Share this page
a tsorace nake wani irin ɓacin rai da tausayi ne ya taso masa bargo yaja ya lulluɓe ni ya zauna yana shafa kaina lumshe ido na yi amma me kamar saukar aradu naji muryar wata tana ihu"sannu bawan mace to ina jiranka kazo ka wani tare anan",ɗago kai ya yi yana ma ta wani bahagon kallo"nazo na miki me ai ke da ni sai in Nana warkewa ta yi",cikin magana da ƙarfi tace"inka isa shegiya nake Habib ada da batanan ma baka kula ni ba shine yanzu ma bazaka kula ni ba",a fusace na watsar da bargon na tashi tsaye akan gadon idanuwa na na watsa ma ta"muguwa muguwa me ihu kawai"saurin shiru ta yi aranta tana cewa'wai wannan yarinyar me take nufi ne kar dai ta manta kowa banda ni',dirowa nayi nayo kanta ya taso ya riƙe ni a jikinsa na kwanta"muguwa muguwa"kaina ya shiga shafawa yana"shiiiiii"hanya ya nuna ma ta jiki a saluɓe ta fita amma ranta kamar ana zuba wuta,da dabara ya jani ya kwantar yana min addu a,rufe ido na yi ba jimawa na yi bacci bai bi takan ta ba kawai ya kwanta a bayana amma bai kai ko hannun sa jikina ba,asubar fari dama yake tashi yanzunma hakan ne amma bai tashe ni ba sai bayan sallar asuba shi ya koya min na yi,sannan na kwanta a wurin can na miƙe ina waige waige na dafe cikina,tasowa ya yi inda nake"me ne ne abinci ko",kai na kaɗa toilet ya kaini"kin iya wanka"kaina na ɗaga masa fita ya yi wai ya barni inyi wanka wani abu na ga ni yana lilo na janyo shi na matsa saiga ruwa dariya na shiga yi na fara fesawa jikina ina tsalle ji ya yi shirun ya yi yawa ya buɗe ya shigo baki ya dafe ganin yanda nawa banɗakin wanka nawa kaina jalaf har kayan jikina,ƙarasowa ya yi ya karɓa abin Allah yaso ba ruwan sanyi ba ne kuma ba na zafi ba ne,tsayawa ya yi a gabana yana kallo na kayan sun manne min a jiki kauda kansa ya yi sannan ya fara zare min kayan saida ya tuɓe ni tass sannan ya kunnata ya fara zuba min ruwan da harna ɓata rai dan ya ƙwace ina wasa na da kansa yamin wanka sannan ya naɗo ni a babban towel mai ya shafa min sannan yasa min doguwar riga mai kyau da gyalenta hannuna ya kama muka fito me ihu da wata na gani ban ko kalleta ba shima haka saida ya kaini ɗayan gidan sannan ya taho ya barni can da yake ina son matar ban ma ta kuka ba sai dai duk inda ta gilma ina bin ta tun tana in zauna har ta barni kome nayi kuma ta yi dariya da mutane da yawa a gidan kuma suna ta jana jikin su wasu na kula su wasu ba na kula su ba amma sunji daɗin yadda na yarda dasu bana musu iskancin nawa. Koda ya koma faɗa sukai ya mata tas sannan ya shirya ya fita Habu ne yazo yana tambayarsa ƙanwarsa yace tana ina Umma dariya ya yi"ai Umma da Baba jiya kamar marayu haka suka zama","Allah sarki badan Nana nada aure ba ai da bar muku ita zanyi","ba komai Oga zamu je wajen likitan ko dan na masa magana jiya","ok to muje ina Habib dan ya riga ni shigowa","ban ganshi ba ina ga yana hanyar fita"," muje in mun ganshi saimu wuce kawai",tare duk suka je anan likitan ya basu file ɗin shi kuma ya kira wanda zai india sannan aka tura masa detail ɗin yace in ya duba zai kira shi sallama sukai da likitan sannan su wuce company. A hannun mutanen gidan na wuni suna kula da ni komai su ba ni suce naci baya la asar ya dawo nan ya shigo kai tsaye ina kwance a falo kaina ba ɗan kwali wata da naji suna Ruma ita tamin sai wa ta Amina naji ana ce mata mai