tana shan kodimo abin ta",dukkansu ukun zuwa sukai suka rungumeni harda kukansu da ƙyar suka saken kowa na wurin yana shimin albarka ya yinda kishiyata keta yankan harara"ku dakata"na faɗa ina duban su Hajiya Harira,tsayawa sukai nan na matsa kusa dasu"ko wacce ta lissafa sau nawa ina kai ma ta kuɗi",da mamaki suka duban nace"ku lissafa mana",lissafawa sukai nakai musu wajen dubu ɗari takwas takwas"to bari kuji yasin kuɗin ku ku ka ci"cikin mamaki suka buɗe baki dariya nayi na kama ƙugu"dame ku ke tunani inta kwaso kuɗin mijina ina baku kuna ci bayan shi kullum yana zarya tsakanin tashar mota da ta jirgi dan tara nasa kuɗin to takardar shaida da Abba ya rubuta ma kowaccen ku da ita nake karɓo kuɗi in naje makaranta sai na kawo muku kunga ko badan Allah ba ai yasha addu a wurinku"dariya sosai ake yi a wajen nan Alhaji Baffa yace"ku masu kuɗi to kuyiwa Nana godiya da kyau sannan Nana ita kuma Fuleran fa?","barta kawai tsoho zaku ganta ta dawo ba shiri dan nata takardun ma suna wurina zan rabama almajirai ko Kawu Iro?","hakane kuwa ƴata ni zan ma kaiki wata babbar tsangaya","kaji ko Alhaji"dariya sosai akai a wurin nan Alhaji Baffa ya yiwa kowa nisiha aka watse sai yaba min ake ni kuwa daɗi kamar ya kashe ni.
Tunkafin mu kai gida Hajara ta kira Abbanta a waya ya bata number Hajiya Fulera nan yake faɗa ma ta ai tunda ta tafi bata kira shi ba kashewa ta yi ta shiga zagaye a ɗakin taya zata raba ni da takardun da nace yana wurina rasa ya zata yi ta yi dan haka saita barwa ranta duk randa bana nan zata bincike ɗakin ta ɗauke.
da yake ranar girkina ne dan haka muna komawa na shiga haɗa break yana bina a baya wai so yake yaga a ina wayo na ya maƙale,in yana maganar sai dai nayi dariya kawai amma nima ina mamakin abin da nake,bayan na gama ya karya ya fita sannan na gyara ɗakin inda na aje waɗancan takardun naje na sauya dan hakanan nake jin ajiyar bataiba,fitowa nayi falo na kame ina kallo sai kwasa dariya nake naji an turo ƙofar kaina na juya naga mata ne su huɗu riɗa riɗa ban kulasu ba ganin ta fito tana musu sannu da zuwa wurin zama ta basu na tashi naje na kawo musu ruwa da lemo sannan na duƙa nace"ina wunin ku"washe baki sukai suna dariya suna amsawa tashi nayi ina kallon ta"bari na koma ciki kuji daɗin gaisawa ko" na wuce a ladab ce a ɗanlokon da daya ɗaga na coridon na laɓe jin ɗayar na cewa"kai Hajara amma akwai ki da sharri dama kishiyar taki haka take da ladabi ga girmama mutane gaskiya tama fiki kirkin","hakane kam ni da take cewa yarinyar bata da kunya bata da mutunci su Zina na tayata na ɗauka gaske ne"cewa ɗayar,kasaƙe tayi tana dubansu dan tabbas ba ta da abin cewa kota faɗa ma bazasu yarda ba dan kowa nawa haka ƙaryar sa ace zanyi wa ta tijira ya amince,dariya nasha na shige ɗaki ina magana ni ɗaya"kina wasa da ni Hajara ni sai na rabaki da mutanen ki ma wallahi duk su dawo wurina suma waɗannan naga ƙaramar ƙwaƙwalwa garesu irinki",anan na zauna"gaskiya bari Babban Yaya yazo ya siya min tv ko mai doro ce"waya naji na ringing na shiga dubawa ashe shine ya manta da ita My number na gani tana kiran saina ɗaga dan na gane da ɗayar wayar kenan