ba kece Mahaifiyar Al'ameen air ways ba",kai na ɗaga musu ina nuna musu shi da sauri suka ɗauke shi suka kaimu wuri na musamman nan da nan suka cika mu da abinci har wanka suka masa sun bamu kulawa sosai har Allah ya sauke mu lafiya sannan dare ne sosai ga sanyi mayafin cikin jirgin muka lulluɓa na rungume shi a gefena dan bazan iya ɗaukar sa ba gashi da ƙyar nake iya ɗaga ƙafata jikina ya gama tsami muna gama sakkowa nai arba da Habib tsaye shi har ciki ma aka barsa ya shigo saboda sanin manya da sukai,shima mu yake kallo tsayawa na yi a wurin kawai na fashe da kuka ban taɓa jin karaya ba a rayuwa ta sai yau,da gudu ya ƙara so gare mu ya ɗauki Al'ameen"sannu"kawai yace min ya nu na min inda zamu dan zamu koma ne a wani jirgin amma sai asuba,ban iya koda motsin komai ba a inda muka zauna har asuba saida kai sallah sannan muka hau jirgin.
Gari ya fara haske muka sauka motar da yazo da ita jiya ya bada ajiya ita muka hayo zuwa gida.
Aunty Hajara na zaune a bakin gado tana sawa Baby kaya ta masa wanka dan ba mai taɓa shi gidan ma madadin barka ja je ake zuwa dan haka gidan kullum cike yake,kamar an ce kalli mudubi sai ta ganni tsaye lulluɓe ina kuka,saurin kallon bayan ta ta yi ta gan ni da gaske ne a guje ta taso"Nana ke ce"tana kai hannu jikina ta ji ni ɗin ce saita rungume ni ta fashe da kuka mai ƙarfi"Nana ke ce wayyo Allah na jama a ƴar uwata ta dawo ina Al'ameen",ƙofa na nu na ma ta da sauri ta fito ta ganshi a kafaɗar Habib,tun daga kallon da ta ke ma sa ta ga ne shine ya samo mu da gudu taje ta karɓe shi ta rungume shi a ƙasa ta durƙusa"mungode mungode Habib ba bu ɗan uwa irin ka a wannan zamanin Allah ya faranta ma ka yadda ka faran ta mana"shima duƙawar ya yi"haba Aunty Hajara miye na durƙusa min kuma",bai gama magana ba yaji saukar muryar sa a bayan sa"riƙe Nana Habib zata faɗi",ai kuwa kan nakai ƙasa kaina ya taɓa center table ya riƙe ni"Aunty Nana"ina na daɗe da barin wannan nahiyar da hanzari ya ƙaraso ya ɗauke ni cak ya fito daga ɗakin zuwa motar da aje yanzu dana bai kwana agidan ba dama yana office dare ya masa ya kwana acan yanzun shigowar sa kenan,ƴan gidan mu rakaɗi ne ya kaure anga Nana anga Nana Aunty Hajara da ta fito ɗauke da Al'ameen Aunty Mama ta miƙama shi shi ita da Gwaggo da Baba Saude suka shiga mota Habib ya jasu suka biyo bayan mu dan har ya fita daga gidan,a asibitin ma abin ya basu mamaki dan jini ya ɓalle sosai yake zuba da ƙyar da siɗin goshi jinin ya tsaya sannan likitar ta fito mamaki ne ya kama ta ganin yanda wurin ya cika da mutane mutmushi ta yi a ranta tace ƴar gata aka kawo da alama Alhaji Baffa tafi kalla ganin shi tsoho amma a tsaye kyam sai ƴar sanda ne kyau,ƙarasowa ta yi nan akai ma ta duru duru da ido dama kowa na dashi dan Iyyo muka kwaso,Babban Yaya ta kalla"yallaɓai a gaskiya tana buƙatar jini cikin gaggawa..."kan ta gama maganar an yo ma ta caa kowa yana a gwada na sa da ƙyar ta shawo kansu sannan aka fara gwadawa maaki ne ya kashe su ganin wani jini duk iri laya masu ɗan kumarin tace a ɗebi nasu su Ya Ashiru kenan da Habib da Kawu iro sai Ya Haruna sai Ya Khamis amma Babban Yaya da aka gwada shi sai tace muddin aka taɓa sa to sai an ƙara masa wani dan jinin sa yafi nawa sama shi nashi har yaje ɗari biyu da biyar tayi mamaki ma da ta ganshi a tsaye,a taƙaice Ya Ashiru ya bata labarin abin da ke faruwa,sosai tai mamaki haka bayan saka min jinin tasa shi a gaba saida yaje akai masa allura aka bashi magani ya sha anan cikin asibitin ya yi bacci da dabara aka ɗakko shi zuwa gida ya kwanta dan samun hutun sa shine mafi alkhairi kan ya rikice shima.
