takeyi ranta idan yayi dubu sai yayi mummunar b'aci!! cikin lallami da kwantar dakai tace "haba autar ammi...! dan allah kiyi hak'uri karki fad'a masa wlhi nima bansan miyasa na canza ba wlhi,dan allah ki rufamin asiri wlhi zan daina kinji...?"haka nan dai ta kalallame salifa, t'saf kuwa ta kalaman suka sata sakin fuska tace "ai kema kinsa ba'ajin kanmu dake my sister,tinda kince kin daina ai shikkenan"
hiransu suka ci gaba dayi cikin raha kamar basu suka gama b'ab'atu ba! ammi kam na gefe tana mamakin yaran nata wato aymana da salifa,idan taji yadda suke zaro magana wlhi kamar wasu manyan y'an matan dasuka zama cikakku!
suna cikin hirar tasu adda mimi da adda zainab sai sameer ma da aka zamaa d'an saurayi su shigo gidan cikin sallama,nan suka baje kolinsu t'sakar gidan sunata hira ammi kuma ta shige kitchen domin d'aura sanwar dare...!
********* _K'ASAR LONDON_
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/20, 7:16 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u
💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 7*
*********Madaidaicin d'aki ne dake malale da wani lallausan kafet kalar milk mai rat'sin baki da fari da yayi matuk'ar tafiya da yanayin kayana na alfarma dake cikin d'akin...! saikuma mamallakin d'akin dake duk'unk'une cikin bargo mai t'sananin laushi da taushi dikdama dai bawani sanyi ne sosai cikin d'akin ba,kasancewar ac na d'akin a kashe yake...! ganin yadda yake ta vibrating cikin bargon ne ya tabbatar min da ba lafiya...!
t'sawon mintuna ashirin ya d'auka cikin wannan yanayin kamin yafara dawowa cikin hayyacinsa, a hankali ya daina rawar wannan jikin da yakeyi har yazoma ya daina baki d'aya...!
a hankali ya zuro da fararen hannunsa waje masu d'auke da dogayen yat'su farare tas ga wasu gashi dake kwance tun daga bakin k'umbar tasa har zuwa sangalalan hannunsa daya gama zurosa yaye bargon dayamini gatanga da ganinsa...!
gumi ne sharkaf ke zuba daga jikinsa kamar wanda yayi wanka da ruwa,bai kuma goge jikin nasa ba...!
fari ne tas kamar ka tab'a fatar jikinsa jini ya fito wanda hakan kuma ya k'ara samun k'arko ne daga lafiyayyar ac d'in dake cikin d'akin nasa!
boxes ne kawai a jikinsa a lokacin da ya bayyana daga cikin bargon,ga wani kwantaccen gashine mai shegen laushi dake kwance a jikinsa na asalin fulani,bugu da k'ari kuma ga zufan dayasa gashin k'ara lafewa dakyau!
fuskarsa dake cikin t'sananin damuwa na kalla dake shimfed'e da wani kwantaccen saje bak'i wuluk dashi sai uban shek'i yake ya kuma zagewa tattausan lab'b'ansa masu taushi dakuma laushi masu launin pink lips mai duhu!
hancinsa daidai misali ne shiba dogo ba kuma ba gajere ba,sannan kuma ba lukutin hanci ba kuma ba siriri ba wanda hakan ba k'aramin tafiya da yanayin t'sarin fuskarsa yayi...! a tak'aice dai kyakkyawa ne sosai ba kad'an ba...!
cike da damuwa ya mik'e t'saye wanda kuma yana da t'sayi daidai misali ba kalan dogaye har can din nan bane,sannan kuma yana da yanayin t'sarin halitta wanda emmata dayawa ke fatan samu ga mazajensu!
cike da kasaala ya mik'e ya shiga bedroom dake cikin d'akin,kimanin minti ashirin yafito yana t'sane jikinsa,wanda hakan ya tabbatarmin da wanka yayi oyo...!
saida yagama t'sane ruwan jikinsa t'saf,kamin ya dakko boxers yasaka tare da feshe jikinsa da daddad'an turare wajen kala hutu,turaren yabada wani kalar kamshi da kai t'saye bazaka iya tantance tak'amammen kalar turaren ba...!
