Share this page
sako dake cikin birnin zuciyarta da kuma duniyarta! su sadeeq kuwa cikin wayannan kwanaki biyun sunyi settling na dik wasu abubuwan da suka kamata! domin kuwa ko wannensu nada nasa masaukin cikin staff quaters dake cikin atbu na likitoci dakuma lectures! sai suka rufe gidan sadeeq din suka zauna a na musty tinda dama komai nasu a hade yake! haka nan haydar ma yasamu nasa muhallin sbd matsayin karatun nasu ba kadan bane! bayan wata daya! *OUM MUMTAZ✍🏿* [11/23, 4:01 PM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥 _ROMANTIC STORY_                                *MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*       Wattpad@UMMIE2018. instagram@itz me real oum mumtaz G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com facebook@oum mumtaz *FREE BOOK.* _LITTAFIN KYAUTA._ *DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️             *PAGE 34* ********** Bayan wata daya. zuwa wannan lokacin komai ya zama dai dai a bangaren su sadeeq,domin kuwa bayan muhallin da aka mallaka masu harda motar hawa ko wannensu dai dai! manyan lectures ne a fannin yan masters! wanda zuwa yanxu sun sake zama manyan yara yan kimanin shekaru 26-27 fes fes dasu son kowa kin wanda ya rasa! sannan kuma a dik karshen mako sukan zuwa gida su ziyarci iyayen nasu da kayayyakin alkhairi,yayan banki sun fara samun muhalli tattare da su ga kuma albashinsu mai tsoka! wanda zuwa wannan lokacin abin farin cikin daya faru shine soyayyar musty da zainab,dakuma salim abokin su musty din tare da mimi! wanda har an riga an tsaida magana nan da watanni uku masu zuwa za'ayi auren nasu! wanda idan an tashi za'a hade ayi bikin auren dana su sadeeq da ba'a samu damar yi akai masu matan su can wuraren aikinsu! wanda salim dama shima acan bauchin yake nasa aikin sch of nursing! haydar oga ne dai har yanxu babu wani kwakkwaran zance a kansa domin kuwa shi yace har yanxu bai samu kalar matar dayake so ba! aymana da sadeeq kullum suna like da waya,suna kashe junansu da kalaman love sosai ba kadan ba! wanda kuma dik randa su sadeeq sukazo sai an dan rage zafi wanda suka gama gwanancewa a wannan fannin babu sauki sbd fitinannu ne baki dayansu a wajen😋 sannan kuma yakan kira salifa ma sosai sunayin waya,amma saidai fah babu wani batun soyayya na aure har yanxu sbd shima wallahi har yanxu kallon wannan kanwar tasa uwa daya uba daya yakan mata bata chanza zani ba! hakan kuma sam baima ammy dadi domin kuwa dama tasan za'a rina,tinda tasan yadda sadeeq ke masifaffen son aymana tin tana kankanuwarta bata mallaki komai da d'a namiji ke so ba a jikin ya mace! ballantana kuma yanxu data mallaki dik wasu qualities da dik wani lafiyayyen namiji ke so a gurin diya mace! tasan cewa salifa ma ba baya bace a wannan fannin! amma kuma saidai tasan dik da namijin dazaiga salifa da aymana ace masa ya zabi salifa tasan da kamar wuya! hakan yana damunta sosai amma kuma tana matikar kokari wajen ganin ta boye tata damuwar,sannan kuma takan daura ita salifan akan hanyoyi da dama da zata iya janyo hankalin yayan nata ya dube ta da idanun rahma!ga kuma tin daga lokacin ta fara gyaran yar tata cike da bai! inda a gefe daya kuma anty ce ke kula da su aymana,zainab da mimi ta hanyoyin daya kamata! domin kuwa tsaf ya iya abubuwa da dama wanda a da dinma sanadiyyar kishi da dai sauransu yasa bata janyo su a jiki ballantana kuma ta