Yau Abba ya yi arba'in duk su Mama suna gidan baƙi da abokansa duk sunzo haka ma sauran matan su kawu Iro kai kace biki ake,a Babban falon da yake zaune da baƙi su Hajiya Fulera suka shigo kamar yadda suka tsara nan mutane sukaita gaida su suna wani yatsina suke amsawa duk abinda suke Alhaji Baffa na kallonsu saida suka gama gaisawa da mutane sannan ba kunya suka zauna wurin suna duban Habib sukai su kuma mutane na dubansu da mamaki dan tabbas sunyi abin mamakin cikin maza ba kunya ba ɗar matsayinsu na mata matan ma masu takaba.
Vote
Share &
Comments
Ƴan uwa
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
chapter 1️⃣8️⃣
Alhaji Baffa tun zaman su yake binsu da kallo shi yasan waɗannan dama ba matan arziƙi bane suna son mijin ne dan dukiyarsa yana tsaka da tunani yaji sunawa Habib magana"to Habib a musulinci ma yaune ya tabbata ka bawa masu gado haƙƙinsu tunda ba naka bane",runtse idanuwansa ya yi dama tun zamansu ransa ke masa zafi kawai yana danne kansa ne,ɗan murmushi ya yi ya nuna musu mutanen dake gefe gasunan harda turawa da alƙali Babba sananne kunga ba ja kenan tsit akayi aɗakin ana sauraransu wannan bature shiya fara magana kamar haka"Alhaji ya bar mana dukiyarsa mu kasafta masa ita yadda yace tunda baya da ƴan uwa na jini sai ɗa namiji da Ƙanwarsa sai tsohuwar matarsa sannan Baffansa da Ummansa,a bisa tsari yadda ya bayar matansa huɗu kowacce da yaranta Hajiya Fulera ga naki,Hajiya Harira ga naki,Hajiya Salma ga naki Hajiya Safiyya naki,Alhaji Baffan sa yana ina",nuna shi akai nan ya miƙa masa takardu daban daban ka duba da naka dana Ummansa kamar yadda yace sannan na ƙanwarsa da tsohuwar matarsa,sannan wannan bayanin da takardun na ɗansa ne amma gashi alƙalin abin zaiyi magana da kansa",duk maganar da yake da turanci yake wanda baya ji na kusa dashi yana gaya masa,gyaran murya alƙalin ya yi ya fara bayani"kafin mutuwar Alhaji ya mallakawa ɗansa dukiya mai tari yawa dan yana da yaƙinin zai taimaki al'umma bila adadin wannan dukiya bawai ya bashi bane dan ya nunawa sauran iyalansa yafisu a wurinsa ba,dan haka wannan muhalli ma da ku ke ciki ya mallaka muku wasu ya barwa danginsa wannan gaba ɗaya dan haka aduk sanda suka buƙata zaku matsa naku ku basu wuri saiku duba dukkan takardun wuraren ku zaku ga inda ya mallaka muku,sannan margayi yabar ragamar ƴaƴansa a hannun yayansu koda kuwa suna wurinku ne kenan bazasuyi komaiba saida izininsa wannan kenan ga wasu takardu daya bar wasiyya wacece Nana ina mahaifinta",Alhaji Baffa ne ya nuna Baffa dake can gefe a zaune"miƙa masa takardun hannunsa ya yi"ga wannan nata ne a kula kuma ya roƙi da'a kula da ita dan akwai wani babban sirri dangane da ita sannan Habib ɗansa ya kasance ya cika alƙawari na maida Nana matarsa komin daɗewa wannan ne wasiyyar sa gata arubuce" ya mimmiƙawa na kusa dashi takardun su gani dan sunfi copy ɗaya,duk wanda ya duba zaice hakane,dukkan mutanen dake wurin sun kance akwai makusanta matan Alhaji kamar Baban Hajara Alhaji Bello yayan Hajiya Fulera tofa sunfi kowa shaƙa dan abin bai musu ba ba haka suka so ba,yana gama bayanan sa kamar wasu fari haka suka miƙe"wallahi ba'a isaba muyi wahala dashi shekaru masu yawa sannan su daga baya aka samesu sai ace