Kwana uku ana kula dani sannan na dawo dai dai harma yau Aunty Hajara tazo da Baby na shayar da shi sosai tai murna da dawowata abin har mamaki yake ba mutane,yau aka sallameni kwana na biyar a asibitin kwana shida kuma da haihuwata kenen gidan fal da ƴan uwa na jaje dana suna a ɗakina na sauka dan haka yau ba masaka tsinke a part ɗin mu Aunty Hajara ko gajiya ba ta yi sai hidima take da mutane washegari yaro suna Ibrahim kawu Iro harda rawa wai shi Nana ta wa takwara to bama shi ba kowa ya yi mamakin haka kuma ni da Aunty Hajara muka yanke hakan Babban Yaya kuma ya yarda,a ranar sunan yaro ya kwashi kayan barka kamar za a buɗe shagon kayan yara duk fa wajen kawu Iro haka aka sha suna abin gwanin sha awa.
Washegari tun farar safiya ƴan nesa sua fara komawa saboda makaranta su Ya Saddi'q ma wannan karon da kaina nasa Babban Yaya kowa ya tasa matar sa su tafi wannan jeka ka dawo ɗin ya yi yawa sunyi mamakin yadda na hangi nesa su ba wanda ya hangi hakan koda su Baffa ne,haka kuwa akai bayan sati guda ina zune sai ga su Ya Maryam wai sunzo min godiya kallon su nayi na kwashe da dariya"ku yanzu bakuji kunya ba kuna mata amma tun waɗannan shekarun ba wadda ta taɓa tada boren zata bi mijin ta kuna gani ni har guduwa ma nayi",kwshewa sukai da dariya"aike ɗin ta dabance mufa bamu kai ki ƙwarin kwanya ba","to a gaskiya bari na baku shawara zaman inda mazajan ku suke sai kun fidda kunya kun kula dasu ada an matan basu kai musu hari ba saboda sungan ba fuska amma yanzu ganin ku wallahi zakuga suna kula su,zan shaidi ƴan uwana bilhaƙƙi na zauna inda suke amma Allah basa kula mata dan haka kuma saiku nu na musu gatan ta bazasu marmarin nacan ɗin ba",da mamakin maganganun da nake amma haka suka yarda dan sunsan wace ni ayi watsi da maganata mutum ya shiga cakwakiya dan ina hango nesa nima,tare muka wuni har suka gyara min ɗakuna na sai dare na cika su da abin arziƙi sannan suka tafi suna ta godiya,,,,, ohhh ni Nana wai ni akewa godiya.
