na ya fiya shi yasa kinsan sunan ki sunan Umman ki kenan Abban ki kuma sunan Babban Yaya zan ɗakko miki hoton su amma fa yana ɓangaren Hajiya Fulera",kaina ta da fa"nagode Ƙawan ta ban ma san me zan ce miki ba ni",janye hannun ta na yi na miƙe da ƙyar dan cikina nauyi gare shi"ba wata Ƙanwar ki mu shirya cikin kutumar uban mu idan Hajiya Fulera ta ga ne na sace ma ta takardu na baki shi kum Abban Babban Yaya fansar iyayen ki ya miki da dukiyar da zai ba ta dan Abban ki abokin sa ne sosai",da mamaki ta riƙe haɓa"Allah wadai na da banwa Abba biyayya ba","ba komai Aunty Hajara shi kuma bai taɓa jin haushin ki ba dan yasan ba daga ke ba ne","to shike nan muje ayi tuwan kar ɗana ko ƴata suji haushi na",dariya na yi ai nan gaba kaɗan cikin nan jikin ki zai koma ni tsoron haihuwa nake karna mutu",baki na ta rufe"kar ki kuma wannan batun ƙalau zaki haihu taho muje ki daina wannan soki burutsun yauwa Aunty Hajara in kin je gida ko kiyi irin abin nan idan ana magana kice Abba wai sunan wa naci ne sannan me yasa nake ƙaunar sunan Habib zaki ga yana gumi wallahi",dariya ta yi"to Mama Nana",nima dariya na yi ranar cikin farin ciki muka wuni sannan muka tafi gidan su Mama dama kowa ya daina mamkin tsakanin mu dan muna futa na koma mara lafiyar kwanya.
INDIA
Ɗakin da suke taro cike yake kowa ka kalla farin ciki ya ke saida aka nutsu sannan shugaban shige da fice da lura da kuɗi wato Babban Yaya ya fara magana"Alhamdulilkahi muna godiya ga Allahda yasa mana albarka acikin wannan company tun a watan baya kowa ya maida abinda ya kashe a wannan company a wata guda komai da aka ƙara samu ya zama riba sannan company ya zama riba shima",murna ce ta ƙara ƙaruwa sai gaisawa ake dakatar da su ya yi"iya mu masu iko a wannan company muna nan amma a masaukin baƙi namu dana cikin garuruwa da ƴan gari ma ga baƙi can sama da mutum dubu shida suna son saka hannun jari kuma dama kun san da haka tun wancan lokacin na faɗa muku yadda komai zai kasan ce dan haka zan gara amsar su daga ɗaya har mutum million guda",haka ne suke faɗa nan ya fiddo musu takar dar tsari da sharuɗɗa da ya fitar kowa ya gani sai jinjina masa ake za ayi abun a tsari yadda bamai cutar wani haka ba za a ƙwari company ba sanna za a daɗawa ma aikata albashi,wannan abu fa ya yi daɗi fiye da tinani,sun daɗe suma tattaunawa sannan suka tashi kowa so yake ya gaisa da shi,yanda ya aɗa haka ce ta kasance sati uku yana karɓar baƙi kullum sama da mutum ɗari da wani abu sai a kwankin sannan mutane suka sauƙi,cikin wata guda kaya suka nin ka da sau ɗari ɗaukakar company ya ƙara zaga duniya sannan aka ƙara ma aikata.
Sai a kwanakin bayan an gama sannan ya samu kansa kullum suna vedio call yana mamakin yanda gidan sa ya zama a laptop ake maganar yana ganin yanda kowa ya ke gilmawa sai hankalin sa yake ƙara kwanciya,amma kullum Aunty Hajara na masa masifar kayan jarirai zaina siya mana in ba haka ta biyo shi ai tasan inda ake sayarwa,da ƙyar yake lallaɓata ta haƙura yana siyan kaya yana turo ma ta a ɗakin ta ma take tarawa ni ban san tana yi ba,da haka cikin yake ƙara girma ni kuma iskanci na sama sai dai ba a gane na warke.
