nasu da sukayi a gidan baki dayansu ko wacce mijinta yayi mata iznin zuwa ashe! ga kuma girki kala kala masu uban rai da lafiya da suka hada masu!
haka nan suka yanyame su aka cika da farin ciki sosai ba kadan ba! su ammy kam ansha labarin bauchi a wajensu ba kadan ba,inda zuciyar ammy ta cika da farin ciki sbd ganin yadda yar tata ta koma kamar ba ita ba!
lalle kam sadeeq ya cika cikakken dan halak mara manta alkhairi! domin kuwa ita tafi kowa sanin halin sadeeq! ta kuma san cewa tabbas biyayyace dakuma son saka masu da kwatankwacin abinda sukayi masa yasa shi kular masu da yar tasu tsakani da allah badan yanayi mata soyayya na aure ba!
BAYAN SATI HUDU!
Yau gidan oga musty na fada,inda na tarda shi tare da matar tasa sai faman shirya ma bakon su yarima sadeeq abinda zasu tarbesa suke sbd yaune ranar da zaizo! sannan kuma ayau dinnan yayi alkawarin har twin broo nasa zai kaima ziyara sbd basu taba haduwa ba,ko a photo bai sansa ba,dikda irn kusancin dake tsakaninsa da musty!
wanda a wannan lokacin kuma naseer dama yazo hutu! sameer da rahma an sasu a mkaranta mai kyau cikin garin ta private.
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/25, 8:42 AM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
instagram@itz me real oum mumtaz
G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com
facebook@oum mumtaz
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 36*
**********Sosai yarima sadeeq ya cika cikinsa tare da wani kyakkyawan yaro yazo dazai kai kimanin shekaru biyu da yan kai! sai wasan sa yakeyi! zainab kuwa ta cika yaron da dangin sweet da choculate sai wasan sa yakeyi!
sun dauki tsawon lokaci suna hirar su da suka jima basu samu zama ba tin graduation na su musty din! inda suka fito baki dayansu harda zainab dake dauke da _PRINCE DIZHWAR_!
gashi kuma ga dikkan alamu wannan yaro sosai jinin sarauta ke yawo a jinin jikinsa sbd rashin son maganar tasa har tayi yawa! shidai barshi da tabe tabe amma badai kaji bakinsa ba!
shirye yake cikin kayan sanyi mai kyan tsari irin na asalin masu hannu da shuni! kamin su fito saida musty ya kira sadeeq kuma ya tabbatar masa da yana gida!
sadeeq ne ya bude masu kofa,inda zainab ta fara shigowa sannan musty sai yarima prince ya shigo kansa a kasa batare daya dago ba!
har saida suka danganta da samun wurin zama kana ya dago kansa inda idanunsu ya sarke cikin na juna shida sadeeq din batare da ya karasa gaisuwar daya fara mika masa ba!
zainab dake zaune tare da prince akan cinyarta kuwa yana sauke idanunsa akan na sadeeq cike da murna cikin zazzakar muryarsa ta yara kananu yace "babii na!"
wanda maganar wannan yaron ne ya katse masu kallon cikin idanu da suke ma junansu! ba komai bane yasa hamma sadeeq kure fuskar yarima sadeeq da kallo sai ma ganin tsagwaron fuskar muradin zuciyarsa karara akan fuskar tasa! (aymana)! domin kuwa tabbas idan mutum yayi ma yarima kallo na tsanaki zai fuskanci ainahin kamanceceniyar halitta dake tsakaninsa da aymana wanda banbancinsu ita mace ce,shi kuma namiji ne!
shi kuwa yarima ba komai ne yasa shi sake baki sakaka harma da murza ido ba,sai don kallon photocopy na yayunsa guda biyu da suka kasance twins wato yarima dalhat(hassan) da yarima aliyu (usaini)! wanda sukayi aure tin shekaru uku da suka gabata!
wanda a halin yanxu har anyi nadin sarauta yarima dalhat mahaifi a gurin PRINCE DIZHWAR!