Yau kwana na Hamsin da biyar da haihuwa kuma yau Aunty zata Hajara zata tafi Ibadan dangin mahaifiyar ta kayan da nasa a kawo mun aka shigo dasu Babban Yaya na shirin fita yaga Murtala na shige da kaya a ƙunshe da alama atamfofi ya ga ni murmushi kawai ya yi ya wuce abin sa dan yasan ba a shiga tsakanin mu,da kaina na kwashi kayan zuwa ɗakin ta tana saka hijabi har ta gama shirin ma ta ganni da kaya niƙi niƙi"a a Nana wannan kayanfa"ajewa nayi ina nishi"kai kayan nan nauyi aradu tsaraba ce na kawo ki haɗa da naki yadda dangi dayawa zasu san kinje kinsan ɗan ƙauye in ka kai tsaraba ko bazai samu yana daraja ka so nake kije a taru akanki",dariya ta yi"Allah ya shirye ki Nana kedai ba zaki canja hali ba ko",zama na yi a bakin gadon ina zuge akwatin Al'ameen"dan Allah Aunty Hajara ki kimin wani alƙawari mana",itama zaman tayi"ki kwantar da hankalin ki Nana indai kan kula da Al'ameen baki da matsala da ni",kallon ta na shiga yi seƙe seƙe"wallahi Aunty Hajara kina bada ni amma ina dawowa kula da Al'ameen ko Mama ce ƙarewarta zata ja dake ne bare ni dan Allah kibar wannan zancen ni in kinje don Allah karki nu na musu bake ki ka haife shi ba saboda zasu so ace a shekarun ki kina da ɗa kema",sanyi jikin ta tayi"taya haka zaiyuwu Nana","me ya sa bazai yiwu ba baya kama dake ne ko kuma da wata matsala ko ƴan uwana sunsan ɗanki ne please Aunty Hajara","shike nan Nana naji daɗi yadda ki ke min akan yaron nan","daina jin daɗe wallahi Mu azzam ma ina ya ye shi zan an tayo miki shi ko kin manta ƴaƴa maza naki mata nawa",tafawa mukai"ban manta ba kice ni daia abayarwa zan ƙare ke kuma a karɓa ko",dariya na yi"eh ai gwara hakan kinga ai baza muyi ƙasa ba ko","to hakane bari mu tashi jirgi ba jiran mu zaiyi ba",miƙewa na yi ian turo ɗankwali gaban goshi"ai kuwa dole a jira uwar me shi muje ni zan kaiku airport ai dan nasan kun gama da Babban Yaya tunda naga ya fita","mun gama kuwa muje to uwar ƴan mata",ƙugu na girgiza ma ta"wannan suna yamin uwar ƴan maza",duka ta kawo min na goce na fita da gudu,Mu azzam tazo ta ɗauka sannan aka sa kayan a mota na wuce kai su air port.
Daga can gantali daɗi gidan Umma na wuce na tarar da ƙanwar ta tazo ita na tasa a gaba tamin kitso tana yi tana mita wai warewa yake ni kuma nace sai anyi tana gamawa tamin dilka cikin lokaci kaɗan na sauya na ƙara haske fiye da da ban bar dai bar gidan ba sai la asar sakaliya nan ma wajen Auntyn Mama na wuce dan Mama ma bata nan tana nasu garin tama fi sati a can,tana gani na ta shiga mamaki"wannan yarinya Allah ya shirye ki gyaran jiki ki ka je",matsawa na yi daga kusa da ita"eh mana Aunty Mama to an daɗe ba a haɗu ba ai gara yaji sauyi",salati ta saka tana dafe kanta"ohh ni Halema to dan gidan ku tashi ki tafi ɓangarenki","yanzu ma kuwa dama tsummin nan nazo ki ba ni kona sata",tashi ta yi tsaye"gashi jeki ɗauka karki min fitsara anan",tashi na yi na lauk Mu azzam na ɗau galan ɗin tsumi amma da wasu na tafi tana ta min dariya ina shiga na kwantar da shi na shige kitchen kazar tarar ango na gasa sannan ƴan abubuwan da bazasu hana ciki sukuni ba ana magaruba na gama na shige wanka na jima ina saɓe jikina da sabulun haɗi na asali na kashe kuɗi akan sa shi yasa ko gifta ka nayi ba tare da nasa turare ba saika ji ƙamshi kwana arba in da biyar kenan ina wanka dashi kunga kuwa ai yabi jiki ko,mai na ma daban yake kudai wannan jiki nashan haɗi ko kun manta burin