Dawowar Habib kenan daga wurin aiki da kayan ma a jikin sa ya shigo ɓangaren mu muna ta musu da Aunty Hajara ya shigo dariya ya yi muna masa sannu da zuwa kallona ya yi"Yaya ta ni dama fa nasan ƙalau ki ke shine ki ke samu tausayin ki kullum muna jajanta abu ɗaya",dariya mukai sannan Aunty Hajara ta ce"kasan mutuniyar akwai tsare tsare yanzu ma tsarin ne ya biyo da haka shi ba ta nu na ba daga ni sai Mama da Gwaggo Ma u sai kai kuma dama kai ta ce tana so ta faɗa ma sai dia batasan ya zatai ba",ɗan murmushi ya yi"to ai yanzu na sa ni sai a faan sirrin"tashi na yi na je ɗakko laptop ɗin ta wajen Abba na fito,zama na yi na kallesu sannan na haɗe rai"amanatun amana a lahira ta ciku ta balbale ku sama da ƙasa",kwashewa sukai da dariya Habib ya ce"ya zaki na kaimu jahannama kai tsaye",dariya na yi baje na kulle ƙofa na saki labule sai bina suke da kallo,dawowa na yi na zauna sannan na kunna juya musu ita suka fara gani na nida Abba muna hira har abin ya dawo na bubuwan da ya faɗa min sannan da sirrin mutane masu mugun yawa ga hoton su nan yana nunan ɗaya bayan ɗaya,fashewa Aunty Hajara ta yi da kuka da buga kanta da bangon da yake kusa da ita innanillahi wa inna ilaihi raju un wai mutane akan kule sai a aikata komai wannan wacce irin masifa ce haka,Habib kuwa kamar zai fashe dunƙule hannu ya yi zai da ki laptop ɗin na janye ya tashi center table ɗin"in ka fasa ta kuma mu kama ina malam gashi nan hannun ka na jini",tashi ya yi ya fita a fusace Aunty Hajara kuma ta miƙe tana kwashe glass ɗin"Nana dama na ce ba mutum ba ce ke kince mutum ce ke ta ya akai Abba da ke kaɗai ya yarda har ya baki wannan sirrin",tashi na yi ina ta ya ta kawai ina murmushi sai bayan kusan sati biyu sannan yazo ya sa me ni mukai magana mun daɗe sannan ya ta fi a kwanakin Babban Yaya ya dawo munsha murna kuma ya tabbar gidan sa ya gyaru duk da ni bamai lafiya ba ce a ganin sa,cikakken kwana ashirin ba a yi da dawowar sa ba ya tafi Abuja,wajen sha ɗaya na dare ina bacci naji kamar ana ta shi na ashe ciwo ne tun ina daurewa har na kasa kamar daga sama sai ga ta ta shigo ganin ina dafe ciki ta fita da sauri ba ta nemi kowa ba ta juya mota tazo ta ɗauken ta ɗauki kayan da ta shirya tuni sai asibiti Murtala ne kawai ya sa ni kuma tace kar ya faɗawa kowa a sanda muka je ciwon baiyi yawa ba muna shiga kamar an kira shi nan da nan abin ya yi yawa kusan an raba dare suka ce ma ta bari suyi min aiki nan tace ta amince amma kafin aikin sai gashi na haihu fitowa sukai suna faɗa ma ta da gudu ta shiga ta ɗauki ɗan amma ɗan baizo da rai ba kuka ta shiga yi kamar ranta zai fita cikin hayyacina na dawo naganta tana kukan murmushin ƙarfin hali na yi"kiyi shiru Aunty Hajara baizo da rai ba ko"kanta ta kaɗa tana ƙara ƙanƙame yaron gashi nan ƙato kamar a kira shi ya amsa da ƙyar suka sa ta fita amma ta hana yaron haka dole suka bar ma ta ta ɗau shawel ta nan naɗe shi ta ƙara rungume shi da ƙyar ta ɗaga wayarta ta kira Gwaggo ta faɗa ma ta asubar fari suka cika asibitin wai jarda ni a bawa Aunty Hajara haƙuri amma taƙi yin shiru saida Babban Yaya yazo da Baffa da Alhaji Baffa da su kawu sannan ta bada ɗan aka sallameni muka koma gida wanka aka masa suka mai sallah suka binne shi.
Zuwan wannan yaro babu rai ya taɓa kowa amma ba ya Aunty Hajara ko falo ba ta fotowa kullum tana maƙale da wayar ta tana shafa wayar dan ta mai hoto yafi goma kowa gida da dangi anzo sai mamakin yadda ni ragal amma kishiya ta damu da rashin yaron a haka akai sati biyu duk mun haƙura da yaron.
