Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [11/20, 7:14 AM] oum mumtaz ce🤠: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u 💥💥 *AYMANA.....!*💥 _ROMANTIC STORY_                                          *MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*            Wattpad@UMMIE2018. *FREE BOOK.* _LITTAFIN KYAUTA._ *DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️                 *PAGE 1*         Misalin k'arfe 2 na daren ranar litinin,yarinya ce yar kimanin 7yrs ke zaune cikin wani d'aki dasuka kasance su uku ne acikin wannan dakin,sauran na ta shirga baccinsu. wanda kallo daya za a mata,a tabbatar da cewa a matukar tsorace take a wannan lokacin... k'arar k'ofar dakin da taji neh yadawo da ita daga dogon tunanin da ta fada a matsayinta na mai karancin shekarun da bai kamata ace tasan ta tashi a dai dai wannan lokacin domin tunani ba! bata gama dawowa daga tunaninta ba, taji saukar tsumagiya mai matukar zafi wanda ta tabbatar wannan dorunar *ANTY CE* ce...!! anty dan allah kiyi hakuri wlhy banyi fit'sari, ba kuma banyi bacci ba kamar yadda kika umarce ni. fadar wannan karamar yarinya cikin karamar muryarta ta yara mai cike da t'san t'san t'soron da take ciki... ay kuwa anty bata sarara mata ba,saida tamata  bulala kusan goma acikin wannan daren allah kamin tabar ta... abin mamaki kuma sainaga tayi ma daya datake cikin wayanda suke kwance k'afa..ma'ana dai ta shure ta, wanda hakan yayi sanadiyyar farkawar yarinyar daga dogon bacci daya d'auke ta... saida taymata bulala itama, kamin tafita daga dakin tana huci,ta koma wani part daban wanda nake kyautata zaton nan take kwana koh kuma part nata ne nan...kamin tashiga saida ta saita kanta kamar ba ita ba! tana shiga bedroom din tayi tazali da *BABA*dake zaune bakin italian bed dake bedroom din ..ta shaida masa akan ta tashe su sunyi fitsarin! daganan kuma suka bi lafiyar gadonnasu,suka koma baccinsu. Wannan karamar yarinyar kam kuka takeyi sosai a wannan daren...dak'yar dayar ta lallashe ta wacce bazata wuce shekaru 9 ba,kamin tayi shuru. rungume da junansu suke kwance,wanda da kyar bacci yayi nasarar yin awun gaba dasu……! k'arfe hudu asuba taji an mata wani kalar bugu mai matu ar zafi, wanda hakan yayi sanadiyyar farkawarta cikin gigicewa da rawan jiki... amma kuma wani abun mamaki babu suprise akan fuskarta saidai ma tsantsar tsoro... kasancewar tasan ba kowa bane mai wannan anyen aikin face anty... "sannu inna uwarsu matar ubansu,kedin ba cewa nayi karki kuskura ki kwanta ba ne wai dan ubanki...?" fadar anty cikin zafin rai kamar wacce take fada da sa arta... "anty kiyi ha uri wlhi bansan nayi bacci ba, dan allah kiyi hakuri karki dakeni ..."fadar wannan yarinya mai kimanin 7yrs cikin t'sant'sar tsoron dukan dorunar da ake amfani dashi wajen dukansu...! aikuwa saiji tayi duka na shigarta amma babu damar ihu kasancewar idan tayi ihu kamar ta karawa kanta wani babban laifi neh... saida anty tamata lilis, kamin ta umarce ta data tashi taje ta wanke kayanda rahma kanwarta mai kimanin 3yrs tayi fitsarin kwance... cikin kuka mara sauti wanda yake da matu ar cin rai ta tashi ta zagaya bayan dakunan su ta wanke su tass,wanda ko wani babba ma albarka... sai wajen 5:15am ta kammala, alokacin kuma baba yashigo da sauran yan gida dasuka dawo daga sallar asubahi...! alokacin kuma har zainab mai kimanin 9yrs ta daura masu dumamen tuwon jiya da dare... wajen six na safe mai masu wanke wanke da shara ta iso itama ta kama aikin ta...!! Amina wacce ake ira da mimi ta ha a ruwan zafi tawuce bayi tayi wanka...bayan tafito zainab ta daibi ruwa cikin damn nasu tayi wanka,daganan kuma tamawa kaninsu sameer wanka wanda bai wuce 5yrs domin tafiya