gyara ga abincin tarba iri iri dan yanzu bama layin tsakure duk da ada ɗinma ba tsakuren mukeba saidai wadatar yanzu tafi ta da Abba da Babban Yaya sun tsaya mana,mun taso a islamiya ina ta gaban ƙofar Iyyo ina masifa naji anja min hijabi a masifance na juyo naga wani wanda ya isa ne ya yi min haka"Baffffaaaaa"na ƙwala ihu ina ƙwaƙumeshi kunnensa ya toshe"wayyo autar mata zata fasawa Baffanta kunne,da gudu Ƙarami ya fito daga gidan Kawu Nuhu ya doso Baffa shima su Ya Ibrahim dake can gefe duk suka taso suma,nan da nan wajen ya cika ana masa sannu da zuwa Alhaji Baffa da Abba ne suka fito a gidan foster Baffa ya yi dan duk abinda ake bai san komai ba,da ƙyar yasamu ya janyo ƙafarsa ya matso kusa dasu,hannunsa har rawa yake ya taɓa Abba yaji mutum ne ko kuwa,tabbatar da shine yasashi yin ajiyar zuciya"Yaya Habibu dama kana raye",ya faɗa maganar na kasuwa,musabiha sukai nan suka koma ciki dama ƴan sannun sun watse anan wajen Iyyo auka zauna kamin suka shiga maida zance ya daɗe sannan na jashi muka shiga ciki,sannu da zuwa gun su Mama kamar bakisu zai yage haka muma kaf mun hanashi motsin kirki.
A ranar da Baffa ya dawo Gwaggo Asama'u tazo wajen Alhaji Baffa harda kukan munafircinta wai abata mukullin wannan gidan can hayarsu ya ƙare kuma basu da kuɗin biya,tausayi su ɗaya Baffa yaji ya bata mukullin saboda mijinta ne yana son mijinta danshi kamilin mutum ne kuma baya taɓa roƙo ko yazo ƙofar gidan dan abashi wani abu,ana bata ta tashi ta tafi ya dakatar da ita kora ma ta ya yi muddin dai dai darana ɗaya ta ɗagawa mijinta harshe ko kallon banza akan wannan gidan saiya tsine ma ta kuma ya ƙwace gidansa tunda ba nata bane bare ace mutuwa ya yi taci gadon gidan, washegari da daddare suka hau kwashe kaya gobarar titi inji Baba dama baya da kuɗin biyan wannan shekara a tunaninta tayi haka dan ta baƙanta masa amma batasan sauƙi ne ta nema masa ba,dama Fatsima duk ta wanke masa kayansa ta masa guga saida Ummansu tazo da niyar kwasar kayansa a wulaƙance sai tagansu a natse a sif dolenta tasa jaka ta kwashe batare da ta ɓata ba,duk fa bala'in Umma tana mutuƙar tsoron Baba saboda bai iya fushiba gashi masifar sonsa take,Hhhhhhhhhhh saboda Baba ma fa ba baya ba wajen kyau kawai dai yana da duhun fata bai kai ƴan uwanta haske ba fari sai Abba Habibu ga hutu ga jindaɗi da jikin yasamu shi yasa baya tsufa ma.
Tunda su Mama suka samu labarin dawowar Gwaggo Asama'u layin suka san da wata ƙasa inba hakaba ba yanda za'ayi ace ta dawo layin lokaci,Aunty Mama ce ta farawa Mama maganar nan tace ma ta"karki damu Halima yanzu fa ba da bace duk matar da ta taka mu mutaka muma ai ba ragowa yazu kingan mufa ciki rufin asiri bamu rasa komaiba wallahi kima cire komai a ranki in ta tako gidan nan munada basawa fa ko kin manta ne"da haka Aunty Mama ta ɗauri aniyar ba ragawa ma ta wannan karon kome zai faru ya faru.
Bayan wata shida:
Gini ya yi nisa an ɗau haramar gamawa shi yasa wannan satin sukayo gida iyasu banda masu cos su shekara zasuyi a ƙasar da suke.
