Share this page
shiba da nake zaman wurin ta indaɗe to kuwa zaki ta zama ke ɗaya ba bu ni saboda ba komai nata nakeso ba face itaɗin gabaɗayanta ni komai nata yamin amma in haɓaka kike so tayi ta zama kamar ke to kiban sati biyu kacal zata samu abinda kike so ta samu saiku jera",ya saki hannun nata ya fita ko ɗar baya ji na ya barni da ita,bayansa tabi da kallo bakin ta yaƙi rufuwa anan ta zauna jaɓar to wai me zatayi ne ma wannan yarinyar ya daina kulata tayi abubuwa da dama amma shiru amma bariki zata nuna masa ta yadda bai bazai iya tsallakewa ba zata nemi zaman lafiya na gangan da wannan zata gasani,wani mirmushi tayi ta miƙe wayarta ta ɗauka ta kira mai aikinta tasanar ma ta ta dawo tai ma za tazo ta gyara ma ta gida,kafin wani lokaci ta iso nan ta shiga gyaran sannan ta ma ta wanki harad pant sa bra dan abin kunya. Saida nasha baccina sannan na tashi ɗakin ba kowa dama tun jiya ya faɗa min zai ɗan fita da sassafe hakan yasa ban damu na tashi na fara gyara ɗakin sannan na biɗeshi da turaren wuta na shiga wanka ina fitowa mai nashafa da kwalliya kaɗan sannan nasa riga mai hannun best ko half best ɗin bansa ba na kwaso kwanukan na fito a sannan su kuma suna tsaye tana aiken mai aikin ta ta,wucewa nayi ina faɗin"Aunty Hajara barka da tashi",harara ta tayi"kyacemin barka da tashi mana tunda da fukafiki kika ganni","Allah baki haƙuri Aunty na ta kaina ina kwana to",na wuce kitchen ban aje kwanikan ba na wanke abuna na goge ina ganin inda ta warewa kayana wuri nai murmushi na aje nan sannan na ɗebo ruwan ɗumi a mug na fito,suna nan tsaye na wuce dining madara da ovaltine na gambaɗa aciki ko sugar bata samu wurin zama ba nazo na wuce su bina da kallo tayi sannan ta kalli ƴar aikin itama ni take kallo harara ta zuba ma ta"miye ki ke ma ta wannan kallon haka","Aunty wallahi yarinyar tana da kyau ta haɗu dayawa wannan namiji ya sameta ai zai huta dan hannu na fara taɓa jikinta zata haɓaka",wani kalar kallo ta ma ta"ita wannan jariyar abin a tsaye a bushe ita maza ke so dan sakarci","ba sakarci bane Aunty wannan a tsayen da ki ke gani maza shi suke so kuma wannan ƙanwar take ko da wuri zata mallake namiji da alama batasan komaiba kome ze ma ta yadda zatai in taji daɗi kuma gobe da kanta zata kawo kanta",wani gumi ne ya karyo ma ta ta zauna ba shiri da mamaki ta zauna a ƙasa"Aunty lafiya kuwa",kallonta tayi"wannan ba ƙanwata bace matar megidan ce",me aikin zabura tayi ta wara hannu"a kin gama Aunty wannan ƴar shilar kina me ki ka bari aka aurota kumanaka kawota nan cikin ɓangarenki duk girman gidan nan","ni nasa akawota nan dan na nuna ma ta manya bakalar yara bane",gudun karta ma ta rashin mutunci saita zuƙe maganarta ta koma"ai ku irinku daban ne Aunty musamman ma ke ki kalleki fa ai wannan zaki mallake mijinki ki korata ta fita ai dama in suka samu gidadawa shine zasu iya ƴwace musu mijin","hakane kuwa yanzu jeki kasuwar ki dawo",to tace sannan ta tashi ta fita amma maganar da tayi harga Allah ba ita tayi niyar faɗaba sai dai tayi kallo. A ɗakin ma zamana nayi na shanye abinda na haɗo sannan na fito na