da dama dadi kwarai da gaske! cikin wannan lokacin kuwa ba karamin sabo da kuma dangantaka mai karfi bane ya kulllu tsakanin sadeeq da yan uwan nasa da wayanda suka fito ciki daya dama cousings din nasa,haka aymana ma!
sosai kuwa mamma da ummy ke masifar ji da su salifa kwarai da gaske! kodon sbd mutunci dakuma girman wannan ahalin da sukayi masu,ko tari salifa tayi zakuji sai an samu mai tambayarta akoi ahinda kike bukata ne!? ko kuma akoi inda ke maki ciwo?
wannan karamcin da ammy taga sunayi ma yar tata yasa taji hankalinta ya sake kwanciya,inda ita kuma kwacokam hankalinta ya karkata izuwa ga bama aymana kulawa ta musamman tinda ta lura dik kara ne yasa sukafi kula da ita salifan bawai don basu damu da aymana ba!
yaya haida kuwa tuni ya gano matar sa cikin gidan wato gimbiya maryama dake masifaffen kama da aymana kamar an tsaga kara!
tin suna soyewarsu a boye har dai abin ya fito fili,haydar yayi tunanin bazasu basa ita ba sbd banbancin matsayinsu amma sai yaga sabanin tunaninsa sbd yadda suka nuna sunfi sa jin dadin hakan,inda aka tsaida lokacin bikin nasu tare dana su gimbiya fatima kanwar hamma sadeeq kenan,da kuma ayna'u ya a wajen umma wato kishiyar mamma sbd suma dama sun samu mijinsu!
dik wanna bidirin da akeyi an hana su sadeeq matan su kan sai anyi auren au fatyma da yayi sauran wata daya ne kwata kwata!
mimi kam mijinta bai yadda ba,domin kuwa ma su tafi kasar america yawon cin amarcin su da basu samu damar yi ba!
a lokacin da ake fara tafiya aiki hajji cikin azumi tare da ammy,anty,abba,baba dakuma sameer da rahma suka wuce saudiya,wanda aka biya masu cikin wannan gida,wanda kuma da zaran sun dawo da sati daya ne auren su haydar!
sunje sun sauke farali sun dawo lafiya cikin hukuncin allah,inda aka fada cikin shirye shiryen aure gadan gadan! inda wayewar wata rana ta asabar aka daura auren amare da kuma angwayen su da ya samu halartar manyan mutane manya da kananu!
washe gari kuma aka mika ko wacce gidan mijinta dakuma fatan alkhairi! inda a lokacin idan kuka su aymana da salifa sai kun sha mamaki sbd yadda fatar su ta murje suka sake zama wasu manyan mata da su! sun wani cicciko sbd samun kulawa ta musamman da sukeyi!
inda sadeeq da musty kuwa dik a takure suke akan hana su matan su da akayi na tsawon watanni biyu!
saida aka zagata dasu dangin ciki da bai kowa ya gansu suma suka gansu kamin aka bama sadeeq da musty matansu a wayewar garin yau !
sosai kuwa suka cika da farin cikin wagga abu! prince kuwa ya makale ma hamma sadeeq sam yaki yadda da kowa,dan haka babu yadda suka iya aka wuce dashi akan idan an koma makaranta a dawo dashi!
an gyara masu gidan su babu wani datti da suka tarar,salifa dama nata laulayin mai saka mutum bacci ne,ita kuma aymana cin abinci kamar babu gobe! dan haka daga lokacin sai suka daura daga inda suka tsaya!
bayan wata biyar da sati biyu!
A cikin wannan lokacin cikin salifa da kuma aymana yayi bala'in tsuma,inda ita salifa harma ta wuce lokacin edd dinta da sati daya! bayan ita kuma aymana saura sati daya nata edd din ya cika!
wanda a wannan lokacin su zainab dakuma mimi dama su hassana da hussaina dik kowaccensu keda shigar karamin ciki!
inda suka zamtoh abu daya,farin ciki da kuma kwanciyar hankali ya sake wanzuwa cikin wannan family din!