ya kira"Hiiii My Sweet Miji"dariya ya yi"kina birgeni My Sweet Mata"ƴar dariya nayi"ya aikin fa","normal ma za jeki get akwai baƙi Murtala yace baisan su ba kuma tace masa ƴar gidan ce yace ko yasanta ya manta ta kinsan na hana abar kowa ya shiga gaba gaɗi","ok yanzu zanje"na kashe nasa Hijab na fito"Aunty Hajara zanje get na dawo"ba yadda ta iya tace"saikin dawo"fitowa nayi ina dariya na ɗan daɗe ina tafiya sannan na isa suna ganina suka miƙe suna"Hajiyar manya"dariya nayi dan haka suke faɗa tun daga auran Murtala buɗe min get sukai na fita nima ban gane su ba saida ta gefen wani saurayi ta juyo ihuu na buga nai kanta da gudu"Oyoyo Ya Fatsima"da sauri itama ta taho muka rungume juna wannan saurayin sakin baki ya yi yana mamakin gani na,da ƙyar muka saki juna sannan na shiga musu sannu da zuwa,bina da kallo wannan saurayi ke yi na juya muka haɗa ido"kai malam daina kallo na ni matar aure ce"dariya suka kwashe da ita ya yinda yace"ai nafi kowa sani ranar da ki ka zama matar auren ma da gaske ina wurin",da hanzari na kalleshi na kauda kai Ya Fatsima ta dafa ni"da gaske ki ke kinyi aure ke Nana bana son sharri","Allah Ya Fatsima ni da Babban Yaya mun jone tuni"dariya sukai har matar da suke tare sannan nace mu shiga mana,tunda muka doshi gidan naga yadda take a tsorace batasan Gwaggon yanzu bata da bace,ƙofar falon na tura da hanzari na"Ya Hadiza fito kiga"na faɗa da ƙarfi daga kitchen da ta fito"Nana nan kuma ki ka taho..."shiru ta yi tana kallon wadda ke bayana ido ta zaro ta taho da gudu"Fatsima"kan tazo itama ta tafi suka ƙanƙame juna sai suka fashe da kuka,wannan matar mumushi ta yi tana jin daɗin ganin akasin abinda suke faɗa ma ta kullum,jin kuka yasa Gwaggo fitowa tana faɗin"ke dawa kuma Hadiza"turus tayi ganin wata matar me kuɗi rungume da ƴarta ɗago kai Ya Fatsima ta yi"Umma",tahowa Gwaggo ta yi da mamaki"Fatsima ce da gaske",sakin Ya Hadiza ta yi tana nufar ta"nice Ummana"da sauri Gwaggo ta taho"ƴata jama a ƴata"sai ta fashe da kuka nan ta rungumeta ƙamƙam"ki yafe ƴata ki yafemin dan Allah",cikin kukan itama take cewa"kiyi shiru Umma kiyi shiru"sai sannan Umman taga matar da suke tare sakinta tayi tana ƙarasawa ga matar"Hajiya Bismillah yi haƙuri an barki a tsaye"ƴar dariya ta yi"ai ba komai naji daɗin ganin hakan a tare daku",nan tashigo ta zauna Umman nata hidima da ita sai sannan nace"Gwaggo ai kin bar ɗan naki a waje","lahh Nana ce su shigo",fita nayi nace su shigo sai sannan suka shigo wannan saurayin sai kallo na yake hararar sa nayi,nu na ni nayi"kin daina hararata ko saina maida ki Niger",kallon mamaki na masa au ashe acan ya ganni shi yasa yake kallona,baki na kama na maka masa harara"ai ni da Niger ko ta aljannace na yafe",dariya sukai nan nace Gwaggo na tafi kai rohoto saina dawo"da sauri wannan saurayin yace"ki kira min mijinki kice ya yi baƙo daga bariki ta Niger","naƙi in faɗa ɗin kaita jiran sa sai biyar zai dawo","jeki ai naga bake kaɗai bace a gidan",fita nayi ina dariya nan naje na faɗawa su Mama sannan na kira Babban Yaya na faɗa masa saƙon wancan kan na gama faɗa ya kashe da mamaki na zare wayar ina bin ta da kallo.
