abincinsa",Aziza ce ta miƙe ta ɗakko masa nan ya zauna yaci sannan ya fice yana musu saida safe,Umma ta kallesu"kuma ku koma ɗakinku gasu Nabila can duk sunyi bacci ammanku kuna nan aje magana",tashi sukai suna dariya"Hajiya Umma mai komai dozin mun tashi saida safe","zan kamaki Aziza badan karatun bama da acan wurin Mubaruka za'abarki wallahi na rage wannan hayaniyar",baki ta turo"ni bazan zauna ba inda ba ke"tashi Umma tayi ta kama haɓa da mamaki "me kika ce Aziza ke da zakiyi aure ki ke maganar bazaki zauna in da bani ba",baki ta zumɓuro"to basai mu tafi tare ba",daƙuwa ta ma ta"tunda agarin mahaukata muke ko "Ibrahim dake shigowa ya katseta","yauwa Babana faɗa ma ta dai ai ni bansan bata da hankali ba sai yau","bama sai na faɗa ma ta ba in ranar tazo saita ɗauke ki ma ta tafi dake malamai ku wuce sai soki burutsun fara jin bacci kuke",dariya sukai"Umma saida safe"da Allah ya kaimu ta bisu nan shima ya ma ta saida safen ya fita shima,Umman zama tayi jikinta a sanyaye Allah dai yaba yaranta miji nagari,sai bayan Babban Yaya ya fita ta tuna bata faɗa masa mutuniyar ba lafiya ba,amma ta bari da safe ta faɗi masa sai dai bata son tada rigima tasan tabbas yaji abin bazai taɓa mutuwa ba sai dai ikon Allah dan tasan shi akwai haƙuri amma zuciyar dake jikinsa tafi ƙarfinsa in ya yi fushi musamman akan Nana to tanƙwarashi baya yuyuwa ta daɗi,tana nan zaune saida kowa gama shigowa sannan ta rufe gidan ta kwanta,a falo ita dama anan take kwana tace me ƴaƴa mata baiga ta bacci ba a ƙuryar ɗaki duk da tasan gidan da maza kuma da kariyar ubangiji wadda take roƙa kullum.
Yana ji kowa ya kwanta sannan ya fito ya ɗebi ruwa a rijiya ya shiga wanka dan shi ya saba da wanka kafin ya kwanta kodan ya yi boading ne oho wankan ma acan har gasar sa ake dan kar ace maka ƙazami gasu maza kaji wani ɗakin ɗum da ƙauri kamar riƙaƙƙun bunsuraye,bai shafa mai ba ya dai goge jikinsa tsaf ya ɗakko kayansa farare tas yasa sannan ya janyo ƙaramar laptop da Alhaji Baffa ya siya masa ya kunna kallo,anan gefen katifar ya jingina ya ajeta aƙasan carfet ɗin,kallon yake amma gaba ɗaya fuskar Nana ke a idonsa kashewa ya yi ya kwantar da kansa a jikin katifar ya lumshe idanuwansa ya fara magana shi ɗaya"ina ƙaunarki Aisha amma baki isa aure ba naso nayi rayuwata dake ɗaya saboda ba wata mace da zata samu gurbin da ki ka samu a rayuwata baki ɗayan ta,amma ke tawace na tabbata ko zanyi mata uku kece ta huɗu saina mallake ki ko bakya sona ni zan koya miki yadda zaki so ni",haka yay ta soki burutsunsa ranar rabi bacci rabi mafarkin Nana ta girma suna zuba soyayya ya yi.
Asubar fari na tashi da yunwa ƙafar ma da sauƙi tashi nayi na zauna Aunty Mama na bacci nan kusa dani,fulas na hanga can wajen inda take sallah saukkowa nayi na buɗe shi abincin ciki da sauran ɗumi bakina na wanko nazo na fara ci kaɗan na rage asannan akai assalatu kamar a kunnen Aunty Mama ta sai gashi ta buɗe ido tana addu'a akaina ta dire"ya ilahi Nana tashi ki kai da yunwa ko",kyaɓe baki nayi"wallahi kuwa Aunty Mama kamar naci bashi haka naji shine naga wannan kwanon na sauke kansa","ai dama naki ne saiki tashi muyi sallah ya ƙafar fa","da gudu kuwa Aunty Mama da sauƙi ai ba sosai take yi ba shima hakan saina matsa","to sannu tashi muje",kaf ƴan gidan kowa ya fito sallar asuba a bakin famfo duk anan mukai alwalar sannan aka tafi bada farali.