nuna masu daidai da kuma akasin haka! bugu da kari kuma dik mazajen nasu sun yarje masu kan shiga jami'a bayan aure,sbd ilmin mace na taka mahimmiyar rawa cikin al'umma kwarai da gaske! wanda wasu mutane da dama kanyi ma ilmin yaya mata kallon wani abu na daban da bai cancanta ba! sameer ma yanxu ya kammala jsce nasa inda idan an koma hutu makaranta nan da sati bakwai zai shiga matakin ss1! ita kuma rahma jjs2! naseer shima yanxu yana hada degree nasa na biyu a cikin jam'ar bayero university kano! a halin yanxu ma yana can abinsa,tsakaninsa da yan gidansu sai waya domin jin lafiyarsu! YAU ta kama ranar litinin ce! da misalin karfe hudu na yamma abba da baba ne suka dawo daga wurin aikinsu! a yanayin yadda suka dawo gida tabbas yau suna cikin tsananin farin ciki ne,ko da daga yanayin da suka shigo gida ya isa ya tabbatar masu da hakan! kowa gidan sa ya shiga, mimi da salifa ne zaune cikin parlon ammy suna kallo inda ammy kuma ke kitchen tana hada masu abincin dare! ammy dake ta cikin kitchen ne ta fito da murmushi akan fuskarta sbd jin muryar abba tanayi masa sannu da zuwa! shima ansa mata yayi ya mika mata babban laidar kayan masarufi daya shigo dashi cikin sakin fuska yace "ammyn su gashi nan wanke shi da kyau a yayyanka mani ki kawomin sbd ina so na sha a yanxu kamin magriba" dan darawa ammy tayi tace "haba abbansu! ai ko bakace a wanke maka su ba kasan dole a wanke ko??" girgiza kai kawai abba yayi batare da yayi magana ba ya shige parlon da sallamarsa! tare suka mike sunayi masa sannu da zuwa! ansa masu yayi fuska sake yana tsokalarsu da amare ya shige dakinsu daya kasance nasa da ammy! ammy ce ta kwala masu kira inda suka fita kusan lokaci daya suna ansa mata! sasu tayi su karasar mata da girkin ita kuma ta wanke fruit din da abba ya kawo ta yayyanka masa ta wuce zuwa dakinsu. (bari nayi nan su dan soye na wani lokacin🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️) aymana da zainab kam dama sun yaye zuwa gidan ammy tintini sbd kunyar ta da sukeji a matsayinta na wacce take a sirikarsu! ammy tayi ta faman yin biko amma sam sun ki yarda suna zuwar mata kamar baya,domin kuwa yanxu idan ka gansu a gidan sun tafi gaishe da ita ne,wanda kuma ana gama gaisuwar suke fecewa abinsu! suma sosai suka sake murjewa abinsu! saidan ramar da akeyi irin na amare dinnan! fatan jikinsu kuwa ta sake fitowa wato ainahin kalarsu sbd gyaran fatar da suke samu bana wasa bane! (yar uwa mai karatu,budurwa da matar aure idan kina so fatar jikinki yayi laushi! dik wasu kurajen dake jikinki irin na su fuska da dai sauran tarkace dinnan ki kullaci amfani da _lalle da manja_ kina hade su wuri daya ki chakuda su saiki mulke su a jikinki gaba daya hatta fuska idan ya rage saura irin minti ashirin zuwa talatin kiyi wanka!,bayan kinyi wanka saiki shafe jikinki da irin mai din da kike amfani zaki ga chanji da iznin ubagiji! domin kuwa koni oum mumtaz ina tabbatar maku da cewa ina amfani dashi kuma wallahi yanaman aiki! ammaa fa kar kiyi sau daya ko biyu kiga bai maki aiki ba kice oum mumtaz ta shimfida maki fyori😲😲😲 kawai ki kullaci yin hakan da yaddar Allah zaki ga chanji) zaune suke kan tabarma suna hirarsu sukaji sallamar baban nasu! anty ce ta karbi laidar hannun baba tanayi masa sannu da zuwa. suma sannu da zuwa sukayi masa hadi da gashesa! Bayan sallar isha'i dik suka tara iyalan nasu! inda suka shaida masu