A wayewa garin yau salifa ta tashi da matsanancin ciwo na nakuda,wanda hakan kuwa yayi masifar daga ma sadeeq dasu aymana hankali! basu tsaya bata lokaci ba suka garzaya asibitin da haydar ke aiki acan domin bata taimako da gaggawa!
banda sharban kuka babu abinda aymana keyi sbd halin dataga salifa a ciki! haka sadeeq ma kawai daurewa yakeyi amma tabbas da akou halin zamanyin kukan tausayinta shi din ma zayyi!
abba ya kira ya shaida masu halin da ake ciki! inda cikin minti talatin su ammy da su anty suka iso asibitin hankali tashe! amma har yanxu shuru kakeji babu wani labari!
su mamma ma sunji labari amma ita bata zo ba sai ummyn aymana dakuma su hajjo ne sukazo su!
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/28, 10:32 PM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
instagram@itz me real oum mumtaz
G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com
facebook@oum mumtaz
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
🔚 *PAGE 39-40*🔚
**********Sun dauki tsawon awanni uku a wajen amma shuru kakeji,wanda hakan yasa hankulansu yayi masifaffen tashe gashi babu halin shiga! hankalin sadeeq dasu ammy ba karamin tashi yayi ba! aymana kuwa banda gumi babu abinda ke tsatstsafo mata daga goshin ta na tashin hankalin halin da aminiyarta kuma abokiyar zaman nata ke ciki!
suna nan sunyi cirko cirko saiga ya haydar ya fito daga dakin shima sharkaf yake da zufa zuwa inda suke! tin kamin ya karaso dik kansa sukayi suna tambayarsa "ta haihu ne?? wane hali take ciki??" wayan nan sune tambayoyin da suka fara wurgo masa,amma bai bama kowa ansa ba sbd bata su yake ba!
kallon sadeeq daya zuwa masa jajayen idanunsa haydar yayi cike da tausayin sadeeq d'in yace "ka biyo ni office"
yana gama fadar hakan yasa kai zuwa office nasa sadeeq ya take masa baya a gaggauce !!
ko zama bai samu damar yi ba,haydar yace "kayi hakuri sadeeq,munyi iya kokarin mu dan gane da halin da salifa ke ciki amma abin ya faskara,in takaice maka bayani dai yanxu ga wannan takardar idan ka yarda zamu shiga domin ayi mata cs,wanda nake tunanin wannan itace hanya mafi sauki da zamu ceto rayuwarta daga yunkurin fadawa cikin wata gagarumar matsala"
hamma sadeeq bai samu zarafin sake magana ba ya anshi papper din da aka basa yasa hannu,hannunsa har karkarwa yake ya rantaba hannu!
cikin kankanin lokaci aka shirya dik wasu abubuwa daya kamata aka shiga da salifa data mugun fita a hayyacinta bata ma san wayanda ke kanta ba sbd tsananin azaba,banda kiran sunan mahaifiyarta babu abinda takeyi!
dik gida abba yasa su koma,ammy,ummy da ayamana sai kuna sadeeq kawai aka bari da suma hankalinsu a tashe yake!
Bayan awa biyu!!
haydar ne ya fito daga dakin tiyatar idanunsa sun kada sunyi jazur,hannunsa nanne de da wani farin yadi wanda nake kyautata zatohn jariri ne a ciki ya dosa zuwa inda su baba ke tsaye!
kansa a kasa ya karaso wurin dik suka zuba masa ido kirjinsu na dukan uku uku! kasa dago kansa ya kalle su yayi sbd baisan da wani ido zai iya duban tsakiyar idanun su ammy ya shaida masu ta allah ta kasance ga salifa ba😭😭
batare da wanin su ya sami zarafin cewa wani abu ba kawai sai ga wata nurse da ake shiga tiyata da ita ta fito tana share zufar dake goshinta zuwa inda suke!
da sauri haydar ya mika ma ummy jinjirin dake hannunsa ya bar wurin sbd bazai iya jurar ganin irin tashin hankalin da yan uwan nasa zasu shiga ba!