makarantar boko kasancewar yau monday,,,,, bayan ta fito aka debowa "NAFEESA" wacce suke kira da "Aymana" ruwan da aka debosa daga randar sanyi, wanda takanas dominta aka zuba ruwa cikin randar tun daren jiya,wanda haka yariga dayabi jikinta...! tana karkarwar sanyi take wanka da wannan ruwa mai tsananin sanyi kasancewar yanayin lokacin sanyin da muke ciki...! tana cikin wanke fuskarta anty tashigo da doruna ta feffenta mata har akayi rashin sa'ah kofar bandaki ya karce mata gefen fuskarta wanda hakan yayi sanadiyyar zubar jinin jikinta kamin tabaro bandakin...! tana kuka mai matukar taba zuciyar mai sauraro tafito daga wankan, wanda kawai anyi wankanne bawai dan an fita ba,sabida sanyin ruwan baya barinta ta natsu tayi wanka mai kyau... zainab,mimi aymana da sameer sun shirya bayan sunci dumamensu,aka zuba masu joloup na taliya domin tafiya makaranta... kuma wai dukkansu acikin flast daya fa, sai a sannan suka shiga dakin baba...dattijo mai cike da kamala da sanyin hali dayake matukar kaunar yayansa dakuma kokari wajen ganin ya sauke hakkokinsu da allah ya rataya masa a wuyansa matsayin mahaifi, cikin murmushi yake ansa gaisuwarsu inda yakebin su daya bayan daya da kallo har idanunsa suka sauka akan aymana dake labe a gefen kujera kamar kace mata as ta fece, take yanayi fuskarsa ya chanza daga farin ciki zuwa akasin haka, sabida ganin gefen fuskarta a karce wanda har sai da wajen ya tashi... "uwata matso kusa da danki kinji...?"fadar baba cike da damuwa a kamilalliyar fuskarsa... mat'sowa take cikin yanayin na ts'ants'ar tsoro, sabida bataso anty ta ganta ajikin baba kasancewar ta gargadeta akan hakan ba sau daya ba... batasan ta iso ba sai jin hannu baba akan fuskarta yana duba inda taji ciwon sannan kuma ya tambayeta a garin yaya taji ciwo? cikin sassanyar muryarta mai cike da sheshsheka kalar ta yaran da basu da hayaniya da rashin son surutu ta shaida masa ai dazu ne data shiga wanka bata sani ba tazo fitowa marfin bandaki ya karce mata fuskar tata... yaji tausayinta sosai wanda har hakan ya nuna bisa fuskarsa, ""mamana zaki iya zuwa makarantar kuwa...?"" cikin gaggawa ta gyada masa kanta kamar wata kadangaruwa har jikinta na rawa...! sabida bazata so a barta da anty acikin wannan gidan ba,idan ba haka ba kuma gawarta za'azo a kwasa yau!! kudi ya ciro naira dari biyu 250 yabasu akan kowa ya dauki naira 50,50 dayan kuma su bama salifa...!! godiya suka masa,inda yamasu fatar dawowa lafiya!! wata kyakkyawar yarinya wacce baxata wuce shekaru shida ba suka tarda kofar gidan, tana aikama da aymana sakon murmushi...itama cikin doki tayi breaking na hannunta dana zainab tayi gaggawar shigewa cikin napep suka rungume junansu cike da dauki,batama lura da wanda ke cikin napep din ba"" sunata murna kamar wayanda sukayi shekara basu hadu ba...nankoh jiya neh ma karshen rabuwar su wajen karfe biyar na yamma... wata zazzakar murya mai matukar sanyi da dadin sauraro dake ratsa k'wak'walwa ne ya katse su daga daga dariyar dasuke yi ta murnar ganin junansu..!! "wato yau ummi bazaki gaishe da hammanki ba koh..." "shikkenan nima yau namaki yajin mgn sai kinyi biko na zaki samu damar zantawa dani..." yarashe maganar da guntun nurmushi akan fuskartasa... ""laaaa kayi hakuri hamman mu,wlhi hankali na neh yakoma kan bestyn tawa""ta basa ansa wanda hakan yasashiyi sassanyar dariyar da ba shirya ba... sannan ya umarce su zainab akan su shiga suwuce kar suyi letti... cikin zumbura baki mimi tace ""haba hamma sadeeq kaduba kagani tun dazu sun cikamu da shirme sai sunsa yau munyi letti amma baka masu mgn ba,saikaima ka biye su"" kallo daya yamata tashiga taitayinta ta suke bakinta... daganan kuma SALIFA ta dale cinyar ummi