Share this page
Aisha yau ƴan uwan sa ne suka cika shi kai kace dubiya suka zo amma su sanin ƙasar da Al'ameen ya ke suka zo jin ba asi kuma ba dalewa ba suka samu dan masu zuwa wurin sa duk sun san kan abin shidai na um ba um um. Mamaki ya isa mutane yadda Abba ke kwaɗa ihu a asibiti saboda rakin masifa Hajiya Fulera kuwa sai wata makarantar almajirai aka kaiwa kuɗi suka binne ta,saura kuma suka cigaba da karɓar atakin wurin azabar ƙuna. Umma baiwarbAllah kullum kuka ta ke da addu'a da godiya ga Allah bisa ga soyayyar daya nu na ma ta dan tsallake wannan bala'in ba ƙaramar nasara ba ce,sai Iyyo ta yi ta yi da ita kan taje ta duba yaran ta amma taƙi zuwa kuma tace bazata taɓa yafe musu cutar da suka ma ta ba Ibrahim ma dake makaranta har yanzu baisan me ke faruwa ba to ɗan secondry me za a faɗa masa,haka aka barta tunda taƙi zuwa. Abin da yay mutuƙar bawa Abba mamaki yanda ba bu wani ƴan ƙungiyar su ta kasuwa ko aboki da ya zo inda yake har yanzu gashi ya yi asarar komai nashi ba takardun wata kadara bare wayar sa,yau da wata masifar ma ya tashi banki sun sun biyoshi jar asibiti kan kuɗin su da ya ci ganin basu sami komai ba suka fito zuwa gidan sa aka saka shi a kasuwa nan aka siye shi kuwa aka basu kulin su canjin da ya ragu sukamkai masa har asibitin ya yi takaici kuka ya shiga yi yana tsine musu har suka bar asibitin. **** Lamari fa ya yi musu tsanani dan ciwukan su Abban su Hajara sai lalacewa suke,ya yinda Umma ba ruwanta rayuwa take free abin ta a gidan mu. Kwana ki na tafiya haka rayuwar na juyawa waɗan da dama basu shuka khairan ba bare su sami sassaucin ta,tun dare nake jina bani da lafiya amma na basar ga Aunty Hajara da Al'ameen sai tambayata suke nace musu ba komai,misakin biyu muna shirya dining ciwon yamin yawa dakatawa nayi a wurin da nake ina cije baki Al'ameen ne ya ƙaraso da gudu"Nana sannu kawo inkai"ni mamakin maganar yaron nake Nana kamar wata sa ar sa shi Auntyn ma bazai iya ce min ba,karɓar kwanon ya yi ya aje a dinnig yazo ya wuce ni da gudu,tana ɗaura ɗankwali ya shigo da gudu"Maama Nana zatai kuka"daina ɗaura ɗankwalin ta yi tayo waje da gudu"ni nasan dama bata lafiya tace ƙalau take wannan taurin kan dai bazata daina shi ba"duk tana faɗar hakan ne kamin ta ƙaraso inda nake,bata kulani ba ta wuce ɗaki ta ɗakko akwatin da ta haɗa ta fito falon"Babana jeka ce Murtala ya juya min mota yanzu"da gudu ya fito baiji nisa ba yaje bakin get yakai saƙon sako shi ya yi a motar ya dawo shi inda ake aje mana namu motocin tallafoni ta yi zuwa motar batare da ta faɗawa kowa ba muka wuce asibiti harda Al'ameen,bamu jima da zuwa ba na haihu ɗa namiji Aunty Hajara tsabar murna kuka ta fashe dashi ji take kamar ita ce ta haihun,ana bata jaririn ta rungume ta ɗau wayar ta takira number sa vedio call ba jimawa ya ɗaga ganin tana kuka ya tashi zaune daga kan kujerar daya kishingiɗa"lafiya ki ke kuka","ka kalli kafaɗata mana