UMMU SADDIQ CE🌹🌹🌹🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
BABAN YAYA
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
38
GIDAN SU HAJARA
Abba ne zaune kusan su shida sai Aunty Hajara da ke gefe tana hawaye kallon ta Abba ya yi yace"wai akan kishiya ki ke wannan kukan kishiyar ma maƙiyar mu",kai ta girgiza"haba Abba jariri fa na kashe",yayar ta ce ta harare ta"to bakin ce gwara abar uwar da rai ba kina sonta yanzu"a fusace ta miƙe"eh nace ina sontan duk abin da na ke ma ta bata taɓa jin haushina ko ta zageni kuma tana faɗa min gaskiya amma ku fa me ku ke faɗan da zan ƙaru bayan halaka da kuke kai ni kuma na ce ku faɗamin me ne manufar hakan kun ce sai nan gaba sai ku riƙe gaban ni ku barni da zunubin da yake kaina"ya ɗau jakar ta ta fita tana kuka,dariya sukai Abba ya dubi ƴar ta shi da abokan sa"da wannan hujar ita zamu kama ta mijin ya saketa dan tabbas bazai zauna da ita ba in yasan ta mai haka kin ɗau vedion iya maganar ta ta kisan ko","eh na ɗauka amma Abba ba yanzu ba sai zaman ya iƙa abin ya ma ta daɗi tana ganin kamar tasha sai kawai mu tona ma ta asiri in ya korota muma nan sai mu koreta shike nan ta koma titi"jinjina ya ma ta sannan suka cigaba tattaunawar su.
kuka Umman su ta shiga ɗaki tana yi da tasan haka ce zata kasan ce da bata bar Hajara ta aikata wannan kuskuren ba wayarta ta janyo zata kira ta saita fasa kawai ta shiga ma ta addu a itama tana neman yafiyar Allah akan abin da tasa baki aka aikata da ita.
Abin ban mamaki Aunty Hajara ta zame min kamar Yaya ba ta son ɓacin raina abin da ke damuna kullum sai munyi faɗa saita na zuwa har ɗakina tana kuka wai na yafe ma ta wannan abu na ɗagan hankali,yau daibtana cikin faɗa na tare ta"nifa wannan neman ya fiyar ya ishe ni ko rai li ka kashe min ai yaci ace na yafe miki"saurin kallo na ta yi sai ta shi da gudu ta fita ni dai ban gane kanta ba sai na barta kawai.
A wata uku na ware na kwashi jiki na bi miji india ba tare sanin kowa ba Aunty Hajara takar da na rubuta ma ta dan wani ɗaukar fansa duk ba shi ba ne ta bakin Abban in wani zai cutu karna ta da komai ya bar su ga Allah.
BAYAN SHEKARA BIYAR
*BABBAR CAKWAKIYA ZA TA ƁALLE*
Na gama makaranta na zama ƙatuwa mijin mu ya ƙara zama hanshaƙi haka ma Habib sai dai shi yana gari biyu kowa yana cikin farin ciki ya yinda waɗanda bamu san ma da zaman su ba sun samu a ƙahon zuci bama ya idon sauran wato Abban su Aunty Hajara dan shine idon su.