maida cup ɗin nazo zan wuce tasha gabana"matan aure masu miji nasan dai abin duk burga ne ƙofar bazata biyu ba dan da an bita da ba za'a yi wannan kaɗiri feren ba",gyara tsaiwata nayi"shi ya faɗa miki bai bita ba Hajiya to bari kiji wannan ta gaban naki wato ni kenan matar aure nake cikakka irinki ni da nake ma mai tsukakken jiki amma nasan kekam",banngama maganar ba ta kawo min danƙa na goce nai ɗaki da gudu ta biyoni kan tazo na rufe ina dariya bubbugawa ta shigayi"saina fasa wannan bakin na marasa kunya shegiya karuwar yarinya kawai",duk ina jinta amma nayi shiru ta gama masifarta tabar wurin,me aikin na kawo ma ta saƙon tace suyi girki haka ta zage sukai girkin amma shinkafa ce da miya sai coslow sai lemukan kwali ta kama ta cika dining,ban fitoba saida yunwa ta isheni tana ɗakinta na fito ban kula dining ɗin ba na wuce kichen ƙwai na soya mai yawa dan ba bread a gidan na kuma haɗa shayi shaf shaf na gudu ɗaki na cinye ƙwan du sannan na kwanta ba jimawa nayi bacci. 1pm ya shigo gidan da kaya niƙi niƙi a falon ya aje ya kuma fita ya shigo da sauran zama ya yi akujera yana furzar da iska mai ɗumi dan ya gaji sosai,Hajara ce ta fito ta ganshi cikin fara'a ta ƙaraso inda yake ta zauna"sannu da zuwa Habibe",wata sabuwa ya faɗa aransa wannan salon fa bai gwaleta ba sai ya amsa tana jujjuya kai tace"da alama ka shawo gajiya ga abinci can",ɗan murmushi ya yi"nagode kuwa amma bari nayi wanka",yana falar haka ya miƙe ya bar wurin zuwa ɗajina murɗawa ya yi ya shigo inata bacci murmushi ya yi ya wuce toilet wanka ya yi sannan ya fito kwanukan dana ci abinci ya kalla da sauri ya dafe kanshi ya manta ƴan sinadaran breakfast bai siyo ba,sanyin ruwa naji na bule ido idona a hankali na ganshi yana murmushi amma kansa ajiƙe da alama wanka ya yi,tashi nayi zaune na shige jikinsa"oyoyo Babban Yaya nayi kewarka",rungumeni ya yi"nima nayi kewarki ma za tashi ki watsa ruwa muje kici abinci",sakkowa nayi a gadon ian faɗin"to Babban Yaya",na shige toilet bin bayana ya yi da kallo ya girgiza kansa kawai. wankan ma ban tsaya nayi mai kyau ba na fito a gurguje na wuce ga mirrow na fara shafa mai duk yana kallona wallahi na manta yana ɗakin na cire towel ɗin harda yarwa na shafe jikina da mai na juyo zan je sif naganshi ƙurii yana kallona baki na hangame sannan na kalli kaina a wurin durƙusa ina dariya"Babban Yaya ka kallar min asirin jikina",tasowa ya yi yana dariya"to nawa zan biya amma sai na ƙara gani",ɗagowa nayi na kalleshi"zaka biya da gaske na miƙe ka kuma ganin bonus","eh mana million guda zan biya",wuf nayi na miƙe"iya wannan kallon a miliyan Babban Yaya to kullum zakana kalla sau goma sha",tsabar dariya saida ya zauna dan tabbas yaga zallar yarinta anan ma",wucewa nayi na ɗaura towel ɗin nima ina dariya sai yanzu na gane wayo yamin ya kalleni sadaka,anan na barshi na wuce sif wata blue body hog mai ƙaton wuya nasa da baƙin trequater na ɗaure gashina da ribom blue na juyo ina murmushi,tasowa ya yi"wow tawan ta haɗufa",yaban hannu muka tafa"ka shirya kaima to","saikin tayani",ni na ɗakko mai kayan yasa sun masa