Misalin taran dare ya shigo unguwar yana sanye da suit blue gashin kansa yasha gyara ya ƙara zama murjajjan mutum kana ganin kasan waye ya cika akirashi namijin gaske,Umma suna falo ana kallo ya ɗaga labulen da sallama,ihu suka fasa ga Babban Yaya ga Babban Yaya tun daga soro na shigo kenan naji ana ga Babban Yaya bokatin da aka aikoni dashi nasaki nan ya fashe fass ban lura ba ma na faɗa ɗakin da mugun gudu a bakin ƙofa yake duk da ban tabbatar ba a haka na daka tsalle na haye bayansa,ajiyar zuciya ya saki yana murmushi sai yanzu yasan ya shigo ƙasar sa dan Nana ce duniyarsa,"sannu da zuwa Babban Yaya","yauwa sannunku Maryam,Umma sannun ku da gida","am Habib ai na kasa magana ne dama kana hanya ?","wallahi kuwa Umma",duk wannan maganganun da yake fa yana tsaye ina bayansa yake yinsu,"saiki sakko ai tunda dai ya dawo adaina bacci da surutai saikace mai ƙwanƙwamai",Ya Aziza ke faɗa,ɗagowa nayi na murguɗe ma ta baki,sakko ya faɗa yana jawo ni na dire a gabansa murmushi ya yi"a lallai su Umma sun iya kiwo kalli yadda ki kai kumatu","kai Babban Yaya kwakwar manja fa nake ci shine nai kumari",dariya suka kwashe da ita,"Darling Yaya zo muje na nunawa su Mama kai harma Baffa kasan ya dawo",hanun nawa ya riƙe muka fito nan akaita shigowa da kayan da yazo dashi,koda mukaje canma sunsha mamaki sai wajen sha ɗaya mukarabu da ƙyar.
Washegarin zuwansa nan Alhaji Baffa yasa asanarwa na kusa dana nesa yana neman kowa nan da kwana uku,aikuwa saƙon ya iske kowa tun ana i gobe taro wasu suka fara sauka kai masha Allah aranar inka shigo unguwar saika ɗauka biki ake kowa ya taru har iyalan Abba gidan ya yi danƙam da mutane bayan sallar la'asar a tsakar gidan akayi shimfiɗu dama gidan Iyyo akwai girma da rushe shi za ayi da an gina Babban gida kowa zama ya yi aka nutsu nan Alhaji Baffa ya fito ya zauna kan farar Kujera iyayen maza ya kalla yana mumushi"Alhamdulillahi ina godiya ga Allah da yasa kaf ɗinku ku ka amsa kirana baƙi daga cikin mu ina fatan yanzu duk ansan juna madalla,na taraku anan ne dan inaɓ sanar muku zan tsayar da ranakun aure na waɗannan ƴaƴa dama nayi magana da manemin kowacce amma wasu ni na haɗa abuna da ƙwarin gwiwar bazasu bani kunya ba,Babban Yayanku duk kun sa ni yana neman aure can gefe wata ɗiya Hajara masha Allahu naje munyi magana dasu sunce kome muka yanke asanar musu tunda mu namu da yawa,kuma anyi sa a babba mahaifin yarinyar yayane ga Fulera to naji daɗin hakanma,bayan shi akwai Maryam babba tanada manemi dama tuni wato Saddi'q ɗin Baffanku Haruna sannan Ruma duk tuwona maina ne ita kuma Isma'il shi ya nema da bakinsa sannan Sumayya kowa yasani akwai ɓoyayyar alaƙa tsakanin ta da Hashim sai yanzu ya faɗa shima bawai cusa masa akai ba sai Dijama itama Haruna ya yi magana sai Aziza ƙanin mijin yayarta Amina shi yace yana so haka Ruƙayya itama tanada manemi tuni kuma an tsaida magana sai Kamal yace yana son ƴar maƙotanmu nan Maryam shima nayi magana sai Aminan Iro Sadisu yace yana so kuma na amsa itama ta amsa sai Abdul'aziz shima yanada wadda yake so shi,sauran Hadiza da Fatsima ku nake jira koba wannan taron ya kamata ku kawo min naku,ina sauraren ku me ku ka ce",Fatsima kallon