na ƙara samun Baby boy"da sauri ya miƙe tsaye"Alhamdulillah ya Nana?","nutsu na Nana tana lafiya yanzu ma zan shiga wurin ta please ka taho muyi murna tare",yanzu ma kuwa kwantar da hankakinki zan biya ko nawa ne na taho a yau","yauwa Habibie saika zo",ta kashe wayar tana goge hawayen fuskar ta"wata nurse ce tazo wajen ta da gudu"Madam bamu ga mai haihuwar ba"wani irin juu ta ji acikin kanta tana wa nurse kallon ban fahimta ba"itama ta gane ta maimaita"mun gyara wadda ta haifi wannan ɗan har wani little boy ya shiga amma yanzu bamu gan su ba ita da ɗan saurayin yaron"wani damm taji a ƙirjin ta"na shiga uku ni Hajara anan ɗinma binmu ake"cikin tashin hankali ta kira Baffa ta faɗa masa tsabar ya ruɗe bai faɗama kowa ba ya taho asibitin shi ɗaya ganin yanda ta ruɗe tana zufa yasa shi tausaya ma ta,itama saida ta ganshi sannan ta fashe da kuka"wai Abba waɗannan mutanen me suke nema ne a wajen mu",ajiyar zuciya ya yi"ki yi shiru Hajaratu haka kuli suka gada ke zamu su sa ayi abinda yafi haka","to Abba ba a tausayin ta da ɗanyen jiki ko wanka ba bu a ɗauke ta ga Al'ameen ma tare aka kwashe su","ki kwantar da hankalin ki ba bu abin da zasu iya ma Nana sai dai in taga za a cutar da Habibu ne zatai komai","wayyo Baffa ni wai a basu kuɗin mana su bar yaron nan ya huta","to Hajara ya zamuyi wannan ce ƙaddarar su ita da ɗan taso muje gida da wannan a masa wanka",kallon yaron ta yi"Allah ya baka haƙuri ɗana bata shayar da kai ba bata shayar dana farkon ba Allah ka taimake mu"kukan ta ne ya karyawa Baffa gwiwa da ƙyar ya lallaɓata suka tafi ya yinda hukumar asibiti suna fita ƴan sanda suka ma ta tsinke dan Habib kan su ƙarasa gida ta kira shi yana bariki amma ya tura musu hukuma dan sunyi saka ci suma Likitar da ta karɓi haihuwar ita ka damƙa amma iya bin cike bata san komai ba saida abin yakai Habib yazo da kansa nan ya gane an shirya komai ne sanda take zuwa awo dan a asibitin take awon dama,da bincike yay bincike ne aka gane ma aikatan da aka ɗiba sabbi acikin su ne aka turo masu musu aiki kuma a yanzu a sabbin ba bu mutum uku kenan dama haɗin baki ne,sosai asibiti ya shiga cikin tashin hankali dan ko address ɗin ma aikatan ƙarya ne abin ya ɗagawa masu asibitin hankali,nan Habib ya gama binciken sa bai bar asibitin ba sai dare. Suna isa guda aka ganta da jariri mamaki aka shiga yi a falo ta zauna ɗauke da ɗan ana magana ta rushe da kuka basu shigo tare da Baffa ba ya wuce wajen Alhaji Baffa ne,ganin yanda take kuka yasa Aunty Mama ta zauna kusa da ita ta miƙa hannu ta karɓi jaririn"Hajara nasan Nana ce ta haihu me yake faruwa to naganki ke ɗaya tana ina ita ɗin?",ƙara sautin kukan ta yi"Aunty Mama masu faƙon ta sun ɗauke min ita tare da Al'ameen","inna nillahi wa inna ilaihi raju un Hajara dama wannan abin bai ƙare ba ya ilahil alamena ka kawowa wannan yarinya ɗauki"tana ƙarashewa muryar ta na rawa itama,Mama kam ƙala bata ce ba tasan wannan