Share this page
dariya"naga me zaki ci yau". Yana fitowa ta tare shi da masifa bai kulata ba ya cigaba da shirinsa maganar ce ta ishesa ya aje cumb ɗin hannun sa ya juyo gareta"kuɗin ki ne?",shiru tayi"to tunda ba kuɗin ki bane in ki ka ƙara min magana saina sauya miki kamanni dan ni ko da asiri ba wanda ya isa ya hanani inyi alkhairi ina fatan kin gane dama kince Nana taci abinci ashe bacci ma take sanda ki ka kai ma ta hakan ya ɓata min rai sosai",yana kaiwa nan ya ɗauki ƴar saman rigar sa ya fito,wani irin tsaki tayi tai wurgi da towel ɗin da ya aje ta zauna jaɓar tana dafe kanta",na gama kenan ya shigo"uwar rigimammu me kuma ake ƙullawa naji ki shiru haka",tasowa nayi na faɗa jikinsa"ina kewar ka Babban Yaya",rungumeni ya yi tsam"nima haka matata",ɗago kaina nayi ina kallon sa na mai alamar kiss sunkuyo da kansa ya yi ya ɗora bakinsa kan nawa biye masa nayi dan ina kallon ta ta labulen ƙofa wato matar nan laɓe ne aikin ta ko bari na ma ta tsiya janye bakina nayi a nasa ina buga ƙafa da sauri ya saki rigar ya riƙoni"me ne kuma",ƙirjina na nuna masa"ba tunjiya da ka barsu ba aukw ƙaiƙayi",wani kallo yamin yana murmushi"cire ma za na kauda wannan ƙaiƙayi bayana na juya shi kuma yana facing labulen hannun rigar na sauke ko kunya banaji na matsa jikinsa hannun sa biyu yasa ya shiga murzar su yanda yaga dama,ba shiri ta matsa a wurin tana mamakin yanda gaba ɗaya ya ruɗe ya rasa ma ina zaisa kansa daga taɓa ƴan waɗannan a bubuwan a wurinta kuwa sai dai ita ta ruɗe shi kuwa ko gezau ba ya yi,mun share mintuna a haka sannan nace sun daina ya barni yana lumshe ido ta bayansa na kwanta na zagaye cinkinsa da hannuwa na bule idon ya yi"zaki bacci ne",kai na ɗaga janye ni ya yi ya tashi"zoki kulle ƙofar ki ni zan wuce office",bin bayansa nayi na kulle na dawo ina tsalle da rawa na maida rigata na janyo waya ta na shiga kiran Ya Nabila. 😀😀😀😀😀 UMMU SADDI'Q CE 🌹🌹🌹🌹 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 28 Jama'a kwana biyu fa Aunty Hajara na neman yanda zata ɓata min ta rasa komi tayi saina maida ta mahaukaciya kona maida ma ta da ɓacin ran kanta gaba ɗaya ya rasa ya zata yi dan haka yau saita kira yayarta ta faɗa ma ta meke faruwa shawara ta ba ta kuma ta ɗauka,gashi kuma yau girkina ne. Tun da safe ya faɗamin zaiyi baƙi hakan yasa na tashi tsaye kamar wata uwar mata na haɗa masa abinci mai kyau bayan sallar magariba ya shigo na zata ma zan gansa da baƙin sai naganshi shi kaɗai wanka na rakasa ya yi"Babban Yaya ina abokan naka fa","suna gidan da na sauke su yanzu zan kai musu abincin amma fara ba ni nawa naci dan yaunwa nake ji",dariya nayi na kama hannunsa zuwa daning sannan na kira Aunty Hajara ta fito tana yanga da yauƙi"Habibe welcome"ɗago kai ya yi ya kalleta"baki iya hausa ba",hararar sa ta yi kaɗan shifa wannan gayen ɗan latsin rainin wayo ne"sannu da zuwa to","yauwa ya gida",wani taɓe baki ta yi"gashi nan dai ba daɗi in baka nan kasan