Share this page
♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡ "A sabo da me wannan sunan duk wasu abubuwan da suke zuwar min ba'a dedeba suke faruwa dani, farko ya fara ne dasa a min promotion ne daga DSP(deputy Superintendent of Police) zuwa SP(superintendent of police) Don wai a tunaninsu ƙarin girman ze sanya na manta da batun case na green snake, daga baya da suka ga bazan dakata ba se suka sanya a sake cire ni akan matsayi na a bani Acp tare da transfer wurin aiki zuwa nan garin, yau kuma gashi an wa yi gari suna son min wani kyarin girman Hannah, a sabo da naki amsa ne suke nemi dakatar dani, bayan sanyoki cikin maganar da babu ruwan ki a ciki da su kayi, se dai case ɗin yaje inda ake da buƙatarsa, wanda nake da tabbacin ko bayan babu raina seya feɗe hasalin gaskiyar kulla kullar da aka jima aikatawa a wannan ƙasar tamu Hannah, yana da matuƙar gaskiyar da na jima ban gani ba dangane da kowanne ma'aikaci tin daga kamo kan ɗan sanda har zuwa sojo, domin kuwa yana aiki ne da rai da ruyuwarsa kuma alhamdulillahi na samu damar tura masa da komai na wannan case ɗin, don na san tin da suka fara haka ba zasu taɓa barina haka ba domin ankai ma kura a buga game's ɗin, don haka ko babu ni shi ne wanda ze ci gaba da jan ragamar buga wasar, kuma da kansa ze bayyana a lokacin da duk zata bata zata ba........ Tin da ya fara mata bayanin daya kusan gigita duniyarta ta gaza koda kyakkyawan motsi ne,Se ma wani irin gumin da taji yana karya ko mata na tashin hankalin yadda rayuwar duniyar ta koma, Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe tana me furta "I'm sorry A Maleek Wllh ni kaina abin ya gama ɗaure min kai, wllh wasu mutanen sammm ZUCIYAR su bata da imani a ƙaiƙashe take babu ko ɗigon imani..." Tay maganar tuno yadda aka jefo ta cikin lamarin tsumu², da tuno yadda ya bata labarin yadda ake lalata duk wani abin da yake so, ko ya shiga rayuwar sa ciki kuwa harda abinda ya shafi iyaka rayuwar sa wani tagumi ta buga tana jin duniyar baki ɗaya na ƙara sa fice mata a rai. Tare da furta "Gaba ɗaya rayuwar duniya taƙi daɗi. Ni kaina Ina mamakin yanda rayuwar duniya ta koma, komai ya lalace amana tayi ƙaranci, inda kuma wanda ka yarda dashi shi yake ha’intarka, wanda ka aminta dashi shi yake cin amanarka, wanda kaso shi yake cutar ka, mutane da yawa son zuciya ya mamaye su, idanunsu sun rufe kowa burinsa duniya, da yawan mutane sun manta cewa zasu mutu, rayuwa ta sauya, ha’inci, zalumci, da kuma tsananin mugunta sun cike zukatan al’umma, yarda ta kau domin wanda ka yarda dashi shi ne makashinka, wanda kayi believing cewa me ƙaunarka ne shi yake zamowa babban enemy ɗinka. Shin dawaye ne zaka yarda? da waye zakayi abota ko kuwa da waye zaka zauna? Kaicon mutane maciya amana, kaicon mutanen dake neman rugujewarka, aloƙacin da baka damu da tasu rayuwar ba, shin menene ribar mutanen da baka damu da tasu rayuwar ba amma su sun damu da taka rayuwar? idan ka cutar da ɗan uwanka musulmi ko ka kun tata musu menene ribar da zasu samu?, hassada, mugunta da kuma son zuciya? wani kaso zaka samu dan wani ya faɗi? meye kuma jin daɗinka da har kake buri na ganin faɗuwar wani, ba kai keyi ba ALLAH Ne, Numfashin wani ya dameka, ci gaban wani ya tsole idanunka, alkhairan da yake samu ya zamo baƙin cikin ka, duk ata dalilin Meye?. Wanda basu sani ba duk wanda yake