al amari ran yarinyar yake nema,Baffa da Alhaji Baffa ne suka shigi da Iyyo tana kuka kan kace me zancen ya karaɗe gidan nan aka yo ɗuuu wajen su Mama dan jin ba asi,suna nan Habib ya shigo ya zayyana musu abinda ya faru amma ya samu hoton ɗaya daga cikin su wata ce ta bashi amma ba wanda yasa ni suma nu na musu ya yi nan aka shiga turawa ko Allah zaisa wa ni yagan ta bama ya mazan da suka shaƙa sukai abin ya fara kaisu bango,Umman su Hajara ce take kuka"wallahi karku yarda kuje har asibiti ku ciwa wancan mutumin mutunci zai faɗa muku inda take nasan ya sa ni"kallon ta Hajara ta yi"Umma yanzu sun zare shi a cikin su bai san komai ba kawai dai muna musu addu a Allah ya kuɓutar dasu"ameen kowa ya amsa nan akai jugum,shigar dare Babban Yaya ya yi yazo ya iske tashin hankali ya jijjiga iya jijjiga amma ya daure ganin yansa Aunty Hajara ta fishi jigata da tashin hankali dole ya koma lallashin ta ga jariri ta hana kowa ɗauka madara kawai take bashi shima yaron mai haƙuri bai taɓa kuka ba. Washegari tun farar safiya Habib ya fice dan bama su haɗu ba duk inda yasan zai sami wannan yarinyar yaje amma ance masa basu daɗe da zama ba a garin dama kuma sun tashi,yamma lis ya kira number sa yana ɗagawa ya ce"Yaya ina son ganin ka"nan ya bashi kwatance ba jimawa sai gashi a wurin,abinci yasa aka kawo masa ya tura masa"ci muyi magana Yaya"kallon ban fahimta ba ya masa","please Yaya"ya faɗa yana haɗe hannayen sa,ba musu ya ci wajen rabin abincin sannan ya sha ruwa lemo kuwa ko arziƙin kallo bai samu ba,kallon sa ya yi yana go ge bakin sa"ina jinka any information",kafaɗa ya ɗaga"no information kawai dama dan kazo kaci abinci ne yasa na kira ka dan nasan Aunty Hajara ba ta da nutsuwar lallaɓaka kaci abinci",wata uwar harara ya zuba masa ya miƙe ko ƙala baice masa ba ya fita a wajen a bakin mota ya tsaya yana murmushi sannan ya buɗe ya shiga ya figeta yabar wurin,bin bayan sa da kallo ya yi"am sorry Yaya bazan iya bari yunwa ta kassara ka ba kamar ɓatanta na waccan lokacin"yana gamar faɗar haka ya miƙe ya fita shima wani ƙaramin gida nan kan hanya ya parker ya shiga gidam sabo ne ba kowa kuma wani ɗaki ya buɗe ya shiga na urorine da abuwan buƙata sai ac da fanka,wata ce zaune kan kujera an ɗaureta tam kamar goro ga baki a liƙe,hararar ta ya yi sannan ya yi murmushi"kin ɗauka zaki ɓoyemin ne da ki ke saka wannan abin kulle fuskar ai bari kiji da ahaka ma ki ke yawon ki ƙila ba lallai ma na gane ki ba amma kin rufe fuska kuma kina kallona in ɗago kuma ki maza ki wayance tunda naga haka a unguwar da ki ka fara zama na ganeki na ƙyaleki ne kawai dan na tabbatar ke ce shi yasa na cigaba da nemanki a duk inda aka sanar da ni kina zama",kanta take kaɗawa saboda wahala da wannan ɗaurin yake ba ta har fitsari saida ta yi a wurin ga kujerar bamai laushi bace ƙarfe ne ma,shima kaɗa ma ta kan ya yi"kin yarda zaki faɗa min ina take na kunce ki?",da hanzari tana