Share this page
du"da sauri ta kwashe dan yau wani mugun shakkar shi taji tana yi lemon kawai yasha ya kwanta a wurin ya jima ita kuma tana zaune can aka buga ƙofar tashi tayi ta buɗe ashe Hajiya Fulera ce tunkan Hajara tayi magana ta tureta gefe ta shigo falon"kai ɗan marasa mutunci tashi ka aikata ta'sa sannan kazo nan ka kwanta a Ac, ai ni tun ganin farko dana maka nasan cewa shigowarka gidannan ba alheri zai haifar ba sai dai masifa gashinan kuwa alokacin in nafaɗa ba wanda zai yarda kalleka kamar nagari amma mugun nufi aranka ya yi yawa to bari kaji wallahi tunda kajiwa ɗan ƴar uwata rauni to kaima sai waɗanda ka ke so sun raunata ka zuba ido ka gani koba yau ba amma wannan alƙawari nayi",tunda ta fara ko motsi bai ba duk da yana jinta amma ya shareta dan maganganunta basu bashi tsoro ba kwata kwata,ganin bazai kulata ba saita fice tana zage zage,bayan ta fita ne ya tashi yana murmushi ko kallon Hajara baiba ya fice,bayansa tabi da kallo anya kuwa wannan mutumin yana da saiti batasan ta ina zata faraba shi yasa itama tabi bayan Hajiya Fulera . Mama na zaune falo ya shigo da sallama"Habibu kaine ya hanya tafiya haka ba sanarwa kodan Umman ka bata nan ne",zama ya yi yana faɗin"ki daina faɗar haka mana Mama banma san bata nan ba,wallahi tafiyarce ba shiri nayota wancan tsohon ne ya dama min lissafi wai Nana bata lafiya shine fa na ɗebo hanya ashe waɗannan shashashan matan ne kewa mutane hauka agida",kai ta kaɗa"kai dai bari ai waɗannan mutane bansan irinsu ba gashi dai agidan ma kowa ya sauya hali dan inkaji ana hayaniya dama to sababbu ne keyi sai mazajansu amma mudai dama kasan ba yi ake ba Alhaji ya maka hakane dan yasa ka dawo shi inzaiyi musu magana yasan baji zasuyi ba amma daga zuwanka naji ana kajiwa wani ciwo Habib ka daina shiga shirgin mutanen nan","bari Mama ai mai ciwan ma yagane bashi da gaskiya sudai keta haukar su","to nidai ka kula dan Allah kaga yanzu babu Yaya kaine komai nasa kaine madadinsa awurina ka taimaka kadaina biye musu","shike nan Mama insha Allahu","amma Habib yunwa ka ke ji ko?",da sauri ya ɗago ya kalleta zaiyi magana ta dakatar dashi ta miƙe zuwa kitchen abinci mai lafiya ta kawo masa"taso kaci inba hakaba anjima kaɗan ka fara daina gane mutane",murmushi ya yi yana tashi zuwa kan capet ɗin ya zauna"Mama taya akai ki ka gane inajin yunwa","saboda kai da Nana in kuna jin yunwa idonku ciki yake komawa",ƴar dariya ya yi"lallai Mama kin gama sanin mu abincin yaci sosai",saida ya gamaci sannan ya zauna suna hira wayarta ce tai ƙara ta duba Aunty Mama ce dama tare suka tafi Gaya suna da Umma can dangin Umman ɗagawa tayi tana sallama kukanta taji da sauri tayi magana zuciyarta na tsistsinkewa"lafiya kuwa Halima",jin batai maganaba tana kuka saita ƙara ma ta magana"Halima kinsa ni atashin hankali fa meya faru ne",da ƙyar tayi magana"Dada Yaya Sa'a ce ba lafiya tunjiya da muka iso ciwan ciki sai gashi yanzu ta tafi ta barmu ta rasu","innanillahi wa inna ilaihi raju'un"wayar faɗuwa tayi ta miƙe da