Share this page
rahma ne zaune suna kallon tashar mbc bollywood da ake haska wasan kwaikwayo na dhamal sai sheka dariyarsu suke sbd yadda film din ke sasu nishadi! saida baba yayi ma abba masauki tare da sadeeq,inda musty ma ya samu damar zama akan lallausar carpet din dake dakin! baba ya kalli su sameer da suka shiga taitayinsu yace ma sameer"kaje ka kiramin zainab da nafeesa!" da hanzarinsu kuwa ya fice daga parlon,inda ya tadda aymana kwance kan katifarsu ita da zainab dake faman bacci sbd babu wanda yasan abinda ke faruwa a cikin gidan! aymana kuwa cikin wayannan kwanakin sosai tayi baki sbd damuwar data daura ma kanta! dik tabi ta rame gwanin ban tausayi! haka nan takejin wani abu na son bijiro mata mai kama da nadama ko kuma ince dana sani akan rayuwar data zabar ma kanta! harma takanyi tunanin cewa anya itace kuwa take aikata muggan halaye kamar haka ba sauya ta akayi ba...? sakon kiran da baba yayi mata saida gabanta ya bada wani sautin ras! amma haka nan ta kokarta ta tashi zainab inda suka shiga parlon da sallama! zuwa lokacin ma kuwa anty da mimi ma sun hallara cikin parlon tare da naseer! shi kuwa haydar dama an dakinsa jama'ar suka turasa sbd mutuncin baba idan aka barsa a waje babu tantama har jifansa yara kan iya yi sbd sun gansa a bige...!ammy da salifa ne suka shigo tare da musty da baba yace a kirasu! idan kuka ga fuskar salifa a lokacin saiku tausaya mata sbd yadda fuskar dik take kumbure sanadiyyar kukan datake ta faman yi tin dazu! saida baba ya sauke nannauyar ajiya zuciya sannan ya dubi abba dashima ke son jin dame yayan nasa yzo ne!? "dafarko dai ina nai neman alfarmarka dan uwa na bisa ga watsa maka kasa a ido danayi a wayewar garin yau dinnan! tabbas nima nasan nayi rashin kyautatawa sbd ko babu komai kamar yadda haydar da nayi niyyar basa auren ita nafeesa ayau din yake dana!! haka nan sadeeq ma ke a matsayin dana! dan haka ina mai sake baka hakuri game da hakan da fatan bazaka kullace ni ba...?" baba ya kare maganar yana mai kallon abba da wani irin tashin hankali ya bayyana a kan fuskarsa sbd jin wasu batutuwan da baba ya sako cikin kalamansa! wanda bama abba kadai ba!!! baki daya mutanen dake cikin palon kallon baba sukeyi da wani irin mamaki dakuma son sake gaskata abinda yake fada mai kama da almara! cikin karfin hali abba yace "babu komai dan uwa ni ban rike ka a zuciya ba dama! amma kuma saida ina son ka sani zuciya ta debeni a yau dinnan da misalin shabiyu na rana na daura auren sadeeq da salifa sbd hana shi auren nafeesa da kayi na tabbata da cewa ba karamin damuwa zan shiga ba saikuma naji akasin tunani ka daura auren sadeeq da aymana dana tabbatar da cewa asali na shi din kayi niyyar bama ba! sannan kuma naji kana sakin wani batu tsakanin haydar da aymana da muke son sanin karin bayani game da hakan!" abba ya karasa maganar tasa yana kallon dan uwan nasa dashima ya kure abba da ido sbd jin cewa wai ya daurama salifa da sadeeq aure...? kowa dake cikin parlon saida ya shiga tsananin rudu kwarai da gaske! inda saida baba ya tsawatar masu kamin suka shiga taitayinsu! sadeeq,aymana tare da salifa ne kawai kansu ke kasa ko tari sun gagarayi sbd damuwar dake dankare cikin zuciyarsu! "ayau dinnan zan bayyana maku sirrin dake boye da muka rufe sa nida marigayiya hauwa'u matata tare da maman mu wato marigayiya inna nafee da babu wani mahaluki daya sani