Share this page
tana dariya"ke Nana kin shiga uku kalli yadda ki ke faɗin abin kaman shekara shida akai ba kamar yau a kai","to ai ni matsalata kenan bana manta abin arziƙi ma bare na tsiya","to Allah ya shiryeki amma kina mantuwa wallahi",wucewa na yi saida na je ƙofar ɗaki sannan na juyo"na fa haɗa miki kitimurmura zaki sha kira daga gidan ku",zaro ido ta yi"me ki ka min kuma",hannu na kaɗa ma ta agefen kunne na shige ɗaki na kulle,tunani ta shiga yi amma ba ta fahimci komai ba gaka ta wuce ɗaki dan tai sallah itama. : Bayan Sallar isha duk munyi wanka mun sha kwalliya munabfalo har Al'ameen sai gashi ya shigo da sauri yaron ya sauka ya rungumo shi"oyoyo Abbu"aje kayan hannun sa ya yi ya ɗauke shi sama yana juya shi dariya yaron ya yi ciki ya ƙaraso yana sallama sannu da zuwa muka masa kallon mu ya tsaya yi dan mun birge shi sosai,zama ya yi yana ɗaukar sa"kansa ya shafa ubana beyi bacci ba",kai ya ɗaga kawai yana kallona,"daina kallo na kar ace ni na hanaka bacci"dariya ta yi"kai Nana ya da tsarguwa haka ba ke ki ke ta shafa mai kai ba",baki na taɓe"nima dai zan haifi ƴata na huta",dariya ya yi"to shike nan muna jiranki"ta faɗa tana dariya tare muka ci abinci sannan ta ɗauki ɗanta takai shi ya kwanta kayan ciye ciye da ya kawo muka haɗa a ƙasa kan capet muka zauna ti tsiye ni ya yi saina faɗa ma sa me ke faruwa gyara zama na yi"kuma duk wanda ya gyangyaɗa saina watsa mai ruwa",dariya sukai yana dungure min kai. "A yanda Abba ya faɗamin bayan ya bar gida yana iya tuna komai amma ya kasa komawa da fari ya yi wani uban gida mai arziƙi a Niger mutumin har masa na antu gare shi da jiragen sama sanda suka haɗu a basu san juna ba amma daga haɗuwar su ta kwanaki sai ya zama tamkar ƙanin sa wannan mutumi na ƙaunar Abba tamkar ransa dan daga baya in an tambayeshi waye wannan sai yace ƙanin sa ne uwar su ɗaya uban su ɗaya,shi Alhajin yana da ƴan uwa mazauna Marocco,Chadi da Gabia sanda Alhajin ke yaɗa cewa Ƙanin sa labari yaje musu ashe abin da bai sa ni ba dama sun saka ido ne a akan dukiyar tuntuni,su waɗannan ƴan uwa nasa ba mahaifiyarsu ɗaya ba ashe shi Alhajin dukiyar tasa ta mamar sa ce dan ita ƴar sarki ce kuma bayan ta haife shi da shekaru harma ya girma yasan komai sannan ta rasu to dama Baban sa ya rigata rasuwa kunga bamai gadon ta sai ɗanta,su kuma waɗannan ƴan uwa nasa da ganin irin dukiyar daya mallaja sai hankalin su ya tashi suka haa metting akan zasu kashe shi sai ɗaya ya ce a a in suka kashe shi za ace su ne su bari sai an kwana biyu tukunna,sun gamsu da shawarar sa dan haka sai suka kauda kai daga kansa sukai kamarbasu san yanabda dukiya ba suka cigaba da zama lafiya,da yake Alhaji mai tsawon rai ne duk sanda suka shirya kashe shi sai ya tsallake har Allah yasa ya kawo girma bai taɓa aure ba shi kuma tasa ƙaddarar kenan sai dai shi mutum ne mai ibada ga kyautatawa na ƙasa da shi ana haka sai Abba ya fara rashin lafiya sai ya fitar da shi ƙasar waje aka duba shi sai aka ce ƙaba ce,nan Alhaji yasa aka mai aiki ya zauna da shi har ya warke sannan suka dawo gida ba bu jimawa dawowar su Alhaji ya fara rashin lafiya saidai kullum ana kawo ma sa takardu yasa hannu yana sawa n amma baisan na miye ba,kwana kusa sai Alhaji ya rasu hankalin Abba ya yi mugun tashi bayan kwana biyu da mutuwar sa sai ga hukuma wai ana zargin shi ya kashe shi dama ya yi tsammanin haka bai