ƙyashi da hassadan kada wani yaci gaba, domin ita hassada cutar zuciya ce, tana kuma cinye imani, abunda Allah ya baka shi ne naka, wanda bai baka ba ba na ka bane, ba kuma zai taɓa zamowa naka ba har gaban abada, masu hassada, mugunta, zalunci, da kuma kafurcewa Allah Basa taɓa ci gaba, wannan tabbataccen abune. Tun daga RABBIL IZZATI, tunda daga ZAJJA WA ALLAH. Ubangijii kasa mufi ƙarfin zukatanmu, Allah ka hani zukatanmu daga butulce maka, Allah kaci gaba da tsare mana Imanin'mu, da zukatan mu, albarkacin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Tabbas Amana tayi ƙaranci yarda kuma tayi wahala. Minene yasa zamu ci amanar wanda suka yarda damu ? Minene yasa zamu ƙi yarda da wanda suka yarda damu? Tabbas sir Maleek Duniya tazo ƙarshe..... Tayi maganar ta na me sake shiga mamakin duniyar kanta, jin Maleek ɗin bece komi bane ya sanya Hanna furta "To amma kayi shiru kuma sir?, kuma yanzu ya zamuyi da case ɗin kenan?,duk da kasancewar kace yaje inda ake bukatar yaje ɗin, amma akwai bukatar ƙarin haske dan dai wannan ba abin a gani a ƙyale bane ko ayyi shiru"...... Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da miƙewa tsaye, yana ɗan shawagi a wurin kafin ya ɗan rankwafo da kansa a natse ya furta. " Wani Shirun baya da wata fassara!,kana kuma kintatar shiru abune me matuƙar wahala,wanda yay shiru ba'a san iyaka tsaunin tunani da tanadinsa ba!!!, AA tabbas shi ne wanda zega ƙarshen wasan ba tare da an iya dakatar dashi ba..... Ya bata amsar maganar a baibai ta yanda ita kanta ba zata iya fahimtar komi ba, a cikin rai da tunaninsa yana ayyana tabbas gishiri da sukari kalansu ɗaya yake, wanda se ka kai ga ɗanɗana zaka ji hasalin banbancin dake tsakanin su me tazarar gaske ne..... Kamar yacce wasu mutanen daga nesa suke burgeka, Seka haɗa hulɗa dasu zakayi ladama, sedai shi baya shakka da ladamar akan mutumin da sau da tari da salonsa yake amfani ta hanyar jajircewarsa, da kuma bada rayuwar sa wa ƙasar sa.... Daga nan suka shiga wata tattaunawa tare da zaro wani wrist watch daga aljihunsa yana bata, tare da furta, "A koda yaushe atasayen wasan kan iya fara Hannah, kai tsaye yana ganin duk wani motsin ki da duk mutanen da zasu fara bibiyan rayuwanki muddin agogon na tare take...." Wani saurin kallon sa tayi tana waro manyan idanunta waje tare da kai bakinta setin kunnen sa tana me furta." Kai kace ko wanne motsi na yana iya gani?, ke nan har abinda ya dangata sirrina kamar su wanka haka da sauran izirirrika, duk suma ze iya gani kenan?" ta faɗi har ga ALLAH kuma zuciyar ta ɗaya. Sosai Shima yayi ƙasa da muryarsa yana me furta. "Kaf duniya babu me iya ganin wannan sirrin se ni kaɗai, domin kuwa nawa ne ni ɗaya danni aka halicce shi...." kanta tayi saurin janyewa daga kansa jin ya bata amsar da ba ita ta tambaye shi ba, wani kyakkyawan murmushi yayi yana mikewa tsaye tare da ɗan rankwafowa daidanta yana me furta. Ganan jar alama itace zaka danna a duk sanda kike bakin aikin ki inspector Haanah Mrs Maleek.... " yayi maganan yana sarkin marsk ɗin dake fuskar shi tare da sun glasses nashi ta yacce babu wanda zai iya gane shi, shine dalilin daya sanya shi shirya musu haɗuwar nan. Ta yanda bai son ma kowa yasan da ziyartar nata da yayi. Ta yunƙura da niyar tashi ne kuma ta dakata sakamakon bayyanuwar waɗansu haɗadɗu fitattun manyan motoci guda