Nana ne kan Babban Yaya saian fi masa ko wacce mace a duniya amma banda Aunty Hajara ta, saida nayi sallar isha sannan na shirya cikin riga mara rufin asiri fam ɗarinka tsirara inji Mama shirya Mu azzam nayi na sashi a gadon sa dan yau bai kwanta min a gado ya takura min,ina falo a kwance kwanciyar ma ta iskanci ba bacci nake ba amma nayi kamar me bacci sanda ya shigo bai ganni ba saida yazo zai wuce kawai ya ganni kwance duk ƙirjina a waje aka ma cinyoyi na kai kace na shekara ne ina baccin da kayana zasu tattare haka,fasa wucewa ya yi ya dawo baya inda nake saurin ƙara rufe idona nayi dan dama kannewa na yi so nake naga zai wuce ne murmushi na yi a raina na ce ka kamu Babban Yaya,zama ya yi a ƙasan kujerar yana ƙare min kallo saukar hannun sa naji a jikina yana sha cinyoyina ban motsaba ganin haka ya ɗauka bacci nake saman wuyana ya shiga shafawa zuwa ƙirjina inda ya fito lumshe ido ya yi"ina ƙaunar ki da komai naki Nana ke ɗin a jinina ki ke bazan iya moruwa ba muddin bakya kusa da ni..."wuƙil na buɗe ido na wuntsulo na faɗa kansa"da gaske ne Babban Yaya",murmushi ya yi yana lumshe ido saboda jikin sa da kaya amma saida ɗumin jikina ya ratsa shi,rungume ni ya yi sosai yana shinshinar wuya"fin ma haka Nana ke iya hakan baki na ya furta miki amma yafi a haka a raina",kaina ɗago a bazata yaji na ɗora bakina akan nasa dama kaɗan yake jira sai dai me yau abin yasha banban da ko yaushe hadda na shiga goge masa dan dana sakesa ya miƙe kasa tsaiwa ya yi,hannun sa na kama ina dariya"taho muje amarya dan yau nice angon ka kaza can babban gashi kaci kai ƙyat",ƴar dariya ya yi ya bini ni na tayashi wanka yasa kayan bacci sannan muka zauna akan kafet a ɗakin dan bamu je ko ina ba anan na aje komai saida yaci ya ƙoshi sannan ya huta yabi jikin sa jimshi ya fara yi ba dai dai sai ya kalleni idanuwan sa na kalla nai dariya"ka fara tsumuwa kenan to taho Babban Yaya ka gama tsumuwa a gado",shi dai yana jina amma baya fahimta ta,tun anan na jefar da rigar na bishi gado tare da aton bargona baƙi saboda ƴan sa ido kalar su o o dan bana so aje min wannan tarihin suna tsokana ta.
Washegari saida nakai tara ina bacci shi kuma yana zaune yana kallo na yana kallon Mu azzam dan shima bai tashi ba,buɗe ido na yi ina miƙa da salati kawai nai arba dashi yana ƙaremin kallo,murmushi na masa shi kuma ya kaɗa kai"faɗa min me ki ka ba ni naci nace shi kuma wancan me tashi tare da me kiran sallar me ki ka masa yake bacci har yanzu"dariya na kwashe da ita ina cire bargon jikina"Babban Yaya kenan sannu jiya ka darzu yajin angwaye na baka mana shi kuma na banka masa maganin bacci dan karya hana amaryar samun nutsuwa bari kaga yanzu zai tashi",kan na gama rufe baki ya tsala ihu"kaji ba yanzu kaima kwanta ni kuma bari na kula da wancan"kai ya girgiza"Allah ya shirya min ke Nana","amma dai ba a wannan fannin ba ko in na shiryu kuma ya za ayi kenan ana kwasar amarcin",cikin bargo ya shige yana kaɗa kai ni kuma sauka a gadon ina dariya.
43
BAYAN WATA BIYAR
Nayi shar kamar ba ni ba a yanzu aka samawa Al'ameen makaranta nagartacciya kuma hankali kwance dan mun daina tunanin komai kuma.
Rayuwar kowa a Familyn mu ta saitu Babban Yaya ya cika burin Abba kowa ya gane ɗan uwan sa ba maƙiyin sa ba ne,yayyen mu da iyayen mu kai ya ƙara haɗuwa su Hajiya Harira ko wacce ta yi aure amma Hajiya Salma da Safiyya miji guda suka kuma aura abin ma abin dariya.
