yi wanka yay nafilarsa sannan ya kwanta awajen ba jimawa ya yi bacci,itama wanka tayo ta sauya kaya jin shiru bai zo ba yasata lallaɓowa ta leƙa ɗakin da take tunanin shine nasa ganin yana bacci sai tayi mirmushi sannan ta koma ɗakinta ta kulle wayar yayarta takira,tana ganin kiranta tai saurin ɗauka itama"gaskiya Yaya ke dabance wallahi baishigo ba ya yi baccin kuma","ai dama na faɗa miki malam ya iya aiki wannan baccin haka zaina yinsa har kwana bakwai sannan angama miki aiki saiki bashi dama akwashi amarci da hujja yana kwanciya dake to kin gama mallakarsa kowa sai abinda kika aminta sannan zaiyi kinga kema saiki sami rabonki tunda shi yanzu ɗan gata ne gun mahaifinsa komai bashi zaina yi","ai fa na aminta dake dan haka duk rabon dana samu tare zamu raba",kamar ba amarya ba haka sukaita hira sai can dare sannan suka kashe wayar Yayar nata ma ta dariya aranta dan ita kaɗai tasan burinta kan Hajara.
Bayan kwana goma ban ƙara tsayawa Babban yaya ya ganni ba kuma saiya shigo gidan su kansu basu san ina nake ɓoyewa ba yauma sallama ya shigo zasu wuce india tare amma inaji naƙi fitowa har suka fita gidan itama ranta ƙal farraƙunta ya yi aiki kenan,yana fita na fito a bayan gadon ɗakin Aunty Mama na zauna nasha kukana sannan na fito ban kula kowa ba na wuce wajen Iyyo ta,itama ɗin bacci ma take sai kawi na haye kujera na kwanta nima.
Tunda suga shiga jirgi baya umm baya ko motsin kirki gaba ɗaya ransa aɓace yake wato dai da gaske ƴar yarinyar nan daya raina kishi take,har suka sauka baya magana sai in ita ta masa gidan da suka sauka ma ya ruɗa Hajara ashe nan ma agatan daya fi nacan yake,Soyayya sosai take nuna masa ko maganar Nana baya ma ta hakan ya tabbatar ma ta ya manta ma da ita har suka ɗebi watanni acan.
*****
Dukkan bin malamai da zuwan gidan Ya Fatsima da Ya Hadiza keyi sai a sanar ma ta bama asan wa take nema ba haka duk wanda ta tambaya baya cewa yasan shi kuma bayan da duk tare suke ita tasani,tashin hankali ta shiga sosai har Umman amma ba yanda zasuyi dan suna magana za'ace da wata a ƙasa shi yasa sukai shiru malamin kuma ya musu alƙawarin wanda ya fishi zaizo,shi yasa suka sakankance ita kuma tana ƙara botsarewa da buɗe ido cikin ƴan bariki.
*****
Basu jima da tafiya ba na shiga SS ONE,amma karatun yana tafiya ne da tunanin Babban Yaya,saidai ba wanda ya gane kai saika ɗauka mantawa nayi dashi.
Yauma ina saka kayana asif Aunty Mama ta shigo"wato ke Nana kishi ko to kiyi sake fadar taki da take hannun Yayanki duk waccan ta haɗa ta ƙwace bakisan wannan burus ɗin da kikayi bashi da alfanun komai sai nesanta kanki da kikayi dashi kalla fa kin fara girma amma kin nesanta kanki da wanda zaki je hanunsa watarana ki dai yi karatun ta nutsu kina wayo ai",tana kaiwa nan ta fita ta fita tabarni,to tun daga ranar kullum saina masa text a wayar Aunty Mama amman in ya kira bazan ɗauka ba,hakan daya gani ne yagane magana dashi ne bazan ba kawai ya bari muyi ta magana ta haka nan dan nan farin cikina ya dawo shima haka nan nacigaba da ƙulla tsiyata dan saima abinda ya ƙaru tsakanina da duk wanda yace bazan iya ba kullum faɗa amma naƙi dainawa gashi Iyyo tayi Allah ya isa ga duk wanda ya dake ni ko bayan ranta waifa ita nan Babban Yaya ta wakilta shi yasa wai takeji dani wannan jin to na mutum biyu take yi.
