BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 3*
Saidia suka shafe wata daya cur a damaturu...wanda alokacin sun fawwalawa alllah lamuransu baki daya kuma suna fatan allah ya sakama iyayensu yakuma gafarta masu duniya da lahira da al ummar musulmai baki daya!
inda suka shaida ma gwamnati akan suna so sukoma makaranta sbd suna shekarar su ta karshe,
babu musu aka amince masu da tafiyarsu!!
amma kuma zasubar kannensu aci gaba da kula dasu anan...aykuwa fir sukaki amincewa da hakan domin koh basuga dalilin dazaisa subar kannen dasuka rage masu a duniya ba cikin yobe ba, sukuma suna wata uwa duniyar daban,,
anyi anyi dasu amma sun kafe kan lallai sai sun tafi dasu,dan haka aka yarje masu!!
anyi masu kyauta ta musamman sannan kuma an biyama masu kudin dazasu biya kudin makarantarsu har zuwa kammalawa tunda dama sauran masu 1yr,
driver ne daga gidan gwanlmnati yakaisu har garin bauchi,anguwa na dai dai talaka suka fara kamawa mai daki biyu sai bayi kwara daya dakuma madafarsu sai karamar tsakar gida...
kayan amfanin da jaleela da kanwarta hauwa zasu bukata dakuma kayan abinci da duk abubuwan daya kamata a cikin gida...
akwai wata mata a makwafciyar gidansu wanda har tsufa yafara kamata
ganin datayi cewa babu mace a gidan duk yarane hakan yasa ta tunkaresu akan inda iyayensu suke!?
ta tausaya masu jin labarin dasuka bata sannan kuma ta basu shawara akan maizai hana susa su jaleela ma a makaranta da islamiyya idan da hali?
aykuwa jaleela ma tace batasan zance ba sbd bazata so tayi boko ba yanda ake cewa yan iska ne keyi saidai asata a islamiyya...basu mata tilas ba sbd sunsan idan sunce lallai sai tayi toh bazatayi karatun ba kamar yadda yakamata!!
sun koma makarantarsu jaleela na zuwa islamiyya tare da kanwarta kuma sun maida hankali sosai a makarantar islamiyyar...!
2yrs letter
abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kammala karatunsu yusuf...
soyayya ta kullu mai karfi tsakanin abdallah da jaleela...
saukar da jaleela tayi ...
ga kuma samun ayki dasukayi karkashin gwamnatin jihar bauchi a ministry of works...
ansa hauwa a makaranta dai dai na rufin asirin alllah...
ga kuma shakuwarsu data kara kaimi tsakaninsu da inna nafeesa...
ayki sukeyi tukuru a wajen aykinsu ga kuma shagon saida kaya na atamfofi,shadduna da dai sauransu dasuka budema kansu“”
yanzu ma baki dayansu suna tare da inna nafee suna hira a gidanta wacce suke ce mata mama sbd kamar mahaifiyarsu dasuka rasa suke kallonta...
ananne abdallah suka naimi alfarma akan tayiwa limamin anguwarsu magana akan suna so adaura aurensa da jaleela zuwa karshen watannan!!
mama dogon numfashi taja tace,
""yanzu kai audu wato abdallah...kun tanaji gidan zamane da kake zancan aure?
koh ko akace maku aure wasan yarane ?
idan baku sani ba baki dayanku ma ku saurareni da kyau!
kun ganku nan babu wanda zan bari yayi aure cikinku sai kun mallaki gidan kanku sannan...
dafatan kunji ni dai koh...?""
"munji mama"...fadar abdallah yana ta jin haushi shikam yusuf koh a kwalarsa domin koh har yanzu bashi da wanda yakeso,saima dariyar ciki ciki dayake ma abdallah ta tsokana...
jaleela dake labe kamar tayi kuka amma babu dama tunda wannan mgnr da mama tayi gata tamasu dukkansu!
bangare guda hauwa na halartar makarantarta da islamiyya gakuma yayar na taimaka mata ta fannin islamiyya!
ita kuma kome takoyo a makaranta saita koyawa yayarta,hakanne yasaka jaleela kome ka bukaci ta rubuta maka daidai gwargwado ta iya!
suna matukar kaunar junansu...hauwa kam a tunaninta inna nafee mamarsu ce tunda bata da wayo tabar gd balle tasan maike tafiya!