jego da ita muka fi shiri dan nama take ta bani ina ci ita kuma wata tsohuwa bini bini ta kawo wani abu mai duhu a leda tace wai na shanye ina sha ne kawai saboda ina ƙaunar ta bansan dalili ba,yana shigowa na ta shi da gudu na faɗa jikin shi,cikin wani irin farin ciki ya rungume ni"Nana ta",ɗago kaina na yi na kama hannun sa na kai shi wurin me jaririn nan nu na ta nayi"ina son wannan"da sauri ta miƙe ta rungumeni"ai da haka duk zaki so mu ƴar uwa dukkan nu dangin ki ne",sauran da ta nu na nakalla sannan na Habib,ƙura masa ido nayi sosai sai naji juwa da sauri ya riƙe ni"ki daina zafafa tunani zaki shiga wata matsalar"zaunar da ni ya yi aka kawo ruwa ya ba ni nasha sannan ya kalli Habib"ɗan uwa tafiya fa bata ganka ba da alama kai take son tunawa anya kuwa zaka tafi",matsowa ya yi ya dafa shi"ba inda zani ɗan uwa nayi magana an ban wata shida ne dama kuma yanzu wata na uku"tashi ya yi ya rungume shi ni kuma na zuba musu ido,janyewa na yi ina kallon me jaririn nan sannan na nu na ma ta su"su waye waɗannan?",matsowa ta yi ta kama hannuna"waɗannan ƴan uwa ne na jini wannan shi yayan wannan kuma shine mijinki","miji"na mai maita"kai ta kaɗa taja baya ta ɗakko yaron ta ta ɗora min a jiki"shi wannan yaron kina so?",da sauri na kaɗa kai"to nima ina da miji shi yasa na same shi",riƙe ɗan nayi sannan na yi dariya na tashi na kai masa yaron"kana so kaima",cikin murmushi ya kaɗa kai"ina so sosai",a bazata suka ji na ce"kace ta bamu tunda kai ne miji",ba shiri suka kwashe da dariya dan sun gane me zan faɗa,wa ta ƴar babba ta taso ta karɓi jaririn tana dariya"ci kwalar mijinki yau ɗin nan ya nemo miki naki",da sauri na kalle ta ina girgiza kai,itama kai da girgiza sai kawai na kwashe da dariya naje na kama hannun shi zuwa hanyar fita,juyowa ya yi ya kalle su suka kwashe da dariya kai ya kaɗa"kun san fa halinta ba tun yau ba bata iya naci ba kuma kun san matsalar da take ciki",wadda tai maganar ɗazu ce ta ƙaraso"karka damu Bross ai wannan ba matsala bace a ko da yaushe tana iya kaucewa kuma wannan halin da take ciki in kana nuna ma ta soyayya shine zata maƙale ma ka bazata yarda da kowa ba sai kai",haka ne suka haɗa baki suna faɗa,baice ƙala ba yaja hannuna yana samin hijabin da suka bashi muka fito ban kula kowa ba ya ɗauki hanyar da muka zo ɗazu. Tun daga wajen part ɗin ka ke jin tashin kiɗa ina ga ka shiga ciki kunne na nake dafewa sai ya tsaya yana canja hanyar daga shiga nan ya nufi wata hanyar wani ƙaton gini ya isa an gewaye shi da shuke shuke wurin a gyare yake tsaf sai ƙamshin flowers ke tashi ƙofar shiga ya buɗe yana riƙe da ni muka shiga har tsakiyar falon bin ko ina kallo na shiga yi jiri nake ji sai na daure a kan kujera ya zaunar da ni yana sunkuyawa a gabana hannuwana ya riƙe"ki zauna anan kar kije ko ina bari na kunna miki kallo amma ba a tv ba kar su baki tsoro zanje na ɗakko miki kayan ki mu kwanan mu anan ko abar mai ihu ita kaɗai",da sauri na girgiza kai ina dariya ya tashi ya ɗakko laptop ya kunan kallo ya ajen sannan ya fita bai jima da fita ba abin da ya kunna ya mutu dama na ita dannan wa agidan Umma Habu yana da ita yana bani na danna sake kunna wani nayi bai min ba na canja haka naita kunne kunne wata ƙofa na gani a buɗe tashi na yi na shiga ɗakin bugawa kaina ya yi wani hoto na gani ana min murmushi ga hoton na