Bayan idar da sallah a masallacin nan suka zauna dan suna tine da maganar Babban Yaya,gaisawa sukai ajuna sannan ya kalle su"dama abinda yasa nace inason magana daku shine so nake a junan ku kuna neman auren ƴan uwanku in babu acan akwai acan karku duba alaƙa kuyi domin Allah saboda ko ba komai in akai wannan aure riba biyu ce gata alaƙar iyaye ga kwanciyar hankalin kowa saboda duk wanda ya cutar da wani kansa ya cutar ni dai wannan wata shawara na kawo karku sa dani aciki kunfi kowa sanin halina waɗanda sukai dai dai na aura aciki babu su in ma akwai to ba a inda nake muradi ba kuma koba yanzu ba zanyi",kai suka jinjina anan suke sanar masa sun amince kuma zasu bi umarnin sa kodan ƙara zunmunci,ƙara tattaunawa sukai waɗanda keda muradi dama suka sanar masa duk ya aminta dasu sannan suka ƙara tattaunawa,atare suke fitowa a masallacin kowa ya wuce gidansu.
Vote
Share &
Comments
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠
Story & written by
*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*
chapter 7️⃣
Ɗakinsa ya wuce direct ya hau azkar saida ya gama tsaf sannan ya fito a ɗakin ya shiga ɗakin Umma tana zaune su Maryam na haɗa koko da wainar gero suna rabawa a ƙasa ya zauna yana gaisheta da fara'arta ta amsa,sannan suka kawo masa nasa kan kujera ya koma ya dubesu"yau waye ya yi wannan wainar",Nabila ce tai saurin cafe maganar tana dariya "ba anan akaiba Iyyo ce tayi wai tana sadaka saboda kar bakin mutane ya kama Nana tsiwa","sadaka kuma akan Nana me akai ma ta kuma take sadaka saboda ita","wai faɗa sukai da Humairan gidan Kawu Iro shine bayan sun dawo gida a hanyarta ta zuwa gidan nan suka tare ta shi kawun da Humairan suka ma ta duka harda targaɗe",tun kafin ya gama ji ƙwarewa ya yi ya hau tari baji ba gani amma kaf maganar sannun da ruwan da ake basa bai bi takansu ba ya fice a fusace,Umma ce ta ɗirka ma Nabila dundu"agidan ubanwa aka ma ta targaɗen kawai ƙarawa abin fetur Nabila kinfa san halinsa irinsu guda da Iyyo amma shine ki tsaya iya gaskiyar abin ma bazaiyu ba shine harda sheri"sosa wurin tayi"wallahi Umma ina sane yaran basu da kunya shekaran jiya fa cemin tayi shegiya na barta ne kawai saboda Ya Ashiru yace na barta kinsan ina ganin mutuncinsa","zaki ga ma kafi mutunsa ke dai kika sa ni, yanzu Allah kaɗai yasan me wannan safiyar zata haifar","ai gara ya yi musu kaca kaca kinsan dai kawu Iro mugun tsoron Yaya yake wai ƙirar samudawa gareshi ya danƙeka zakaci ubanka kinsan tunda yawa Garba dukan tsiya yake shakkarsa saboda sunfi su goma amma sun kasa ƙwatar Garba kuma kinsan me ya yi to Aunty Maman ce tace yazo ta aikeshi yace ai itama ta haihu ta aiki nata","kai Nabila bansan sharri","shike nan Umma ki tambaya Ya Ruma a gabanta akai Iyyo harda kaɗa jarka",dariya Umma tayi"kai Iyyo Allah dai yaja kwana su kuma Allah ya shiryesu","ameen Umma harda mu",Maryam ce ta galla ma ta harara"kai Nabila akwai magana ana hutu wannan karon gidan Honorable zan fece dama Adda Usanina ba surutu gareta ba kuma kullum yara makaranta suke wuni ko ba komai bawa ya shawo ac","tare zamu ko"Aziza ta tare zancen","kutt kibi wa wallahi nemi wurin zuwa ko kuma ki tafi can Kaduna ku cancare keda Ya Hasiya dama kinga Ya Hashim nacan","ai shike nan canma ai akwai ac manya ma",Umma dai najinsu suna tayi kamar walƙiya Nabila taja hijabi"na tafi wurin Iyyo muyi hira","kin tafi gulma dai",Khadija da ta shigo ta amshe zancen"kai Ya Dijama","ba wata Ya Dijama shige kya bamu labari",tana dariya ta fita.
