bayani itama nan take ta amince dan abin ya fara bata tsoro nan da nan ta fito ta shiga shiryani ba jimawa jiniya ta karaɗe asibitin nan wanda sukai waya ya shigo da sauri kayan bacci ne ma a jikin sa yana ganin ya taho ya rungumeshi"me ya faru ne Habib"lumshe ido ya yi ya shiga masa bayani wani irin tashin hankali ya shiga nan likitar ta fito wanda ta gani ne a asibitin yasa ya sauri ƙarasowa"rankai daɗe da kanka","dole ki ganni anan wannan abokina ne na musamman an gama haɗata",kai ta ɗaga yace a fito da ita dukkan su har sojan suka ɗunguma inda jirgin yake musayar number sukai da sojan ya bashi tacan sannan suka rabu yana faɗa masa zaije ya ɗau motar sa yi waya ya faɗa masa wa zai zo ya karɓa, sojanan yana ji kamar zai rabu da ɗan uwansa ne,saida jirgin ya bar wurin sannan abokin nasa ya koma mota.
India
Kamin saukar mu ya kira su Saddi'q hankali tashe suka je madakatar da zamu sauka da motar asibiti suna jiran mu.
UMMU SADDIQ Ce 🌹🌹🌹🌹🌹
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
BABAN YAYA
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
30
A bin da suka gani suma ya ɗaga masu hankali sosai amma da yake ƙwararru ne a kwanaki suka gama komai harma na fara motsi sai dai ban tashi ba,da inda muka baro da gida kawai yace musu ya koma da ni ne saboda wani aiki su Saddi'q ma basu faɗa ba kowa ma sai uziri mai ƙarfi yake kunna wayarsa abokan aikinsa kuwa ransu ya ɓaci so sukai susa a bincike musu jejin ya faɗa musu akwai mai wannan aikin ya baro,kwana na goma sha huɗu sannan ya samu cikakken result a kaina shi yasa ya shibo da sassafe har office yaje ya sameta gurin zama ta bashi sannan ta cire glass ɗun fuskarta ta fuskance da kyau"Sir matar ka ta samu matsala mai wuyar warkewa duk kuwa inda zaka a duniya nan kat inda za ace kuzo to muma mun bincika da wuya mahaifarta ta iya haihuwa duk kuwa sanda kuka gantaa da ciki to ku kawo mana ita nan",lumshe ido ya yi yana jin wani hawaye na taruwar masa girgiza kai ya yi sannan ya buɗe idon ya sauke kan likitar"ba komai Allah ya bata lafiya","kuma kota warke ka bata saman wata huɗu saboda wajen a kwai duk sanda aka taɓa shi jini zaina fita kuma hakan yana iya kai barazana ƙwaƙwalwar ta amma a wannan wata huɗu komai nata ya zama normal","ba matsala Dr","zaka iya shiga ka ganta",tashi ya yi jikinsa a sanyaye ya wuce ɗakin da nake,ƙofar ya turo ya ahigo Ya Saddi'q ya gani a tsaye ya nale hannu a ƙirji yana kallona komawa ya yi da sauri,Ya Saddi'q da yaga fitar ya fito shima"Babban Yaya ya ka fito ai ni ba haushin ka nake ji ba bafa laifinka bane",joyowa ya yi"nasan da haka Saddi'q in naga Nana a kwance a wannan hali bana iya yafewa kaina","ka bara wannan maganar ka shiga ka ganta ai tana samun sauƙi",ba yanda ya iya haka ya shiga ɗakin amma ba ya iya tsayawa ya kalleni da kyau,da haka na ɗebi wata biyu sannan na buɗe ido ganin su Ya Saddi'q sai na fara kuka dan ban manta komai da gudu na tashi Ya Saddi'q ya riƙe ni"ina zaki kuma",duka hannunsa nayi"ni ka sake sun kashe shi ko dama basu da imani ai wallahi saina rama",wani irin abu ne ya taso ya tsaya masa a wuya yana kallon ko me nake ta wayar gaban aljihun Ya Saddi'q dan shi bazai iya zuwa inda nake ba,kokawa sosai nayi dashi saida ya nemi cin ubana sannan na haƙura na zauna"wa yace miki ya mutu yana nan bazai iya zuwa inda ki ke ba ne ya kasa yafewa kansa akan shi ya miki haka madadin ya fanshi ke da ransa to bazai iya tsayawa wani ya miki haka ba yana raye"ara volume wa kukana nayi "to ai ni nace ya yi me yasa zaice haka ni na yafe masa dan Allah kuce yazo",ina duk wannan abu da ake har na koma gidan su da zama bana ganinsa kuma kome zanyi inje wajen aikin ma bana samun ganin sa kuma kowa yace yana nan ko ace yanzu ya fita a haka na ƙara wata biyu.