kaine sinadarin gidan","madalla to"daga haka yay shiru ba haka taso ba sotai ya biye ma ta suyi ta maganganu,ni kuwa ko a jikina abinda ta yi,tavriga kowa zuba abincin sannan na zuba masa naja gefe na zauna,kallona ya yi"ke baki ci ne",kai na kaɗa"naci dana gama ai",maida kansa ya yi kan abincin ya ɗiba yakai bakinsa ba zato ba tsammani wani azababban gishiri da mugun yaji ya kaiwa kwanyar sa ziyara a take ya fesar da abincin bakinsa nan da nan idanuwan sa sukai ja ya ahiga tari baji ba gani da sauri nayi kansa"Babban Yaya lafiya"kafin kace me hawaye ya wanke min fuska ruwa na bashi yasha sannan tarin ya lafa,amma duk ya yi wujiga wujiga,sannu nake ta jero masa sai dai ko ɗaya bai amsa ba,wani kallo ya ɗago yamin wanda yasa cikina ƙugi sarai nasan Babban Yaya bai iya fushi ba sunkuyar da kaina nayi kawai gabana na faɗuwa,itama ci tayi ta furzar da sauri"Nana wane irin abinci ne wannan yaji da gishiri kamar zasu fasa ƙwaƙwalwa"ɗagowa nayi a fusace na ce"ke ce ki ka zuba yaji da gishirin ko amma ni dai nasan ƙalau na gama abinci na s...."tass naji saukar mari a fuskata ɗagowa nayi da sauri naga Babban Yaya a tsaye kamar zai rufe ni da duka dafe kuncina nayi na fashe da kuka,tsawa ya daka min saida na tsorata"rufe min baki mara kunya ta faɗa miki gaskiya ne zaki ma ta rashin kunya",cikin kuka na ɗago kaina nace"wallahi banyi abincin nan da yaji ba bansan ya akai yaji da gishiri suka je ba",tass ya ƙara min wani"to ƙafa garesu da zasu kenan"tashi nayi da gudu ina dafe fuska ta na wuce ɗakina gado na faɗa na shiga kuka dan abin yamin ciwo ba marin ke damuna ta ya akai gishiri da yaji yaje cikin abincin da naci ɗazu amma banji ba a sannan sai yanzu ga abincin da yawa kenan sai dai ayi a sara kuka sosai nake har kaina ya shiga ciwo ba ƙaƙƙautawa amma naƙi shiru,Hajara ce ta tashi tazo inda yake ta shige jikinsa"kayi haƙuri Habibe kasan yara a hankali zasu gyara kaga abinci can nayi su Yaya sunce zasu amma sun fasa sai jibi ka kai musu kawai shima da yawa",godiya ya ma ta sannan ta rakashi da kwanukan mota ya fita,banji sanda ta shigo ba sai dai naji maganar ta a kaina"ya dai manyan mata ta ya a kai haka ta kasance ne,ko da yake na faɗa miki karki kuskura ki haɗa sabga da ni amma kinƙi ji to kisa ni da irin waɗannan salon sai kin gudu da ƙafar ki kinbar gidan nan",ina daga kwancen na go ge fuskata sannan na ɗago fuskata duk shatin yatsun hannun sa,wani kafirin murmushi na ma ta na shafa fuska"kece baƙuwar kiga Babban Yaya ya dake ni to bari na baki wani labari Babban Yaya harda belt ɗin injin markaɗe ya dake ni ya zane ni da bulalar dorina a makaranta gaban kowa ke a titi Babban Yaya ya mazge ni amma bari kiji wata sabuwa a gaban Mama Babban Yaya ya durƙusa ya ba ni haƙuri dan nayi fushi dashi,wannan marin kuma da yamin gyara ne in baki sa ni ba kinga ya nu na in nayi abu in na lura saboda miyagu,sannan kisa ido ki baje kunne zakiga ya zata kaya a gidan nan