Share this page
ba me yasa acikin yaranku ba zaku haɗa wata aure da wannan zankaɗeɗen matashin ba","wani matashi kenan Tasalla","Habibun nan mana",gyara zama tayi"ki bari kedai Tasalla wannan maganar har Alhaji Baffa nayiwa ita amma ya takan burki kuma yace kadan na kuma wannan maganar saiya saɓa min","tabɗi amma kuwa ya kwafsa muku agaskiya ina hango babban al'amari dan gane da wannan yaron da ganinsa ƙashin arziƙi gareshi kuma naga yafi shigewa su Halima akan ku","hakane Tasalla aisu waɗannan kyan yaransu ke ruɗar mutane ake sonsu musamman wannan me kama da zabayar Nana, amma ai in bamu same shi ta wani fannin ba to ta wani fanin zamu samesa","Allah ko saiku dage dan naga wannan ƴar jariryar yarinyar ta iya salo ga iyayi tsiya kamar babbar mace","kai Tasalla ai Nana ta wuce tunanin ki bata da kunya kuma ƴan gidansu kawai take so agabana take faɗawa yaran nan ita bata ganin kowa da gashi amma barni da ƴar banza za'a sha mamaki akanta", suka tafa nan dai sukaita maganganun mutane daga wancan sai wancan,Tasalla na famfata har abinma da ba'aiba sai labarun ƙarya take girba ma ta ita kuma tana yadda,kafin su rabu saida ta ƙara dasa ma ta tsanar su Mama aranta,haka ko bayan fitar Tasalla zama tayi tana cin burika tamanta Allah ke komai ko muguntar zakai sai yabaka dama sannan zakayi. ***** Shida saura aka tashemu naƙi biyo kowa naja gefe ina tafiyata,fancam naji an watsamin wani abu me ɗoyi,da sauri na waiga naga Humaira na dariya"yi haƙuri Nana bansani bane nataka kwata ta fantsamar miki",ganin tana dariya nasan ƙarya take tana sane tamin haka,nan na zuciya wata yarinya na bawa riƙon jakata na kwasa da gudu na shaƙeta na hau dukanta duk da ta fini girma amma na fita ƙarfi,duka na mata ga yakushi da cizo,da ƙyar Ya Ruma ta rabamu taja hannuna zuwa gida bamu faɗama kowaba mukai shiru,Mama ke tambayar meya sameni nace kwata na faɗa tace" kije kiyi wanka mana" wankan nayi nasa riga da wando masu laushi sosai,ina ɗaki raina sai ƙara ɓaci yake in na tuna abinda Humaira ta min naji Mama na kirana"Nana Nana","na'am Mama gani nan zuwa",fitowa nati inasa hijabi nasan aikena zata yi"ki ɗauki wancan kwanon ki kaiwa Ummanku karki zauna kinga an kusa sallar magariba","to Mama",na ɗauka ina fita naje kusa da ƙofar gidan Kawo Iro naji an hankaɗe ni Allah yaso kwanon kula ce bai buɗeba,kafin na tashi Humaira ta danneni ta hau jibga ta kamar jaka saida tamin duka sannan naji Babansu na magana"barta haka ai kin rama",ɗagani tayi duk jikina ƙasa na miƙe ina hawaye ga ƙafata na zafi musamman babban yatsana,ranƙwashina naji anyi na ɗago na kalleshi"daina kallona mayya in kika kuma dukanta sai naga wa ya tsaya miki",ƙuri na masa da ido banyi magana ba dan in nace zanyi zatayi zafi kuwa,a kusa damu taxi ya tsaya saiga Aunty Mama ta fito ganina a haka ta nufoni da sauri,da gudu na tafi na rungumeta ina rushewa da mugun kuka kamar raina zai fita,ruɗewa tayi"lafiya wa ya dakeki faɗamin"cikin shassheƙar kuka nace"Kawu Iroro ne suka min duka shida Humaira akan ta watsamin kwata muna dawowa a makaranta kuma tahaumin dariya shine mukai faɗa a wurin wai yanzu shine suke tareni suna duka da zagin