu a wanni Allah yasa Samiha ta farfado daga dogon suman da tayi farinciki kamar ya kashe su suka rasa inda zasu tsoma ransu saboda momy gani take tamkar Samiha mutuwa tayi sai da ta farfado tukun hankalin ta ya dawo jikinta.
Abu dayane ya tayar musu da hankali yanda Samiha ta farka gaba daya agigice tanayin wasu abubuwa tamkar mai aljanu ko wata zaucacciya gaba daya ta rikice magan ganun takeyi marsa kan gado sannan masu gigita lissafin wanda ke sauraro "Yaya Dr dan Allah karka tafi kabarni kada kayi nisa da rayuwata bazan taba iya rayuwa babu Kai ba na fadimaka duk abinda na fadamaka ne saboda bansan ta ina zan karya alkawarin auran Yaya Ahmad ba bazan taba iya watsa masa kasa a ido ba kai kai ne wanda ya rayu dani tun Ina yarinya yabani farinciki,sannan alokacin da ka gujeni shine wanda ya zo yabani farinciki alokacin da nike tunanin narasa duk wani jindadi hakika duk cikin ku babu wanda yakamata na juyawa baya saboda duk kaunata kuke domin Allah,ni bansan ya xanyiba Allah ubangiji kabani mafita kuka takeyi tunkarfi cike da damuwa tashin hankali mara lissafi ita kanta bata san tanayi ba,wani kuka ne ya kubcewa momy wanda bata san lokacin da ta fara ba dady ne yace "Kiyi hakuri hajiya inshallah Allah zai kawomana mafita"Haba alhaji kagafa duk yarannan neman zaucewa sukeyi Kuma duk dan sanadin soyayyya damuwa tayi musu yawa suna rayuwar su cikin farinciki amman wanann tsinanniyar nihal din ta zo ta tarwatsa musu farinciki wallahi da nasan zata zama matsala acikin gidana bazan taba bari suyi mu'amala da Samiha ba kukan da momy takeyi yana matukar taba zuciyar dady saboda sai ka rantse karamar yarinyace ke wanann kukan"
Rarrashin ta dady yafara duk da cewa shima juriya yakeyi duk wani karfin gwaiwar sa yakare yama rasa ya zeyi hajiya ko da nihal bata shigo rayuwan Samiha ba tunda Allah ya tsara haka zai faru da su tom sai yafaru sanadin wata duk abin da Allah ya tsara babu wanda ya isa ya kaucewa wannan kaddarrar rarrashinta dady yayi tayi da kyar ya samu ta tsagaita kukan da takeyi,Samiha sukaji maganganun da takeyi sunyi yawa gaba daya ta koma mahaukaciya futuk Kai idan ka ganta sai ka tausaya mata,kan ta sukayi suna ta kama sunanta amman ina bata san sunayiba dady ne yayi sauri yaje yakira likita shikansa likita sai da ya tausayawa Samiha alluran bacci yayi mata saboda ita kadece mafita bashi da wani abu da zai iyayi.
Nan ta samu bacci ya dauketa nan likita yace "A dauke Yaya Dr a akawo shi dakin da Samiha take yana ganin hakan zai taimaka wajan bashi farinciki a dullokacin da ya farfado "
Haka kuwa akayi da yake asibitin kudine na masu kudi kowa shi kadene a dakinsa aka dakko sa aka sanya gadonsa kusa da na Samiha.
Haka suka kwana a wanann asibitin ba tare da sun run tsaba har asuba kuma duk cikin su biyun babu wanda ya farfado bayan dady ya dawo daga sallan asuba yacewa momy taje gida ta kintsa ta hado break fast "Fuskarta car da hawaye tace alhaji bazan iya ba idan na hadoma waye zai ci daga ni har Kai babu mai iya ci"Tom ai ko saboda su Idan suka farka suma ko sunfarka ba iya ci zasuyi ba kawai kaje ka hado musu wani abun a restaurant saboda kar su farka ba wani abin ko yaya nasan zasu taba tom hajiya.