jallabiya fari tas ya ciro daga cikin sif d'in dake dak'in ya zura a jikinsa,inda ya fito hak kamar balaben saudiya...! zama yayi cikin wani lunt'sumemen kujera daya kasance shi kad'ae ne cikin d'akin mai t'sari dakuma fasali...!
janyo k'aramar center table d'in dake wajen yayi wanda ke shake da abubuwa na mot'sa baki yafara cinsu cikin nat'suwa,saida yagama cin abinsa kamin ya d'akko wayarsa dake bedside drawer k'irar iphone 12 ya lalumo wani number da akayi saving da _"ammi na"_ ...!
har wayan yagama ringing ba'a d'auka ba...!baiyi k'asa a gwiwa ba wajen sake lat'so number d'in wanda cikin sa'a kuwa yaji an d'auka...!
********* _ *NIGERIA*
hirarsu sukeyi baki d'ayansu hatta mimi da yanxu itama ba kasafai take masu t'siyar tata ba sai abin nasu ya mot'sa...! ammi kuma na kitchen tana tuka masu tuwon semo...!
sameer ne yaji kamar k'aran wayar ammi amma bai tashi ba har wayar ta t'sinke,kuma babu wanda yaji k'arar wayan kaf cikin su,sake jin wani ringing d'inne ya tabbatar masa da wayr ammi d'ince...! ba tare da yama kowa magana ba ya fad'a d'akin ammi ya dakko wayar yayi recieving na k'iran sbd fahimtar wanda ya k'ira tinda yaga ansa *babana* ...!
"hamma sadeeq ina wuni" fad'ar sameer cikin t'sananin farin ciki ...!
ta b'angaren sadeeq ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauk'e kamin ya ansa a kasalance yace "lafiya qalaou d'an gidan amminsa...! ya karatu...?"
"lafiya qlaou hamma sadeeq,yaushe zaka dawo...?"sameer ya tambaya cike da zak'uwa...!
guntun murmushi yasake yace "ka kaima ammi wayan zan fad'a mata saita fad'a maka kaji...?"
baikoyi musu ba ya fito zuwa bak'in kitchen ya mik'oma ammi wayan yace "hamma sadeeq ne ke k'iranki..."
batayi k'asa a gwiwa ba ta k'arfi wayar tana fad'ad'a fara'ar fuskar tace "salamu alaikum babana...! ya karatun ? yakuma london d'in...?"
murmushi mai sauti yasake jin yadda ammin nasa take cikin t'sananin farin ciki,cikin kasalalliyar muryarsa yace"wa alaikumussalam ammi nah...! nayi kewarki sosaii !"
cikin dariya ammi tace "nima nayi kewarka sosai babana...! ina fatan ana maida hankali sosai akan abinda yakaiku makarantar ko?"
"sosai ma ammi na! kuci gaba da samu a addu'a dikdama nasan kunayi amma ku k'ara mana sbd shi mukafi buk'atarsa a halin yanxu..."
"insha allahu babana allah ya maku albarka ya baku sa'a akan abinda kuka saka gaba idan dae na alkhairi ne...! idan kuma akasin hakan ne allah ya musanya maku shi da mafi alkhairi...! yakuma k'ara t'sare mana ku bisa tafarkin addinin musulci! kuci gaba dajin t'soron allah a dik yanayin da kuka t'sinci kanku "
cike da farin cikin addu'ar mahaifiyar tasa yace "amen amen amen ammina! ina alfahari dake allah yabarmin ke...! ina auta ne abata mu gaysa"
mikama salifa ammi wayar tayi ganin yadda dik suka mata cirko cirko akai tin a lokacin da suka fara wayan!
karb'a tayi itama cike da farin ciki ta k'ara wayar tata a kunne tace "Hamma sadeeq nayi kewa ka sosai..." tayi maganar fuskarta washe da farin ciki...!
b'angaren sadeeq kuma shiuru yayi bayyi magaba ba yana taune bakinsa wanda hakan kuma kusan d'abi'arsa kenan...! hakan yasa salifa kama bakinta tana dariya k'asa k'asa tace "salamu alaikum hamma sadeeq" sbd tunowa da tayi ta hana fara ce masa koma kamin sallama...!
k'aramin murmushi yasake kamin ya ansa da "wa'alaikumussalam y'ar autar ammi kuna lafiya...?"