fili babba abdallah yasaya batare da sanin yusuf ba,ko kuma su mama...cikin kudinda ardo yabasu,tunda yazama mallakinsu!
yasamu masu ayki inda aka dankara masu gininsu hadadde sosai,
get na gidan ma dayane
saidai kowa da part nasa, sai kuma karamin part na inna nafee a tsakiyar part nasu daidai misali mai kyau dashi,
gida kam yayi kyau gwanin sha awa cikin 5month aka kammala
yazuba masu komai cikin gidan wanda ko yau zasu iya tarewa saidai kawai a kwaso kayan sawa.
ranar kamar ya taka rawa dan murna zai mallaki rabin ransa
yasaya masu mota kirar 206 bakake ya ajiye a gidan a parking space!
ranar da dare bayan sun gama cin abinci...yace"" mama dama dan allah gobe idan kinada lokaci zan kaiki wani guri kedasu broo dasu jaleela?""
"toh shikkenan alllah yakaimu amadu" yace "amin".
yusuf kam yanda yaga dan uwansa nata fara ah ne yasa shi yake allah allah gobe tayi domin yaga abinda dan uwannasa ke murna, yataya dan uwansa farin ciki!!
washe gari
wajen karfe 10 na safe sun kammala shirinsu...taxi suka samu suka dunguma zuwa unguwar new gra...
har kofar gidan aka ajiyesu...su inna nafee kam ta tsaya ganin iko allah,
sai gani sukayi ya bude masu gidan
cikin jindadi yace masu su shiga
shikam yusuf ya sake baki yana kallon ikon allah domin koh ya fahimci abinda dan uwannasa ya kewa murna yanxu.....
cikin gidan suka kutsa inda suka nufi part daya daga cikin wayanda suka kasance iri daya
saida yanuna masu komai na part din sannan suka shiga part na mamansu aykuwa sai koda gidan suke tayi!
murna kamar suyi me daya shaida masu akan nanne sabon gidansu !!
yusuf yadauki daya sannan shima yadau daya sai kuma na inna wanda baikai nasu girma ba...
tana tasa masu albarka,jaleela ma tayi murna hakama hauwa...
bayan sun koma gida suka yanke akan sati mai zuwa zasu tare amma kamin nan za'ah daura auransa da masoyiyarsa idan antashi kai amarya sai kawai a wuce chan gidan da ita...
inna yanzu kam tadawo kan yusuf kan lallai shima ya fidda mata idan ba haka ba kuma ita tanemo masa...
baiyi musu ba yace ya bata wuka da nama...
aykuwa tayi matukar farin cikin hakan ta naima masa auren wata jikar kawarta mai suna hafsat
ba laifi tana da hankali amma akwai masifa...
saidai idan a gabansu take ko yatsa kasa mata a baki bazatayi mgn ban
yace basai anyi mata komai ba tunda already komai ya kammala a gidan...
hakan ko akayi bayan 2weeks aka daura masu aure da amarensu...dangin inna nafee sune suka zamana a matsayin danginsu yusuf...!
an mika amare gidansu, inna nafee ta tare a nata part din tare da hauwa domin koh tana matukar jida yarinyar sosai...!
Zaman jaleela da hafsat a matsayin facaloli kam saidai ace alhmdlh...babu abinda yake hadasu na wani tashin tashina sabida kowacce ta kama kanta...
saidai matsala daya da suke fuskanta acikin gida akan hauwa ne...domin koh hafsat takafa mata kahon zuga na babu gaira babu dalili...
hakanne yasa kwata kwata yanxu ta daina shiri da inna nafee, domin ko mama duk wanda yace zai taba mata hauwan ta basa zama inuwa daya sam!
yusuf da abdallah dai basu san ma mai ke tafiya a cikin gidan ba, sannan tsakanin matan babu wanda ya taba tunkararsu da zancen...