prince shi shi kadai ne yaro cikin wannan gidan,domin kuwa har zuwa wannan lokacin tsakanin su gaba daya babu wacce ta haihu cikin hassana da hussaina,sai gimbiya aneesah da ita kuma allah yayi mata rasuwa tin a ranar data kawo sa duniya sanadiyyar zubar jini da tayi,hakan ya daga ma baba waziri(yunusa) hankali fiye da tunanin mai tunani daga shi har hajjo sunji mutuwar yar tasu!
tausayin wannan yaro ne ya darsu cikin zuciyar mutanen gidan baki daya hadi da soyayyarsa sbd rashin mahaifiya da yayi a lokacin dayafi bukatar kulawarta fiye dana kowa a duniya!
bugu da kari kuma shine jika na farko da aka farayi masu cikin gidan,kuma bacin shi har yanxu shuru babu wani labari mai dadi!
ajiyar zuciya mai karfi sadeeq ya sauke inda yayi kokari wajen kore wannan tunani daya bijiro masa cikin murmushin yake yace "barka da zuwa kanin mu! da fatan kazo lafiya??"
gyara zama sosai yarima yayi shima cikin dakewa yace "lafiya qlaou fatan mun sameku lafiya??" "lafiya qlaou alhmdlh,ya mutanen gida??" sadeeq ya sake fada! kamin su samu zarafin sake magana sai ga nan prince ya haye cinyar sadeeq ya kwanto jikinsa gaba daya batare da yayi magana ba!
murmushi mai kyau yarima ya sake,sbd ya fahimci prince din ma yanayi ma hamma sadeeq ne kallo a matsayin mahaifinsa,domin kuwa kamar tasa har ta baci!
zainab dake zaune gefen musty suna kallon ikon allah tin dazu ta mike tace "hamma sadeeq ina matan gidan suke ne banji duriyarsu ba tinda muka shigo??"
harara ya watsa mata kawai batare da yayi mata magana ba ya maida kallon sa izuwa kan prince da kallo daya yayi ma yaron ya fuskanci tsantsar kamar da sukeyi da juna,harma yaron ya zarta shi a kyau nesa ba kusa ba!
haka nan kawai zuciyarsa ta shaida masa da cewa _NESA TA ZO KUSA_ !
kwance zainab ta tarda salifa shame shame akan katifa tana ta faman zazzaga baccinta hankali kwance! kuma gashi tayi wani irin shafal da ita alamun bata jin dadi ya nuna karara a fuskar tata!
bata tashe ta ba sbd kar tashin nata ya zamana ta kasa komawa baccinta! inda ta wuce dakin aymana! zaune ta tarda ita tsakiya gadon da kayan bacci! wanda hakan ya nuna mata karara cewa ko wanka batayi ba kenan? gashi yanxu ana naiman azahar
bugu da kari ma kuma ba komai ne yafi daukar hankalinta ba,sai yadda taganta tana cin kwadon garin kwaki,hannu baka hannu kwarya kamar irin koron yunwa dinnan!
sarai aymana ta ganta,amma sai ta dauke idanunta,taci gaba da cin abinci uwa bazata daina ba! sosai take ci wanda hakan yasa ko arzikin sannu da zuwa zainab din bata samu ba!
zainab kuwa data sake baki sakaka tana kallon ikon allah sai ta samu wuri tayi ma kanta masauki a bakin gadon ya tsura ma aymana ido da har wani gyada kai take tana lumshe ido alamun garin kwaki na aiki🥱🥱
"waike lafiyar ki kuwa aymana??" zainab ta fada tana gyara zamanta da kyau! dan dakatawa da cin abincin aymana tayi cikin dan tsuke face "tace mai kika gani??" girgiza kai zainab tayi tace "yanxu ke tsakaninki da allah wannan wace iriyar kazanta kika kwaso?? kuma ma a ina kika samo wannan dabi'ar sbd nidai ba haka nan na sanki ba? ace wai yanxu ma ana kiran sallar azahar ko wanka bakiyi ba? sannan kuma nazo wajen ki babu koman sannu da zuwa sai wannan garin da kika saka a gaba! kuma ma wai tsabagen iskanci akan gado tsakiyar gado kike cin abinci da hankalinki??"
zainab ta karashe maganar a dan zafafe! wanda hakan yasa aymana dakatawa da cin abincin nata tafara kananun guna guni wai zainab ta sata a gaba!