an mallaka musu komai wallahi ba wanda ya isa a haɗe komai a rabashi kuma gida ba wanda ya isa mubarshi sai kaf suzo mu zauna tare",wannan suɓul da baka da Hajiya tayi bata sa ni ba shi yasa alƙalin murmushi"ai hajiya gado ya rabu kuma zamanku dole sai sun amince sannan zaku zauna tare in basu aminta ba kuwa saidai kubar musu muhallinsu,sannan ki shiga hankalinki bamai ƙwace wannan abu da Allah ya basu dan da basu samu ba shine yanzu ya turo mai basu maija da wannan to zashi kotu ayi acan inda raban wannan ma asake kasawa shinkenan bisimillah ina jinki"yayanta ta kallah ya kaɗa ma ta kai alamar karta yadda da hakan shiru tayi suna ta muzurai,Hajiya Salma ce tai ta maza"mun yarda da rabon gado amma bamu yarda da barin gidaba"Alhaji Baffa ne ya riga kowa magana"mun yarda zamu zauna dasu rankai daɗe",wani murmushin kun tafka kuskure matan suka saki duka Alhaji Baffa na kallansu"masha Allahu to sun amince muku dan haka ku zaku tattara awaje ɗaya saiku basu sauran wuraren tunda ba'a buƙatar komai a wuraren zaman,Alhaji tsoho wannan karramawa taka Allah ya biya Allah yaja kwana,ke uwargidan Alhaji gaba ɗaya ƴan uwan zamanki zaku tattaru a ɓangarenki dan karki manta nasan wurin mata shida zasu iya rayuwa batare da wani ya matsantawa wani ba ga takarda zansa hannu nan da kwana bakwai zaku haɗe su kuma zasu dawo Allah ya jiƙan Alhaji ku dage masa addu'a da sadaka shine gatan kawai da zaku masa da dukiyar da yabar muku kai Habib kabi lawyer zai baka address inason ganin ka",yasa hannu ya miƙawa lawyer shi kuma ya miƙawa Alhaji Baffa,ba yanda su Hajiya suka iya haka suka fice gwiwa sage amma sunyi alƙawarin duk wanda zai zauna dasu da ƙafarsa zai bar gidan,basu san akwai uwayensu hauka ba a dangin nan Gwaggo Asama'u kaɗai ta ishesu riga da wando bama azo kan matan Kawu Iro ba,a wurin Hajiya Fulera suka haɗu nan sukai jigum suna kallonta,ajiyar zuciya ta saki ta kallesu,"nasan zakuce taya na amince muka karɓi wannan dukiya ko to inaso ku sa ni wannan alƙalin ba kanwar lasa bane kuma in bamu karɓa ba zamuyi biyu babu saboda wannan da ku ka ga anbamu ba ƙaramar dukiya bace bare ga maƙudan kuɗi na fitar hankali dan haka inaso ku nutsu kuji ba sanya awannan zaman da za'ayi ba ragawa wani ba mutunci har sai sun gaji sunbar mana gidan sannan wannan ɗan banzan magajin sai naga bayansa ku wuce kar ace wani abu muke kuma ku adana takardun ku ko ku kawo su nan na haɗa na aje mana kunsan yanzu zasuna harin abinda aka bamu baran kunsan akwai ƙarti adanginsu kuma banyarda da wannan tshon ba",da yake watan ɓatan basira da rashin rabo ne ya kama musu sai suka miƙa ma ta tai wani mugun murmushi ta karɓa ta buɗe locker duka ta saka,tashi sukai suka fita kowacce farin ciki fal ranta dukiya tasamu,rashin sani yafi dare duhu su Hajiya Harira sun faɗa tarkon Hajiya Fulera basu sa ni ba da sun san wace ita da basu bata dukiyar su ba,kuma basu isa su amsheta ba dan damata gama dasu daga maganar farko ta kubani kuma suka amince,suna fita ta fice acan wani saƙale suka haɗu da yayanta kaf abinda tayi ta faɗa masa jinjina ma ta yay kuma yasanar ma ta akwai wani boka can enugu yake zaije akan wannan abin yakamata kuma suje tare tace ta amince tama manta takaba take.