Tunda suka zo sai a wannan lokacin ta lura yana cikin farin ciki sosai kuma yana bata dukkan kulawar da ta dace,shi yasa kaf ta allaƙa hakan da aikin malamin su,yauma yana dawowa yake sanar ma ta tashirya sati mai zuwa sazu koma tunda komai ya gamu sannan kowa ya kama aiki cikin kulawa da cikakken tsaro da ƙasar ta basu,bataji daɗin hakan ba amma dolenta tashirya dan tana gudun yin wani da zai ɓata nasa rai yanzu zai birkice kamar wani mai iskokai.
*****
1:30 muka tashi a makaranta dan haka a ƴan mituna na shigo gidan takalma na gani a ƙofar ɗakin Mama sai na shige ɗakin Aunty Mama a kujera na jefa jakar haka hijabin nima na bisu ina faɗin wash"sannu Darling sis"naji maganar sa bagatatan da fari tunani na zaunayi wake tsokanata ko Ya Ashiru ne sai dai na daure na kalli gefe"Babban Yaya" na zuba uban ihu na juya na haye kansa ina ihu"zaki karya ni fa ƴar afiruwar Aunty","wayyo Allah yaushe ka dawo","kina makaranta shine nai zamana nan sai naganki zan fita","wayyo tsaya ni mu fita tare dan Allah","to ina jiranki"ɗaki na shige da gudu na faɗa banɗaki ruwa kawai na watsa na fito na saka doguwar riga da ƙaramin hijabi na fito"kai harkin gama","ƙwarai makuwa har wanka nayi fa",haɓa ya riƙe "ainasan ki sarai da tsaka tsaka mi",ƙafa na fara dirawa aƙasa"amma kasan ina wanka ai",hannuna ya riƙo"farin sa ni ma kuwa to muje",tare muka fito"Mama mum tafi gidan Yaya"da sauri ta kalleni shi kuma yana musu sai anjima suna amsawa,Mama dai banda kunyarsa da tace bazani ba dan tasan sarai sainayi wani abin kuma ta lura da matarsan ma basan wani ya raɓeshi take ba amma adole tai shiru tana fatan a wanye ƙalau.
Tunda aka buɗe masa get ta leƙo ta ganshi amma bata ganni ba dan yamin tsawon da ba lallai ta ganni ba,turare akaje aka ƙara shafawa saboda salon birge maigida Babban Yaya Hhhhh,sai dai wannan karon tana fitowa aɗaki muna shigowa nice agaba shi kuma abaya daurewa tayi ta washe baki"My Love ƙanwata ka kawo min"murmushi ya yi"eh naje na ɗaukota ne tazo muyi hira dan na daɗe banjita akusa dani ba kuma hakan cutuwa ne agareni",wani malolon baƙin ciki ne tokare ma ta maƙoshi saboda kalamansa sunfi saukar ruwan zafi a jikinta,itama murmushin ta ƙaƙalo amma dana kalleta wani mugun kallo take watsamin,tun daga nan nagane dama maganarta bata kai zuci ba,zama ya yi yana ajiyayar zuciya ganin ban zaunaba yasa ya kamo hannnuna na zauna kusa dashi hannun tabi da kallo kamar ta guntuleshi,amma ta daure itama ta zauna tana ƙaƙalo hirar dole"ajinki nawa yanzu a makaranta",Babban Yaya na kala naga shima ni yake kallo"ajina huɗu ss 1",kama baki tayi tana kaɗa kai"ashema yarinya ce ke to saiki dage da karatu kiyi nisa sosai kema kiyi ƴar digiri ɗin da akeyi sannan ki asamu zankaɗeɗen saurayi a aura miki ko",wani kallo muka shiga bin ta dashi amma na shanye maganganun ta nayi murmushi"ai Aunty Hajara ni mijin da zan aura ma ba'a auri uwarsa ba dan haka ki daina tunanin zanyi aure nan kusa","Allah ko amma kiyi a hankali karki tsufa baki aure ba danmu asannan mun aurar da ƴaƴan mu","Aunty ai saiki aurar damu tare ko","to shike nan Nana da nayi murna kuwa",wani irin takaici ne