"zakuwa kiga na saki a gaba yarinya! wallahi ammy da anty zan kira yanxunnan suji labarin wannan kazantar dana ga alama harda rashin kunya ya koya maki! zainab ta fada tana mai fice wa daga dakin sbd ta dakko wayarta data barshi a parlo!
sbd rashin jin karfin jikinta yasa batayi yunkuri mai karfi ba,a hankali ta sauko daga kan gadon wacce ke sanye da wani riga da wandonta da sukayi mata yawa sosai,sai yawo takeyi a cikinta ta biyo bayan zainab din cikin muryar shawabar ta dake narkar da zuciyar hamman nasu tace "adda zainab karki kirasu dai am! hamma sadeeq kace karta hadani da su ammy allah kunya zanji"
ta fada idanunta na cikowa da kwalla a lokacin da ta gama shigowa cikin parlon,dik hankalinsu ne ya dawo kanta! dauke kansa musty yayi daga kallon barayin da take sbd idan ba haka ba kuma yasan kallon matar wani haramun ne dikda kusancin dake tsakaninsa da sadeeq din,amma shaidan sam ba'a iya masa.
shi kuwa yarima jikinsa har kyarma yakeyi a lokacin daya kallo fuskar aymana zufa ta fara karyo masa kamar wanda ke cikin tafashashshen ruwan zafi!
prince da har yanxu yake kan cinyar sadeeq cike da tsagwaron tsokala akan fuskarsa da sai yanxu nagani yace "goggo maryamu"
dik kallonsa sukayi sbd jin abinda yafada,da sauri yarima ya fice daga gidan da gudun tsiya,dik kiran da suke masa amma yayi biris dasu yayi ma motar tasa key kamar zai tashi sama,kowa in banda kauce masa babu abinda akeyi sbd alamu ya nuna ma mutane matukin cikin motar ba a hayyacinsa yake ba,cikin kankanin lokaci ya iso cikin masarautar tasu!
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/26, 9:49 PM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
instagram@itz me real oum mumtaz
G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com
facebook@oum mumtaz
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 37*
********** Bai wuce ko ina ba sai shashin mahaifiyarsa wato sarauniya khadeeja,matar galadima mai murabus!
sai mika masa gaisuwa kuyangin su keta faman yi amma sam bata su yake ba a halin yanxu,wanda hakan yasa bai tsaya ansa masu gaisuwar tasu ba, a lokacin daya karasa shigewa cikin shashin nata bai tarda ba!
kira yake ta faman kwala mata kamar wanda zai tashi wajen gaba daya! su kuwa bayin dake hidimta mata dik sun shiga tai ta yin su! "ina ummy??"
ya tambayi daya daga cikin bayin dake wurin ya tambaya! cikin kyarmar murya tace "tana shashin sarauniya mamma"
da sassarfa ya fice daga shashin nata batare daya tsaya sake jin wani batun ba kamar ana hankada shi! kowa kallon sa yake da mamaki sbd yadda ya shigo a birkice! gashi kuma ba'a gansa tare da prince da suka fice tare ba!
kamar wanda aka hankado sa haka nan ya fado shashin mamma! a kusan lokaci daya mamma da ummyn nasa suka mike sbd yadda ya shigo masu alamu ya nuna ba lafiya ba!
mamma ce tayi kokarin zaunar dashi akan wani dakakkiyar tumtum na inda take zama,sannan itama ta zauna kusa dashi tana kwantar masa da hankali ta hanyar bubbuga masa bayansa alamun lallashi!