Kirane ya shigo wayan dady ya dagawa yayi dafa gefen da ake Kiran aka gaisar da shi akace Basma ce kawar Samiha ayyah!!Basma yakike alhamdulillah dady tunjiya nake kiran wayan momy amman bata shiga shine nace bara na kiraka sai kahadani da ita mikawa momy wayan yayi yace mata Basma ce.
yana mikawa momy wayan ta fashe da wani sabon kuka abin da ya gigita zuciyan Basma momy lafiya mai yake faruwa tunjiya nida Yaya Ahmad mike ta Kiran wayar ki amman shiru yanzuma shiyasakani a gaba na kira wayan dady na tambayar ma sa ko lafiya da kyar momy ta iya cewa Basma Samiha da Suraj momy ta sake fashewa da matsanancin kuka mai bada tausyayi momy dan Allah ki fadimin mai yake faruwa dasu momy ki fadimin dady ne ya ansa wayan a hannunta saboda ta kasa magana sautin kukan tane kawai ke futa dady ne yace "Basma mina asibiti nan ya fadimata address din asibitin ya kashe wayan".
Gaba daya hantar Basma jitayi tana Kadawa tom mai ya samesu Kuma de ai Samiha ce batta lafiya ita za a iya cewa ko jinyar ce ta sake tashi aka kai ta asibiti tom amamn Yaya Dr fa? "Innalillahi wa inna ilahiee raji'un shine abinda take ta furtawa"Yaya Ahmad ne yace "Duk wanan abun ba zai kai mu ba ki tashi mu shirya mu tafi asibitin"Yaya da wanann asubar haka zakice taya kike tunanin tunjiya bansan halin da matar da zan aura ke cikiba hankalina zai kwanta taya kike tunanin nutuswa zata sameni bayan mai samar min nutuswar tana can bansan halin da takeciki ba haba Basma Samiha fa ita ce rayuwata Ina son ta Ina matukar kaunarta wallahi Ina Jin tamkar idan nasarasata bazan iya rayuwaba.
Haba yaya duk mai yakawo fadin wanann inshallah babu abin da zai sa karasa Samiha kana tare da ita har karshan rayuwanka Allah yasa ta shi kije ki shirya wane shiryawa yaya shijab dina kawai zan zurmiki maitafi bana cikin nutuswan da zan iya wani shiri nan suka fita ba tare da maman su da abban su sun saniba,mai gadi suka barwa sallahun idan sun tashi ya fadi musu sunje unguwa nan suka tafi asibitin Ahamd jiyake kamar ya tashi sama saboda babban burinsa yaje yaga mai yake faruwa da Samiha.
Sun isa asibiti lafiya suna shiga dakin abun da ya ganine ya sake fadar masa da gaba ga gadon Samiha ga na Yaya Dr hakan na nufin tare aka kawo su kelan gaba daya tsorata yayi tashin hankali ya ziryaci zuciyan sa Yana matukar tsoron rasa Samiha a rayuwan sa yana wanann tsoron.
Mai ke shirin faruwa? tambayar da Ahmad ke tayiwa zuciyarsa kelan amman yakasa samin ansar shiga sukayi sukayi sallama momy ce ta dago Kai ta kallesu yanayin yadda sukaga idanuwan momy sunyi jajir fuskanta tayi lubu-lubu tsabar kuka hakan yasake tayar musu da hankali tabbas ba karaman matsala bace.
Ahmad kameewa yayi aguri daya yakasa zaune yakasa matsawa ko'ina Basma ce tayi karfin halin matsawa kusa da momy ta tambayeta mai ke faruwa da jajayan idanuwanta wanda suka rine tsabaer kuka damuwa da tashin hankali ta dago kai ta kalli Basma nan ta labarta mata komi tundaga abinda yafaru daga gida da su ka dakko Yaya dr suka kawoshi da abinda likita yace da kuma dalilin faduwar Samiha nan duk ta fada musu Basma batasan lokacin da ta kece da wani matsanancin kuka ba,shiko Yaya Ahmad saboda tsabar tashin hankali da takaici yakasa cewa komi yakuma kasa kukan kawai zuciyarsa yakejin tamkar ta buga saboda matsanancin tashin hankalin da yake ciki...............
