soyayyar mahaifiyarsa yaa gaza samun yadda ya kamata dik a ta sanadiyyarsu!
haka nan mamarsa wato malika b da taji tijarar daya afka saida tayi masa tatas kamin ya shafa ma mutane lafiya bakuma dan yana jin cewa ya hakura kenan ba saida yadda yabarma zuciyarsa abinda zai iya kulla masu daga yanxu zuwa har illa masha allah!!
kowa ce amarya an mikata nata shashin a cikin wannan masarautar! inda kuma alhmdlh suna zaune cikin koshi lafiya ne da matayen nasu sosai!!
hatta ga su yunusa da kowannensu daga shi har zulaihat din na ciki,na ciki ne kawaii!
kusan lokacin daya kuwa dikkansu uku suka samu ciki zulaihat,rumana dakuma khadeeja!
wanda hakan yasa aka fara zuba ido tsakankaninsu domin son ganin wacce zata haifa masu MAGAJIN SARKI...!
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/20, 7:18 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u
💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 14*
********Wayewar garin wata ranar laraba kwatsam saiga zulaihatu ta tashi da tsananin ciwon nakuda! wanda hakan yasa mutane da dama saurarawa domin jin mai zata haifa...? shine mace zata haifa ko kuwa da namiji...?
waziri yunusa a wannan ranar sosai yake ta faman addu'a allah yasa matarsa ta haifi namiji wanda zai zamto sarki! haka nan nannawaji ma keta faman tsubbace tsubbacenta data sabayi batare da sanin kowa ba,sai dan kawai yarinyar tata ta haifi magajin sarki!
sosai zulaihat keta faman shan azaba,wanda hakan yasa aka kaita asibiti bisa ga jagorancin wasu daga cikin masarautar tasu sbd ungozama suma sunyi iya kokarinsu abin yaci tura!
acan asibitin ma saida akayi masu gargadi kan karsu sake barin matansu na yin dogon nakuda a gida sbd gujewa faruwar matsala da akan sameshi a yayin da mace tazo haihuwa!
wasu sun gamsu!wasu kuwa basu gamsu ba,sbd bawai ilmin boko yagama ratsa su bane a wannan lokacin!!!
cikin hukuncin allah ko mintina talatin basuyi ba da zuwa asibitin zulaihatu ta sauka tare da taimakon likitoci!
yarinya MACE aka haifa ma yunusa!!! wanda hakan ya kusa zautar da kwakwalwarsa a lokacin dayaji labari!
a wannan ranar aka juyo da zulaihatu da itama keta faman risgar kuka sbd taso ace itama ta samu sa namiji a farko amma gashi burinta bazai cika ba tanaji tana gani!
ranar suna na zagayowa aka rada ma yarinya suna MARYAMA wato mahaifiyar abdulwahap kenan bisa ga umarnin da malika b tabama yunusa badon ransa yaso ba!
anyi shagugulan biki kuwa daidai gwargwado! gimbiya maryama nada sati biyu a duniya ciwon nakuda ya taso ma rumana! matar sarki abdulwahap kenan! nan kam basuyi garajen barinta tayi doguwar nakuda a gida ba aka wuce da ita asibitin dake garin bauchin inda aka kai zulaihatu kenan!! labour room aka wuce da ita cikin gaggaww!
wanda itama cikin ikon allah bata ci wani bakar wuya ba ta haifo da yaronta namiji!!! amma saidai kash😔 yaron bai yi cikakken mintuna goma ba yace ga garinku!
sosai hankulan mutane ya tashi kuwa cikin wannan masarautar!!! abinku ga masu aiki da abinda basu da tabbaci akai,wasunsu keta faman tafka shirma kan ai wani dan bakin ciki ne ya kashe yaron ta hanyar ture🤣
malika rumana kuwa kanta na kasa tinda aka sallamo su banda kukan rashin yaron nata babu abinda takeyi! sbd itafa sarautar bawai ya dameta bane sam!! ita ta yaronta takeyi amma gashi wanda ya fita sonsa ya kwace abinsa !