"lafiya qlaou hamma sadeeq...! munyi kewarka sosaii wlhi...! kaikuma ka tafi abinka kabarmu t'sawon lokaci batare da ka waiwayemu ba...!" k'aramar dariya yasake cikin muryarsa mai matuk'ar dad'i yace "nima ai nayi kewarku sosai amma nafi kewar ammi na fiye da ku fa..." kyab'e fuska tayi kamar tana gabansa tace "wato mu ba'ayi kewarmu ba ko hamma sadeeq...? shikkenan nima banyi kewarka ba ga su adda zainab" daga haka ta mik'a ma zainab dake ta faman murmushi tin dazu...!
k'ara wayar tayi a kunnenta tace "salamu alaikum hamma sadeeq ina wuni ko ina kwana?"
murmushi kad'an yayi yace "wa'alaikumussalam zainabu abu lafiya qlaou,ya kuke......?" "alhmdlh wlhi,ya karatu hammanmu...?" "lafiya qlaou,dafatan kuna karartu sosai ko...?" "sosaima yaushe zaka dawo...?" iyayen surutu bama wara mugaisa nikam"
babu musu ta mik'ama mimi dake ta wani ciccin magani tin dazu wai dan ba ita aka fara bama wayar ba...!
"hello ya sadeeq ina wuni..."
batare daya ansa mata ba yace "ke baki iya sallama kaman sauran y'an uwan naki ba ko amina...?" zumb'uro baki gaba tayi kamar yana kallonta tace "wai kai ya sadeeq kullum akayi maka abin arziki saika gwale mutum ne...?"
cikin murya mai d'an sauti alamun ransa yab'aci da kalar rainin mimin daya lura yana kanta tun na yarinya yace "zaki bama ammi wayan ko kuma sai ranki yab'aci stupid girl kawai..." a hasale itama cike da raini tace "danma kasamu an gaisheka ne zakayima mutum mita ai! kuma bazan sake gaisheka ba...!" tana kawowa nan ta dungurar da wayan a k'asa tasa takalmanta ta fice daga gidan duk suka bita da kallon mamakin kalar raininta...!
d'aukar wayar salifa tayi ta k'ara a kunnenta tana jin yadda yake ta sauk'e numfarfashi alamun ran maza yab'aci...! cikin muryar d'ar d'ar tace "hamma sadeeq dan allah kayi hak......!" bai bari ta k'arasa ba a hasale yace "zan fasa maki kai idan kika sakemin magana wlhi...! oya ki bama ammi wayan yanxunnan...!" cikin muryar t'sawa ya k'are maganar,wanda hakan yasa salifa mik'ama ammi wayar data nuna kamar ma bata gurin tun d'azu! dikdama dai rainin da mimi kema sadeeq d'in ba k'aramin b'ata mata rai yake ba! amma a mat'sayinta na babba dole ta koyi shanye fushinta gaban yara...!
"babana sai hak'uri kaji...? kasan har yanxu su d'in yara ne ba gaba zasu daina insha allahu...!saikaci gaba da masu addu'a..." ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauk'e yace "ammi rabu dasu dik zanyi maganin rashin kunyar yarannan dik randa allah ya dawo dani...! akoi inda nake son fita yanxu...! idan abba ya dawo a gaishesa ace masa zan kirasa mu gaisa anjima...!"
"toh babana aci gaba da t'sare mutunci kaji...? allah yamaka albarka...! amma baka gaisa da k'anwarka bafa yau...?"
"insha allahu ammi...!nagode da addu'oinki...! ammi barta kawai,saina sake k'ira mai gaisa da ita sauri nakeyi...!" daga haka bai bata damar k'arayin wani magana ba kit ya kashe wayar yana sauk'e ajiyar zuciya,ransa ba k'aramin tafarfasa yakeyi ba akan abinda mimi ta masa...! amma kuma yayi alk'awarin saiya koya mata hankali sosai dik randa allah ya had'a su...! daganan ya wat'sar da batun,bakuma dan yamanta ba,saidan kawai kar hakan ya hanasa watayawa son ransa...!shiryawa yayi cikin k'ananun kaya dasuka matuk'ar dace da t'sarin jikinta tare da wani had'ad'd'en takalminsa,agogo dakuma belt nasa campanyn gucci...! turarensa mai dad'in k'amshi ya fesa kamin ya kad'a kansa zuwa...!
b'angaren su ammi kam aymana har kuka tayi wai hamma sadeeq ya t'saneta shiysa yagaisa kowa amma banda ita,wanda hakan yasa sukayi ta mata dariya...! ganin hakan yasake kafular da ita ta fice daga gidan ta fad'a gidansu domin taje ta cima mimi data janyo hakan mutunci...! dik kiran da ammi ke mata tak'i kulata,salifa kuma cewa take gwanda ma abarta taci ma mimin mutunci ko gaba zata daina yima su hamma sadeeq raini...!
