a sake ba ruwan su kaɗan ne a damuwa,inda yaron yake aka kaisu yasha wuya duk ya yi baƙi fito masa dashi akai nan ya kalle shi ya kalli ƴan sandan"wa yace kuna dukan shi haka",ɗaya ne yace sorry sir ya yi gardama ne shine mai abin uace a hukun ta shi ta yanda zai faɗi gaskiya",dafe goshin sa ya murza kamar wasa ya fesa ma ɗan sandan nan mari da sauri sauran suka ja baya cikin masifa ya ce"saboda shi zai koya muku yadda ake bincike ko shi zai nuna muku ga yadda zakuyi aikin ku ko to ku kissafim waɗanda suka dakeshi kaf albashinku shi zan ba a ƙasa suka sunkuya suna bashi haƙuri kafaɗar Habu ya dafa"kayi haƙuri abokina kuɗin nawa ne ya rage",ɗago kansa ya yi zaiyi magana suka haɗa ido da Babban Yaya"lahhh Babban Yaya"da mamaki ya kalle shi"na am kasan ni ne",matsowa ya yi ya kama hannun sa"ni ne fa mai mashin ɗinnan dana kaika gidan Alhaji Aminu kace kaima ranar ka fara zuwa",zaro ido ya yi yana dafa shi"ayya abokina kayi haƙuri waccan wayar ta faɗi ne","ba komai wallahi","waye ka sayarwa mashin","Wallahi Babban Yaya ƙanwata ce Babu lafiya na rasa yadda zanyi naje sayar kuma fa Babana ya basu fin rabi ya ce zai cika amma duk da haka basu yadda ba","ba komai Baba ka kaimu wurin mutumin",duka suka fito da motar su data hilux ta ta ƴan sanda suka shiga unguwa da ke gidan su na farko kan na Alhajin mutane suka ga ni a wurin sannan ga kaya ana watsi dasu wata ma ta na gefe rungume da ƴarta suna kuka ga Alhaji sai baza riga riga yake shida wasu mutane kana ganin su kaga dillalai,da sauri Baba ya fito"yallaɓai ka gani ko yadda suke mana tozarci akan kuɗi",duk kansu ran kowa ya ɓaci tsawa Acp ya daka ƴan sandan sa"ku kamamin kowa masu watsi da kayan nan",matsowa Alhajin ya yi"kaga yallaɓai sun ci min kuɗi shine zan koresu a gidan in sun biyani sa dawo",bai gama magana ba Habib daya gama shaƙa ya sheƙa mari hagu da dama da gudu dillalan nan suka baje suna guduwa,wayansa ya danƙa duk girman sa"in ka koresu a bola ka ke so su zauna kenan anan zasu samo kuɗin su baka ko",wuri wuri Alhaji ya yi nan Habib ya kalli matasan"ku mayar musu da kayan su ko mutum yasha ruwan zafi yanzu"daga wandon jikinsa suka gane waye dan haka da rige rige suka fara kwasar kayan suna mayarwa,sakin Alhajin ya yi ya matsa ga matar dake kukan yace"kiyi haƙuri za a biya shi kuɗin sa ga ɗanki nan ya dawo"godiya ya ta ahiga musu ya yinda Abdallah ya ƙirgi kuɗinsa ya miƙa masa ba kunya ya karɓa yana ƙirgawa cif dubu ɗari da hamsin babbar riga ya baza ya sa a ciki ya wuce,kati Babban Yaya ya basa yazo ya same shi kuɗi masu yawa dukkansu suka ba Baban sannan suka shiga motocin su suka juya a motar Habib kallonsa ya yi"yadai kayi shiru haka",kansa ya girgiza"ba komai Habib ji nake kamar naje inda Nana take",dafa kafaɗar sa ya yi"ka kwantar da hankalin ka cikin ruwan sanyi zamu sa meta",haka dai sukaita bashi baki har yaji sanyi a ransa.