sosai kuwa waziri yunusa da zulaihatu sukayi farin ciki da hakan amma basu bari kowa ya fahimta ba sbd kar ace su suka kashe yaron dama!!
a washe garin haihuwar tata allah yayima sarki mai murabus wato mahaifinsu abdul rasuwa!!! sosai aka shiga alhinin mutuwar tasa kasancewarsa mutum,mai matikar riko da gaskiya da amana dakuma jin kan talakawansa!
allah sarki malika b idan kuka ganta a lokacin saikun tausaya mata sbd rashin mijin nata a doron kasa!!! haka nan shima aka sallaci gawarsa aka binne sa cikin makabartar masarautar tasu kamar yadda ake binne dik wanu wansa yake cikin masatautar idan ta allah ta kasance!
anyi sadakar uku na rasuwar yaron rumana yau,washe gari akayi sadakar uku na marigayu dalhat! inda nakuda ta kuma tasoma khadeejatu!!! kamin ma ayi wani yunkurin kaita asibiti cikin hukuncin ubangiji ta sauka!!! inda masarauta ta karade da farin ciki na samun yara maza kuma ta gwaye!!
wanda wannan haihuwar ta yaye ma mutane da dama damuwar dake cikin zukatansu na babbab rashi dasukayi!!
a wannan ranar karamin hauka ne kawai baba waziri bayyi ba!! inda nannawaji ke sake pumping nasa daga gefe sbd tsananin son zuciya kalar nata! shikuma son mulki dakuma kishi na neman kaisa ya barosa batare daya an kare ba!!
malika b kam sosai take kula da masu jego! tare da taimakon malika fatima wato mahaidiyar muhammad surukar khadeeja!!! ita kuwa malikah rukayya (mmn su rumana) sai take kula da zulaihatu sbd ganin yadda su malika b ke nuna rashin damuwarsu akanta kamar yayanta!! wanda hakan kuwa sosai ya sake ta'assasa zuciyar yunusa akan su na ganin yadda mahaifiyarsa sam bata nuna damuwarta ga dik abinda ya shafesa,tafi bada hankalinta sosai akansu wanda kuma shi sam baisan mai ya tsare mata ba! ita kuwa malika b sam bata ganin wani aibu don tana kulawa da matan su abdul din batare data kula da matar yaron nata ba!!
ranar suna na zagayowa aka rada masu suna DALHAT(HASSAN) da kuma ALIYU (HUSSAINI) (baban muhammad)!!
anyi shagali amma ba sosai ba sbd rasuwar da akayi basu bada jimawa ba!!! inda yara en gata ke samun tsaftatacciyar kulawa daga kowa da kowa ! wanda kuma MAMMA (rumana) ta maida shashin yar uwar taata kaman nata! ko nan da can ba'a yadda fita dasu batare da kyakkyawan tsaro ba,wanda hakan kuwa ya bakanta ran yunusa sbd yaso ace ya dauke yaran idan yaso sai yaga ta ubanda za'ayi amma haka nan ya zubama sarautar allah ido yana neman ta hanyar daxai raba wayannan yaran da gidan sarauta allah bai basa sa'a ba!
gimbiya maryam,yarima hassan da usaini nada 2yrs a duniya UMMY(khadeeja) da HAJJO zulaihat suka sake haihuwaa cikin sati daya!! inda wannan karan ma hajjo ta haifi ya mace,ummy kuma da namiji! kasa rike takaicinsa yunusa yayi a fili saida mutane da dama suka fuskanci hakan kuwa!! amma babu wanda ya isa ya tanka sbd rigima irin tasa!
yarinya tasa taci sunan nannawaji watoh JUWAIRIYYA anace mata GIMBIYA ANEESAH!! shi kuma yaron ummy sunan babansu ummyn aka rada masa wato ABUBAKAR SADDIQ!! YERIMA SADDIQ...!
a kuma lokacinne sarki abdulwahap ya karo aure!!! sbd hakan ma na daya daga cikin dokokinsu babu zama da mace daya a tsarin mulki!!