tana dariya wai yau ta rigata hawa cinya,sbd wajen bazai isa su zauna baki dayansu kan seat ba!!! zainab kuma sameer nakan cinyarta, sai mimi dake gefe tanata cika tana batsewa kamar ta fashe dan takaici...! harzai tada napep ya hango fitowar dan uwansa shima cikin uniform kamar nasa... "dan uwa sai yanzu ka fito koh? ai nikam da tafiyata ma zanyi na barka a gidan" "am sorry twin bro wlhy akasi aka samu shiysa kaga ban fito da wuri ba""fadar daya matashin daya fito,kallonsu na tsaya yi jin y ambaci twin bro!! amma saidai kuma basuyi kama ba koh kadan,dalewa yayi napep din,zama yayi a gefen mai zaman banza daganan sukayi gaba cikin annashuwa... INUWA DAHIRU MEMORIAL shine sunan makarantar dasuke baki dayansu...!! saida yayi parking suka fito inda kowa zai wuce class nasa!!! tsaki kawai mimi tabuga tabar wajen, domin koh a ganinta tawuce ajin ganta dasu a ce yan gidan ne koh kuma wani alaka a tsakaninta dasu!! da harara salifa ta rakata sabida bata da hakuri dukda kuwa kankantar ta... "hamma sadeeq da hamma musty zankai sameer class daganan kuma na wuce class namu""aymana da auta kuma sai anjima zamu hadu"... fadar zainab cikin murmushinta, "toh shiikkenan zee zee ayi karatu lpia allah y bada sa ah"..."ameen hamma musty" kallon sadeeq tayi tace ""hamma sadeeq kai bazaka mana addu ar bane wai?" murmushi kurum yamata yace"" toh zainabu abu alllah y bada sa ah ayi karatu sosai"...ai kuwa suka soma mata dariya wai ance mata abu ...bata biyesuba ganin ynda lkc yy kawai tawuce takai sameer nursery 2 itakuma primary 3 kasancewar class nasu daya da mimi amma kowa da seat nasa... salifa kam tariqe hannun hammansu sadeeq akan lallai yau shi zai kai su class nasu...ummi kam na gefe murmushi kawai takema salifa ganin yadda take son yayan nata...! aykuwa har class nasu yakaisu wato primary1, kamin suka wuce ss block shida musty ... basuyi 5mins dazama ba sai ga haidar wato yayan su ummi yashigo class din ......! *OUM MUMTAZ✍🏿* [11/20, 7:14 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u 💥💥 *AYMANA.....!*💥 _ROMANTIC STORY_                                          *MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*            Wattpad@UMMIE2018. *FREE BOOK.* _LITTAFIN KYAUTA._ *DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️                 *PAGE 2* 10:10am aka tashe su break domin cin abinci dakuma refreshing na kwakwalwarsu kamar yadda akeyi a sauran makarantu dadai sauransu...! aymana da salifa na hango suna tunkarar ss block,salifa na kuka harda majina,ummi kuwa tayi kalar tausayi kamar tayi kuka haka takeji... direct class nasu hamma sadeeq suka wuce, inda suka tardasa tare da abokinsa azaune... sai zuba abokin kemasa amma shikam yazuba masa ido kamar wani basarake...amma kuma rashin yin maganarsa da dukkan alamu bai dami abokin nasa ba,,,ga dukkan alamu dai bayan yasoma ganin hakan ba... jin kukan kanwarsa a gefensa ne yajawo hankalinsa zuwa garesu dawani kalar bacin rai kwance bisa kyakkyawar fuskarsa, aykuwa sai ta kara sautin kukanta domin yau so take a rama masu muguntar da aka masu ita da aymana...! cikin sanyin muryarsa da baxaka gane yanayin dayake ciki ba idan har baka karance halinsa ba... "autar ammi wayaci zalinku kuma yau...?" "hamma ba adda mimi bace..."takare maganar tana kara k'wak'wulo sabbin hawaye! "mai ta maku...?"shine tambayar daya kara wurgo mata a takaice! "wai kawai danni da fiyen ita munje nace tabani abinci, saboda tun a class tace man tanajin yunwa shine wai bazata bamu ba,kuma yanju haka ma sun cinye ita da qawayenta koh adda zainab bataci ba ballantana kuma boy ma yanju kukan yunwa yakeyi a kofar class nasu..."" takarashe maganar tana sharbar majina tsakaninta da