Su Mama kaf sunje sauran matan ma saiga Babban Yaya cikin hanzari har falon ya shigo da sallama wannan saurayin ne ya tashi yana dariya"kaga angon garin wasu"hannu ya bada suka tafa ya yinda ya juya ga matar nan da sauri matar ta miƙe ta dafe ƙirji baya ta ja tana nuna Habib tana son yin magana amma ta kasa.
UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
BABAN YAYA
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
32
Da ƙyar ta samu baki tace"amma kai ɗan Habibu ne ko?",cikin mamaki kowa ya bita da kallo a hankali ya kaɗa kaɗai"eh nima sunan Babana Habibu amma ba ka lallai asance wanda ki ke sa ni ba ne",kai ta kaɗa jinin Habibu ko a mafarki na gashi zan gane dan Allah ka nuna min ko hoton sa ne in tabbatar"kunsan ni da shishshigin masifa a wayar hannuna na kamo hoton na matsa gaban ta na nuna ma ta,danƙar wayar tayi"wallahi shi ne wannan mijina Habib ga ɗan uwanka nan kama ka daina min tijarar na haifeka ba ta hanyar aure ba",cikin tsantsar mamaki kowa ya buɗe baki,amma fa ta dage sai da aka kira Alhaji Baffa shima ya yi mamaki nan nace kowa ya dakata ina zuwa,shiru akai ana kallona nan na tafi can gida na bin ciko wani hoto ƙarami fuskar ma ba sosai ake gani ba na dawo bata nayi nace"wannan hoton waye"karɓa ta yi ta duba"ni ce wannan ai a ina ki ka samu?",murmushi nayi na dubi Babban Yaya"gaskiya ta faɗa"cikin mamakin mamaki aka saka salati"ke Nana taya akai ki ka san da zamanta?"ɗan murmushi nayi"kun ɗauke ni yarinya amma shi Abba baiga yarinta a gare ni ba har yake sawa a ɗakko masa ni yaban labarai nayi dariya sannan yaban wasu sirrika nashi wanda bai taɓa faɗawa kowa ba a irin wannan labaran ne yake faɗamin ya auri wata mata a Niger amma ƴar Algeria ce ya barta da ciki sanadin wani abu da Babanta yace, dai dai da sakin da ya ma ta Babanta ne yace in bai sake ba zai tsine ma ta to ganin shi baƙo ba shi da kowa sai ya sauwaƙe ma ta to ya tafin ne kawai sai yaji ya ƙara mantawa da komai akuma sanda ya tuna lokaci ya ƙuri dan wannan allurar da mugayen can suka masa ta fara tasiri...",saurin shiru nayi ina wai gawa naga Babban Yaya da wannan ɗayan Habib ɗin sun zura min ido ganin basu min magana ba sai na gane basu fahimci me nake nufi ba dan haka saina cigaba"to shine ya zayya ne min komai yaban wannan hoton yace ita kaɗaice mai hoton in ta gani zata san itace a jiki ɗan kuma ko baya kama da kowa zai yi kama da Mama dan Babban Yaya ma da ita yake kama",cike da mamaki Alhaji Baffa yace"tabbas shi yasa Habibu yace a kula dake to kai Habib saika ƙara kulawa da matar ka kallon juna sukai wato Habib da Habib da ne,Mamace tace baiwar Allah taya akai kika yarda ki ka auri mutumin da bakisan a salin sa ba?",a jiyar zuciya tayi"gaskiya na aminta dashi ne dan yaron Babana ne sunkai wata biyar da haɗuwa amma bansan a ina ska haɗu ba sai yazo dashi gidan mu dama asannan za