Share this page
Kuma tana adduar Allah yasa tana fita mota ta bigeta shikkelau ta huta. Tana tsakiyar tattara kayan momy ta tsaye akanta ta gama ta bar mata gida yaya Dr yayi sallama wani sanyi taji a ranta tamkar ance mata cikin gidan zata koma,ikon Allah hakika Allah yanaa sona Abdullokacin da nake cikin matsala yaya Dr shine wanda ke futarni acikinta, gabansa ne yayi mummunar faduwa tom mai yake faruwa da sauri ya zo momy lafiya sai ka tambayeta ai ita nace ta tattara kayanta tabar min gida ne bazan iya cigaba da zama da ita ba momy Samiha ce fa eh Samihan uwata ce kasa cewa komi yayi kawai ya wuce daki. Samiha cikin zuciyar ta tace shikkelau shima ba zai taimakamin ba na shiga uku har ta gama hada kayan ta tafita Yaya Dr bai fito ba hakanne ya sake cire mata yakini na zai taimaka mata ta fita ta Kalli gabas ta Kalli yamma amman Ina ta rasa duk wata madafa bayan minti goma tana tsaye a kofar gidan da tunin ko yaya Dr zai futo amman shiru hakanne yasa ta hakura zata tafi ta juya kelan zata tafi taji ankwala mata kira juyowa tayi da sauri taga Yaya Dr ne "Alhamdulillah" shine abinda ta furta karasowa yayi da sauri ya rungume ta Samiha kiyi hakuri momy mahaifiyatace bani da damar tankamata nasani yaya Dr. "Amman yanzu ya zanyi da rayuwata Ina zanje Ina zan dosa wanann duniyar da tacika da mutane marasa gaskiya duniyar da tacika da mutane marasa tausayi duniyar da cika da mutane suna da shi amman baza su taimaka makaba,yaya Dr wa zan dosa nace ya taimakamim na shiga uku yaya Dr" Dagowa yayi ya kalleta cikin bacin rai amman Samiha kin ban mamaki kina da ni kike tunanin rayuwanki zata salwanta Kina da ni kike tunanin zan barki cikin matsala kina tunanin zan barki ki tafine tom idan na barki kika tafi miye amfanine?ashe banni da wani amfani inde bazan taimakawa wacca nake so ba ashe banni da amfani inde banyi bakin kokarina wajan sharewa wacca nake so damuwanta ba Samiha inde zan barki ki tafi sai de mutafi tare domin kece rayuwata Kuma kece duk wani farinciki na wallahi bazan taba iya yini daya ba kya kusa dani ba duk wani tsanani duk wata damuwa Ina tare dake bazan taba barinki ba domin Ina sonki". Dagowa tayi da jajayan idanuwan ta tace "Nagode sosai da kakasance cikin rayuwata ba domin kaiba tabbas da rayuwata ta salwanta duk da ubangiji shike kula damu ammam kai ya aiko Kane dan ka zama sanadi Ina sonka yaya Dr bazan taba rayuwa da wani da na miji matsayin mijina idan ba kai ba" Handkerchief ya dakko ya mika mata ta share hawayan ta amman takasa karba domin tana Jin wanan hawayan baza su taba tsayawa ba Janta yayi suka zauna akan wani dan damali ya fara share mata hawayanta adede lokacin sai ga nihal da kawarta Atika sun zo wucewa zuciyarta taji tayi wani mugun bugawa duk da tabbas taga tabbaci akan abin da aikin da malam yayi na baza suji kunyan kowa ba gahsi nan akan titi sun zauna yana share mata hawaye cinyoyin su hada dana juna taji dadin hakan hakanne ya tabbbatar mata ainkinta yana kan dede,sai de yadda taga suna abubuwa cikin soyayyya da kulawa ya sake tayarmata da hankali tabbas dole tayi wani abin juyowa Samiha tayi kawai sukayi Ido hudu da ita tunano abin da ta mata tayi taji tamkar taje ta shaketa ta mutu sai kuma zuciyar ta ta kawo mata wata dabara akantayi wani abu da idan de ta tuna shi ko da nan da shekarane sai taji babu dadi. Kamar an hankadota ta sake matsowa kusa da inda yaya Dr yake dan shi wayan shine a hannunsa