gudu zata fita Babban Yaya ya bita ya riƙeta"Mama lafiya meya faru"tsabar ta ruɗe ta manta waye Habib bakinta na rawa tace"Sa'a! Sa'a!! ce"wani dam ƙirjinsa ya bada ko bata gama faɗaba ya gane metake nufi saura ƙaɗan ya faɗi ya daure ya riƙe Mama"ki yi haƙuri Mama haka Allah ya nufa",hannunsa ta kama tana kuka sosai,dawowata kenan daga islamiyya na tarda su abakin ƙofar falo ganin halinda suke ciki saina ƙarasa da sauri ina tambayar"Babban Yaya lafiya","jeki kira Alhaji Baffa da Iyyo",da sauri na wuce naje na tattagosu mukazo tare,suma tashi hankalinsu ya yi nan suka fara tambayar lafiya,runtse ido ya yi"Ummace ta rasu Vote Share & Comments Ƴan uwa Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂ 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 chapter 2️⃣0️⃣ "Innanillahi wa inna ilaihi raju'un",gigita da tashin hankali ne ya ziyarci kowa ya yinda wani irin yanayi mai kama da suma naji ya ziyarce ni lokaci ɗaya ya yinda sauran ma hakan take sai a hankali naji su Alhaji Baffa suna salati amma daga nan ban ƙara gane komai ba,zuwa jimawa na tashi a firgice ɗakin ba kowa da gudu na fito ina kuka na tarar da ƴan gidan duk a waje kowa da shiri gasu Murtala atsaye bangaje su nayi na isa ga Babban dukansa na shiga yi ina kuka"wallahi ba haka bane Umma tana nan"janye ni Ya Dijama tazo zatayi ya hanata da ƙyar na daina dukansa na faɗa kansa ina kuka kai kace uwata mahaifiya ce ta rasu tunda kowa ke kuka shi sai yanzu yaji hawaye ya zubar masa da sauri ya share ya kamani na miƙe da uniform ɗina yasa ni amotar sannan shima ya shiga ranar kowa dashi aka tafi ba abar kowa ba sai ƴan mulkin gidan saboda wulaƙanci ko mace ɗaya bata biyo mu ba Hajara ma motar su Iyyo ta shiga dan ko kusanshi ma bata zoba,a motar ma kan ƙafarsa na kwanta har Allah ya kaimu sannan tara ma na dare ta kusa Sallar magaruba da isha suka ja burki sukai sannan suka shigo ciki har an haɗata fuskarta aka buɗe mana Allah sarki tamkar tana murmushi,kuka sosai Mama tayi anan ta kwana a gabanta tana kallonta washegari tun bakwai akai ma ta sallah aka kaita makwancinta gidanta na gaskiya duniya kenan. Kwanan Umma bakwai muka dawo,gidan duk ba daɗi haka kowa yasauya dan rashin Umma ba ƙaramin giɓi bane a ahalinmu mun daɗe bamu saba da rashinta ba sai da ma aka dawo dasu Ya Dijama gidan mu sannan muka ɗan sake bayan Umma tayi arba'in haka Babban Yaya ya koma saidai gidan ba me gane inasu Hajiya Fulera suka saka gaba amman yaransu muna tare koda za a musu faɗa,bayan Umma tayi wata bakwai Alhaji Baffa ya saka ranar su Ya Dijama su biyar ciki harda Ya Hadiza ta kawo bazawari dan ba'ace masa saurayi ba Alhaji Bukar gashi ɗikeke abin bankyan gani amma tace taji ta gani shima Alhaji Baffa ya amince ma ta aka sa ranar da ita murna kamar ta kasheta dan yanaji da ita ga gata yana nuna ma ta kuma yana kashe kuɗi ita da Babarta shi yasa idonsu ya kulle akan shi,sai dai Ya Fatsima shiru har yanza amma Baba kullum yace tana lafiya shi yasa hankalinmu ke kwance. Baffan mu ya dawo