Tsaye nake ina saka kayana a akwati ga tiket ɗina a gefe zan koma gida sai kuka nake dan har yanzu ban samu haɗuwa dashi ba,bayan na gama haɗa kayan na ɗau fayafina na saka na janyo akwatin a ƙasan bene naga Ya Saddi'q yana jirana sakkowa nayi muka fita agidan ƙala baice min ba bare yace nayi shiru,a haka har airport tare zamu taho da Ya Saddi'q shi yasa muke tare a jirgin ma kujerar mu ɗaya,muna zama ya ɗago kansa daga sadda shi da ya yi ashe shine a kujerar bayan mu bamu sa ni dukkanmu,duk wannan tafiyar muna tare har Allah yasa muka sauka lafiya Ya Ashiru ne yazo ɗaukar mu a yadda ya ganni jikinsa ya masa sanyi da muka zo gidan ma da kukan na tasa su na yashi hankalin kowa na gidan,dalilin wannan kukan tashin hankali suke nema na kuwa bayyane musu kome kowa ya ahiga tashin hankali sukaita kuka suna min sannu ni ina au nemo min mijina haƙuri suka shiga bani da na dangana zai dawo komai daɗewa nafa san halin sa in ya yi zuciya kwana na uku a gidan na kwashe kayana na koma ɗakina.
Wata sabuwa...🙄🙄
tunda na koma gidan bana kula kowa iyakata makaranta sai in dafa iya abinda zanci ganin haka ya sa matar gidan fara shiga shirgina kamar dai yau riga ta siket ne a jikina sun min in ka ganni baka cewa nice na ƙara dau komai ma na daina sha amma jikina kamar ma ƙara tura shi na ke ta gabanta na zo na wuce kitchen na dafa abin da zanci na dawo zan wuce naji saukar muryar ta"keee ƴar bariki kalli yadda ki ka bige min ƙafa",ɗan dakatawa na yi nai dam sai kuma na wuce bance ma ta uffan ba dan nasan neman magana ta ke ba bu abin da na ma ta,saura kaɗan na shiga ɗaki naji ta tankaɗa ni gaba da hanzari na dage ban faɗi ba na ƙarasa shiga ɗakin na turo ƙofa ta na kulle na zauna naci abinci na na ƙashi sannan na fito maida kwanon tana gani na saita miƙe"ke wallahi zanci...","kutumar uban mu ni da ke Hajara"na juyo da zafina na faɗa ina ɗaga ma ta hannu,wani tashi ta yi tana nu na kanta"ni ki ka zaga Nana",gyara tsaiwa na yi"eh na zaga rama dan Allah",kaina tayo da dukkan ƙarfinta na ɗiba da gudu na shige ɗaki ina kulle ƙofar,dukan ƙofar ta shiga yi ba ji ba ga ni amma na shareta na shiga hidima ta,daga haka saida nai kwana huɗu bana bari mu haɗu.