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/20, 7:17 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u
💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
_Na sadaukar da page d'innan xuwa ga my k'wallina(rahma) tare da my cweet amash had'i da queen aicha (niger) k'aunarku ta musamman ce a gareni! allah yabar k'auna ameen_
*PAGE 8*
******** "Ke malama wlhi idan baki kiyayi ma hamma sadeeq rashin kunya ba kina b'ata masa rai dik randa yak'ira waya aka baki ranki idan yayi million sai ya b'aci...! wawuya k'aramar mara kunya kawai...! allah wata rana saina sa an guggurje maki bakin rashin kunyar taki..."
a hasale mimi ta d'aga hannu da niyyar kwad'a ma aymana bari na ganin yadda take d'aga mata murya a mat'sayinta na wadda ta girmeta karaf taji an rik'e hannun nata,wanda hakan yasata juyowa a hasale domin ganin wanda ya hanata aiwatar da abinda tayi niyya...!
zainab ce t'saye ta rik'e hannun mimin tana jifanta da wani shegen kallon baki isa ba...! wanda hakan yasa mimi d'auko d'ayan hannunta ta kwasama zainab mari,kamin ta sauk'e hannunta kuwa aymana ma ta sharara mata mai shegen zafi...! wanda hakan yasa mimi yin kukan kura tayi kansu gaba d'ayansu fad'a ya kaure t'sakanin su...! aymana da zainab suka rufama mimi,wanda dama tun can a k'ule suke da ita sun k'ullaceta tin suna k'anana...! wanda a wannan ranar saida suka fanshe domin kuwa kare jini biri jini sukayi mata ga anty,naseer da baba dik basa gida ballantana su raba fad'an..!
salifa kuwa da tazo daga baya saka sakatan k'ofar tayi ta ciki cike dajin dad'in cin uban mimin da akeyi,wanda itama haushin mimi dama takeji sosai...! dik bugun k'ofar da ammi take ta waje salifa tayi mirsisi tak'i budewa...!
mimi kuma banda kururuwa da ihu babu abinda takeyi sbd ba k'aramin bugun huce haushi suke mata ba...! wanda ihun nata ne ma yayi atracting na ammi da mak'wafta suka jiyo su har aka taru a k'ofar gidan amma salifa tayi biris dasu zuciyarta cike da farin ciki...!
hmm abu fa yayi t'samari,domin ko an rasa yadda za'ayi a shiga gidan kota saman katanta ne,sbd akoi security waya akan k'aramar katangar tasu...! ana cikin wannan bidirin anty ta dawo daga gidan bayan layinsu dataje wajen wata k'awarta,wanda aka samu wani yaro da t'surku yakai mata rahoto...!
kamar wata zautacciya haka take buga wannan k'ofar sbd jin kalar ihun da mimi keyi na naiman taimako...! rahama itama sai kuka takeyi sbd jin kukan da yayar tata keyi...! dawowar nasir shima daga makaranta daya zama matashi sauraayi ya tarda abinda ke faruwa wanda hakan ba k'aramin bak'anta masa rai yayi ba...!
cikin kakkausar murya yafara ambatar sunayensu,wanda hakan ya haut'sina ma salifa hanjin ciki da tun dazu ake cewa ta bud'e amma kuma cikin t'siwa tana d'aga murya kan bazata bud'e ba...!
zuwa d'akin tayi ta fad'a masu su gudu su b'uya ga ya naseer,kasancewar yadda suke t'soron shi sbd baya masu da wasa idan sukayi laifi suka jawo mimi kamar kayan wanki data matuk'ar jigata suka ajiyeta t'sakar gida sannan salifa da aymana dakuma sameer dake ta faman dariya shima tin d'azu suka shige d'akin suka saka key ta ciki suna jiran shigowar zainab su k'wamushe k'ofan...!