ubana da uwayena",kaf maganar da nake abin dariya ce amma amma Aunty Mama sai ta shaƙa tafara faɗa"wallahi kaji kunya Iro faɗan yara ka ke shiga kalli yadda ku ka daki ƙaramar yarinya saboda zalinci wallahi anji kunya ke kuma ki ke zare ido kamar baƙuwar mujiya zan kamaki ne",hannuna taja nace"aikena akai Aunty Mama ga yatsana yana zafi","kai Ƙarami ɗakko wancan flas ɗin ina zaki kai","Umma zan kaiwa","wuce ka kai ma za, ke muje gida naga ƙafar taki",su kuwa saƙare sukai jin yanda na gindaya musu sheri na faɗi magana kamar duka haka akai,yanzu baya raba layan biyu sai wannan abin ya zama babba. Vote Share & Comments Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂ 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 *𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔* 𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠 Story & written by *FATIMA AMINU* *Ummu Saddi'q* chapter 4️⃣ Shigowar mu ina ɗingishi yasa Mama kallon mu taganni da Aunty Mama dariya tayi tana faɗin"kice da rabon faɗa kika fara daga dawowarki",kallon Mama tayi rai ɓace"haba Yaya taya za'ace kina gidan nan amma anawa yarinyar nan haka kalli fa saboda aikin banza wai Iro ne ya biyewa ƴarsa sukai ma ta duka haka",dariya Mama tayi"kibar batun nan kawai ƴar uwata bana son tashin hankali kinga mijinmu baya gari ace in ya dawo yana samun irin waɗannan labaran bazaiji daɗiba ko",sanyi jikin Aunty Mama ya yi ko nima haka"shike nan Yaya","yauwa sannu da zuwa,to ko na ɗumama muku ruwa ne ki gasata","barshi bama so ai zamu iya dafawa",dariyar Mama ta kuma tayi dama tsokana ce"Allah raka taki gona daga taimako","bama son taimakon naki",sukayi dariya,ɗakin muka shiga wanka ta min ta shafa min mai da maganin zugi a ƙafar, anan Ya Ruma take faɗa ma ta abinda ya faru,"nasani zasu aikata Ruma Nana fa kawai dan bata barin kota kwana ne shine ake ma ta kallon maraji amma yaran gidan Iro ga fitsara da rashin kunya da baƙar mugunta ba komai",kaɗa kai Ya Ruma tayi"shi kenan Aunty Mama na tafi zanyi karatu ne","to Ruma jibi Fatu da Usaina sun ce suna tafe na haɗu dasu can tasha zasu unguwa suma ","Yauwa sai sunzo da wuri zan dawo a makaranta","ai shikenan",suna magana ni kuwa har nayi bacci nan kan kujera. Ana sallar isha Umma ta shigo gidan nan tsakar gida suka zauna suke maida zancen nan Umma ke cewa"ni dai abin mutanen nan na bani mamaki wallahi yanzu wannan ƴar yarinyar miye na Iro ya taya ƴarsa su duketa","hakane kam amma abar zancen kar yaje kunen Alhaji Baffa da Iyyo dan akan Nana zasu iya ciwa kowa mutunci",kuka sukaji a bayansu nan suka waiga da sauri Iyyo ke kuka nan suka tashi da hanzari suka nufi wurinta hankali tashe"Iyyo lafiya"suke tambayarta atare"wallahi kin cuceni Halima yanzu ƴar amata kallar wannan dukan amma kice abar zancen da ba ke ki ka haifi Aisha ba sai nace mugun tace ko ƴar fari kina nuna ma ta so amma banda autar ki wallahi sai Iro yasan ya taɓa min Nana",tana kaiwa nan ta fita da sauri,dafe kai Mama tayi"ki bar wannan abin kawai Halima kinsan Iyyo sai ta ɗauki mataki dole","wallahi bana son tashin hankali",Aunty Mama ta kalla da take dariya"hankalinki ya kwanta ba","wallahi kuwa