Baba tayi nan ya ɗaga ma ta kai,da ƙyar ta zaƙulo kalmar "Baffa ina da shi yace ma da daddare zaizo kuyi magana","to shike nan ƴar albarka ina jiransa Hadiza fa" Umman su ce tayi magana"Baffa a barta ita sai nan gaba",da yake Baffa ba ɗan zafi bane sai yace"Allah ya kaimu da alkhairi,maganganu da tsare tsare sukai tayi har magaruba ta taho sannan akai addu'a aka tashi,matan kawu Iro na komawa gida bala'i ya tashi Umman su Amina tace ƴarta bazata auri faƙiri ba ana haɗa kowa da inda zai huta amma su sai ahaɗasu wanda kasuwar ma basan zuwa yake ba,Alhaji Baffa tazo ta gayawa yace tayi banza dasu danshi Baban nasu harda duka wai baisan suna soyayya ba da tuni ya raba su,kuji fa kamar wadda aka cikin maƙiya ɗanfa nashi ne tunda na ɗan uwasa ne uwa ɗaya uba ɗaya amma suke wannan abin sun manta aure haɗi ne na Allah ba ruwansa da gidan kuɗi kona talauci matar mutum kabarinsa.
Duk abinki a wurin Abba sai kin tafi da jari mai tsoka kwana uku bayan taron kowa ya watse saimu yamu kwana huɗu bayan tafiyar kowa Babban Yaya ya sauya min makaranta masha Allahu ina karatu sosai har Babban Yaya ya koma,lamuran gidan mu dai dai suke tafiya cike da farin ciki in kaga matsa sai a sauran gidajan dan gidan Kawu Iro dama kamar filin yaƙi yake.
Vote
Share &
Comments
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
chapter 1️⃣4️⃣
Bayan wata takwas:
Cikin taku nan na Babban Yaya kamar wani ɗan sarki yake fitowa acikin jirgi yasha baƙin yadi ɗinkin zamani hafjamfa sai baƙin cover shoe gashin nan sai ƙyalli yake yasha baƙin glass bayansa Ibrahim da Saddi'q ne sai Haruna sun murje duk sunyi kyau bakace su bane,Abba da kansa yazo ɗaukar su ya yi farin ciki ganin yanda ɗansa yazama, waɗanda suka rayu cikin kuɗi da hutu da gata ma basu kaishi ba kai ko rabinsa basu kai ba,cikin layinmu suka shigo dama layin yasha gyara hakama gidajan sun koma kalar na zamani ga tiles yasha, soron gidan ya shigo ban lura dashi ba naji muryarsa a kunnena,"ina zaki ki ke dube dube"kamar saukar ruwan sama naji muryar sa karma na juyo naga bashi bane yasa na juyo idona arufe,wani dam ƙirjinsa ya bashi ganin yanda wani kyau ya futa a fuskata gashi fuskar a murje ba rama,hannunsa ya ɗaga ya ɗora a fuskata shafa fuskar ya yi cikin nutsuwa a hankali na buɗe suka sauka ciki nasa da hanzari na faɗa jikinsa na fashe da kuka,bugun da zuciyarsa keyi ne ya sauya jin yadda jikina ya taɓa nashi cikin muryar mai sanyi ya fara magana"ya akai ne ki ke kuka",cikin shassheƙa nace"bakaine kaita cewa zaka dawo ba tun wancan watan amma kaƙi","am sorry Sweet Sis gani na dawo uzuri ne ya tare ni",ɗagowa nayi ina murmushi wanda ya kusa tarwatsa masa zuciya ya kira sunana bai sa ni ba amsawa nayi"kina yawo ko kina kula maza kiyi faɗa ahanya ko","wallahi Babban Yaya bana yi kuma ka tambaya kowa sai dai in anmin in tama mutum yana shigowa gidan Iyyo yofa zai gane bashi da wayo",murmushi ya yi yasan bana ƙarya shi yasa yake yadda da maganata,hannuna ya kama muka shiga ciki, ihu da murna ne ya fara tashi saima da sauran suka shigo farin ciki ya kama Umma ta rasa ina zata saka kanta ganin sun zama mutane,saida suka huta sukaci Abinci sannan aka fara gaishe gaishe.