kan an masu promation zuwa ainahin ma'aikatar tasu acan cikin bauchi! wanda dama acan suke makiya ne kawai suka sako su a gaba har aka cillo su garin azare,kuma gashi yanxu cikin hukuncin allah da sukayi hakuri na tsawon lokacin gashi nan an maida su harma da samun karin girma! an kuma basu nan da watanni hudu zasu tattara kwamutsansu su koma! sosai kuwa suka cika da farin ciki irin nasarorin da suke samu acakin watannin nan cikin family nasu! wanda hakan yasa ranar sukayi kwanan farin ciki kwarai da gaske,idan suka tuna zasu tashi daga geto zuwa cikin birni! wanda hakan yasa na suka yanke hukuncin sama ma sameer da rahma makaranta acan bauchi din idan yaso bayan aure dik sai su tattara su koma abinsu! su musty ma da sukaji labari ba karamin farin ciki suka taya iyayen nasu ba! haka nan naseer ma! lokaci na gangarawa rayuwa na tafiya satuttuka na sauyawa zuwa watanni gashi ayau dinnan cikin wannan family din an tashi da shirye shiryen daurin auren yayansu bayan shagulgulan da suka rakashe sosai ba kadan ba! abba da baba sunyi kokari kwarai da gaske wajen gwangwaje yayan nasu da ingan tattun kayayyakin zamani kama daga daki har zuwa parlo! baba shi yayima aymana da zainab kayan daki,abba kuma yayi ma salifa da mimi! sosai amaren sukayi tsananin kyawu na ban mamaki! dik inda suka tashi sai sun bar maku tsaraban kamshi! lefe mai rai da lafiya angwayen suka charkwada ma matan nasu! wanda salim ma sosai family nasa suka taka nasu rawar gani! abin kam sai wanda ya gani wallahi! bangaren ammy da anty kuwa su suka taka rawar gani wajen ganin sun feshe yayan nasu da kayan kitchen na zamani! su haydar kuwa ko kunyar babu haka yake murjewa abinsa babu abinda ya dame sa dik tsiyar da abokansu ke masa kan shima yayi ya fiddo da tasa a rangada mashi aure! naseer ma yazo auren gidan nasu bayan ya dauki escuse a makaranta! su rahma da sameer kannen amare da ango kowa ka gani tasa fuskar washe take da farin ciki! Bayan sallar juma'a aka garzayo zuwa kofar gidan nasu,inda dubban jama'ah suka shaida daurin auren ZAINAB DA ANGONTA MUSTAPHA! AMINA (mimi) DA ANGONTA SALIMA AHMAD! akan sadaki naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba! fuskarsu musty uwa gonar auduga a wajen daurin auren sai gaisawa sukeyi da mutane,haka nan sadeeq ma ke cikin tsananin farin ciki sbd sanin da yayi cewa gobe iwar haka matansu na chan sun killace abinsu! *OUM MUMTAZ✍🏿* [11/24, 1:44 PM] oum mumtaz ce🤠: 💥💥 *AYMANA.....!*💥 _ROMANTIC STORY_                                *MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*       Wattpad@UMMIE2018. instagram@itz me real oum mumtaz G:MAIL@fatimafateh5@gmail.com facebook@oum mumtaz *FREE BOOK.* _LITTAFIN KYAUTA._ *DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️  _HOOOOHHH!!!🥱a gaskiya mutanen duniya da abinda dariya suke🤔🤔 keda kike karanta novel kina maijin nishadi kuma kina naiman abinda zai amfane ki amma har ki iya biyoni ta private kina cemin wani wai ban waye ba sbd bani saka abubuwan gayu cikin littafi na🥴🥴to abinda nake so ki sani daga ke harma wayanda ke tunanin hakan cikin zuciyarsu to ni ummi fatima dama can ba daga gidan masu hali na fito ba sai rufin asirin allah balle ace kuma dole nasan abubuwa irin na gidajen masu kudi tinda babu a house💁🏻‍♀️💁🏻‍♀️💁🏻‍♀️ ina fatan kin fahimceni malama🦻🏿 so dan haka a kiyaye_            *PAGE 35* ********** Wajajen