a min aure bana son mijin kawai sai nagansa nace shi nake so kowa ya yi mamaki shi kuma Babana ya amince saboda ni kaɗai ya haifa mace sauran duk maza ne,bayan auren mu da wata biyu sai Habibu ya ɗaukaka kasuwanci kamar ƙasa har yafi Babbana mutane to sai Babana ya fara jin haushi watarana aka zo aka ce yaje inji mahaifina sai yamin sallama ya tafi sa ilin ina da ciki wata huɗu to tunda ya tafi kuma ban kuma ganinsa ba har yau dan Allah yana ina",sunkuyar da kai kowa ya yi da salama Hajiya Salma tace"ya rasu muma matan sa ne"fashewa ta yi da kuka ya yinda Habib ya sunkuyar dakai yanajin kaɗaici ina ya taɓa haɗuwa da shi ko sau ɗaya ne ai da ƙarar da koda kamar sa ce,hwnnunsa Babban Yaya ya kama sannan ya ɗago ya kalle shi"kayi haƙuri dan kaine yanzu take sabuwa a wurinka"kaɗa kai ya yi yana ɗan murmushi saida kowa ya nutsu sannan aka maida zancen ya Fatsima godiya kowa ya musu da yadda suka bata kulywa ga ɗanta ƙato, A gidan aka ƙarasa wunin yau sai da magariba sannan Alhaji Baffa yasa aka kira masa Habib da mamarsa sannan kawun sa sai ni da Babban Yaya da Mama da Baffan mu dubansu ya yi yace"Hajiya gashi Allah ya kawo wani ɗan na Habibu sai dai an raba ga do tuni amma ni..."da sauri na katse shi"Alhaji Baffa shima fa da nasa zan ɗakko masa yana can ɓangaren Abba ni nasan inda ya aje",da mamaki suka dube ni sai dai ni dariya nake shima Baffa dariyar ya yi"Hajiya Nana kice shima wannan sirrin kin iya ɓoye shi to kunji kai Habibu matar yayanka tace zata baka naka kason",ƴar dariya ya yi"ai zan ɗauke su ita da mijin nata mu koma barikin Niger da zama"da sauri na galla mai harara"kai kuwa anya kana son yayan naka ka ke haɗashi waccan jahannamar"dariya sukai gaba ɗaya yana cewa"Niger ɗin ce jahannama","eh mana ai ni duk kuɗin goro na musu malam kaga bacci na ke ji ka lallaɓani gobe na ɗakko maka dumus yaro",kwashewa ya yi dariya"to matar Babban Yaya zan kuwa lallaɓa ki yanzu ma tashi kije ki kwanciyar ki",miƙewa nayi na musu sallama Mamma da Mama suna Allah ya tashe mu lafiya ban bi takan Babban yaya ba na shige gida frig ɗin Aunty Mama naje nai sibare dan tun yamma naga ta haɗa wani ta juye a robar faro shine yanzu naje na ɗauke kunga koma na waye na jaza ma ta ko? direct gida na wuce dan akwai haske bana tsoro kuma bana son takurawa Babban Yaya shima ya zauna da ɗan uwansa suji ɗumin juna.
Baya sun fito Mamma ɗaki guda Gwaggo ta ba ta ita kuma Ya Fatsima suna manne da Ya Hadiza suna ta hira da bawa juna haƙuri dama Baba baya nan yaje garin su ɗaurin aure ai da bire ɗen yafi haka,daga wajen Alhaji Baffa mota suka raka Alhaji Mustaphan ya wuce sannan su kuma ya wuce da Habib ɓangaren Abba Habib yasha mamaki yanayin wurin kamar ana rayuwa a ciki har ɗakin ya kaisa yace"ka kwana anan sai kafi jin daɗi zakaji kamar Abba na nan ne",godiya ya masa sannan ya fito zuwa nasa makwancin.