*MAROCO*
Dai dai sanda Daddyn Aisha yace zai bawa mutanen nan ita lokacin nayi yazo tafiya da ita amma me yana shiga ɗakin ta yaga wayam da sauri ya sakko yana tambayar masu aikin gidan tana ina suka ce ta fita da kaya tace musu taje bikin ƙawarta,ɗakinsa ya wuce abin mamaki ya gansa a buɗe yana shiga yaga babu komai a safe sannan ga takarda a ajiye ɗauka ya yi cikin sharar zufa ya fara karantawa, *"Daddy nasan kaso ni ada kenan sanda ka ke ɗaukata ƴa amma yanzu daka gano ni ba ƴarka bace shine kamin zagon ƙasa kasa na cutar da wata akan wani buri naka to kasa ni ta gudu daga hannuna kuma sirrin naka dai tana nan ta tasa ni kuma ita take faɗamin nayi ta kaina sabosa zaka kashe ni ka maida dukiyar ka daka mallaka min wajen ka abin ka to ka sa ni da wadda ka ba ni dama wadda baka bani ba na kwashe duka na gudu kuma ko a lahira bazaka ƙara gani na ba"* anan rubutun ya datse ihuu ya kurma ya faɗi a wurin da gudu masu aikin suka shigo anan suka sami Alhaji baje a ƙasa ya samu shanyewar ɓarin jiki me mu ni.
UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌹
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
BABAN YAYA
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
34
Koda suka koma gida yau dai Hajara ta bashi abinci yaci harma ya ma ta magana da ɗi kuwa kamar ya kasheta da kuwa shashin Abba ya koma da zama ko kuma ya buɗe asalim part ɗina ya shiga ya kwanta bacci kowa sai ɓarawo amma ba kullum yake yi ba dan ta yi iya kwarkwasarta amma ta kasa jawo hankalin shi gareta ya manta da ni,bincike kuwa ta bin cike ɗakina kaf amma bata samu takardun Hajiya Fulera kai na Babban Yayan ma ko gilmawar ta bogi bata ga ni ba bate ta gasken a haka dai ta gaji ta haƙura tsinuwa kullum saita min tana addu'ar Allah yasa kar a gan ni.
Bayan kwana ki kaɗan Babban Yaya ya samawa Habu aiki a wajensa yaji daɗi sosai dan albashin wata uku aka basa nan da nan ya ciro mu acin wara abin da ya basu mamaki da ni bana gane komai a binci amma ina gane nama shi yasa kullum sai Baba yasa sa ni a gaba da nama ina ci yana dariya in ya ƙare nace"Umma a zuba nama",sai suyi ta dariya,duk wannan abin kuma yana kaini asibiti dan likitannan yace ana kawo ni.
Yau da wuri Habu ya dawo ina zaune akan tabarma inawa ƴar tsana kitso ya zauna kan kujera"ƙanwata zaki unguwa?",kai na ɗaga ina dariya,"Umma fito kiji",fitowa ta yi"ubana ƙalau dai ko yau naganka da rana haka","eh Umma suna ake gidan su Oga shine nazo ku shirya na kai ku kinga ma ai kyawa iyayen sa godiya ko","a lallaikam to bari na shirya taso ƴata",da sauri na watsar da kayan wasan na bi ta ɗaki a tamfar da ta ɗinka min sabuwa dal ta saka min da hijabi sai wani ƙaramin niƙaf bamai takura ba dan bata fita da ni haka fuska buɗe,koda muka fito saida ya yi dariya"wai Umma tsoron me ki ke ne ki ke ɓoyeta haka","kai Habu wannan yarinyar lamarin ta tsorata ni kullum na kwanta sai nayi mafarkin wasu gungun mutane suna bin ta tana gudu wai sun kamata sun raba naman ta sunci","subahanallah Unma to Allah ya ki ya ye ta","ameen Habu Malam ɗin yana waje","a a amma ai shi na fara biyawa kasuwa na faɗama kamin nazo nan dan mota Oga ya bani nazo na kai ku motar ma tasa",kai ta kaɗa"to dai a riƙe amana Habu irin waɗannan mutanen ka riƙe musu amana shine zaka zauna dasu lafiya dan in wayo zakai sunfika wayo saboda su a ankate suke da kowa","hakane Umma kuma zanyi iya ƙoƙarina wurin ganin bai samu matsala da ni ba","to Allah yasa Habu",muna fitowa na kalli motar na nuna shi nayi tsalle,kai ya