isa ina kai hannu sai ya ɓace ya ƙara komawa wani bangon bin sa na yi haka yay tamin ni kuma sai na maida abin wasa wata laptop ɗin na gani tayi datti ɗakkowa na yi"bari na kunna wannan waccan ba kallo a ciki",da kaina na kunna sai wani vedio ya fara ni ce da wa ni mutum na sunkuyar da kaina shi kuma yana murmushi sai ya fara magana"Nana",da sauri naji cikin kaina ya amsa nan da nan naji wani irin zafi ya rufe min jiki"kalle ni mana Nana haba uwa ta",da sauri na kalli laptop ɗin"Abba" naji bakina ya faɗa miƙewa nayi da hanzari kaina yana juyawa ina kallon inda nake cike da mamaki na kalli kaina ba kayan da nasan ni dasu ba ne zama na yi na jawo laptop"Abba Abba"na faɗa ina fashewa da kuka na tuna komai yanzu cigaba da kallon na yi ina gyaɗa kai kamar a sannan yake magana da ni"Abba maganar ka ta zama gaskiya gashi har losing memory na yi"sai kuma na yi murmushi Allah sarki Umma da Habu duk na tuna komai tashi na yi na maida laptop ɗin zan fito a ɗakin cikin ɗoki sai naji a cikin an ce"ke saiki nunawa mutane kin warke ai wannan wa ta dama da hanya Allah ya baki danki cikawa Abba alƙawarin sa"cak na tsaya ina faɗin haka ne fa amma za a sha iskan ci"sai na kwashe da dariya na koma inda nake na kunna abin da ya kunnan na cigaba da kallo sai nishaɗi nake ji a cikin kaina ko ina mutanen Maroco Allah dai yasa jakin can bai kashe Aisha ba dan bashi da imani motsi na jiyo za a shigo nai ma za na tuɓe rigata daga ni sai bra na kwanta ina kulle ido nai kamar na ga ji na yi bacci ne dan yafi awa biyu da fita yanzu ma kiran sallah ake,da kaya da yawa ya shigo teddy ɗima ɗima kamar mutum ga ƴar tsana ƙatuwa mai baho wata ƙatuwar dariya ce tazo min nai saurin haɗiyewa wai ɗimemiya da ni aka kawo wa wannan abubuwan wato dai na zama yarinyar da gaske ake nufi ai kuwa zaku ga aikin yarinta kaca kaca musamman mai ihu,aje kayan ya yi ya juyo gareni da mamaki ya kalleni ya ganni a tuɓe amma ban zare rigar ba da dabara ya mayar min ya miƙe ya shiga ciki ya yo alwala ya kuma fita ina kallon sa ƙofar ya kulle da key sannan ya wuce,buɗe ido na yi ina tashi zune alwala nayo nai sallah saina kwanta a wurin har akai isha ina ta tunane tunanen abubuwan da suka faru da iri wuyar da nasha tashi na yi nai sallah sai na tume kayana duka bra da bomshort kawai na bari na kwanta a ƙasan na ɗago ƙirjina sama dama brar ta ƴan gayu ce mai kyau bawai ɓoye su take ba rabi a ciki rabi a waje suke ɗai ɗai nayi ina ta nishi ina riƙe mara,"wohoho duniya"na kwashe da dariya. 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 BABAN YAYA Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 36 Tun daga bakin ƙofa ya hango ni da azama ya ƙaraso kaina tattaro ni ya yi zuwa jikinsa nan yaji wani irin ɗumi ya ratsa shi lumshe ido ya yi ni kuma namai gwalo ina ganin zai buɗe na ƙara mannewa a jikin sa ina mutsu mutsu riƙe ni ya yi yana magana da ƙyar"me ne ne Nana saurin tashi na yi zaune na haɗa hannuna namai alamar jijjigar yaro,murmushi ya yi"shifa yaron nan da ki ke so ba haka ake samun shi ba"da sauri na ɗaga kai"wato kin sa ni kenan"ƙara ɗaga kai na yi na ƙara komawa jikin sa,kasa jure abin da nake masa ya yi ya juyo da kaina ya ɗora bakin sa kan nawa lumshe ido na yi ina jin wani irin da ɗi har cikin raina yau na ƙara dawowa hannun mijina hannun sa ne ya fara yawo a