sallar magriba aka hade amare dakuma angwaye a parlon abba,abokan arziki dakuma wasu daga cikin dangin anty harma dasu ammy,abba,baba da kuma anty sukayi masu nasiha dakuma sake nutsar dasu dangane da rayuwar daya shafi yanayin zaman takewa na aure! sosai suka sha kukansu a wannan ranar! da kyar aka banbare salifatu daga jikin ammynta sbd yadda ta kankameta! haka nan mimi ma ta rike anty dakyar aka samu aka fita dasu! wanda hakan kuwa sosai yasa aymana da zainab kukan rashin mahaifiyar da zasu rika suyi kukan rabuwa! daga gidansu salim aka aiko motocin da zasu kai mimi! zainab,aymana da salifa kuma aboka nan su ne suka bada motocin da za'akaisu! a cikin mota daya aka hada aymana da salifa tare da sadeeq,zainab da musty! suka kamo hanyar bauchi tare da rakiyan wasu daga cikin family nasu! wajajen karfe tara saura sukayi ma garin bauchi dirar nakiya! inda aka wuce da ko waccen su muhallin mijinta! zainab dasu aymana unguwa daya ne,dan haka tawagar yan tafiyansu ma daya! banda masha allah babu abinda mutane da dama kan fada sbd tsari dakuma haduwar da gidajen nasu yayi! ranar kwanan kuka dakuma kewar iyayen nasu dakuma garin da suka taso cikinta sukayi bana wasa ba! washe gari order na abinci akayi masu daga restaurant mai kyau sukayi karya har zuwa lunch dashi,sai bayan wuraren sallar la'asar kamin sukayi masu sallama suka kamo hanyar azare! sosai aymana ke kuka fiye da tunanin mai karatu a wannan ranar sbd tunanin iyayenta daya tsaya mata a rai! salifa kukan kewar ammynta takeyi dakuma yan gidansu! haka nan suka hade kansu a parlo suna ta shekar kukansu kamar babu gobe! a cikin wannan yanayin sadeeq da wasu daga cikin friend nasa suka shigo gidan bayan sallar isha'i! ............ A gidan mimi kuwa tare da dangin mijinta dakuma wasu daga cikin na anty suka kwan mata! inda washe gari suma suka wuce aka barta da kewar gidansu dakuma yan uwanta dikda suna gari daya! salim shikam baiyi wani gayya ba na abokanai zuwa gidan sa sbd wayanda yake tunanin zasu iya rako sa su dinma da nasu amaren da zasuji dashi! a wannan ranar dai oganniya hajiya mimi akasan mainene auren,sbd yadda haji salim ya fanshe sadakinsa! ya murjeta iya son ransa,an ajiye batun tausayi a gefe saidai mu masu fatan Allah ya basu zaman lafiya mai dorewa har abada👏🏼 .........Haka nan gidan zainab kuwa musty daya tashi zuwa gidan amaryarsa mutum daya ya gayyata wato yarima sadeeq, wanda bayama kasar akayi daurin auren,saukarsa kenan wanka kawai yayo ya fito ko sallama bayyi da yan gidan nasu ba,sbd alkawarin da yayi ma musty kan insha allahu zai hallacci zuwa rakiya! sosai yaji ya yaba da gidan yayan nasa kuma abokin karatun,harma yaji dama ace shine yayi aurensa yanxu😲 amma kuma shi sam ajendar aurensa ba nan kusa bane,yafi son sai irin nan da 6 yrs dinnan a gaba! addu'oi sukayi kamin nan ya masu sallama kan insha allahu zai dawo bayan kwana biyu idan ya huta,musty ya raka sa inda ya kulle kofar gidansa yana doko man harara🙄 nikuwa nace allah ya tashe mu lafiya💁🏻‍♀️💁🏻‍♀️💁🏻‍♀️ .........Bayan an masu yar nasiha sannan sukayi masu sallama sadeeq ya rakasu zuwa bakin kofa kamin ya rufe kofarsa ya dawo cikin parlon,inda ya tadda su zaune kan kujera 1 seater kamar zasu shige cikin junansu irin syden dinnan! sosai suka bama sadeeq dariya,amma da shike yanxun lokaci ne mafi mahimmanci a gare su baki daya sai ya karasa inda suke