Ɗakin Hajara ya shiga ya ganta sai kwasar bacci take tana warti fitowa ya yi yana ja ma ta ƙofar harna fara bacci naji motsi buɗe ido nayi na gansa yana sa riga da alama wanka ya yo tasowa nayi na kwanta a bayan sa ina zagaye hannuwana a cikin sa,murmushi ya yi ya ɗora hannunsa kan nawa"Madam Habib sarkin basira yadai",zagayowa nayi ta gabansa ina langwaɓar dakai"wallahi yau nayi magana da yawa kaina ciwo yake",ɗora hannunsa ya yi a goshina"ayya sorry bari na samo miki magani"yana ambatar magani na sau shi"ai ma na warke Babban Yaya dama,kaci abinci taho mu kwanta bacci nake ji",ɗan murmushi ya yi ganin na masa wayo akan maganin na waske,hannuna ya kama zuwa bakin gado ya zaunar dani sannan ya kawo pracitamol ya bani ba yanda na iya haka nasha ina ɓata rai fushi nayi na kwanta na juya mai baya maida ruwan da maganin ya yi sannan ya kashe ya hayo inda nake,banyi motsiba nai shiru wani bacci a cikina naji hannun shi yana shafa nan ma shiru na masa kome zai min na masa shiru saida ya birkitoni dukkana ya ɗora kansa sannan ya kamo fuskata ya ɗora bakin sa kan nawa wannan juyayin ne na kasa juyawa baya a dole na miƙa wuya dama naje na sato tsumin Aunty Mama ai kuwa na gurzu.
Kwana uku da zuwan Ya Fatsima mukai taron family har su Ya Saddi'q sun wanko ƙafa sun dawo anyi dasu wannan abu ya dasa farin ciki a zuƙatan mutane kuma anyi yafiyar juna bama ya Kawu Iro da matansa sun nemi ya fiyar Iyyo sosai dan haka wanzar da yadda za'a cigaba a gidan akai kuma gashi an ƙaru dan Habib shima ya zama ɗan family sai yamma na ɗakko masa wasiyarsa kowa yasha mamakin abinda ya bar masa kuma acan Niger da Ageria ne suke zan wuce ya zaro wata takarda ya miƙo min"ga ladan ajiye sirri matar Babbar Yaya"tsayawa nayi ina kallon sa sai kuma na kwashe da dariya"kaga bana son salo nima ina da nawa yamanfi naka yawa",dariya ya yi"ai nasan da haka da nawa yafi naki da haɗa miki zanyi duka dan kin cancanta a miki komai","nifa bana son salo kaga ɗan Niger",dariya ya riƙe"kuma dama acan abinda na baki yake"da sauri na ƙara gaba"bana so bana so kaba matar da zaka aura"a bazata ya juya ya miƙawa Ya Hadiya"cak na tsaya ina kallon sa washe baki nayi"da gaske ka ke ita zaka aura",ƴar dariya ya yi"indai kin amince nasan zata amince dan na ma ta magana tace ana tambayeki",kallon ta nayi"ni matsala dake Ya Hadiza ƴar Sakkwato ce ke madadinbtun alokacin ki amsa",tasowa tayi ta kama hanuna"ban amsa bane saboda a yanzu kece mudubina dake nake so nayi koyi ko kaɗan ne dan haka saikin amince sannan zan amince",rufe ido nayi ina jin tausayin ta ita babba amma ta maida kanta ƙarama saboda kuskuren da ta yi tun farko,buɗe idona nayi"na amince Ya Hadiza Allah ya sanya alkhairi"ƴar dariya tayi ta juya ta karɓi takardar,tafi su Ya Hasiya suka shiga yi ya yinda wani sanyin daɗi ya kama zuciyar Mamma yau burinta ya cika ɗanta a danginsa sannan zaiyi aure a danginsa,shagalin mu ƙaruwa ya yi har kwana biyu ana taron sannan aka gama.