A lokacin da wannan nurse din ta shaida masu allah yayi ma salifa cikawa ba karamin firgice game da razana bace ta bayyana karara akan fuskokinsu baki dayansu hatta ga su abba dake karfafa masu gwiwa kamin su sami wannan labarin!
wani irin bangaza da sadeeq ya bama likitar ne yasa ta faduwa a gefe! kamar na mijin zaki haka nan ya dumfari zuwa cikin dakin tiyatar da ba'a kai ga fitowa da ita ba!
aymana kuwa dake daga gefen su wata iriyar jiri ce ta kwashe ta a wurin sbd masifaffen shock daya dibeta,take taji cikinta ya masifar murda mata daya sata kwallara wani irin uban ihu daya sa hankalin mutane ya dawo kanta !
wani irin masifaffen nakuda ne ya taso mata daya sa wannan nurse din karasa wa wurin ta kira emergency! abba da baba dakuma naseer ne sukayi kanta a lokaci daya suna ambatar sunan allah!
inda lokaci daya ammy ta yanki jiki ta fadi sbd shiga shock! emergency aka shiga da aymana da kuma ammy! wanda labour ne gadan gadan ya tasar mata!
ummy kuwa dake rike da jariri fari tas da shi kamar sadeeq yayi kaki ya tofar banda addu'a babu abinda takeyi zuciyarta na dokawa!
shigar sadeeq cikin wannan wurin yayi dai dai da lokacin da ake rufo ma salifa fuskarta da wani shudin kyalle!
yayi abin rufar yayi inda fuskarta dake shimfede da annuri dake fidda haske ya bayyana kamar ka kirata ta ansa amma kuma ina?? hakan ba mai yuwa bane domin kuwa dai aymana ta ansa kiran ubangiji😭😭
wani irin fashe wa da kuka hadi da sulalewa sadeeq yayi a wurin kirjinsa na bala'in bugawa! gashi kuma ya kankame gawar salifa da ake kokarin ficewa da ita daga wurin yana sakin sambatu kan miyasa zata tafi ta barsu a dai dai lokacin da suka fi bukatarta...?
abba da shima zuciyarsa ta bala'in karyewa sbd ido biyu da yayi da gawar yarinyar tasa amma haka nan yayi kokari wajen ganin ya rarrashi kansa sbd yasan mutuwa akan kowa take shidin ma kuma bawai tayi jinkirin zuwa wurinsa bane kawai dai lokacin sa ne bayyi ba!
dago sadeeq yayi ya rungumesa sosai cike da tsantsar tausayin kansu sbd rashin salifa da sukayi a dai dai wannan lokacin da basu taba tsammata ba tabbas ya girgiza su!
wanda hakan yasa aka samu damar ficewa da ita daga dakin tiyatar akayi dik wasu cike ciken da suka kamata aka hada baba,ummy da kuma naseer da gawar tata zuwa gidan su ammy din kenan! hankulan su anty da kuma su sameer da rahma dake gidan ba karamin tashi yayi ba a lokacin da suka samu wannan mummunar labarin!
inda cikin kankanin lokaci kamin kace kwabo gida ya cika da jama'a banda koke koke babu abinda sukayi sbd yadda mutuwar ta shige su a dai dai lokacin da basu taba tsammata ba!
mimi da zainab ma idan kuka gansu sai kun tausaya masu kwarai da gaske! wanda kuma hakan ma nasu nafila ne! idan akayi compearing da halin da hamma musty ya fada a ciki a lokacin daya samu labarin rasuwar kanwar tasa da dik duniya bashi da tamkar ta! gida ya cika makil da jama'a,domin kuwa har aynahin gidan su hamma sadeeq dik sun zo gidan su ammy manya da yara!