a duniya sai ubangiji!!" take kuwa ko wannensu ya kasa kunnuwansa domin son jin abinda baba zai zayyane masu a yau dinnan hatta su aymana da sadeeq yanzu kam hankalinsu ya karkata ne kan baba inda yafara magana kamar haka' _WAIWAYE_ *OUM MUMTAZ✍🏿* [11/20, 10:02 AM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥 _ROMANTIC STORY_                                *MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*       Wattpad@UMMIE2018. instagram@itz me real oum mumtaz G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com facebook@oum mumtaz *FREE BOOK.* _LITTAFIN KYAUTA._ *DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️             *PAGE 28* ********** _WAIWAYE_ Bayan dawowar su abba cikin garin azare daga bauch sbd sako su gaba da makiya sukayi ne hauwa ta sake samun cikinta na biyu bayan zainab kenan! (idan baku manta ba nace maku tin tsakar dare takejin ciwon baya amma saita daure wai karta tadawa dasu baba hankali...?shima kuma bai lura da yanayin da take ciki ba ko kadan! wajen karfe hudu baba ya fito domin zuwa masallaci da yar tocilarsa kamar kyaftwar ido sai kuma ya koma kaman wanda yayi mantuwa a hanzarce... _kuje page 3_) a lokacin da baba ya fito din tuntube yayi da wani abu kamar katifa wanda hakan yasa shi dallewa da torch light dake hannunsa! waro ido waje baba yayi cike da tsantsar al'ajabi hade da mamakin abinda ya gani! kwali ne a bude da wata jaririya sabuwar haihuwa dakana gani zaka gane ko wanke ta ba'ayi ba a lokacin da aka haifo ta balle kuma yanke cibiya! sosai zuciyar baba ke bugawa cike da tsantsar tausayi da kuma al'ajabin rashin imani irin na mutanenmu! kuma koda wasa baiji aransa cewa wannan jinjirar dayake gani aljana bace! sai kawai ya jujjuya yaga cikin unguwar tasu! saida ya tabbatar da ceqa babu wanda yake kallonsa sannan ya dakko yarinyar kamar ana hankada sa ya shige gidansa inda ya wuce dakin hauwa! dai dai sawo kansa cikin dakin faya ta fashe ma hauwa ashe fitarsa keda wuya nakuda ta tasar mata inda kuma cikin hukunci na ubangiji babu wanda ya juyo ta sbd baccin da yau sukayi a gidan kamar hadin baki! ciro yarinyar yayi daga cikin kwali ya ajiyeta a inda jaririyar da hauwa ta haifa wato cikin jininta wanda hakan yasa su zamowa kamar wasu yan biyo! dikda zuciyar baba bugawa takeyi amma haka nan ya cika da tsantsar farin ciki hadi da tsaftatacciyar kaunar wannan yarinya fiye da kima yakanji cewa kamar yarsa ta cikinsa ce! shine ya taimaka ma hauwa wajen kimtsawa bayan ta yanke ma yara cibiya sannan ya shiga dakin inna nafee da itama ta idar da sallar asuba nata ya shaida mata komai batare daya boye mata komai ba hadi da naiman alfarmar kar kowa yaji wannan zancen sbd sirrinsu ne! sosai inna nafee ta shiga tausayin jinjirar a lokacin datayi arba da ita! ruwan zafi to jona masu na catle a cikin wani babban baho sbd zaifi yin sauri wurin tafasa sannan ta hura wutan murhu ta hada ma hauwa kunun hatsi mai kyau domin ta sha,wanda zuwa lokacin ruwan ya tafasa,dan haka ya juye ma hauwa ta hada mata dik yanda ya kamata ita kuma ta hada ruwa ta tsaftace yaran dikkansu biyu sannan ne kuma su hajiya hauwa aka fito inda taji wani bakin ciki na ganin hauwa ta haifi yan biyu ita bata haifa ba wanda hakan yasa taji wani munnunar tsanar yaran ya kamata kamar ta soke su nankuwa ta allah ba tata ba! wuraren karfe goma na safe gida ya cika da