dama ke ke tsoron fitina ni kuwa bana tsoronta tunda zalinci akai dama biyayya na miki matsayinki na wadda ke da iko da gidan sannan kuma wadda ta girmeni ke kuma yanzu saiki yi biyayya ga wadda ta girmeki kuma uwa agareki kinga ƴata ma tayi bacci ni kuwa na tafi kallo dan da abaka labari gara ka bayar"tana kaiwa nan ta fice dama da hijabi kanta da tayi sallah,kallon Mama Umma tayi"narasa me yasa waɗannan mutanen huɗu kewa Nana mugun so haka Habib duk da suna faɗa kuma yana dukanta amma mugun so yake ma ta in kika shiga ɗakinsa ko zaki sha mamaki kaf ɗakin zanen Nana ne da hotunan ta tun tana zanin goyo,Iyyo duk faɗanta da masifarta kina taɓa Nana kun gama duk shirin da ku ke sannan Alhaji Baffa shima haka baya ganin laifinta sai uwa uba abokiyar zamanki ba mai cewa ba ita ta haifeta ba","eh mana bakiga ma da ita take kama ba har zubin jiki na Halima ne kinga Ruma ko ita bata kama da ita yanda Nana keyi Allah dai ya barsu tare nikam naja kaina gefe",dariya Umma tayi"ai da yafi kam muzauna tsaiwar ta isa haka sukam gidan sunga banu yau ai sai abinda suka gani","hakane Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi","amen dai". Kwasar tuwo Umman su Humaira ke yi fuuu taga wucewar Iyyo kafin matan gidan suyi wani motsi Iyyo ta janyo Humaira ta fara jibgarta,kansu matan gidan sukayo amma Iyyo ta dakatar dasu"duk wadda tazo nan saina haɗa da ita wallahi tunda ta daki Nana ita da ubanta saina rama ma ta mugwaye kawai",ta cigaba da dukanta saida tayi san ranta sannan ta barta sai ihu take tana kuka"kuma dan ubanki ko kallon banza ki ka ƙara ma ta saina karya ki bar gani na tsohuwa sai in ɓalla mutum da wannan jikin nawa",sannan ta kalli matan"kuma in Iron ya dawo yazo ina nemansa yau basai gobe ba",tai wucewarta Aunty Mama tagani tana dariya"muje Halima ko uwar Nana kadan ta daketa ba akan tayi komai ba saina rama ma ta bare waɗanda dama basu san mutuncin kowa ba",haka suka fito Iyyo nata masifa Aunty Mama na zugata can gidan Iyyon ta bita sukai tayi suna jiran Alhaji Baffa. Umma ce ta kalli Mama"Halima dama inaso muyi magana","inajinki Sa'adatu","dama cewa nayi muyiwa Alhaji Baffa magana akan Habibu yace ya samo mata kuma sunce ya turo to kinga ba maza atsakani tunda Baffansu bayanan sauran kuma ba abokan shawara bane mune ɗin dai","haba Sa'adatu ai wannan mai sauƙi ne tunda naji ana sauran yaran ma su Ruma duk suna gama makaranta za'a aurar su ai sai a haɗa kawai zamuje da safe saimu faɗa masa","to shike nan dama yace min wai zata ƙarasa kartunta ma sai nan da shekara wajen biyu","hakan ya yi Sa'adatu Allah yasa alkhairi","ameen ameen Halima yaran da za'aiwa auran ai yawa ne dasu in hakane nan ne ma kawai Ruma amma ni ai mutum wajen shida ne harshi sauran gidanjan ma za'a samu uku uku","hakane fa to Allah ya hore mana dan biki ba wasa ba","wallahi hakane amma Allah zai dafa mana ai dashi muka dogara","lallaikam dan Ruma nice uwarta dan Marƙofa ita ta koma tana magana ita ɗaya duk dai akan Aunty Mama. Ƙarfe tara Alhaji Baffa ya dawo dama yaje zaria ne ɗaurin aure kasantuwar yau asabar yana da kayan barkono su ya siyar,a tsakar gida ya samu su Iyyo suna maida