jikina yana shafa duk inda yaci karo dashi,sakin jikina na yi sosai ba wani fulako muka darji amarcin da bamu taɓa yin irin sa ba,da gasken gaske na basa mamaki ya zata zan masa raki ganin yanda na koma komai kuka amma sai yaga aksasin haka da kansa ya min wanka yazo ya kwantar da ni yana ta lallaɓa ta ni kuma ina narke masa a jiki ga bamai riga a cikin tudun ƙirjina da yake ji duk sai ya ruɗe jikin sa har rawa yake kaina ya shiga shafawa yana control kansa dan kar ya cutar da ni tunda ba lafiyar kai gare ni ba,ban damu ba nai bacci na bar shi da aikin jijjiga ta yana sumbatar gashi na a hankali ya fara magana shi ɗaya"Allah ka yafe min amma a kan ki kawai Nana nake jin daɗin rayuwar aure nake cikakkiyar gamsuwa"shi kaɗai ya yi murmishi ya tuna a yadda ya tsinci kansa yau,shima ba wani jamawa ya yi bacci,rana ta fara ɗagawa sannan na buɗe ido cikin farin ciki wai na baro waccan uƙubar ba tare da sa ni na ba Allah na gode ma,juyawa na yi ina kallon kyakkyawar fuskar sa da ta yi shar gashin da ya ta ra ya yi masa sai ya zama kamar ɗan Pakistan a hankali na ɗora hannuna akan gashin kansa na shafa a hankali ina murmushi,ban sa ni ba ya buɗe ido yana bina da kallo idanuwan sa ne sauka zuwa wuyana ya bi jikina da kallo da sauri na kalli kaina nai ma za na kifa a kansa ina dariya ƙasa ƙasa bayana ya shafa"yadai kina kallo na ko kin san ni ne"dariya ce ta kamani amma na maza na kaɗa kai alamar ban san shi ba,"zaki san ni a hankali ko Maman Baby",kai na ɗaga ina dariya a sakaye,kaina ya ɗago"zo muje muyi wanka zan fita da wuri ina da shigar kaya yau"kai na ɗaga ya fito a bargon ya sunkuyo ya ɗauke ni cak a wankan ma sai lallaɓani ake kamar wanda yake taɓa ƙwai,Allah sarki wato baka gane me son ka sai wata sakayayyar ƙaddara ta sameka musamman ma ta baƙin ciki dan baka gane maƙiyan ka dan abib farin ciki ya sameka,shirin ma da kansa yake min yana yi yana nasa Allah sarki sai abin kuma ya koma ban tausayi dan kana gani kasan sauri yakr ga wayar sa na ta ringing kaya na ya rage min shi kuma yana ɗaura agogo tashi na yi naje ta bayan sa na tsaya,juyowa ya yi yana hannayena"sorry zo na ƙarasa miki shirin ki kinji",kau na kaɗa na nu a masa kayan sannan na nu na kai na sai na nuna hanya,murmushi ya yi"kina nufin zaki sa kayan sannan kibtafi wurin su Mama",kai na ɗaga ina mai jinjina rungume ni ya yi yana sumbatar kaina sannan ya sake ni yana tallabo fuskata"please kar ki kuka in kinga ba dawo ba da wuri aikina nada yawa"kai nabɗaga ina mai bye shima haka har ya buɗe ƙofar ya fita juyawa nayi na zauna ina shafa cikina hakanan nake jin shauƙin shafa cikin da nake na jima a haka sannan nasa kayan na gyare ko ina na ɓangaren sannan nasa hijabi na fito ban nufi wurin su Mama ba sai na shige wajen Hajara tana falo tana break na shiga,tana gani na ta miƙe tana bina da kallo wajen ta na nufa ina nuna ma ta kwanon abincin cikin mamaki take dubana"zaki ci ne?",kai na ɗaga saita kama hannuna ta zaunar da ni ta miƙo min abin cin karɓa nayi na nuna ma ta cup na tea"Nafi miƙomin wani cup ɗin"da sauri da ta kawo ma ta shaga haɗan tea yadda nake yi sannan ta miƴomin karɓa na yi zansha naji zafi sosai ajewa nayi na kamo hannun ta yatsun ta na kama na tsoma a ciki wani ihu ta zun duma da sauri na toshe kenne na cikin masifa kamar zata dake ni tace"dan ubanki