Ubangiji rabbi Kaci gaba da dafa mana kasake rufa mana asiri duniya da lahira
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf
CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER
*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~
Page 25
Ahmad tunani yake mai zai faru sannan mai ke shirin faruwa ta Ina zai rabu da Samiha bayan sabawar da yayi da ita a dan karamin lokacin nan baya tunanin zai iya sadaukar da soyayyyar sa ga wani alhalin yana ganin yadda Samiha ta karbeshi tom amman ba lalle yadda Samiha taga Yaya Dr ya dawo gareta ta amince da niba,irin wannan sake -saken su Ahmad yayi tayi acikin zuciyarsa amman yakasa samin mafita addua yake kawai acikin zuciyar sa Allah ya kawo masa mafita yakuma zaba masa abin da yafi zama alkairai.
Haka suka zauna dukan su su ukun momy Basma Ahmad,kowa da kalar tunanin da yakeyi acikin ransa sun shafe wajan awa uku a haka can suka jiyo tari dagowar da sukayi sukaga Samiha ce ta farfado alhamdulillah ta farfado ba wanann suruton karasowa kusa da ita Ahamd yayi Samiha taji yayi magana sai tace
"Dan Allah yaya Dr ka tashi karka mutu Ina nan tare da kai Idan ka mutu bazan iya rayuwa acikin duniyar nan ba dan Allah ka tashi"gaba daya Ahmad jiyayi gwiwarsa tayi sanyi yarasa mai yake masa dadi "Innalillahi wa inna ilahiee raji'un "yake ta furtawa tabbas tawa ta kare yakamata na hakura da Samiha na tabbata daman ta karbenine dan kar ta watsamin kasa a ido domin kuwa na tabbata da tana tare da Yaya Dr nima bazan tarki cewa Ina son taba haka yake ta sake-sake har Samiha ta dawo cikin hayyacinta dede lokacin dady ya shigo yayi musu take a way kamar yadda momy tace.
Bamsa ce ta karbi abincin taje ta tashi Samiha ta kaita bandaki tayi mata brush suka dawo nan de da kyar ta samu taci abincin bayan ta kammala ta dan sami nutuswa Ahmad yakarasa kusa da ita ya mata sannu.
Tace "Yaya Ahmad kaga yau mince xamije mu gurin mai photon nan amman Allah bai yiba gani nan kwance a a gadon asibiti".
Karki damu Samiha Allah yabaki lafiya Kuma ko kinsamu sauki bana tunanin ai zuwan zai yiyu mai yasa?
Yaya Ahmad yace "Samiha zuciyanki cike take da kaunar Suraj na tabbata kin amince danine dan karki watsaminn kasa a ido kuma kar mahaifan ki suce kinbijire musu Samiha Ina sonki Ina matukar kaunarki hakanne ma yasa bazan taba yarda na biya son zuciyata na cutar dakeba wallahi Samiha zan iya bada rayuwata domin ke zan iya komi domin ke,Ina sonki matukar so Samiha, saboda haka na hakura da soyayyyar ki tunda Allah ya dawo da suraj cikin hayyacinsa ki auresa na sadaukar masa dake domin farincikin ki shine nawa Kuma na tabbata idan kika auresa zanyi farinciki saboda nasan kinsami farincikinki""
Aah Yaya Ahmad Aah bazan taba iya karya alkawarin da na maka ba Allah yariga da yaraba soyayyya ta da yaya Dr ya hada da kai babu wani abu da zai rabata sai na cika alkawarin da na dauka maka na bazan taba barinkaa ba inshallah bazan barka ba din Ina tare da kai.
Samiha mai ne amfanin kincikamin alkawari amman cikin zuciyarki kina rayuwa da soyayyyar wani kina son kiyi rayuwan auranki cikin fushin ubangiji Samiha Ina son yi adalcine kada na biya son zuciyata Ina son dukkanin mu mu rayu mina ganin kirki da mutuncin juna.
Hakane Yaya Ahmad amman koma mai ne babu abinda zai hana auran mu rana itayau Koda ana daurawa zan mutu a wuce dani makarbarta.
Daga gefe suka jiyo ka salalliyar murya mai cike da da na Sani da tausayi Samiha dan Allah ki tausayamin kiji kaina bazan taba iya cigaba da rayuwa ba tare da keba bansan ya xanyiba idan kika aure wani a yanzu haka Ina jin zuciayata tana yimin wani zafi wanda nakejin tamkar zafin mutuwane samiha bazan iya rayuwa babu keba bazan iya ba ina sonki Ina matukar kaunarki dan Allah kutaimakamin kiyarda dani a karo na biyu dan Allah .