zancen,da sauri Aunty Mama ta ɗakko mai shimfiɗa nan suka fara mai sannu da zuwa ruwa da abinci aka fito mai dashi"sannunki Halima lafiya dai naganku atsaye A'i","ƙwafa tayi sannan ta fara magana"kai dai bari Alhaji wai dan abin kunya yara sunyi faɗa shine dan zubda girma Iro zai kama ya daki Nana wai ya ramawa ƴarsa",hannun da yake wankewa ya daina ya ɗago yana kallonta"wane Iro ɗin kuma","kaji ka ma Alhaji Iro nawa muke dashi babban Iron dai","me ya haɗa yaran da ya kama ya shiga har ya daki jaririyar yarinya",bayani Iyyo ta shiga kwance mai kamar gabanta akai"amma wai Halima tace a bar maganar sai wannan Halimar ce ranta ya ɓaci amma ta nuna",kansa ya girgiza"kwantar da hankalinki A'i kema Halima koma gida zanwa tufkar hanci",sunkuyawa tayi "to Baffa,Iyyo saida safe","to ƴar nan Allah ya miki albarka saida safen","ameen Iyyo",ta wuce tana jin daɗin yanda tun zuwanta gidan mutanen basu taɓa daina nuna ma ta so ba har yanzu da girma ya sawo kai". Alhaji Baffa abincin shi yaci ya ƙoshi sannan yasa aka kira masa Ya Ashiru da sallama ya shigo"kai Ashiru jeka tasomin kawunka Iro ku taho tare injini","to Alhaji Baffa",ya tashi ya fita yana dariya yasan yau akwai drama. Vote Share & Comments Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂ 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 *𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔* 𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠 Story & written by *FATIMA AMINU* *Ummu Saddi'q* chapter 5️⃣ Baffa kallon Iyyo ya yi"narasa me yasa kwata kwata Iro yake irin haka baya da ɗabi'a irinta Rabilu gwarashi ba komai yake shigaba amma shi sai kace mace komai shiga yake","bari kai dai Alhaji kuma matansa ne ke ɗaurewa yaran gindi suke abinda sukaga dama suna tsefe kama kamar majinyatan birarrika",ƙwafa ya yi"ai zasu haɗu dani kaf har yaran nasu","Assalamu alaikum",sallamar su ta dakatar da Alhaji Baffa daga maganar da yake"ameen wa'alaikumul salamu Ashiru yauwa ka samo shi,sannu Iro yanzu fisabilillahi ƴar ɗan uwanka ba ƴarka bace shine gotai gotai da kai zaka kama ka duki Nana ƴarka ta wajen ashirin dan girman banza,kuma ku riburbuɗi yarinya kaida ƴarka",dafe kai Kawu Iro ya yi dan sharrin Nana baisan zaiyi tasiri haka ba"wallahi Baffa ban duketa ba kawai dai na ranƙwasheta nace karta kuma","shi ranƙwashin ba duka bane kuma sa'arka ce ma wai ka kiyayeni fa akan Nana zamu raba hanya dakai",ƙara kallon Baffa ya yi yana ƙifta ido saboda ɓacin rai"yanzu Baffa ace wai wannan ƴar yarinyar tana kitsa abu amma kuna ɗauka kuma kaf yarannan jikokin ka ne amma kana nu na kafi san ta duk yawansu","an nuna ɗin kaji nace an nuna ɗin",Iyyo ce ta dakatar dashi"kai har kana da abin cewa anan yarannan naku inba tasu ta kawo su ba ko ƙeyarsu da niyar gaisuwa muna gani har matanku basa shigowa nan sai su Halima da yaran su sai Sa'adatu in aka tashi kullum safiya sai sun shigo sungaida mu inda aiki suyi haka masu auran ma suna da iyaye amman in sukazo nan suke sauka daga baya suje ga iyayensu amma naku fa,to bari kaji ko hararar Nana ƴaƴanka suka kuma yi basu zan daka ba kai zan daka agaban ƴaƴanka sai dai ciwon zuciya ya