uku, A babban filin farfajiyar THICKSAKE FACTORY ɗin. suna shigowa a jere, yadda suke a jeren nema kuma ya sanya mafi akasarin mutanen dake wajen meda hankalinsu kan tarin car's ɗin, kowacce motar kuma ɗauke da tint glass a jikinta yadda na waje bai isa ganin na ciki ba. Kafin kiftar idanu duka ƙofofin motocin suka shiga buɗewa ta hagu da dama. Kamar da wasu ƴan second wani ɓakin magidancin ba can ba ya bayyana akan sawayensa. Tin daga yanayin suturan dake jikinsa kaɗai ya isa sanar maka cewar shi ɗin wani ƙusa ne, bare kuma azo kan yanayin yadda tarin escort ɗin dake zagaye dashi. to anan ne kaɗai zaka gane cewan shi ɗin wani ne ta fannin aljihu sannan kuma da alamun sun zarce shekarun samartakarsa. Tunda daga yanayin yadda zaratan soldier's ke kewaye dashi suna sanya shi tsakiyar su. Wanda kai tsaye yake akan ƙafafunsa, wanda ke nuni da rashin sakakkar fuskar sa da take baƙa wuluk, A kallo ɗaya mutum zema matashin magidance ya gane cewar lallai zuciyar sa baƙa ce, tamkar dai yadda yake baƙin nan yawa ɗin ya, A jere kamar masu yin layi haka zaratan soldier's ɗin suka rufa masa baya har zuwa cikin ainihin wurin. Kanta sam sam ba'a wurin yake ba tinda ta mai kallo ɗaya. Bata zata ma se ganin sa tayi tsaye gabanta, samudawansa ko nace ƴan dabarsa zagaye da shi. "Inspector Hannah Ayoub me Kano" yayi maganan yana kaiwa zaune kusanta, wanda zaman nasa yayi daidai da muguwar faɗuwan da gabanta yayi, tabbas idan har kintacenta ya bata gaskiya wannan mutumin ta gani tare da commissioner ranar suna fitowa daga offishin sa a washe garin da yazo, dan haka ma se kawai ta gimtse fuskar ta tana kawar da kanta gefe bayan ta ce dashi. "Kwarai ba saɓanin lamba yallaboi" wani shegen murmushi ya saki wanda ya sanya munun fuakansa bayyanuwa yana me furta. "Da dukkan alamu kema ƴar wasa da rai ce yarinya, amma a takaice ina me baki shawarin ƙara ki koma daga gida kisha baccinki, idan ma ta kama da sutale kayan aikin naki to ki sutule, domin baki san girman irin haɗarin da kike shirin jefa kanki a ciki ba..." se kuma ya ɗan dakata tare da ci gaba da cewa.." Kin kuwa san irin girman haɗarin dake tattare bincike akan Green snake??? " ♡ Wani ɗan iskan kallo ta jefa masa irin na ka kama kan kan nan, ka kuma iya bakinka kafin ta buɗi baki cikin muryanta me amsa amo tana me furta. "Da farko dai kai ɗin wanene? How dare you talk about my life? Kana menene haɗin ka da rayuwana Ms Hannah Ayoub Me Kano?, ka zo se wani famar gindayamin sharruɗa da famar sharhi kake min kan wani banza na da...... " ai tin kafin ta kara sa kaiwa ƙarshen maganar nata yaran da suke tare da shi suka wani yo kanta, kamar irin zasu cinye ta ɗan yar nan, amma ya dakatar dasu ta hanyar ɗaga musu hannu yana wani mirgina kansa gefe. Hanna kuwa cikin wani irin tafasar zuciya ta furta. "idan har hasashe na ya bani daidai kaima ɗaya ne daga cikin su kenan?" babu ko alamar shakku tattare da ita ta furta hakan. "Cikin gaggawa haka ms Hannah Ayoub ?..... Yay maganar da wani murmushin da yafi kama dana mugunta shimfiɗe a saman bakar fuskar sa, wanda ya sanya ta tsare shi da kaifafan tsayayyun idanunta. Shi kuwa ata ɓangarensa yadda ta tsaida fararen idanuwan tan cikin tsaƙiyar nasa idanun ne ya sanya shi janye kallonsa daga gare ta.Wani irin kwarjininta me tarin yawa na bebayeshi karon farko kenan da wata ƴa mace ta