kamilalliyar fuskarta ta dago dake cike da tsananin kwarjini gami da haiba na cikakkun mata masu riko da addini sosai! kallo daya tayi ma bayin dake zagaye dasu,suka fice daga shashin kansu a kasa!
ummy kuwa dake zaune tin dazu ta zubama yaron nata ido da suke tsananin kama da juna! deep down hankalinta a mugun tashe yake,amma kuma sai tayi kokarin boyewa sbd kawaici irin nata!
sun dauki tsawon mintuna 4 shuru babu wanda yayi magana,sannan mamma ta katse shurun nasu ta hanyar wurga masa tambayar daga inda yake...???
saida ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kamin ya kalle iyayen nasa cikin wani irin yanayi mai kama da farin ciki yace "Nagansu!"
a kusan lokaci daya mamma da ammy suka hada baku nan su da har rawa yake "su waye...?"
amma ya gagara fada masu magana daya kwakkwara sai na gansu yake ta faman maimaitawa fuskarsa na fidda annuri na tsantsar jin dadi!
ganin yadda abin yayi yawa ne yasa mamma kallon amintacciyar baiwarta dake zaune daga can gefe! inda ta umarce ta data je tayi mata kiran su baba galadima tare da baba waziri da kuma sarki masu murabus acan inda suke zaman zumunci tsakankaninsu!
Ba a dauki tsawon lokaci ba kuwa saiga kamilallun dattawa sun shigo shashin su ukun su sanye suke da wasu rantsatstsun al kyabbu masu kyan tsari sai baza kamshi suke!
a yanayin yadda suka tarda su ummy zaune sunyi jugum jugum ne hasashen su na ba lafiya ba da sukayi ya sake tabbata!
bayan sun samu wurin sun zauna ne baba galadima ya masa jan ido kamin yarima sadeeq ya bude baki yayi masu bayani:
"mustapha da mukayi makaranta daya dashi wanda nake baku labarinsa ya taimaka min a dangane da karatu na lokaci da aka kaini! toh dama akoi wani dan uwansa daya ke yawan bani labari,wanda a fadan sa cemin yayi su tagwaye ne! ban taba ganin dan uwan nasa ba ko a photo! balle kuma a zahiri! a maganar da nake maku a halin yanxu ko wanne daya daga cikin su yana da matar auren sa! sannan kuma suna zaune da matan su a cikin garin nan ne! wanda na kai ma shi mustapha ziyara a yau dinnan! bayan mun gama gaishe gashen da zamuyi ne yayi man iso zuwa gidan dan uwan nasa domin mu san juna dani da shi ko don zuwa gaba!
abinda ya matikar bani mamaki hadi da dauren min kai a lokacin da muka shiga gidan ba komai bane,sai wanda yake a matsayin tagwayen musty idan kuka gansa to tabbas kunga su ya yarima!
ma'ana dai kamanceceniyar da sukeyi na halitta harya zarce ka'ida! wanda ban gama shan mamakin wannan abin al'ajabin ba saida idanuwa na suka sauka akan wata matashiiyar yarinya da bazata wuce shekaru 16-17 ba da suke tsananin kama da maryam! wanda haka zalika nima sosai muke kama da ita wallahi! babu abinda ya banbanta mu in banda ni namiji ne ita kuma diya mace!"
a kusan lokaci daya dikkansu suka mike tsaye jikinsu banda tsuma babu abinda yakeyi! sarki mai murabus kuwa in banda kabbara babu abinda yake zubawa a wannan lokacin domin kuwa dikkansu dake wurin a yadda yarima sadeeq ya basu labari suna kyautata zatohn cewa yaransu da suka baza manya manyan malaman addini dake masu addu'a a kansu tin shekara daya da ya gabata lokaci ne da allah ya anshi addu'arsu!
malika maryam data zama tsohuwa sosai aka kaima wannan daddan labarin daya sata mikewa da kafafunta babu wani tangarda! wacce a shekarun baya bazaka taba iya cewa ita din bace sbd yadda tsufar tayi mata yawa! shekarun nata yaja kwarai da gaske!