kashe ka,tashi ka bamu wuri anan",baice ƙala ba a matsayin su na mahaifansa ya ɓata musu rai sai ya wuce yana wulla hannu kamar wani yaro ƙarami,Ya Ashiru ne ya zauna inda Baffa ke zaune yana ta dariya tun ɗazu",Alhaji Baffa ne ya kalleshi"kai kanka ɗaya ka ke ta dariya,da ƙyar ya dakatar da dariyar"yanzu Alhaji Baffa kan Nana ku ke wannan ɗaga muryar",Iyyo ce ta harareshi"kanta ne fa ubanmu ya akai","wallahi ku daina biyewa Nana batajin magana itama..."bai kai ayaba Iyyo ta ɗakko taɓarya da gudu ya miƙe ya fice yana dariya"lallai ma tsaffin nan sunyi nisa bari na kama kaina dan tsaf wannan tsohuwar zata gicciyeni"ya wuce wurinsu Ibrahim daya hanga can rumfar me shayi ana zabga hira kamar yaƙi. Kamar wata ƙaramar yarinya haka Aunty Mama ta shigo tana sanɗa amma kash kamar a sama taji muryar Mamar da take sanɗar dan karta ganta"sannu uwar Nana kun gama ɗaukar fansar",dakatawa Aunty Mama tayi tana juyowa"sannu da gida Dada wallahi mun gama kuma agaban iyayenta Iyyon ta lakaɗeta itama kai ai yau naji daɗi","ai kun kyauta taho muci abinci ke nake jira",da sauri ta ɗago ta kalle Mama wadda ta shige cikin falonta,jiki sanyaye tabi bayanta a falon ta cire hijabinta suka zauna,abincin ta janyo fulas ta tura ma ta"zuba mana Mamar Nana",ƴar dariya tayi"kai Dada","to me kike so nace na lura nan gaba kaɗan filin dambe zaki buɗe saboda Nana",tana zuba abincin tayi ƴar dariya"sakko Dada, nifa baki sa ni ba wani irin so nakewa Nana kawai ki barni Allah wallahi kinji na rantse bana son su Ruma yanda nake son Nana shi yasa bana daure abu in aka ma ta",cikin sanyin murya Mama ta e"na yarda dake Halima amma kinayi a hankali wataran kar dai ta kaiki ta baro",dariya tayi"karki damu akan wannan nasan Nana nada tsokana amma tanada faɗar gaskiya wani sa'in ne in tsiyarta ta motsa abinda ma ba'aiba sai tace anyi","to dai ku kuyi a hankali kar wataran ta jawo azo har gida a muku dukan tsiya"kwashewa tayi da dariya"haba dai Yaya bamai dukanmu kafin takai wannan matsayin ta girma kika sa ni ko tashiga ɗakinta da wuri","uhmm magana kanta ta isheni kinga ɗazu Ruma kece min waɗannan yaran zasu zo gobe","eh kuma sunce kwana biyu zasuyi","to Allah ya kaimu goben","ameen Dada gashi ma ƴata tayi bacci bata ci komaiba wallahi","saiki tafi dashi dan kinsan tabbas zata tashi ta nema komai dare","haka za ayi kuwa"bayan sun gama cin abincin sun jima suna hira sannan Aunty Mama ta ma ta saida safe ta fita. **** Kamar an kunto shanu haka ya shiga gidan ball yake da duk abinda ya tare masa gaba Umman su Humairan suna tsaye dama suna ta zage zage kan abinda ya faru,ihu bayan hari kenan sai gashi kuwa ya shigo Saude ɗaya daga matansa kenan ita ta fara magana "haba Malam miye hakan kalla yadda ka ke ball da kaya inka fasa mana fa siya mana zaka yi",cikin masifa ya hayayyaƙo kanta"bazan siya ba kinji nace bazan siya ba kuma saina ma fasa",yasa ƙafa ya take buta ƴar lamba biyar"gashi na fasa yi uwar da zakiyi ingani ɗauki mataki nace ni sai inci uban mutum wallahi",Umman Humaira ce ta tare"wai Malam maye hakan kalla abinda akazo har gida aka mana amma kazo kana ta mana hayaniya maimakon ɗaukar mataki","rufe min