ya kama min wuya na haɗiye abinda nake ji na juya na kalli Yaya naga ya rufe ido ya jingina kansa da kujerar,tashi nayi "Yaya na tafi",kafin suyi magana nakai bakin ƙofa,ina fitowa nasa takalmana na bar gidan,ban shiga gida ba na shige gidan Umma tana zaune kan tabarma tana yankan alaiyahu,kan ƙafarta na faɗa na rushe da kuka"subahanallahi Nana lafiya wa ya taɓaki haka",kasa magana nayi sai kuka,kaina ta shiga shafawa har kukan ya lafa"me aka miki ne",da ƙyar na saita kaina"ba komai Umma makaranta ne wata ta zageni na rama shine aka duke ni","wayyo yi shiru kiyi haƙuri ki daina faɗa a makaranta bakiga kin girma ba","ai ba ni na jata ba Umma itace ta fara","to kiyi shiru kinji ƴar Umma"kai na ɗaga taita lallashina har zuciyata tai sanyi sannan na tashi na tafi gida,suma suna ganina suka tabbatar da matsala amma ba wanda ya tanka min.
Ina fita ya kalleta kana gani kasan ransa ya yi masifar ɓaci"yanzu abinda ki kai kin kyauta kenan wannan ƴar yarinyar kika tasa da waɗannan maganganun",fari tayi da ido ta taso ta dawo kusa dashi ta zauna kamar zata shige mai ciki,cikin salo tana shafa jikinsa tace"haba My Love yanzu me nayi baka gani itama ta iya magana ai Nana ba yarinya bace tafi Babba iya magana ko baka gani ba",ture hannunta ya tashi ya wuce ciki bai kulata ba,itama ko ajikinta ta miƙe sosai ta ƙure speaker tana shan kiɗa,a ɗakin kasa zama ya yi baima san tunanin me zaiyi basai safa da marwa yake agabansa akaiwa Nanan sa haka amma baiyi magana ba kuma tabbas yasan ranta ya ɓaci shi yasa ta tafi tabar gidan, yana nan yana zagaya ɗakin har akai la'asar sannan ya yo alwala ya wuceta tana ta shaƙar bacci,bayan sunyi sallar a masallaci da Alhaji Baffa sukai hira saiga Abba ma yazo sun jima sunayi sannan ya tashi ya fita ya barsu,gidan Umma ya shiga da sallama bayan ya gaisheta ya samu wuri ya zauna kallonsa Umma tayi"me kukaiwa Nana ɗazu tazo nan tana kuka kuma kune sanadi sai dai yarinyar saboda tana da sirri duk haukanta da ke gani bata faɗamin me aka ma ta ba kuma an sanar min daga gidanka ta fito tunda na aika kiranta akace kun fita tare",kallon Umma ya shiga yi"Umma ita da Hajara ne ni banma san me zance miki ba","to tunda bakasan me zaka ce ba kar ka ƙara zuwa da Nana gidanka muddin ba ita taje da kanta ba,kun ɓata ma ta rai nan tazo tana kuka amma dana tambayeta saitace wai amakaranta ne aka taɓata",shiru ya yi abin na basa mamaki kenan Nana zata iya rufa masa asiri aduk halin da yake"kiyi haƙuri Umma hakan bazai kuma faruwa ba","ai ni bance komaiba kawai dai ka ankarar da matarka Nana ba kanwar lasa bace tun tana ma ta tana kuka wallahi randa tajuyo kanta ita zatai kukan kuma ta rasa mai lallashinta","to Umma",Dijama ta kira ta fito a ɗaki sanye da hijabi"ki ɗauki wannan kwanon ki kaiwa su Iyyo abincinsu ne kuma ki dudduba gidan inda aiki kiyi","to Umma"ta ɗauka ta fita ƴar hira sukai kamin ya tashi ya wuce,abin mamaki tana nan a kwance tana bacci abinta ta manta ma a inda take wataƙila,tashinta ya shiga yi tai sallah da ƙyar ta motsa duk da haka haushin tashin da aka ma ta take ji da ta shiga ɗakin ma saita ƙara kwanciya batai sallar ba.