kaɗa"daina murna ba tawa bace amma zan siya saboda kai ƙanwata unguwa da yawo",dariya nayi dan ban fiya magana ba saita kurame,muna shiga naji kaina ya yi dum da sauri na kalli Umma na kalli bayana,hannuna ta riƙe"me ya faru ne ƴata",kai na kaɗa na cigaba da shafa kujerar motar ina jin kamar zanyi tunani amma na kasa,koda ya tsaya a ƙofar gidan ana ganin motar aka buɗe masa get ya shiga gidan danƙam da mutane mamaki ne ya kama Umma"kai Habu wannan gida ne ko unguwa",dariya ya yi"gida ne Umma amma mutanen ciki na unguwa guda ne",kai ta kaɗa"lallaikam",hannuna ta kamo nan ƙafata ta shiga rawa dafe ƙafar ta yi"sannu ciwo take ?",girgiza kai nayi sannan na fito muka fara tafiya zuwa cikin gidan wani fili da aka sawa rumfa yace"Umma ku zauna anan zanje naga Mamar su Oga sai na shiga daku ciki",tom tace tana zaunar da ni kusa da mutanen dake zazzaune,ciki ya shiga bai daɗe da shiga ba wani yaro yama mamar sa amai dama akwai famfo wurin nan Umma ta tashi dan ta taya ta gyara yaron da jikin ta,tana matsawa naga gilmawar hannu ana kira na tashi nayi na tafi wata ƙofa mai kyau na gani a buɗe na turata na shiga takalma ne birjik a wurin ba wata sallama na shiga duk suna cin abinci ko ga ni na ma basu yi ba na shige cikin wani ɗaki ƙofar dama a wangale take,ƙarewa ɗakin kallo na shiga yi kamar nasan shi niƙaf ɗin fuskata na ɗaga na fara janyo kome na ga ni ina yarwa ƙarar fashewa abubuwa tasa Hajara da suke hirar kar Allah ya dawo ni ta taso zuwa ɗakin dan tasan yanzu ya fita kuma baici ace ya dawo ba,leƙowa ta yi tana faɗin"ka dawo ne dama",shiru ta yi ganin yanda aka wargatsa ɗakin ƙarasa shigowa ta yi"ke ke ƴar uban waye ke da ki ka shigo mana gida har ɗaki",ganin ban kulata ba saita ƙarasa shigowa tana kai hannu zata taɓani na juyo,a razane tai baya ta kwaɗa ihu nan da nan mutanen falon suka ƙaraso suma duk tsorata sukai kowa yay baya a guje dan ba wanda zaice ga sanda na shigo da gudu itama ta fita tana ihu bin bayansu nayi ina kallon su ina dariya turus mutane sukai ganina nan da nan aka buga kwakwazo ga Nana ga Nana su Mama na tsakiyar mutane maganar kowa dai da hirar ta Nana sai sukaji ana ga Nana kamar saukar aradu haka suka ji takai takai kowa ya fito kamin suzo Umma tazo ta kama hannuna"kuyi haƙuri dan Allah wani abu ta yi ƴata ce bata da lafiya ne",tana cikin magana ƴan gidan sukai da ira a wurin duk kaina suka yo amma na yi ma za na ɓuya a bayan Umma jikina na rawa su idon su Mama idona suka fashe da kuka sunawa Allah godiya mamakin abu guda dana basu shine na ƙi zuwa wurin su sai wurin wa ta da basu santa ba ma,ƙara duban su Umma ta yi"kuyi haƙuri dan Allah",Gwaggo ce ta matso tana cewa"baiwar Allah bakuyi komai ba ita wannan yarinyar ta bayanki ƴarmu ce wannan gidan kaf nata ne haka mutanen ciki danginta ne",mamaki da murna ne ya kama Umma ta fara faɗin"Allah na gode maka dama ƴar nan gidan ce ai ɗana ne yaron mai gidan nan Habibu shine wai ya kawo ni suna nan ya barmu ne ya yo magana da Mamar Ogan nasa shine tayo nan",matsowa Gwaggo ta yi zata kama hannuna na janye kai kowa ma so yake ya taɓa ni amma naƙi yadda Iyyo kuwa kuka kawai take tana azo a kira ma ta Alhaji Baffa,zamewa Ya Usaina ta yi ta ɗakko wayar ta tai kira ba jinawa tana ringing aka ɗaga"Hello Usaina",fashewa ta yi da kuka nan da nan hankalin sa ya tashi"lafiya Usaina","kazo"kawai tace ta kashe,Habib ne ya kalle shi"lafiya dai",ya faɗa yana gyara parking a cikin gidan dama sun shigo a tare suka fito bin gidan sukai da kallo ganin yanda