Su Abba ana nan ana wahalalliyar rayuwa rai kwa kwai mutu kwa kwai ko sau ɗaya kuma basu taɓa ba mu tausai ba Umma ce kawai abin tausai ƴaƴa uku tayi asarar haihuwa amma da yake mace ce ita mai kai zuciya nesa ko tunanin su bare maganar su ma ba ta yi kullum tana tare da Iyyo ko tana wajen su Mama iya nan take rayuwar ta.
Habib ya koma Niger dama akwai yarjejeniyar duk sanda yake son dawowa zai koma dan haka ya koma shida matar sa da ɗansa dukiyar sa kuma yana juyata yadda yake so.
Umma da Baba da Habu sai sam barka dan Habu ya tsaya da ƙafar sa shima da taimakon ni da Babban Yaya a yanzu ma baka cewa ba ƴan uwa muke ba saboda yadda muke zumunci shima anan gidan namu ya samu wadda yake so ƴar Kawu Iro an ma tsaida magana an bashi ita aure ne ya rage kawai .
********
Yau tun safe na tashi dan Babban Yaya gobe zai tafi kuma tare da Aunty Hajara zasu wuce shine wai kwanan ta ne tabar min na riga shi tashi dan yanzu bama shirin wa ni abu dama dan ba mace a tare dashi ne dalilin da muke masa shiri,to yanzu akwai dan haka kayan sa kawai na haɗa masa saboda da daddare zasu bi jirgi Abuja gobe su wuce kuma.
Ina saka kayan sa a jaka naji an mintsinar min ciki,da sauri na goce dan nasan shi ne"bashi kaci kasa ni bana yafiya","ni kuwa nasan bakya yafiya yarinya dan gashi na ga ni kin rama abin da na taɓa miki",ƙara juyowa na yi"me ka min Babban Yaya da har ban manta ba na rama ban san na rama ba?",ƴar dariya ya yi yana jawo ni jikinsa"kawo kunnen ki kiji",kunnen na miƙa masa,a bazata ya cije ni ya miƙe yana dariya"dama tsokanar ki na ke malamma Nana ustaziyyyya Nana",dafe kunnen na yi"saboda kasan duk bana ɗaya daga ciki shine kasa musu alamar ja haka",kai ya dafe"ihuu ai kuwa ke ce Babbar Malama kalli fa yadda ki ka janyo ra ayin Hajara duk tsaurin ta da masifar ta take mugun son ki kamar ba kishiya ba"ƴar dariya na yi"to ai duk macen da ke tsoron kishiya ma ni ta bani kunya kuma mazan in aka nu na muku ana tsoron ta kunfi yin na ta","inye ke nan har me zaki cewa mata kuwa","kasan Allah a yanzu a taron mata na duniya a tsaida ni a gaban su wallahi ina da abin faɗa musu","in tambayeki mana Nana","ina jinka Babban Yaya Sahibin Hajara da Nana",ɗan murmushi ya yi"me yasa bakya tsoron kishiya? kuma ki ke jin haushin wadda tace baza a ma ta kishiya ba?",ɗan numfashi na ja na jawo shi ya zauna kusa da ni"maganar me tsawo ce zauna kaji in da gyara saika min,kasan ita wannan rayuwar yanzu kowa kanshi yake so,a zamanin da mata da kansu suke gano wa ta macen suce mijin su ya aura badan sun gaza komai ba sai dan kawai a zauna tare kuma matan kan layi sun ragu,mu matan yanzu wallahi hassada ce ta mana yawa mijinki na da kuɗi ko rufin asiri saiki ce ke a dole ba za a miki kishiya ba kuma wata shegiyar ƙwandala ma bazata bari wani ya ƙaru da shi a adukiyar mijin,wata ma kamar kuɗin ubanta malamai da bokaye zata shiga ta hanashi alheri kai wallahi ko zakka za ai sai dai ita ya ba ta,kuma masu wannan ka ɗiri feren da yawan su mata huɗu suka taso suka ga ni a gidan su kai wata ma