hajja ce ta riketa zuwa bakin motar da aka tanada masu domin son zuwa tantancewa da idanunsu!
cikin kankanin lokaci labari ya karade cikin masarautar ai anga yaran gidan guda biyu da ake nema tin kamin a tabbatar!
motoci kusan guda goma sha suka fice daga gidan,kuma ko wanne dankam yake da yaran gida da abin ya shafa! dama wayanda basu da labari!
motocin su basu sulale ko ina ba sai cikin jami'ar abubakar tafawa balewa universty! mutanen cikin gari dama student da dama sai suka zamto yan kallo! domin kuwa kowa bama idanunsa hakkinsa yake dakuma mamakin abinda ya shigo da yan gidan sarauta masu uban yawa har haka!
yarima ne yayi masu jagoranci har zuwa gidan! inda ya kwankwasa masu kofa sbd umarnin hakan dasu sarki suka basa!
Tin a lokacin da yarima ya fice a kidimen nan,musty ma ya fice kan bari yaje dubo sa,zainab kuwa da gasken take,domin kuwa su ammy ta kira kan kazantar data ga aymanar nayi! wanda hakan yasa ammy tace abama sadeeq wayar,bayan sun gaisa ne ta umarce sa kan ya kawo mata salifa da aymana din idan da sarari!
hakan yasa musty da zainab ma shiryawa kan zasu je su! a lokacin da suka shirya tafiyar tasu ne sukaji ana masu knocking na kofar! hamma sadeeq ne yaje ya bude da prince dake sabe kan kafadarsa har yayi bacci!
wanda ya kalla a kofar ne yasa shi sakin fuska kadaran kadahan! iso yayi masa kan ya shigo mana ? amma sai ya shaida masa kan tare suke da baki idan da hali zayyu su shigo??
gyada masa kai sadeeq yayi batare da yace masa kala ba alamun eh!
juyawa sadeeq yayi da niyyar shigewa cikin gidan haka nan yakejin gabansa na bala'in faduwa! kawai saiji yayi an basa wani irin kyakkyawar rungumar da tinda yake a tsawon rayuwarsa ba'a taba masa kalar saba!
wata iriyar ajiyar zuciya suka sauke tare da mamma dake rungume dashi ta baya tana sakin sheshshekar kuka mai cike da tsananin kewa hadi da begen abinda aka jima ana tsumayinsa!
sosai sadeeq ya rintse idanunsa sbd jin yadda kukan matar da bai kai ga juyowa yaga wacece ba ke ratsa masa jinin jikinsa!
dik wayanda ke gurin da suka san asalin labarina abinda ya faru saida suka tausaya ma mamma sbd kukan da takeyi! hatta ummy dake ta faman wulga idanuwa sbd son ganin ta inda tata yar da ko kallon ta bata tabayi ba saida ta tausaya ma mamma! domin kuwa yin shekaru ashirin da shida zuwa da bakwai batare da ka san taka mai mai inda gudan jininka yake ba ba karamin abu bane!
malika b dake gefe ne ta ratso zuwa inda suke ta zagayo ta gaban sadeeq da har yanxu ya gagara juyo wa ta tsura ma fuskarsa ido!
idanunsa da suka canza launi daga farare zuwa jajaye ya bude su fes! ya sauke su akan tsohuwar dake gabansa! sosai suke kallon kallo a wurin kowa yayi tsit kamar anyi ruwa an dauke sbd son ganin kalar reaction din da malika b zatayi!