A kusan lokaci daya suka samu ciki,bayan 9month hafsat ta haifo danta namiji wanda a gida ma ta haihu sbd haihuwan yazo mata da saukii...
bayan sati uku da haihuwar hafsat nakuda ta tasoma jaleela wanda tasha wahala matuka amma kuma shuru haihuwar shuru,tun suna t'sammani abinda sauki sai suka ga akasin haka...
babu shiri aka garzaya hospital da ita, aka wuce labour room da ita...
suna tsaye har mata uku daga baya sun sauka amma itakam shuru, saidaga baya allah yabata ikon haihuwa dakanta,
cikin ikon allah sai gata da twins nata jazur dasu, kyawawa dasu son kowa kin wanda yarasa...sunyi matukar farin ciki sosai ba kadan ba...
ranar suna hassan yaci suna mustapha...hussaini yaci suna abubakar sadeeq
bayan two years hafsat ta kara haifo danta namiji inda yaci suna nasir,
alokacin hauwa nada shekara 11
wanda har mmkin girmanta suke kamar irin wacce takai irin 13yrs dinnan...!!
tana da 16yrs takammala secondary school...kuma a lokacinne yusuf ya ballo da magana akan yanason auren hauwan...wanda hakan ba karamin gungumin tashin hankali ya haifar masu ba, domin koh hafsat ta tada masu bori kan basu isaba...dama ita tun yarinyar na karama takejin haushinta,ashe aure mata miji zatayi,su zauna a matsayin kishiyoyi...!!
lallashinta yayi sosai, domin kou yasan dole zataji babu dadi tunda babu macen dazata so ace an mata kishiya...
amma kuma kamar kara zugata akeyi tana kara botsarewa tana masa bori...ganin da yayi bazataji ta lallama ba yayi mata jan ido...
dolenta badan ta so ba ta hakura,amma kuma wani kalar tsanar hauwa ne yashigeta sosai ba kadan ba wanda kou yau akace mata ga wuka ta kasheta tana ganin zata iya aikatawa...
anyi auransu inda ta tare a part na yusuf
zaman doya da manja akeyi gidan kwata kwata babu sauki ta fannin hafsat...saukin abinma hauwa mai sanyi ce inba haka ba kam da gidan yazama gidan yan caskale...
kusan a tare hafsat da hauwa suka samu ciki...
gasu sadeeq,musty da aliyu(dan hafsat na farko) suna makaranta...primary one going to two...
cikin week daya suka sauka duk suka samu yaya mata...yarinyar hafsat sunanta amina sai kuma yarinyar hauwa taci suba zainab
alokacinne kuma makiya suka sako su yusuf da abdallah a gaba saboda tsayuwarsu kan gaskiyar su da rashin son zalincin na kasa dasu a wajen aykinsu“”
kasancewar rayuwar yanxu kowa kansa yasani baya duba na kasa dashi, har akayi munafurcin da kulla kulla akayi aka masu transper na wajen zuwa karamar hukumar bauchin wato azare!!!
da farko suna zuwa wajen aikinsu ranar monday zuwa friday sudawo suyi weekend da iyalansu...!! inna nafee takawo shawarar mai zai hana sunaimi gida kawai acan garin yaso saisu koma baki daya sabida sha'anin hanya yau da gobe???
suna matukar son matar nan sosai kuma basa jayayya akan duk abinda tasasu sabida sunsan baxata taba kawo masu shawara mara kyau ba ...
dan haka basuja tsawon lokaci ba suka sayi fili acan azare irin middle level area dinnan,sunyi gininsu dai dai na rufin asiri cikin watanni takwas suka tarkato kwanutsansu,sukayima garin azare tsinke harda inna nafee...
Dawowarsu bada jimawa ba ciki ya bayyana jikin hauwa,ai kuwa inna nafee taji tana mugun son abin cikin dukda batasan mai za a haifa ba...tace ma baba tayi kamu indai macece mai sunarta take so asaka mata...!!
A lokacin da cikinta yashiga watan haihuwa ranar wataa asabar tun cikin dare takejin ciwon baya amma saita daure wai karta tadawa dasu baba hankali...shima kuma bai lura da yanayin da take ciki ba ko kadan...!!
wajen karfe hudu baba yafito domin zuwa masallaci da yar tocilarsa kamar kyaftawar ido sai kuma yakoma kaman wanda yayi mantuwa a hanzarce...
yana shiga faya ta fashe ma hauwa saigashi ta sauka kamin ta haifo wata
baba kamar yayi yaya dan murna...shima yasamu twins take ta bugama inna nafee ita tafito ta kinsa yaran da uwarsu...
washe gari da safe akayi ta murnar haihuwar yan biyu
wajen karfe 10 na safe dayar yarinyar takoma ga mahaliccinta...
hauwa kam tayi kuka saboda soyayyar yarinyar har ciikin zcyrta...
sai kuma duk soyayyar tasu takoma kan dayar wanda har sadeeq da baison hayaniya yarinyar tashiga ransa sosai ba kadan ba...
ranar suna ta zagayo inda yarinya taci sunan inna nafee wato NAFEESAT sai aka mata alkunya da "Aymana"...mutane dayawa kan cewa tana kama da sadeeq ta wani fannin...