Bayan sati uku
Abin ya ishe ni haka nan ba bu Babban Yaya ba bu labarin sa amma ita naga ba ruwanta nice dai nakai maƙura a damuwa har na fara zazzaɓi wanda saida ya kai ni ga kwanciya a asibiti kowa abin na basa mamaki saboda Babban Yaya na zama haka kwana na biyu aka sallameni.
Washegarin sallamata ban tsaya gun kowa ba na koma ɗakina da sassafe nayi shirin makaranta na wuce,an fito break na samu can kusurwa staff room nan ne ba hayaniya nayi zamana,monitor ɗin mu ve tazo"Aisha kije inji pc","ok Fatima",na tashi na nufi office ɗin da sallama na shiga wani irin dam naji a ƙirjina,Babban Yaya zaune kan kujera yana murmushi,murza ido na na yi na buɗe na ƙara ganin sa mintsinin kaina nayi na ƙara ganin sa,wani irin kuka na saki na nufe shi da gudu na faɗa kansa na cukwikuye shi gaba ɗaya a hijabina ina kuka kamar ana min duka,ƙara rungumeni ya yi sosai"am sorry Nana",a fusace na ɗago na rufeshi da duka"ni ban haƙura saika faɗamin me yasa ka guje ni",bai riƙe hannuna ba ya barni nayi na gaji na ƙara rungumeshi,wani irin hawaye ne ya zubo masa yasa hannu ya share akan idon pc hakan ya faru,zaro ido tayi"rankai daɗe wannan karatun yaufa bazai yiwu ba ɗauki matarka ku tafi gida kayi lallasshin acan",kansa ya ɗan shafa"to Madam nagode sosai,kama ni ya yi na tashi tsaye fuska duk hawaye na kalleta nace"Mommy sai wani satin",daga shi har ita dariya suka saka tace"to Aisha kin ɗau hutu kenen ko"sunne kaina nayi a bayan hannun sa ina kaɗa ma ta kai"to Allah ya kaimu",hannuna cikin nasa muka fito kowa kallon mu yake amma ni ko ajikina.
Sanda muka isa gida su ashe sun san ya dawo direct muka wuce gidan mu Aunty Hajara an tafi yawan barbaɗar ba a dawo ba tunda muka shiga na dasa kuka ina bori ya rasa ma ya zaiyi da ni tashi ya yi ya maida ƴar saman rigar sa"to bari na koma tunda bakya son ganina dama na sani",ina kallon sa yaje bakin ƙofar da gaske dai naga fita zaiyi da gudu na tashi nabi bayan sa kan yakai ƙofar na faɗa bayan sa na rungumeshi sosai na ƙara fashewa da kukan"dan Allah karka tafi mana",dakatawa ya yi"to daina wannan kukan ko na koma sai na shekara ban dawo ba",kan ya rufe bakinsa nayi ɗif sai a jiyar zuciya nake",jiyowa ya yi cak ya ɗauke ni"ƴar lukuta ta haka ki ka ƙara zama",kwantar da kaina nayi a ƙirjinsa"Babban Yaya me ya sa zaka min haka ka tafi ka barni bayan kasan bazan iya rayuwa ba ba bu kai",bakin gado ya ƙarasa ya zaunar dani yana zare hijabin jikina bina da kallo ya shiga yi a hankali ya shiga zaren kayan makarantar"inyee ta Babban Yayan ta ba kice mun girmi half best"binsa da kallo na shiga yi nima Babban Yaya yabrame sosai sai tsawon sa daya ƙara bayyana