Gaba daya Samiha gigicewa tayi zuciyarta taji baza taba samin nutuuwaba idan bata karasa gurinsa ba mikewa tayi tamanta da jinyar dake damunta ta karasa gurinsa rungumeshi tayi tana wani kuka mai tsuma zuciya da lissafinta ta rasa mai keyi mata dadi tace "Yaya Dr dan Allah kadena fadin irin wanann magan ganun kasani cewa kai ne farinciki na kuma kai ne rayuwata Ina sonka bazan taba son wani bayanka ba amman mai
ne hukuncina ankusa dauramin aure naci amanar hakan ya zama dole miyi hakuri da juna"
Ahamd ne yayi saurin karasowa gurinta samiha wai meke damunki kina cikin wani hali shima yana cikin wani hali ammman Kina maganar aurena dake wallahi Samiha na hakura Ina Kuma yi muku fatan alkairai Yaya Dr ne ya dago kai ya kallesa yana magana da kyar "Nagode Ahamd nagode yadda ka farantamin ubangiji Allah ya farantamaka"
Yaya Ahamd kansa da Basma kuka ne ya kufce musu kuma kukan ba wai na tausayawa kansa akan rasa Samiha da yayi ba Aah na tausayawa Samiha da Yaya Dr akan kaunar da sukeyiwa juna da halin da suka fada.
Hakika kauna jigo ce Kuma farinciki ce matukar bawa ya fada tarkon soyayyya yana shiga matuakar damuwa kafin Allah yakawo masa mafita Yaya Ahamd ke fadin wanann aransa ""Hakika nasani zanshiga matuakar damuwa na rashinki Samiha amman inshallah albarkacin sadaukar muku da farinciki na da nayi na tabbbata Allah ba zai tozarta niba Ina fatan ubangiji Allah ya kawomin da sauki ya bani ikon cinye wannan jarabawar Ina kaunar ki Samiha"
Kawai ya fice daga cikin asibitin kuka wiwi Basma take tare da alhinin halin da Yayan ta zai shiga saboda ita ce sheda akan matsanancin son da yakeyiwa Samiha momy da dady kuwa sun kasa furta komi sai hawaye dake futa acikin fuskokin su sun kasa jurewa.
Basma ce ta tashi ta karasa kusa da Yaya Dr da Samiha tace "Ina fatan baza ku sake bawa kowa kofar shigowa rayuwan kuba Ina fatan zaku kula da soyayyyar ku fiye da yadda kuka kula da ita abaya Ina yi muku fatan nasara zanje gida na dawo anjima "
Nan tayiwa so momy sallama ta tafi bayan tafiyan ta momy da dady suka jawo Samiha da yaya Dr kunne sannan sukayi musu fatan alkairai.
Bayan kwana uku aka sallamesu daga asitibi kullum Basma na zuwa ta yini sai ta koma gida Yaya Ahmad kuwa tunda ya tafi bai dawo ba domin ganin Basma tamkar tadawa kansa ciwon dake cikin zuciyar sane.
Ansallamesu sun koma gida sunci gaba da rayuwa cikin farinciki.
A bangaran Yaya Ahmad kuwa ya sake karfafa ibadarsa a kullum yana cikin karatun alkur'ani tare da tashi tsakar dare duk da cewa yana matukar cikin damuwa sannan kullum sai ya zubar da hawaye saboda kewan Samiha amman ya daure yakuma kaiwa Allah kukansa domin shi kadene ya san dalilin da yasa haka ta samesa,yace ba zai tuhumi ubangiji ba Yana Kuma matuakar godiya da kaddarar da Allah ya dora masa ya tabbatar shi zai yaye masa.
Kwanci tashi sun shafe wata daya da sallamowa daga asibiti Kuma alhamdulillah jikinsu yayi matukar sauki soyayyyar su kuma ta sake kankama fiye da da,a yanzu Yaya Dr ya sake rike Samiha matuka baya son duk wani abu da zai sa yayi nesa da shi yakuma sake samin kusanci da ubangijin sa domin sake kare kansa daga dukkan mai nufarsa da sharri.