Kamar daga sama Mama taganshi ya shigo a fusace tasan halinsa sarai in ranshi ya ɓaci bai iya control ɗin fushinsa ba"Habibu ƙalau ka ke kuwa","Mama ina Nana","tana nan ɗakinsu mana",ina jin muryarsa nasan cewa a kunne yake dan haka da sauri na tashi tsaye ina ɗingishi na nufi Aunty Mama,kallon mamaki ta shiga bina dashi ganin na sauya tafiya lokaci guda zatai magana na rigata cikin shagwaɓa da hawaye nace"wallahi Aunty Mama ƙafar nan kamar na cire na yar haka nake ji zafi take",haɓa ta kama zatai magana aka ɗaga labulen ana sallama,kaɗa kai Aunty Mama tayi sai yanzu ta gane kan abin mamaki ne ya kasheta wai ina nufin wannan makirci nayi,amsawa tayi"shigo mana Habibu",shigowa ya yi ganin ina kuka yasa ya duƙusa kusa dani"sannu kinji Darling saina rama miki kema",a gwiwarsa na kwantar kaina shafa kan ya yi yana haɗiyar zuciya,kallon rashin fahimta Aunty Mama ta shiga yi masa badai akan wannan abin yake wannan uwar haɗiyar zuciyar ba,da idanuwasa da sukai ja ya ɗago ya kalleni"zaki iya tafiya",kaɗa kai nayi na taɓe baki ina kallonsa hawaye na zuba,share min ya shiga yi"am sorry kinji sweety tashi muje zan riƙeki ",miƙewa na yi hannuwana a nasa muka fita,ajiyar zuciya Aunty Mama tayi tafara magana a fili"kan uba akwai babbar cakwakiya nan gaba kaɗan a wannan ahalin",fitowa tayi taga Mama tsaye da ludayi tayi foster,dariya tayi ta taɓata"Dada ƙalau kuwa kuwa","inafa ƙalau kalli yarinyar nan bata warke ba amma yana zuwa ta zama kamar wata jaririya kalli yadda ya wani tarota kya rantse wata uwar mata ce ke naƙuda",kwashewa da dariya tayi"au danma ba'a gabanki akai film ɗin ba kenan yi aikin ki fansa ta biyu za'a ɗauka","to Allah ya kyauta duk akan wannan uwar tsiwar ake wannan jelen",ta shige kitchen Ƙarami da Ya Ruma suna kwasar dariya suma.