Kashe komai ya yi ya jingina kansa da kujerar ya lumshe ido yana son Nana amma baya son Hajara ta gane yanzu dan tabbas yasan in ta gane zatai mugun tsanarta shi kuma bazai lamunci hakan ba dan yasan komai nata a yanzu haka kullun saita bincike masa waya in taga number mace saiya ma ta baya nin wace ita agareshi sannan zai samu lafiya,kwata kwata ya kasa nutsuwa barin ma da Umma ta faɗa masa yarinyar ta rufa maganar sai yaji wani mugun ƙaunarta ya ƙara shigarsa,a nan ya zauna saida ya gaji sannan ya shirun ya yi yawa ya bita ɗakin a gado ya ganta tanata bacci da alama ma batai sallar ba dama haka take masa da rana taita shirgar bacci da daddare ta hanashi nasa gata kamar mai shan ƙwaya abu kaɗan baya isarta saidai aitayi kamar wasu injina,da ƙyar yasamu ta tashi tai shiga toilet saida tayi wanka ta watstsake,koda ta fito cikin wasu kaya masu kama tsirara ta shirya sannan tasa hijabi tai sallar da ake binta sannan tayi magaruba dan har an shiga ma,tana idarwa ba addu'a ta miƙe ta shiga kitchen taliya da miya tayi dan tana da markaɗaɗɗen kayan miya suna dawowa aka kawo ma ta daga gidansu,tana cikinyi ya shigo bai nemata ba ya shige ya fesa wanka kamar wanda zashi babban taro ya shirya cikinn ƙanun kaya ya gyara kansa walet ɗinsa kawai ya ɗauka ya baro ɗakin kichen ɗin ya bita tana ganin sa ta zagayo tana faɗin"wow Habibe ni kawa wannan kwalliyar",kai ya kaɗa da bana kwalliya ne sai yau,to fita zanyi",haɗe rai tayi tashi guda dan kishin sa taji wata ta gansa a haka tasan dole ko azuciya ne sai an yaba ma ta miji"fita fa kace zuwa ina awannan lokacin",juyawa ya yi yana faɗin"zuwa saita rayuwata mana inba hakaba kema zata shafe ki",yana gamafaɗar hakan ya ƙarasa fita a kitchen ɗin,ludayin hannunta ta buga a ƙasa ta kama kwankwaso yanzu duk wannan shigar bata gigita shi ba yake nufi taga alama ma ko kallo bata ishesa ba amma zai dawo ya sameta ai,da ƙyar ta kammala girkin ta kai falo kwanciya tayi ta jawo wayarta ta shiga chatin da ƙawaye da abokai da groups na wayarta amma ta ciki na ciki.