wa yace miki haka ake abu na zafi shegiya kina ma da juyayyar kwanyar ba zaki daina mugunta ba",tashi na yi na je ma ta abincin na ma ta gwalo"mai ihu mai ihu kawai"hanya ta nu nan"fita anan shegiya gadon mugunta"gwalo na ƙara ma ta tai min banza ta cigaba da kara hannunta jikin fankar ƙasa ga ruwan sanyi an kawo ma ta tana tsoma hannun,fita na yi na tsaya a wajen naita dariya"da wannan damar zanta gasa ki wallahi kuma kece shegiya",jin motsi nai ma za nabar wurin ina tafe a hanya duk wanda ya min magana bana kula shi har na isa gida Aunty Mama na hango a falo ita da Mama da gudu na shiga na faɗa kanta da sauri da saki ajiyar zuciya"Nana wa ya biyo ki?",kai na kaɗa ina kwantar da kaina a kafaɗar ta dafa ni naji anyi na ɗago Mama ce idon ta fal da hawaye ya yin da na Aunty Mama ke zuba nima haka muryar ta na rawa tace"zaki ci abinci?",kai na ɗaga ina kama hannunta a raina nace"ku daina kuka ina jin ba daɗi da da hali dana nuna muku na warke,kwanon kusa da ita ta miƙo min na karɓa a hankali nake cin chips ɗin sannan aka ban tea na sha muna haka a Baffa ya shigo tashi na yi na tafi wurin sa dariya ya yi ya kama hannuna"Nana zaki bi ni ne gidan Iyyo zani"kai na ɗaga murmushi ya yi ya ja ni muka fita su kuma suka bimu da kallo,fashewa da kuka Aunty Mama ta yi"duk mai hannu a cutar da yarinyar nan Allah ka watsa rayuwar sa mugwaye kawai ace mutum iyayen sa ma bai sa ni ba",dafa ta Mama ta yi"wannan ita ce ƙaddarar ta Halima insha Allahu zata koma kamar da"kai ta ɗaga ma ta tana go ge hawayen fuskar ta. Muna shiga falon Iyyo ta miƙe tana kama hannuna"ƴar nan sannu kinji an cuci rayuwar ki"wani irin kuka ne yazo min ganin kaf dangina suna sona har haka ashe anan wurin ta nai ta zama , ta shiga ɗaki na silale na fita,Gwaggo suna zaune da Ya Hadiza na shiga itama da sauri ta miƙe tana kallon bayana"waye ya rako ki Nana kar ki wani wajen fa",kai na kaɗa alamar ba kowa,zaunar da ni ta yi dai dai Ya Hadiza na goge hawayen fuskar ta ta ɗago da murmushi ta kalle ni"Nana kin tashi lafiya"kai na ɗaga ina ɗaga ma ta hannu kasa jurewa ta yi ta tashi ta shige ɗaki tana fashewa da kuka Gwaggon ma haka gefe da gefe na kalla na kalli Gwaggo"ki daina kuka Gwaggo nafa warke"saurin kallona ta yi sai kuma ta dawo in da nake tana riƙe ni"kin warke fa ki ka ce","eh mana ke ba Gwaggo Asama'u bace ƙanwar Babana",cikin murna zati magana na toshe ma ta baki"amma ai ke kaɗai na nunawa na warke a kwai aiki a gabana shi yasa ban nuna na warke ba kiyi shiru na baki wani labari amma karki faɗawa kowa sai dai zaki ta ya ni kin san ƙwaƙwalwar yaro tunanin ta ba kamar ta manya bace kuma kome nake na bansan kowa ba kina taya ni a ban sa ni ɗin ba","to shike nan Nana zo mu koma ɗaki kar wani yaji mu",a ɗakin ma saida ta kulle ƙofa sannan ta zo in da nake ta zauna"ina jinki Nana me ya faru"...munfi awa biyu ina bata labarin komai tsabar tausayin Abba saida ta fashe da kuka"amma mutane ƴan iska ne ina ganin ina da san zuciya da son abin duniya ashe akwai kakanni na ki kwantar da hankalin ki ƴata insha Allahu burin ki zai cika Habib ƙarami za ki samu sai ki a sannu yanda zai gane kin warke shi kaɗai ne zai iya ta ya ki kiyi komai ba sanin kowa kin san Yayan ku shi yana sa ni tawatsima za ai kuma wasu zasu iya wanke kansu gwara ai mai dumu dumu","yauwa Gwaggota nagode