saida zainab ta lek'a ta k'asan k'ofa dakyau ta hango mutanen unguwar ta tabbatar hankalinsu baya wurin yana ta yadda zasuyi a b'alla k'ofar ta zare sakatar a hankali ta yadda babu wanda yaji k'aran kamin ta koma a d'ari cikin d'akin suka rufesa gwarai suka saka key sannan suka barsa a jiki sunata sauk'e numfarfashi kamar wayanda sukayi fad'a da gardi...!
k'aran k'ofar da anty tajine yasata k'ara bubbuga k'ofar a hargit'se tanata auna masu ashariya k'ofa kuwa ya bud'u abinsa wanda hakan yasa aka fara tururuwar shiga cikin gidan,anty ce a gaba inda tayi tozali sa aika aikar dasu aymana sukayima y'artata da zuwa yanxu ko mot'si batayi alamun a sume take...!
"wlhi baku isa ba...! zaku san kunyima y'ata taron dangi a cikin gidan nan...! saina nuna maku asalin kalata yau a cikin garin azare...!" haka anty keta faman sauk'e maganganu cikin kuka na ganin yadda yarannan sukayi ma y'ar tata...!
ammi kam tama gaza mot'sawa daga bakin k'ofa na ganin yadda yarannan sukayi wannan aika aikar wai dik akan sadeeq...? itafa tana t'soron abinda kan iya faruwa t'sakanin yarannan baki d'ayansu...! idanun nasir kamar garwashi haka ya canza kala sbd b'acin ran abinda suka aikata,dikda ya daina shiga shirgin wannan yaran amma dole ya koya masu hankali ta yadda gaba koda kud'i akace su aikata abu makamancin haka bazama su soma ba...! ruwa rahama ta d'ebo a randar sanyi bisa umarnin ammi ta shashshafama mimi a fuska ta farfad'o daga gajeren suman datayi tana mai fashewa da kuka ta k'ank'amr anty da itama kukan take wurjanjan da hawayen tausayin y'ar tata...!
ana cikin haka abba da baba suka shigo gidan dasuma aka tare su tin a layi aka kit'sa masu zancen...!
batare da abba yace k'ala ba ya sungumi mimi yakaita mota suka kaita asibiti tare da baba bayan yasa naseer rufe gidan ta ciki sbd kar mutane su cika cikin gidan,wanda hakan yasa y'an gulma wat'sewa...!
K'aramin asibiti mafi kusa dasu suka kai mimi dake ta faman kuka tana jama su aymana allah ya isa takeyi cikin zuciyarta...! dak'yar likitoci ma suka karb'eta sbd sunyi tunanin y'an fashine sukayi mata kalan wannan dukan da basu san cewa yarane sukayi mata hakan ba...! emergency aka shiga da ita...! sai bayan sallar isha'i aka gama nata treatment na ciwukan jikin nata aka surkud'a mata allura dakuma magungunan da aka rubuta mata aka sallamesu wajen k'arfe tak'was na dare...!
lokacin da suka dawo suka tarda anty dasu ammi dasukayi jigum na zaman jiran suga ta inda zasu b'ullo...! wanda kuma har zuwa lokacin su salifa sunk'i bud'e k'ofar d'akin dikda kalar bugun k'ofar da naseer yayi tayi kamar zai b'alla k'ofan amma sunk'i yin magana ma ballantana asan ran zasu bud'e...
naseer ne yashigar da motar baba cikin gida tinda da motar abban salifa suka tafi...! wanda yanxun ma shi ya bud'e masu get d'in,tinda dama a gida d'aya suke ajiye motocin nasu wato gidan su ummi sbd anan ne sukayi wajen ajiye mota !
naseer ne yakamo mimi suka shigo madaidaicin parlon nasu inda anty da ammi suka tashi kusan tare suna tarbo su amma anty ta bangaje ammi,wanda kad'anne ya rage bata kai k'asa ba abba ya taro ta da yanxu shigowansa cikin parlon...!
mugun kallo baba yabi anty dashi amma ta d'aure fuska tamau kamar hadari,sbd tayi alk'awarin shima baban daga yanxu zata fara nuna masa asalin kalarta tinda taga kowa kansa yasani...!
shikam abba murmushi kurum yayi dikdama dai hakan datayi ya sosa ransa...! kan 3seater naseer da anty sukayima mimi masauk'i,inda baba da abba suka zauna kan 2 seater,anty da ammi kuma na zaune kan one one seater dake palon,naseer kuma ya d'aura kan mimi akan cinyarsa tanata lanjaremasa shikuma cike da tausayin k'anwar tasa yake biye mata...!