Da mota ya fito a ƙofar gidan mu yay parking saida ya yi salkar isha sannan ya shigo muna tsakar gida nida ƙarami ina koya masa home work bai gama shigowa ba na miƙe da gudu na shige ɗaki,baki Mama ta kama ta kalleshi"da alama dai kunyi halin ko",ƴar dariya ya yi yana shafa kansa"barta Mama mutuniyar akwai zuciya","ai dama sai dai gaka gata nan",tashi ya yi yashigo ɗaki Aunty Mama da sallama ina bayan labule kuma kusa da wurin ya zauna yana kallon labulen dan yasan ina wurin"fito kiji mana tawan"ya faɗa cikin karya murya,a hankali na fito na raɓashi zan wuce ya riƙo hannuna"haba Zaisha ban sanki da hakaba ni ne fa"fashewa nayi da kuka ina buga ƙafa aƙasa,sakina ya yi"shike nan bari na tafi to tunda bakya son nazo inda ki ke",kumbura baki nayi"inka tafi na daina kulaka kuma",dawowa ya yi ya zauna"to zoki ji",zama nayi kusa da ƙafarsa,"yauwa ƙanwata shi yasa nake ƙara sonki kiyi haƙuri kinji da abinda ya faru ɗazu",katsae shi nayi"dan Allah kabar maganar nan Babban Yaya ta wuce","yauwa tawan",murmushi nayi araina nace'ai bakai kamin ba kuma ita wadda tamin taci bashi ne a wurin ma darajarka taci shi yasa ban faɗan ma ta wadda zata tasa ma ta hawan jini ba sai dai muje zuwa',girgiza kaina ya yi"ana haɗawa wani kitirmurmura ne",saurin jallonshinnayi"kai haba Yaya bani da matsala da kowa",amma araina nace'saida matarka',"tunda ba matsala tsakaninmu da kowa to bari naje na sayo miki abin daɗi ko","yauwa Darling Yaya saika dawo",har waje na rakoshi ya shiga mota ya wuce,na dawo ciki ina dariya harda buga ƙafa"Allah ya shiryeki Nana","amen Mama inama Aunty Mama ta tana nan yau da munsha caskale a gidan nan",bata kulani ba muka tafa da ƙarami.
Vote
Share &
Comments
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
chapter 1️⃣6️⃣
Koda ya fita bai zame ko ina ba sai babban mall kaya ya siyo min dogwayen riguna da takalmi da hijab sai kayan ciye ciye fal ledoji sai wajen goma ya shigo ina tsakar gida nasa doguwar riga ta material nasha red jambaki da kwalli baɗau ita kanta Mama saida tayi dariyar wai nan me nake nufi amma dai tayi shiru taga ikon Allah,ina ganin ya shigo na tashi da sauri na karɓi kayan hannunsa,ajiyar zuciya ya yi yanata kallon fuskata kai kace kyau nayi amma shi a wurinsa sai yau ya taɓa ganin zahirin kyan fuskata kunsan kwalli fa babban sirri ne dashi,ganin yanata kallona yasa na ce"Darling Yaya ya akayi ne",goshinsa ya sosa" jeki kai kayan ɗaki kizo",ɗakin Mama na shiga dashi dan Aunty Maman bata dawo ba sai gobe,tana kallona na ajiye na kuma fitowa inda yake,nida bansan kan maza ba sai nazo gabansa nai tsaye inajin numfashinsa a fuskata"tawan kinyi kyau sosai yau amma in zaki fita karkina yin irin wannan kwalliyar,sannan dan Allah ki maida hankali kiyi karatu in kika bari wannan lokacin ya wuce ki baki karatu ba tofa bazakiyi ba dan ƙwaƙwalwa bata ɗaukar karatu inta fi taki girma,ni kuma so nake kiyi ilimi mai zurfi ki zama babbar mace kafin kiyi aure",dariya nayi daɗi zai kasheni"shikenan Sweet bro bazan nayi ba kuma sannan zannan karatu sosai zanma ƙara dagewa over yadda zakai alfahari da ni fiye da kowacce mace","yauwa ta wajena haka nake son ji shi yasa nake sonki"muka tafa"bari na wuce ko kinga dare ya fara yi ko","hakane Darling Yaya saida safe",yana tafe yana juyowa ina ɗaga masa hannu har ya fita,ɗakin na faɗa na tarar Mama nata dariya"Mama me aka miki kike dariya","zonan Nana",kusa da ita na zauna ina jin tsoro"waike me kika ɗauki kanki ne kina nufin nan mace ce ke",rasa me zance ma ta nayi kawai nasa ma ta kuka"a a ni me na miki wannan fuskar taki kamar aljana wai ita Habibu yaga kinyi mugun kyau",dariya na shiga yi nima"eh mana Umma baki ji yace kar in nayi ba in zan fita waje kuma nasan baya so ne wani ya kalleni",dariyace ta ƙara kamata"Allah ya kyauta muku to",tashi nayi na baje kayan ita kanta Mama saida ta jinjinawa kayan"gobe ki bishi har gida ki masa godiya","to Mama"na faɗa ina tuna tsiyar dana shiryawa wannan goɗamar matar ta Babban Yaya,ranar saida nasha kayan ƙwalam ɗin daya kawo min sannan na kwanta bacci.