kyau sosai jeans da riga mara nauyi,najuya ya riƙoni yana nuna ƙirjina"waɗannan yara baza'a samusu tasu rigar ba",dariyace ta kamani amma na ƙwace jikina na matsa"ni a haka zan zauna",na faɗa ina maƙale kafaɗa"baki isaba kuwa"ya kawo min danƙa na fito da gudu ya biyo ni Aunty Hajara na zaune na wuceta na tsaya a kwiɓinta"Aunty Hajara ki masa magana yana barinsu su huta wai dole sai ya jasu sunyi girma kamar naki wai naki yake so ba nawa ba",da mamaki tana hararata tace"me kenan?",ba kunya na nuna ma ta ƙirjina,da sauri ta miƙe tsaye"zance ubanki in ki ka min karuwanci anan shegiyar yarinya kamar aljana kinƙi ki barni ko tunani nayi kin kanainaye mijin shine yanzu zaki biyo takaina kimin iskanci wato dai saikin faɗa min yana taɓawa ko",kai na kaɗa ina taɓe baki"jiya har ma cewa ya yi suna birgeshi musamman in yana kallonsu","innanillahi"ta faɗa tana zama jaɓar yayinda Babban Yaya ke bayanta yana dariya harda riƙe ciki,ni kuwa nayi mirsisi sai taɓa baki nake wai ni shagwaɓa. Ɗago kaina nayi zan ma ta magana tai saurin ɗaga min hannu"kina magana saina mareki",maida ta bakina nayi na sumkuyar da kai kamar wata tagari,tasowa ya yi yakama hannuna"zo muje kici abinci kin tsaya fitina",kamar wata ƴar ya ye haka na bishi zugwi zugwi yaja kujera ya zaunar dani sannan ya koma itama ya kamo hannunta yazo ya zaunar da ita dana ɗago kai saimu haɗa ido harara take watsamin ni kuma nayi iya dauriya na riƙe dariyar da ke cina,da kansa ya buɗe abincin ya fara zubawa kowa yana murmushi ina hangar naman kaza da coslow na ture abincin na janyo kwanon naman da coslow ɗin na fara ci ina zare ido tana kallona taƙi min magana danta lura danja ce ni kowacce magana ina da amsarta,saida naci na cinye sannan na harari kwanukan su naman kwanonsa na janye na faraci yamin banza saida na cinye sannan na miƙe na kwashe nata na zura da gudu ɗaki kamar zata ƙware tace"zoki ajemin ko mijin naki ya biyani gomanshi ke kuma na kamaki saina miki dakan sakwara",hannu kawai na ɗaga ma ta na shige ɗaki a ƙasa na zauna na faraci nafa ƙoshi tsabar neman magana ne yasa na ɗakko ma ta,kallonsa tayi"ka sa ni saika biyani namana ko in na kamata na daki abuna",wani hamagon kallo ya ma ta"wai Hajara bake ki ka ce zaki iya da Nana ba Nana kuna mutunci ma ya aka cika bari bakwayi nama kuma ai gashi nan a gidan ko ɗanye ki ke buƙata gashi nan inshi zaki ci",hararar sa ta yi"saboda ka maida ni mayya ko",ƙala baice ma ta ba ya gama ya tashi ya barta a wurin dan dama ita haka take akwai ci,ina nan zaune na wanko hannuna ya shigo fuskarsa na kalla nagansa a Babban Yaya na farko dana sa ni saina shiga hankalina,wucewa ya yi ya zauna abakin gado"zo nan Nana"jiki sanyaye na tashi naje a ƙasa na zauna na sunkuyar dakaina"gani"na faɗa murya ta na rawa"me yasa ki ke raina Hajara ko na taɓa gaya miki bana sonta ne",kai na kaɗa ina ƙaƙalo hawaye"to karki kuma bari naga kin ma ta rashin kunya dan ina son matata"kai na kuma kaɗawa ina rushewa da kuka,cikin mamaki ya shiga bina da kallo"me aka miki kuma ki ke kuka haka",ƙara sauti nayi kamar ana cizona,da sauri ya ɗagoni