Rayuwa ta fara yiwa wasu tsanani dan wasu daga cikin su sun fara tuhumar juna ko suna cin dunduniyar junan su dan komai na su ya tsaya ta ko ina wannan dalili yasa Abban su kiran Hajiya Fulera ta ce zata turo masa da kuɗi ya jira dan shima abubuwan hannun sa da kadarorin sa bai san ina suke zuwa ba dan sun fara ƙarewa,yana tsaka da jiran ta ta kira shi bata ga komai ba fa har waɗancan da ta ƙwace na kishiyoyin ta wannan abu ya kusa sata ta yi hauka nan tace ma sa tana hanya nan da kwana biyu ta dawo gida ta duba a kwana biyun kuwa ta dawo kwatsam muna taron suna Ya Ruma ta haihu da sanyin safiya sai ganin ta mukai muna ta re da Aunty Hajara munsa kaya iri ɗaya wa ta uwar atamfa mai golden sai sheƙi muke kana ganin mu kasan muna hutawa,ba tare da kowa ya lura ba sai ga ni akai ta shaƙeni dama ƙarfi gareta nan da nan aka taso kanta amma an kasa ƙwata ta ni kuwa sai zaro ido nake ina jina a sama wani kukan kura Aunty Hajara ta yi ta haska ma ta mari wanda saida ya razana kowa bare ita da ta sake ni ba shiri da sauri ta janye ni zuwa bayan ta sai huci ta ke kowa yasha mamakin abin da ta yi ta mari ƙanwar uban ta akan kishiya,cikin tsanin mamaki Hajiya Fulera ke duban ta" ni ki ka mara Hajar akan na shaƙi kishiyar ki?",itama duban tsabar idanuwan ta ta yi"to me ta miki da zaki shaƙe ta ko baƙar muguntar ce ta motsa wallahi bari kiji Fulera duk wanda yace zai taɓa Nana ko mijin ta ne sai inda ƙarfina ya ƙare dan haka baki da gurbi a gidan nan fita wato kinje ɓangaren ki kinga wasu a ciki shine zaki zo ki huce akanta dan ita ta miki kashi a gado",wani irin duba Hajiya Fulera ke wa mutanen gidan sai nan ta nu na ta"Hajara naja da uwar ki ma bare ke zaki ga abin da zai same ki a yau ba sai gobe ba"tana kaiwa nan ta juya ta fita,juyowa ta yi tana shafa wuyana"sannu Nana yi haƙuri",hawayen fuskata na share na rungume ta nan aka shiga mana dariya amma baiwar Allah ita kaɗai tasan me ta ke ji a cikin zuciyar ta faɗuwar gaba kamar ƙirijin ta zai ɓurma.
Tana shiga falon gidan yayan na ta dama Umma ba ta nan kallon sa ta yi"me ka shirya kan Hajara so nake naja rayuwar ta kan titi na tarwatsa ta",ba kunya ya taso ya kama hannun ta ya zaunar da ita wayar sa ya janyo ya nu na ma vedion shekara biyar ba ya take tasa shi a aka turawa Babban Yaya.
Yana tsaka da magana da Ya Hasiya saƙo ya shigo ma sa nan ya ɗakko ya duba tun kamin ya gama ga ni ya fara gumi karɓa Ya Hasiya ta yi ta shiga ga ni ta ɗago zatai ma sa magana taga yay ya fita kanta ta dafe ba ta so ayi abin kunya a gaban mutane duk ba baƙo a gidan ina ɗaura manta ɗankwali ba tare ta sa ni ba naji an ture ni an fizgo ta ya kwaɗa ma ta mari nan take hakan ya janyo hankulan mutane aka taso kansa ana tambayar miye hakan kanta ta sunkuyar amma ta dake zuciyar ta ba tai kuka,tasowa na yi daga hankaɗar dana sha na ture shi shima"Babban Yaya miye hakan zaka dake ta akan idon mutane in wani abu ta maka basai ka bari sai mun koma gida ba..."ban gama magana ba ya haskan nawa marin da sauri ta janye ni ta tsaya agaban sa"in laifi na maka ka hukunta ni ni ɗaya amma karka kuma dukanta",ƙara marinta ya yi ya rufe ta da duka da gudu Habib ya ƙaraso ya janye shi"miye hakan Yaya ka ke dukan matarka kamar kana dukan ƙato",cikin hasala ya ɗago kansa"ka barni na kashe ta wannan muguwar dama ban yarda da ita ba tun farkon nu na son Nana da ta nu na ashe kuwa zargi na ya tabbata ita ta kashe yaron da kanta",wannan magana ta doki kowa amma banda ni vedio aka kawo aka shiga ga ni kowa ya shiga tashin hankali ana ma ta tofin Allah tsine,wayar na fizga na kalla kai da gani kasan an yanke ne tamfatsa wayar na yi da ƙasa"wallahi wannan vedion