bai masan mai akeyiba bakinsa ta kama ta fara sakarmasa wata kyakkyawan sunbata wacca ta saka ba shi da akeyiwa ba harta nihal da kawarta Atika sai da suka fara fita a hayyacinsa saboda yacca Samiha ke abin cikin salo da matukar birgewa babu shiri suka bar gurin. Suna matsawa Nihal tace lalle yarinyar na ta rainamin wayo agabana takeyiwa yaya dr wannan abin Atika akwai matsala Ina matukar son yaya Dr wai ba yacca za ayi asake wani abin ya so ni sai de mu sake gwada wani malamin amman de kinji abin da wancan malamin yace tomshikkelau inde akwai wanin mijemana akwai su sosai makuwa kuma wadanda suka fishi mugunta da iya aiki aiko zamuje tom sai kishirya gobe mije. Samiha da yaya da kyar suka samu sukayi control din kansu yace mata ta shi mije ina xamije Samiha kelan kede ki tashi . Daman bai shiga da motarsa gida ba nan ya dauki kayanta ya sanya mata cikin mota sanann yaja nan bayan layinsu kadan yaje yayi parking akofar wani hadaddan gida juyowa Samiha tayi ta kallesa zatayi magana ya rufe mata baki. Bayan sun tsaya ya dauki kayanta ya shiga da shi ciki ita ma ta shiga babu fargaba ko tsoro. "Samiha anan zaki zauna har karshan rayuwanki domin da kanki kika bada xanan gidan nan kikace ayi da kanki kika bada duk wani fasali na wanann gida a matsayin gidan da zamu zauna idan minyi aure tom yanzu zaki zauna anan kafin inshallah nan da wani lokacin zan san yadda za ayi zan fadiwa dady sai a daura mana aure" Wasu zafafan hawaye ne suka zubo acikin idanuwan Samiha ta matso kusa da yaya Dr ya durkusa bansan mai zance da kai bansan Kalmar da zanyi amfani da ita wajan gode maka ba,ka zamo tamkar uba agareni ka sharemin duk wani kuka na inde ka ganni cikin damuwa kafin nayi magana akan abin dake da muna kake karantar halin da Nike cike kasmaarmin da shi hakika samin masoyi kamar ka a wanann lokacin yana da matukar wahala Ina kaunar ka yaya Dr Ina maka fatan nasara cikin rayuwan ka yadda baka da buri sai na kulawa da ni Ina fatan ubangiji yaci gaba da tabbatar da farincikin ka ya sake buda maka. Durkusawa yayi ya dagota ya rungume ta akirjinsa karki damu Samiha inde Ina tare da ke inshallah bazan taba bari ki wulakanta ba goge hawayan ko so kike nima kisa na fara Aah yaya tom goge ta goge hawayan tana murmushi kama mata kayan ta yayi sukaje aka ajje a dakin gado da yaake babu wani abu da Yaya Dr bai saka acikin gidan ba jitayi zuciyarta ta fara samin nutuswa da sukuni amman ta Ina zata fara rayuwa ita kade ba tare da momy ba wadda tayi sabawar da ita sabawar da batayi da mahaifiyarta ba hawaye taji na kokarin zubo mata sai tayi kokarin tsaidasa da yakinin inshallah momy zata hakura ta barta ta koma gida. Samiha na'am yaya zanje na samomiki dan kayan abincin da zakina dafawa sai Kuma na siyo Meiki ko dan karamin gas ne tom yaya nagode sosai ke ni kidena wannan godiyar kin manta cewa ke masoyi yata ce idan ban miki abububa wa zanyiwa idan ba kyautawa wadan da mike so ba wa zami kyautatawa hakane yaya tom sai na dawo ki kuka da kanki, inshallah Yaya. Bayan yafita Samiha ta xauna take ta tunanin yacca rayuwarta ke sauya da turgudewa da yardar Allah ke kawo mata mafita "Alhamdulillah"shine abin da kawai take furtawa. Ba jimawa kadan ya dawo ya kawo mata uban kaya sai kace wanda zata shekara Yaya wanann kayan abincin ai yayi yawa,kin manta ba ke kade bace ni da wane keda yaya Dr mana ko kina tunanin zan na cin abinci a wani gurinne bazan iyaba na saba da