jama'a yan barka kuma a lokacin ne allah ya dauki rayuwar jinirar hauwa ma'ana dai ta koma! sosai hauwa tayi kuka amma kuma saita gode ma allah da yayi mata chanji da wata batare da dabararta ba! wanda hakan ya sa ta rungumi jinjirarta ranar suna akayima inna nafee takwara wato NAFEESATU! sadeeq ne ya zaba mata sunan lakabin da za'ana kiranta dashi wato AYMANA!! tin ranar suna baba ya kudirta aransa cewa da dansa HAYDAR zai daura mata aure sbd baison rayuwar yarinyar ta tagaiyara zuwa gaba idan taji ainahin ita din YAR TSINTUWA CE...! saidai kuma ance wai matar mutum kabarinsa! domin kuwa a lokacin dayake kokarin daura auren aymana da haydar ne ya ga haydar ya fito cikin yanayi na maye! wanda hakan ya sa shi sarewa da wannan hadin dayake da niyyar yi sbd yasan ba karamin kuskure zai aikata ba idan har ya hade haydar da aymana matsayin miji da mata! dalili kuwa shine idan yau akace aymana na shaye shaye...? sannan kuma haydar na shaye shaye...?? shine wace iriyar zama zasuyi? sannan kuma a cikinsu wanene zai na nuna ma dan uwansa cewa rayuwar dasuka zabar ma kansu bamai inganci bane! wanda kuma zasu tsyaa tsayin daka wajen ganin sun tarbiyantar da yayansu da zasu iya haifa zuwa gaba? ganin su sadeeq da baba yayi a lokacin da suke tunkaro wurinne yasa shi maida akalar daurin auren izwa gareshi sbd yasan ko zuwa nan gaba idan sadeeq yaji ainahin tarihin aymana bazai taba gudarta sbd yabawa da hankalinsa da baba yayi! kuma yasan tabbas sadeeq mai iya maida ta kan hanya madaidaiciya ne! _back to story🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️yanxu dai ina fatan an fahimce ni reader's🤤🤤_ Wani irin shiru ne ya ratsa wurin kamar wanda mutuwa ce ta riske su sbd bama kwakwalwarsu hutu na wucin gadi akan labarin da baba ya gama basu a wannan lokaci! babu abinda zaku iya hangowa a wurin daya wuce tsananin shock akan fuskokinsu! sadeeq da aymana sosai suka kure fuskar baba da wani irin kallo da kai tsaye zaka iya kiransa da matikar rudu a kuma fuska daya matukar girmama wa da kauna mafi tsanani akan wannan bawan allah! kowa jikinsa ba karamin sanyi yayi a wannan wajen hatta ga anty da mimi sbd ganin yadda duniya kan zoma mutane da dama ba'a yadda ka dauka ba! wallahi da ace a bakin wani sukaji wannan bayani bazasu taba yadda kan cewa aymana bar yar baba bace ta cikinsa amma kuma a bakinsa sukaji dasuka tabbatar cewa bazai taba fadin hakan domin dadin bakinsa ko wani abu ba! lallai duniya cike take da mutane iri iri mabanbantan halaye masu kyau dakuma akasin haka! (yanxu tabbas a duniyar nan tamu mutane gani suke mutanen kwarai sun kare tin a zamanin shekaru da dama na baya dasuka gabata sai mutanen banza! wanda kuma sam abin ba haka yake ba! da ace mutane zasu yi duba da kyau na musamman tabbas zasu san cewa mutanen kwarai sunfi na banza yawa a duniyarmu! abinda yasa bazamu iya fuskantar hakan kai tsaye ba shine bamu taba yada alkhairin da zamuji wani yayi bama kamar zamanin yanxu a social media kamar yadda idan yau akace mutum yayi wani abu na banza nan da nan zakuga ya zaga duniya cikin 24 hours!! wanda hakan kuma sosai yake bada gudummmawa wajen zubarmana da mutunci ana ganin cewa acikinmu babu na kwarai saidai na banza🤔🤔hmmm) hawaye ne suka fara sulalowa daga cikin idanun aymana a wannan lokacin sbd jin tayi dikta muzanta a cikin yan uwan nata! ashe dai ita din ba yar baba bace? basu