wata yarinyar SHAMAKI mai suna SADAM aka aura masa sunanta JAMEELA...!! suna zaune da rumana kadaran kadahan babu zagi babu tsangwama kasancewarsu ba masu son hayaniya ba dikkansu!!
a lokacin dasu gimbiya maryama suka cika shekaru takwas cif na haihuwa su gimbiya anisah tare da yarima saddiq kuma shida shida kenan mamma,ummy,hajjo dakuma FULANI (jameela) suka haihu a cikin wata daya!!!
wanda sai a wannan lokacin cikin hukunci allah zulaihatu ta haifi da namiji dasuke ta mafarkin samu daga ita har mijin nata! DALHAT (yerima) sunan daya ci kenan!
fulani kuwa yammatanta guda biyu ta haifa mai sunan mamanta wato (HINDU) (gimbiya hassan) saikuma BILKISU (gimbiya) mai sunar malika b kenan!
ummy kuwa still yaro namiji ta sake haifa sai yayima kanin nasu takwara wato YUNUSA...! dikdan kawai yana daukansu a matsayin yan uwansa bawai abokan gabansa ba!
mamma kuma FATIMA mai sunan mmn galadima kenan da itama allah yayi mata cikawa shekara daya data gabata.
auren yar gidan limaminsu aka sake dafko ma sarki abdul cikin wannan shekarar batare da neman shawararsa ba!! inda aka kawo amarya iyama mai suna RUKAYYA (UMMAH)!
nanma dai kowa gashi nan ne suna zaune na ciki na ciki sbd yadda ko wacce ta iya takunta cikin matan gudun gulmammaki na gidan sarauta da baka rabasu!!rumana ta sake samun ciki tare da umma dakuma ummy...!
yarinyar mamma sunantaMARYAMA...! umma kuma AYNA'U sai yarinyar ummy kuma babu ita...! anyi shagali daidai gwargwado cikin wannan gidan kam daidai gwargwado! inda jameela,rukayya da hajjo suka sake haihuwa cikin shekara daya hajjo mace ta haifa HUDAH,umma kuma SULEIMAN fulani kuwa SADAM...!
wanda zuwa wannan lokacin yaran sarki abdulwahap guda bakwai kenan!!! baba galadima kuma (kamar yadda suke kiransa) yaransa hudu! baba waziri shima yaransa hudu kenan cif cif...! wanda tin daga kansu sadam haihuwar ta tsaya masu kenan baki dayansu!
inda lokutan rayuwa na gangarawa cikin hukunci na ubangiji wanda kuma cikin wannan shekarun dasuka gabata wasu daga cikin al'ummar wannan gida mai cike da tarihi allah yayi masu cikawa!!
wanda a cikin kakanninsu malika b ce kawai ta rage dik sauran ta allah ta kasance masu da aka taso tare! sai kuma nannawaji dataga babu sarki sai allah babu alamun nasara akan dik abinda tasa a gaba saita watsar da kashinsu baki daya,tinda wanda takeyi dominsa ma shi ya,jima da barin duniyar baki dayanta!!
wanda yanxu suke dan zaman mutunci da malika b da tsufa ya kamata sosai!!! kuma har zuwa wannan lokacin tana kulawa dasu sarki abdul tana daurasu akan hanya idan taga suna gargada kan lamuransu!!!!
shikuwa baba waziri,daya ga dai shidin bashi da rabo ne cikin wannan sarautar tasu sai kawai shima ya saduda tare da matarsa hajjo suka rungumi yayansu suna fatan allah yasa hakan shine ya fiye masu alkhairii!!!
suna kuma cike da nadamar abinda suka taba aikatawa da suka san cewa tabbas dik wanda yaji wannan abu sai anyi tir da halinsu na son zuciya irin tasu!
inda ayau na fado cikin wannan masarautar bayan wasu shekaru na tadda ana shirye shiryen tafiya can asalin babban fada domin yau za'a daura auren yaran nasu har guda shida...! wannan shine takaitaccen labarin wannan masarautar...!