A ƙofar gidan sukai karo da Humaira kan tayi wani abu ya ɗauketa da mari saida ta faɗi,nan ta buɗe baki zatai ihu ya ɗora hannunsa akan leɓensa"shiiii kina tari saina murjeki anan wurin wawuyar banza kawai"gum tayi tana jan numfashi,tsawa ya daka ma ta"muje ciki inga kawun a gabanshi zan farfasa miki jiki harda nasa duka duk zan haɗa na miki tunda ina da tarbiya bazan iya dukansa ba",sumi sumi ta wuce gaba,ko sallama basu samu arziƙinta ba sai ganin Humaira sukai dafe da kunci muna shigowa kawu ya zabura"kaima rama matan kazo yi saboda an taɓa ƴar gwal ko","eh kawu shi me gaskiya masoya gareshi fili da ɓoye",ƙara hayayyoƙo wa ya yi"wannan fitsararriyar yarinyar itace mai gaskiya",katseshi ya yi"ga fitsararru nan ka tara a gidanka duk sun fitsare ƙafarsu yasa basa ganin girman kowa ciki harda kai,wallahi kashedi nazo nayi koda wasa wani daga gidan ya kuma dukanta saina nasa shi jinya ke kuma fuska kamar jiƙaƙƙen abinci in ki ka kuma jan wani faɗa bama ita ba zakiga yanda zanyi dake",cikin ɗaga murya kawu yace"kace harda ni a kashedin mana kaga yanda zanyi daku",shima muryar ya ɗaga masa"ai gida nace kaga kuwa igiyar gugar gidan ma harda ita bama kai ba,muje kinji Darling sis","tom Darling Bros",muka fito kowa ya kasa cewa komai sai Jammai da ta sheƙe da dariya"amma anji kunya Iro ɗanka yazo har gida ya yanka maka kashedi kuma ka karɓa",zaburowa ya yi kamar zai duketa"ki iya bakinki Jummai zan karya ki fa",wani gantsarewa tayi"haba saikace Saude kai kasan ko mota zata karya ni ne saboda ƙarfin gudu amma ba wai dan girman jiki bare kai kamar ana ɗibanka ana miya",ta buga cinya ta wucewarta,fuffuka da zage zage ya shiga yi amman a banza tunda wanda yake dansu basu san yana yi ba.
Bamu shiga gidan ba muka shige gidan Iyyo tana zaune kan tabarma a baranda ta gama sadakar"a a kune haka da sassafe ya yadai langwai ƙafarce har yanzu",kyaɓe baki nayi"eh Iyyo","sannu kinji ai har gida naje naci musu mutunci babu mai ƙara taɓaki","nagode Iyyota","kai kuma ina kakaita haka","nima kashedin naje nayi","yauwa ɗan albarka shi yasa nake sonka to kuzo ku zauna"hira mukai tayi har wajen tara da rabi sannan ya maida ni gida ya wuce.
Wajen goma da wani abu Umma tazo suka shiga wajen su Iyyo suna tsakar gida suka shigo,tabarma Iyyo ta shimfiɗa musu sannan suka gaisa Alhaji Baffa ne ya dubesu da gani yasan akwai abinda ya kawo su"Sa'ada lafiya dai ko","dama Baffa akan yaran nan ne Habibu akwai wata yarinya da yake nema to iyayenta sunce ya turo in da gaske yake asan da maganar kafin yarinyar ta gama makaranta a tsaida lokaci",numfashi yaja"hakan ya yi kyau dama anan ma inaso su gama karatun yaran nan mata a tsaida musu da lokaci suma amma tunda hakan yazo ki turo min shi ya kaini gidan su yarinyar tunda wanda ya kamata yaje bayanan","to shike nan za a turo maka shi insha Allahu mungode Allah ya ƙara girma zamu koma Hajiya iyyo kakar Nana","ku faɗa da ihu wato harda ke ko Sa'a",dariya sukai nan suka fito Iyyo na musu a gaida,bayan fitarsu Iyyo ta kalli Alhaji Baffa tace"Alhaji infa Habibu zai auri mata uku sai an cika min alƙawarina kan na mutu kai ko bayan na mutun ma ayi",Insha Allahu kuwa A'i zaki farin ciki ke dai Allah ya bamu lafiya da tsawon kwana","to amin Alhaji amma nikam yarannan mata masu auren suna da yawa fa",eh mazan su sai gaba gara kowa ya yi ƙwari tukun bana son yawan haya A'i kowa ya gina gidansa duk ƙanƙantar sa haya masifa ce musamman su yara ace kullum kana kwasar kaya kana sauya wuri wataran ma tashinka za'ayi baka shirya ba kuma balallai ka samu inda zaka zauna adaidai lokacin ba ko kana da kuɗin kamawar,amma kinga ni yanzu inada inda kowa zai gina in bayason wurin sai ya saida yaje inda yake so ya saya ya gina ni duk maiso ma aginin zansa hannu miye amfanin kuɗin dana ke tarawa tun ina jeji","Allah sarki Alhaji Allah ya biyaka ina alfahari dakai a kullum baka duba yadda sauran ƴaƴanka suke maka duk da bani na haifesu ba wallahi Alhaji bana son abinda Rabilu da Iro keyi kalla Nuhu baya yi amma su sai suna nuna ba'a sonsu kullum,amma shawara guda yaran nan kawai duk maison auran ya yi ","to shike nan Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alkhairi,su kuma ki barsu ai Hamisu da Sadisu saida naci musu ƙaniya sannan suke shiga cikin su Ashiru dama shi Haruna bashi da matsala","hakane kam to Allah ya shirya","amin A'i bari naje nan wajen Malam Bala akwai maganar mu dashi","adawo lafiya a gaida shi".