sosai lura da kamar baya son maganar da nake sai na barta na shiga biyewa maganar da ya ke"eh mana baka yanda suka zama ba sai bashin susar ƙaiƙayi da suke bin ka",rigar jikin sa ya fara cirewa"su sha kurumin su duk abin da suke ji dashi nima ina ji da shi",da sauri na miƙe ina ja baya rigata dake kusa na ɗauka na kare ƙirjina girgiza kai nayi"ina wannan susar banda yau shugaba ka manta ba girkina ba ne",daina abin da yake yi ya yi ya min zuru,murmushi ya yi"zo nan Nana","to tsaya nasa riga kar Aunty Hajara tazo ta ganni a haka ta zargi wani abu",ina tsaka da saka rigar naji bam an banko ƙofa banyi zato ba naji saukar muryar ta"to ƙaramar kilaki ya dawo ɗin kenen shine ki ka saka shi a ɗaki saboda tsabar ƙwarewa a satar kwana har kin fara tuɓe riga wallahi kina ba ni mamaki ƴar yarinya dake amma kin daɗe da sanin daɗin namiji",wani baƙin ciki ne ya kama ni kamar zanyi kuka amma na shanye ya yinda shugaba yana tsaye ya zura ma ta ido kan nayi magana ya riga ni",kin gama zubda girman?",juyowa ta yi kansa"kamarya zubda girma?"ta faa tana wani girgiza,cire hannun sa ya yi a aljihun ya nu na ta zai yi magana na saurin shan gaban sa na riƙe hannun lumshe ido nayi na ɗora hannun kan breast ɗina"kayi haƙuri ko dan waɗannan sunyi kewar ka ne sosai kasan sun saba kai tun kan nazo nan yanzu ma suna son su gaisa dakai ne shi yasa da ganin ka suka fara ƙaiƙayi amma sun haƙura suma sai ranar su sa samu biyan buƙatar su yanzu dai"na cire hannun na kamo nata na haɗa da nasa"kuje can ka ƙaiƙaya ma ta kasan na manya basa jure rashi kamar namu na yara su nasu yanzu sai ya fara zuba",ina kaiwa nan kamar yara na jasu zuwa ƙofa na tura su waje na saki hannun su na kulle ƙofa ta.
Tsaye ya yi a wurin ya ma rasa me zaiyi dariya zaiyi ko haushin abin da Hajara tayi zaiji,sharewa ya yi ya cire hannun sa anata ya bar wajen zuwa ɗakin ta.
Ina rufe ƙofar na jingina a jiki sai maida ɓacin ran nake da ƙyar na samu na dawo hayyacina na wuce ciki na watsa ruwa na dawo nayi zamana ji ma nake me yasa na dawo a makarantar ko da yake ido na ya rufe a lokacin na manta ma da ita a gidan,a ɗakin nai ta zama har sallar magaruba dama ina da abinci a ɗakin sai sallar isha sannnan nayi wanka banyi kwalliya ba sai riga mara hannu da na sa roba ce kuma da kaɗan ta wuce gwiwa duk rabin ƙirjina a waje yake humra mai sanyin ƙamshi na shafa gashina na ware ya zuba a bayana,a gaban mudubi na tsaya na gama ƙarewa kaina kallo murmushi nayi na ɗau pink jambaki mai ƙyalli na rambaɗa sannan na fito da zummar ko da suna falon inyi ba wurin su nazo ba,ilai kuwa suna zaune kan dining a raina nace,'wato abincin ma ba zaki kira