allah... ai kuwa take abokin nasa ya barke da dariya sosai, sabida yawan maganar yarinyar,domin koh wannan surutunnata harda fada ba a tambaye ta ba, shikansa sadeeq da da hali zayyi dariyar amma kuma kamar ya kara ballo ma kansa ruwa neh ...sannan kuma dariya ba dabi arsa bace saidai murmushi kuma shidin ma saita kama...sannan kuma bazakaji shi yana yawan magana ba idandai ba da ummi da salifa yake tare ba sai kuma amminsa...! "yanzu ina zainab da sameer din?"itace tambayar daya kara wurgo masu "adda tana class nasu, shima boy yana class nasu"fadar aymana cikin yanayinta na sanyi! "okay yanzu ke auta jeki kira man zainab,...ke kuma fiyen jeki kira man boy kuzo tare kunji?" tom hamma na! fadar aymana kenan cikin yanayinta,inda tafita! sannan salifa ma mara mata baya"... ajiyar zuciya ya sauke domin har wani zafi zafi yakeji a makogoronsa sabida sunsa shi dogon magana bai shirya ba... "kai amma pha sadeeq kanaji da kannenkannan sosai ba kadan ba naga alama,amma tsabar iskanci  ji yanda nake ta zuba kamar akku amma kazuba man ido kamar tsohon maye..."" tsaki yayi ciki ciki kawai yadauke kansa daga kan saleem...saboda shikam saleem badai surutu ba, gashi kuma sam bai son yawan magana kwata kwata...shigowarsu class neh yasa saleem dakatawa daga zubar dayakeyi! "hamma gani wai inji auta kana kirana ?"fadar zainab kallonta kwai yayi cikin second 5 yafahimci kwantacciyar yunwar dake nukurkusarta, mikewa kawai yayi batare da yabata ansa ba ya umarce su dasu zauna yana zuwa... abinci yaje yasayo masu fried rice da drinks mai sanyi ya ajiye nasa dana dan uwansa sannan yabasu nasu...saiida suka koshi sukayi nak! suka sha coke nasu mai sanyi har abincin yarage sai zainab ta dauka ta tafi dashi saboda yace idan sukaci abinci yarage suna tafiya dashi gida saisu cinye idan ba a basu abinci ba... ""Aymana kutafi class,auta kuma banda surutu a class kunji koh"" tom hamma mungode fadar nafeesa daganan suka wuce class nasu. sai 1:20pm aka tashe su,suka hau napep kamar yanda sukazo ...mimi kam a tsorace take domin koh tasan halin hamma sadeeq sarai idan tashi ga hannunsa sai ta yabama aya zakinta sosai ba kadan ba! ta tabbatar wannan mara kunyar ta fada masa abunda tamasu dazu... wai salifa kenan! bayan sunje gida suka cire uniform nasu su hudun, zainab ta wanke masu harda dana mimi sannan tayi sallah tama sameer wanka itama tayi nata tacema aymana tazo ta mata, amma sai taki wai ita kunya takeji kar a kalle mata jikinta... nikam nace mai zamu gani iya aymana?? duk saida sukayi wanka suka kule daki su ukunsu suka cinye sauran abinsu da hamma ya sai masu sannan sukasa uniform nasu na islamiyya ...karfe 2 suke zuwa a tashi karfe 5 na yamma! sallamar anty cikin gidanne yasasu shiga taitayinsu hatta da sameer saboda tsanar da anty ke gwada masu, muraran ma kuwa, more especially aymana,yan unguwa suna mamakin tsanar datake nuna mata wanda bata iya boyewa a gaban kowa sai gaban baba! gaysheta sukayi ta ansa tana wani yatsina fuska kamar da kashi take mgn ba da dan adam ba! abinci tazuba kamar wani na mabarata wanda ba ubansu ke kawo abincin ba tabasu,amma koh ajikinsu sbd a koshe suke sannan bayau suka soma ganin hakan ba kaman ba ubansu bane yakawo abincin... tas suka cinye abinsu sukayi nak babu saura space nawani abincin a cikinsu tunda dama sun rage hanya  itakam mimi tana dakin anty koh wanka batayi ba,ballantana shirin islamiyya! suna fita suka shiga makotansu wato gidansu salifa,itama ta shirya cikin uniform kalan nasun suka gaishe ammi daganan kuma suka wuce islamiyya wajen 5 da wani abu baba suka rabu da babansu salifa bayan sun dawo kowa da motarsa kasancewar gurin aykinsu daya...bayan yaci abinci yayi wanka ya