3month da haihuwarta ammi(jaleela ) tasamu cigar ciki wanda akayi ta murna sosai ba kadan ba sbd yanda ta dade bata haihu ba...
9month ta haifo ya mace itama murna kamar ta kashe sadeeq anan...yarinya taci suna saleefa
haka zai dauki salifa da aymana yayi tamasu wasa...wata rana kam har hana daukansu yakeyi
more especially mimi idan ta daukesu sai ta dinga muntsilinsu shikam idan yakamata sai ya mammaketa kamar ba gobe hakanne yasa taji ta tsane aymana da saleefa wanda kiyayyar data ke masu ta wuce gaban misali misali...
wani abun mamaki anty tun aymana na karama ta dauki karan tsana na ban mamaki ta daura akan karamar yarinyar da bataji bata gani ba!!
shekerar aymana 2,zainab da mimi 4,nasir 10,salifa 1 sai sadeeq,musty da haidar suna 12
anty kuma nada tsohon ciki haihuwa yau koh gobe...
alokacinne akayima goggo rasuwa a garin bauchi ta tarkata ta tafi ta'aziya, ashe dai babu rabon kara ganawa tsakaninta dasu yusuf ,wanda akan hanyarsu ta dawowa daga bacci sukayi accident inna nafee ta tafi,tabarsu da kewarta...!
koda akaje asibiti na sun shaida masu akan tariga data cika
wayar baba (yusuf) aka kira ta karamar waya, da aka tsinci goggo da ita...yana tare da hauwa alokacin,,,,jin wannan hargitsatsen labarin dayafaru ne yasa labour ya taso mata gadan gadan ba tare da ta shirya ba,babu bata lokaci ba aka wuce asibiti da ita abdallah kuma yawuce A AND E domin cike files na karbo gawar goggonsu...
hauwa kam tasha wahala kamin ta haifi danta namiji itama take a wurin tace ga garinku nan nabar maku shi!!!
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/20, 7:14 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u
💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 4*
Ga rasuwar inna nafee,gakuma rasuwar hauwa, wanda haka ba karamin daga masu hankali yayi sosai ba kadan ba...
wanda akayi zaman mutunci dasu ma mutuwar tashigesu, ballanta suda inna nafee ta zauna dasu cikin amana kamar wanda itace tahaife su...wanda sun tabbatar ko iyayensu iyakaci!!
mutane da dama basusan cewa inna nafee ba mahaifiyar su bace sai a mutuwarta wanda yan unguwa suka cika da ajabi dakuma fatan dacewa har ranar lahira...!!
itakam saidai muce alhmdlh tasamu kyakkyawan karshe wanda akewa duk wani musulmi
fatan samun sa...!!
hakan take ga hauwa itama alhmdlh saidai muce alllah yajikansu da rahma,sbd itama ba mace bace mai hayaniya ba...
ranar sadakan bakwai aka radawa yaro suna sameer sannan kuma ammy(jaleela) ce ke shayar
da yaron...kuma alhmdlh zamuce sbd yaro yayi bulbul dashi sai muce allah ya raya sa!!
bangaren hafsat kam tunda hauwa ta rasu ta tsiro da sabuwar muguntar datake ganawa zainab da aymana dasuka zamto abin tausayi...bama kamar aymana wanda ita takance ai baba yafi fifitata akan yarta mimi...!!
nikam nace ANYA KUWA....??
sameer nada 2yrs hafsat takara haifo yarinyarta mace taci suna rahma
rayuwa kenan akace idan da ranka kasha kallo...aymana da zainab sun taso cikin wata iriyar rayuwa da ake tauye masu hakkinsu a wannan gida kamar ba gidan ubansu ba...zainab nada seven yrs babu kalar aykin dabata iyaba...itakam aymana bawai aykin ake sata ba...
duka,zagi,hantara shine take fama,dashi a wannan gidan...
bangare guda kuma wani kalar shakuwa ce ke tsakanin salifa da aymana na ban mamaki, wasuma kan dauka yan biyu ne...sbd salifa akoi garin jiki...itama aymana babu laifi amma bata da girman jiki sosai...!