Ana gamawa Alhaji Baffa ya musu godiya nan suka wuce kuma alƙalin ya tafi da takardun wurin Baffa sannan yace Babban Yaya yazo da nashi kaf anjima,hakan kuwa aka yi kaf ya ɗiba yaje dasu ya jima acan sannan ya dawo direct gida ya wuce yay wanka a gaba ya taso matarsa yazo ya tarar Alhaji Baffa ya tara su Mama yace kowa ya shirya rana ita yau zasu koma can gidan wohoho zoka murna ciki da bai na wannan gidanjan bama ya Gwaggo Ma'u haka itama Hajara sai dai ita tafi kowa murna da hakan dan su kaɗai suka san cikinsu ita da iyayenta wannan dangin tsiyar.
A satin kuwa rankatakaf muka koma can Alhaji Baffa da kansa ya nunawa kowa inda zai zauna kuma hakan ya dace da kowa suma kuma yanda yace haka kowa ya yi ɓangaren gidan Babban Yaya kuwa ai burin danginta yanzu ya cika gata ga Innar ta sun tabbatar komai zaizo musu da sauƙi yadda basuyi zato ba da ita zasuyi amfani komai nashi ya dawo hannunsu.
cikakkun wata uku ana zaman kadaran kadahan sai dai Alhaji Baffa yasa ido sosai akan kowa kuma duk masu miji yajawa mazajansu kunne kan suyiwa matansu kashedin duk wadda taja rigima to zata koma inda ta fito ta zauna ita ɗaya ko ƴaƴa basu bin ta,makaranta kowa nazuwa haka masifarmu ni da Aunty Hajara tana nan saima abinda ya yi gaba zagi dai ina shansa ko agaban waye dan yanzu kowa yasan tasan meke tsakanina da Babban Yaya itama,kuma duk wanda take tuntuɓa yasanar ma ta wannan al"amari fa kawai tayi haƙuri kuma abinda bama yanzu ba duk wannan bayanai basu gamsheta ba ita kawai na bar ma ta mijinta.
Yauma na dawo daga makaranta du arikice dan inacan Babban yaya ya bini wai zai koma India na ɗauka wasa yake sai ya nuna min harda kayansa a mota,ina tuɓe kayana na sheƙa gidan Iyyo ita ta tabbatar min ya tafin kuka nasaka ma ta da mamaki take dubana"ke miye hakan ki ke kuka dan ya tafi",baki na buntsuro"to meyasa zai tafi da waccan ƙatuwar matar salon ana masa dariya acan su da suke da matansu ƴan caras","waya ce miki da ita ya tafi tana nan gida yace ba yanzu zai ƙara komawa da itaba"wani uban ihu na buga na miƙe ina rawa da cashiya,dariya Iyyo tai tayi"Allah ya shiryeki Nana","ameen Iyyota",na gantsare ma ta ƙugu na fito da gudu mukai karo da wani baya nayi zan faɗi ya taroni na faɗa jikinsa ƙamshin turarensa yasa na saurin ɗagowa ina kallonsa ihu na buga"wayyo Babban Yaya bai tafi ba Iyyo",saki na ya yi ya toshe kunensa"Nana zaki fasa min dodon kunne"hannunsa na riƙo Babban Yaya ka sayi ticet kuma kayi asararsa sabodani dan Allah ka tafi ai kuɗin ba aƙasa ake ɗebowa ba",kaina ya ɗago yana murmushi da ban taɓa ganin ya yi irinsa ba"Iyyo fito kiji Nanata ta zama babbar mace tasan zafin