damu ba ya bisu sai dai basu kai shi police station ba sai suka kaishi wani wuri suka ɓoye shi ya daɗe sosai dan yace zai kai shekara sai kwatsam mai bashi abinci yazo yake ce ma sa bafa ƴan sanda ba ne waɗanda suka kamoshi anzo an ɓoyeshi ne dan su tattara dukiyar da Alhajin ya bari sannan su sake shi tofa dukiya an duba ba bu komai Alhaji ya kyautar da ita kuma kai ya ba wa to yau sunce zasu kashe ka ai dole a basu,sai dai shi mai basa abinci yace kuncesa yazo yi ya gudu kar ya damu da dukiya ya tsira da ransa tukunna watarana Allah ya ba shi wa ta,ya gamsu da maganar sa kuɗi mutumin ya bashi sannan ya sake shi ya gudu ta jirgin ruwa Abba bai samu kanshi a ko ina ba sai Algeria da farko a bakin kasuwa yake zama sai ya yi ubangida shine kakan Habib Mama ta bamu labarin sanadin rabuwar aubti haka Abba ya faɗa min amma sanadin kuɗin Abban ba wancan kuɗin ba ne shi Baban Mama in yaro ya shekara yana mai aiki sai ya ware shi ya bashi shago da jari,to Abban ma haka ya masa sai dai shi Abba yana bashi jari sai wani bawan Alkah da suke tare yazo ya same shi da maganar ya bashi bashin kuɗin da aka basa zaisa wani jari amma nasa kuɗin bai kai ba kuma abin da riba,ba tare da shakku ba Abba ya ɗau kuɗi duka ya ba mutumin shi kuma si ya fara kasa dankali anan sukai faɗa da Baban Mama har yace sai ya dawo masa da abin da ya bashi mutane saida suka shiga maganar akace ina ruwan sa ai ya bashi in ma zubarwa ya yi bashi da haƙƙin magana akai da wannan batu ya rabu Abba bayan ɗab lokaci shagon Abba ya zama na kayan gona ana ciniki sosai da sosai ana ƙara wani lokaci ba sai Abba ya ƙara shago ba har guda biyu kuma siya bawai haya ba,kwatsam saiga kuma wannan mutumin ya dawo masa da kuɗin sa da riba ninki biyar na kuɗin daya ba shi anan fa Abba ya gawurta a kasuwa ya zama na ɗaya to wannan shine sanadin faɗan su da Baban Mama har ya rabasu,watarana kawai sai yaji yana son barin wajen sai kawai ya kwashe kayan sa yabar garin ya koma Ghana,sanda Abba ya koma Ghana sai ya haɗu da abokan kasuwancin Alhajin nan take kuwa suka nu na masa karamci aka nema ma sa shaguna har guda shida nan ya fara kasuwanci abin mamaki nan da nan sai ya haɓaka ya yi ƙaurin suna. Waɗannan mutane da suka zo dan kashe shi suka ga bayanan sai mai bashi abinci a kwance cikin jini asibiti aka kaishi bayan ya farfaɗo sai yake faɗa musu ai wannan mutumin ya gudu sunyi farin ciki da fari saida suka koma akan mahukunta su basu dukiyar shi wancan ya gudu sai suka ƙi akace ko bayan shekara ɗari ne in ya dawo zasu bashi abin sa,ba yanda suka iya haka suka tafi nan suka shiga neman sa gari gari gashi basu san ma ɗan asalin ina ba ne da suka rasa shi sai suka haƙura a dole suna jiran ranar ganin sa ai in ya shahara dole za a nuna shi a duniya. Zaman Abba a Ghana ya zama me kuɗi na gaske shekarar sa biyar ya dawo Nigeria da zama sai ya sauka a garin Katsina kan kace me ai ya ƙara shahara fiye da baya,anan ne Abba ya yi aure har mata huɗu zaku ji su ukun ta ya akai ya aure su,amma Hajiya Fulera ya aure ta ne sanadiyar yayanta wanda suka haɗu a Ghana sanda Abba ya fara kasuwanci a Ghana a duniyar kasuwar yayanta shine babba amma da Abba yazo saibya doke shi ya yi niyar kassara Abba ko ya kashe shi amma sai ya gasa ya haɗa metting da sauran ƴan kasuwar dake jin haushin sa,akwai wani babban ɗan kasuwa shi baya zama sai yaran sa