ni naci ba ko to wallahi saina ci koda uban ki ke yawo',tun da na fito ya zuba min ido kamar zai haɗiye ni,ita ma ganin ya raja a a kallon wani wuri ta ɗago taga me ne sai ta ganni wani dam taji har ranta nan baƙin ciki ya kamata wai yarinyar nan me take sha ne take zama haka kalli ƙirjinta ai dole namiji ya kalleta,hannunta ta miƙa ta juyo da fuskar shi gareta ƴar dariya ya yi kawai dan abin nata dole ya ba da dariya nan kishi ne kenan,bankula su ba nai shigewata kitchen bayana ya zubawa ido mamaki duk ya kashe shi wai yaushe na zama haka bai sa ni ba,saboda neman fitina da sanin me na taka ban sawa tukunya komai ba na ɗora ta na kunna gas ba jimawa kaɗan na kai hannu na taɓata tukunyar ihu na kwaɗa na janyeta,dama kamar akan gwiwa ya ke da hanzari ya miƙe zuwa kitchen ɗin ina ta yarfe hannu da tsalle"mijina ka taimaka min hannuna"a gigice ya shigo kaina ya nufo duk ya gigice"Nana me ne ne?"da sauri na ƙaraso na faɗa jikinsa na ƙanƙame shi ina kuka"hannuna! hannuna!! Mijina",kai kanajin wannan ihun kasan iskanci ne tunda taimakon ma akwai wanda na zaɓa ya kawo min shi,ƙara ruɗewa ya yi ya ƙanƙame ni sosai"me yasa mi hannun naga"ƙi nayi ya gani sai kuka nake ina burbuwa a jikinsa ɗagoni ya yi daga jikinsa ya zubawa fuskata ido bakina sai walwali ya ke haka ga hawaye sai zuba ya ke rasa ya zaiyi da ni ya yi kawai ya sunkuyo kansa ya ɗora bakin sa kan nawa ware hannuna nayi na rungumeshi,shigowar ta kenan ta yi turus ganin meke faruwa wani irin hawa ta shiga yi ina kallon ta amma nayi kamar bana ganin ta saida ya jima yana ssarrafa bakina sannan ya ɗago kansa yana bin fuskata da kallo,murmushi nayi shima haka"yadaina ko",dariya nayi"ba dolensa ba tunda ga ingataccen maganin sama yawa ƙasa aiki ai dama abinci nazo zan ɗora",kamo hannuna ya yi"ga abinci can zo muje kici",ya kamo hannuna zai ja ni na turje"ban zuwa ko ina da ba kunsan dani ɗin ba ku ke zaƙalƙalal abin ku baku kira ni ba",saki na ya yi ya kama kunnen sa"sorry Aunty"kama kunnen na yi"da fatan bazai kuma mantawa da ni ba",haɓa ya kama"shi ya isa wane shi amma a mai a fuwa yau ɗaya",dariya na kwashe da ita"kai Babban Yaya kana da abin dariya wallahi",tashi ya yi daga ƴar risnawar da ya yi"tunda kin haƙura muje",muna juyowa muka ganta kame da ƙugu ko tun yaushe take oho saida ma mukazo dai dai ita sannan yace"muje mana"wani a jiyar zuciya ta saki sannan ta wuce,a dining ma tsokana ta hana naci abincin sai da ƙyar yamin jan ido naci anan na barsu dan kar ma ya biyo ni sai nace"saida safe iyayen gidana"ganin na faɗi haka saita saurin cewa"Allah ya kaimu"shi kuwa ya bi ni da kallo dan yasan me nake nufi sallamar.