mimi kam babu wayanda ta tsana a rayuwarta kamar ta bude ido taga aymana acikin gidannnan wanda itakanta batasan mainene dalilin hakan ba, tunda akoi yarinta akanta!
sannan kuma akoi zigin anty tunda ita takoyama yayanta yanda zasu tsani yan uwansu,
alokacinda ummi zata shiga primary one salifa zata tafi nursery 3 amma fir taki tace lallai saisun tafi class daya...hakan kou akayi tunda dama tana da kokari babu laifi ...!
tare suka shiga primary one seat nasu ma daya neh...saidai salifa akoi dan banzan surutu kamar me...ummi kuma ta kasance miskalar gaske wanda bazakji bakinta ba sai tana tare da salifa kou kuma hamma sadeeq kamar wata sarauniya...
hamma sadeeq da hamma musty yan biyu masu matukar kaunar junansu sosai ba kadan ba...sana'arsu kuma shine sadeeq na jan napep,saikuma musty yana dinki tare da haidar...
naseer kam dan zauna gari banza neh dama,shikam dama akan mugun halin uwarsa ya kwaso...!!
Ahalin yanzu suma sun shiga ss 3 tare da haidar kuma alhmdlh duk suna kokarii...
saikuma naseer yanzu ne yake ss 1 saidai shi yataso cikin sangartar da uwarsa ta daurasa akai tun har zugan hayaki yakeyi amma kuma babu wanda yasani sai ita...kuma takasa daukar kwa'kwa'ran mataki akai,kuma bataa sanar da baba ba ballanta shi yayi maganin matsalar...
saikuma mimi da zainab suma dai toh gashinan saida muce ala san barka,zamansu...
back to story
washe gari kamar kullum haka suka kammala shirinsu domin tafiya makaranta...suna dakin baba sadeeq da musty sai salifa suka shigo domin gaishe da baba...
cikin murmushi yake ansa gaysuwarsu...sbd shikam alllah yagani yadaura masa son yarannan bama kamar sadeeq,gashidai bawani babba ba amma kam akoi shi da cika da cika ido,ga halin dattako...
suna nan zaune saiga nasir ya banko dakin babu koh salllam
a tsayen dayake yagaishe da mahaifinsa babu ladabi kwata kwata a lamarinnasa, amma a haka uwarsa ke cewa wai danta kam nan gani nan barii dumamen mayya!!!
kallo daya musty yamasa yadauke kai sbd indai tashine ai da tuni ya mammasgesa...saidai akoi wanzuwar wanda yake matukar jin nauyi a matsayin mahaifinsa...kuma ya tabbata duk wanda yau aka taba dansa a gabansa sai yaji wani yanayi na rashin jin dadi koda kuwa nashi ne da laifin,saidai ya dauke kai yanuna komai ba komai ba sabida wasu dalilai da ake cewa KAKI NAKA DUNIYA TASO SHI......
muryar baba ne yadawo dashi cikin hayyacinsa...
""babana tunanin mai kakeyi neh haka kodai anyo mana sirikane take gara man dan nawa ? ""aikuwa duk suka soma masa dariya kasa kasa harda aymana daya kasance ita kam dariya bai dameta ba shikam duk kunya takamasa sai wani sunkuyar dakai yake kaman wanda yake gaban siriikinsa...
cikin jin nauyi sadeeq yace ""baba zamu wuce makaranta kar muyi latti...""
"to toh shikenan allah yamaku albarka sannan kumaida hankalinku kan abinda yakaiku karku biyewa kawayen banza ku rike kanku da amana sannan kuji tsoron alllah a duk inda kuke kusani koda bama kallonku allah yana kallon ku...""
kutashi kuje allah yabada sa'a...cikin sanyin jiki suka mike suka masa salllama
hadda uban fitsararru...
dasuka je wajen napep ne kuma sai nasir yadoshi hanyar tafiya inda zai sami abin hawa
sai kuma sadeeq yaji babu dadi kwata kwata""nasir zoka shiga mutafi daga yanxu kana jiranmu muna tafiya tare kaji kou?""
kallonsa kawai nasir yayi domin ko magana na fatar baki kwata~kwata bata hadasu da sadeeq har gwanda ma musty,
saboda shikam allah yagani kishin dan uwannasa yakeyi sosai ba kadan ba wanda yarasa dalilin faruwar hakan...