gumi ta fara kaɗa kai"good girl"ya faɗa yana matsowa inda take,yana ɗaye gam ɗin bakin ta ta ce"tana Algeria! Algeria!!"da mamaki ya ke kallon ta"Algeria kuma?","eh can suka kaita sunyi hakane dan sun san baza ai tunanin can ba","kin tabbata?","na tabbata wallahi har ƙaramin yaron yana can tare da ita",,"good"ya faɗa yana miƙewa","ka kunce ni mana dan Allah ina da Mama bata da lafiya nasan tana can tana jira na",juyowa ya yi ya watsa ma ta mari har sau biyu cikin fushi ya fara magana"au dama kina da imani ki ka yarda ka haɗa kai dake aka raba uwar da ta haihu take da ɗanta ita kin san ya zata ji",kuka ta fashe dashi"wallahi dole aka min anan ƙasar bansan kowa ba daga can Ghana aka bawa ƙanin mahaifiya ta dake riƙe dau kuɗi nan ya basu ni aka kawo nan aka nema min aiki tare da wasu biyu da fari ba a faɗa min me zanyi ba sai daga baya da farko naƙi shine suka je suka zo da Mama na da bata da lafiya suka ce in banyi abin da suka ce ba zasu kashe ta,ni ban ma ta komai ba na mugunta nadai bule musu ƙofar Emagency wadda ba kowa ke shigowa ba sumka fita da ita tanan ban ma san ina zasu kaita ba a wajen ɗayar naji tana waya nima",girgiza kanshi ya yi"wow amma kunyi ƙoƙari sai dai sun ɗebo ruwan dafa kan su zan sake ki amma da sharaɗin zamuyi aiki tare zaki cigaba da magana dasu har kisan wane waje ta ke","na yarda tai saurin faɗa dan burin ta kawai ya kwance ta Ba musu kuwa ya kwancetan da sauri ta miƙe tana murza hannauen ta da ƙafafunta"amma kai soja ne ko?",saurin kallon ta ya yi"taya akai ki ka sa ni?","saboda sune farkon marasa imani za suyi abu sun san da azaba amma zasu murje suyi kamar normal abu sukai",ƴar dariya ya yi"madalla to ta ina zamu fara?",ɗan jim ta yi"ban waya ta daka ƙwace mana",jakar ta ya janyo ya miƙa ma ta"karɓa ta yi ta ɗakko wayarta da hanzari ta fara kiran wa ta number ana ɗagawa ta ce"Mama ya ki ke","lafiya lau Ummi baki dawo ba yau","zan dawo Mama aiki ne yamin yawa kinsha maganin ki?","eh nasha","to saina dawo duk wanda ya ƙwanƙwasa ƙofa karki buɗe kiyi kamar bacci ki ke","to Ummi amma dai lafiya ki ke ko?","lafiya na ke Mama saina dawo ɗin",ashe wayar ta yi tana ajiyar zuciya sannan ta kalle shi Allah ya taimake ka da naji Mama ba lafiya ko zaka kashe ni bazan taimaka maka ba",hannu ya ɗaga ma ta"ai kinjita lau ko maganin ma ni naje na bata wawuya kawai kina ba ta magani daban ciwo daban Maman lau take damuwa ce ta ma ta yawa ki faɗa min me ke damunta"saurin kallon sa ta yi"kaje gidan namu yaushe a ina ma kasan gidan namu?",hararar ta ya yi"kiban amsar tambaya ta malama","to ai haka binciken lafiyar ta ya nu na ciwon zuciya ke damun ta","eh naji gwajin lafiya ya nu na tana da ciwon zuciya amma ai bana shan magani ba ne na samun kwanciyar hankali ne na ta me ya faru da ita da ta kasa mantawa?",ɗan jim ta yi tana zama akujerar daya ɗaure ta"ni kaina bansan me ke damun ta ba kawai dai nasan cewa Abba na ya