Watansu guda da zuwa aka haɗa kayan lefe salo salo a gidan Iyyo amma na Babban Yaya hidimar na gidan Abba Hajiya Fulera ke komai amma fa tana tatsar kuɗi wurin Abba shi kuwa tilawa kawai yake wai lefe ake haɗawa nan,ranar daya haɗu aka kawo gidan Iyyo su Mama ne suka kai gidan an karrama su sosai kuma sunyi murna da wannan kaya dan abin fa ya ɗau hankali da yawa,dama duk kayan da za'a kai to da ranar auren suke tafiya wata uku masu zuwa,tunda ake maganar bikin Babban Yaya ban taɓa sa baki ba dan haushinme faɗa ma nake ji kuma shima baya firar dani sai dai fa a lefen can da aka kai kaɗan ne basu kaiba kayan da Abba yamin dan kaf kayana na sif Mama takwashe ta bayar wai sun min yawa hakama Babban Yaya kamar zai goyani yake min amma hakan bai hanashi ba jiya ya zane min jiki wai nayiwa Gwaggo Asama'u rashin kunya shike nan na daina masa magana in ma naganshi sauya hanya nake in yaga nayi hakan sai dai ya yi murmushi ya wuce shima.
Kawo kayan lefen Ya Fatsima ya ɗagawa Umma hankali sosai saboda kaya ne harda na hauka komai kamar za'a buɗe shago a gaskiya kayan sunyi amma ƴan gidan basu san angon ba itama sau ɗaya yake zuwa asati ba lallaima in taganshi a hanya ta gane shi ba.
Bacci nake hajaran majaran naji ƙamshin turaren Babban Yaya a hancina juyawa nayi naji na dunguri mutum buɗa ido nayi nagansa zaune kusa da ƙafafuwana,tashi nayi zan bar wurin ya riƙo hannuna ya jawo ni gabansa na tsaya,juyar da kaina nayi wai bazan kallesa ba lanƙwasa murya ya yi sosai"haba Darling Sis wannan horon ya isa haka mana kalli yanda na rame fa bana iya bacci bana iya cin abinci sabida kina fushi da ni,ki sassauta min haka mana tawan",murmushi nayi masa sannan na zauna kusa dashi,yana ganin hakan yasan na haƙura kenan,tun daga ranar muka shirya nan akaita mana dariya,ban damu ba amma fa ta ko ina Shirin biki ake har yazo yau mutanen gidan suka fara sauka washegari ƴan nesa suka fara sauka musamman dangin Umma ita mai aurar da mutum shida gaskiya amaren sunsha kyau sun ɗau gyara fa ba ƙarya haka Aunty Hajara Babban Yaya yasakar mata kuɗi sosai shi yasa take fantamawa ga kuma gatan da ake nuna ma ta a gidan su.