pls wattpad bakwa min vote pa😖😖😖😖
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/20, 7:18 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u
💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 15*
********Bayan sallahr juma'a dake cikin masarautar bauchi dibban jama'a suka shaida aurin auren DALHAT MUHAMMAD SARAKI tare da matansa har guda biyu reras wato JUWAIRIYYA YUNUSA DALHAT da HINDU ABDULWAHAP DALHAT...!
saikuma aka gangaro kan na ALIYU MUHAMMAD SARAKI da BILKISU ABDULWAHAP DALHAT...!
daga su kuma sai aka daura auren GIMBIYA MARYAM YUNUSA DALHAT da ABDULLAHI JALALUDDEN( an gidan sarkin kano)!
aurin auren daya samu halartar manya sarakuna dakuma gomnoni daga yankuna daban daban cikin fa in kasar mu ta nigeria!
daga wurin aurin aure aka yada zango a fadar mai martaba inda akayi walima aka cicci abinci wanda a wannan ranar sarakuna da dama suka koma inda suka fito bayan sun shiga amare dakuma angwaye da abubuwan alheri!
an masu nasiha sosai a wannan ranar aka wuce da gimbiya maryama masarautar kano gidan mjin nata tare da rakiyar wasu daga cikin en gidan nasu dakuma bayinta!
wanda a cikin wannan daren aka mika gimbiya hassana dakuma gimbiya aneesah shashin mijin nasu tare da rakiyar bayinsi dakuma dangin nasu!
inda aka mike gimbiya hussaina ma sashin nata mai gidan wato yarima!
_bari mu koma bangaren aymana nasan su goggo an osa🙃...!_
kuka sosai aymana keyi daga wurin datake dur ushe kuma tarasa dalilin sani ainahin abinda yasata kukan!
shi kuwa jarababben gani reaction in da aymana ta nuna a wannan lokacin yasa ko mutuwa zayyi to kuwa tabbas bazata bashi ha in kai ba yasa shi mikewa daga kwancen da yake ya fa a toilet! wanka yayi ha i da aftace jikinsa kamin ya fito yana wani shashshan amshi sbd ganin samu da rashin da yayi na abinda ya jima yana umaye ! kuma shi a tasa a idar baya tilasta mace a wannan fannin saida amincewarki!
saida yagama kimtsa jikinsa kamin ya wurgoma aymana harara cike da takaicinta yace "malama idan baki shirya barin hotel in bane saiki gayamin ta kama gabana kinji ko...?"
batare data bama maganar tasa mahimmanci ba ta mi e ha i da maida suturarta jikinta cike da sanyin jiki ta kallesa alamun ta gama!
baice mata ala ba ya fice daga room in ta take masa baya! tana sharar walla...! har ofar gidansu yaje yayi droping nata wanda cikin motar ma babu wanda ya tanka an uwansa!!
bin bayan motar tasa tayi da kallo tana jin zuciyarta sam babu da i na ganin kamar huzaifan yayi fushi da ita...! wannan karan kam bataga ko urar naseer ba a ofar gidan nasu da alamun yayi wani wurinne...!
ko gidan ammy bata shiga ba ta fa a gidan nasu batare da tayi ko sallama ba,bata tarda kowa a cikin gidan nasu ba da alamun basa nan ko sunyi bacci!
akinsu ta fa a ha i da cire kayanta ta auro towel inda daya tsaya mata daidai cinya,ta tari ruwa cikin tap ta fa a bandaki! wankan tsarki tayi kamin ta fito zuwa baki tap in tayi alwala ta fa a akin nasu! sbd ganin lokacin sallah na neman shigewa!
saida ta idar da sallarta kamin ya saka wata rigarta transparent innan batare da damuwar komai ba zum ula hijap har asa ta akko wayarta ta fa a gidan ammy bakinta auke da gajeriyar sallama!
bata tarda kowa ba akan barrandar,dan haka ya ku a kanta cikin parlon gidan! salifa ta tarda kwance kan kujera ta 3seater sai shar an uban baccinta takeyi hankali kwance!
ammy ce ta fito sbd sallamar dataji a lokacin datake salla! ganin aymana ne yasata sakin fuska ta sami wuri ta zauna tana mai kallon fuskar aymanar!