.........Acan asibiti kuwa emergency aka shiga da ammy da kuma aymana! inda cikin kankanin lokaci kuwa ta sauka! inda ta santalo da yaron ta namiji itama mai masifaffen kama da hamma sadeeq kamar an tsaga kara! dik irin soyayyar dake tsakanin da da uwa amma ita sam bata wannan yaro take ba,in banda sambatun kiran "AUTA" babu abinda takeyi a wannan lokacin!
bedrest na awa biyu aka bata,wanda idan ta farka zasu sallamota!
inda a gefen ammy kuwa saida su ya haydar sukayi da gaske kamin suka samu nasarar dawo mata da numfashinta dai dai ta dawo cikin hayyacinta!
abba ne ya hado sadeeq,ammy da kuma aymana tare da jinjirin data haifa a lokacin da aka gama masu settling na komai a lokacin la'asar ce!
wanda jama'ar da suka tarda a gidan sosai hankulansu ya sake tashi! zuwa lokacin mamma da anty sun riga da sun mata wanka har an shiryata! wanda aka ajiyeta mutane da dama na tofa mata addu'oi na neman dacewa a lahira kamar yadda suke kyautata mata zatoh tin a nan!
kofar gida cike yake da maza,inda cikin gida kuma ke cike da mata! baba ne keta faman aikin tausar zuciyar hamma musty sbd firgicin daya shiga! kaman wanda ake controlling nasu da remot haka nan suka karasa zuwa cikin gidan nasu!
wani irin imani ne gami da tawakkali ya ratsa zuciyar ammy a lokacin sbd tasan kukan d takeyi babu abinda sai amfana ma yar tata! wanda ta sata a gaba hawaye na zuba cikin idanunta tana zubo mata addu'a sosai ba kadan ba!
haka nan hamma sadeeq da dik wasu wayanda take da alaka da su saida suka sakeyi mata addu'a kamin akazo fita da ita zuwa gidanta na gaskiya! a lokacin ne kuma gidan ya kuma hargitsewa kamar me?
aymana yar suma saida tayi a wannan lokacin sbd tsananin zaucewar da tayi! haka nan gida ya sake cika da hayaniya fiye da kima!
inda aka wuce da ita gidanta ma gaskiya da muma muke jiran namu lokacin daza'a birne mu cikin kasa ta rufe mana idanuwa! Allah kasa mu cika da imani👏🏼👏🏼😭😭😭😭😭Allah kasa muyi kyakkyawan karshe ka kuma sake shirya mu bisa koyarwar fiyayyen halitta Annabi muhammad(S A W)😭😭😭👏🏼👏🏼
sai bayan magriba kamin suka dawo daga makabarta! inda aka sake sabon zama a kofar gidan har su sarki da kansu saida suka halarci wannan wurin!
a cikin gida kuwa mamma da kanta ta bada umarnin aymana ta shayar da yaran dikkansu biyu sbd kananun kukan jarirai da suka soma! wanda dik wanda ya gansu idan baisan asalin cewa ba ciki daya suka fito ba tabbas zai ce yan biyu ne! kuma yan biyun ma identical twince sbd masiffafe kamar da suke yi da junansu!
Bayana anyi sadakar bakwai gida ya sakr zama shiru sosai! wanda dama mai surutun nasu Allah yayi ikonsa akan ta!
hamma sadeeq sosai yayi rama a lokacin sai uban kashin wuya daya tara sbd idan yace ma baya son salifa zuwa wannan lokacin to kuwa yaci karya ya kwana da yunwa!
ranar sadakan bakwai dinne aka rada ma yaron da salifa ta haifa sunan abba wato abdullahi,shi kuma yaron aymana mai sunan baba wato yasuf! ana kiran su da _NORAIZ da NURAZ_
yara yan gata sunyi bul bull da su abinsu gwanin sha'awa sbd kulawar da suke samu daga mahaifiyar tasu bama kaman _NURAZ_ wanda shine mai sunan abba d'in!
a lokacin ne su mimi da zainab ko wacce ta koma gidan mijinta inda dik gida aka watse aka bar su ammy da kewa!
wanda kuma ammy ce kema aymana wankan jego! tare da taimakon anty sbd tana kallon aymana ne a matsayin marigayiya salifa!
saida suka shafe watanni biyu cur a gida kamin su ammy suka sallama,ma sadeeq matar sa tare da yaran sa bayan an yi zama an sake nemar yafiyan juna tare da kuma fahimtar juna!
wanda zuwa wannan lokacin kuwa mutuwar auta ta riga da tabi jikinsu sai dan abinda ba'a rasa ba!
an gyara komai na gidan nasu tsaf tsaf da shi gwanin ban sha'awa wanda hakan kuwa sosai ya birge aymana! shi kuma sadeeq yajia sa cikin farin ciki sbd ganin zallar farin cikin hakan akan fuskar matar tasa kuma uwar yaransa noraiz da nuraz!