ya ɗora a kan ciyarsa yana tallabo fuskata"me aka miki ki ke kuka",taɓe baki nayi cikin shagwaɓa nace"bakai kaine kace baka sona ba matarka ka ke so",kansa nu na"niɗin nace bana sonki Nana"kaina kaɗa"eh mana gashi nan kana min kashedi akanta ni shike nan baka sona",na ƙara rushewa da ihu saurin rungumeni ya yi"shiiiii ni bance bana sonki ba kece mace ta farko da naso kuma ta ƙarshe ko wacce mace da zata shigo rayuwata sai dai ta zauna a wajen zuciya ta badai a ciki ba",ƙara rungumeshi nayi ƙamƙam na ɗago namai kiss a baki,ƙara rungumeni ya yi ya ɗora bakinsa kan nawa ya shiga tsosarsa kamar sweet ni kuwa ƙara rungumeshi nayi muka kwanta ina kallon ya tabar jikin window nayi murmushi kawai'badai kince da Nana zaki ja ba',irin ta jiya aka maimaita murje ni ya yi tas ƴan breast ɗina sunci ubansu maganina ma kenan,buguzum ta shige ɗaki ta tuge ɗankwalin kanta ta faɗa gado a haukace ta miƙe ta koma gaban mudubi"me kenan Hajara kina nufin zaki barwa ƴar wannan yarinyar mijinki,inaaaa"ta faɗa da ƙarfi tana watsar da kayan kan mudubin wayarta ta wartako ta danna kira wanda ta kira ko magana baiba ta fara aje masa bayani,ashe yayarta ta kira katseta tayi"kinga Hajara ki nutsu zaki iya komai amma ki bari sai kwananta ya fita anan ne zaki gasa tunda dai dole ranar ɗakin ki zai kwana ba saina koya miki komaiba yaushe ne zai koma ɗakinki","jibi ne","yauwa to kibari gobe kin magana bayan sallar magariba",to shike nan tace ta aje wayar ta nemi wuri ta zauna sai asannan zuciyarta ta lafa. Daga ya mutsani nayi bacci shima haka sai la'asar muka tashi,tsiya da taɓara na tashi da ita na hanashi sakat rasa ina zaisa ni ya yi kawai ya ɗaukeni zuwa toilet ya aje ni ya kunnamin ruwa ina gani ya min tas yasa soso yamin wanka ya naɗo ni a towel ya dawo dani ɗaki mai ya shafa min yasa min komai na ciko sannan doguwar riga ta les ya ɗakko min Hijab yasamin"taso muje"ya kamo hannuna nasa takalmi muka fita tana ɗaki batama sa ni ba,bai zame dani ko ina ba sai gidan Ya Ruma,murna da tsalle na shiga yi anan ya barni ya fita,a falonta na kwanta ta shigo da kofi a hannunta na karɓa ƙaremin kallo ta shiga yi"ke Nana me kike ci haka kalli ƙirjinki",a tsorace na tashi ina kallon ƙirjin nawa"me ya sami ƙirjin nawa Ya Ruma",zama tayi tana ƴar dariya"gani nai ba haka ki ke ba amma yanzu naga sun cika"a jiyar zuciya nayi"to Aunty Ruma ba dolensu su fito ba tunda maisu yana buƙatarsu da wuri",baki ta kama tana dariya"au ashe abin na manya ne to bari zan baki wani sirri zaki jure ai ko","sosaima kuwa amma da zaƙi ko","sosaima kuwa Nana ta",yanzu zo muje na koya miki wani abin daɗi,shanye abinda ta bani nayi sannan nabi bayanta naji daɗin kuwa abinda ta koya min sannan ta nuna min abinda tace sai ayan sallar magariba sannan yazo zamu tafi a bayansa na laɓe a bakin get"me ne ne Nana",kasa magana nayi na shiga yarfe hannu kamar wadda aza'a doka"hannun ya riƙe"faɗamin me ki ke so"um um dama"janyo ni ya yi jikinsa"ki nutsu faɗamin me ki ke so","dama dama kuɗi zaka bani zan baya Ya Ruma ta siyo min wani abu",ƴar dariya ya yi ya janyeni a jikinsa