tsakanin ni dake na miki alƙawarin saikin daka yajin da yafi na farkon aure ne da kikai kin ƙara nufar gidan ku kuka kuma wallahi sai kinyi goman nawa ai ni nan da ki ke gani sau ɗaya ake nasara akaina ba na barin ayi ta biyu saboda ni ɗin ta musamman ce kinyi da ƴar halak uwargidan Babban Yaya ko ba komai kin nuna min insan zaman da zanyi dake ni da na zauan Gwaggo Asama'u birnin masifa duk duniya nita tsana kamar ance ma ta nice ajalinta amma Allah bari kiji da ƙanwar gyatuminki na ma ta tarko saida ta kirani da ƴar albarka kinga ƙanwar ubana ce amma da daga mayya sai shegiya take kirana kinga kuwa ke ba komai bace,fitar min a ɗaki tunda ba kiranki nayi ba ko billahi in miki sharrin da har ki mutu bazaki manta da ni ba",tun da na fara magana tayi zuru tana kallona kunsan ni mutum ya faɗi ɗaya na faɗa masa tamanin ne,ƙala ba ta ce ba ta fita dai tana dariya batasan na ganota ba yaƙe ne take. Ina idar sallar isha na samu nayi wanka da towel ɗin na kwanta hawaye nabin gefen ldanuwa na ga yunwa inaji amma na kasa cin komai,sai wajen goma kuwa ya shigo sanda ya shigo gidan tasha wanka ta matse cikin kayan bacci fan ɗarin ka tsirara kome take tunani oho da hanzari ta shi ta rungumeshi jansa kujera ta yi ya zauna tana ta shafa shi sai niyar kiss take masa,gajiya nayi da kwanciyar gudun kar yunwa ta lahanta ni yasa na tasho a haka na fito dan zuwa kitchen in samo ruwan ɗumi ko tea nasha,fitowa ke da wuya na gansu amma sai na ɗauke kaina na wuce ita ta ganni shi kuwa saida na shiga kitchen ya ganni ruwan ɗumi da kullum yana buta shi na ɗiba a bakin ƙofar na tsaya na goge hawayen fuskata sannan na fito na koma,tashi ya yi yana ma ta saida safe kan tayi magana ya wuce,tsaye nake ina zuba madara a ruwan ɗumin dana ɗebo ya shigo da sallama da sauri na aje kofin na go ge hawayen fuskata na juyo da murmushi a fuskata"sannu da zuwa Babban Yaya",wani irin sanyi jikin sa ya yi rigar ya jefar a ƙasa ya nufoni,da hanzari na juya wani irin hawaye na sauka a kumatuna duka hannuwan sa yasa ya rungumo ni jikinsa wani irin zafi yaji a jikin nawa ya lumshe ido,kuka mai ƙarfi ne ya ƙwace min na rufe idona na shiga reroshi kamar raina zai fita,juyo da ni ya yi ya rungumeni sosai"am sorry Nana nayi kuskure ki yafe min"kwantar da kaina nayi a ƙirjinsa jikina har rawa yake wani haushin kansa ma yaji yana ji ta ya akai kawai ya mareta daga ɗan kuskure kuma ma ai tayi ƙoƙari da ta iya yunƙurin girki mai yawan haka,ɗaukata ya yi cak ya aje akan sofa share fuskata ya yi da hannunsa sannan ya ɗakko kofin yazo gabana ya durƙusa da kansa ya shiga ba ni tea ɗin ina sha ina kuka kaɗan nasha na kauda kaina na janye hannunsa daga gabana"ina baki ƙoshi ba kinga fa jikinki na rawa kuma yunwa ce","ni na ƙoshi"na faɗa cikin kuka aje kofin ya yi ya tashi tsayi ya ɗau key zai fita"Babban Yaya ina zaka je","zan samo miki abinda zakice ne bazan iya jurar ganin kina haka ba saboda yunwa",tasowa