baki Rabi ai nagani kuma nasani ko an faɗa miki ban sani ba bane,ni kinsan mai akai min to ki barni ai itama Aishan dan uwarta tasan halin waccan sheɗaniyar yarinyar da baƙin sheri amma ta shiga sabgarta ita ta sa ni nidai abinda na sani saina kassara rayuwar yarinyar wallahi dalla malamai ku wuce ni ku bani abinci"ya wani bugo wata kujera ya zauna akai,taɓe baki sukai suna jan tsaki nan mai girkin ta kawo mai abincin tuwone na masara miyar kuɓewa bashasshiwa amma in ka ganta saika ce kai aka wanke,wani ashar ya lailayo ya ƙunduma"wannan wane irin tuwone Rabi kalli tuwo kamar talge kalli miya kamar a bursun ina kuɗin cefanen da na bayar,kinyi zubin dashi wallahi baki isaba mutum yaci wannan ai sai ya yi zawo zoki kwashe shi kan naci miki mutunci wallahi",sumi sumi ta zagayo ta kwashe ji yake kamar ya rufeta da dukan tsiya amma ya barta,tashi ya yi ya fice bin bayansa tayi da tsaki tana hararar sa anan Saude ma ta harareta ta kyaɓe baki tace"dama an auro jinin zazzagawa ai dole aci tuwo mai ruwa kamar ba garin ɗaure shi miya kuwa ana burin kere sa'a ran auren ƴa ai dole asha garara Allah dai ya kyauta","ke Saude ki kiyayeni wallahi saina zubar da waɗannan haƙoran kamar ɓarin tsaba ai gwara wannan tuwon kan nagidan tsoho da ace nacan yafi na nan ai da tuni an ware amma an nane saboda hakan samune","wallahi kinsha ƙarya Rabi ina zaman gidannan ne dan ƴaƴana ba dan ina gudun karna fita a dafa su a cinye dan nasan kurayen gidan nada yawa"cak Jummai da tazo wucewa ta dakata kanta ta ɗago ta ƙare ma Saude kallo"ke Saudala ki iya bakinki kuma ki tsaya iya inda aka ja ki karki sa wanda zai soya ki dan haka ki iya bakinki ko yanzu kinsan nasa a aunaki gidanku mu dafa mu suye ƴaƴan tunda dangin mu ɗaya dake duk mayu ne mu",tana kaiwa nan ta antaya musu harara tai gaba tana juya ƙugu kamar na kura",Saude ma hararar Rabi tayi ta buga tsuka tai gaba nan ita Rabi tai ball da kayan gabanta ta shige ciki tana zage zage. Yana fitowa ya haɗu da Kawu Rabilu ganin sa fakan fakan yasa shi tsaida shi"Rabilu ina zuwa haka kamar zaka tashi sama",tsayawa ya yi yana tsaki"bari Iro ace wai mutum ya haɗa mata amma kaf ba tagari kalli ace wai megida a gidansa amma abinci mai ɗanɗano ba za'a iya yi masa ba kullum rana ta Allah ina jiyo ƙamshin abincin gidan margayi kona gidan Nuhu amma ni matana sai son zuciya da burin tara abin aljihu",tsakin shima ya yi"muna ɗaya dakai ai muje muci abinci mai kyau da kuɗin mu kowacce shegiya taci wanda ta girka tunda haka sukace",wucewa sukai zuwa ga wajen me shayin da su Ashiru ke hira, kallon su Ashirun ya yi yana son yin dariya yana tsoro amma shida Ibarahim da Haruna sai dariyar ciki suke suna gani suka zauna kowa yace abashi indomie guda uku manya da ƙwai huɗu sai shayi da biredi,ba a ɗau wani lokaci ba aka miƙo musu nan sukaita zaƙal ƙala tashin duk yawan abincin sukai tas sannan suka biya kuɗin kamar wasu samari suka koma gefe suna hira amma kaf ta baje sirrin gidajen su ce sai bawa juna muguwar shawara suke a haka suka rabu,Ashiru ne ya kalli Haruna da Ibrahim ya kwashe da dariya sunsan halinsa sarai akwai jan magana"gaskiya ƴan uwa mun mori iyaye bari