Goma da ƴan mintuna yashiga gidan bayan ya gyara parking ya fito ya shiga ciki tana nan hakimce ranta in ya yi dubu a ɓace yake amma da yake namijin duniya ne sai ya washe baki"uwargidan Habibu ta gaban goshin Habibu",ya faɗa yana zama kusa da ita,ba shiri tayi dariya"yanzu ka kyauta kenan kalla lokacin da ka ke dawowa gida wannan adalci ne",murmushi ya yi"babban adalci ma kuwa shi namiji da kike gani wani sirrine shi da Allah ya aje a ban ƙasa mata su aka halattawa tuhumar me suke daga ina suke ko ina zasu amma ba namiji kamata mai hankali ba,dan haka ki kula tunkan na fita na sauke haƙƙinki na gaya miki cewa na fita dan haka ba ruwanki da ina naje,shigowar namiji gida ba tuhumarsa akeyi daga ina yake face sannu da zuwa dan wataƙila fitar ma ke zata amfana ba shi ba",kauda kai tayi dan duk abinda yake faɗa bazata ce ga ɗaya da ta gane me yake nufi"naji to amma ka daina kaiwa warhaka a waje",ɗan murmushi"naji to amma banda uzuri in yakamani zan fita,bani abinci tukun",gabanta ne ya faɗi dan tasan ba kasafai yake ƙaunar talliya ba daurewa tayi tace yana dining",tashi ya yi ya isa biyo shi tayi ta fara buɗewa tana murmushin yaudara,saboda yasan shima ya ɓata ma ta sai ya basar yaci taliyar haka,amma yana mamakin yanda akai kamarta bata iya sarrafa abinci daban daban ba,gashi yana gani agidansu duk yara ne amma in suka zuba girki kamar a babban hotel akayi,tunani ya yi ita agidan hutu ta tashi sannan kuma ita bama a takura ma ta kamar sauran saboda an fi sonta wanda nu na hakan annabi ya hanemu fifita wasu ƴaƴan mu akan sauran ƴan uwansu ƴaƴa,tun kan ya gama ci ta fara shafa mai jiki tana shinshina shi bai kulata ba ya barta harya gama,yauma kamar kullum ya gaji amma ta hanashi sakat daga ƙarshema kunna hasken ɗakin ya yi yana ƙare ma ta kallo sai wani miƙa take alamar bata gajiba ko kuma harkar bata isheta ba"please ka taho mana"ta taso ta ƙara faɗawa jikinsa tana neman haɗa bakinsu,kauda kansa ya yi ya riƙe ma ta fuska"kinsan Allah kodawa kike yawo bacci zanyi yanzu kalli agogo biyu da rabi ma ta wuce to ko Annabi kasa darensa yake dan haka baki isa ki ƙarar min da nawa daren anan ba dan haka kwanta ko na bar miki ɗakin",batare da taji daɗin abinda ya ma ta ba ta kwanta dan tasan ya gaji ita kuma ƙwayar da Auntyn ta bata ce take ma ta haka yanzu ko bata shaba ma sai hakan ta faru gashi tanajin shi iya namiji ya kai a wurinta da ƙyar tayi bacci shi kuwa ai ya daɗe a birnin lantsandan baima san tayi bacci ba ko batayi ba,asubar fari ya tashi duk da idanuwan sa na cike da bacci amma ya gabatar da nifilfilu sannan ya tasheta da akai assalatu shi kuma ya wuce massalaci dan gabatar da farali mai girma wato sallar asuba dan tun baifi shekara shida ba sallar asuba ta shiga jikinsa kuma hakan abu ne mai kyau ga duk ɗa namiji dan ita salkar asuba tana ya ye dukkan damuwa da baƙin ciki.