mutu ta hanyar cin guba",kallon ta ya yi"to ya zaki ce bakisan me damun ta ba bayan ga gaskiyar abin da ke damun ta nan kin faɗa yanzu,da yaushe ne ya mutun?","wata tara kenan ko takaba ba ta gama ba aka kawo mu nan",wani ɗan murmushi ya yi"a haƙiƙa kenan shima babanki su suka kashe shi dan sunce suna buƙatar ki shi kuma yace bai yarda ba dan ke mace ce ba namiji ba ko?",tashi ta yi tana masa kallon tsoro"ta ya akai kasa ni",hular hannun sa aje yana murza yatsu"duk maganar da ki ke me amsa ki ke yi ai koma ya ya ne dai Allah ya jiƙansa ya kuma bi masa haƙƙin sa ita kuma kin ƙoƙarin kwantar ma ta da hankali bawai kina danna ma ta ƙwaya ba",ɗan murmushi ta yi"all right bari na kira naji halin da suke ciki"ta ɗaga wayar ta ta kara a kunne". UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌹 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 BABAN YAYA Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 END 42 Tunda na buɗe ido ina kallon sama na tabbatar ba a asibiti nake ba cikin tsamin jiki na samu na yunƙura na tashi zaune idanuwa na ne sukai arba da Al'ameen dake yashe a ƙasa yana bacci sakkowa na yi daga kan gadon da nake cikin cije leɓe na taka nazo inda yake da sauri na ɗago shi dan na zata baya numfashi fuskar sa na ga ni ta yi ja jir ga jini gefen bakin sa tun kamin aje ko ina na hasasho a hannun su wa muke kenan su suka dake shi dan rashin imani,ɗan murmushi na yi ina shafa kansa"wato kayi gadon taurin rai da turin kai kenan shi yasa aka duke ka",maganar da nayi a fili ita tasa ya buɗe ido,saurin rungumeni ya yi"Nana ina jalilin nace cu maida ni wajen blos cine cuka duke ni","shafa kansa na shiga yi"ka kwantar da hankalin ka muddin ina numfashi zaka rayu da ɗan uwanka koda ni bazan rayu da shi ba",kaɗa kai ya yi ya ƙara lafewa a jikina,muna haka aka turo ƙofar aka shigo wasu mutane ne sunkai su goma kowa kana gani kaga babban mutum amma a riga a zuci kam ba girman an sheƙe shi gun son abin duniya,guard ne a bayan su suka shigo da kujeru nan aka buɗe musu kowa ya zauna suna kallon mu,nima a tsaitsaye nake bin su da kalkon dan na lura ba mutunci ne dasu ba ko daga yanayin kallon da suke mana,ɗaya daga cikin su ne yay wa wani guard alama nan ya nufo kanmu gadan gadan ya kawo hannu zai taɓa ni na daka masa tsawa cikin juya ido murya kamar gardi na ce"ka na taɓa ɗayan mu zaka mutu"da sauri ya janye hannun sa yana matsawa baya,kallon ogan nasa ya yi ya ce"sir kaji me take cewa","naji mana sai a kai ya ƙarya ta ke aljana ce ita dalla ƙwato mana ɗan shine burin mu ba ita ba",zazzare ido ya fara gaban sa ina faɗuwa amma ba yanda ya iya haka ya kuma kawo hannu,kallon sa na yi kawai"ashe ƴaƴa biyar mata biyu da uwa da uwa ba zasu mutu lokaci ɗaya"wani rugugu yaji a zuciyar sa yay ma za yaja baya"Allah ya baki haƙuri ai dangina ki ka lissafo duka sune rayuwata dan Allah kar su mutu","to kacewa oganin ka su faɗi me suke so da