ba haka yake ba yanke shi akai kuma ka duba waye ya turo manka kana gani kasan munafirci"kaina ya yo ta tari gabansa"duk abinda ka ga ni haka yake amma na fi son Nana akan yaron shi yasa na aikata hakan"tsawa ya daka ma ta"fitar min a gida munafuka mai fuska biyu"cikin sanyin jiki ta wuce na bita da sauri"wallahi sai dai mu fita tare amma bazaki fita a gidannan ba"tsayawa ta yi"Nana ni ce fa kashe gudan jinin ki ba ki da maƙiyiyya sama da ni","nifa ki daina faɗar haka dan ban yarda in ma kin kashe ai ɗanki ne"yanda haƙiƙan ce yasa aka fuskaci ashe dama lau na ke na warke daga wannan ciwon sanadin hautsinin da ake yasa ba wanda ya kula hakan har shi kuwa,duk yadda na yi ita sai da ta wuce ba jimawa ta fito da ƙaramar jaka da jakar ta ta hannu ta wuce tana ɗaga min hannu,wani irin mahaukacin kuka na saki na faɗi a wurin da gudu na tashi nai ɓangaren na mu na ɗakko hijabi da jaka ta na fito ina kuka tare ni sukai duk yanda muje da kowa na gidan naƙi amma naƙi jin maganar Baffa da yanzu ya tsinkayi abin ya fara min magana na zaro wuƙa nakai kan wuyana"duk wanda ya matso saina kashe kaina har Habib mai magana ban kula ba na fita a gidan kan a kawo inda na ke na hau ɗan sahu mota Babban Yaya ya shiga ya biyo mu ina kallon sa amma saida nasa muka ɓace ma sa gidan Umma na nufa dama Habu ba ya ƙasar bare yasan ina gidan faɗa ma ta komai na yi nan ta fara min faɗa shiru na yi iba kallon ta"in baki shiru ba nima zan shiga duniya"shirun ta yi ita da Baban suka shiga bina da nasiha amma na ƙi ji,duk inda zasu duba ina nake sun duba amma ba nan cikin ƙanƙanin lokaci gidan suka shiga tashin hankali ni kuma ina gidan Umma ko ruwa na kasa sha.
Gida Aunty Hajara ta wuce ilai kuwa anan ma kaca kaca suka ma ta suka faɗa ma ta asalin ta ba ta damu ba ta fito ta ɗau wayarta ta kira wata ƙawar ta sukai magana sannan ta wuce gidan ƙawar ta ta anan ta kwana washegari ta hau jirgi tabar ƙasar.
*EGYPT*
Tun a washegarin ranar ta sauka taxi ta shiga zuwa wata babbar unguwa a ƙofar wani gida ta sauka ta danna ƙararrawa sallama wani ƙaramin yaro kyakkyawa shi ya buɗe da sauri ya faɗa jikinta"Maama"rungume shi ta yi itama"oyoyo My Blood"ta ɗaga shi sama wata farar mata ce ta ƙaraso wajen tana dariya"tun jiya dama yake kiran ki har zafi jikin shi ya yi"shigowa ta yi ganin ta ba jaka ta ce"Ƙawata ina kuma kaya ababen tafiya",murmushi ta yi tana shafa kansa"ba zama nazo yi ba zan ɗauki AL'AMEEN na mayarwa iyayen sa dama na faɗa miki watarana zai koma",murmushi ta yi"gaskiya ne ƙawata kin cika jaruma wadda za a yaba miki amma sai gobe zaki wuce ko","a a jirgin dare zan bi na riga na shigar tun kan na taho","to shike nan muje ki huta"a ranar matar ta haɗa ma ta komai na yaron zuwa dare ta kaisu airport harda hawayen ta ta rabu yaron da take matuƙar so.
Washegari da safe ta sauka a gidan ta waɗanda suke cikin takardun nan saida ta huta yaron ya yi bacci sannan ta shirya shi shigar magaruba ta nufo gida.
Tunda nabar gidan komai ya dame aka rasa kan Babban Yaya, mamakin yanayin abin kamar wasan kwaikwayo ake,a gidan Umma ma ta gaji da faɗan ta yi shiru amma da daddare kasa runtsawa na yi kar kuyi zaton tunanin miji nake ko halin da yake ciki,ina ba wannnan ni tunanin kishiya na ke da fargabar ko a wane hali take.
HHHHHHhhh
Su Hajiya Fulera kuwa komai ya musu dai dai amma me ta biyo dare asalin ɗakin ta ba kowa saboda kayan ta bincike ko ina tayi ba waɗannan takardu babbar mahaukaciya ta zama haka ta koma ga ɗan uwanta shima haukar ta kusa saka shi dan abin ya girgiza shi haka ma ƴaƴan sa da suka sha alƙawura ba yanda suka iya haka suka zauna suna jimami ita kuwa uwar gayyar sai surutai take.