Umma gida ta wuce wai ta tafi dambu dan yau akwai manyan baƙi Ya Fatu da Ya Ushe na tafe shi yasa bata shiga ba Maman kawai ta shige itama.
Umma na shiga yana fitowa a ɗaki"a a sai ina kuma Habibu","Umma zani wajen wani bawan Allah ne daga ganina akan titi yace wai nayi masa dama yana neman mutane irina","ikon Allah to me kayi da ka birgeshi haka","wallahi Umma daga rabon faɗa kuma ɗaya ne keneman cutar ɗaya kuma mai cutar yafi wancan baki duk ya zaƙalƙake ni kuma na fahimci me ke faruwa shine nashiga fa ashe mutumin kuma akan idonsa akai komai shine yasa aka masa magana dani yaban adress wai nazo yau dama yana da matsala yana neman mai masa maganin ta,shine zanje","to kayi addu'a Allah ya baka nasara mai ɗorewa a dawo lafiya yauwa inka dawo Alhaji Baffa na neman ka","ameen Umma nagode in na dawo zanje",ya fito su Maryam na masa Allah ya bada nasara.
Bayan Rabuwar mu da Babban Yaya na ware ƙafar na miƙe Ya Ruma ta kalle ni"ubangiji ya shiryeki Nana waike nan makirci ki ka ƙulla wallahi ki kiyayi kanki ko kuma ki jajubowa kanki masifa Allah ya haɗaki zaman aure da kishiya",wani juyi nayi agabanta na haɗa hannu na buga"he he he Ya Ruma ai ni dama bazan auri saurayi ba me mata zan aura shi yasa ki barni na goge tun daga yanzu",ranƙwashina naji anyi na dafe wurin na harba can bayan Ya Ruma ashe Mama ce,daƙuwa ta min"wallahi Nana ki kiyayeni ƴar ƙarama dake sai zancen manya mijin ma ashe kin ware wanda zaki aura"baki na buntsuro ina buga ƙafa a ƙasa muhucin hanunta ta jefa min"ja'ira zoki wuce ki bar wurin nan ko in kamaki in miki dukan tsiya",ihu na ƙwala"Aunty Mamataaa",da gudu ta fito daga ɗakin zaninta a hannu"Nanata! Nanata!!waye ya taɓaki,zagayowa nayi na koma bayanta na rungumeta,haɓa Mama ta kama"yau naga takaina ni Halima bari dai na fita shirginku keda uwar taki",ta wuce kitchen,kama hannuna Aunty Mama tayi muka shige ɗaki Ya Ruma sai dariya take dan gidan mu ba'a faɗa sai dai dariya,muna shiga ɗakin Aunty Mama ta kalleni tace"buduruwar Yayanku wacce irice",kwashewa nayi da dariya"wallahi Aunty Mama banufiya ce","banufiya kuma","eh wallahi Aunty Mama har yaren suke kinsan nasan Mama Mari to kallar yaren komai da komai",dariya Aunty Mama tayi"kice tafi ki komai koda nan gaba kin girman",wata zubura nayi na miƙe daga kan kujerar"kaiii da wannan bajajjen hancin Babban Yaya fa yace ba macen da zata kaini haɗuwa idan na girma","au haka yace shima","eh mana","to shike nan saiki dage kina cin abinci kina kumari karki girma ki zama kamar sanda kinga yace baya sonki ko",kuka na saka"wallahi kina bani abin sa kumarin dan wallahi Babban Yaya nake so","ai nasan da hakan dan haka duk abinda na baki kina cinyewa banda wasa","na yarda Aunty Mama","to goge hawayen naki kinga ma Ummansa da ƴan gidan su kowa nasonki kirki na musu tsiyar taki","ai banayi kuma nima ina sonsu ai","to shike nan kwanta ki huta kiyi baccin ki abinki","to Aunty Mama"na kwanta kuwa dan tasan halina da bacci muna shiri,kai ta girgiza kawai ta fito suka kama aiki da Mama nan da nan sukai dukkan abinda zasuyi kafin azahar saboda baƙin.