Yau kamu gidan ya cika da mutane ansha ankon atamfa da akayi ni ina nan duk na burkita kayana ina neman ɗankwali ban ganta ba Aunty Mama na kalla"Aunty Mama ina ɗankwalin atamfar ankona",kanta ta dafe tana tsaye jikin sif"ki duba cikin ledar kayan mana kinsan dai babu daidaike agidan nan bare aɗaukar miki ɗankwali ba",tana rufe baki na hangeshi can kan kaya ɗakkowa nayi na fito da sauri da Ya Amina na haɗu"ke me hankali zoki rufe wannan gashin in ba haka ba mutane su cinye shi",ɗan kwalin na ware na yafa sannan na fita,gidan Iyyo na shiga ta bayan Ya Hasiya na zagaya na fasa ma ta ihu a kunne,salati tayi tana kawo min wafta"wallahi Nana ciwan kai ce ke",wata mata ce a gefenta tace ma ta"ai Nana zama da ita sai mai hankali bama mai haƙuri ba","wallahi hakane ai mutanen nan dake tare da ita suna ƙoƙari",ni dai tunda na gudu ban kuma bi takansu ba inda za'ayi kamun na tafi ni kowa ma haushi yake bani,Ya Amina ce ta ganni ta ƙwala min kira zuwa nayi ina tura baki"ta Babban Yaya ya akai ne",kwaɓe fuska na ƙara yi "bashi nake ta nema ba tun jiya ban gansa ba",dariya ta ɓoye"kiyi haƙuri mana wurin baƙi yake tun jiya zai dawo ai ina ganinsa zan faɗa masa jininsa na nemasa",kai na kaɗa na fita a gidan,ina shiga gidanmu naga kowa na fara'a yana washe baki magana in an min saidai na harari mutum kawai,mamaki abin yake bawa kowa Mama ce kwwai ta girgiza kai takalli Aunty Mama"ga ƴarki can kishi zai kasheta",tana ɗago kai ta ganni na shige ɗakinta"bari kedai Dada kullum da zazzaɓin dare take kwana abin har mamaki yake bani","ya daina baki mace haka take indai tanason mutum taga wani zai raɓeshi","to ai shike nan bari naje na lallashi a bata","saiki ɗaura niyya kar ciwan zuciya ya kamata"dariya tayi "kai Dada"ina rizgar kuka ta shigo"ƴar Mama wa ya taɓaki ne",cikin kuka nace"ba Babban Yaya ba ne ya share ni dan zai yi aure","kai kai bai kyauta ba kam ungo waya ta ki kirashi"da sauri na ansa ita kuma ta fita,number sa na kira bugu ɗaya ya ɗaga"Assalamu alaikum Aunty",shiru nayi ina jan numfashi"Nana",rushewa nayi da kuka,muryarsa ya sanyaya"am so sorry Darling zaisha nasan lafina baƙi ne dani kinji amma gani nan zuwa",kashewa nayi ina goge hawayen fuskata.
*****
Daga can dama yana gidan da Abba ya bashi ya sauki baƙi shida su Abdallah da sauran da suka haɗu daga baya sai asalin abokan sa amma kamar ansan juna tuni yana wayar suna kallonsa yana saukewa suka fara masa dariya suna tsokanarsa wai amaryar ta matsu ne haka,kai ya girgiza''ba ita bace","kamar ya"har suna haɗa baki wajen faɗa"Ƙanwata ce","ƙanwa dai kuma ka ke wannan abin kamar wata matarka",tashi ya yi yana gyara agogon hannunsa"ai ba wai insha Allahu",Yusuf asalin abokinsa ne ya kallesu"ai shi wannan yana da wani buking ɗin bayan wannan amaryar to akwai wata",tafawa sukai cikin shaƙiyanci wani daga cikinsu yace"kaga kogin wayo wato bayan wannan tayi sanyi akwai wata me ɗumi kenan to wallahi ku tashi muje muganta",tashi sukai ya kallesu yana dariya"ku yanzu Nanar zaku gani yarinya ce fa","ko yau aka haifeta sai munga me kakewa wannan zumuɗin",murmushi ya yi ya wuce duk suka fito motocin suka shiga nan suka wuce unguwa su,idona a kulle naji ƙamshin turaren sa a kusa dani buɗe ido nayi mukai ido huɗu,baki na buntsura na juya mai baya,dawowa ya yi inda nake kallo ya durƙusa yana kama kunensa"afuwa Ruhina ba laifina bane",ƙara rushewa nayi