aka taru waje ɗaya,Ya Mabaruka ce ta gansu tazo ta kama hannun su ta jawo su har gaba inda nake,kukan nake ban daina ba Ya Ruma ta zagayo ta ɗaga masa kaina fuskata ta yi jage jage da hawaye,wani irin dam yaji nan da nan wani irin farin ciki ya lulluɓe shi haka ma Habib da kansa ya ƙaraso inda nake zai kama hannuna na maƙale kafaɗa na matsa baya duk binsu da kallo nake amma ban san su gashi sun ruɗa ni sai miƙo min hannu suke,Habu ne ya ƙaraso"yallaɓai ƙanwata ce bata da lafiya ne",lumshe ido ya yi dama ya fahimci hakan tuni,Habib ne ya ce'?"Abubakar wannan ƙanwar ka ce da gaske","a a yallaɓai tsintar ta nayi itace wadda na saida mashin ɗin nan na biya ma ta kuɗin magani",gaba ɗaya zuba masa ido akai bama ya Babban Yaya kamar yana neman wani abu a fuskar sa,Habib ne ya matso ya kama hannun sa"dama akan wannan kasha wannan wahalar kuma ka jure",kai ya ɗaga"eh ai sanda na ganta naji tausayin ta ne inka ganta a sannan bazaka ɗauka mutum bace dan har purple jikinta yake",rungumesa Habib ya yi"mungode Abubakar",ɗagowa ya yi"ban gane ba yallaɓai",nu na ni ya yi"wannan ai matar Ogan ka ce ƴar nan gidan ce sace ta akai",salati Abubakar ya yi yana kallon Umman sa kai ta ɗaga masa,murmushin farin ciki ya yi ya matso yana kama hannuna Babban Yaya"kayi haƙuri yallaɓai dama itace wacce ka ke nema ai ban sa ni ba ta daɗe a wurin mu ba tun wancan lokacin ina police station tama yi sati shida a gidan mu,sai dai bata da lafiya karka yafewa wanda ya ma ta haka cocain akaita shaƙa ma ta ana ma ta allurar sa shine ya birkita ma ta ƙwaƙwalwa ance na kaita ƙasar waje tun sanda aka sallame ta a asibiti amma bana da hali shi yasa ban kaita ba",kafaɗar sa ya dafa"ban san ma me zance muku ba Abubakar na rasa da wane baki zan maka magana ko na ma godiya ko na jajanta ma ka wahalar daka sha akanta amma i promise u sai ka yi dariya a rayuwar ka kuma ƙasar waje za a kaita ka tabbata ƙafarta ƙafarka tabbas kaine ɗan uwan Nana na gaskiya ba taron mu nan ba",murmushi ya yi sanda taron ƴan gidan sukai caa da godiya haka ma Umma nan aka jata ciki amma na ƙi sakinta acan ma da ta zauna ina manne da ita kowa kalla farin ciki yake haka ana ji da ni kamar a haɗiye ni,inda aka barsu nan Habu yace"ka bi a sannu Oga zata zo inda ka ke",wani musulmin murmushi ya yi wanda saida Habib ya sara masa yana dariya,duban su ya yi a gayance yace"zata zo wurina ma kuwa yanzu ku shiga mota muje wani wuri",a take suka wuce Habu ke jan motar.
Hajara kuwa ai ina kamar mahukaciya ita da ƴan uwanta suka koma ciki a gaba suka sata wancan yace ka za wancan yace ka za ita dai sai kuka take shikenan annoba ta dawo yayarta ce tace"yanzu waɗannan mutanen zasu zama masu kuɗi wanda ya shekara talatin ma ba zai kaisu tarawa ba",ƙaramar ƙanwar su ce tace"wallahi kuwa ina ma nice na samota wayyo",ɗaka ma ta duka Hajara ta yi"dake ki ka samota da kashe ki zanyi",baki ta tura gaba"akan me zaki kashe ni ai ko ban kawotan ba gashi nan masu ƙashin arziƙi sun kawota",ta miƙe ɗauki ƴar swagger ta tayi tafiyar ta,haƙuri suka cigaba da bata suna faɗar ba sanya bakiga mahaukaciya bace,sauri shiru ta yi"au ku dama can kallon me hankali kuke ma ta to wallahi wannan aljanar yarinyar ba haukaba kome take kina ma ta makarci zata ƙulla miki kitimurmura ni fa har yanzu ban manta sharrin da ta ƙullamin ba nasha shaƙar mutuwa",dariya sukai amma dai duk haka anata kiyi ka za ki ma ta ka za da kanta zata ƙara guduwa,ta yarda da magan ganun su dan haka taɗau ɗamara dafa ni cikin ruwan sanyi.
UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
BABAN YAYA
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
35
Su Mama sun rasa ina zasu sa kansu dan daɗi hakama da Alhaji Baffa yazo ya yi murna daga haka gidan suna ya ƙara ɗaukar mutane bila adadin kan kace me jikina ya ɗume da zafi sai kar kar wa nake su Mama Umma ta faɗama nan Aunty Mama ta ce"haka take in aka takura ma ta bari a bata magani,da dabara aka ban nasha amma a ankare nake da kowa kome zasuyi ina kallon su wai kar a taɓani.
Basu jima da fita ba sai yace sukai shi inda ake saida nama ai kuwa Habu me zaiyi inba dariya ba"Oga kace dama halinta ne cin nama","au tana muku ne","sosaima kuwa ai yanzu har mu ta koya mana in bamu ci nama ba hankalin mu baya kwanciya ita kuwa batawa ahinkafa loma uku ta ƙoshi sai nama dan a sanda ta fara na tashi daga Habu mai adaidaita na koma Abubakar ma aikaci ai inaga wataran sai dai na karɓo bashi cifa take bawai lasa ba",dariya sukai wacce rabon su da ita sun manta nama kuwa aka siyo mai yawa dan saida suka siye shi aka musu take a way abin dariya yau aga wata jaraba take away ɗin nama a gidan suna,sanda suka shigo unguwar ana magariba dan haka sallah sukai sannan suka shigo gidan bakin shi ɗauke da addu a Allah yasa na yarda da shi.
Sanda akai kiran sallah ɗakin Aunty Mama aka kai mu Umma sai mamakin girman ko ina na gidan take da ƙyar tasa ni nai alwala ana koya min sallar ina yi abinda yasa Aunty Mama fashewa da kuka kenan da ƙyar Umma tasa ta ta yi shiru amma ba abin da take sai kallona,duk kansu suka shigo gidan har ɗakin Aunty Mama ina ganin su na taho wajen Habu ina miƙa hannu kafaɗa ya ɗaga yana taɓe baki sannan yamin alamar ba bu,Umma na kalla na nu na ma ta shi,haƙuri ta ba ni da hannu da mamaki Babban Yaya yace"bata magana ne",Umma ce tace"tana yi amma saita san abu sosai take ke magana akansa",kai ya ɗaga yana ƙara zuba ido yadda na rame sosai hannun sa yakai ya kama nawa kamar an tsira min allura nai ma za na janye ina nu na wa Habu shi"ki bishi zai baki nama da yawa ya siyo miki"saurin kai duba nayi bayan sa naga wayam sannan na kalli fuskar sa,murmushi ya yi"kin sanni ne",idona na so sa sannan na kalle shi na ɗaga kai"a ina ki ka sanni",cikin bazata sukaji nace"kana zuwa in ina bacci kace zaka tafi dani india sannan ɗazu ma muna zuwa gidannan kaita kirana da hannu har naje wani ɗaki anan wa ta jarababbiyar mata tai min ihu",saurin ta shi Umma ta yi saboda mamaki shi ma Habu mamakin yake su kuwa Aunty Mama da Habib ba suyi mamaki ba dan sun ko ada bana wa kowa magana shi in yazo zan masa,kai ya kaɗa yace"kina son wannan ɗakin",da sauri na ɗaga kai"to zo muje na kai ki"juyawa na yi na kalli Umma ta ɗagan kai haka ma Habu sai nabi shi,mun juya Habu yace"kar wanda ya ma ta magana Oga ana tanka ma ta zata fasa binka wallahi",dariya sukai nan ya kamo hannuna muka fita duk wanda mana magana sai ya kaɗa masa kai sai mutum ya fasa ni kuwa tsoron su ma nake ji,har ƙofar falon muka je ya tura ya shiga yana riƙe da hannuna matar ɗazu mai ihu na gani da sauri na ƙwace hannuna nayi kanta da azama ta miƙe ina zuwa na tureta ta faɗa kujerar"muguwa mai ihu",saurin riƙo ni ya yi yana mamaki wato faɗan mu a jini yake kenan sai yau ya shaida,ita kuwa mamaki ne ya kamata ganin ba tsoro ko ɗaya a idona na ma ta haka,hannu ya ɗaga ma ta ya ja ni zuwa ɗakin ƙara kallon ɗakin nayi nai dariya har haƙora na suka bayyana a gabana ya tsaya na kalle shi sosai kamar nasan shi sai kuma na tuna mafarkina sai na barshi a anan na sanshi,kama hannuna ya yi zuwa bakin gadon