mashi kwarjini irin haka. Duk kuwa tsawon rayuwar wa da yawon duniyar sa, inda ya saba hulɗa da manyan matan da suka ninka ta ninkin ba ninkin, amma wata bata taɓa masa kwarjini irin haka ba kai harma da namiji se wani shegen soldier ɗin da ya taɓa masa ƙamshin mutuwa... Tsammm ya miƙe tsaye yana me mata wata alama da hannunsa kafin kuma a fusge ya furta "abin burgewa kwarai kin birgeni, kamar yadda zafin kanki yasa zanyi wannan wasar dake, Kafin sannan kuma Kin yi min kuma, dan haka kada ki manta zan dawo na kwamisheƙi...... Se kuma ya ɗan dakata tare duƙo da kansa sosai yana me sake furta.*"CHAKO MAYIK CHAKO" *daga haka suka ɓace daga wurin suna ficewa a T.... F ɗin baki ɗaya ma, wanda dama da alama shi ne abin da ya kawo su kenan. Yana barin wurin. Mayik haka tayi ta nanata sunar a cikin brain nata, tana kasa samun amsa ko ma'anar hakan..... ♡ *In the night* Bayan mun kammala dinner na dare tare da firan da mukan taɓa time to time dasu Abbu tare da ammey, ta shige ɗakinta wani bin ma harda ya Aliey ake zaman firan. Ina shiga ɗakina wuta na kunna na shiga zare kayan jikina ɗaya bayan ɗaya, towel na zara na ɗaura a jikina na faɗa toilet ɗin dake manne da jikin ɗakina. Domin bana iya bacci se jini on top fresh up a cikin ruwa, Cikin bathtub na shige na zauna bayan na tara ruwa mai ɗumi, ban jima a ciki ba na fito. A cikin toilet nayi kimtse ² da zanyi, kana na fito zuwa bedroom ɗin. Kayan barci na saka marasa nauyi, ka yana dana bari a tsakar ɗaki na tsince na watsa cikin kwandon da nake tara kayan datti don nasan idan na bari Ammey ta gani gobe kashina ya bushe. Domin Ammeyna mace ce mai tsabta da bata jurar kowacce irin ƙazanta ko ta anini ce kuwa. Saman lafiyayyen haɗaɗɗen gado na nayi tsalle na haye kamar wata karamar yarinya, waya na na zare daga jikin socket na kunna data, social media na shiga na fara chat da friends nawa don rage tunani da damuwa. Sosai kuwa na rage kewan da damuwan da kusan a yanzu da shi nake rayuwa cikin yan sati kan da basu wuce uku zuwa biyu ba. Sosai muka sha cafta a group na class room namu. Inda daga nan wajajen goma sha ɗaya na fita daga cikin group ɗin ina musu seda safe, daga nan kamar wacce ake jana zuwa ga kallar status na mutane da ya zame min ɗabi'a, Da na ƙawata Najma na fara cin karo, inda ta sanya pisc na dariya tare da rubuta, _idan kinsan kina rushing samrayinki inga naki? _ ta rubuta tare da emog na dariya, na biyun kuma ta rubuta. _Wasu mutanen fa basa gane ihu bayan hari su ke yi akan abinda yake ba mallakinsu ba, Se daga baya idan ƙura ta tashi kaji ana buy bla bla, labarai nata tashi anyi snatching samrayinsu oh yayane_ nikam daga haka dana ga yau kamar rashin hankali take ji dashi sena wuce ta ba tare dana sake bin ta kan status nata ba. Haka nayi ta kallar status na mutane har na tsallako kan *Special cutie* Yaya Aliyu kenan. _Wasu labaran ba namu bane, kamar yacce take iya Iyuwa wata rayuwar ba tamu bace_ to na sake furta wa a raina wato yau status ɗin bad ne kenan, babu nishaɗantarwa kamar kullum. Don haka se nayi ta gaba. _Me wannan duniyar take nufi da rayuwa, me wannan rayuwar kuma take nufi damu?_ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ Shi ban fita a nashin ba kamar sauran, har sai da na kai ƙarshen rubutun inda yafi kowanne ɗaukar hankalina ma, _Wata Rayuwar tafi ƙarfi ko kwatancen a ƙirata da sunan Duhu, wataƙil babu mamaki Shi duhun ne ke dukan duhu a ƙarƙashin kowacce rayuwa... _ sosai naji zuciya tayimin nauyi akan waɗan nan kalmomin, Se dai bana da amsar kowacce daga cikin su, don haka na fita a WhatsApp ɗin ba baki ɗaya da niyar in kashe data na, naga wani messages ya faɗo, yi nayi kamar in share amma kuma se zuciyana taƙi aminta da hakan. _Me kika tsaya yi da har zuwa wannan lokacin baki bacci ba? _ shi ne saƙon da Ya Aliey ya tura min. Rasa ma me zance mishi nayi, don haka se kawai na runuta masa cewan. _Wani assignment na tsaya yi ne lolly Amma plsss _ ko kifta ido ban kai ga yiba ya rubuta _Sauƙa yanzun_ Ko amsa ban bashi ba kuwa na kashe data ne tare da kashe wayan ma baki ɗaya. Ko washe garin ranar ma gaba ɗaya a gajiya na tashi, tunda na tashi naji jina cikin rashin sukuni da rashin cikakken kuzari, bayi kawai na faɗa nayo wanka tare da nufar gaban dressing mirror ɗin dake dakina,tare da jan kujera ina zama tare da kallon fuskata ta cikin mirror ɗin, gaba ɗaya sake jin raina da Jikina nakeyi babu daɗi ko kaɗan,fuskar sa ne kawai ke gilma min ta cikin idanuwana,cikin karaya da saddaƙarwa tare da rauni me matuƙar girman da nake ji cikin gangar jikina da zuciya ta, a ɗan kasalance na miƙe ina nufar closet nawa, sanye na fito cikin wata armless chiffon gown,yatsun hannuna da suka sha jan lalle iyaka yatsun hannuna se kyalli ta ke yi. Kai tsaye directly ɗakin Ammey na nufa tare da mata knocking na shiga, tana zaune a gefen gado da dan littafin hisnul Muslim a hannun ta. Kai duban ta takai a kaina tare da furta "Idan kin kammala breakfast naki Ki miƙama yayanki nashi abincin yana garden" rass naji gabana ya faɗi kasancewar kuma dama weekend ce yau ɗin. A natse na miƙe na fita ina zuwa dining room ɗin, Seda na zauna na ɗan tsakuri kaɗan naci kana na miƙe da basket dinner na Lolly. Kai tsaye ina nufar room na shi, baya falonsa don haka kai tsaye na nufa Gym nashi. Nan ma baya nan kuma dai na san a irin haka baya bedroom nashi, _garden_ haka naji zuciya ta ta raya min yana can. Don haka na nufi garden ɗin. Babban garden ne mai cike da ababen kallo da ni'imtattun korayen ciyayi da ƙawatatun filawoyi. garden ne me wani irin tsari da girma daidai da rayuwa da kuma abinda rayuwar zata buƙata wajen kwantar da hankali da kuma sanya nishaɗi a wasu zukatan, a rayuwa ba abinda nafi buƙata irin kasancewa a wannan garden se dai ni kaina na kan iya ɗibar watanni van ko iya leƙa shi ba, kasancewarsa ba na kowa ba se mamallakinsa mutum ɗaya, idan nace zan tsaya lissafa muku irin haɗu wa da ƙawatuwar dake cikin sa ma ɓata lokaci ne kawai me zaman kansa. A zaune na tarar dashi ya ma duk wanda ze shigo baya. yana Sanye cikin ƙananun kaya farare tas da suka fidda ainahin suffarsa ta masu ta'amalli da ƙarafuna, gashi sun sake fidda ainahin hasken fatarsa da sheƙinta irin na asalin larabawan nan domin dasu yake kama. Laptop ce gabansa yana gudanar da aikinsa ciki kwanciyar hankali. Babu zata haka naji sauƙar muryarsa a tsakar kaina. "Mi kake buƙata?" Kai tsaye tambayar daya fara cillo min kenan,wanda ya sanya ƙirjina sake harbawa a karo na ba adadi har ina jin tamkar ƙirjina se faso rufin fata bakwai ɗin dake cikin ta ta fito. Bana da niyyar cewa komai, bayan kuma alhalin gani tsaye gabansa tamkar an dasani haka naji na gagara ko ɗaga kai