daddadan girkinki murmushi tayi tace Yaya Dr dina ni kade nan suka kwashe kayan suka Kai kitchen bayan sun fito sun zauna yace rintse idon ki ta rufe idon ta ya dora mata abu akan tafin hannunta yace bude tana budewa taga waya wani wawan tsalle tayi ta rike Yaya Dr tana ta murna wani farinciki yayi ganin Samiha cikin wanan farinciki domin ya kwan biyu bai ga hakan daga gareta ba nan fa tace "Nagode sosai da sosai yaya Dr ubangiji Allah yaci gaba da dafa maka albarkacin annabi ya sake buda maka kofofin samu Yaya ka zamomin uba kana min komi kana bani komi ka bani farinciki kaciremin duk wata damuwa ta kabani duk abin bukata Yaya Ina matukar kaunar ka. Samiha ya isa haka sai de zan fadamiki wani abu gashi nan da sim card aciki Allah duk ranar da naga wani na miji ya kiraki zan kwace Kuma bazan sake baki wayaba hakama baza ta faru ba Yaya. Nan yace mata zai tashi ya tafi anjima zai dawo okay sir nagode yafita kowannen su fuskar sa cike da farinciki da walwala. Rayuwan ta fara tafiyawa su Samiha cikin farinciki sai de fa suna nan kullum cikin aikata alfashan su amman suna cikin farinciki. A can kuwa momy na tunanin ko ina Samiha ta tafi abin na damun ta amman Kuma zuciyarta na fada mata abin da ta aikata shine dede Yaya Dr yayiwa Samiha matukar gargadi akan kartayar da tafito domin kar Jama'a su gane anan take kar aje a fadiwa su momy sai de su Jama'a duk yacca ka Kai ga boye abu sai sun tonoshi yanzu sunfara gane rayuwan da Samiha da Yaya Dr sukeyi acikin wanann gida sun Kuma gani tare suke sun Kuma san ba aure garesu ba domin duk unguwa dayane da unguwan su babu nisa. Watarana tace yaya Dr Ina son ganin Basma mai Zaki mata dan Allah nasan bata san inda nakeba na tabbata ita ma tana can tana nemana kataimaka min kaje ka dakko, ta har gida yaje yayi sallama da ita yakuma fadamata abin da yakawo shi tayi murna sosai domin tana cikin matuakar tashin hankali da taje gida momy ta mata rashin mutunci takuma fada mata Samiha ta koreta,ta zo ta fadawa Yaya Ahmad kullum Samiha da yaya Ahmad suna yawo ko Allah zai sa adace su san inda take amman Allah bai ba,ta shiga ta fadiwa maman su suna tare da yaya Ahmad ta fadi musu cew yaya Dr ne ya zo zai dauketa Samiha na son ganinta yaya Ahmad mikewa yayi cikin murna yace "Alhamdulillah tun ranar da Samiha ba a san inda takoma ba nake cikin tashin hankali sai yanzu na sami nutuswa" Yanzu a Ina take ina xakuje ban saniba ya de cemin Idan minje na gani tomshikkelau sai kindawo yaya Ahmad yace "Dan Allah kice Ina gaidata inshallah Yaya zan fadamata". Nan ta futa fuskarta cike da walwala da farinciki ya kaita gidan da samiha take farinciki kamar ya kashe su sunga juna nan suka zauna Samiha tabata labarin abin da yafaru tundaga farko da dalilin da yasa momy ta koreta. Basma abin dake bani mamaki da Yaya Dr shine kinsan Allah ada ki tafi hannuna bai taba dora hannunsa ba saboda matuakar taka tsantsan din da yakeyi akan bazai aikata ba dede ba dani Yaya Dr yana da matukar tsoron Allah ammam lokaci guda ya sauya Basma a kullum yaya Dr sai yazo ya aikata abin da zai aikata dani ya jagwalwalni ya mayarni tamkar kayan wanki,abin Yana damuna. Tabass Samiha akwai matsala tom mai yasa ba za ki hana saba idan ya zo zai aikata bazan iya ba Basma bazan iyaba. Amman Ina da wata tantama Anya ba nihal bace ta sake aikata wanann abin akan Yaya Dr haba de basma mai yasa nihal zatayi haka Ina tunanin baza ta tabamin abin da zai