zaman gida ya yi retire amma ba ruwansa da kowa bashi da abokan hira sai mu sai Alhaji Baffa da Kawu Nuhu dama su Kawu Iro suna nan da halinsu sai fatan Allah ya gyara. Sirrin dake ƙadan dane da Hajiya Fulera ba wanda yasanshi sai ita. Yau biki saura sati biyu gashi anyi hutun makaranta jiya sai murna muke,ɗinki muka tafi karɓa har magaruba tamana can zoo road bamu dawoba Ya Ashiru ne naga ya tsaya da mota a bakin shagon dariya na kwashe da ita na kalli Ya Nabila nace"Ya Nabi kinga can me ke ne ya biyoki dan kar amasa kasassaɓa ya riga ya ƙulle kunkuminsa",zaro ido sukai kamar na watsa musu yaji"miye hakan kuma ku ke min kallon baƙunta","mun shiga uku Nana dama haka kike waye ya ɗaure kunkumin nasa",baki na murguɗa musu"wancan mana"na nuna Ya Ashiru,kunne ne na Ya Dijama ta kama"Nana dama haka kike kina magana kamar wata yayarmu",ƙwacewa nayi"malamai ƙyar fa nake kallon kowa bari ma kuji Nana ba kalar ku bace da kwanyar ta",ina kaiwa nan na fito ashagon ina dariya"Ya Ashiru ka biyo kayanka ne kar mu maka wasa dashi",baki ya riƙe yana muzurai"ubanki dama baki da kunya to ba kayana na biyo ba Babban Yaya ya dawo ya tarar bakya nan shine ya kaɗo ƙeyata ina masallaci ina addu'a yace nazo na ɗaukar masa ke kinga bani na biyo kayana ba shine da yake tattala nashi wanda sai nan gaba zai samu shime yace nazo kinji yanda akai",dariya nayi ina sara masa na shige motar suma sukazo suka shiga muka ɗauko hanyar gida,dai dai wani restuarant da Babban Yaya ke saya min ice cream mukazo ihu na sheƙa da sauri ya taka burki ya yi gefen titi,duka ya kawo min na matsa jiki murfin motar"keee baki da hankali zaki kashe mu da shegiyar muryarki kamar ta gyare"dariya nayi"ba mai mutuwa sai kwanan sa ya ƙare Ya Ashiru ice cream zaka siya min anan Babban Yaya ke saya min",hararata ya yi"bazan saya ba ko ni Babban Yaya ne ",ya kunna motar muka tafi ana buɗe masa get dama gidan kamar rana dan hasken fitulun na daban ne, Babban Yaya na hango a jikin wata mota shida amaryar tasa yana sanye da jeans da Tshirt sun masa kyau ita kuma tana sanye a rigar atamfa da mayafi kamar wata ƴar budurwa,tun kamin ya gama parking na zunduma ihu ina rushewa da kuka kan ya tsaya fuskata har tayi ja kamar wadda akama bugun tsiya ko aka mammara yana tsayawa na fito da gudu na nufe shi shima da hanzari ya ƙaraso na faɗa jikinsa rungumeni ya yi jikinsa har rawa yake"Nana waye ya taɓa min ke faɗamin",ɗagowa nayi na taɓe baki kamar zan faɗi abin arziƙi nace"ba Ya Ashiru bane mukazo wucewa ta wannan wurin masu ice cream ɗin shine nace ya saya min sai ya dungure min kai wai bazai saya ba inma cikin Babban Yayan gareni sai dai ya zube ko yazo ya saya min da kansa,danace ya taimaka sai yace na sauka nabar masa mota duk abinda zai sameni yasameni in yaso ka mutu",da yake suna bayana suma sun fito kowa aka ya ɗora hannu suna mamakin maganata baranma ta gefe wato Aunty Hajara wadda ta zama kamar sumammiya"fuskata ya tallafa hannu biyu"yi shiru kinji zan saya miki ko ma menene kai kuma