anty kam banda harare² babu abinda takeyi a wajen tana jiran taga zasu d'auki mataki ne ko² ah'a...?
abba ne yace "naseer ina sauran yaran suke...?" cike da ladabi kamar ba naseer wannan marar kunyan nada ba yace "abba sun rufe kansu a d'aki tinda suka gama yin abinda sukaga dama sunk'i bud'ewa...!" ya k'arasar maganar cike da jin zafin abinda sukayi...!
mik'ewa abba yayi batare da yayi magana ba yaje k'ofar d'akin dayake kyautata zaton suna ciki...! cikin kakkausar murya yace "idan na k'irga uku baku bud'e ba ranku idan yayi dubu sai ya b'aci yau a gidannan wlhi...!"
aikuwa kamin ma yagama rufe bakinsa sameer da dama yagaji da zaman cikin d'akin yayi wuf ya bud'e...!
hmm wato abin dariya kura a rumbu...! sharkaf suke jik'e da gumi sbd sunsan sun shuka ba daidai ba sunata rarraba idanuwa na ganin yadda abba ke binsu da kallo...! aymana da salifa suka mamuk'e da junansu kamar zasu shige cikin junansu...! sbd sunsan yau mai k'watarsu sai allah...!
kad'a kansu abba yayi baki d'ayansu suka fito,wanda hakan yayi daidai da fitowar ramata ma daga d'akin antyn nasu itama ta zauna gefen nasir daga k'asa...!
banda kallon zakuci ubanku babu abinda naseer kemasu salifa wanda sukuma suka fara tuttura baki gaba cike da rashin kunya...!
gefen baba salifa ta gudu,ganin yadda ammi ke aiko mata da wata k'atuwar harara,wanda kuma hakan nada nasaba da k'in bud'e k'ofar da salifa tayi ne...!
zainab da aymana kamar munafukai kansu na k'asa suna ta wajen k'afar ammi...! shima sameer dayasan bayyi komai ba a gefen baba ya zauna yana rarraba ido...!
gyaran murya abba yayi wanda hakan yasa kowa maida akalar kallon nasa zuwa gareshi domin saurararsa...!
cikin kakkausar murya yace "ke zainab mainene ya had'aku da amina har kukayi mata wannan d'anyen aika aikar da idan kukaga wani ma zai mata hakan ku masu iya karb'anta ne a mat'sayinku na y'an uwanta...?"
kallon kallo aka t'sayayi t'sakaninsu,wanda saida baba yabugama zainab razananniyar t'sawa da tin d'azu baiyi magana ba,ta bud'e baki cike da zullumin abinda zaije ya dawo ta fara basu labarin abinda yafaru yaud'in tiryan² har zuwa yanxu...!
shuru kowa yayi a parlon cike da mamaki dakuma al'ajabi amma banda ammi da kanta ke k'asa tin d'azu...! shikam abba abinma dariya yabasa sosai amma kuma baiyi ba...! abba kuma kansa na k'asa yana tunanin wasu abubuwan dasuka shud'e a baya! dakuma hasashen abinda kan iya faruwa a gaba...!
d'ago kansa yayi yana kallon zainab,mimi da aymana...! zuciyarsa cike da t'soron abinda kan iya zuwa ya dawo a gaba...!
nasiha sosai abba da baba suka masu tare da sasu bama mimi hak'uri da ba haka taso ba...! amma kuma tasan dole anty zata d'aukin mata mataki koba yanxu ba,dan haka ta nuna komai yaawuce wanda anty ta bita da kallon baki da hankali nikamm ban hak'ura ba...!
sosai ba su abba suka nuna masu b'acin ransu wanda hakan yasa sukaji dama basu fara ba...!, barin parlon naseer yayi ba tare daya jira an k'are maganar ba ya tafi d'akinsa...! murmushin manya kawai abba yayi ! sbd yasan halin naseer sarai sai ya masu abinda yafi wanda sukayi tinda har ya fusata haka...!
anty ma mik'ewa tayi takamo y'arta zuwa bedroom suka shige suka barsu abba dasu baba...! wanda hakan ba k'aramin sosa ma baba rai yayi ba! ganin anty na neman nuna cewa gidansa yafi k'arfinsa...!