nema da nakeyi",fitowa tayi tana dariya"bana faɗa maka ba ai Nana gaba kaɗan saita kere kowa hankali da hangen nesa a yaran nan","na aminta dake Iyyo tamu ta mutunci",wayarsa ke ƙara ya fito da ita daga aljihu ya ɗaga"ok"kawai yace yana dubana"zan wuce yanzu jirgi ya samu dama wancan matsala ya samu ashe rabon zan dawo na ganewa idona ne Nanata ta girma",fuskata na rufe"zan bika to","da ace hakan zata yiwu basai kinfaɗa ba amma wataran ƙafata ƙafarki duk inda zani","kayi alƙawari","nayi",ya faɗa yana dafa kaina,hannunsa na riƙe muka fito agidan kowa na kallon mu ƙawata abokiyar faɗana ce muka haɗa ido na ma ta gwalo,ba kunya ta ɗaga hannu biyu tamin daƙuwa ni kuma na kwantar da kaina a hannun mijinta tana kallo kuma,muna jikin motarsa ta ƙaraso ana kwarkwasa ta gefensa ta tsaya jikinta na taɓa nasa,baki na taɓe na faki idonsu na ƙwala ƙara da sauri ya juyo har yana tureta bai lura ba kamin na dire a tsallen ya ɗaukeni cak a wurin ya yi gefe dani yana tambayar lafiya,taɓe baki nayi nai rau rau da ido"ba ji nayi ba kamar wani zare zare nabimin ƙafa",na rushe da kuka sunkuyawa ya yi yaja rigar jikina sama har gwiwata sannan ya juyo da ita zare da yagani a jiki ya fizge sannan ya sau rigar ya miƙe yakama hannayena ya janyo ni jikinsa kamar zai rungumeni "ya isa haka mana kukan kina sosamin raina",goge fuskata na shiga yi"na daina Darling Yaya kaga ma Aunty duk ta damu",juyawa ya yi yana kallonta shi wallahi yama manta da ita awurin basarwa ya yi amma mamaki yake yadda ta aza hannu aka alamar ta shiga uku"ke kuma miye na aza hannu aka",saukewa tayi tana harararsa"mai zaisa bazan aza hannu aka ba kalleka gotai gotai da kai amma in kana agaban wannan jaririryar saika rasa nutsuwarka",dake Babban Yaya babban ɗan rainin hankali ne sai ya yi murmushi"au Nana jariryace awurinki amma naji daɗin hakan kinga saina ɗakko abata tun yanzu tafi miki daɗin raino",yana kaiwa nan ya shige mota,da sauri tace "wallahi karma ka fara kawo min wannan ƙadangaruwar gidana zan soyeta kuwa","da nafi murna saina tama ki ci "ya kalleni nai kamar banji me suke cewa ba,hannu na ɗaga masa na juya dan in na bari muka kalli juna da Aunty Hajara tabbas dariyar mugunta zan ma ta amma na tausaya ma ta tunda mijin ma fecewa zaiyi ya barta da ni ɗin dai.
Vote
Share &
Commentss
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
chapter 1️⃣9️⃣
Bayan tafiyar Babban Yaya da kwana biyu lamarin gidan ya fara canjawa su Hajiya Fulera suna barin maza gaba gaɗi suna shigowa gidan kuma Alhaji Baffa nagani ya barsu dan ya riga ya gane wato Babban Yaya suke tsoro sai ya barsu ai insun san wata basu san wata ba.