kuga zuwa goma ƴan matan gidan ma zasu fara zuwa siyan tasu haka ma su Sumayya wallahi gwarama su musu aure har tausayi suke bani ace agidanku ba za a girka mai daɗi ai dole suyi son kuɗi","zancenka haƙƙun yanzu su Maryam duk randa suke son abu bamu da kuɗi ko to su suke haɗawa ko su faɗawa Babban Yaya a kawo musu kaza kuma wallahi ko taya ne sai ya kawo musu in ba ranar ba washegari",cewar Ibrahim"hakane nima ni ɗaya amma matar nan da kuɗinta take mana abu ni da Baba kasan ƴar kasuwa ce",Haruna ya faɗa kwashewa sukai da dariya suka tafa,Ashiru yace"wallahi Ibrahim Nabilan gidan ku nake so to amma nasan ita bata sona dan nasan tana da saurayi ko na ma ta magana bazata saurare ni ba","kai haba amma nayi farin ciki sosai da kaina zan ma ta magana shi wanin na yafi nagida ne ai ka kwantar da hankali kawai kamar ka samu ƴar farar yarinyar nan suka saka dariya","sannunku sarakan gulma",juyawa sukai sukaga Babban Yaya"a a Babban Yaya yau kuma yawon dare kaje","kuji min yara yawon dare saikace wata mace karuwa,ban sani ba ku biyoni gida akwai maganar da zamuyi ko kuma ku bari ma haɗu a masallaci da asuba naso harda sauran amma nasan ba zasu fahimce ni ba kawai iya ku kuɗin ma haɗu",tom suka amsa sannan ya wuce gida garejin gidan Iyyo ya shiga ya aje mashin ɗin sannin sunyi bacci yasa bai shiga ciki ya fito ya shige gida,tsakar gidan shiru sai ya wuce ya buɗe ɗakinsa ya shiga ko ina ashare tas har turaren wuta aka saka kuma yasan aikin su Maryam ne sun san shi baya shiri da datti. Vote Share & Comments Ƴan uwa Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂ 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 *𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔* 𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠 Story & written by *FATIMA AMINU* *Ummu Saddi'q* chapter 6️⃣ shirt ɗin dake jikinsa ya cire ya zauna bakin katifa yana sauke numfashi maganganun mutumin da suka haɗu ɗazu na faɗo mai aransa wane irin aiki zai bashi da yace dama mutum irinsa yake nema ya yi iya tunaninsa amma bai hango komai ba da sanyin jiki ya miƙe ya ɗau riga mara nauyi yasa ya fito tsakar gidan zuwa ɗakin Umma tana zaune dasu Maryam ana shaƙiyanci ita kuma tana musu dariya,ya yi sallama ya shigo"Babban Yayan mu ba irin nakowa ba sannu da zuwa"suke faɗa,kaɗa kai ya yi"Allah ya shirya minku kuna nan kuna zuba ba kuyi bacci ba",dariya sukai sukace"kai muke jira ka kawo mana tashi watstsake",hararar su ya yi"a a tashi aguje zan kawo muku yau bani da kuɗi kunga wata yaje ashirin kuma na biya bashi da kaf kuɗin ko account ɗina wayam yake sai dai in Umma ce zata zuge wannan babbar lalitar tata ta bamu mu siyo ƙwai da hantun"ya faɗa yana kallonta","mai ƙwan zan baku ku siyo ba ƙwai kai wuce ka bani wuri","to kunji ku bari gobe zan samu wasu kuɗi jibi duk Katsina zamu sada zumunta tunda kunga juma'a ce ranar lahadi saimu dawo",ihu sukai aka kashe hannu"Allah ya biya Babban Yaya"saiku faɗawa Ruma",suka ƙarasa "da ƴar rigimarka ba kasan ko a ƙasa zamu saitaje",ɗan murmushi ya yi"na sa ni ai harda ita","tom Babban Yaya",Ummace ta kallesu"in kun gama zubar saiku ɗakko masa

Chapter 2 of 32