nayi nazo na kwanta a bayansa na zagaye cikinsa da hannuwana"karka fita miye amfanin abincin gidan zan dafa naci ka raka ni kitchen",aje mukullin ya yi ya kama hannuna muka fito da sauri ta koma ɗakin ta tana haki"kaga shegiyar yarinya na zata zatai fushi tamai rashin kunya ya koreta ko kuma ya dawo ɗakina mistttt wannan ƴa ko mayya wallahi" . Muna shiga na fara haɗawa indomie kayan ƙwalam sannan na ɗorata kome nake yana ta bina da kallo amma ni ban kalle shi ba ko sau ɗaya,jingina nayi da sink nai shiru kafaata ya dafa ya juyo dani zanyi magana ya sunkuyo ya ɗora bakinsa kan nawa wani irin sumbata ya shiga masa yana tura hannunsa kicin gashin kaina saida ya gaji dan kansa sannan ya zare bakinsa a nawa nai saurin juya masa baya ina goge hawayen dake zuba,lumshe idon sa ya yi ya dawo gabana ya kama hannuwa na ya durkusa gwiwarsa a ƙasa"ki yi haƙuri please mana *RAYUWA TA* nima durƙusawa nayi na faɗa jikinsa ina sakin kuka"kayi haƙuri bazan ƙaraba wallahi bansan ya akai haka ba amma zan kula a gaba",ƙanƙameni ya yi yana shafa kaina"baki min komai ba kuma nayi kuskure dana mareki amma zaki rama ai ko?",dukansa na shiga yi"ni bazan rama in mari mijina ko naci masa kwala sai ka ce jaka". Da sauri Aunty Hajara tabar ƙofar kitchen ɗin tana kama baki ranta in ya yi dubu ya ɓaci kenan ita yarinyar ke nufi da jaka. Tashi nayi ma za nayi ina sauke indomie sannan na soya ƙwai mai yawa suk yana kallona a tire na ɗora ya ɗakko da kansa muka fito zuwa ɗaki tare muka ci yana ta lallaɓa ni kamar ƙwai shi ne kawai ya yo wanka sannan yazo ya ɗaukeni cak ya kashe glope ya kwanta yana janye towel ɗin jikina zallana na kwanta a jikinshi,ganin ba haske yasa a dole tabar window ta koma ɗakin ta,amma ta kasa bacci ta rasa ina zata kanta dan baƙin ciki. Washegari kan ta tashi ma ya fita dan yana da aiki tunani ma yake zaije india ne dan akwai taron da yake so suyi na nasarar da suke samu. Wanka na ɗauka na tsuke cikin jeans pencil da wani ja mai kyau da baƙar riga ko ƴar cikin ma ban sa ba ɗaure gashina nayi na fito da kwanukan da nama Babban Yaya break tun da farar safiya,fitowa ta ke da wuya muka haɗa ido da ita na aika ma ta wani musulmin murmushi na wuce ina ce ma ta"kin tashi lafiya",jefo Ni t yi da filon kujerar hannun ta"ta ina zan zauna lafiya ina tare dake shegiya ƴar bariki",ban kulata ba saida na kai kwanukan ma dawo na tsaya a gabanta cak na kama ƙugu"wai me ki ke tunani Aunty Hajara inji haushi dan ya daki halalin sa in ya dawo na masa hauka lala mu namu salon fushin shine wanda ki ka gani jiya bama hauka amma sai an kai gwiwa ƙasa a kan mu kinga kenan salona daban ne dan haka ki bi ni a hankali madam Habib"nai wucewa ta na barta,tsaki ta yi"zanyi maganin ki ne salon naki sai ya gudu ya barki ƴar ƙarama dake sai kaɗiri fere",kome take faɗa ina jinta amma nai shigewa ta ɗaki na gyara shi tas sannan na kwanta kan sofa ina dan na wayata kira ne ya shigo naga Babban