ɗan buƙulu sai dai kaga zubewar ciki akan matarka amma ba akan ta ba kuma ba abinda zai meta bare ta na mutu"ya zuba masa ranƙwashi yaja hannuna muka wuce mota da kansa ya buɗe min na shiga sannan shima ya shiga muka fice a gidan,jifff sukaji an faɗi da sauri suka juya sai sukaga ashe Aunty Hajara ce sai zare ido take kamar an kama ɓarawo dama ba shiri take da kowa ba hakan yasa basu kulata ba suka wuce sai a hanya sannan suka fara dariya koda suka bawa su Mama labari suma dariyar sukai dan abin baka cewa nice na faɗa ko Baffa da ba komai yakewa dariya ba saida saida ya dara yana kaɗa kai. Kayan ice cream yamin da alawa kala kala sannan muka dawo,gida ya wuce ya tarar da masifa na jiransa da ƙyar ya ƙwace kansa ya shige ɗaki ganin haka ta gama masifarta ita ɗaya sannan ta wuce ɗakinta ta shiga wanka dake bata da zuciya saita shirya da rigar baccinta ta biyoshi ya kwanta kenan ta shigo yana jinta ta kwanta a jikinsa murmushi ya yi daman yasan haukar ta banza ce ba inda abin zashi musamman da abin yake dare ita kuma yafi komai daɗi awurinta yau ba bacci ya faɗa aransa,ilai kuwa sai wajen biyu da rabi ya ƙwaci kansa ya kwanta yana jinta tana ta mita wai yafiya ragwanta banza ya ma ta danshi bai taɓa gamsuwa da ita ba yana dai biya ma ta tata buƙatar ne. Ni da ita kuwa ban ƙara yarda mun haɗu ba dan inta gano ni tun daga nesa take yanko min daƙuwa dan haka da gudu nake canja hanya ina ma ta gwalo. Ana gobe kamu aka shirya tafiya lalle amma kowa yaƙi biya min dama gidan ya cika da kowa da kowa an hallara,Babban Yaya na hau nema can ɗakin Iyyo nasamoshi suna magana ganina rai ɓace ya riƙo hannuna"Rayuwar Yayanta waya taɓata ne",baki na tura masa"ba lalle duk suka tafi ba amma an rasa me biyamin har amaren sunma yi tafiyarsu",kumatuna ya riƙe"muje na kaiki zasu gane basu da wayo in muka haɗu",da murnata muka fito sai gidan lalle can Fagge dama can muke zuwa tun muna tsohuwar unguwa shi yasa sun sanmu mun saba kuma,a ƙofar gidan ya tsaya muka fito samarin layin sun masa zuru suna kallon haɗuwa ta musamman,"jeki kira min mai lallen nayi magana da ita da kaina"ina juyawa saiga Yayarsu ta fito"a a Nana tsiwa yanzu nake tambayar ina tawajena ne aka ce min banda ke za awa shine nace to ba wanda zanyiwa kuwa gidana ma zan koma","yauwa Ya Aisha ga Yayana yace na kira mai lallen tunda gaki shike nan",fuskarta washe tace"Babban Yaya ne da kansa ai naganeka sunanka ya iso ni tuni",ɗan murmushi ya yi"hakan ya yi gatanan amata nata yafi na kowa kyau"yasa hannu a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙa ma ta,karɓa tayi tana"baka da matsala da hakan amma ba ciki zamu shiga ba nayi aure ga gidana can acan zamuyi namu batare da kowa yagan mu ba kawai dai ka kawo ma ta abinci dan nasan ita ƴar gayu ce ba komai take ciba","baki da matsala a dai fito min da ita",ya shiga mota ya koma mu kuma muka wuce gidan nata,kurkur da dilka tamin sannan lallen iya ja sai wani sample shiba purple ba ba pink ba dashi akai madadin baƙin bayan la'asar