"Allahu akbar! allah mai iko yau ya nuna mana ikon sa bayan tsawon shekaru batare da tsuminmu ko dubara ba! tabbas wannan yaro jika na ne koda kuwa dik duniya zasu taru suce min ba haka ba"
ta karashe maganar tana mai rushewa da kuka tsakaninta da allah! wanda hakan yasa hamma sadeeq juyowa sa hanzarinsa sbd son ganin iya adadin mutanen dake wurin!
idanunsa ne suka sarke cikin na juna tare da mamma dake kallon sa idanunta na zubar da kwalla na tsananin farin ciki! domin kuwa babu tantanama wannan yaron jininta ne!
daya bayan daya yake binsu da kallo yana jin zuciyarsa na kadawa kamar tayi tsalle ta fado kasa,bama daya kalli fuskar mamma da ummy dakuma maryam hadi da yarima sadeeq!
babu tantana ma wayannan family na aymana ne sadeeq ya aiyana a ransa! sbd tsantsar kamar da ummy da mamma keyi! wanda yarima sadeeq ya dakko fuskar mahaifiyarsa wanda hakan yasa yake kama da mamma! ga kuma maryam data kasance yace a wurin mamma itama mai masifaffen kama da aymana kamar an tsaga kara!
sadeeq bai gama yin suman tsaye ba a wannan wajen sai da yayi tozali da sarki mai murabus wato ABDUL_WAHAP ! domin kuwa wannan mutumin suna tsananin kama dashi hammma sadeeq din fiye da tunanin mai tunani saidai shi fuskar manya ta sadeeq kuma fuskar yarinta!
1hr letter
kowannen su in banda sharar kwalla babu abinda yake sbd bayani na asalin sadeeq da aymana dasu ammy sukayi masu! inda ammy da mamma kam da suka hadu kallon farko da sukayi ma junansu ko wacce ta shaida yar uwar ta!
wanda a wannan wajen nema sukaji cewa ashe a lokacin da waziri yunusa ke kan bakarsa ta tsananin son mulkinsa ne ya aika yaransa asibitin da aka haife su sadeeq kan cewa idan da namiji rumana ta haifa su kashe sa karsu barsa da rai!
wanda basu san cewa ashe wata amintacciyar baiwarta ta juyo sirrikan su ba,inda ta shaida ma rumana kan akou masu farautar rayuwar abinda zata haifa idan ya kasance cikin jinsi na yaya maza!
wanda hakan yasa rumana sukayi musanyen da da ammy a cikin labour room sanadiyyar daya raba sadeeq kenan dik a sanadiyyar son zuciya irin na wasunmu!
wanda batan aymana kuma daga cikin yan uwanta dakuma danginta ya samo asali ne dik ata sanadiyyar yunusa da kuma matar sa hajjo da sukayi amfani da masu aiki a bangaren abinci aka zuba maganin bacci daya sa ranar gaba daya sukayi wani irin bacci da basu taba yi ba,inda a cikin abincin khadeeja kuwa wato ummy suka zuba mata maganin dazai tasar mata da nakuda,wacce sam bata cikin hayyacinta ma ta haifi yar tata! su kuma sukayi amfani da wannan damar wajen batar ma da kowa dake cikin gidan hankali dangane da cikin ita ummy din,wacce aka wayi gari babu ciki a jikinta babu dalilinsa ammma an gagara samun mutum daya dazai iya sanin dalili _(rumana,umma da kuma ummy nace maku sun sake samun ciki lokaci daya a page 14 inda yarinyar rumana taci sunan maryama,umma kuma ayna'u sai ummy kuma babu ita......... haka nan na rubuta maku amma nasan hankalin mutane da dama dake cikin ku bakuyi tunanin da wata a kasa ba🥰)_
wanda saida ga baya ne a lokacin da yarima yunusa ya tuba yake shaida masu dangane da batar da aymana da yayi! inda sai a lokacin kowa ya farga da hakan,an nuna masa bacin rai kam kwarai da gaske,inda daga baya kuma suka rungumi kaddara suka saka addu'a a gaba kan allah ya baina masu ita a dik inda take!
inda a lokacinne mamma ta shaida masu itama abinda ta boye masu dangane da sadaukar da yaronta dayayi izuwa ga matar da bata sani ba!
ankai ruwa rana kamin aka samu fahimtar juna,tinda babu wanda yafi karfi aikata kuskure a duniya!
sannan kuma su ammy ma sun shaida masu dik abubuwan da suka faru a rayuwar yayan nasu da basu rayu da suba na tsawon lokaci!
idan kaga fuskar su oga sadeeq a lokacin sai kusha mamaki sbd tsananin farin ciki! haka nan aymana ta makalkale ummy da taji soyayyar mahaifiyar tata da a baya cikin rashin sani tayi masu gurguwar fahimta!