fuskarsa na fidda annuri irin na sabon ango dinnan yace "maza ku tashi ko waccen ku ta tashi tayo alwala" basu musa masa ba kuwa,amma abin dariya kuma shine wai sai suka shige dakin aymana mai makon ko waccensu ta shige dakinta hannunsu sarke dana junansu kamar irin wasu yara kananu dinnan🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️ girgiza kai kawai sadeeq yayi zuciyarsa fari kal kamar takadda yanajinsa a sama yau dinnan sam wallahi bazai daga masu kafa ba,dik wacce ta fado hannu saiya bata a salansa kwarai kuwa🤸‍♀️ shi kuma ya shige dakin sa ya cire manyan kayansa,inda yayo wankansa sannan ya dauro alwala ya fito zuwa gaban mirrow,saida ya mummulke jikinsa da daddadan mai dinsa sannan fesa body spray daga lokaci zuwa lokaci yakan saki murmushinsa mai karama kyakkyawar fuskarsa kyawu shi kadai! jallabiyarsa fara kal ya saka ya sake binta da lafiyayyen turare ya dakko dardumarsa manya dinnan ya fito! zaune ya tadda su zaune kan kujera wanda zuwa yanxu bar kuka saidai kuma alamu ya nuna yau din kamar dodo suke ganin hamma sadeeq din nasu! ko wacce a zuciyarta addu'a take kan allah yasa badaga ita za'a fara ba(nace me kenan aymana da salifa🦻🏿) shimfidawa yayi cikin yalwataccen parlo din dake ta faman tashin kamshi sannan ya shiga dakin salifa dake ta gefen dakinsa ta hannun hagu ya bude wadrop nata dakyar ya samu damar zakulo hijabai guda biyu! ya mika ma ko waccensu dai dai ya umarce su da su daura niyya ya tada kaffarar sallah sukabi bayansa! raka'a biyu sukayi,bayan sun idar ya kama kan ko waccensu yayi mata addu'ar neman tsari daga sharrin mutum da aljan! dakuma kade fitina a cikin zaman takewarsu! gargadi da kakkausar murya sadeeq yayi amfani dashi wajen nuna masu cewa shidin tsayayyen namiji ne da bazai dauki wani shirmen da zasuyi masa da sunan kishi ba m,daga yau har zuwa illa masha allah! wanda hakan kuwa sosai yay tasiri cikin zuciyarsu kwarai da gaske! salifa itace uwar gida,aymana itace amarya! aymana ta mutunta salita a matsayinta na wacce igiyar aurenta ya fara hawa kanta! sannan salifa ma ta mutunta aymana a matsayin na wacce ta girme mata a haife! wannan shine batun da sadeeq ke sake jadda da masu! ya raba masu kwana kuma bibbiyu idan ya kammala kwanaki biyar biyar din daya dibar masu na amarci! sosai jikinsu yayi sanyi! suka sake shiga taitayinsu! sbd sun san idan ma sukayi ma sadeeq misbehaved to sune a ciki ba kowa ba! kaza dakuma drinks din daya shigo dashi a wani babban laida na mall ya dakko! inda yasa su dakko plates da cups! sunci abinsu basu kwari kansu ba irin na wasu sauran amaren sbd yanayin shakuwar dake tsakaninsu! bayan sun gama komai suka tattare wurin tare inda ko waccen su tayi cirko cirko! kallon su yayi ya kamo hannun aymana bayan ya zaunar da salifa akan kujera! har dakinta yakaita saida ya tabbatar da cewa ta kwanta kamin ya lullubeta da lallausar bargonta kasancewar lokacin sanyi ne! sumba mai kyau ya bata a goshinta kamin ya tofa mata addu'oi ya fice daga dakin kirif ya rufe kofar! jin karar rufe kofar dakin da yayi ne yasa aymana sauke nannauyar ajiyar zuciya tana jin zuciyarta kamar zata faso kirjinta ta fado! bata san dalili ba,bata san ya akayi ba,saiji tayi kawai wasu hawaye masu dumin gaske na sakkowa daga cikin idanunta! Sadeeq kuwa bayan ya fito ya tadda salifa ta buga uban tagumi! bataji shigowarsa ba saiji tayi anyi sama da ita kamar