kamar kullum salifa na cinyar aymananta...sai kuma zainab sameer na cinyarta sai mimi uwayen bakin raii
sadeeq ke jan napep saikuma musty da nasir suke zaune a gefensa both dama da hagu...
aliyu kam dama badasu yake tafiya ba...bashi da matsala koh kadan tunda shima ba shiga shirgin gidannansu yakeyi ba...
haka fa rayuwar take tafiya cikin dadi da rashin dadiii saidai a godewa allah tunda komai kalar matsalarka a rayuwa saika hadu da wayanda nasu ya dame naka ya shanye...
gashi yanxu su musty sun kammala secondary school nasu kuma sunyi exam na schoolarship
and suna kyautata zaton samun nasara tunda dukkansu ba baya bane wajen ilmi...
sannan gasu salifa an shiga primary2
wanda tun daga yanxu tanajin kewar yan uwanta sosai ba kadan ba...
aymana kam gatanan kawai zamuce,tunda ni kaina bansan mai nene a zuciyarta ba...dukda ance labarin zuciya a tambayi fuska...
su zainab ma an shiga aji hudu
komai na tafiya yanda yakamata...
shikam sadeeq abinda yakeji allah ne kadai yasani saikuma zuciyarsa...
sbd yasan 8yrs ba wasa ba...kuma yayi alkawari muddin yasamu schoolarship shida nigeria sai wani ikon allah inbadai ya kammala karatunsa baki daya ta yadda bazai kara komawa wata k'asa wai da sunan karatu ba..!
*********Alhmdlh zamu ce komai na tafiya yanda yakamata inda a halin yanxu musty yasamu adminssion a kasar india zai karanci PHARMACY...
while sadeeq la london yasamu inda zai karanci GYNAECOLOGY...
haydar yasamu a australlia...ranar kam ba k'aramin farin ciki ne yasamesu ba da akace wai duk su ukun sun samu schoolarship zata d'auki nauyinsu harsu kammala karatunsu a kasashen ketare wanda babu wanda ya tab'a tunanin hakan cikin family nasu....!
saidai kuma zasu cika da kewar junansu matuk'a...! tunda koh tafiya zuwa wani waje d'aya bai tab'ayi ba,batare da dan uwansa ba,wanda dama hakan sam baya cikin t'sarinsu,ballantana ma ina zasuje...?? wa suka sani da zasuje wajensa ma...? tunda basu ma dangin...! amma sai gashi karatu zata nisanta tsakanin y'an uwa guda biyu masu matuk'ar k'aunar junansu da tun tasowarsu basu ma raba wajen kwanciya...!
A b'angare d'aya kuma hamma sadeeq ji yake kamar zai tafi yabar wani sashi ne na kusa dashi mai girma a nigeria...!
sbd shikam allah yanagani koda yana cikin farin ciki ne sai yanajinshi kamar bai cika full ba...!
ma'ana dai yanajin kamar yana buk'atar mutane sama da haka daya kamata ace tare suke tayasa murna ba iya kacinsu ba! wanda kuma way'annan mutanen sun kasance masu matuk'ar girma da daraja a tare dashi...!
*********Tun ana saura sati d'aya su tafi aymana tafara rama na babu gaira babu dalili wanda hakan ba k'aramin damun zuciyar baba yakeyi ba amma kuma shima yasan dole hakan tafaru...!
dama kuma aymana gatanan ne, bawani auki bane da ita na azo aganii...
anyi settling na komai daya kamata dangane dasu salifa dakuma aymana,nasir ne zai fara kaisu makaranta a napep tunda yanzu sunga dasauran hankalinsa ba kamar daba...!
*********Yauma kamar kullum sadeeq shine zai kaisu makaranta kamin lokacin tafiyarsu...!suna tafiya a napep salifa sai karad'inta takeyi tanama yayan nata surutunta kasancewarta yarinya mai d'an banzan surutu...! har suka isa uffan aymana batace ba wanda sadeeq ke ankare da hakan wanda yaji zuciyarsa sam babu dad'i...! bayan ya ajiye su a makarantar duk suka wuce class nasu amma sadeeq sai ya kasa tafiya kawai ya tsaya a bakin gate nasu yana tunane tunanen da baisan na minene ba...! har saida gate man yamasa magana kan mai yakeyi t'saye bai tafi ba...? yace akoi wacce yake jira ne...! hakan ne yasa baba ma gadi komawa bakin aikinsa!