Watarana nihal ta fito domin tsawon wata guda bata ji labari akan suba da alama wani abu bai faruba ta tabbata da wani abu yafaru zataji labari abu ya yada gari kamar yadda boka ya fadamata hakanne yasa ta shirya domin komawa gurinsa yace mata "kwata kwata aikinne yaki yiyuwa Yaya Dr yakarawa kansa tsari matuka fiye da da hakama Samiha ya sake bata wasu addu'aoin masu matukar zafi amman yana so ne dullokacin da ya shiga bandaki anan zai tura masa aljanin da xai gigita masa lissafi yakuma lalata musu rayuwan su ko Ina ana xaginsu akan abunda za su na aikatawa amman boka sai yaushe yanzufa yau tsawon wata guda kelan narasa maike min dadi Samiha ta samu damar sake mallakarsa aka ro na biyu karki damu dole aikinnan zai wakana.
Tom kasake dubawa yanzu mana ko xa'adace aiko yana dubawa aka dace Yaya Dr ne ya shiga bandaki domin wanka nan ko murna kamar ta kashe su nan a take a lokacin yace aiki ya kammala ki koma daga nan zuwa kwana uku na tabbata sai kinji labarin da sai kinzo nan Kina min godiya nan ta sake ajjemasa makudan kudi ta tafi tana murna.
Bayan yaya Dr yafito a wanka ya Saka kayan sa yake jin jikinsa wani iri cikin xazzafar sha'awarar da tunda yake bai taba tsintar Kan saba yanajin idan bai sami mafitaba zai iya mutuwa kamar tsohon mahaukaci yafito falo yaga babu kowa dakin samiha ya wuce adede lokacin ta fito a wanka sanye take da towel a tsorace ta juyo Yaya Dr lafiya?domin ta sani baya taba shigowa dakin ta ba tare da neman iziniba kanta yayi tamakar wani tsohon maye ya wawireta nan yafara aikamata da sakon ni wanda ta kasa gane ina suka dosa Yaya Dr kabari kabari dan Allah anya kana cikin hayyacinka kuwa bai san tanayi ba tayi-tayi ta kufce ta kasa haka yayi tayi har yagama abin da zai gama ya sami nutuswa kuka kawai takeyi tana da na sanin zuwanta duniya wanann wace iriyar kaddarace da jarrabawa ta rayuwa nan ya juyo ya kalleta tana ta kuka kusa da ita ya matso yana ta bata hakuri dan Allah Samiha kiyi hakuri bansan yadda akayi haka ta faruba kiyafemin yanzu Yaya Dr da ace ansami matsala ka batarmin da mutunci nafa kiyi hakuri ai hakan bai faruba amman da yafaru ba da ya zanyi da rayuwata inshallah bazan taba zubarmiki da mutunci ba sai kinkaishi gidana,tom mai ne maraba akan abun da ka aikata din Aah Samiha da maraba dan Allah kiyi hakuri bazai sake faruwaba kuka take sosai nan ya rarasheta ya fita.Kuka taci gaba dayi tana tunanin mai ya sauya Yaya Dr haka tabbabsa akwai wani abu Allah kasa kar haka ta sake faruwa in kuwa ta sake faruwa lokacin zamana agidan nan ya zo karshe bazan zauna ya ciremin mutunci naba.
Shikuwa daki yakoma yana shiga yafara matsanancin kuka mai dauke da dana sani yana tunanin shine ya aikatawa Samiha haka yah Allah ka yafemin haka yayi ta jera kuka tamkar karamin yaro da kyar ya iya mikewa yayi wanka yafita .........
Astagfirullah astagfirullah ubangiji Allah ka gafarta mana zunubanmu Kaci gaba da bamu ikon yaki da shedan ka tsearatar mana da imanin mu kakuma rabamu da duniya da iyayanmu lafiya.
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf
CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER
*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~
Page 26
Bana son na kasance daya daga cikin samarin dake kokarin aikata fasadi da emmatan su kafin aure, ban taba sakawa azuciyata dede da hannun Samiha zan rike da sunan sha'awaba har sai lokacin da na aureta, amman sai gashi wai nine yau nayi kokarin ketawa Samiha haddi"Innalillahi wa inna ilahiee raji'un"Allah astagfirullah.