BAYAN WATA UKU
A gidan mu a ka sha bikin Ya Hadiza kamar kar a daina kwana uku da gama biki suka ɗaga Niger Mamma da Ya Fatsima dama gida ɗaya zasu zauna.
Daga kitchen na fito naji Aunty Hajara na magana a ɗakin ta dama yayarta tazo har zan wuce naje ƙofar ɗakin na tsaya ni ba laɓe nai ba amma in baka da hankali da cikakkiyar nutsuwa to bazaka ganni ba ita kuwa ta dage sai zuba take"ai ni Yaya na rasa ya zanyi da wannan ƴar masifar yanzu fa kiga ƙanin sa da nake faɗa miki ƴar gidannan fa ya aura su sai dai suyi ta cin dukiyar a tsakanin su kin sanfa Abba yana shirya wani abu amma yaƙi faɗama kowa..."katse ta nayi"zai raba Babban Yaya da Babban company ko to kima faɗa masa karya soma in ji ni in ba haka zai tsinci kanun labaran badaƙalar da ya aikata wani satin a jaridar daily trust sannan da kafar ƴaɗa labarai ta BBC ke kuma tsohuwar kilaki ko zuwa ki kai kashe ma ta nata auran kijata barikin? ko ki fita ko kuma na tona miki asirin sanadin ɗanki na fari",kamar ƙiftawar ido ta suri jakar ta ta fita da gudu tun da take wani bai taɓa bata tsoro ba irin na yau,itama Aunty Hajarar tsuru tsuru tayi kamar kaza a ruwan zafi,fita nayi a ɗakin dan in ina kallon ta ji nake kamar na kasheta.
Rayuwa tayi nisa, tsaka ni na da mijina yana ba ni kulawa yadda ta dace a tsakanin mu da Hajara ma baya banbanta mu sai in faɗan namu ya motsa muyi kaca kaca amma agaban wasu sai in nuna ƙalau muke wannan abu kuwa na damunta,sannan tayi tayi ta shiga tsakanin mu da Babban Yaya amma abin ya gagara sai dai fa tayi alƙawarin sai ta shiga koda kuwa zatai sanadin nata auran.
******
Yau tun safe ta tafi gida ta samu Abbanta ta falo ta zauna ta faɗa masa kome ke faruwa murmushi ya yi yana duban ta"ki kwantar da hankalin ki ba bu abinda zata iya yarinya ce fa ƙuruciya ke damunta amma kafin takai matakin hankali zan rabata da hankalin nata",girgiza kai ta yi"Abba in kuna cewa wannan sheɗaniyar yarinya abin da ta ke wai ƙuruciya abin na bani haushi Abba wannan ƴar abar da ka ke gani zata haɗa wutar da baka tunani",duk naji ƴata ki kwantar da hankalinki kedai ki samu ɗakko waɗannan takardun sannan ki ɗakko min na mijinki ma iya wanda ki ka gani","to shike nan Abba","yauwa yaushe ne tafiyar tasa",saura kwana huɗu","ok ki kula kisan yadda zaki ki bishi kome yana can","to Abba",ranar wuni ta yi bata nan sai dare ta dawo dama girkinta ne shi yasa ba ruwana da su nifa ranar da yake girkina bana taɓa tunanin akwai wata shi kaɗai nake gani kuma nake ji araina ni kalai ce ba wata.