dan shi a Marocco yake,to shine yake faa musu kar suyi komai sai ya shigo to sai kuma Abba ma yabar kasuwar sai suka ɗauka aikin su da suka wani boka ya musu shine ya ci,auran Hajiya Fulera sai Abba yake nu na ma ta bashi da wayo shibyasa ta shige jikin sa har ya gane alaƙatar da wannan ɗan kasuwan da ya yi niyyar sakin ta sai kuma kawai ya barta dan yaransu biyu,kasuwan ci ne ya kai Abba Niger nan wani babban lawyer na Alhajin nan ya ganshi bibiyar sa sukai ta yi har suka gano inda yake kwatsam ya dawo Nigeria sai gasu sunzo wannan dukiyar suka kawo baiyi niyyar karɓa amma da ya karanta wasiyyar Alhajin nan sai ya karɓa,tashin hankali kenan dan labari yajewa ƴan uwan Alhaji anga wannan yaron an bashi dukiyar kuma,nan suka shiga nemansa lungu da saƙo ana suka samu mutanen da suka zauna dashi kuma wannan mutumin na Maracco yana da ga cikin ƴan uwan Alhaji amma baisan wancan case ɗin ma da Abban ba ne,shine yayan Hajiya Fulera ya haɗe kai dasu nan suka shiga narka masa dukiya akan ya kula musu da duk motsin sa. Sanda Abba ya ganmu ya yi murna sosai amma matarsa Hajiya Fulera ji tayi kamar tabyi bindiga dan haushi ,Allah sarki Abba rashin lafiya ce ta kama shi aka koma wancan asibitin da aka taɓa masa wannan aikin anan sukai masa allurar nan ba ta fara tasiri ba sai da ya dawo da wata guda Abba yasha wahala jikin sa na ciwo fatar sa Abba yana jinsa kamar me sikila baya bacci baya iya cin abinci amma duk da haka yana ɓoyewa yana nuna ba komai a wannan rintsi ne Abba yaje metting na ƴan kasuwa ta duniya ransa ya yi masifar ɓaci da jin wasu tsare tsare da suke zayyana masa kawai yana buɗar baki sai ya ce ai shi dukiyar ya barwa jikin sa wanda bama a auri uwarsa ba bare a haife shi,abin ya ƙona musu rai tunda manyan alƙalai ne na duniya a wajen takardar shaidar mallaka ya karɓa ya rattaba hannu ɗaukacin dukiyar wajen Alhaji ya barwa jikin sa,sannan ya dawo gida ya kasa mana iya wadda ta rage a wajen sa sannan Hajiya Fulera ko allura bai ba ta ba dan da bakin ta a masa allurar gubar nan kuma ita tasan wa yake burin a aura a haifi wannan ɗa dan tasan ta lalatawa Aunty Hajara mahaifarta,sauran matan Abba duk ya aure su ne ta hanyar hanya su Hajiya Salma kuwa ƙawar sirri ce ta ƙawarta shi yasa suka auri miji ɗaya da sun ɗau duniya da zafi amma sai Allah yasa sukai laushi ta ruwan sanyi,Habeb yasan wannan bayanin kamin kai amma baisan fuskokin mutanen ba,saceni da akai anyi wani abu a murɗe,ƴar ɗan uwan Alhaji mai gidan Abba itace ta sace ni akan tana son Habeb shi kuma baya sonta shine zuwan sa nan da auren Ya Hadiza da ya koma sai ta ga ni anan yake kora ta ma ta harda nu na ma ta hoto na ita kuma saita fara bincike akaina bayan kwanaki sai take faɗawa Abban ta anan ya gano wace ni zugata ya shiga yi ya haɗata da wasu criminal mata nan aka sato ma ta ni a ganin ta ita ta sato ni shi kuma baban ta yana ganin shi ya sato ni,ni kuma ina ganin ni na sato su dan ni na tura musu address ɗin inda nake sanda suka kai ni na shiga ran matar da ta sato ni sai waccan ta fuskanci haka saita raba mu shine ta gana min wannan azabar da cocaine ni kuma na haɗata faɗa da uban ta yanda ko zai haɗiye ƙur ani bazata yarda dashi dan nace mata ba shi ya haifeta ba kuma zai kashe ta ne shine taje ta kwashe dukiyar sa kaf ta gudu shi kuma ya yi mutuwar ɓarin jiki na gama da wannan kenan ɗaya a cikin