lalatamin rayuwa ba karki manta irin amincin da ke tsakanin mu wancan ma da tayi tayine saboda sonsa.Amman nihal nasan bazatayi abin da zai wargaxamin rayuwaba. Ke Samiha dadina dake yarda shi wancan din da tayi kinsan zata aikatane har kike wani yabonta akan baza ta aikataba king ni nagama sawa araina ita ta aikata Kuma inshallah nihal sai tayi da na sanin abunda ta aikata ki kwnatar da hankalinki inshallah xan kawo karshan komi. Ta Yaya Basma?idan tayarda da boka mukuma minyarda da ayar alkur'ani tare da addu'a babu wani abu da baza su iya magancewa ba inshallah duk wanann abubuwan da tayi sai sun koma kanta,akwai wani limami a unguwan bayan layin mu Allah yabashi ilimin matuka akan wanann abin yana karya asiri sosai xanje na masa bayanin komi inshallah albarkacin darajar annabi sai nihal tazo ta durkusa agabanki ta nemi yafiyarki kici gaba da Hakuri Samiha inshallah duk tsanani Ina tare dake..... Barkan mu da ranar juma'a ubangiji ya hadamu da dukkanin alkairain dake cikin ta yakuma rabamu da dukkanin wani sharrinta Albarkacin darajar fiyayyan halitta annabi muhammadu (SAW). https://chat.whatsapp.com/FdN9LskESVf6ESy63R3QWf CREATED AND WRITTEN BY ZEEY NASEER *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION'S🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بِسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~~~ Page 28 Basma tashi tayi ta koma gida ta tsinci kanta da bawa mamansu duk labarin abin da yake faruwa dede lokacin Ahmad zai shigo yaji tana bada labarin sanin watakil idan ya shigo zata iya dakatawa yasaka ya tsaya sai da yagama Jin komi kuka wiwi yakeyi saboda tunani iri-iri da ya sarkafe masa zuciya tausayin samihane yai matukar kama shi ya rasa mai yake masa dadi fasa shigowa gidan yayi kawai ya juya ya tafi. Maman su ce tace "Basma karki damu inshallah komi yayi farko zaiyi karshe zan taimakawa Samiha kamar yarda idan kece a irin halin ta tsinci kanta nasan Kinga dole zanyi fafutuka wajan ganin kinsami maslaha tom da yardar Allah itama zanyi mata haka, domin kuwa na dauki Samiha a amtsayin diyata wacca na haifa" Tom mama nagode sosai da sosai ubangiji Allah yasaka da alkairai,a wanann rana de Samiha batayi wani baccin kirki ba gaba daya hankalinta da tunanin ta yana kan Masoyiyarta Samiha,haka Ahmad gaba daya bacci yakaurace masa ya hau kan sallah yana kuka yana rokon ubangiji akan Allah yakawowa Samiha mafita,shi kansa yayi mamakin irin kalar kukan da yayi domin bai san lokacin da yakeyin saba. A bangaran Samiha kuwa wayar da yaya Dr ya siya mata ita ta Kunna ita ce ke dan debe mata kewar wasu abubuwan,da magrib yayi ta tashi ta dora girki ta kirashi awaya akan zai zo yace mata eh zai zo nan ta dora musu abincin tare. Kwnaci tashi Samiha ta shafe watannni a wanann gida amman har yau momy bata san tana nan ba,yadda kasan a rufe wa mutane baki akan sanar da ita,sai de babu abinda mutane basu saniba tunda Samiha sukan fitowa ita da Yaya Dr suje siyayya ko kuma idan zai kaita gyaran kai,duk mutanan yankin babu wanda yake mu'amala da ita dan harta gaisuwar ta babu mai ansa shiyasa itama ta hakura tadena gaida kowa. Watarana sai abubuwa suka fara sauyawa duk da yaya Dr yana abin da yaga dama da ita amman yana yin komi ne cikin shauki da soyayyya,tom amman yanzu ta sauya zani kullum cikin cin mutuncin ta yake yadena nuna mata kauna kwata kwata,kuma kullum cikin zuwa yayi abin da yaga dama da ita yakeyi. Samiha ta