Ranar da zai tafi girki na ne kuma tunda na tashi gabana ke muguwar faɗuwa sai dai nayi ta addu a sannan na kira Mama na faɗa ma ta tace nayi addu a ba abin da zai faru,wajajen ƙar fe shabiyu zai tafi ya fita yakai ma Alhaji Baffa saƙo sai gata ta shigo har ɗakina tana dariya hannun ta ɗauke da kofin ruwa ban kulata ba saida ta dubeni tace"matan aure yau zanyi wasa da auren naki",dariya nayi"Allah ya baki sa a dama shi ai rai ne dashi in ya mutu ba komai bane sai dai ki tuna shi ramin mugunta gajere ne in zaka gina shi gina shi gajere",dariya ta kwashe da ita"to wannan ramin naki ne yarinya"shiru ta yi jin ya taho sai ta fara yayyafa ruwan hannun ta wurin harda jikina da saurin na miƙe"ke miyi ruwanki da ni ne ki ke shiga rayuwata",sanyaya murya ta yi"haba Nana daga nace ki daina shan maganin hana ɗaukar ciki ya kamata tunda ni banyi ba ke kiyi shine zaki zageni","what"na faɗa cike da mamaki cikin fusata Babban Yaya ya ƙaraso ya warce maganin a hannunta yana dubawa da idanuwan sa da sukai ja lokaci ɗaya ya ɗago yana dubana"miye wannan Nana?"nima kallonsa nayi"ita da ka gani a wurinta ita zaka tambaya"tass ya kwaɗan mari wanda saida naga taurari dafe wurin nayi na faɗi a ƙasa daɓas na fashe da kuka,tsawa ya daka min mai razanar wa"ina sauran maganin yake"ɗago kai nayi"ita da ta baka wannan saita ɗakko maka sauran ai ita ta bani tace maganin infection ne shine nake banka kuma kullum huɗu nake sha",cikin tsanin faɗuwa gaba ta gwalo ido tana dubana shima ɗaga kai ya yi yana kallon ta"Hajara"magana zatai ya fesa ma ta mari ya ƙara ma ta wani saida ya ma ta huɗu sannan ya danƙi wuyanta ya haɗa bango nan take idanuwan ta suka fito waje cikin tsananin fushi ya fara buga ma ta kashedi"wato kinga batasan magani ba shine zaki cutar da ryuwarta bakisan matsalar da ta ke ciki ba dama to bari kiji wallahi wani abu ya samu matata saina kashe ki",kuka na rushe da shi ya sake ta ya taho takaina da sauri ya rungumeni"shiiii Nana Allah ya kare min ke"saki na ya yi ya buɗe sif ya ɗakko trolly ta dana zo da ita wancan karon ya shiga loda kayana komai ma ɗauka yake ni dai ina tsaye ina kuka ya yinda itama take baje a ƙasa dafe wuya tana tarin wahala,yana gama zuba kayan yaja hijabina ya ɗakko jakata duka trollyn ya jawo waje sannan ya kamo hannuna muka fito a ƙofar ya dakata yana juyawa ya nu na ta"fito aɗakin nan kan nazo na ƙarasa ki",da sauri ta rarrafo ta fito ya rufe ɗakin ya jawo hannuna muka fito banwa kowa sallama ba yasa ni a mota muka bar gidan,a airport ba tare da ɓata lokaci ba aka bashi tiket ɗina sannan ya dawo inda ya barni wayam ya gani mutanen dake zaune a wurin ya kalla "Malam ina yarinyar dana bari anan yanzu",tashi ya yi tsaye"yanzu wasu mata su huɗu suka zo suka tafi da ita mun zata gudowa tayi daga gida shi yasa muka barsu suka tafi da ita",wani dam yaji a cikin kansa in ya fahimta mutumin na nufin ta ƙarfi aka tafi da ita kenan.
*TUR ƘASHI*
*WA YA ƘWAMUSHE NANA MASIFA YA ƊAUKAR WA KANSA MASIFA?*
Ummu Saddiq ce🌹🌹🌹
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
BABAN YAYA
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
33
Cikin lokaci ƙan ƙani Babban Yaya ya hautsina airport ɗin nan amma ba amo ba labari kuma cameras nasu basu ɗauki komai ba kafin biyar na yamma tashin hankali ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 32