Bayan kwana biyu ras na rayu da su duk salon Aunty Hajara na ta ɓata min wai tanawa Babban Yaya abu a gabana dan naji haushi saina wanke mata kai ta hanyar nu na ma ta ita da mijinta miye nawa da zanji haushi abin da ke ƙara ƙular da ita da ni kenan,a kwana biyun nima na shiryawa mijina ras dan ina karɓar shawar wari daga mutane daban daban shi yasa nayi nawa shirin na musamman nima yanzu ai ba yarinya bace nasan komai,dan haka tun sha biyu na shiga kitchen na haa abinci mai lafiya har biyar saura sannan na gama dama yau yaje office sauri sauri na shiga nayi wanka na haɗe cikin material dack brown nayi kyau dama na wanko kaina dan haka saina sauke gashin na ɗaura ɗankwalin akai humra kala daban daban na shafa nan da nan na ɗau ƙamshi gama gyara wurin dana ɓata nayi sannan na haɗa ruwan wanka na fito kenan a toilet nagan mutum tsaye yana tuɓe riga murmushi nayi"oyoyo Babban Yaya",naje na faɗa bayan sa,lumshe ido ya yi dan tabbas wannan ƙamshin ya shige shi sosai,kamoni ya yi na dawo gaban sa ya rungumeni sosai kaina na ɗago zan masa magana yay saurin ɗora bakin sa kan nawa lumshe ido nayi jin yanda yake sarrafa harshena tsaiwar gagarar shibtayi saida ya sada mu sofa sosai ya samu nutsuwa da hakan sannan ya zare bakin sa a nawa ya sumbaci goshina banyi magana ba na jashi yaaɓ shige toilet dan ya watsa ruwa,bayan ya fito yana ɗaure towel da kaina na ta mashi ya shirya sannan na jawo shi falo har dining ganin bata falon yasa nace masa"zan kira Aunty Hajara",kai kawai ya kaɗa min dan yau na lura a zumin magana yake,tana baje a gado na shiga daga bakin ƙofar na tsaya"ki zo kici abinci"wani kallo ta ɗago ta watsa min"bana ci bar nan mayyar maza",maganar ta ɓata min amma sai nayi murmushi"ba laifina bane mijinki ne ya saba latse ni tun bansan wace ni ba kinga dan na manne masa ai ba aibu"ina kaiwa nan na fito na barta mamaki amsar dana bata take ina zama sai gata ta fito ko kunya ba taji ba ta sauya riga zuwa wata ƴar ƙarama mai hannun best murmushi nayi kawai a raina nace'wannan matar sai na ma ta bariki da farar rana sannan zata kiyaye ni inaga'cije baki nayi na fara zubawa kowa abincin saida na gama na zuba nawa kaɗan sai naman dana kusa juyewa yana kallona kawai yana murmushi yasan halina ina ƙaunar nama,a bazata naji muryar ta"ke me yasa bakya da aiki saicin nama kamar kura",da sauri ya ɗaga kai ya kalleta zaiyi magana na girgiza masa kai sannan na kalleta ina murmushi"ke bakyason nama to wallahi ki canja tunani dan nama abinci ne na haƙika musamman ki samu ƙashi wanda yay laushi ma ana yaron nama wayyo kina cinshi yana danƙo danƙo sai ki gama ci bai bushe ba haka ƙashin ma in kina buƙata ki taune ƙashin ki ma haɗiye shi amma in nama ya tsufa ko ragone ga wuyar dahuwa ga ta ci gashi ya bushe ƙayau saima kayi ƙoƙarin ɗanyata shi da yawun bakin ka sannan yake ciwuwa kan ka gama kayi tilis kaji haƙoranka kamar ka bada a jiya",banyi shiru ba naji ya fashe da dariya ni kaina nayi mamaki bare ita datai dagalo tana kallona a magana goma bata fahimci rabin ɗaya ba sai dai tasan duk yanda akai baƙa na yaɓa ma ta,mutmushi kawai nayi"Aunty Hajara in baki gane ba kiyi bayani bawai kiyi shiru ba",da sauri ya katse dariyar"ci abincin ki zan sa ma akawo miki frig na je nama",miƙewa nayi na daka tsalle na juya na ƙara juyawa ko ina nawa saida motsa kansa nayo na zauna a cinyar sa"yau kana da babban tukwici fatan kana da wurin ɓuya"kai ya ɗaga yana