****
Daga ɓangaren Iyyo na fito ina tafiya mukai karo da Hajiya Fulera baya naja"yi haƙuri Mommy banganki bane",ban gama magana ba naji saukar mari mai zafin gaske,dafe kuncina nayi na ɗago ina kallonta a mamakance"dan na baki haƙuri shine kika mareni",hararata tayi"ko zaki rama ne",kai na girgiza"bazan rama ba dan inada tarbiyya amma zakiga abinda zai biyo baya","ina jira dan dama an faɗamin ƴar sharri ce ke","iya nan aka faɗa miki aini ƴar masifa ce ma bari kiga sample" bataga abinda nagani bane Gwaggo Asama'u ce tazo zata wuce nai gwaraf aƙasa na rushe da kukan masifa,da sauri tai burki ta juyo"ke Nana wannan tsiyar taki baki dainawa ko agaban matar Baban naki kike wannan borin"ƙara kware murya nayi"wallahi Gwaggo dukana tayi wai danna gaisheta bata amsa ba nace inatamiki magana baki kulani ba shine tace ai kaf danginmu ba wanda ya isa ta kulashi kuma ko Ma'u da kuke taƙama da ita bata isa na kulataba ke saima na dakata tunda ba gado gareku ba gidan kawai taka haye aka musu aka bamu",kafin in gama magana Gwaggo Ma'u ta hayayyoƙo kanta da masifa zagi ta uwa ta uwaba tana kai ma ta duka kan kace kwabo antaru a wurin, wallahi Hajiya Fulera takasa magana saidai in mun haɗa ido na ma ta gwalo Gwaggo Ma'u nakai ƙarshen maganarta ta kamo hannuna"zonan ƴar albarka muje kuma karki ƙara gaida ta "kai na kaɗa ina taɓe baki muka bar gun,tsbar dariya Aunty Mama saida ta zauna a ƙasa,Iyyo dake dariya ce tace"wallahi Halima ƴarki sai a hankali kalli yadda ta shirya da uwarta wadda tun haihuwarta basa shiri sai yau",tashi Aunty Mama tayi tana bin Hajiya Fulera da kallo"kisan me Iyyo gatsefa ta ma ta ita kuma Nana ba hankali shine ta haɗasu faɗa da ita kuma fa kawai wucewa Ma"un tazoyi dake kusan halisu guda fannin sharri shine ta saƙale ta haɗawa Fulera kitimurmura da ita","Allah dai ya gyara amma Nana tabb",wucewa sukai dama Mama kome ake bata fitowa kalla ita haka halinta yake,muna wucewa nace"Gwaggo zanje intafi islamiyya", sakin hannun nawa tayi"ma za karki makara to".
Hajiya Fulera kasa zaune tayi ta kasa tsaye ita wannan yarinyar zataiwa haka dama Hajara na faɗa ashema yarinyar tafi haka masifa da sharri to ta taɓo inda bazata ƙara kwana lafiya ba da ƙyar ta saita kanta sannan tazo ga baƙin da tayi dama su zataje tara bakin get tsautsayi ya haɗa mu.
Yau watan Abba huɗu da kwana shida Alhaji Baffa yaga yadda ake shirya biki agidan amma bai kula ba baƙi tako ina ake wato matan wai zasu fita takaba saura kwana biyu da daddare ina kwance ɗakin Iyyo Alhaji Baffa ya dubeni" karɓi wayar nan kira min Habibu",karɓa nayi na kira masa shi dayake su acan rana ce yanama office yaga kiran ɗagawa ya yi yana magana na miƙa masa ya karɓa ya yi sallama"Alhaji tsoho","na'am Alhaji yaro ya aikin","Alhamdulillahi lafiya dai naji muryarka kamar baka jin daɗi","lau nake Aisha ce dai ba lafiya kaganta nan sai amai take duk ta fita ahayyacinta sai kiran sunanka take kowa yakasa gane kanta",a razane ya miƙe muryarsa na rawa"meya sameta dan Allah",kafin Alhaji Baffa ya yi magana ya katse wayar,saukewa ya yi daga kunensa ya ajeta yana kallon mu ni da Iyyo ganin yanda mukai duru duru kamar kaji,ɗan murmushi ya yi"hakan dana masa shi zaisa yazo batare da tambayar kowa ba'asi ba inda cemasa nayi ga abinda ake shiryawa agidan cewa zaiyi abarsu suyi ni kuma bazan bari awa Habibu bikin iskanci ba da dukiyarsa",ajiyar zuciya nayi ina dariya"kace su barikin ma su basu iya ba yau ga tsoho zai gwada musu duniya",da carbin hannunsa ya kawo min duka na goce ina dariya.