ya ciro kuɗi a aljihu ya ciri dubu goma ya bani tsalle nayi na rungumeshi"nagode Darling Yaya",hancina yaja"kai ma ta kizo mu tafi",da gudu na koma nakai manta na dawo muka tafi,matar gidan na zaune a falo ta saki kiɗa sai rawa take muna shiga na fizge hannuna na yadda Hijabin na mara ma ta baya tsayawa tayi tana kallona shima haka da hanzari ya ƙaraso yamin ɗaukar yara ya nufi ɗaki dani na wantsala ƙafa bai aje ni a ko ina ba sai toilet"yi alwala kizo kiyi sallah",daga haka ya fito,ni kuma nayi abinda yace,yana fitowa falon ya kashe kayan kalkon duka ya nunata"bana nason ki ƙara kunna min kiɗa a gidannan na faɗa miki",ya dangwarar da remort ɗin ya juya ya fita hararar bayansa tayi"ƙaryar banza ihu bayan hari wallahi saina kunna ta shige ɗaki,bayan ya idar da sallar isha yaje ya siyamana abinda zamuci iya daren dan ya shigo baiga alamar abinci ba gashi yasan daga sallar isha nake bacci muddin a zaune nake waje ɗaya. wucewa ya yi ya zauna abakin gado"zo nan Nana"jiki sanyaye na tashi naje a ƙasa na zauna na sunkuyar dakaina"gani"na faɗa murya ta na rawa"me yasa ki ke raina Hajara ko na taɓa gaya miki bana sonta ne",kai na kaɗa ina ƙaƙalo hawaye"to karki kuma bari naga kin ma ta rashin kunya dan ina son matata"kai na kuma kaɗawa ina rushewa da kuka,cikin mamaki ya shiga bina da kallo"me aka miki kuma ki ke kuka haka",ƙara sauti nayi kamar ana cizona,da sauri ya ɗagoni ya ɗora a kan ciyarsa yana tallabo fuskata"me aka miki ki ke kuka",taɓe baki nayi cikin shagwaɓa nace"bakai kaine kace baka sona ba matarka ka ke so",kansa nu na"niɗin nace bana sonki Nana"kaina kaɗa"eh mana gashi nan kana min kashedi akanta ni shike nan baka sona",na ƙara rushewa da ihu saurin rungumeni ya yi"shiiiii ni bance bana sonki ba kece mace ta farko da naso kuma ta ƙarshe ko wacce mace da zata shigo rayuwata sai dai ta zauna a wajen zuciya ta badai a ciki ba",ƙara rungumeshi nayi ƙamƙam na ɗago namai kiss a baki,ƙara rungumeni ya yi ya ɗora bakinsa kan nawa ya shiga tsosarsa kamar sweet ni kuwa ƙara rungumeshi nayi muka kwanta ina kallon ya tabar jikin window nayi murmushi kawai'badai kince da Nana zaki ja ba',irin ta jiya aka maimaita murje ni ya yi tas ƴan breast ɗina sunci ubansu maganina ma kenan,buguzum ta shige ɗaki ta tuge ɗankwalin kanta ta faɗa gado a haukace ta miƙe ta koma gaban mudubi"me kenan Hajara kina nufin zaki barwa ƴar wannan yarinyar mijinki,inaaaa"ta faɗa da ƙarfi tana watsar da kayan kan mudubin wayarta ta wartako ta danna kira wanda ta kira ko magana baiba ta fara aje masa bayani,ashe yayarta ta kira katseta tayi"kinga Hajara ki nutsu zaki iya komai amma ki bari sai kwananta ya fita anan ne zaki gasa tunda dai dole ranar ɗakin ki zai kwana ba saina koya miki komaiba yaushe ne zai koma ɗakinki","jibi ne","yauwa to kibari gobe kin magana bayan sallar magariba",to shike nan tace ta aje wayar ta nemi wuri ta zauna sai asannan zuciyarta ta lafa. Daga ya mutsani nayi bacci shima haka sai la'asar muka tashi,tsiya da taɓara na tashi da ita na hanashi sakat rasa ina zaisa ni ya yi kawai ya ɗaukeni zuwa toilet ya