ki maida ni wurin su Mama",tashi ta yi muka fito da kanta ta maida ni sai sannan hankalin su ya kwanta an sun dudduba basu ganni ba,bacci na wuni yi ranar sai yamma sannan Aunty Mama tasa ni na yi wanka tai min kwalliya na yi kyau ina zaune a kujerar mirrow ta kalle ni ta mudubin ta go ge idon ta kaina ta dafa"dan Allah ki tunani ƴata na kasa jurewa zuciya ta ciwo take"cikin razana na kalleta da gaske take dan ta rame har duhu ta yi,hannun ta na kama na ƙora saitin zuciyata saurin kallo na ta yi"kin san wace ni ne",kai na ɗaga tai ma za ta rungumeni"Allah yasa ki tuna baya duka",cikin ƙaramar murya nace"to kice zuciyar ki ta daina ciwo",ɗago ni ta yi ta tallabi fuskata"taji saƙon ki kuma zata daina ta jirayi ranar da za a ce kin zama Nana ta da",murmushi na yi a raina na ce'wannan Nanar ta ci uwar ta da ma iskancin da zatai duk sai kun gudu',kaya ta kawo min tasa min da kanta ta ɗaura min ɗankwali gyalen na ɗauka na nuna ma ta hanya"zaki gane kona raka ki dai",kai na ɗaga ina murmushi na nuna ma ta zan gane,tare muka fito saida taga na ƙule sannan ta koma ciki ɓangaren Abba na koma na kwaso duk kayan wasan jiya Hajiyar gidan na zaune da ƙwayen ta na shiga ban kulata ba na wuce su. Ɗaki na na shiga ina bin sa kallo sai naga ya yi ƙura cire hijabin nayi na fara tattara shi lokaci bamai yawa ba na shigar dashi hankalin shi na kwashe kayan shimfiɗar nayi na ɗakko sabon zanin gado nai shimfiɗu da shi in ka gani saika ɗauka gadon hotel ne ƴan fation kiran sallar magaruba akai ɓnaje nayi wanka da alwala nazo nai sallah har nai isha bai shigo ba dama yace zai daɗe riga mai kyau da ɗaukan hankali na saka na kwanta a ƙasa kamar marainiya,ji na yi an tsaya akaina na ɗago naga waye naganta cikin wasu kaya rabin ta tsirara wani kallo ta bi ni dashi kamar mai neman wani abu a jikina sannan ta durƙusa ganin na tashi zauna kunnena ta kama"dan ubanki yau kwana na ne kuma ki sa ni ba kina cutar mantuwa ba ko hauka ke tuburana bazan bar miki kwana na ba wai ma ke ɗin ba lafiyar ki lau ba anya ba iskancin ki ba ne kalli yadda ki ka gyara ɗaki saboda a haukar ma kinsan daɗin namiji",kafin ta gama rufe baki na shaƙeta da ƙarfin zuciya zaro ido ta yi ta fara ƙoƙari ƙwace kanta amma ta kasa idanuwana na zaro ma ta"dan ubanki ɗan iskan nan mai neman ƙanwar sa dan tsafi munafiki ya miki ƙarya ke kin yarda saina kashe ki muguwa kawai mai zuwa wurin boka ya ma ta wanka"da azama ta ture ni tana dafe wuyan ta cikin gigita da kiɗima take kallo na sai huci nake kamar zanci ba bu tashi ta yi tana nu na ni cikin magana da ƙyar ta ce"ni na sani ba losing memory ki kai ba hauka kawai ki ke"kanta nayi da gurna ni naji an riƙe ni ta baya saurin shiga hankalina na yi dan nasan waye juyowa na yi na faɗa jikinsa jikina na rawa rungume ni ya yi sosai ya yinda yake watsa ma ta wani kallo na razanar wa"me ki ke anan Hajara?",ya watso ma ta tambaya a firgice ta kalle shi saita mazr tana ɗan murza wuyanta"shigowa nace tazo taci abinci shine ta shaƙe ni",hararar ta ya yi"ita da jikinta yake kamar na jarirai ta ya taga ƙarfin shaƙe ki",miƙewa ta yi cike mamaki"wannan mai ƙashi ɗayan ce mai jikin jarirai to walllahi ina ga da baka zo ba kota kashe ni kota illata ni",ɗan murmushi ya yi"dan Alllah baki ji kunya ba kice wai Nana zata kashe ki kalle ki fa","na

Chapter 24 of 32