A ƙofar gida ta tsaya ta sauke mai kayan sa shi dai sai bin ta da kallo yake dan baya gane me take niyar yi sunkuyawa ta yi a gaban sa"ka t ya cije leɓen ƙasa"sunana Al'ameen ɗan Habeb da Nana Kawuna sunan sa Habeb Aunty na sunan ta Khadija Kaka ta sunan Halima Kaka na sunan sa Haruna",jinjina ta masa a ranta tana cewa"in baka iya magana ba ai ba ace Nana ce ta haifeka ba,gefe ta laɓe"ƙwanƙwasa ka cewa megadi wajen Habeb kazo in ku ka haɗu saika basa wannan takardar",hakan kuwa ya yi megadin yana ganin sa jikin sa ya fara rawa kayan ya fito ya kwasa ya sa yaron a gaba har cikin gida duk suna falo kowa ya yi tagumi Babban Yaya yana kan kujera a kwance me gadin ya yi sallama yaron na bayan sa kayan ya shigo dasu yana faɗin Alhaji Habeb ga baƙo ka yi"kowa juyowa ya yi Baffa yana cewa"ina baƙon"dan yanayin akwatinan kana gani kasan na yaro ne,juyawa ya yi yaga bai shigo ba labulen ya ɗaga ya kamo hannun sa ya shigo da shi,wani irin tashi tsaye kowa ya yi yana dafe ƙirji dan kana ganin yaron basai ka tambaya ba,shima kallon su ya shiga yi yana murmushi kai kace Nana ce tana ƙarama Baffa ne ya matso inda ya ke"yaro waye kai?",ɗan murmushi ya yi ya sosa wuya kawai Aunty Mama ta kwashe da dariya"ka daina tambaya fa Baffa wannan ɗan Nana ne kenan dama bai mutu ba to ya akai haka",ƴar dariya Baffa ya yi"na sa ni Halima bari na ƙara yarda tukunna,ina jinka yaro",nu na shi yaron ya yi"Ni sunana HABEB amma ana ce min AL'AMEEN kai ne Haruna?",ya faɗa yana ɗora hannu a jikin sa,dariyar da Baffa bai taɓa yi ba ya sa ki"eh ni ne kasan ni ne?",kai ya kaɗa"nasan sunan ka dai kuma nasan sunan Baba na da Mama na amma Babbar Mama ma sunan ta HAJARA"wani irin lumshe ido Babban Yaya yana juya kai da sauri ya tashi ko takan yaron bai ba ya fita da gudu amma ina tabar ƙofar gidan tambaya ya yi aka faɗa ma sa lallai ta shigo da mota amma ta fita daga layin,a wajen ya zauna ya rasa ina zaisa ransa ina ma ya saurari Nana da baiyi wannan ɗanyen aikin ba yanzu ina zai kai wannan abin kunyar,cikin lokaci ƙalilan ɓangaren su Mama ya cika da ƴan gidan ansa yaron agaba amma fa duk wanda ya tambaye shi yana da amsa sai dai baiga Baban nasa ba amma ya yi shiru bai sa ni ba ko baya nan ne kamar daga sama Habeb ya shigo layin hasko mota da ya yi ne yagan sa zaune a waje parking ya yi ya fito zuwa inda yake"Yaya lafiya me ka ke anan?",juya kai ya yi"Habeb yaron nan bai mutu ba ashe yana nan Hajara ta ɓoye shi ban san dalilin ta nayin hakan ba nayi kuskure Babba yau gashi ba bu ita ba bu Nanan",lumshe ido ya yi"naji taso mu koma ciki kamin musan ya zamuyi"da ƙyar ya shawo kan sa suka loma ciki.
A falon ma zama ya yi kawai yana kallon yaron wanda da ga ni kasan yaji gata da hutu wato kenan duk wata tafiyar da Hajara ke yi sarin turare ba wani sari da take in ma tana yi to akwai me ma ta duk yadda akai tana zuwa inda ta ɓoye wannan yaron ne a gaskiya ya cika wawa a shekara biyar ace be taɓa bincikar ina take zuwa ba,shima yaron ƙare mai kallo ya shiga yi yana kuma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 32