Vote
Share &
Comments
Ƴan uwa
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
*𝗕𝗔𝗕𝗕𝗔𝗡 𝗬𝗔𝗬𝗔*
𝚁𝚎𝚗𝚎𝚠
Story & written by
*FATIMA AMINU*
*Ummu Saddi'q*
chapter 8️⃣
******
Babban Yaya gidan Iyyo ya shigo yana sallama,kamar zubar ruwan sama ta tareshi da magana"malam Habibullahi sai ina haka aka sha shadda","Iyyo kenan tamu ta mutunci albarka nazo asamin zani wani waje duk da bansan dalilin kiran nawa ba",yashe baki tayi "to Habibullahi nawa ni kaɗai Allah ya haska fuskarka akan tasu ya baka nasara ha haska maka alkhairin dake cikin lamarin",kusa da ota ya duƙusa dan yaji daɗin batun ta"ameen Iyyo ta nagode sosai da wannan addu'a Allah yaja kwana ya ƙara lafiya,Alhaji baya nan","eh amma baiyi nisa ba kabi ta hanyar babban titi zaka samesa anan wajen wannan abokin nasa",tashi ya yi"tom Iyyo saina dawo","a dawo lafiya Allah ya kiyaye","ameen ameen Iyyo ya fita,ta can inda ta faɗa ya biyo yana nan kuwa,tun daga nesa suka hangoshi nan malam Bala ya kalli Alhaji Baffa yace"Alhaji a gaskiya kayi dace da zuria kalli jikanka namijin gaske yana birgeni yaron yasa mu tarbiya sosai",ɗan murmushi ya yi"ni kaina ina son Habibu ya ɗauke ni mahaifi ne ba kaka ba yanzu haka ka zuba ido kayi kallo abinda zaiwa mahaifinsa shi yazo yamin","kamar ya fa Alhaji"bai bashi amsa ba ya ƙaraso wurin yana sallama"Assalamu alaikum manyan tsofifin wannan ƙasa",ƴar dariya sukai"amin wa alaikumul salamu Habibu manyan yaran wannan ƙasa",ɗan murmushi ya yi ya durƙusa"ina wuninku",cikin fara'a suka amsa sannan yacewa Alhaji Baffa"Alhaji zamu wani wuri asa mana albarka",murmushi ya yi"to Habibu Allah ya bada nasara ya bada sa'a a kula da kalar mutanen da za'a shiga cikin su, kasan mutane adole duk inda zaka shiga sai kaga masoya da maƙiya dan haka ayi a hankali da mutane","nagode Alhaji kuma zanyi sai na dawo kiran da ka ke min ma in na dawo zanzo","to adawo lafiya Allah ya bada nasara","amin amin",daga haka ya wuce zuwa bakin babban titi dan ba da mashin zashi ba,yana bada baya abokin Alhaji Baffa ya ɗora"gaskiya ka faɗa Alhaji Allah ya musu albarka ya haska rayuwarsu","amin nagode sosai Malam".