shiga wani sabon tashin hankali wanda yakusa sakata zaucewa nikam na shiga uku mai ke shirin sake faruwane "Innalillahi wa inna ilahiee raji'un".Haka taci gaba da kasancewa cikin wanann halin cikin Wanann yanayin bata fadiwa kowa ba sai ranar da Basma ta zo ta gani da idonta. CIGABAN LABARI Basma ta ci gaba da kasancewa da Samiha takuma yi alkawarin babu wani abu da zai rabata da ita saboda tana son Samiha tsakani da Allah baza ta taba iya kaurace mata ba Koda ace Samiha ita ta sakawa kanta abin da take aikatawa baxata gujetaba,ballantana kaddarace wacca babu wanda yafi karfin ta. Ranar mama na zaune ita da Basma tace mata "Yaushe zakije wajan Samiha ga maganunuwa nan na tsawon wata guda na hadosu idan ya so in zakije sai ki tafi mata da su kowanne akwai yadda zatayi amfani da shi ajiki Kuma inshallah inde ta bisu yadda suke a ka'ida duk wani abu da nihal tayi zai war ware". Tom mama nagode sosai da ubangiji yasaka miki da alkairai,nima Samiha diyata ce ya zama dole na kula da ita. Basma ta shirya tsaf cikin farinciki da murna taje gidan Samiha tana zuwa ta tarar da yaya Dr yasaka ta gaba sai jibga yakeyi kamar ya sami jaka zama tayi tana kallonsu har yagama dukanta sanann ya wuce ya ficewarsa,bayan yafita ta matso kusa da ita ta share mata hawayanta ki kwnatar da hankalinki besty inshallah komi ya zo karshe ta dakko ledan maganunuwan nan tamika mata su,sanann anan suka bude kowanne da yadda za ayi amfani da su ciki har da wanda zata zubawa Yaya Dr a abinci da wanda zata zuba masa ya tsallaka,tayi tayiwa Basma godiya matuka nan kowannann su yakasance cikin farinciki saboda kawai gani suke tamkar komi ya zo karshe. Amman Samiha wani hanzara ba guduba malam ladan yace a afadimiki duk wadannan maganunuwa baza suyi amfani ba ko baza suyi aiki ba har sai kin sake nutuswa kincigaba da tsaida sallah akaan lokaci sannan kici gaba da dawwama wajan karatun alkur'ani wannan shine babban abin da zai sa aikin yayi cikin hanzari da sauki inshallah Basma zanyi nagode sosai. Nan suka ci abinci tunda daman ta dafa abinci tare suka yini suna shira agidan sai da magariba da yaya Dr ya zo ya mayar da ita gida. Tun a adaran ranar ta fara amfani da wannan magani anfadimata Koda taci abincin da ta sakawa maganin babu wani problem anan ta zuba wanann maganin da taje dakko musu abinci sukagama yayi mata sai da safe ya tafi gida. Tsawon sati guda Samiha tayi tana amfani da wanann maganunuwa kullum tana fata da adduar Allah yasa komi ya dedeta,acikin satinne Basma ta zo take fadimata ai nihal sun tashi babanta ya sami sanjin gurin aiki amman taji labarin ba lalle su jima ba zai yi kokari ya sami canji ya dawo murna kamar ta kashesu Kinga wanann na daya daga cikin nasarar da mika samu alhamdulillah alhamdulillah,abubuwa shikkelau sukacigaba da tafiya takuma cigaba da amfani da maganunuwanta yadda yakamata ita kanta ta fara ganin sauyi domin yanzu Yaya Dr yadena hantarar ta da zaginta yadena dukanta haka kuma sai yayi kwana uku bai bukaci yayi wani abin da ita ba,ba karamin murna takeyi ba da hakan domin kuwa tabbas ta sami saukin zuciyata Kuma tanaji ajikinta komi ya kusa dawowa dede da izinin ubangiji. Basma ta Samiha yanzu kusan kullum tare suke yini domin dadyn Basma ya tafi america wani project hakanne yasa maman su ta kara karfafawa Basma baya akan taci gaba da mai da hankali wajan ganin rayuwan Samiha tayi dede. Bayan wata daya da sati biyu da fara amfani da