Yaya na da sauri na ɗauka"Babban Yaya namu na mutunci",dariya ya yi"ya ki ke","lau nake kaifa","lau ba lau ba","meya same ka na faɗa cikin shagwaɓa"kewar kyakkyawar matata nake","to ka dawo gida mana","sai anjima akwai abubuwan da nake settling ne","to Allah ya yi jagora ya bada sa'a",kiss ya min ta wayar nima na masa mai ƙara yana dariya ya kashe. Bayan kwana huɗu ya fara shirin tafiya india dama bansa rai ba da dai matarsa ne saida sukai kaca kaca sannan ta haƙura,sosai Ya Rumana ta shiga tayya ni masa shiri kayan ciye ciye kala daban daban na masa shi kansa da ya gansu yaji daɗi sosai ana gobe zai tafi ya shigo gidan da kaya a hannunsa kuma abin takaicin wurin ta shine kwana na ne ba yanda zatai dole ta bar min shi,tun magariba na saka abuna a ɗaki ina kuka yana tsaye riƙe towel a hannunsa ya juyo ya kalleni"wannan kukan naki fa na iskanci ne na sa ni",tasowa nayi na faɗa jikinsa"to in tafi ba waɗannan zasuyi tamin ƙaiƙayi ba",hannunsa ya ɗora a ƙirjina"daga yau in muddin ba ana gobe zan dawo ba kar ku kuma ma ta ƙaiƙayi zan saɓa muku",yanda yake yi ne yasa ni dariya ba shiri sura ta ya yi muka faɗa gado yana ina samansa bakina ya laluba ya ɗora nasa wani zazzafan kiss na shiga karɓa mai haukata kwanya,a ranar kuwa sunci ubansu bakina har wani zugi yake kuma duk leƙen da take bata gano komai ba dan dinɗin yawa ɗakin yau. Tun safiya na haɗa masa break ya karya ina ta binsa sau da ƙafa kamar tare zamu tafi daman kayansa sunyi ready a mota tuni yana gamawa nace"to ka yo ma ta sallama mana a bata kulawa sosai yadda bazata damu ba in baka nan ai kana da sauran wajen awa biyu tunda sai tara zaku tashi ni bari na jiraka a gida",nasa hijabina yana ta bina kallo"ka taso mana"tare muka fito na wuce ƙofa ina ɗaga masa hannu"kayi komai fa ni na yarje maka"na fita ina dariya,kai kawai ya kaɗa yana jin wani irin sanyi a ransa,tana kwance tana kuka ya shiga tana ganin sa ta tashi ta rungumeshi tana sumbatarsa biye ma ta ya yi ta yi mamaki sosai ganin yanda ya biya ma ta buƙarta ba tare da damuwa ba,bata biyo shi ba shi kaɗai ya ƙaraso ban nu na komai ba na fito zamu rakashi motar da ya shiga na shiga tun da banyi kukan ba sai yanzu shi kansa dariya ya shiga yi sannan yace"ki nuysu mana kiji zan ɗora miki wani nauyi zaki iya"shiru nayi ina kaɗa kai,wani chek ya ɗakko ya yagi uku yasa hannu sannan ya bani"ga waɗannan ki riƙe da kyau ki ɓoye karki bari fa wani ya gani nayi magana da masu aikin gidan su Sadiya zasu zo gidan nemana duk kuɗin da suka ce za'a kashi ki rubuta kina cirowa da wannan chek ɗin ki basu,duk abinda Sadiya ke nema kuma kuɗin ɗakin ki ai kinga nake ɗakkowa kina ɗauka anan ki ma ta amfani dashi shima Murtalan na sallameshi kema in zaki amfani da kuɗi ko zaki bawa wani kina ɗauka kanki tsaye Hajara ma na sallameta dan haka ki kula da kanki banda tsokana kinji na yarda dake ne shi yasa na barki a gidan tare da ita,sannan akwai leda a ɗakin ki ƙasan