mutane sha huɗu Hajiya Fulera itace ta biyu na talauta yayanta shine target ɗina na gaba zan tona masa asiri sannan dukiyar sa sadaka ce a gidan marayu dan yasa hannu a takardar da nasa aka kai masa office da sunan ta ƴarin tsaro ce wa dukiyar sa manyan ƴan iskan kuma sanin Al'ameen zaisa sunkawo kansu ba wanda zamu haɗa da hukuma face su ɗanɗani azabar da Abba ya ɗan ɗana,kayi haƙuri Babban Yaya ba a baya ba har yanzu zan ba da raina akan Abba da kuma Al'ameen dan Aunty Hajara a makance aka saka ta a cikin lamarin batare da sun faɗa ma ta tushen komai,ƙazantar dake Abban su da ƴaƴan sa mata da ƙanwarsa ta ɓaci shi ba ya zina a waje sai a cikin gida ashsha yaso ya yi wa Aunty Hajara dan yasan ba shi ya haifeta ba amma Allah ya kareta gata nan ta faɗa ma ka wace ita ni dai kaji iya ba tuna"ina kaiwa nan na miƙe na shige ɗaki a ƙasa na faɗi na rushe da kuka mai tada hankali,haka suma ina jiyo su Aunty Hajara na yi shi kuma ya yi shiru zuciyar sa kamar ana hura wuta. : Kasa ta shi ya yi da ƙyar ta lallaɓa shi suka shiga ɗaki amma ita tafi shi ɓacin rai dan ta daɗe da sa ni amma ta yi alƙawarin gobe saita je gida ta tona ma Abban asiri a gaban Umma koma me zai faru ya faru. UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 BABAN YAYA Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 40 Ranar kwana ya yi kai kukan sa ga Allah,washegari bai fita ba ni kuma ban fito ba ina gado,motsi naji na ɗago kaina ina kwance a gado Al'ameen ke tsaye a bakin ƙofa yana leƙowa"taho mana Babana",shigowa ya yi kamar mai jin tsoro har bakin gadon ya tsaya yana murza"morning Nana",dariya ce ta kama ni kamar ahi ya raɗa min sunan"morning Al'ameen ina Maama na ka?","ta fita da fushi tana sauri",da hanzari na hantsilo daga gadon"da fushi kuma Abbu fa?","yana ɗaki a kwance",agogo na kalla goma saura hannun sa na kama na ɗora shi a kan gado game na kunna masa a waya ta nan ya fara dariya"yauwa My Boy yi game ina zuwa"kai ya kaɗa"thanks Nana"murmushi na yi da sauri na fito sanin ba ta nan na tura ƙofar ɗakin da sallama na shiga yana kwance yana kallon sama idanuwan sa sunyi jajir,"Babban Yaya lafiya?ina Aunty Hajaran fa?Al'ameen ya ce ta fita me ya faru ne",kai ya kaɗa"kai Nana waɗannan tambayoyin fa sunyi min yawa ai",ɗan murmushi na yi naje kusa da shi na zauna"yi haƙuri wallahi duk na ruɗe ne","ta fita na ce ina zata ta ce ba ruwana",da sauri na miƙe"bari na bi ta ni nasan ina zata",baki ya taɓe"kudai ku ka sa ni inda rabon kunsha matsiyacin duka ai kwa dawo",kai kawai na girgiza na fita Al'ameen na kawo ma sa na fito da sauri yau mota ta ga Nana. Tana fita bata zame ko ina ba sai gidan su kuma kowa yana nan a tsakiyar falon ta tsaya tana riƙe da ƙugu cikin ɗaga murya ta sheƙa musu kira"KUUU A HALIN TSIYA",kamar kuwa sun san sunan daya dace dasu sai gasu riii kamar kaji,Umma ce ta ƙaraso wajen ta"Hajara ke ce shigo mana","ina kwana Umma ni ba zama nazo yi ba ina tsohon ɗan tashan ya ke",Abba da ke sakkowa ne ya kalle ta"Hajara dan uban ki ni ne ɗan tasha in baki abinci a gidana kina cemin ɗan tasha",kallon sama da ƙasa tamai"kaban abinci kuma kodai kaci abinci da dukiyar ubana azzalumi macuci",Umma ce ta rufe min baki" a a Hajara babba ne fa",janye hannunta tayi"waye babban Umma?babban macuci ba yana nan tun shekaru masu yawa yana cutarki shi da waccan tsohuwar kilakin",kallon su ta yi ta