ma hada dangi dashiba amma gashi a sanadiyyar ta har ya dannawa matarsa uwan yayan har saki biyu??! "Nafeesatun ina fata wannan takaitaccen bayani dana bayar game da asalinki bazai sa kimani kallo na daban ba? ina fatan a matsayin mahaifi nake a gareki har yanxu? sannan kuma yan uwanki ma bazaki masu kallon wasu na daban ba zaki ci gaba da rikesu a matsayin yan uwanki??" baba ne yake tambayar aymana! ita kuwa bata samu zarafin magana bama sai kada masa kai dakeyi sbd kukan dayake kokarin cin karfinta! ba'a bama kowa zarafin sake magana ba abba ya bukaci kan kowa ya watse gobe idan allah ya kaimu za'a sake sabon zama sbd warware masu wata kullalliyar kuma game da auren sadeeq da salifa ! badan kowannensu ya so ba,saidan babu yarda zasuyi suka watse ammy ta kamo hannun salifa da aymana dake ta faman ambaliyar hawaye zuwa gida sbd su samu isasshiyar kulawa a wajenta domin gujema su kamuwa da wata ciwon! sadeeq kuwa sosai ya shiga cikin zullumi na wannan al'amari haka! wanda shima tsornsa daya kar azo ace shidin ma ba dansu amny bane wanda ya tabbata idan hankalinsa na jikinsa tabbas sai ya zauce! mimi kwanan kukan nadamaa sukayi daga ita har mahaifiyar tata!data ji ashe dan nata data kwallafa rai a kansa shaye shaye shima yakeyi!? tabbas allah ba azzalumin bawansa bane wanda sai a yanxu ne take dana sani hankalinta yafara dawowa jikinta akan dik kurarkuran data aikata a baya wanda ta tabbatar allah bazai taba barinta ba muddin bata naimi gafarar su ba! haka nan salifa keta faman sauke ajiyar zuciya hadi da tsananin fargabar kar dai ace itace ba yarsu ammy ba🥱 anyi kwanan zullumi dai in takaice maku cikin wannan gida kwarai da gaske🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️ washe gari🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️ allah idan banga ruwan sharhi ba bazan maku post ba anjima da dare sai bayan kwana uku😡😡🙄🙄🙄🙄🙄 *OUM MUMTAZ✍🏿* [11/20, 11:29 AM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥 _ROMANTIC STORY_                                *MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*       Wattpad@UMMIE2018. instagram@itz me real oum mumtaz G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com facebook@oum mumtaz *FREE BOOK.* _LITTAFIN KYAUTA._ *DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️             *PAGE 29* ********** _WASHE GARI_ gaba dayansu zaune suke a cikin palo na baba kamar jiya inda dik suka natsu kamar ruwa yaci su! idan ka kalli idanunsu baki dayansu to kuwa tabbas za'a fuskanci rashin samun wadataccen baccin da sukayi a daren jiya! anty da su mimi yaukam harda hijabansu suke sanye sbd nadamar tsani da allah da sukayi ayau din! bawai na bogi bane! kuma anty taci alwashin tona ma kanta asiri ayau dinnan koma wani irin hukunci baba ya yanke mata zata anshe sa hannu bibbiyu tinda ita tajama kanta ba wani ba! sadeeq kuwa na kusa da ammy shida salifa zuciyoyinsu na faman bugawa sbd ko wannensu gani yake kamar shine ba dan gidan ba,su yanxu bawai ta auren dake tsakaninsu suke ba sai son sanin asalinsu! haydar ma yau ya halarci wurin taron nasu sai faman lullumshe idanu yake alamun yau din shima ya kora dikda ya fuskanci iyayen nasa sunsan da cewa yana shaye shaye sai yakanji a cikin zuciyarsa ko a kwalar rigarsa wanda nikam nace alhaki kenan! musty dasu zainab data kwana tana kuka itama sbd auren da aka daura