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/28, 9:56 AM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
instagram@itz me real oum mumtaz
G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com
facebook@oum mumtaz
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 38*
********** Kowa dake wurin saida ya jinjina hukunci irin na ubangiji! haka nan mamma bakinta yayi kadan wajen nuna godiyarta da kuma yabo zuwa ga ammy akan namijin kokarin da tayi wajen rainon gudan jininta da zuciya daya batare da wata cutarwa ba!
anyi farin ciki iya farin ciki! aymana na rungume da mahaifiyar tata datake jin babu wanda yakaita farin ciki a fadin duniyar nan!
haka nan hamma sadeeq ma na kusa da mahaifin nasa kamar ya shige cikinsu yakeji a wannan lokacin don tsananin farin ciki da yake ciki!!
bama kamar yar tsohuwa kam itama bakinta ya kasa ruhuwa sbd farin ciki! abinka ga manya kuwa tuni suka gano shigar karamin cikin dake tattare da salifa dakuma aymana sbd yanayinsu!
an yafi juna,kuma kowa ya dauki laifinsa,wanda ba komai bane kuma silar abubuwan da suka faru saina rashin kulawar da malika b ta nuna ma yunusa tin yana kankaninsa tare da iyalansa! wanda kuma hakan ma babban kuskure ne kwarai da gaske!
baba da su abba kuwa sosai suma suke cikin farin ciki na wannan ranar da allah ya sada sadeeq da aymana da ainahin iyayensu! wanda anty kuma kunya ce ta kama ta sosai idan ta tuno da abubuwan da ta aikata ma aymana akan dalilinta mara tushe!
da su salifa aka wuce masarauta da suka tashi tafiya! inda can ma suka samu tarba na ban girma daga cikin wannan gida,kowa sai haba haba yakeyi da su! sbd girmamawa da kuma mutunta bako irin nasu!
kowa kuwa saida ya jinjina irin kamar dake tsakanin sadeeq da su hassan da usaini! domin kuwa kamat harta yi yawa!
da dare aka maida su ammy gida amma banda su aymana da kowa yasan da shigar cikin da salifa ke dashi na tsahon sati bakwai,ita kuma aymana sati biyar!
wanda hakan yasa kowa keyin haba haba da su! zuwa wayewar gari kuma labari ya gama karade kasar nigeria dan gane da bayyanar yaran gidan da suka bace shekarun baya da suka gabata,amma kuma babu wanda aka fada ma musabbabin dalili!
wanda hakan yasa kowa da kowa sai barka ake ma su!
bayan sati daya!
cikin wannan sati dayan kuwa gata iya gata sadeeq da aymana sun ganta cikin danginsu! wanda sai a wannan lokacin suka dada tabbatar da cewa babu abinda yafi ka rayu cikin danginka dadi dakuma dorewar farin ciki har abada!
wanda baba galadima yaso a sauke dansa wato yarima dalhat a matsayin sarki don sbd dokar masarautar su batace haka ba,amma kowa bai basa goyon baya ba,sbd allah ne kadai yasan dalilin daya sa hakan ta faru batare da wani tsumin su ko dubara ba!
inda kuma aka daura alkawarin aure tsakanin PRINCE DIZHWAR da kuma dik yarinyar data kasance itace yar fari da sadeeq zai haifa! wanda aka ajiye sa cikin kundin su na sarauta ko bayan babu su ne a doron kasa!
wanda hakan kuwa sosai yayi ma mutane
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 14