mu kamin tabar kanka ta shafi kowa"a tsorace ya kalle su"dan Allah sir ku faɗi me ku ke so a wurin ta ko ma tsira da ranmu dama an faɗa muku ƙaya ce ita",ɗan murmushi sukai suna tunanin komai zaizo musu da sauƙi,wata takarda suka wullo ta faɗo a gabana,ɗauka nai na fara dubawa sannan na wulla musu nima"baza a sa hannun ba kuyi abinda zakuyi"daga cikin su akwai wanda tunda suka zauna ƙala baice shine yafi hasala"ku harbe min ita ku ɗakko min yaran ya dangwala mana da yatsan sa"wancan dai baizo ba dan ya tsorata da gaske kusan makashi akwai tsoron mutuwa,ina a wurin wasu uku suka ƙaraso suka danƙeshi amma abin mamaki sun kasa ɓamɓare hannayen sa a jikina gashi kuma kamar me bacci tofa nima ɗin ai sai abin ya bani tsoro kuma ganin yanda ake ƙoƙarin janshi yaƙi jawuwa sai suka miƙe tsaye dan abin daban mamaki,wani irin ihu ya yi ya watsar da ƙartin ya miƙe tsaye yana zare ido nima baya naja ya yinda suma suke ja bayan dan basu san me zeje yazo ba,cikin murya wadda kana ji kasan ba Al'ameen ba ne ya fara magana"ba za a sa hannun ba kiyi yadda zakuyi"ya buga ihu yay kansu nan kowa ya watse an tunkari ƙofa ta kulle kanta nan fa aka watse a ɗakin ga window da ƙarfe ba za a iya ratsa shi ba,ni kaina gefe naja na maƙure yau naga abin da yafi ƙarfina a ina Al'ameen ya kwaso Aljanu kuma,a cikin ɗakin ya ruɗa kowa sai ihu suke inka yarda ya riƙe ma hannu ko ya shafa ka saika ji kamar wutace take ƙona ka cikin ƴan sakanni ya ruɗa manyan Alhazai sai kwakwazo suke suna ihu duk ga alamun ƙuna nan a jikinsu ihu suak cigaba da yi suna zagaye ɗakin kuyi haƙuri bazamu kuma"to ina dukiyar ku da ku ke neman ta haram ko ku ku ka tara mai ita ne",suna iface iface sana faɗin munyi kuskure kuyi haƙuri"ba wani kuskure kuna sa ne kuma iya tsawon lokacin nan ni nake gadin dukiyar yau kun kaini bango ne na sa ɗaya mutuwar ɓarin jiki nasa ƙona ɗaya shi kama ɗayan daya sa wutar ya ƙone shida tawagar sa saura ku kuma zaku ƙone fiye da su",fashewa sukai da kuka ninkuma na fashe dariya ban sa ni ba dan wallahi dole ka dara muddin kaga yadda manyan mutane ke ɓarin hawaye,nufar su ya yi gadan gadan nan suka ƙara tsagewa da kuka"mun tuba mun tuba rankai daɗe aljani bazamu kuma saka ido ko baki a wannan al amarin ba wallahi zamu maida su gida a yau ba sai gobe ba bamu ƴara bi takan su tamu dukiyar mungode Allah ma daya ba mu ita",dakatawa ya yi a inda yake"to maza inga alama kunbar zancen nan",da rarrafe mai maganar ya matsaya ya jawo takardar ya shiga yaga ta yana turawa a bakin sa ganin tamai yawa ya turawa na kusa da shi a baki"ka gani ko yallaɓai aljani mun cinye ma dan Allah kuyi haƙuri","bazan haƙura ba saina kun saka su a jirgi sannan zan bar ku ko kuma yanzu na bayyana a suffata ta gaskiya"riiii suaka fara rigegen ɗaukar waya suna danna kira ba jimawa suka kashe"mun faɗa za a kaisu yanzu dan Allah a mana afuwa",sharaf Al'ameen ya zube a wurin da sauri na matsa