tsakanin aymana da sadeeq domin kuwa ba karamin kaunarsa takeyi ba,amma saidai kuma yanxu kam itama ta kudirtama ranta cewa ta hakura dashi sadeeq din har gaban abada sbd ta dauki aymana ne a matsayin kanwarta! wanda bataji zata yadda su hada miji koda wasa sbd tasan yin hakan tamkar wargaza masu alaka ne tinda ita zuciya bata da kashi akan abinda takeso! mimi kuwa batajin zata iya daina son sadeeq a rayuwarta sbd yadda ta rayu da kaunarsa tinda ta bude ido tagansa! wanda sai daren jiya ne ta fuskanci dalilin dayasa ta tsani aymana da salifa tin suna kanana! ashe dai su dinne zasuyi mata katanga da abinda ta taso tana maradi tin tana kankanuwarta! rahma da sameer sukam dama bawai sun gama tantance abubuwan dake faruwa bane sbd tunaninsu dakuma kwakwalwarsu batakai ta fahimci komai daki daki ba! kwana naseer yayi shima jiya yana mai tausayama kansa! domin kuwa allah ne kadai yasan kalar kaunar dayake ma salifa tun tana karamarta amma gashi farat daya batare da wani jinkiri ba da ransa da lafiyarsa an aura ma waninsa kuma ba kowa ba sai sadeeq...? no wonder! ashe dai dalilin daya sa yake jin masifaffen kishin sadeeq din tun suna kananu basu kai haka ba! aymana ma tagumi ta buga tana bin kowa dake cikin palon da kallo! daga ranar da huzaifa yakawo ta gida cikin yanayi na maye zuwa yau dinnan ba karamin ramewa hadi da dishashewa tayi ba! zuwa wannan lokacin kuwa cikin hukunci na ubangiji ta gama dawowa cikin hayyacinta daga asirin shaye shaye dakuma bin maza da aka lika mata! sosai takejin zuciyarta kamar zata faso kirjinta ta fito waje sbd damuwar data daura ma kanta! tunaninta shine su wanene iyayenta da tsabagen kiyayyar da sukayi mata suka jefar da ita ranar dasuka kawo ta duniya...? anya kuwa ita din ba shegiya bace😢 wannan sune tambayoyin dasuka dankare mata cikin zuciyarta! saida abba ya sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan ya kalli ammy dake rungume da sadeeq tana shafa masa lallausar sumar dake kansa alamun lallashi sbd kalar damuwar dayake ciki daga jiya zuwa yau itama sosai ta shiga fiye ma da hakan! saida ta share dan kwallar data gangaro mata daga cikin idanunta sannan ta sunkuyar da kanta domin kuwa kallon da abba yayi mata ta fuskanci ma'anar hakan,cike da yanayi na damuwa da rashin son bayyana sirrin dake boye ammy ta fara magana kamar haka: _WAIWAYE😢😢_ *OUM MUMTAZ✍🏿* [11/21, 12:23 PM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥 _ROMANTIC STORY_                                *MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*       Wattpad@UMMIE2018. instagram@itz me real oum mumtaz G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com facebook@oum mumtaz *FREE BOOK.* _LITTAFIN KYAUTA._ *DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️             *PAGE 30* ********** _WAIWAYE_ _HAR YANXU DAI A WANNAN PAGE DIN WATO PAGE 3 KU TUNO DIK WASU MOMENTA NA RANAR DA AMMY ZATA HAIFI SU MUSTY_ shekaru ashirin da shida (26) da suka gabata wanda lokacinne yayi daidai da haihuwar sadeeq dakuma mustapha! a wata rana,wato ranar dana tashi da nakudar haihuwarsu acan cikin garin bauchi,nasha wahala sosai amma kuma shuru haihuwa kamar an shuka dusa,wanda hakan yasa aka wuce dani asibiti cikin labour room! a daidai lokacin da aka kawo ni ma akoi wasu matan da suma aka kawo su dakin haihuwa! wanda zan iya cewa ma kusan lokaci daya muka sauka