Samiha kuwa ta ma kame gaba daya aguri daya ta rasa mai ke mata dadi mikewa tayi ta shiga tayi wanka ta zo ta Saka kayanta.
Abubuwa sunci gaba da tafiya ire_iren wadannnan kuma boka ya fadiwa nihal tabbas aikin su yayi murna take tayi matuka sai de yace mata suna yin abunsune cikin shauki da kaunar juna shi Kuma so yayi ya cire wannan a tsakanin su yanayi mata abin wajan tilastawa,hakanne yasa yakara wani sabon aikin yacca Yaya Dr zai ji ya tsani Samiha sannan ba shi da buri illa yayi ta lalata da ita yaga ya lalata mata rayuwar ta aikin boka kuwa yayi domin adede lokacin da yake kan aikin Samiha da Yaya Dr suna kwance kan gado suna sheke ayansu cikin soyayyya da farincikin kasancewa da juna hakanne yasa asirin yayi saurin ta siri akansa.
Bayan sallar magrib sun zo zasu ci abinci yaya Dr ya fito agaban su dady ya zo ya wawuri Samiha yafara sumbatarta kamar ba gobe dady da momy gaba daya rikicewa sukayi suka fara innalillahi magana suke musu amman Ina dukkanin su sunyi nisa wajan aikata abin da suke aikatawa kuka wiwi momy ta fara da kyar dady ya wawiri Yaya Dr ya daga shi da kan Samiha.
Kasa yi masa fada yayi saboda kawai jikin ya bashi tabbas ba lafiya ba mikewa Samiha tayi ta tafi daki shi Kuma yaya dr ya fice.
Da kyar dady ya rarrashi momy nan yace mata su tashi suje gurin liman din masallacin unguwarsu su fada masa abin dake faruwa nan ta mike sukaje ya basua adduoi ya Kuma fada musu da izinin Allah komi zai yi sauki har kace ta asiri nan suka dawo gida ranar tayi dede da ran da nihal takoma gun boka nan yake fadimata mahaifansu sun dauki hanyar lalata komi nan tace ayi musu abin da zasu tsani Samiha nan ko boka yace angama ta basa yan kudadansa ta tafi.
Da daddre momy sun zo kwnaciya take cewa dady "Alhaji Ina ganin mikori yarinyar nan daga cikin gidan taje ta nemi wani gurin in ba hakaba bana tunanin mina da mafita "abinka da abin asiri nan da nan dady ya amince.
Da safa Samiha tagama aiki yadda ta saba taga momy ta shiga dakinta ta hadomata duk wani kayanta kan kataraf tace ta fita ta bar gidan momy ban ganeba na fita naje Ina Ina da wani gun da ya wuce nan ne,ki fita duk inda zakije kije amman baza ki zauna mana agida ki lalata mana tarbiyyar yaro ba kije duk inda kikaga Zaki iya zuwa kije kiyi karuwancinki .
Tabbas rayuwata cikin kaddara da jarabwa zata kare Samiha ke fadin wanann cikin zuciyarta na shiga uku Ina zan saka Kai na Ina xanje ya zanyi da rayuwata na shiga uku yah Allah ka ka kawomin mafita,matsawa Samiha tayi ta kama kafar momy tana ta rokon ta da Allah akan tayi hakuri tabarta tayi mata alkawarin zata fita a aharkan yaya Dr amman dan Allah ta barta taci gaba da zama acikin gidan fur momy ta murze I donta tace Samiha baza ta zaunaba daga karshe da taga Samiha na niyyar sawa makota suji abin dake faruwa daukan kayan Samiha tayi ta watsa waje sanann ta kulle kofanta.........
https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf
CREATED AND WRITTEN
BY
ZEEY NASEER
*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙*
We shine all over the world
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~
Page 27
"innalillahi wa inna ilahiee raji'un"shine abin da Samiha ke ta furtawa,tana kokarin tattara kayanta ta fice domin ita bata san ko Ina ba su sune wanda ta sani Kuma bata San garin kakantaba wato baban mahaifiyarta da can zata tafi kuka takeyi tana tattara kaya amman tabbas zuciyarta ta yanke ta Kuma rikice duk wata dabara ta ta takare fatan ta da addu'ar ta ubangiji ya kawo mata mafita ta wani bangaran
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 15