BAYAN WASU SHEKARU!
Wanda zuwa wannan lokacin abubuwa da dama na farin ciki da kuma akasin ta sun faru cikin wannan familys din! an samu karuwa kuma ansa samu raguwa!
domin kuwa yanxu haka bacin su nuraz yaran aymana guda hudu ne kuma dikkansu maza ne babu ta mace ko guda daya! wanda idan an hade su yaran sadeeq guda shida kenan cif cif!
su zainab da su mimi,hassana sa usaina,matar su haydar dik suna da yara daga masu uku sai masu hudu amma basu da diya mace ko guda daya da suke mafarkin samu akan cikin aymana da kuma zainab dake dauke da kananun ciki na tsawon wasu watanni!
farin ciki da kuma annashuwa game da walwala ya sake wanzuwa cikin wannan gidan! daga cikin babban abinda sukayi rashi kuwa shine rasuwar malika b,sarki abdulwahap da kuma baba ! wanda muke masu addu'ar allah ya jikansu ya kuma gafarta ma dik wani musulmi dake fadin duniya baki daya👏🏼
PRINCE DIZHWAR a halin yanxu yana cikin shekarun sa na sha uku kenan da haihuwa! wanda kuma izzah game tsananin miskilanci mai tafe da kewar mahaifiya ce ke nukurkusar wannan yaro! yana masifar son aymana da suke kiran ta da OUM! wanda a bakinsa su nuraz ma sukaji sunan da yasa suka mike dashi a bakinsu!
bayan wasu watanni kuwa cikin hukunci na ubangiji saiga aymana da zainab da haihuwar yaya mata dai dai abinsu!
ALKAWARIN ALLAH YA CIKA! ranar suna na zagayowa kuwa yarinyar aymana taci sunan salifa suna kiranta da "AUTA" kamar yadda ake kiran mai sunarta kawo girmanta!
ita kuma yarinyar zainab sai taci sunan mahaifiyarta wato hauwa suna kiranta da jidda yara yan gata gaba da baya ta ko wani fanni! saida muce allah ubangiji ya raya mana yaran mu bisa tafarkin addinin musulunci!
_ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!! DIKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH UBANGIJI SUB HANAHU WATA'ALA MAI KOWA MAI KOMAI DAYA BANI DAMAR KAMMALA WANNAN LITTAFIN NAWA WATO 💥AYMANA💥 ABINDA NA RUBUTA DAI DAI INA FATAN ALLAH YA KARA MAN BASIRAR DA ZAN SAKE RUBUTA FIYE DA HAKAN ZUWA NAN GABA! WANDA KUMA NAYI KUSKURE ALLAH YA YAFE MANI AMEEN!!_
_GA MASU SON CI GABA DA KARANTA LITTAFAINA DA ZASU ZO NAN GABA KAMAR SU :_👇🏻
1- RIJIYA TA BADA RUWA! (na kudi ne)
2- RAYUWAR DARAKHSHAAN(na kudi ne)
3- PRINCE DIZHWAR(kyauta)
_SAI A TUNTUBE BE NI AKAN WANNAN LAMBAR 09076427357 THROUGH WHATSAPP! BANDA KIRA PLS☺️☺️☺️_
A huta lafiya🙌🏼
KARKU MANTA NICE DAI MARUBUCIYAR LITTAFIN👇🏻
ZATOH
👇🏻
AYSHAT
👇🏻
NUNA SO GABAN KISHIYA
👇🏻
NIGERIA KO NIGER(wacece bora)
👇🏻
TA'UMMU KA (aure saida kaka)
👇🏻
HAMDEEYERH
👇🏻
NURAAZ (treasure of noor)
👇🏻
SILAR AL-MAJIRANCI(200)
👇🏻
AYMANA(romantic story)
👇🏻
KUNJI MUNAFUKI.
*OUM MUMTAZ✍🏿*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 14