tasa keyar duka yayansa maza suka wuce masallaci, basu suka dawo gida ba saida akayi sallar isha'i aka rufe gidan kana sukaci abincin dare baki dayansu,wanda babane yasaka dokar cin abincin dare tare da ahalin nasa baki dayansu,saida suka gama tattara komai kana suka zauna hira, wanda hakan dabi'ar baba yake wai idan da mai matsala kowa yafada masa a dai dai wannan lokacin,tunda bashi da lokacin zama tare da su da rana! amma kuma dukkan su tsoron fada masa abinda anty ke masu sukeyi sbd gudun cin zalinsu da takeyi a bayan idonsa,amma a gabansa kam suna ganin gata na kin karawa... wajen 9 suka dakko takardunsu inda ya tayasu sukayi assignment nasu na boko! sannan kuma akazo fannin islamiyya kowa yana kawo haddansa zuwa inda suka tsaya aykuwa mimi yau da bataje ba ta gagara yi sbd dama kan dai gashinanne sai uban baki.....""mimi wasa kika tsayayi har yar uwarki takawo nata amma ke kin tsaya wasa kin gagara kawo naki koh?""fadar baba cikin kakkausar murya... ""wlhi baba yaune banje ba kuma sbd ciki na yana ciwo neh ka tambayi zainab ma kaji kuma" hmmm kawai baba  yace,bai kuma bi takanta ba... anty kam ko uffan bata ce ba,sbd kar yace ita ke daure ma mimi gindi,shiysa take kin zuwa islamiyya,haida da nasir ma basu ce komai ba... sallamarsu yayi kan suje kwanta kuma kowa yayi addu'a,duk suka wuce makwancinsu... *ASALINSU* jihar yobe a karamar hukumar damagum akwai wani kauyen fulani da ake kira da jajere...garin yakunshi zallar fulani a cikinta,wanda dazaka bincike su sosai toh kuwa baki dayansu za'a iya kiransu da family daya sabida kansu hade yake baki daya,kuma dama dangin juna ne !! malllam ardo na daya daga cikin mazaunan wannan kauye inda yake rayuwa tare da iyalansa kwai da kwarkwatarsu baki daya... matansa biyu ne kacal furere itace uwar gida,suna kiranta da inno yayanta biyu ne...yusuf ardo da salifa ardo……sai kuma amaryarsa mai suna harira,suna kiranta goggo, yayanta uku abdallah ardo,hindatu ardo dakuma ramata ardo wacce takasance autar gidansu,duk suna zaune lfy cikin kaunar junansu sbd ardo tsayayyen namiji neh akan iyalansa babu nuna banbanci koh kadan tsakaninsu ballantana suce zasuyi masa banzan kishi tunda duk daya yake daukarsu! (wanda wasu mazan sune suke kara dulmiyar da rayuwar iyalansu wai wannan matar so wannan kuma itace/shi aka fi so kaf cikin yayansa bazayyi kokari wajen ganin ya boye ba gudun aukuwar kiyayya tsakaninsu ba...wanda hakan babban kuskure ne kwarai da gaske). auren ardo da inno har akayi shekaru uku bata haihu ba,hakanne yasashi kara aure inda ya auro goggo duk itama na daya daga cikin danginsa ne,aykuwa ciki ya bayyana jikinsu baki daya goggo da inno, wanda haka yasa ardo matukar farin ciki sosai ba kadan ba... bayan wata tara inno ce ta fara sauka inda ta haifo danta namiji bayan kwana uku goggo ma ta haifo danta namiji inda yaran ranar suna suka ci ragon yusuf da abdallah...! haka suka taso cikin kaunar junansu sosai saida suka shekara goma kamin goggo takara haihuwa inda tasamu yarinyarta taci suna hindatu, hindatu nada shekara biyu inno ma ta haifo yarta mace wacce taci suna salifa! alokacin yusuf da abdallah suka kammala primary school nasu sbd ardo na burin yayansa maza suyi karatun boko, makarantar kwana yanema masu acikin garin bauchi wanda wasu daga cikinsu suka jahilci ilmin boko a wannan lokacin kasancewar sun taso cikin duhun kai basusan amfaninshi ba,dan haka sukadaine kaf kauyen ke karatun boko... suna da 18yrs suka kammala secondary school inda suka dawo suka dawo gida daganan kuma yafara masu ciku cikun wucewa jami ar atbu zasu karanci physics kasancewar abu daya suka karanta...! cikin sa'a suka samu admission, inda suka wuce jami'a,kuma su  suna