kalle ni"ban ga ne ba Hajara","Umma Abba da Fulera manyan fasiƙai ne na ajin ƙarshe tun basu san kowa ba kansu suka fara sa ni sun kashe Mama na dan ta gansu suna masha a sun faɗawa Babana hakan ya yi sanadiyar mutuwar sa dama nasan kin san asalina amma ai baki san asalin me ya faru ba Umma Abba shi yake hana ƴaƴan sa zaman aure dan yana fasiƙanci da su yana tula musu dukiya a gabana Umma kinsha faɗar abinda yake musu yana yawa ashe abin da yake aikatawa dasu kenan suma manyan a wakai",wani irin jiri ne ya ɗauke ta sai gata a ƙasa"Umma"suka yo kanta,suna kawo hannu jikin ta ta dakatar dasu"karku taɓa ni Allah ya isa tsakani na daku kaima Alhaji kaje ga duniya nan Fulera kuwa zaki ga sakamakon abinda ki ka min Allah ya saka min",kama ta tayi ta tashi tana kallon Abba"albishirin ka ɗan kwangilar kisa ɗan da ka sa ni na kashe ban kashe ba yana nan yana ta ka ƙasa",wani irin razana yay yi saura kaɗan ya faɗi a inda yake yana bazo ma ta ido kanta ya yo ya shaƙeta sosai saida ya kaita bango Umma ce ta biyo shi tana janshi"saketa wallahi Alhaji mugu"tana kuka tana janshi",cikin kakkausar murya yake ma ta magana"dan ubanki ni zaki tozarta",cikin kakari itama ta ce"eh zan tona ma ka asiri ma a duniya kowa yasan me ka ke su waɗancan ƴan iskan na ka basu nu na maka hoton yaron ba ai Nana ta tura musu kaga suma munafukai ne kenen kuma dakai muƙarraban na ka duk sai kun ɗebi abinda ku ka shuka kuma nasan dakai ka ashe Abban Habib",cikin rawar jiki ya sake ta yana ja ba ya,dan ya razana jin abin da ta faɗa duk da su basu ji ba dan muryar ba fita take ba sosai saboda shaƙar da ya ma ta,wuyanta ta shiga murzawa tana mai Allah ya isa a cikin ranta wayarta ta ɗakko kalli nan Abba"wannan shine jikan Alhaji Habib magajin dukiya mai tarin yawa jiragen sama da kamfanoni ya ku ka iya Al'ameen kenan wannan ɗana ɗana kainuwa kenan",ba bu wanda ya lura ya ɗakko wani ƙarfe fau ya kawo ma ta duka dashi da sauri na hankaɗe ta ya sami kujera sai kowa ya tsorata dan tabbas da ya sameta saiya kashe ta,ƙarfe na riƙe"haba tsohon najadu waɗan da ka kashe a baya basu isa ba ne saika kashe ta itama",ƴaƴan gidan ne sukayo kaina da sauri na fizge ƙarfen hannun sa na ɗaga sama nai kansa,ai da gidu suka watse har shi bin shi na shiga yi"saina kashe ka nima kamar yadda ka kashe min Abba matsiya ci",kamar irin mai haukar nan sai kuma na yi turus wuƙil na juya sai idona ciki na Hajiya Fulera"tsohuwar ƴar bariki ya aka yi ana nan ana jimamin ba bu dukiya ne to ni na kwasheta nai sadaka da ita ko baki sa ni ba ne na kwashe komai na ki naba Aunty Hajara diyyar uwarta da ta ubanta sannan da ta mahaifarta da ki ka sa ta ta lalata ya da magana ne",da yake ita dama ba tsoro gareta ba saita ma tso inda na ke","dan kin ɗauki waccan ƴan tsirarun kuɗin shine ki ke wannan ɗaga kan to kina zaune da dangwalen yatsa ɗaya na lanki komai na shi zai dawo gare mu",dariya mukai har Aunty Hajara"dan gwalen wa kenan Al'ameen wai"kecewa na ƙara yi da dariya"baki san har an ba ni file ɗin ba tun ranar da na haihu"zaro ido ta yi tana ja baya sai tik ta faɗi a wajen,da gudu ni da Aunty Hajara muka fito a gidan motar da ta zo da ita muka shiga fiii muka fe ce". Kanta sukai dan duba me ya sameta nan suka ganta jirkice baki ya goce fuska ta gicciye ido ya ɗaya ya janye ihuu suka saka nan aka cicciɓeta Umma kuwa na zaune a inda ta ke ko