na fito kamar amaryar nima fatata tayi wani mugun kyau sai laushi da ta ƙara har wanka tasa ni nayi sannan yazo ɗaukata,ai Babban Yaya kasa gane ni ya yi da kyau shi kansa ya yaba da yadda nayi bama da mukazo gida ai amaren harda dungure min kai saida Babban Yaya ya shigar min sannan suka barni a ranar da daddare mukaje gyaran kai wannan ai muna da yawa sai kasuwa ma mukai amma anga kala kalar gashi. Washegari akasha kamu munsha ankon less a gidan akayi komai dan Alhaji Baffa ya hana wani shagali yadai ce ayi komai agida amma banda waje hakan yasa sai dare aka watse,da safe tun wajen tara ƴan ɗaurin aure sun fara cika gidan abokan kowa da ƙawaye da manyan mutane iyaye da ƴan ƙauye duk sunzo,su Hajiya Fulera ma suna nasu taron daban kaji gulma. Ina saka kaya Ƙarami ya shigo"Babban Yaya na kiranki",to nace amma matsalar ban tambaya yana ina ba sai na wuce part ɗinsa saida na shiga sannan naga basu bane aciki ashe ƙawayen Aunty Hajara ne sun cik ɗakin sai shisha suke sha mamaki ne ya kamani amma saina daina nasan zata iya ma'amala da kowa saboda ƴar masu kuɗi ce itama kuma suma da gani babu tambaya,ido suka zubamin kamar sa cinye ni hakan yasa na juyawa zan fita mukai karo da ita baya nai zan raɓata na wuce saita tare hanyar,wani kallon ƴan iska ta shiga bina dashi"ƙaramar karuwa ya dai ko an biyo shi nan ne aƙara lallatsa masa jikin dan nasan a jikinki dai babu abin latsawa tunda dai ɗan breast ɗin bai wuce ƙuli ɗan tara sisi ba,amma ahaka kike taɓa maza har wani rawar jiki suke in sun taɓaki konace in ya taɓaki dan na lura ke naki karuwancin iya kansa ya tsaya dan kinga yafi kowa haɗuwa ko,to bari kiji bazaki taɓa haɗa makwanci da mijina ba dan iya nawa ne ni ɗaya kuma na masa farraƙu da mata musamman ma ke alƙawarin na kakanni sai dai ya kashe kowa ciki harda ku,ni banga ta inda kika isa awa namiji kamunki ba koda yake tsammani ake jikin naki zai haɓaka nan gaba ba'asan na kasheshi ba a haka zaki ta zama inda kike masa kamu kuma ko pencil bai shiga bare ingarman namiji irin mijina",wani irin duka maganganun ta suke min dama wannan mara hankalin haka take kalla yadda take zayyane ya mijinta yake agaban ƙawaye da alama to halinta kenan,tureta nayi zan wuce ta dawo dani baya"malama sake ni kona kula ki ne",hannu ta ɗaga zata mareni na riƙe"kula kuma dan in kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri wannan fuskar saidai hannun mijinki ya taɓa badai naki ba kuma ki rubuta ki aje yau saina kwana da mijinki koda kuwa a bola ne"na yarfar da hannun nata na fita,wai amma nan jinjina suke ma ta tamin rashin mutunci. Tsabar yadda zuciyata ke tafasa ban nemi kowaba na wuce wajen Iyyo batama ɗakin na kwanta kan kujera Alhaji Baffa ne ya shigo"Nana ta meke damunki haka kowa na waje ke kina ɗaki","Baffa kamin wani abu mana","ME NE SHI ƳAR LELE",tashi nayi na zauna ina kallonsa nace.......................