murmushi sannan na tashi na koma mazaunina na fara yagar tsoka,yana ta kallona ganin ya raja a akallon wani wuei itama ta kalla rabin ƙirjina ne ya fito waje saboda motsin da nayi ɗazu,wani irin haushin shi ne ya kamata ƙiri ƙiri taga alamar zalamar wannan ƴar jariyar a tare dashi murmushin ƙeta tayi a ranta ita kaɗai tasan me take kitsawa'zan lalata wannan daren yau sai dai wataran amma ba yau ba',ba hamagiya a tunanin ta yau ne farko batasan Niger aka barwa wannan tarihin ba,muna tsaka da cin abincin aka ƙwanƙwasa ƙofa da kansa yaje ya buɗe aka shigo labulen dining na ɗaga"Ya Hadiza"na faɗa da ƙarfin masifa saida ta toshe kunne,da gudu na taso na ɗane ta tana dariya"kau Nana karki karya ni"dariya nayi"wane ni na karya matar Alhajin Abuja masu ci ta bayan hannu",dariya tayi tana dafe kanta,dungure min kai tayi"wallahi Nana kisan abu ma matsala ne",kwashewa nayi da dariya na kama hannun ta muka zauna a falon,Babban Yaya ya yi saƙare wannan amintar da yaushe aka fara ne bai sa ni amma sai ya bincika akwai lauje cikin naɗi,"Dije ba magana ne"juyowa tayi"afuwan Babban Yaya wannan tsiwar ce ta ɗauke min hankali ina kwana au ina wuni","kwanan dai Hadiza","a a Babban Yaya wunin dai",gaisawa sukai ya koma dining,tashi nayi na kawo ma ta abincin da lemo da ruwa sannan na ɗauko nawa,kalla ta yi"na shiga uku Nana halin na nan",juya ido nayi"saima abinda ya yi gaba Ya Hadiza ke dainci naki ki ka biye ta ni baki ƙoshi wallahi",dariya ta yi ta fara ci,tsagal na aje nawa kwanon na kama hannunta"Ya Hadiza ina da tambaya",tsorata ma ta yi"kai Nana kin ba ni tsoro wallahi tambayar me",dining na kalla gama muje ɗaki",kai ta kala sannan muka cigaba da cin abincin shegen zance na ƙwaƙulata,bamu gama ba Aunty Hajara ta taso ta wuce ɗakin ta da kallo Ya Hadiza ta cike da mamaki goɗoɗo haka da irin wannan shigar ko girkin ta ne ai bai dace ba amma sai dai ta yi shiru dama aranta take kitsa haka tana gamawa na kwashe kwanukan nakai kitchen shi Babban Yaya ma fita ya yi mukuwa muka shige ɗaki harda kulle ƙofa.
Kan sofa ta zauna tana ƙarewa ɗakin kallo"kai Nanata kin samu ɗaki amma fa ya yi kyau",kusa da ita nazo na zauna"wa ya ga ya miki ɗakina ne nan to kinga part ɗina can wannan ƙallagaggiyar matar ita tasa aka dawo da ni nan","ban gane ba da wajen ki kuma adawo dake cikin part ɗin kishiya","eh mana to ai ita ta nema ni kuma nace na amince darajar su Alhaji Baffa","eh haka ne kam nima jiya mun dai daita dashi da Iyyo","kai amma naji daɗi sauranki miji gangariya kiyi auren ki tunda bazawara ai bata wuyar auruwa","haka ne kam Allah ya kawo nagari to","ameen ameen yauwa tambayata fa",juyowa ta yi muna fuskantar juna"ina jinki Nana","yauwa nace ba kinga wannan matar ko kullum sai tana zaƙewa ita miji nata ne kalleta fa yau girkina ne amma tayo wannan shigar",ƴar dariya ta yi"eh mana ai haka kishiya take kullum sobtake tana nuna miki ta fiki a wurin me gida","to ya zanyi ne in yiwa Babban Yaya abin da ko gilmawa ta ya gani sai yaji ni kawai yake da buƙata",zaro ido ta yi"Nana ai wannan lamarin da wuya zaki iya kuwa","wallahi zan iya faɗa min kawai","to shike nan kinga wannan al amarin na kwanciyar aure sai kin daure karki na zama raguwa da yawan ƙorafin kin gaji ya kasan duk sanda yazo wajenki kina maraba da shi",fannin rikita oga fa","eh shima abu ne musamman dole saikin cire kunya ya zama duk abinda ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 32