ammi ma kad'a kan salifa dake ta mat'sar k'walla tayi suka wuce gida tana duddungure mata kai abba yabiyo bayansu bayan sunyi sallama da baba...! aymana,zainab da sameer saida sukayi sallah abinsu kamin suka zubo guntun abincinsu suka cinye daga nan suma dariyar abinda sukayi d'azu kawai suke,sun tabbatar yanxu mimi zata rage masu wani fitsarar ...!
baba ya nunuma anty b'acin ransa akan bar masu parlon datayi d'azu ta hayayyak'o masa kamar itace mijin,wanda hakan yasa baba kyaleta sbd gudun hayaniya suka kwanta kowa rai babu dad'i...! mimi da rahma na d'akin anty abinsu,wanda dama tun can acan suke kwana...!
_~K'WARAN K'WASI DUBU SAINA HUTA ZAKU JI SABON UPDATE TINDA ABIN ER HAKA NE😒 DIK WANNAN TYPING D'IN DANAKE MAKU BAKWA GANI SAM BALLE A FARANTA MIIN? IDAN KUMA KUKA GA NA CI GABA DA POSTING SAI KUN HAD'O DUBU D'AI D'AI(1K)TA YADDA ZAN SAYI KAZA INA CI KULLU KULLUM IDAN YASO SAI INA RANGAD'A MAKU😒😒~_
*OUM MUMTAZ✍🏿*
[11/20, 7:18 AM] oum mumtaz ce🤠: : https://chat.whatsapp.com/JWpooLoGGHj4HQW9f71U1u
💥💥 *AYMANA.....!*💥
_ROMANTIC STORY_
*MALLAKAR:-OUM MUMTAZ*
Wattpad@UMMIE2018.
*FREE BOOK.*
_LITTAFIN KYAUTA._
*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️
*PAGE 9*
******** Washe gari da safe.
bayan sun tashi sameer da zainab dik a t'sorace suke da naseer sbd sunsan yau idan suka shiga hannunsa mai karb'arsu sai allah!
da wurwuri sameer da zainab sukayi shirin tafiya makaranta abinsu,ko karya basu t'sayayi ba suka fice daga gidan suka fad'a gidan ammy dasuka tarda salifa kam na sharb'an baccinta hankali kwance,ammy ce ma tafarka tana kitchen sbd ta shirya masu abin kari!
gaishe ta suukayi ta ansa masu fuska d'aure sbd haushin abinda sukayi jiya itama sosai taji babu dad'i! cikin t'sukewar face ammy tace "ina ita aymanar...?"
"tana gida har yanxu bata farka ba ammy" fad'ar zainab kenan tana janyo tea plast d'in dake gefen ammy!
cup guda biyu ta d'akko cikin kitchen d'in had'i da tea spoon ta shiga parlon ammyn ta zuba madara da milo had'i da sugar ta fito zuwa bakin kitchen d'in ta had'a masu shayi ita da sameer dake taya ammy hira shima!
mik'a masa cup d'aya tayi itama tafara shan nata hankali kwance! cikin hikima ammy ta sake nut'sar da ita abinda sukayi jiya ba daidai bane sbd koman lalaci mimi er uwarsu ce bai kamata su mata haka ba,tinda suma masu iya tare mata idan suka ga anayi mata hakan a wani wuri!
bayan sun gama shan tea nasu abba ya fito daga d'akinsa a lokacin kuma ammy ta sauk'e masu joloup na taliyar data dafa masu ta zuba masu a flast na salifa wanda zasu tafi dashi makaranta sbd tasan ko sama da k'asa zata had'e anty ba basu abincin zatayi ba!
Fitowar abba ne yasa suka gaishe sa ya ansa masu cikin sakin fuska yabasu 200 kan suci abinci dashi suka masa godiya suka fice !
aymana kam baccinta tasha hankali kwance batare dajin fargabar komai ba sbd shegen t'saurin ido kalar nata da aka lik'a mata shi a yanxu ta hanyar sihiri k'arfi da yaji!
saida ta gama shan baccinta kusan k'arfe goma kamin ta tashi tana mik'a!
cikin jerin akwatinanta dasuka kasance guda hud'u harda k'aramin kit kuma shak'e suka da kaya na alfarma wanda ba kowa bane ya sai mata face saurayinta huzaifa ta ciro brush nata sannan ta lat'so macline ta fito
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 14