👉👉👉👉👉👉👉👉👉 Vote Share & Comments Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂ 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 PAGE 21 "Kome nace kamin zakamin","zan miki mana faɗi kawai Aishatu",Iyyo na kalla na maida kallon gareshi"NIMA KA ƊAURAN AUREN DA BABBAN YAYA","an gama ƴar lele amma karatunki fa kinsan dai muddin aka ɗaura miki aure dashi bazai bari ki fita zuwa wata makaranta ba","na aminta Baffa ai nayi karatu wanda Allah ya bani nagode inda rabo da hannunsa zaikai ni makaranta","shike nan Aishatu",ya tashi ya fita,kwanciya na koma nayi gabana na mugun faɗuwa ƙirjina har wani ɗagawa yake dafa ni akai na ɗago naga Iyyo ce,zama tayi tana cewa"Aisha kefa kika nema dan haka karki damu nima ina bayanki amma ki kula kinsa kanki a uku",tashi nayi"wallahi ko a ɗari nasa kaina nasa ni kawai ku cika min burina",kaina ta dafa Allah ya miki Albarka tashi maza ki koma cikin mutane",dariya nayi na miƙe na fito Ya Amina na hanga tana bawa su Walida wani abu a leda da gudu na ƙarasa ta bayanta na warce ledar na zura aguje,kanta ta dafe tana dubansu"saiku haƙura uwarku ta ƙwace",dariya sukai"zamu bita ta bamu",suka watse aguje,dariya tayi ta wuce suka bini bansan sunzo ba naji an kama min riga tsayawa nayi ina dariya"ku tsaya mu raba to da alawar madarar za'a shanye ba ni". Babban Yaya dasu Abdallah ne suka zo wucewa yana sanye da manyan kaya shadda gizzinace harda babbar riga amma ta gayu da akeyi yanzu bai ganni ba saboda jan magana na ɗaga murya sosai"Angon yau",tsayawa sukai suna waiwaye na ɓuya ciki yara dariya sukai shi kuma ya girgiza kai suka wuce amma yasan waye,a wajen ɗauri auren an gama na kowa sai Alhaji Baffa ya kalli Baffanmu ya miƙa masa kuɗi rafa biyar ƴan dubu dubu ya karɓa sannan ya kalli Kawu Nuhu ku ɗaurawa NANA AISHA da HABIBULLAHI aure"kallon kallo aka shiga yi"ku ɗaura mana lasifiƙar tamkar an ƙara ma ta zaƙi sanda suka fara,Babban Yaya ji ya yi kamar an ɗura masa ruwa akunne anya kuwa dai dai yakeji ba ɓata akaiba a waɗanda za'a ɗaurawa auren ai bashi",amma ina yana tsaka da wasi wasi yaji fatiha sai fuskokin abokansa dake kallonsa suna dariya tashi ɗaya yaji wani farinciki ya lilliɓeshi nan yaga mutane sun gayeshi kamar shi kaɗai aka ɗaura aure a wurin hannu kala kala ya shiga gaisawa dasu ana masa Allah yasanya alkhairi kan kace kwabo labari ya watsagidan nan al'ajabi ya cika gidan,inacan cikin yara muna rabon alawar madara naji an shaƙeni ta baya watsar da ledar nayi na riƙe hannun koma waye nan yaran suka watse suna kiran iyayen su,da sauri Ya Hasiya ta watsar da kayan hannunta ta ƙaraso iya ƙarfinta tasa ta ƙwace ni da hanzari ina nishi na koma bayanta na ƙanƙame ta ina numfashi da ƙyar sai sannan naga ashe Aunty Hajara ce wani sanyi ne ya tsirga min har ƙafata wato aikin gama ya gama shine taji tazo kasheni ita kuma,Ya Hasiya ce ta daka ma ta tsawa cikin ɓacin rai tace"dalla malama kina hauka ne da zaki ma ta wannan shaƙar ko kuma ita ta ɗaurawa kanta aure da mijin naki to bari kiji wannan haukar taki ba inda zata kaiki anan gidan kuma ki gwada ma ta haka a gabanshi kiga ya zaku kwashe",kasa magana tayi