mudubi ki duba miye a ciki duk a binda ki ka gani ki kirani kawai",a kafaɗar sa na kwantar da kaina"duk zanyi abinda kace Babban Yaya Allah ya tsare ya bada sa'a",kaina ya ɗago"ameen Nana ta kina min addu'a kinji",kai na ɗaga masa ya sunkuyo da kansa ya min kiss a baki,dai dai motocin na tsayawa tare muka fito saida ya shige ciki sannan muka koma mota sai gida ban tsaya ko ina ba na shige cikin ɗakina na ɓoye chek ɗin da ya bani sannan na ɗakko ledar da ya faɗa ina buɗewa na buga tsalle na kwaɗa ihu uniform ne a ciki kala uku da sandals uku da jaka sai littafaina da text books wani kati ne aciki na ɗakko na duba anan naga makarantar mu ce ai rawa na shiga yi nai ma za na kira shi dama bai shiga jirgi ba ya ɗaga"yadai ƴar makaranta","wayyo Babban yaya nagode nagode Allah ya maka a binda kamin","ameen Nana kikula sosai banda wasa banda ƙawaye barkatai ki faɗa musu ke kina da aure ba kowa ki ke kulawa ba","shike nan Babban Yaya Allah ya kare ka","ameen Nana zan kira ki"tom, nace na kashe na aje ina faɗawa kan kayan,tashi nayi da aauri na ɗakko dutaen guga na tuɓe kamar zanyi dambe na go ge su tas sannan na fito"Aunty Hajara sai ina kuma",juyowa tayi tana hararata"inda ki ka aiken can zanje ƴar rainin wayo",taɓe baki nayi"ni na fasa aiken koma to",filon kujera ta ɗauka ta jefo ni dashi"shegiyar yarinya mai kama da mutanen farko",cafe filon nayi"a dawo lafiya a yo min tsaraba ko na ada tsiya","uwar tsiya zaki tada"tasa kai ta fita,nayi dariya kawai na wuce kitchen doya mai yawa na fere na dafa sannan na soya ta da wai na cika kula wanka naje nayi nasa doguwar riga da gyalen ta na ɗau kulata na rufe gidan na kamo hanyar gida. Hayaniya na jiyo a falon Mama na nufi can da sallama na shiga,da sauri na aje flas ɗin na an taya kansu ina ihu dariya suka fashe da ita"Allah ya shirye ki Nana","Aunty Fatima amma yanzu ku ka zo naga ban daɗe da tafiya ba","yanzu muka zo yau zamu koma kuma hanya ce ta biyo damu kaya muka zo saya nan da wata huɗu za'ai bikin ƴan mata huɗu a gidan mu amma duk zaku zo ko","sosai ma kuwa"na juya ga Aunty Mamaa tashi nayi na faɗa kanta"Aunty Mama zan koma makaranta",da sauri ta rungumeni"da gaske ƴata","eh wallahi ya siya min komai ran monday zan fara zuwa kinga ai gobe friday basai naje ba","hakane Allah ya bada sa'a to","ameen Aunty Mama ta",anan gidan na wuni sai yamma na koma bata dawo ba banji tsoro ba nai zamana ni ɗaya har dare ya yi shiru bata dawo ba kulle ko ina nayi na koma ɗaki nai addu'a na kwanta a buna dan na kirashi ba ta shiga ba. Washegari da safiya ya kira ni da sauri na ɗauka na rushe da kuka,daga can lumshe ido ya yi"yadai sweet Nana","nayi kewar ka fa sosai","nima haka matata amma da fari ki daina kukan nan tukunna kashe na kira ki vedio call",da sauri na kashe na tashi na tashi na sauya riga zuwa halb best na kunce hashina na gyara kwanciyata a kan gado saiga kiran ya shigo da sauri na ɗauka"Hii Husband",lumshe