wata jinjira! baki zata fara masa amma yaki bata damar hakan! bai direta a ko ina ba sai kan kan sallayar dake shimfide cikin dakin daya shimfida ta tin shigowarsa ta farko! sallah suka sakeyi raka'ah hudu! bayan sun idar kuma oga sadeeq daya ce salifa kanwarsa ce uwa daya uba daya sai gashi nan yabi wata jihar ta daban🙆🏻‍♀️🥴. Washe gari kam sosai hajiya salifa aka sha gashi,wanda tasha albarka a hannun yayan nata da suka riga suka zamtoh abu daya! fuskar nan dik ta kukkumbura gwanin tausayi,hamma sadeeq kuwa allah ne kadai yasan kalar farin cikin daya tsinci kansa a ciki daren jiya dinnan! albarka kuwa tasha sa a hannunsa yafi cikin kwando😚 dikda aymana kanjin wani yanayi maras dadi dangane da yar uwar tata amma haka nan ta danne cikin zuciyarta,kasancewarta mace mai kishi akan abinda take so amma dai ba irin na hauka dinnan ba! normal kishi da akasan ko wacce diya mace da allah ya halitta! sadeq dik yana lura da yanayinta amma kuma bai bata fuskar da zata kawo ma zaman nasu targanda ba kamar yadda wasu mazan ke daure ma karya gindi😕a haka nan aka shafe kwanaki biyar dinnan cas wanda zuwa lokacin zuciya da kuma gangar jikin salifa ta gama sabawa da yanayin yayan nata dakuma soyayyarsa ta musamman a cikin zuciyarta! domin kuwa sadeeq ya cancanci a so shi ta ko wacce kofa sbd iya zama da mutane ta hanyar tsafta tacciyar ilmin addini da kuma na boko abin kam sai son barka! kuma a cikin wayannan kwanakin sosai yake kwatan ta adalci a tsakaninsu babu tauye ma daya! wanda ya hana su yin girki har sai bayan sun gama kwanaki goma cif na amarcinsu! Ayau itace ranar da sadeeq keta faman tsumulmularta na tsawon shekaru daya kwashe cikin koginta! fuskarsa tayi kuf kuf da ita! sai fidda yalkin sabbin ango yake abinsa! Ai kuwa itama salifa a lokacin da sadeeq ke mata sallama da zai wuce dakin aymana sosai taji wani irin kibiya mai tsinin gaske ya caki kwahon zuciyarta! kai jama'ah kishi bala'i ne wallahi🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️ sosai sadeeq yaji tausayinta,amma kuma sai ya kauda sa gefe sbd gudun shiga hakkin daya allah ya kamsa da wannan laifin! saida ya lallaba ta ya tabbatar data kwanta sannan ya wuce zuwa dakin aymana! kwance ya tadda ita ta dukunkunu cikin bargonta kamar kyanwa tana baccinta hankali kwance! ji tayi kamar ana yawo da ita a sararin samaniya! wanda hakan yayi sanadiyar farkawarta dga daddadan baccinra data farayi bada jimawa! idanunsu ne ya sarke cikin na junansu! sosai suka kura ma juna idanu kamar wayanda yaune farkon haduwarsu! hmmmmm🥱 salla sukayi suma raka'ah hudu kamar yadda yayi da salifa! inda ya bata fresh milk tasha shima yasha abinsa! inda daga nan kuwa sadeeq yayi mani kitufo da kafa zuwa kofar daki ya danna ma kofarsu key ta ciki🥴🥴🥴 wannan dare ya zamana dare biyu mafi mahimmanci da kuma kafa tarihi cikin zuciyar hamma sadeeq! babu abinda zai iya saka ma matayen nasa guda biyu dangane da kyauta mafi tsoka da sukayi masa face mallaka masu zuciyarsa dakuma gangar jikinsa na har abada! lalle kam ya yadda mata ma ni'imace ga rayuwar yaya maza kamar yadda suma mazan suka kasan rahma ga yaya mata! sosai ya gasa abarsa yana ta faman lallabata sbd shi kansa yasan ya gurjeta ba tare da tausayawa ba,kamar yadda yayi ma salifa! basu kwanta da najasa a jikinsu ba sam,saida suka tsaftace jikinsu kamin suka kwanta bacci! basu wani jima da kwanciya