dan ta shaƙa kawai saita fara ɗura ɗuren ashar tana hauka,da sauri Aunty Mama ta ƙaraso ta janye ni zuwa jikinta wani kallon warning ta watsa ma ta nan ta tasani gaba zuwa cikin gida ita kuma aka barta dasu Ya Hasiya da ƙyar ƙawayenta da Hajiya Fulera suka janye ta zuwa ɓangaren Hajiya Fulerar dan tabbas suma abin ya ɓata musu rai. Can ƙuryar ɗaka Aunty Mama tasani"karki kuskura ki fito na faɗa miki kiyi zamanki anan","to Aunty Mama"na faɗa ina fashewa da kuka","kiyi shiru ina zuwa"ta fita,kuka sosai na shiga yi amma wallahi bansan dalilin yinsa ba,tana fita ta tarar ƴan uwan Hajara da sukazo sai zage zage suke amma ƙirmisisi Mama ta hana kowa tankawa kuma hakan akai bamai kulasu daga baya ma sai suka tattara yanasu suka tafi can ɓangaren Hajiya Fulera suka ɗora daga inda suka tsaya anata zugata ita kuma tana daɗa hawa,bai biyo sahun angwayen ba zuwa ciki ya zame ya kira Ya Usaina da Ya Hasiya sukazo can inda ya gaya musu tun daga nesa suka tabbatar yana cikin farin ciki wasu mukulai ya basu ya nuna inda zasu buɗe da kansu zasu san me zasuyi sunyi mamaki amma auka karɓa sukaje can gidansan suka buɗe inda ya gaya musu suka shiga shashin tsan tsar mamaki ne ya kamasu ganin komai na kayan ɗaki aciki duddubawa sukai sannan suka fito"Usaina wannan kayan kuwa ba Abba ne ya tanedusu ba","gaskiya Ya Hasiya nima nayi tunanin hakan amma meyasa to ya nuna mana tun yanzu dan ayanda akai auaran yasan ba yau zata tare ba","hakane Usaina inaga ya nuna mana ne ko in munji za'a siya muce akwai",tafawa sukai"hakane kuma" suna shiga suka tarar Iyyo nata rawa wai burinta ya cika ɗan baƙin ciki sai dai ya mutu,mutane da yawa dariya suke amma banda matan Kawu Iro su sunso ace ƴarsu ɗaya ta aureshi itama ta gaji wannan dukiya,Ya Saddi'q da da Ya Isma'el keta liƙi saiga Ya Ashiru shima ya shiga tayata rawar yana baza babbar riga ciki kwalliya ta gani ta faɗa amaren suka fito nan da nan auka ɗau hankalin mutane aka zagayesu anata hotuna daɗi ya ishi Iyyo Alhaji Baffa ne ya shi har cikin gidan yagansu ƙarewa kallo ya yi yace"ina Nana","tana ɗaki"Ya Ruma ta faɗa"kamarya taya za'a ɓoyeta kamar abin abin munafurci ina uwar tata ne ko da yake tana aiki ke Hasiya, Mabaruka, Fatima Amina ku shirya min ita itama ta fito yanzu ta shiga cikin ƴan uwanta ai kayanta su waɗannan ma amaren shirin basu da irinshi",guɗa Ya Mabaruka tayi"angama tsoho mai ran ƙarfe kuma ka faɗi gaskiya ja ka zauna yanzu zaka ganta. Ina nan inda Aunty Mama tabarni suka shigo da sauri na tashi ina zare ido ƙarasowa sukai fuskarsu ba rahama na zata Alhaji Baffa ya faɗa musu abinda nayi ne ganin zan fashe muau da kuka sai suka kwashe da dariya Ya Fatima tace"su Nana matan aure an shiga sahun mu shekara mai zuwa war haka mu ɗau ɗan mu",wani razanan nan kallo na musu kamar mara wayo sai kuwa na rushe da mugun kuma nai baya na faɗa gadon dariya suka shigayi Ya Mabaruka ta zagayo ta zauna kusa da ni ta dafa ni"ke daina kuka mana ai burinmu yau ya cika dan haka ba kuka zakiyi

Chapter 11 of 32