Bai shigo ba saida rana ta ɗaga kuma ya tarar bata ko motsaba,mamakin ta kullum ƙara kamashi yake da ƙyar ya samu ya tasheta tayi wanka sannan tayi sallar azkar ɗinsa ya gama sannan ya tashi ya koma ɗakinsa ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya masu kyau ya gyara sumarsa kamar yadda ya saba,tara da rabi ya shiga ɗakinta amma tana bacci bai tasheta ba ya wuce ya fita ko taɓa get wai duk bata ji ba,sanin Abba na jiransa yasa ya wuce bai nemi kowa ba,koda ya isa gidan ma ba kowa a falon dan haka sai shima ya miƙe ya kwanta kan doguwar kujera dama shi yafi kowa buƙatar bacci,bai jima da kwanciya ba Abba ya fito ya gansa yana bacci,murmushi ya yi ya duƙa kusa dashi ya shafa kansa"sannu Habib wannan matar bata dace dakai ba tabbas huta mun fasa fitar ma",miƙewa ya yi ya kulle ƙofar falon dan kar aturo a shigo daman inka ƙwanƙwansa ma baji za'ayi ba,ɗaki ya koma yaja glass ya saka ya cigab da karatun alƙur'ani dan yanzu aikinsa kenan saboda wannan matsala ta baya da aka magance kuma alƙur'ani shine maganin farko na kowanne ciwo kuma ya yaye ƙunci da damuwa ko wacce iri dukkan wanda yazo ya taɓa ƙofar yajita a garƙame saiya koma.
******
Wajajen goma da rabi nai wanka na tsaf na shirya zuwa gidan Babban Yaya amma har falon na shiga wayam ba kowa tabbas ajikina nake ji baya gidan nan shi yasa na haye kujera na kunna tv nasa chasu abuna tsabar neman rigima.
Bata farkaba sai bayan shaɗaya wanka tayo sannan tayi sallah tasa wasu kaya kamar ƴan can garin kai bakace ta iya hausa ba,alamar ƙiɗan nan ne yasata fitowa tana rangwaɗa ta zata shine sai kawai tai arba dani na kishingiɗa kamar wata yayarta ko matar gidan ga ina cikin doguwar riga wadda sai wance da wance masu mallakarta ina kallon duk kallon da take min amma na basar da ita jira nake ta tanka min,ilai kuwa kamar zata rufeni da duka ta ƙaraso kaina"dan ubanki wayace ki shigo min gida har ki kunna min kiɗa",duk da naji zafin zagin da tamin kuma zan iya ramawa amma bazan rama ba sai gaba kaɗan dan haka saina miƙe"gidan ki gatsau ko kunya baki jiba gidana dai koda yake in baki sa ni yau ki sani wannan gidan ma na fi ƙarfinsa inzan kwanta da mijinki wannan gidan da ɗakunansa sun min kaɗan saidai ke ɗin....",ban gama magana ba ta kawo min yaga kamar karya da gudu na nemi ƙofar fita amma ta tare"wallahi saina kashe ki yau agidannan da mijin nawa zaki kwanta kalla ƙirjinki ƙirgen dangin ma bai nuna ba",katseta nayi"daina tantama malama da wannan ƙirgen dangin saina gigitar da mijinki na sumar da shi kalla nan jiya kin ɓata min ya tafi wurina tun magarubar fari wannan rigar ta jikina ma ta ban haƙurice dan bashi da bakin magana akaina inyaga raina ya ɓaci","rufe min baki shegiya mai zubin zabaya dama ni tun ganin farko da miki ban yarda dake ba nasan cewa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 32