ba aka kira sallar asubahi amma basu ji ba,sbd baccin da basuyi ba a wannan daren! sai wuraren bakwai da wani abu sadeeq ya samu damar farkawa,inda idanunsa suka sauka kan agogo! ganin yadda lokaci yaja ne sosai yasa shi mikewa a gaggauce ya dauro alwala ya data kabbara! bacin ya idar ne yayi addu'oinsa,sannan ya sabi aymana dake ta faman sharara baccinta,fuskar nan tayi jazur da ita abinka ga farin mutum! domin kuwa ta wujijjigu a hannun sadeeq bana wasa ba, cikin baccin nata ta jiyo ta cikin ruwa mai dumi! nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,kamin ta bude kumburarrun idanunta da suka jaa sosai ta sauke su cikin na sadeeq da shima ke kallon fuskar tata cike da tsantsar soyayyarta! sosai suke kallon junansu! wanda aymana taji tamkar yanxu ne abinda ya faru daren jiya,idanunta ne suka fara tara ruwan hawaye bayan ta kauda kanta daga kallon barayin da sadeeq yake! tausayinta yaji ya sake kamasa hadi da zazzafar kaunar daya ke mata tin tana kankanuwarta! haka nan dai ya daure yayi mata wankan sannan ya nadeta da towel! bayan tayi alwala ya sake fito da ita daga bandakin,ya dakko mata wata doguwar rigarta tare da hijjap bayan ya sa mata ya daura ta akan sallaya! bayan ta idar da salla dinne ya sake daukarta zuwa kan lafiyayyen gadon nasu shima ya haye! runguma kyakkyawa ya bata yana sakin ajiyar zuciya! mutsu mustun kwace kanta aymana keyi cike da shakkar abinda sadeeq din kan iya sake yi mata kamar na jiya,amma yaki bata damar hakan,saima rungumeta da yayi sosai a jikinsa yana fada mata dadadan kalamai masu gardi da taushi cikin kunnuwanta! da irin matsayin da take da shi cikin zuciyarsa! wanda hakan kuwa sosai yayi tasiri cikin zuciyarta! harma bata san ta bada kai bori ya hau ba saida taji ta a ruwa tsundum ta sakar masa kuka🤤🤤 bayan sati biyu da yin auren nasu! wanda zuwa lokacin sosai ko waccen su ta saba da halin jarabatu irin na sadeeq sbd sam shi kam bai daga ma ko waccen su kafa idan ranarta ya zagayo! tin sunayin korafin hakan a munafurce! har suma suka zamtoh yan hannu! kunsan ance zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai💁🏻‍♀️. haka nan gidajen mimi da zainab ma sosai suke more amarcinsu da angwayensu babu kakkautawa! wanda zan iya cewa ma har sunfi su aymana morewa tinda basa sharing😛 sannan a gefe daya kuma sadeeq,musty da haydar sun hada hannu wajen gyara gidan su baba dake cikin bauchi din! wanda dama tuntuni gidan a kulle yake sbd tarewar da su abban zasuyi cikin satinnan! an zuba masu komai na more rayuwa inda komai sabo ne a gidan! yau aka kawo kayan gida a babbar mota! inda sadeeq da haydar ke tsaye akan komai wanda hakan yasa sam basu samu damar zama ba a yan kwanakinnan! an ajiye koma a mahallin daya dace gida yayi kyau! inda musty kuma washe gari da sassafe yayima garin bauchi tsinke a wata motar kirar high lander daya karba na wani abokin aikin su aro! inda su ammy suka sake yin sallama da wasu daga cikin yan unguwa da akayi mutunci harma da wanda ba'ayi ba suka kamo hanya tare da su abba baki dayansu cike da kewar azaren kanta da sukayi zama na dan lokaci a cikinta! wuraren sallar azahar suka iso! inda basu zame ko ina ba sai gidan su! sosai suma suka yaba da gidan ta yadda yaran nasu sukayi namijin kokari wajen ganin sun gyara masu shi kamar daga ingila! sosai su ammy suka cika da tsananin farin ciki sbd tadda yaran

Chapter 12 of 14