in kalle sa, Jin shiru ba amsa ne ya sa shi sake furta "Out" ba tare daya ɗago ɗin ba sema ci gaba da aikinsa da yay. Ba tare dana ankare ba harya mike tsaye dai-dai da isowar wani nutsatstsen taku mai tafiya da sassanyan ƙamshin turarensa, tamkar shi kaɗai iska ke tsintowa tana busawa a ƙofofin hancina. ƙirjinane yay wata irin harbawa lokacin da naji sauƙar kaifafan idon sa cikin tsakkiyar nawa tsumu tsumu, wanda suke cike da Ƴar fusata da kuma ɓacin ran da bansan ko na miye ba. Da ƙyar na iya fisgar nawan daga cikin nasa ɗinta cike da dakiya. Shi kuwa a nasa ɓangaren Idanuwansan ya sake zuba mata yana mata kallon gaskiya da gaskiya na abinda yakeji a zuciyar sa, Yana rasa ko menene yake Jin ɗin akanta, Haka za lika ba tare da ya san menene suna ko ma'anar abinda yake ji cak a tsakiyan zuciyarsa game da ita da duk abinda ya shafe ta ba. Cikin sanyi da kasalan idanuwansa a kaina na ɗago nawa idanuwan ina sauƙesu a kansa, Daman kamar abinda yake jira kenan ko zai samu sassaucin abinda ya tsaya tsakiyar zuciya nesa, Se dai amma still kallan nata kaman sake nauyin koma Menene yayi. Wanda se a lokacin Idanuwansan suka sauƙa akan basket ɗin dake riƙe a hannuna, cikin yanayin da bazan iya fahimta ya min nuni dana ajje na fita kawai. Don haka na ajje a natse cike da bugun zuciya ina saurin juya baya tare da barin wurin. Kollon yadda take tafiyar tamkar wata ƴar sarki ne ya sanya shin bin bayan nata da kallo kawai... Ni kuwa ina samu na fita a garden na sauƙe wani hawaltaccen numfashi, kai tsaye Reemah Classmate nawa na ƙira akan ta shirya gani nan zanzo muje saloon ɗin, kamar yanda muka yi zancen da ita jiya, daga nan kuma se mu wuce shan ice cream tare da yayanta Ayaan kamar yanda ya mana alƙawari. Duk ma sena tsinta kaina a cikin rashin jin wargi ko dan Najma kuma bata nan ne mebi, don nafi sake wa da ita cikin kafff ƙawayenmu na BUK Wuse zone. Sallama kawai nama ammey zuwa saloon ɗin kasancewar yau bana da paratical a asibitin da nake tifin.(I'm so sorry a fage na baya na saka Nufaisa cikakkiyar dactor, na ɗan yi mantuwa ne tana dai dab da zama tifin take yi a wani babban asibiti) first da saloon ɗin muka fara wanda da iyaka wanke min kan za a yi, amma kawai se nace amin kitso daga baya. Hakan kuwa aka yi sedai ba wasu masu hayaniya aka min ba, Daga nan ne kamar yadda Ayaan ɗin ya mana alkawarin zuwa shan ice cream ɗin muka je kuwa, da chicken republic muka fara zuwa ya sai mana gashin kaji, daga nan muka tsaya a freeze center ɗin ya sai mana ice cream da tarkacen snacks kana muka koma gida. Se dai ban biya ta gidansu ba na wuce gida. Kasancewar yamma tayi sosai zuwa lokacin, Se dai me ina shiga cikin gidan naji na rasa duk wannan nishaɗin dana sama a waje, Kaina na kifa saman starring na motana, a cikin rai da ruhina nake furta. _Wai shin me ke damun kaina da rayuwa ta ne? Me yasa nake jin abinda na san har gaban abada hakan bamai iwuwa bane, kuma wanda na san har gaban abadar bazai taɓa iwuwarba? Me yasa zuciyata zata dinga jefa ni cikin damuwa ne a koda yaushe? Shin menene yasa nake jin duk ire iren waɗan abubuwan ba a kan kowa ba se iyaka kan shi? Me zan fito in gayawa duniya? Ince musu son yayana nake wanda muka fito ciki ɗaya dashi ko kuwa yaya?, Shin Anya kuwa Duniya ba zata zage ni ba kuwa?_ Ban san tsayin wanne lokaci na ɗauka

Chapter 10 of 23