Acan ba yanda bayyi yasamu tiket aranar bai samu ba saina washegari adole ya karɓa amma kwana da wuni bai runtsaba kuma bai kira kowaba har tsawon wannan lokacin.
Tunda muka tashi da safe ranar gidan ya kacame da ƴan soye soye da dafe dafe,tunda kowacce danginta ta tara masu yawa inka shigo gidan saika ɗauka bikin mutum goma ƴan gata ake,ana sallar azahar manyan ƴan Dj da aka ɗakko suka gama jera komai nasu nan da nan sauti ya fara tashi ƙawayensu da ƴaƴan ƴan uwa mata da maza sai cashiya suke,yana sauka a airport ya hau taxi zuwa gidan batare da yasanar da kowaba tunda suka doso layin yaga mutane nata shige da fice ga kiɗa har titi kafin yaƙarasa get anan yasa aka sauke shi ya shigo gidan tun daga bakin get yasa hannu a aljihu ya lumshe idonsa ya tabbatar Nana ƙalau take wannan al'amarin yasa Baffa yace masa Nana ba lafiya dan yazo bawai dan bata da lafiyarba yama tabbatar in rashin lafiyarce baza a faɗa masa ba sai yanzu ma hakan ta faɗo masa,buɗe idonsa ya yi ya yana ƙarema ƙarti zunduma zunduma kallo ganin yanda suke yawo agidan su na matan aure matan sunna,nan danan idanuwansa suka sauya cikin ɓacin rai ya taka zuwa cikin gidan kotakan su Murtala masu sannu da zuwa baibi ba,daga ɓangaren mu na fito zan tafi islamiyya adole saina biyo ta wurin da ake kiɗan dan haka ba ruwana na ratso ta tsakiyarsu Aunty Hajara sai cashiya ake a tsayar maza wai ƴan uwa ne nan kallonta nayi ina dariya ta harareni tana cije baki,zan giftata wani ya kawo zai taɓani na maza na matsa"dalla malam miye hakan an faɗa ma jikina na irin wannan waɗannan jakan ne"na faɗa ina nuna su Aunty Hajara da ƙanenta,wani tun zurowa tayi tasha gabana",yau zanci ubanki abinda ki ke taƙama dashi dan mijina saina sa wasu sun latse su yanzunnan",hannu na ɗaga ma ta"da kuwa kin tarowa kanki ruwa ko aurenki bai mutu ba zaiyi muguwar girgiza",da hannu tawa mazan alama suka matso mari ta kawo min na kauce tasa hannu ta tunkuɗa kan ƴan uwansu mazan nan,ƙarasowasa kenan wajen idanuwansa sukai kai abinda ke shirin faruwa ganin yanda ta hankaɗani yasan shirinta ne hakan da hanzari ya shiga tsakiya na faɗa jikinsa runtse ido nayi mai makon jikin wasu sai naji ƙamshinda ko bacci nake idan najiyoshi zan faɗi waye,hannuwana na buɗe na rungumeshi na rushe da kukan tashin hankali kuji fa dan Allah da banyi kukan ba sai yanzu,cikin tsananin ɓacin rai ya ɗago yana dubanta ta razana sosai amma ta dake,su kuwa mazan da basu gane waye ba tsautsayi ya ɗebesu suka kawo hannu gareshi yana dafe dani a jikinsa ya ɗaga ɗayan hannun ya kama hannun wancan sai ji kake ƙarasss,cikin ƙiftawar ido ya ɓalla mai hannu ba ita ba ba mai karayarba harta ƴan Dj saida ƙarar ta isa garesu kan kace me mata da mazan sun dare sai gudu shi kuwa mai karaya ya zube a wurin yana shure shure da ihu,masu gudu na gudu amma shi yana nan riƙe da ni a wurin har su Hajiya Fulera labari yaje musu nan akai dafifi awurin ana kallon mu ni kuwa naji sauyi na lafe ajikinsa ina shan ƙamshi,duk wanda yake