aje ni ya kunnamin ruwa ina gani ya min tas yasa soso yamin wanka ya naɗo ni a towel ya dawo dani ɗaki mai ya shafa min yasa min komai na ciko sannan doguwar riga ta les ya ɗakko min Hijab yasamin"taso muje"ya kamo hannuna nasa takalmi muka fita tana ɗaki batama sa ni ba,bai zame dani ko ina ba sai gidan Ya Ruma,murna da tsalle na shiga yi anan ya barni ya fita,a falonta na kwanta ta shigo da kofi a hannunta na karɓa ƙaremin kallo ta shiga yi"ke Nana me kike ci haka kalli ƙirjinki",a tsorace na tashi ina kallon ƙirjin nawa"me ya sami ƙirjin nawa Ya Ruma",zama tayi tana ƴar dariya"gani nai ba haka ki ke ba amma yanzu naga sun cika"a jiyar zuciya nayi"to Aunty Ruma ba dolensu su fito ba tunda maisu yana buƙatarsu da wuri",baki ta kama tana dariya"au ashe abin na manya ne to bari zan baki wani sirri zaki jure ai ko","sosaima kuwa amma da zaƙi ko","sosaima kuwa Nana ta",yanzu zo muje na koya miki wani abin daɗi,shanye abinda ta bani nayi sannan nabi bayanta naji daɗin kuwa abinda ta koya min sannan ta nuna min abinda tace sai ayan sallar magariba sannan yazo zamu tafi a bayansa na laɓe a bakin get"me ne ne Nana",kasa magana nayi na shiga yarfe hannu kamar wadda aza'a doka"hannun ya riƙe"faɗamin me ki ke so"um um dama"janyo ni ya yi jikinsa"ki nutsu faɗamin me ki ke so","dama dama kuɗi zaka bani zan baya Ya Ruma ta siyo min wani abu",ƴar dariya ya yi ya janyeni a jikinsa ya ciro kuɗi a aljihu ya ciri dubu goma ya bani tsalle nayi na rungumeshi"nagode Darling Yaya",hancina yaja"kai ma ta kizo mu tafi",da gudu na koma nakai manta na dawo muka tafi,matar gidan na zaune a falo ta saki kiɗa sai rawa take muna shiga na fizge hannuna na yadda Hijabin na mara ma ta baya tsayawa tayi tana kallona shima haka da hanzari ya ƙaraso yamin ɗaukar yara ya nufi ɗaki dani na wantsala ƙafa bai aje ni a ko ina ba sai toilet"yi alwala kizo kiyi sallah",daga haka ya fito,ni kuma nayi abinda yace,yana fitowa falon ya kashe kayan kalkon duka ya nunata"bana nason ki ƙara kunna min kiɗa a gidannan na faɗa miki",ya dangwarar da remort ɗin ya juya ya fita hararar bayansa tayi"ƙaryar banza ihu bayan hari wallahi saina kunna ta shige ɗaki,bayan ya idar da sallar isha yaje ya siyamana abinda zamuci iya daren dan ya shigo baiga alamar abinci ba gashi yasan daga sallar isha nake bacci muddin a zaune nake waje ɗaya. Washegari da sanyin safiya aka tashi Hajiya Fulera da yaranta ba bu kowa kuma ko tsnke basu ɗauka sai takarda da ta bari Alhaji Baffa ne yace a kira masa shi,wayarsa aka kira ina shafa mai a jikin mirrowa na gani na ɗaga saboda Baffa nagani"Nana kice mijinki yazo ana kiransa","to Baffana",na kashe dai dai yana buɗe ido miƙa ya yi"waye Nana","Baffa ne yace wai kaje yanzu",da hanzari ya sakko ya saka jallabiya na wuf na zira riga da hijabi na bisa dan mu ba'a bamu labari gara mu bayar yana fita yaji ina tsayani mana,hannuna ya kuma muka nufi gidan,duk mutanen jihar suna gidan saboda gulma su Hajiya Harira anyi wuƙi wuƙi ga Hajiya Salma da Safiyya,yana shigowa aka mai caaaa da magana baima gane me kowa ke faɗa ba saida ka bashi