*********Ana masu lesson amma kwata kwata hankalinta sam baya tare da uncle d'in nasu...! ji take muddin hamma yatafi toh kuwa tabbas babu wani dazatayi tutiya dashi a koh ina tace wannan jininta ne mai share mata hawayenta a duk lokacin da takowo kukanta,dikda k'arancin shekarunta wanda ita kanta batasan dalilin yin wannan tunanin da takeyi ba.....!! sannan kuma ga uban kewarsa daya mata katutu tun daga yanxu, sannan kuma muddin yatafi to kuwa akoi gagarumin abinda yake tunkarota wanda a cikin jinin jikinta takanjii......!
tana can tana dogon tunaninta da babu wanda zai bata ansa...!batama san malaminsu namata magana ba kwata~kwata wanda har saida yabuga desk na gabanta da d'an k'arfi kamin ta dawo hankalinta,shikam yana mamakin wane irin tunani yar kankanuwar yarinyar nan keyi har haka dazaisa tafice hayyacinta har ana magana bataji ba...?
firgigit ta dago kanta tana kallonsa da dara daran idanunta da kana ganinsu zaka fuskanci tsantsar damuwar datake cikinsu wanda har idanuwan nata sun canxa kala....!
"lfyr ki kuwa nafeesatu...? fadar wannan malamin cikin gurb'atacciyar hausarsa da ba ganewa akeyi sosai ba,kasancewarsa baye rabe...!
"uncle zanje na sha ruwa dan allah..." fadar aymana cikin muryarta dake rawa kaman zatayi kuka wanda tabawa malamin tausayi sosai ba kadan ba...!!
babu musu ya lamunce mata zata iya fita...salifa ma mik'ewa tayi da niyyar tabita amma malamin yanata fita babu yanda ta iya takoma tana zumbura baki tana mat'sar k'walla,tadamu matuk'a dayanda taga aymananta yaud'innan...!!
direct gate na fita daga makarantar ta dosa, kamar wacce aka ce tafita
tana fita kuma taga sadeeq bakin makarantar ya kifa kansa akan steary na napep din,wanda hakan yasa ta nufi wajensa...!
yaga lokacinda tafito amma kuma bai nuna yaganta ba,ita kuma shiga tayi cikin napep tasamu guri tazauna batare data kara kallonsa ba ta kifa kanta kan cinyata ...!
nikam nace yan miskilancin sun motsa kenan...
haka shima bai kalli inda take ba ballantana tasa ran zai kula taba,yatada napep nasa suka fita daga cikin makarantar amma dikda haka batayi magaba sanin da tayi cewa d'an uwan nata bazai tab'a cutar da ita ba...!!
gidan ammi ya t'sayar da napep nasa dukansu suka sauk'a yashige cikin gidan itama ta mara masa baya.
sai kallonsu kawai ammi tayi sun shigo mata gida babu sallama wanda hakan sam ba d'abi'arsu bace, da mamaki take ta binsu da kallo tunda itadae tasan bata taba ganin sunje makaranta sun dawo gida ba...
gashi kuma yau ta lura dukkansu yan miskilancin a kusa yake wanda bayau suka saba ganin hakan ba daga y'ay'an nasu...!
gefen ammi yaje ya zauna ya kwantar da kansa a kafadarta...itakuma aymana tana tsaye kou motsi batayi ba ta lumshe idanunta kamar wata babba!
saida ammi tagama kare musu kallon tsaf ta sauke ajiyar zuciya...domin kou tun bayau ba zuciyarta ke kitsa mata abubuwa da dama akan yarannan amma kuma tana wat'sarwa sbd ganin rashin k'wak'k'waran hujja a ganinta yarinta ne ke dawayniya dasu kawai...!
"inna ta matso kusa da amminki ki fad'amin abinda ke damunki kinji...?"
fadar ammi cikin kwantar da murya dakuma lallashi!
tahowa tayi a hankali kamar mai t'soron k'asa tana zauna a d'ayan gefen ammi suka sakata a t'sakiya, shikam yakafe da mayun idanunsa damutane sukance wai idanunsu ma kala daya ne...!
harma wasu kance suna kama kawai dan ita mace shikuma namiji neh...
sannan kuma ita yarinya ce idan ta girma kamannin nasu zaifi fitowa sosaii!
kwantar da kanta tayi kamar yanda yayi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 14