a gefenta aymana ta samu wuri ta zauna cikin sanyin murya tace "ina yini ammy...?" "lafiya alau ar albarka!! yau ina kika shiga tin safe ar uwar taki keta faman naimanki umm...?" ammy ta tambayeta tana kallon fuskarta kamar mai son gano wani abu...!
asa tayi dakanta taja bakinta ta tsuke alamun bata son zancen! sau e ajiyar zuciya amny cikin rashin jin da i tace "tashi ar uwar taki ta gabatar da sallar azahar idan yaso sai kuci abinci"
tana gama fa ar hakan ta mi e ha i da shigewa bedroom nata tana tausayama rayuwar yarinya arama kamar aymana ke neman gur ata ma kanta duniyar tata!
Bayan salifa tayi salla tare suka shi abincinsu suna hirarsu jefi jefi har suka kammala...! zainab da sameer ne sukayi sallama alamun dawowarsu kenan daga makaranta! sallah sukayi kamin suka ci abinci daga nan suka wuce gidan nasu bayan sun gaisa da ammy...!
_MACQUARIE UNIVERSITY DAKE ASAR AUSTRALLIA_
wani pack ne dake yankin makarantar mai suna _macquarie center ice skating_ waje ne da zaka samu yawancin aliban cikin wannan jami'a a lokuta da dama suna wasannin su gwanin birgewa...!
kowa ka gani a wannan wurin zaka tarda fuskarsa cike da walwala da alamun rayuwar wurin na mati ar yi masu da i warai...!
_IDAN NAGA CANJI KUMA ZAKU GA CANJI DA YADDAR ALLAH_
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/20, 7:18 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u
💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 16*
********Tin daga wannan lokacin kuwa haka rayuwa taci gaba da garama aymana da dadi babu hadi!! inda suma suka shiga mataki na ss1 a makarantar boko tare da salifa a tsakankanin wannan lokacin!!
naseer ma tuni ya koma makaranta abinsa yama mance da batin wani abinda su aymana sukayi ma mimi!
inda kuma suma suka samu samu salama na rashin arzikin da mimi take tsula masu sosai sbd yanzu kam ita kanta shakkar masu rashin kunya takeyi sbd tasha jiki kamin ta warware sumul tafara zuwa makaranta!!
anty kuwa dik shige da fice da zatayi saida tayisa! domin kuwa yanxu baba sam yaki jinin aymana kwata kwata!! baya shiga shirginta ko kadan!! kullum cikin zaginta da aibata ta yakeyi! wanda hakan kuwa sosai yayi ma anty da mimi dadi! itama aymana sosai abin ke bakanta mata rai amma haka nan babu yadda ta iya takan shanyewa!! wanda har takai takawo ma kudin makaranta da komai nata abba da ammy ne kanyi mata!
bakuma wai da baba bashi dashi ba!! saida uban tuggu da makirci irin na anty na tsantsar tsanar datake ma aymana mara dalili!!!
wanda zuwa wannan lokacin munanan dabi'un aymana sai wanda yayi gaba! wanda har takai ta kawo yanxu shaye shayen datakeyi yayi tsamari kwarai da gaske! wanda cikin unguwarsu yara kan mata ihun yar maye!
sosai hankulan ammy da abba ya tashi dasu salifa harma dasu zainab!amma abin mamaki ko a kwalar rigar baba sbd shedanci irin na anty data gama shanyesa!
haka nan ma wai wani zubin ammy kan kulle aymana a daki idan taga marece ta doso sbd sanin da tayi cewa muddin tabar aymana kara zube a matsayinta na uwa allah bazai barta ba!
karatun da aymana kanyi ma dai gashi ga kamarsa ne!!! abin sam babu kyan gani!! ana cikin wannan yanayi zainab da mimi suka shiga ss3! salifa da aymana kuwa ss2 sameer kuwa jss2...!
naseer ma yanxu an zama matashi sbd yanxu ya kammata degree nasa har anyi posting nasa acan area na kudu domin yin nysc nasa...!