da kuka na kifa kaina akan kafaɗarsa,wani abu me ɗaci ne yaji yana tsirga mai har cikinsa,da ƙyar ya haɗiye shi hannunsa yasa ya shiga shafar gashin kaina daya wargatse duk gyaran daya sha da haka nayi shiru,ɗago ni ya yi"tashi ki shirya ina kayanki ki saka mu fita",ajiyar zuciya nake na girgiza kaina"ban zuwa ko ina ka tafi wajen amaryarka bayan saboda hidimarta ka manta da ni",da sauri ya riƙo hannayena"kalle ni nan Nana",ɗaga kai nayi na kalleshi"bana jin ko mutuwa nayi tunda gawa najin komai tana ganin komai ace zan manta dake kuma kinsan dikkan mai hidima dole amasa uzuri ko,to ki daina wannan tunanin tashi kiyi abinda nace",tashi nayi na shiga cikin ɗakin Aunty Mama fuskata na wanko sannan na shafa mai da hoda kamar gaske les doguwar riga na ɗakko na saka sannan farin hijabi ƙarami nasa takalmi na fito,ajiyar zuciya ya yi ya miƙe yana kama hannuna muka fito mutane na kallon mu amma ba mai magana danshi ba fara'a ce dashi ba bare amai wasa dama dai acikin ƴan gidan ne,muna fitowa naga mutane a tsaitsaye da mamaki nake kallonsu nasan wasu abokan Babban Yaya ne amma bansan sauran ba,har wajen muka ƙarasa"to ƴan ganin ƙwaƙwaf gata",baki suka hangame Abdallah yace"wallahi kana da gaskiya nima yau nabi bayanka kuwa"dariya sukai nan na gaishesu,da fara'a sosai suka amsa min,jinjina ya musu"ya zaku koma ne ko kuma nan zaku zauna ni unguwa zamu",''ku dawo lafiya komawa ai munsan hanya malam","ok saikun ganni",motarsa muka shiga ban san ina zai kani ba sai gani nayi a wani ƙaton super market shiga mukai yace na ɗauki kome nake son ɗauka ba wata tantama naita jidar kayan banza har saida na fara dariya sannan ya saki nasa ran sai magaruba muka dawo gida sai mamaki suke wannan wane irin abu ne saidai kawai ayi dariya ni kuwa ko ajikina ,washegari ɗumbin jama'a suka shaida ɗaurin auran mutane daban daban anfi awa biyu sanan aka gama aka tashi kowanne ɓangare a unguwar kadan ka duba sha'ani ake angwaye keta shiga gidaje ana gaisawa dasu na Ya Fatsima ne suka shigo gidan anata musu maraba,gaishe she aka shiga anan aka nuna musu angon kamar akan idon Ya Hadiza wa zata gani saurayinta mai kuɗinnan wanda suka kai wajen malamai dan ya aureta shine ya auri Fatsima Bashir lallai akwai tashin hankali babba,wani luuu taji badan tayi ta maza ba da tuni ta faɗi a wurin ganin zasu tashi yasata fitowa sosai dan yaganta,ai kuwa dama ita yake raba idon gani sai gashi kuwa yana ɗago kai sunzo fita suka haɗa ido murmushin nan nasa mai kasheta ya ma ta sannan ya ƙarasa fita inta fahimci wannan murmushin yana sane kenan yazo ya auri ƴar uwarta dan bata tunanin Fatsima tasan Bashir sai daishi lin da biyu ya yi hakan,wani tunani tayi kawai tayi murmushi tana gyara zamanta a bakin gadon ɗakin da take kome ta ƙitsa kuma oho,gidan Kawu Rabilu suma taro ya yi taro haka gidan Umma ai nan ne cambar bikin sai gidanmu a gaskiya Ya Ruma ta wanku kamar yanda Ya Isma'il ya faɗa to yaga kala malam ga gyara ta ɗauka abinka da farar fata kalar fulɓen usul ba jaja amare ba ko jikin bliching,a wannan biki Alhaji Baffa da Baffa fa Abba sun hana bidi'a saidai da yamma aka shirya gagarumar walima wadda ta ƙawatar ko fatin baza suyi abinda akayi a wurin ba,sai bayan sallar isha sannan aka fara fitowa da amare ana sawa amota har aka fice dasu,ƙarfe tara saura sannan aka kawo matar Babban Yaya nan bayan mu dama Abba ya gina babban