tare da daya daga cikin matan dake cikin dakin da kallo daya idan mutum yayi mata zai fuskanci cewa badaga gidan kananun mutane ta fito ba kodaga yanayin tufafin dake sanye a jikinta! ni na haifi twins ne a lokacin duka maza! ita kuma saita haifi guda daya amma itama da namiji ta haifa! sosai matar ke kallon yaran nawa dake kwance idanunta na zubar da hawayen da bansan na minene ba! gani nayi tana juye juye! wanda hakan yasani kallon cikin labour room din da gaba daya nurses din dake cikin dakin hankalinsu yakoma ne kan wata mata dake labour abin tausayi dai! dama a lokacin ba'a sanar ma kowa da muke tare dasu kan cewa mun haihu ba! matsowa tayi zuwa inda nake inda a lokacin ta ankarar dani ashe cewa daya daga cikin yaran dana haifa yakoma ga mahalliccinsa! sosai hankali na ya tashi sbd soyayyar dake tsakanin da da uwa ba karamin abu bane! "baiwar allah rayuwar wannan jariririn nawa yana cikin hadari! wanda hakan yasa nake so dan allah kiyi ceton rai kamin a ankare damu! sbd kallo daya dana maki nasan kedin mai amanace kuma na aminta dake! wanda hakan ne yasa nake rokonki kan dan allah ga yaro na muyi musanye da yaronki dinnan daya koma nikuma saina baki nawa!" kallon matar nayi da kyau sbd yadda take kuka tana roko na abin ya munana! take naji zuciyata ta karye tausayinta ya kamani! kamar wacce ake controlling dina banyi jayayya ba saima daukan yaron nawa dake mace nayi masa addu'oi a gaggauce na mika matashi da yarjejeniyar karta wulakanta man gawar dana haka nima namata alkawarin insha allah zan kular mata da yaronta har zuwa lokacin dazai cika shekaru 30 din kamar yadda ta bukata saina fada masa a inda take! "kisa masa suna ABUBUKAR SADEEQ"harta budi baki zata sake fadaman kan ita wacece sai muka ga wata nurse ta doso inda muke da sassarfa wanda hakan yasamu shan jinin jikinmu baki daya muna kallonta! ajiyar zuciya muka sauke sbd ganin ta karbi yaron dake hannun wannan matar fuskarta da murmushi tace "bari nakaima mahaifiyarki dake waje gaba daya ta ishe mutane da surutu inajinta ta window wai ita akawo mata jikanta!" kuka matar ta fashe dashi sosai tace" yaron nawa yakoma sister" sosai jimami ya bayyana akan fuskarta inda takamo hannunta suka fice daga wurin matar nata faman waiwayowa tana kallon danta dake ta faman callara kuka gwanin tausayi! daukan yaron nata wato abubakar sadeeq nayi na rungumesa ina jin tausayinsa hadi da kaunarsa na ratsani a wannnan lokaci! bayan wani lokaci aka sallame ni muka dawo gida! a lokacin dana fada ma abba sosai yayimin kan abinda na aikata ba tare da naiman shawararsa ba! inda daga baya kuma sai shima kawai ya hakura muka rufe sirrin tsakaninmu mu kadai batare da kowa ya sani ba! abin mamaki kuma munyi munyi da shi sadeeq ya karbi nono kamar yadda dayan kansha amma fir yaki bude bakinsa ballanta na ya ansa! idan ma muka matsa masa sai ya sha saiya fashe mana da kuka sosai! wanda hakan yasa muka yanke shawarar shayar dashi da nonon akuya kuma alhmdlh sosai yake shan abinsa idan mun basa! ranar suna data zagayo muka radamasu suna da MUSTAPHA DA ABUBAKAR SADEEQ!! "wannan shine takaitaccen bayani game da sirrin dake boye tsawon shekaru batare da mun bayyana sa ba sbd ina ganin kamar da sauran lokaci!" ammy ta karashe maganar tana mai sake fashewa da kuka sosai sbd gani take kamar a yanxu ne komai yake faruwa! sadeeq kuwa dake jikin ammy wani irin