anty kam liyafa taci gaba!!! bakin hassada mara kan gado yasa kwata kwata idanuwanta dakuma kunnuwanta sun rufe wajen rashin tsoron allah!
bayan shekara daya!
zainab da mimi sunyi graduation!! inda suka fito da kyakkyawar sakamako tin shekarar daya gabata! wannan shekarar da muke cikinta kuwa su aymana ne suka zana paper na ssce sbd jumping da dasukayi! wanda da yanxu ne suke ss3 din!!!
wanda kuma har zuwa wannan lokacin babu abinda ta canza zani cikin rayuwar gidaje guda biyu saima abinda yayi gaba!!!
kuma cikin sati mai zuwa ake saka ran dawowar su hamma sadeeq sbd kammaluwar karatunsu da sukayi na tsawon shekaru takwas curr!!
sosai su,ammy ke shirye shiryen tarbarsu !! haka nan anty ma keta fama shirye shiryen tarbar yaron nata da takejin har cikin zuciyarta tafi kaunarsa kaf cikin yaran nata!!!
baba da abba ma shirye shiryen tarbarsu suke ta famanyi gida ya kacame da farin ciki!! dikda aikin sihiri dake tattare da rayuwar aymana amma haka nan ta tsinci kanta da yin sanya wajen aikata munanan abubuwan data san muddin su hamma sadeeq sukaji to kuwa tabbas kashinta ya bushe!
wanda hakan sosai yayima ammy da su salifa dadi harma allah allah suke su sadeeq din su dawo ko allah zaisa sanadiyyar hakan ta dawo cikin hayyacinta ta fuskanci alkibla...!
Rana bata karya saida uwar diya taji kunya...!!inji mallam bahaushe...!
wayewar garin wannan ranar da misalin karfe takwas na safe jirgin farko ya sauka a babban filin jirgin kasa na cikin garin abuja daga kasar australia...!
iyayen yara ne kinkam dakuma yan uwansu zaka gani suna ta malangarin kowa fuskarsa washe da tsananin farin ciki suna ta faman kai kawo domin tarbar yaran nasu dasuka shafe tsawon shekaru basa tare dasu!!
daga cikinsu kuwa harda su abba,baba,naseer,sameer dakuma abokinsu baba dake nan garin abuja! sunzo tarban yaran nasu fuska washe da farin ciki...!
a lokacin da dalibai suka suka fara fitowa daga cikin jirgi kowa sai faman mimmika wuya yakeyi domin gano nasa dan uwan! wanda cikin wayanda suke saukowa daga matakalar jirgin na hango wani tsayayyen matashi wankan tarwada data tsuke cikin wani rigar suit dakuma wandonsa bakake...! fuskarsa dake da kyawu na asalin fulani na sagaye da wani kyakkyawan sajensa irin na yan gayu manne da bakin glashin da akafi sani da no respect!
hannunsa janye yake da wani akwati irin na matafiya daidai ajiye su laptop da irin tarkacen takaddu dinnan!
sai faman baza uban kamshi yakeyi inda idanunsa suka sauka akan iyayen nasa dasuka zubo masa idanuwa daga inda suke fuskarsu shimfide da tsantsar farin ciki!
sameer da naseer ne suka fara hangosa daya sa sameer kwala ihun kiran sunan YA HAIDAR cike da wani irin farin ciki dakuma kewa!
sake akwatin nasa yayi shima cike da farin ciki ya rungumo yan uwan nasa da yayi matukar kewarsu bana wasa ba!