ido ya yi"Hello wife kinyi kyau sosai"murmushi nayi namai kiss",ba shiri ya yi dariya"Nana ta takaina","Babban Yayana na kaina ji nake kamar na biyo ka","in kin biyo ni me zaki min madam Habib",tashi na yi zaune na janye gashin dake ƙirjina"sosa min su zakai kaga ba suji maganar ka ba jiya hana ni bacci sukai",dariya ya saka ba shiri,turo baki nayi na maida kaina na kwanta saiga hawaye sharr"shiiiii yi shiru mana matar ai da wuri zan dawo bazan daɗe ba kamar da kiyi ta tar ƙaiƙayin ki",dariya nayi"au dama ana tara ƙaiƙayi","eh mana in ma ba'a ayi za'a fara daga daga kanki","to shike nan yimin waƙa sai nayi shiru ko kuma nayi ta kuka","karki kuka My Madam buɗe kunan ki da kyau",kamar wasa Babban Yaya ya shiga rera waƙar Aisha ina ta dariya mun dale muna vedio call sannan ya kashe sai naga kamar tare muke tashi nayi na gama aikina na fito falo Sadiya na shara,kallon ta nayi"uwar mutane dayawa ashe kin shigo wa ya buɗe miki ƙofar","Hajiyar ki mana"ta faɗa tana ɓoye dariya,kama baki nayi"Hajiyar su dai"yauwa in kin gama kizo muyi magana","to Aunty",duka nakai ma ta"wallahi ni ba Aunty ki bace ɗimemiya dake kina ce min wata Aunty",dariya ta yi"to matar oga",da gudu na biyota"matar oga sai kace wasu arna",dariya take tana"yi haƙuri na daina Nanar Babban Yaya"tsayawa nayi"a she ma kinsan wace ni ƴar rainin hankali","yauwa zo kiji Madam",ta faɗa tana matsowa,a kunne tami raɗa na ɗago ina zaro ido"wallahi ba ruwana in ta kama mu zance kece","karki damu inta fara bacci sai rana tsaka take tashi",tafawa mukai muka shige kitchen. UMMU SADDIQ🌹🌹🌹🌹 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 BABAN YAYA 08146711395 Tsaida bikin Sadiya yasa muka zama ƙawaye muje siyayya tare dake itama ƴar yi ce tace muyi wancan mu ci miyi wancan musha sannan ina zuwa makaranta ga abubuwan da Aunty Mama ke ɗora ni akai cikin wata biyu na canja jikina ma haka daga ranar in kuma in ya kirani vedio call bana ɗauka sai nace ba ya yi,bamu sami matsala da Aunty Hajara ba dan bata zama ma a gidan tun safe in ta fita sai dare sannan ma nayi bacci. Wata biyu da tafiyar sa a kai bikin Sadiya komai da Babban yaya yace na ma ta,na mata shi harma da ƙari kuma dani akai bikin nan gidan namu kuma da kaina na shige gaba aka gyara Boys quaters aka ma ta jere abin ta Sadiya ba ta da matsala tun da tayi aure ni nake gyaran gidan kullum amma ban taɓa nu na na gaji ba madam ce wai bazata iya zama ƴar aiki ba sai ƙara ɗakko wata me wankakken ido dan randa ta fara zuwa naga zata min isa gaban Aunty Hajaran naci ma ta ƙaniya sannan na buga ma wadda ta ɗakkota kashedi akan ta shiga tsakanin mu in ba haka ba zan tarwatsa ma ta tunani. Bayan wata uku Kwance nake ina bacci naji wayata na ƙara ɗauka nayi inji waye naji muryar Mama tana Ruma ta haihu,ihu na daka na sakko a gadon na fara tiƙar rawa,gadon kawai na gyara na faɗa toilet nayi wanka ƙaramar kit ɗita na ɗakko na ɗebi kayana

Chapter 17 of 32