gida tunda yasan da zaman auren sa gidan nan ya yi kyau sosai suma sun cikashi da kaya na gani na faɗa,sun daɗe da kawota sannan suka baje sunata santin gidan ƴan uwanta marasa hankali sunata ma ta famfo karta ragawa duk wanda bai raga ma ta ba,abin mamaki anata hira bayan goma sai ƙafar Babban Yaya suka gani a cikin gidan,Ya Usainace da mamaki ta kalleshi"ango me kuma ka ke anan bayan kamata ya yi ace kana gidan amarya",hannun sa ya ciro a aljihu ya yafito ta "zo na faɗa miki dalili",ya ɗaga labulen ɗakin Aunty Mama ya shiga",saboda tsautsayi yasa ta biyo shin kuwa,zaune ta sameshi saman kujera itama ta zauna","inajinka Babban Yaya",in serios ya kalleta ya fara magana"Usaina har acikin zuciyata nai baƙin cikin da za'ace ɗakin matar da zan shiga yau ba Nana Aisha bace a yanzu nazo naganta ko zan sami sauƙin abinda nake ji acikin zuciyata,kuma koda naje inda take itama zata bar tarihin angon da daya tsallake amarya kamarta ya yi asarar daren farkonsa",yana kaiwa nan ya tashi fice a ɗakin yabar ma gidan gaba ɗaya,kasa motsi Ya Usaina tayi gumin goshinta ta share kenan abinda suka ɗauka wasa ashe gasken gaske ne yanzu Babban Yaya yafi son Nana da kowacce mace lallai abin ya shige wasa",dafata akai da sauri ta ɗago kanta taga Ya Hasiya ce,ajiyar zuciya tayi murmushi tayi"ki daina damun kanki wannan al'amarin yafi gaban tunanin mu dan gwarama ki cirewa kanki shakku ki kalli gabanki Nana ta Habib ce",dariya tayi "to Allah ya nunamin randa zanga ƴaƴansu","insha Allahu kuwa muje",nan suka wuce ɗakin da suka sauka dan kwanciya,ni kuwa ɓuya nayi a bayan gado dan kar ma naga shigowar shi wai shi mai mata har nayi bacci ban ma san ya shigo ba.
Vote
Share &
Comments
Û̬m̬̂m̬̂û̬ ŝ̬â̬d̬̂d̬̂î̬q̬̂
🌈🌈🌈
🌈🌈
🌈
Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments.
08146711395
chapter 1️⃣5️⃣
A cikin wannan daren bayan ɗaukar Ya Fatsima Ya Hadiza take faɗama Umman su kaf abinda ya faru,ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba kuma tayi dana sanin ko sau ɗaya batacewa Baban saurayin bazaizo ya gaisar da ita ba,rasa sukuni tayi tace taje ta kwanta ta barta da wannan abin ita tasan me zata shirya sai wannan aure ya mutu kuwa,duk abinda suke ƙullawa Baba na jinsu kawai ya yi murmushi sannan ya wuce ɗakinsa saboda yau yana jinsa sakayau kamar an ɗauke masa wani kaya akansa,gidan kowa ya yi kyau dan Abba ya yi ƙoƙari ya hana Alhaji Baffa ya yi komai wai miye amfanin kuɗin nasa in baiwa Alhaji Baffa amfani dasu ba,albarka sosai yay tasa masa.
******
Wurin Umma ya shiga nan ta haɗasu ta musu nasiha mai ratsa jiki sannan kowa ya fito ya kama hanyar gidansa,
Gidan Babban Yaya da maigadi shi yasa ya buɗe masa ya shiga,da addu'a ya buɗe ƙofar falon ya shiga ko ina fes amarya na zaune kujerar falo,sallama ya ma ta sannan ya ƙarasa inda take dai daita kansa ya yi ya saita muryarsa da ta cunkushe masa,"amarya amarya barka da warhaka",ɗan murmushi ya yi ganin yanda ta motsa alamar taji me yace,a kusa da ita ya zauna yana ɗaga mayafin"masha Allah kiyi kyau sosai",murmushi ta saki tana fari da ido"ai kafi ni kyau masoyina",baki ya kama"wuu wane ni Habibu nai dai dai da kyan ki","abar dai maganar nan","ok to mushiga ciki",da yanga da yauƙi ta miƙe tabi bayanshi kowa da ɗakinsa dama nata ya rakata sannan ya fito ya wuce nashi,kamar yadda ya saba haka ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 32