_IDAN NAGA CANJI KUMA ZAKU GA CANJI DA YADDAR ALLAH_
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/20, 7:18 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u
💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
instagram@ itz me real oum mumtaz
G:MAIL@ fatimafateh5@gmail.com
facebook@oum mumtaz
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 17*
******** Sosai suka nuna farin cikin gani ya haidar dasukayi fiye da tunanin mai karatu! inda daya daga cikin yaran abokinsu baba ya wuce dashi gidansu ya huta kamin su musty su iso!
bangaren su baba kuwa bayan kamar minti talatin jirginsu hamma sadeeq ya sauka!
wanda hakan yasa sosai suka sake rudewa da farin cikin ganinsa,harma suka rasa ta inda zasu tsoma sa suji dadi! shima kuwa sosai yayi farin cikin dawowarsa cikin ahalinsa sai wani narke masu yakeyi!
baba ne ya bukaci da shima ya tafi yaje ya huta kamin jirgin su musty ya iso amma sam yace shi baisan zancen ba! sai ya jira twin broo nashi yaso su koma baki dayansu!
hakan kuwa akayi,sai bayan kamar awanni biyu kamin jirginsu ya sauka! a takaice dai a wannan wurin sosai suka cika da farin cikin ganin junansu bayan tsawon lokutan dasuka shafe batare da junansu ba!
musty da sadeeq suna manne da junansu yau su hamma sadeeq an ajiye miskilanci a gefe!
burinsa a yanxu shine kawai ya gansa a gaban ammynsu yasan itama tana can tana sake tsumayin dawowarsu!
da suka isa gidan ma haydar suka sha hirarsu su abba nacewa sunyi girma dayawa yanzu kamar basu ba! sunayin sallar azahar suka kama hanyar garin bauchi,inda driver na alh ne yakaisu sai godiya suke ta faman suburbuda masu!
da goshin magriba suka iso cikin garin azare inda motarsu ta faka a kofar gida! tin kamin motar ta gama samun damar kammala parking musty ya diro daga cikin motar da hanzarinsa ya fada gidansu kamar wani karamin yaro yana kwada ma ammy kira daya sata fitowa daga parlonsu tare da salifa dakuma adda zainab fuskarsu cike da tsantsar farin ciki!
fadawa yayi jikin ammynsa cike da farin ciki mara misaltuwa,itama ta sake rungume dan nata cike da tsananin kewarsa na tsawon shekaru tana jin wata iriyar nutsuwar zuciya na saukar mata!
salifa da adda zee kuwa kofar gida suka nufa inda sukaci karo da hamma sadeeq da dannowarsa cikin gidan kenan cike da tsananin kasala data rufesa lokaci daya!
gaba daya sun kanainayesa kamar wayanda zasu kayar dashi sbd farin ciki! dikda a gajiye yake haka nan ya sake fuska ya biye ma kannen nasa sbd shima sosai yayi kewarsu! sai baza ido yake a kaikace yaga ta inda aymana zata billo amma baiga gilmawarta ba! hakan yasa dole yaja bakinsa ya tsuke sbd son girma irin nasa wai kar a raina sa amma kuwa tabbas ya matsu daya sanya ta cikin idanunsa!
muryar ammy daya jiyo ne yasa shi banbaresu,daga jikinsa cike da tsananin kaunarta ya bata kyakkyawar runguma yana sauke nannauyar ajiyar zuciya batare daya ce uffan ba!
itama sosai ya taro yaron nata ta jasa zuwa cikin gidan da ta baza masu babbar tabarma musty na zaune salifa na gefensa kamar zata shige cikinsa dadi uwa ya kashesu!
zainab kuwa tuni ta afka gidansu inda ta tarda haydar dasu anty,mimi,naseer,rahma dakuma sameer sai raha sukeyi sbd ganin junansu!
abba,baba dakuma driver suka wuce masallaci inda zasu shiga gida idan sun fito a salla!
aymana kam...!
_DAWOWAR NAN TA MUSAMMANCE! IDAN NAGA RUWAN SHARHI TABBAS BAZAN BAKU KUNYA BA INSHA ALLAH🤠🤠 dan haka kuyi manage da wannan💃_
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/20, 7:19 AM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
instagram@ itz me real oum mumtaz
G:MAIL@ fatimafateh5@gmail.com
facebook@oum mumtaz
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 19*
*******Saida suka gama shan murnarsu kamar babu gobe kamin suka sarara ma junansu! cike da doki aymana tace "ina hamma sadeeq yana cikin gida ne??"
juyo da kansa yayi da niyyar bata ansa amma saidai babu sadeeq a inda yayi tsammani babu dalilinsa! "ki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 14