awurin nan salati yake mahaifiyar yaron Yayar Hajiya Fulera ita tai kansa tana ihu tana tsine ma wanda ya yima ɗanta haka ko kallon inda take baiba,tattaro shi sukai zasu wuce ya janyeni ajikinsa ya tare su yana kallonsa"ka buɗe kunne da kyau kasaurareni koda wasa ka ƙara niyar taɓa abinda yake mallakina ko kuɗine ba mace ba indai nawa ne to ka kiyayi haɗuwa ta dakai",yana kuka yace"wallahi bansan taka bace Yaya Hajara ce tasa ni amma ko inuwar gidanka bazan ƙara kalla ba bare abu mallakinka",cikin faɗa uwar ke kallonsa"au harma magana kake da wannan azzalumin",katseta ya yi"kinga Umma wayace miki azzalumine ADALI dai ni kinsan me nayi ne to? kuma sakeni nakai kaina aɗorani maganina ma yanzu ke da kika gayyatomu ace namu uban ne ya mutu haka zakiyi kuma mu kalleki wallahi bamu kyauta ba Allah ya baka haƙuri",yana kaiwa nan yaja hannunsa ya bar wurin,wasu jikinsu ya yi sanyi yayinda iyayaen suka ƙara ɗaukar zafi,hanuna yaja mukai ciki yayinda tunkan yama ƴan Dj magana suka kwashe yana su yanasu suka fece ba shiri tunda Alhaji Baffa yaji shiru sai ya yi murmushi ya aje carbin hannunsa adai dai lokacin mukai sallama falon"Habibullahi ɗan Habibullahi Allah ya maka albarka ɗa ɗaya tamkar da dubu","kai Alhaji tsoho ai saika fasa min kai dayawa",Iyyo ce tayi magana"ai yabon gwani ya zama dole maraba sannu da hanya",saki na yayi ya zauna yana amsawa ƙafa na doka aƙasa"ni ka taso ka rakani makaranta inba hakaba dukana za ayi kamanta wannan basu Ya Sayyadi bane da NAke ci musu kashi aka",fasa zaman ya yi ya miƙe"Iyyo bari nayi rakiya kar ataɓamin jikin ƴar Baby","kai Babban Yaya ɗimemiya dani shine ka ke ce min Baby",ƴar dariya ya ɓoye "to Big Girl",dariya nayi muka fita tare har makarantar ya rakani sannan ya juyo gida,da sallama ya tura ƙofar falon ya shiga ba kowa hakan yasa ya wuce ɗakinsa yay wanka sannan ya fito kaya marasa nauyi yasa sannan ya fito falo a zaune ya ganta ko bi takanta baiba ya ɗau wayarsa yana dannawa daurewa tayi tace"wai kai yanzu akan Nana saika karya mutum",wani kallo ya ɗago yana wurga ma ta"da bake nakarya ba shine ki ke tambayata to bari kiji na fiki hauka da rashin ta ido in kika bari na juya miki baya baki da abinda zaki da zai sa na juyo gareki dan haka tashi ki bani abinci ko na sauke kaf fushina akanki wato ku ne masu mana budiri akan ankai mahaifinmu rami ko to daku da naku iyayen kaf kowa sai yaje inda yaje kunyi da ɗan halak zakuga rashin mutunci mara wando wallahi tashi anan kiban abinda nace ko nayi awangaba dake",jikinta har rawa yake ta wuce kitchen tana mamakin shi sai taga kamar abinda take masa baya aiki kalli yanda yake ma ta tsawa kamar bata masa maganin ko kallon banza bazai iya ma ta amma ya rufe ido yanka ma ta masifa baki ta cje tana kaɗa kai, dama an kawo ma ta kaf abubuwan da aka dafa su ta jero ta kawo masa da lemon kwali buɗewa ya yi ya gama kallon abincin"wannan na fatin ne da akai kwasheshi kan nasa ki cinyeshi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 32