rawa sosai jikinsa ya dauka kamar mai ciwon farfadiya! rungumesa sosai ammy tayi tanajin wani kukan na sake bijiro mata cike da tsantsar tausayinsa na halin da zai shiga! kowa dake cikin parlon na jinjina hukunci irin na ubangiji! lallai duniya ba'a bakin komai take ba! aymana kam take ta naimi tata damuwar ta rasa sbd ganin yanayin da sadeeq ke ciki a yanxunnan amma kuma bazata iyayi masa komai ba sbd kunyaryin hakan datakeji cikin iyayenta! salifa kam a lokacin da ammy ta ida karasa zancen nata saida ta sauke nannauyar ajiyar zuciya mai karfin gaske tana kallon sadeeq dake rungume jikin ammy! kowa dake wurin saida ya tausaya masu kwarai! haydar da musty ne suka taimaka ma sadeeq ya kwanta akan doguwar kujera ta 3seater dake cikin palon kansa na kan cinyar ammy kamar ya shige cikinta! an dauki tsawon lokaci babu wanda yace kala har saida hankulansu ya gama dawowa jikinsu sannan abba yace "zaku iya tafiya amma kuma wallahi koda wasa karmuji kar mugani cewa labarinnan ya fice wani wuri ina fatan kun fahimta??" dik gyada kai sukayi da fadin "insha allah" har zasu mike kuma sai anty ta durkushe a wurin ta kamo kfar baba dake zaune kan 2.seater tare da abba tana sakin kuka na nadama akan abinda ta aikata mashi shida aymana! a lokacin data gama tona ma kanta asiri kan sihirin datayi ma baba da aymana kowa dake cikin parlo din sosai ya ke kallonta da mamaki irin mugun halinta akan wani banzan kishi mara amfani! sosai ran baba ya sake baci yana da niyyar idashe mata sakinta amma abba yaki basa damar hakan! domin kuwa idan mutum ya nuna nadamarsa akan abu bai kamata a nuna masa wani halin na daban ba saidai a sake jawo sa jiki sbs gudun karya koma ruwa! in takaice maku dai wannam family guda biyu din ranar nan saida suka tabbatar da cewa anyi settling na komai kamin aka watse zuciyoyin kowa wasai kamar babu abinda yafaru! an yafi juna anyi komai,baba ya maida anty dakinta,mimi ta naimi gafarar yan uwanta,ga nan komai dai alhmdlh! BAYAN SATI DAYA! a cikin wannan sati dayan ba karamij fahimtar juna bace ta wanzu tsakankanin wayannan gidaje biyun! idan kukaga yadda mimi da yan uwanta suka koma gwanin ban sha'awa babu wannan tashin tashi nan ko kadan! bangaren auren dake tsakanin aymana da sadeeq,salifa da sadeeq kuwa an jingine sa a gefe ne zan iya cewa! sbd tin daga wannaan ranar babu wanda ya sake yin zancen! sai ma makota irin masu son jin kwakwaf dinnan akance masu na aymana da sadeeq ne! ba'a fada masu na salifa sbd gulma irin tamu🤤 naseer ma an rungumi kaddara yanxu akan soyayyarsa da salifa tinda ya lura tayi masa nisa ba kadan ba! haka nan musty shima dama tuni ya hakura da aymana tin farko balle kuma da a halin yanxu take a matsayin matar aure! sannan su abba da baba sosai suka sa akema haydar addu'uoi game da wannan dabi'ar tasa sbd lura da sukayi kaikayi ne ya koma kan mashekiya bawai haka nan ba! kuma alhmdlh suna samun progress sai godiyar mai kowa mai komai! ga wata iriyar tsaftatacciyar kulawa da anty kan bama su zainab,sameer tare da aymana da suka rasa a baya! kamar yadda take kulawa da nata yayan na cikinta! hakan kuwa sosai yayima baba dadi harma yafara sakkowa daga kan dokin zuciyar daya hau da anty abinka ga mata da miji dama akace sai allah! bangaren hamma sadeeq kuwa kallo daya idan mutum yayi masa a halin yanxu za'a fuskanci matsanancin damuwar dayake

Chapter 10 of 14