******
GIDAN GWAGGO MA'U:
Ƴar wayar nokia ta Gwaggo Ma'u keta tsuwwa,kware murya tayi tana magana"ke Hadiza miƙomin wayar nan mana kinaji tana ta ƙara",Hadizan ma cikin ihu ta maido ma ta da maganar"nifa aiki nake kizo ki ɗauka mana","inye dani kike Hadiza",kumbura baki tayi"to a zaune fa ki ke kuma nasan wannan ƴar takurar ce Ya Aisha tun ɗazu take kira kuna magana amma kunƙi gamawa itama dama ga gulmar tsiya",a fusace Gwaggo Ma'u ta taso zuwa ɗakin kanta ta hayayyaƙo"zanci ubanki ƴar iska mara kunya kin min shiru ko kuwa",baki ta muguɗa ta kauda kai tana ƙunƙuni,wayar ta ɗauka tabar wajen tana ɗagawa,
"Halo wake magana ne",daga can ɓangaran aka amsa cikin laushin murya"kai Umma kinƙi ki waye kullum na kiraki saikin ce waye","ai Zainaba ce","nice Umma ya gidan","lahiya lau ya megidan da yaran","kowa lafiya Umma zamu shigo ai wani satin","to Allah ya kaimu ya maganar mu dake",ɗan jim tayi"gaskiya nifa Umma bazan iya waɗannan abubuwan ba mijina namin komai bana neman abu a wajensa in rasa to Umma miye na mallake shin",tsawa ta daka ma ta kamar tana gabanta ne"ke dalla wawuya rufen baki ai abinda za'a masa ba wai saikin tambayesa abu ya kamata ya miki ba da kanshi zaina dunƙula ya baki ba kya kallon waɗannan yaran su Fatu harfa mota ce dasu ga filaye suna siya","to Umma ca aka miki malamai suke bi, su ɗinma dukkan su tsantsan biyayya ce tasa suke samun cigaba a gidajansu da rayuwarsu",katseta tayi"rufen baki shashar banza ana nuna miki gabas kina ga yamma","ni dai Umma kibar maganar nan gaskiya",ta kashe wayarta tana fashewa da kuka a fili ta fara sambatu"wannan wacce irin uwace haka ace dakanta take nu na miku inda zaku halaka wallahi bazan bi ba saidai tamin ko me zata min amma ni mijina da zuciya ɗaya nake sonsa kuma da ita zan zauna dashi",ta goge hawayenta ta gyara fuskarta sannan ta fito a ɗakin,da sauri ya shige ƴar kwanar wajen ɗakin dan kar ta ganshi komai take faɗa ya gama jinta tsaf wani so da ƙaunarta yaji yana daɗa yi kuma zai ƙara jajircewa wajen ganin ya kyautata ma ta shima.
A kan tabarmar da take ta wullar da wayar tana tsaki"wannan ƴa ko shegiya dama nasan bazata amince ba yanzu ƴan kuɗin da malam yace in na kawo mutum zaina bani tamin buƙulu wawuyar yarinya kawai amma tunda Aisha ta amsa tasan zata samu wani abu mai tsoka ta wajenta",sallamar da ake tasa tai shiru tana amsawa,haɓa ta kama"au Fatsima ke ce ke doka sallama haka kamar kin shigo gidan mutane dubu",ƴar dariya tayi"to Umma in banyi sallama ba kai tsaye ki ke so na shigo",dakatar ta tayi kamar kashi na ma ta magana"naji ni yimin shiru ni miye wannan a hannunki","cefane ne Baba yace na taho dashi","mitsss nazata ma saurayi kikai kukaje ɗan yawo aka kawo min ƴar kaza",da mamaki take bin Ummar tasu da kallo"saurayi kuma Umma sannan da bakinki ki ke ambatar yawo Allah ya tsareni koda kuwa ke kinason hakan,kuma dan uwar saurayin koda wasa yace muje yawo saina jefar mai baki da dutse wallahi",ta aje ledar ta shige ɗaki,da harar tabi bayanta"banza wawuya wallahi keda Zainaba banyi dacen ƴaƴa ba gara ma ita ni na haifa amma kam"sai tayi shiru ta janyo ledar tana buɗawa,wani koren tattasai da attaruhu ne sai wani tumatur ƴan ficifici kamar tumaturin tsohuwa"na shiga uku ni Asama'u yanzu shi Ya'u wannan kayan miyan ne saikace na wasan yara wallahi bazan girka komai ba sai dai kowa ya zauna da yunwa",Hadiza dake fitowa a ɗaki ta kalle ta kamar wata sa'ar ta"wallahi ke zaki zauna da yunwa Umma shi dai kinsan kullum yana tuburin mai shayi kuma ai ba zaman banza yake a wurin ba zaici ya ƙoshi abinsa,mu kuwa kinsan ba mai zama da yunwa gwarama waccan ustazar dama nasan Baba dan ya mana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 32