kallon su batai ba sai kuka ta ke dana an cuceceta,asibitin da aka kaita kuwa suna zuwa aka tabbar musu ta yi paralyze me mu ni hankalin kowa ya tashi nan aka shiga da fice amma an sanar musu ko ina zasu bazata tashi ba sai dai ta mutu a haka Abba ya fi kowa shiga tashin hankali nan ya shiga kiran ɗan yan shegen da ke Maracco aɓma aka sanar masa gashi a gadon asibiti ya yi paralyze ai Abba faɗuwa ya yi a wurin yana sambatu"kai wannan yarinya Allah yabtsine ma ta wato bama zata kai abin kotu ba shine take kashe mu a tsaye to wallahi itama zan kashe ta kamin tazo kaina",tashi ya yi fuuuu ya fita a asibitin bai tunkari gida ba dan tsoron haɗuwa da Umma ya ke sai ya wuce gidan iskancin sa da ya keɓe. Saida muka hau titi sannan na kalli Aunty Hajara ina dariya"waii ba dan nazo ba da yanzu kin mutu ko kina doguwar suma",dariya itama ta yi"wallahi Nana muguwa ce ke","wane irin mugun ta ko gaskiya wannan sambaɗeɗen ƙarfen da ya sambaɗa miki shi a ka wallahi da tuni kina barzahu in shiga takaba",ɗaka min duka ta yi"sai kace wani namiji zaki min takaba",kai na juya"abar zancen nan haka in ki ka mutu wallahi binki zan dan zuciyata tsayawa tai",haɓa ta kama"kai na ciri tuta ashe Nana masifa na so na",kai na jijjiga"sosaima kuwa kawai ke kin da ce",kwashewa ta yi da dariya"wato ma na da ce ko",horn ta yi aka buɗe ma ta get tana shiga na ce"ina zamu ce munje ne?",kai ta ɗaga sama"ke dai muje kinsan mijin namu muna ƙarya ma zai ga ne kawai a faɗi gaskiya","shike nan",ai kuwa muna shiga suna tsaye a falo sun kama ƙugu waisu sun yi fushi,carkewa mukai muna kallon su suma haka"daga ina ku ke?",sosa ƙeya na shiga yi ina kallon gefe,tunda yaga ina haka yasan bazan faɗi gaskiya ba sai ya koma kallon ta itama saita ce"gida na je mana shine ta bini",girgiza ya yi"ai kun kyauta shine kuka je kukaiwa Abba duka shi da Hajiya Fulera ba ku barsu ba har saida ku ka ga ta daina motsi yanzu gashi nan ɓarin jikin ta ya shanye",saurin kallon sa mukai"duka"har muna haɗa baki wajen faɗa"shi Abban ganɗameme da shi shine ya zabga mana alkazzibu haka shi ko kunya baiji ba ya ce ma ka mun dake shi duk yawan su nasan dai na kai musu raraka dan sun kusa taɓa min Aunty na",dariya ya fashe da ita yana matsowa inda muke"kun mun dai dai ƴan daba na koda dukan nasu kukai amma a yanzu ma kun rage min raɗaɗin abinda dake cikin raina koda hukuma muka je ba abinda zasu mana gwara kowa ya gane kuren sa a ƙarshe kuma sa haɗu da Allah"a tare muka rungume shi Al'ameen ma yazo ya rungume mu,tun daga ranar kullum muna saƙa ya zamu yi har Habib Gwaggo kuma na bamu hasken kai na manyan ƴan duniya dan nasan baku manta Gwaggo Ma'u ba. Bayan wata biyu Hajiya Fulera daga asibiti an turota gida komai sai an ma ta Umma kuwa ta daina kula kowa kayan ta ma ta kwashe ta koma can bayan gidan da zama kowa tsoronta ya ke shi yasa ba a ma ta magana ita kuwa rayuwar nan tafi ma ta daɗi kan tana cikin su dan in tana ganinsu ciwo zai iya kama ta ta mutu lokacin ta bai ba kai zaman nan ma dan ba inda za ta ne to baka da kowa aure shekara talatin da takwas,masu kula da Hajiya Fulera ma Abba ne ya ɗakko su wasu ƴaƴan arna kuɗi yake tila musu shi yasa suke kula da ita amma a bayan idon mutane dukan ta suke suna ranƙwashinta dama arna akwai mugun tar masifa to da haka aka samu sauƙi akanta su kuma ƴaƴan gidan kowa barikin sa ya

Chapter 28 of 32