auran uban nata yakai sau goma sha,wai kuma itace ke cewa ba za a ma ta kishiya kai bazama ta zauna da kishiyar ba kamar dan ita aka halicci she,to indai kina da tunani da hangen nesa dole ki bari a miki kishiya kai kishiyoyi ma kuwa muddin kina so ƴar ki ta auru kuma ƴar uwar ki ko ƙanwar ki su auru to dole ki bari a miki ita to,ko dan kinje a ta farko a gidan ki saiki ce lallai naki ma ana farko zasu waya faɗa miki haka, kar shakkar komai ki tuna kamai ya yi zafi maganin sa Allah duk bin bokaye da ƴan tsubbun ta ki gama ta da Allah kisha kallo komai daren daɗewa sai ta faɗo ƙasa warwas,sau tari mata ba kishiya muke tsoro ba dame zata zo muke tsoro,to wallahi ni koda uwarta zata zo indai miji na sona an wuce wajen tabbas zan saita ma ta zama ko na saita ma hanya ta koma inda ta fito,dan wata shegiyar a gidan tazo ta same ki ke da ƴaƴanki sai tace sai kin fita kin bar ma ta gidan da mijin kamar wani ƙanin uban ta, to wallahi bana tsoro saina kwana dadduma ina miki muguwar addu'a ni da ke aga wazai nasara,wata kuma zata zo da lumana ita uwargidan ce za a samu matsala daga ɓangaren ta kowa dai akwai nasa amma tabbas dole ama mata kishiya ko kisamu kishiyar bariki dan basa wuya",ƴar dariya ya yi zai magana Aunty Hajara da ke tsaye da Mu'azzam tun ɗazu ta riga shi"zan buɗe miki makarantar faɗakar da mata Nana dan ko ni bazan iya zayya no wannan bayanin naki ba amma zan na bada labarin farkon zaman mu kin wahalar da ni nima",dariya na yi na miƙe tsaye"ai Aunty Hajara ina sassauta miki ma dan ina ƙaunarki tun farko wallahi da ƙin gaske nake miki da yanzu kina da tabbai na bama tabo ba dan bana da tausayi indai na siƙe",jinjina tamin"ni zan faɗi haka mana tunda haka nan ki ka liƙamin suna wai muguwa muguwa me ihu kawai",kashewa mukai da dariya ta miƙo min Mu'azzam tana faɗin"wallahi tsoron ki nake Nana tun da can,dan ko a fuska aka kalle ki ansan makira ce ke shi yasa nake fatan kar yaran ki suyo halinki dan in suka yo ki to zamu ɗinka gajerun wanduna ne dan ko basa fita ayi a waje ai za a je makaranta, Allah dai ya ƙara haɗa kanmu ","to ameen"ya faɗa,dariya muka ƙara sawa na ce"Allah ka shirye ni gaskiya na haɗa *GWARAMA*"
Alhamdulillah ƴan uwa anan kawo ƙarshen wannan littafi ina godiya ga Allah da ya ara mana dama ni na rubuta ku kuma ku ka karanta fatana Allah yasa mu dace da alkairin da ke ciki kuskurena kuma Allah yafe min kuma ku yafe min taku a kullum *FATIMA AMINU*
*(UMMU SADDI'Q)*
*FATAN NANA TA FAƊAKAR DA KU BA SHIRME KAWAI TA MUKU BA*
*Mu sake haɗuwa a GWARAMA ɗin danjin wace badaƙalar ce kuma a ciki,shima fa masa salon daban ne ku dai ku kasance da UMMU SADDIQ*
*Ina godiya ga Iyayen Jariri*
Mrs Abdullahi Writer
Mamie Yusuf Dabo
Maman Afrah Writer
Ameera Adam Writer
Leemart pinky Writer
Zee frety Writer
Meenerh Writer
Shamsiyya manga Writer
Hauwa Aliyu Sani(Maman Sajad)
N.Yarema
Muhammad MK
Abbas MK
*Ina gaishe da ƴan ƙungiyar First class kafatanin su*
UMMU SADDIQ TAKU 🌹🌹🌹❤️🖤💞♥️🤩💓❣️🙏
08146711395
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 32