wannan maganunuwan Basma da Samiha na zaune suna shira sai ga Yaya Dr ya shigo gaba daya hankalinsa a tashe a firgice baya cikin hayyacinsa,Samiha tace yaya lafiya mai ke faruwa mai aka maka?. Kasa cewa komi yayi yace mata zo ciki Ina son zanyi magana dake abin yabawa kowanann su mamaki toupa yau Yaya Dr ne ke son privacy su kebe batare da kowa yaji mai zasu tattauna ba babu komi yaya Basma ce babu abin da bata sani ba a arayuwan mu,kayi maganar ka kawai. Wani azababbbe wahalalallan kuka ya saki wanda gaba dayan su suma ya saka su zubar da hawaye ba tare da sun shiryaba duk rahsin tausayinka kaga yadda Yaya Dr ya xage yana wanannan kuka sai ka tausayamasa domin gaba daya ya gigice sai kace wani mahaukaci, kukan kawai yakeyi ya kasa furta komi.... Samiha ce tayi karfin halin cewa yaya dan Allah ka fadimin mai ke faruwa tunkafun hakurina yakare bazan iya jurar ganin damuwarka ba Yaya Dr bazan iya jurara ganin tashin hankalin kaba,bana son duk wani abu da zai zame maka matsala bana son duk wani abu da zai zamemaka damuwa dan Allah ka fadimin abin da yake damunka. Samiha "Nasan na cutar dake na bata miki suna kowa yana miiki kallon mazinaciya mara tarbiyya Samiha Ina zan Kai wanann hakkin Samiha taya zanyiwa ubangiji bayani akan wadan nan abubuwan da nayi miki Samiha dan Allah Kiyi hakuri kiyafemin Samiha kiyi hakuri nasan tabbas kafin ki yafemin za ajima amman dan Allah ko bayan raina kisani nayi da nasanin abin da nayi miki Kuma Ina sonki fiye da yadda nake son Kai na. Kuka wiwi Samiha takeyi idanuwan ta sun kunbura sunyi sintim murna fal cikin xukatansu ita da Basma komi ya dedeta,Samiha tace "Yaya Dr babu wani abu da zakamin aduniyar nan da bazan iya yafe maka ba Ina sonka irin kaunar da take hana sukuni irin kaunar da ake bada rai da rayuwa dominta bazan taba iya rayuwa babu Kai ba,bazan taba iya bari na zama Sanadiyyar salwantar farincikin kaba Yaya Dr kayi hakuri kai ma,Kuma na yafe maka duk abin da kamin Ina Kuma Neman alfarmar da karaksake tuna kayimin wani abu acikin zuciyarka komi ya wuce mufara shinfida sabuwar rayuwa " Matsowa yayi ya rungume ta suka cigaba da azzaba kukansu da kyar Samiha ta samu ta nutsu ta dedeta tunaninta ta rarrashi yaya Dr da kyar yayi shiru ya zama tamkar karamin yaro zuciyar sa gaba daya ta narke,nan de duka suka nutsu Basma ta sake yi musu nasiha matuka,tare sukaci abinci cikin farinciki da walwala,suna zaune suna shira sukaji sallama dukkanin su sai da suka tsorata amman banda Basma saboda daman tasan da faruwar abin. Daga kan da sukayi sukaga momy da dady wani faduwar gabane yasake ratsa Samiha na shiga uku shikkelau bazan taba samin farinciki a rayuwata ba a lokacin da nike tunanin na fita daga wata matsala a alokacin wata matsakan ke sake tun karoni Innalillahi wa inna ilahiee raji'un abinda tayi ta fadi kelan cikin zuciyar ta. Shima kanshi yaya dr yayi matukar tsorata ya shiga sake-sake iri iri akan mai yakawo su gidan sanann Kuma waya fadimusu anan suke,nan momy da dady suka zauna . Momy ce tace " ya naga gaba Dayea Kun firgita kamar kunga wasu aljanu". Samiha zo nan ki zo ki xauna kusa dani nayi matukar kewarki mikewa tayi cikin tsoro da fargaba da takarasa,dady ne yace nasan duk kunyi mamakin ganin mu babu bukatar dogon bayani,Basma taje ta samemu ta Kuma fadamana duk abin da yafaru miyi da na sanin abin da mika aikata miki Samiha duk da Ina da tabbacin yadda kukayi tayin abu

Chapter 10 of 15