ya zaunar da ni sai binsa da kallo nake ɗan india ne shima nake faɗa araina,kayan dana watsar ya kwashe ya share wurin sannan yazo gabana ya duƙa gwiwarsa a ƙasa"zaki kwana anan ɗakin"ɗakin na kalla sannan na kalle shi kai na girgiza alamar a a"me yasa","bana son mai ihu","ai bazata ƙara miki ihu ba",murmushi nayi"zaka rama min inta min ihun","sosaima kuwa Nana ta",bakin sa na kalla nai dariya"dama kasan suna na","au sunan ki Nana"kai na ɗaga masa yay murmushi yana ɗaga hannuna ya ɗora akan ƙirjin sa"Nana rayuwata ce",zaro ido nayi na nuna kaina da sauri ya ɗaga kansa ya fahimci na gane me yace,murmushi nayi na ɗora kaina akan hannun sa shafa kaina ya yi na ɗago"muje ki faɗawa Umman ki zaki zauna da ni",tashi na yi da sauri shima ya miƙe yana riƙeni muka fito tare wajen da na ga me ihu na kalla ba ta nan sai na yi murmushi su Umma harsun fito nai ma za na tafi wurinta ina ma ta magana da hannu,dariya ta yi"wato kinga mijinki shine zaki gujeni ko",kai na ɗaga ma ta alamar eh,kawai sukai dariya nan ta juya tana masa magana yana amsawa sannan suka shiga mota saida aka janye ni sannan suka tafi wannan matar da nai sallah a ɗakin ta ne naga ta zo ta kama hanuna da kanta tamin wanka sannan tasa min kaya masu kyau a gaban mudubi ta tsaida ni"kallar min kanki anan dan Allah ki tuna ni",murmushi na ma ta na koma bayan ta na kwanta,ajiyar zuciya ta yi"Allah ya isa wanda ya cutar dake ɗiyata,wani Babban mutum ne ya shigo da sauri na nufi wurin sa ina dariya yasha mamaki dan an faɗa masa komai amma hakan da nayi sai na burgeshi hannunsa na kama ina nuna masa jikina kaina ya dafa"kinyi kyau Nana ta",murmushi na yi dan murna shima yasan suna na,ba jimawa saiga wannan ɗazun ya dawo da azama na tafi wurinsa ina miƙa masa hannu girgiza kai ya yi"zo muje ɗakin ɗazu na baki",da sauri na shiga gaba mayafin ma da ƙyar ya sa min sannan muka fita.
Muna shiga na fara raba ido banga me ihu ba har ɗakin ɗazu ya kaini gyalen na cire na yar na haye gadon girmansa da yadda yake da kyau shine yake burgeni shafa shi na shiga yi ina dariya table ya janyo ya aje min take away masu yawa matsowa na yi ya ɗauka ya buɗe ya miƙo min da saurin karɓa ina kallon shi kaian na nu na ya ɗaga min kai da sauri na fara ci shi kuma naga ya shiga wata ƙofa yana ciki na cinye na fara raba ido sai hawaye sharr fitowa ya yi daga wajen yana kai idon sa kaina da sauri ya ƙaraso yana kama hannuna"me ne ne ki ke kuka",kwanon na nuna masa,murmushi ya yi"kin cinye baki ƙoshi ba ko ai ba kuka zaki ba wannan duk naki ne da saiki ɗauka ki ci",kafaɗa na maƙale sai ya ɗauka wani ya buɗe ya bani ƙin karɓa na yi sai baki dana buɗe masa wato ya ba ni,zaunar da ni ya yi ya shiga ba ni ina ci saida na kuma cinyewa sannan ya ɗakko wani ya buɗe karɓa na yi na leɓo na kai bakin sa kai na kaɗa masa ya buɗe na bashi yaci murmushi nayi na ƙara ɗebowa na bashi da haka da haka saida ya cinye nima na ƙara ɗakkowa na bashi ya cinye waige waige na fara ya shiga bina da kallo sakkowa nayi zan fita ya taso ya riƙe ni"ina zaki","ruwa",dawowa ya yi da ni sannan ya ɗakko ruwa da da lemo buɗe murfin ya yi ya miƙo min karɓa nayi maimakon na sha saina nufi bakinsa da shi"au ashe ni ne zan sha"kai na ɗaga sha ya yi har lemon sannan yaban nasha,hannuna ya kama"zo muje ki wanke bakin ki",bin shi na yi da kansa yamin sannan muka fito a bakin gadon ya zaunar da ni yana kama gashina ya ɗaure"kwanta to"kallon wurin nayi na kwanta a hankali kamar me tsoron wani abu,daga yanayin kwanciyar zaka san
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 32