zaman hostel ne! rayuwa na tafiya cike da abubuwa na farin ciki da akasin haka,nasara da rashin nasara, alokacinda sukeda shekaru a shirin kuma suna level2 zasu shiga level3 kenan sukayiwa gida tsinke inda suka tarda abun farin ciki, haihuwar da goggo tayi,ta haifu ya mace inda akayi suna yarinya  taci suna rahma suna kiranta da ramata... bayan anyi suna da wajen wata suka fara shirin komawa makaranta domin shiga sabon aji, ardo ne ya kirasu su biyu yakara masu nasiha kan surike junansu da gaskiya amana basu da tamkar junansu karsu bari kuma wasu susan matsalolinsu...! wanda suke zuwa siyan dabbobi ne sukazo, inda yasaida garke guda wanda ba kananun dukiya bace,...shikuma yakirasu yabasu ajiyan kudi akan su tafi da kudin baki daya su ajiye masa a banki,idan amfanin kudi yataci masu kuma zasu iya amfani da kudin... idan amfanin kudin yatashi zai neme su! sun koma makaranta har suka cinye semester na farko,kasancewar continuos semester ne sai kawai suka zauna kawai batare da sunje gida ba har saida suka kammala scnd semester level3 sukayi wa garinsu tsinke inda suka tarar da mummunan tashin hankali a garinnasu... gawarwakin da suka faracin karo dashi ne yayi mugun daga masu hankali dama kuma karamin garine a wannan lokacin gidaje basufi a kirga ba , kisan gilla aka masu a cikin garin, wato manoma kasancewar a kwai bakar gaba tsakanin manoma da makiyaya ta wannan yankin wanda suka ritsasu a wannan daren suka kai,masu farmaki saida suka tabbatar da babu wanda suka bari darai kamin suka gudu! cikin gidansu suka shiga direct dakin ardo inda sukayi tozali da abunda ya matukar girgiza masu zukatansu baki daya wanda hakan yy sanadiyyar zubewar yusuf war war a sume! kukanda abdallah ke jiyowa kadan kadan daga dakin  kanin ardonsu na tashi yasashi hanzarin mikewa a zauce domin ganin waye cikin dakin daya rage masu?... shigansa bai ga kowa ba amma kuma yanajin sautin kuka cikin dakin zuciyarshi na bugawa ya yaye zanin gadon inda yayi tozali da jaleela...yar gidan kanin ardo ce jawota yy inda idanunsa suka sauka akan yarinya yar kimanin 3yrs sai wurga idanuwa takeyi... bai tsaya wata wata ba ta sungume yarinyar yakamo hannun jaleela suka wuce dakin ardo... itama tozali da gawarwakin dake dakin ardo yasa jaleela fasa kuka domin koh gasunan birjik ardo,inno,goggo,salifa,hindatu,ramata babanta da mamarta dakuma wasu daga cikin yan uwansu rabi da kwata duk dakin ardo suka hadu domin jimami dasukaji wai manoma sun kawo masu farmaki a garin,sai akayi rashin sa a kasancewar abu yazo da karan kwana suka masu kisan gilla baki dayansu a cikin dakin yan sanda sai a lakacin suka iso da motar asibiti aka zo da manyan malamai dakuma wasu manya acikin gomnati mai ci na wannan lokacin! gawarwakin baki daya aka tattaro su, wasu kuma suka hako makwancin mamaci wato kabari...saida aka masu wanka baki daya aka sasu makwacinsu har zuwa lokacin yusuf bai farfado ba aka sasu a ambulance aka wuce dasu garin damaturu asibiti aka wuce aka fara basa treatment jaleela,hauwa  da abdallah ana kula dasu a gidan gwamnatin dakeci a wancan lokacin sai bayan sati biyu sannan ya farfado ya warke saidai dukkansu kana masu kallo daya zaka masu ka fahimci har zuwa lokacin shock din da suke ciki bai gama barinsu jikinsu ba... ana kula dasu sosai babu tsangoma wanda hakan yayi ma jaleela dadi amma banda su abdallah domin alllah allah suke koma makaranta subar yoben ma baki dayanta!         *OUM MUMTAZ✍🏿* [11/20, 7:14 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u 💥💥 *AYMANA.....!*💥 _ROMANTIC STORY_                                          *MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*            Wattpad@UMMIE2018. *FREE

Chapter 1 of 14