takarda sannan Alhaji Baffa yace"karanta kowa yaji",a fili ya fara karantawa. "Barkanku kishiyoyina marasa wayo na tabbatar sanda zakuga saƙona na yi nisa daku nayi tunanin na zauna na ƙwaƙule duk abinda yake hannun ɗan mijina kamar yadda na ƙwaƙule na hannun abokan zamana ko basu faɗa muku ba ni na faɗa muku na ƙwace komai nasu yanzu ziro suke kaima Habib naga wannan yarinyar bazata barka ka tsinanawa kowa komaiba shi yasa ma na barka amma ina nan dawowa kar kayi tunanin har abada na barka su kuma sai kuna tallafa musu da shinkafa da mai amma su da dukiyarsu sunyi bankwana". Ɗagowa ya yi ya kallesu kawai ya yi murmushi ƙala baice musu ba ya juyo ya kama hannuna muka fito a gidan ya yinda suka shiga ihu suna kuka amma bai iya mai iya taimaka musu dan sanda zasu bata ba suyi shawara da kowa ba. UMMU SADDIQ🌹🌹🌹 🌈🌈🌈 🌈🌈 🌈 Babban Yaya Free ne amma me so ya biyo ni Pc in sa a group don shagalin Nana na buƙatar comments. 08146711395 26 Tun a hanya nake ce masa"Babban Yaya wannan matar amma cikakkiyar ƴar duniya ce","wa ya faɗa miki ta gwada musu cikakkun mahaukata ne su"dariya na kwashe da ita"amma wallahi basu da wayo ai ko ni baza'a min wannan wayon ba na yarda","ai ke ki ka ce su kinga ai an musu yanzu sai inga ƙaryar a raba a basu kar na cinye","au haka sukace ma to Allah shi ƙara Allah yasa yanzu tana china",ba shiri ya yi dariya"nifa matsalata dake addu'ar mugunta in tana china yanzu ai su da kuɗinsu sai a ƙiyama","eh hakan nake musu fata mana ni aƙiyamar ma kar abasu suyi ta zama a matsiyata",matse min hannu ya yi"ai yanzun ma suna da kuɗi musamman Salma da Safiyya ɗayar ce dai abin tausayi","kai ka ke tausaya ma ta amma goɗogoɗo da ita ace kawo na aje miki kamar ƴar yaye ta ɗauka ta bada"sakina ya yi yana dariya"Nana anya kuwa ba babbar ƙarama ce ke ba"dariya nayi"ai in hakane kafi kowa sa ni yauwa Babban Yaya please zo muje gida kaga wani abu","to Nana ta muje",Aunty Hajara na ta bacci muka shigo mai aikinta harta gama tana niyar tafiya muka shigo da sauri ta durƙusa" Alhaji ina kwana","lafiya lau zonan uwata",zuwa tayi ta durƙusa"gani","in tambayeki mana","Allah yasa na sa ni Alhaji","ba tun farkon zuwanki gidan nan ba naji kince ansa miki rana amma har yanzu shiru ko lokacin baiba ne",kanta ta sunkuyar"harma ya wuce da wata tara","subahanallahi"nai saurin faɗa"me yasa ke kuwa","Aunty wallahi lokacin da yazo ba bu kuɗin kaya kuma dama ɗan unguwar ne shine aka zigeshi wai ko ya aureni shi zaina ci da gidan mu kuma ya yarda shine yace ya fasa",wani haushi ne ya kamani"kai amma mutane basu da kirki wallahi kiyi haƙuri Allah ya zaɓa miki abinda yafi zama alkhairi","ameen ameen nagode",ɗagowa ya yi ya kalleta"sanda abin ya faru baki faɗawa uwarɗakin naki ba","na faɗa ma ta tace Allah ya kyauta maza ƴan iska ne",runtse idonsa ya yi"kiyi haƙuri kina irin wannan gidan kina aiki amma a kasa taimaka miki lokacin da ki ke cikin matsala ki yafe mana","dan Allah Alhaji ka daina roƙona","dole mu roƙeki muddin baki yafe mana ba sai Allah ya miki sakayya babba akanmu",da sauri tace"na yafe muku

Chapter 15 of 32