ina jawo shi jikina,mutumin ɗazu ne ya cire hular kansa yana fifita hannun sa da wuyan sa sannan yacewa yaran nasu"ku fitar mana da waɗannan gayyar tsiyar anan wallahi da na san haka ce zata kasance da tuni na haƙura da kuɗin nan kalli yanzu yanda muka ƙoƙƙone ko me zamu cewa matan mu gaskiya dai munji kunya"tsawa aka daka ɗakin nan ƙofa ta nemi yin kaɗan mu kuma aka kwaso mu kamar kayan wanki aka watsa mu a wani jirgi da dai mutane amma ba yawa sai kallon mu ake dan ana ganin mu anga baƙi,anan suka barmu suka tafi suma ɗin dai sun ƙone ɗin sun samu ladan gadi. Suna hanyar komawa gida jansu wayar guard ɗin nan ɗaya tai ƙara ganin me kiran yasa ya ɗaga yana ɓoye dariya ya ce"Hello Nurse",itama da sauri tace"ya kuwa sun muku abin da ku ke so"da yake shi ɗaya ne sai ya kwashe da dariya"ina fa suka mana munci ubanmu dai ashe aljanu ne waɗannan mutanen wallahi kiyi hankali kema dan duk mun ƙone jiki yanzu haka mun kaisu cikin jirgin zuwa nan ƙasar Allah ya rufa asiri amma mun sha wuya a hannun su",ƴar dariya ta yi"ban gane wuya ba",a harzuƙe ya ba ta amsa dan yana jin dariyar da take"ban sa ni ba ki dai yi takan ki"ya kashe wayarsa,da hans free ta sa kallon juna sukai ita da Habib dan shima yaji komai"to yanzu ya za ayi ba a san wane jirgi ba ne kawai ka faɗawa yayan ka tunda shi yasan ma aikata da yawa sai ya tambaya wane jirgi ne zai sauka da daren nan daga Algeria","haka ne bari na kira sa to"wayar sa ya ɗauka ya kira shi. Yana zaune riƙe da jaririn a hannu saiga kiran Habib da bazai ɗauka Aunty Hajara ta ce"haba kai kuwa dan yasa ka kaci abinci shine bazaka ƙara ɗaukar kiran sa ba ka sa ni ko ya samu wani baya ni ne akan su",ɗauka ya yi yasa maganar a fili"Hello Bro please am sorry da abin da na maka dan Allah ka any airport wane jirgi ne zai suka a daren nan daga Algeria",a daƙile ya ce"ok"ya kashe ya kira wajen mutum goma sannan ya samu aka ce masa akwai mai sauka a Abuja zuwa 2am,kiran sa ya yi ya faɗa masa,da shi da wannan Nurse suka fito nan kuma aka tsaya jimamin ta ya za a tafi Abuja yanzu,ƙara kallon Habib ta yi"ka kira shi kace ma sa ya sama maka jirgin Abuja Emagency ko nawa zaka biya",kallon rainin hankali ya ma ta"ko nawa zan biya to shima ɗan sa jirage uku gare shi",zaro ido ta yi"am sorry ashe abin yana da yawa shi yasa waɗancan mutanen suka ruɗe da yawa suma",kiran sa ya kuma yi"Bro za ni Abujan ka nema min kujera mana",kai ya dafe"Habib!!!","please Bro","ok ten mint",kashewa ya yi ya kira Abdallah dan ƙanin sa na aiki a air port ne an samu ya kira sa ya faɗa masa amma ya yi sauri minti arba in da biyar ne ya rage,anan suka rabu da nurse ta nufi gida shi kuma ya wuce air port. A inda aka watsar damu nama kasa tashi bare yaro ƙarami da ya sha wahalar ga jijjigar aljani ma aikatan jirgin ne suka ƙaraso kanmu da mamaki suke kallon nan da nan suka yo kanmu suka kama muka miƙe ɗayar ce ta ce"sannu Hajiya

Chapter 30 of 32